x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 2 - ABOKAN GABA

  • 3001 words
  • 6000 words
  • Out of 11905 words

Category: Adventure Stories

Views 44

09 Aug 2025
Start ads
After Image Ads
kaga matattu suna
zubowa qasa a haka ya ci gaba da yaqarsu suma
suna qara danno shi. Haka suka xauki tsawon
kwanaki biyu suna wannan gwagwarmaya shi bai
saduda ya gaji ba suma ba su qare ba, yaqi ya ci
gaba da gudana mutuwa ta ci gaba da shawagi tana
xauke rayukansu. Can bayan tsawon lokaci a
lokacin gajiya ta soma kama Farsu ya soma sauya
salon yaqin a zuciyarshi yana mai tunanin abinda
ya kamata ya yi a lokacin ne bai yi aune ba wata
qara gami da walqiya ta cika cikin fadar, sannan
lokaci xaya wani baqin aljani mai girman gami da
mummunar siffa ya bayyana da ganinsa sai duk
rundunar aljanun suka tunzura suka razana suka
zubar da makamansu suka ruga a guje. Ya juya ya
dubi Farsu ba tare daya ce masa komai ba ya miqa
hannu xaya ya damqoshi ya buxe fuka-fukanshi ya
tashi sama da shi suka fice daga cikin fadar sarkin
aljanu Gamsu.

Farsu ya leqo qasa da idanunshi ya dubi
gawarwakin aljanun da suke kwance fululu.
**
A hankali Gimbiya Lusa ta saka
hannu ta xauko jakarta ta buxeta ta xauko wani
garin magani ta buxe bakinta ta zazzagashi tana
gama haxiye maganin take taji qarfi a jikinta,
lokaci guda ta yi murmushi ta yunqura ta tashi ta
dubi aljanin daya xaukota cikin murya qasa-qasa
tace masa.
“Waye ya aiko ka ka tafi da ni?”
aljanin ya ci gaba da karkaxa fuka-fukanshi
sannan ya bata amsa da cewar “Ni bawan
mahaifinki ne sarkin aljanu Gamsu, a yanzu na
baro wani bil’adama yana yaqar jama’armu bayan
ya sace ruhin mahaifinki” Wannan maganar ta zo
wa Gimbiya Luna a bazata, tun data samu wannan
labarin ta fita take yaqar duk wani sadauki da take
tsammanin zai iya zuwa ya sace ruhin mahaifinta
amman ashe qaddara ta riga fata, bata san lokacin
data kwarara wani irin ihu ba, take idanunta suka
kaxa suka yi ja, saboda tsananin fusata cikin
damuwa tace wa aljanin.
‘Qara gaggawa domin mu samu mu
qarasa gareshi domin na yi gagawar sadashi da

ajalinsa” Aljanin ya qara qarfin karkaxa
fuka-fukansa suka tunkari fadar sarkin aljanu
Gamsu. A lokacin da rana ta kusa faxuwa Suka
qaraso fadar tun daga nesa Gimbiya Lusa ta riqa
hango gawarwakin aljanu a kwankwance bila
adadi, suka qaraso cikin fadar Gimbiya Lusa ta
dubi gawarwakin aljanun dake kwance a cikin jini
wani baqin ciki ya lulluve mata rai.
Wannan shi ne karon farko da wani ya
tava shigowa cikin fadar sarkin aljanu Gamsu ya
yi nasara ga rundunarshi.
Ta mayar da dubanta ga karagar sarkin
aljanu Gamsu, ta gano gangar jikinshi a zaune a
kan karagar babu ruhi a jikinsa, da gudu ta nufi
wajen da yake taje gabansa ta tsaya tana kallonshi
hawaye yana kwaranya daga cikin idanunta.
Takaici da baqin ciki ya cika mata cikin zuciyarta,
hawayen ta ya ci gaba da kwaranya daga cikin
idanunta, ta ci gaba da kallon gangar jikin sarkin
aljanu Gamsu.
A rayuwarta ta duniya babu wani
mahaluki da taji tana matuqar qaunarsa kamar
mahaifinta sarkin aljanu Gamsu ta yi matuqar
mamaki yadda ta shaqu da shi kamar yadda
mafiya yawan lokuta take matuqar mamakin

yadda kamanin halitarsu suka bambanta, sau tari
tana iya lokutan da take kallon surata a jikin
madubi, sannan ta dubi ta kuyanginta ‘yan matan
aljanu sai taga akwai matuqar bambanci sosai da
su, domin ita tsarin jikinta jiki ne mai santsi babu
gashi sai farar fatarta da take faman sheqi da
xaukar idanuwa. Qafafunta suna tattare da ‘yan
yatsu su kuma dukansu suna da kofato tamkar na
dawakai, tsarin surasu bai yi kama ba sam.
Sau tari idan sun so sukan sauya kamanin
halittarsu daga kyawawa zuwa munana, amma ita
bata iya sauya kamani kamar yadda suke sauyawa.
A lokacin tana da quruciya ta sha tambayar
mahaifinta sarki aljanu Gamsu ko mai yasa
kamaninta suka bambanta da na su kamanin? Mafi
yawan lokuta yakan dubeta sannan yace mata.
“Akwai lokacin da za ki gamu da wasu
halita waxanda zubin halitarku iri xaya ne”
Wannan maganar ya tabbatarwa Gimbiya Lusa
bambanci da take gani a bayyane yake. Lokacin
farko data soma shigowa cikin bil’adama data ga
jinsi mai irin nata sai mamaki ya cikata, ta kuma
haqiqance a cikin ranta wannan zubin halitar sune
jinsinta sune ‘yan uwanta amma da yake ba
buqatar sanin asalinta da halittarta ne ya fito da ita

ba don haka bata mayar da hankali kan haka ba. A
lokacin ta fito ne domin nemo sadaukin da aka
bata labarin zai zo ya sace ruhin mahaifinta.
Duk data samu nasara kashe sadaukai,
amman nasara bata yi mata amfani ba, ta gama
farauce rayukan jaruman wanda suka yi suna suka
sami xaukaka a duniya amma wani baqar fata
wanda ba a saka shi a cikin lisaffin jaruman
duniya ya zo ya sace ruhin.
Wannan shi ne anyi ba a yi ba! Ta rufe
qofa da varawo.
Duk abubuwan da suke ta faman zuwar
wa Gimbiya Lusa a rai, suka gama zuwar mata, ta
dubi makamanta da kayan yaqinta bata buqatar
sauya wasu ta mayar da dubanta ga sarkin aljanu
Gamsu da yake zaune babu ruhi a jikinsa taji
damuwarta ta qaru da fusatar zuciya tace “Halaka
ta tabbata a gareka maqasqancin bawa, tabbas gani
nan zuwa gareka domin farauce ranka” Da xaga
murya tace, a lokaci xaya ta dubi aljanin daya
xakota tace masa/
“Ka xaukeni bisa gaggawa ka kani domin
riskar ABOKIN GABA domin mu yi GABA DA
GABA da shi” Tana gama maganarta tayi tsalle ta

haye bayansa shi kuma aljanin ya buxe
fuka-fukansa ya tashi da ita sararin samaniya.
Gimbiya Lusa ta jiyo ta dubi gangar jikin
sarki Gamsu lokaci xaya tana jin hawaye suna
kwaranyo mata, a hankali ta kai hannunta ta shafi
takobinta.
‘Zan ladaftar da kai BAQAR FATA’ tace
a ranta.
SADAUKI ANSAR
Yana kwance cikin tagaiyara da fidda rai
daga tsammanin ci gaba da rayuwa, domin irin
raunikan da suke jikinsa. Lokaci zuwa lokaci ya
kan xan tuna cewar wannan shi ne yaqi xaya a
duniya da suka tava kare jini-biri-biri-jini da
abokin gabarshi. A irin jarumtar da yake da ita
babu wani sadauki da ya tava xaukar sa’a xaya a
gabanshi ba tare da ya farauce ranshi ba. Amman
sai gashi mace ta wanzu tsawon wasu lokuta a
gabanshi suna xauki ba daxi.
Wannan abun mamaki ne ga sadauki mai
sadaukantaka kamar Ansar wannan baqon abu ne a
gareshi da bai tava tsammanin faruwarshi ba.
A hankali ya xaga idanunshi ya dubi
ungulayen da suke ta faman shawagi a sararin
samaniya suna jiran ya hallaka domin su samu

suyi kalaci da namanshi. A hankali ya buxe
bakinshi ya soma faxin “Allah kai ne ubangiji
xaya wanda ya halicci komai, kai muke bautawa,
Allah kar ka wulaqanta gangar jikina na zamto na
hallaka na zamto abincin ungulaye, Allah ka
suturta gangar jikina”.
Ya gama addu’ar tashi yana mai lumshe
idanunshi a lokacin ya ji saukar wani abu a kusa
da shi ya yi saurin buxe idanunshi ya dubi abinda
ya sauka a kusa da shi. Wani farin aljani ne mai
kyawun siffa daga cikin jinsi aljanu dudud
shekarunsa ba za su gaza xari uku zuwa huxu ba,
wannan aljanin ya zamto mai ganiyar quruciya a
jikin shi kuma mai ji da sadaukantaka.
Yana sauka ya dubi sadauki Ansar yace
masa “Ungulaye ba za su ci gangar jikinka ba
domin ranar mutuwarka ba yi ba” Yana gama
faxar hakan ya yi gaggawar xauko wata buta ya
zubawa sadauki Ansar wani ruwan da yake cikin
butar a gangar jikinsa nan da nan sadauki Ansar ya
soma jin qarfin jikinshi ya soma dawowa jikinshi.
Bayan wucewar awanni uku sadauki
Ansar ya ji duk wata gajiya da wajen da yake masa
ciwo ya daina, ya zamto tamkar wani abu bai tava

samunshi ba, ya dubi farin aljaninan da duban
girmamawa sannan a hankali yace masa.
“Godiya gareka da ka zamto ka
taimakaeni ka kuvutar da rayuwata” Sadaukin
Ansar yace masa. Shi kuma ya dubi Ansar a
hankali yace masa “Sunana aljani zammaru na
zamto xaya daga cikin ‘yan qabilar bamu shammat,
kuma na zamto daga cikin jinsi aljanu mabiya
addinin musulunci na zo ne domin na taimakeka
na kuvutar da kai daga halaka, domin duniya tana
buqatarka idan ka halaka za a rasa jarumin da zai
sasanta rigimar da zata mamaye duka duniya ta
sace ruhin sarkin aljanu gamsu” Sadauki Ansar ya
dubi Aljani zammaru da matuqar mamaki sannan
yace masa.
“Ta ya zan sasanta rigimar da dominta
aka so hallakani? Ni musulmine babu ruwana da
abinda ya shafi kafirai” Ya tabbatar masa.
Aljani zammaru ya yi murmushi sannan
yace “Akwai matsala babba tun da aka sato ruhin
sarki aljanu Gamsu matsalar ita ce sarkin aljanu
Gamsu ya zamto adalin sarki mai taimakon
talakawa mai kare addinin musulman aljanu duk
da cewar ya zamto shi ba ma’abocin musulunci
bane, hakan yasa a lokacin da aka sace ruhin na

shi duk wani musulmin aljani ya shiga cikin
fargaba da tsoro domin sun san za su soma samun
tursasawa daga sauran azzaluman sarakunan aljanu,
shi yasa na zo gareka domin neman ka taimaki
musulmai ‘yan uwanka a sassanta a dawowa da
adalin sarki ruhinsa ko ma ci gaba da ibada a cikin
kwanciyar hankali ba tare da zullumi ba”.
Sadauki Anwar ya yi shiru na tsawon
wani lokaci yana tunani daga bisani ya xago da
kanshi ya dubi aljani zammaru yace masa.
“Na yadda zan nemo wannan ruhin duk
inda yake domin mayarwa da sarkin aljanu Gamsu
koda hakan yana nufin sai an gabza yaqi, da izinin
Allah nasara tana gareni” Ya kammala maganar
yana dubansa kafin ya qara da cewar “Yanzu ina
za mu riski wanda ya sace wannan ruhin?” Aljani
zammaruu ya dube shi sannan ya bashi amsa da
cewar.
“Wata bokanya ce baqar fata, ta saka
wani hatsabibin bawanta shima baqar fata ya sato
wannan ruhin, domin haka za mu iya riskarsa a
hanya kafin ya qarasa zuwa gareta” Sadauki Ansar
ya girgiza kanshi cikin gamsuwa sannan yace wa
aljani zammaru “Za mu iya yin gaggawa domin
zuwa riskarsa” Yana gama maganar ya yi tsalle ya

haye bayan aljani zammaru lokaci xaya shima ya
buxe fuka-fukanshi ya tashi da shi sararin
samaniya.
Suka bi bayan baqar fata bawa Farsu
daya sace ruhin sarkin aljanu Gamsu.
BAQAR FATA BAWA FARSU
Yana zaune a bayan aljani a ranshi yana
jinjina irin girman siffa da muni da wannan aljanin
yake da shi. Suka zo tsakiyar wani teku mai girma
da faxi, tun da farsu yake a rayuwarsa bai tava
ganin teku mai girma tamkar wannan ba. A
hankali ya leqo da kanshi yana kallon ruwan tekun
yana cike da al’ajabi.
A dai-dai lokacin da suka zo dai-dai
tsakiyar tekun a lokacin tamkar walqiya su
Gimbiya Lusa suka bayyana a gabansu.
Aljanin da yake xauke da Farsu ya dakata
da tafiya da yake yi cike da tsoro da fargaba.
Ganin ya dakata yasa Farsu ya dawo da hankalinsa
gabansa idanunsa suka gane masa su ya girgiza
kansa cike da jimami. A hankali su Gimbiya Lusa
suka matso daf da juna ta miqe tsaye daga kan
aljanin da take kai, tana zuwa dai-dai inda aljanin

da Farsu uake kai ta daka wani tsalle ta dawo
kanshi.
Farsu ya yi gaggawar miqewa domin
ganin ganin abinda ya faru, suka tsaya suna
kallon-kallo da shi da Gimbiya Lusa. Cikin
tsananin hasala tace masa.
“Na zo domin amsar ruhin mahaifina
sarkin aljanu Gamsu wanda ka sace” farsu ya
dubeta a fusace shima yace mata “Amman kin
yaudari kanki ‘yar budurwa da kike kiran aljani
mahaifinki, kin tava ganin aljani ya haifi mutum?
Sannan saboda tsananin ganganci shi ne za ki
sadaukar da rayuwarki domin ki halaka kika
biyoni domin amsar ruhin” Ya saurara kafin ya
qara da cewar.
“Yar kyakkyawar budurwa duk kyawun
surarki hakan ba zai hanani saka takobi na a
tsakiyar siririn wuyanki na raba kanki da
kyakkyawan gangar jikinki” Ya gama magana
yana mata wani shu’umin murmushi.
“Kai baqar fata gafalalle kayi sani cewar
ni ce Gimbiya Lusa mai maganin duk wani xan
iska! Dan haka ka bani ruhin da ka sato cikin
ruwan sanyi ya fiye maka kafin wannan
mummunar baqar fuskar taka ta gamu da azabar

kaifin takobina wacce bata san komai ba sai shan
jinin sadaukai ma su ji da jarumtaka da taurin kai”
Cikin murya tsawa-tsawa tace masa.
Farsu ya dubeta a fusace cikin daka tsawa
yace da ita “Ahir! Xinki da dubana ki gayamun
irin waxannan kalaman bana tunanin akwai wani
jarumi da zai iya tsoratani da jarumtakarsa ko
kalamansa na kurari na baki, balle ke mace mai
raunin jarumtaka” Gimbiya Lusa ta girgiza kanta
cikin tsananin takaici ta sassauta murya tamkar
mai yi masa raxa tace da shi cikin fushi.
“Ka yaudari kanka da har kake tunanin
gwara na amshi ruhin da tsananin jarumtaka, a
yanzu ne za ka san cewar ka yi gagarumin kuskure
kuma zaka rabe tsakanin aya da tsakuwa, domin
yanzu zan farauce ranka na kuma cilla wannan
mummunar gawar taka cikin teku” Tana gama
faxa masa ta zare takobinta lokaci xaya ta dubeshi
tace “Yau zamu yi gaba da gaba da kai domin
sanin bambanci a bayyane yake”. Ta sake yin
murmushi.
“Ni da kai ABOKAN GABA ne, don
haka mu kan iya soma farautar rayukan junanmu”
Tana gama maganar ta kai masa wani wawan sara
da zumar tsinke zaren da yake sarqe da ruhin cikin

zafin nama ya kaucewa saran sannan ya wuce tare
da wani hucin iska mai qarfi.
Farsu ya dubeta ya girgiza kanshi, sannan
ya gyara riqon takobinsa. Suka yi xauki kan
junansu lokaci xaya suka gauraya da mummunan
artabu a wuri xaya suna musayar kai sara da
suka.qara gami da tartsatsin haxuwar makamansu
ya karaxe sararin saman tekun. Ko wannensu ya
himmatu domin ganin ya samu nasara akan abokin
gabansa. Gimbiya Lusa ta samu Farus ba yanda ta
yi tsamaninsa ba, domin ta same shi dakakken
namiji mai tsananin jarumtaka, turjiya gami da
zafin nama. Haka shima Farsu ya sami Gimbiya
Lusa cikakiyar jaruma mai qarfin damtse da zafin
nama wajen kai sara da kare kanta. Jarumar da tafi
jarumai da dama qwarewa da sanin salo-salo na
yaqi.
Haka suka ci gaba da mummunan
gwamza yaqi mai tsananin ban mamaki a
tsakaninsu, suka wanzu wajen kaiwa junansu
miyagun sara da suka da niyar farauce ran juna.
Bayan sun xaki dogon lokaci suna wannan
fafatawar a lokacin wani abu ya sauka a
tsakaninsu.

Jin saukar abin shi ne ya tilasta musu
dakatawa da yin yaqin su duka suka dubi abun. A
lokacin idanun Farsu ya sauka akan Bokanya
Namsu uwar gidanshi da ta saka shi aikin idan ya
sami nasara zata ‘yanta shi. Ganinta ya saka ya ji
wani daxi ya lulluve shi. Bokanya Namsu tace
masa cikin sassauta murya.
“Maza miqo mun ruhin naga ko wannan
qaramar qwaruwar zata iya amsa a wajena, kai
yanzu ka kammala aikinka ka gama yi mun bauta
don haka na ‘yanta ka” Waxannan kalaman sun
matuqar qayatar da zuciyar Farsu. Don haka cikin
gaggawa ya miqa hannu ya xauko ruhin daga cikin
inda ya adana shi ya dubi Bokanya Namsu itama
ta dubi Ruhin.
Gambiya Lusa ta dubi ruhin mahaifinta
sarkin Aljanu Gamsu. Ba su yi aune ba sai jin dirar
wani abu suka kuma ji Yif! Kamar an sauke
nannauyan dutse cikin gaggawa suka kai kallonsu
idanun Farsu ya kuma ganin wata Bokanya Namsu
a tsaye ya dubeta cikin tsananin mamaki yanzu sun
zama su biyu ma su kama iri xaya sak kamar an
tsaga kara.

“Wace ce kenan ta gaskiyar?” Ya
tambayi kansa kamar amsar tambayarsa ya ji ance
masa.
“Ni ce uwar gidanka Bokanya Namsu”
Da kakkausar murya tace masa.
Xayar itama ta matso gareshi tace masa
“Ni ce uwar gidanka Bokanya Namsu”.
Farsu ya zuba musu idanu yana kallonsu
cikin ruxani ya kasa tantance wace ce ta gaskiyar
wace ce ta qarya.
A lokacin aljani Zammnaru ya qaraso
shima xauke da sadauki Ansar a bayansa shima ya
bi ruhin da kallo ya mayar da kallonsa ga Gimbiya
Lusa sanna ya haske mata fuska da murmushi
lokaci guda kuma cikin tsananin zafin nama ya
zare takobi ya kaiwa farsu sara a hannun da yake
xauke da Ruhin sarkin Aljanu Gamsu take ruhin
ya zame daga hannunsa ya yi qasan teku.
Farsu ya juya ya dube shi ya kuma dubi
Gimbiya Lusa yace mata “To kyakkyawa ruhin
mahaifinki ya faxa cikin teku, ko za ki biyoni
cikin tekun mu ci gaba da fafatawa” Yana gama
maganar ya sulmiyo daga kan aljanin ya biyo
ruhin daya sulmiyo qasan teku.

Gimbiya Lusa ta girgiza kanta tunda take
a rayuwarta ba ta tava ganin hatsabibin mutum
kamar wannan baqar fatar ba. Itama ta daka tsalle
ta biyo bayanshi.
Ganin haka ne ya sa sadauki Ansar shima
ya sulmiyo ya yo qasa shima ya biyo bayan Ruhin
sarkin Aljanu Gamsu da ya yo qasan taiku.
A cikin tekun sarauniyar aljanun cikin
ruwa ta tara mayaqanta suna tsaye suna sauraren
qarasowar ruhin sarkin aljanu Gamsu. Tun kamin
shekaru xari uku Bokanta ya faxa mata cewar
Ruhin zai faxo a nan wurin tun lokacin ta zauna
zaman jiran faxowarsa.
Ruhin ya faxa cikin ruwan tekun ya
zamto tamkar an cilla wani nannauyan dutse mai
nauyi lokaci xaya ya yi qasan teku. Sarauniyar
aljanun cikin ruwa tana zaune akan karagarta tana
jiran faxowar ruhin. Tsayin shekara xari uku
kenan tana zaune zaman jiran faxowarsa. A
lokacin da bata yi aune ba taji faxowar abu akanta
tayi gagawar buxe idanunta ta dubi abin da
idanunta suka gane mata abinda ta jima tana zaune
zaman jira tsawon shekaru, tabbas Ruhin sarkin
aljanu Gamsu ne wani daxi ya mamaye cikin

zuciyarta da gaggawa ta miqe cikin azama ta miqa
hannunta ta xauki ruhin ta zuba masa idanu tana
kallonsa.
Ta juya cikin gaggawa ta xagashi sama a
gaban idanun jama’arta cikin xaga murya tace
musu “Abinda muka jima muna zaman jiran shi
yau mun same shi” Duka hankalin dakarun ya
tattara akanta suka zuba mata idanuwa suna kallon
ruhin sarkin aljanu Gamsu da yake riqe a hannunta
sannan lokaci xaya suka ruxe da shewa da
kururuwa suna ma su xaga makamansu sama.
A lokacin Bawa Farsu ya faxo tsakiyar
wurin ya miqe tsaye da matuwar mamaki domin a
tsammaninsa zai yi nutsu a cikin ruwa ya yi qasan
tekun amma ga matuqar mamakinsa sai ya ga ya
faxo tsakiyar wani fili mai yanyame da dakarun
aljanu cikin shirin yaqi. Ya zuba musu idanu yana
kallonsu suma suka zubo masa idanu aka soma
kallon-kallo a tsakaninsu kamar akuya da kura.
A lokacin suma su Gimbiya Lusa suka
faxo tsakiyar wurin suka miqe tsaye suka zubawa
wurin idanu cike da matuqar mamaki. Sarauniyar
aljanun cikin ruwa ta dube su cikin mamaki lokaci
xaya yanayin fuskarta ya sauya daga farin ciki
zuwa vacin rai ta dubi Ruhin sarkin aljanu Gamsu

da yake hannunta ta yi murmushi sannan ta buxe
wata jaka da take xaure a gefen qugunta ta saka
Ruhin a ciki ta mayar ta rufe kafin ta mayar da
dubanta zuwa ga su Farsu dake tsaye carko-carko
kamar wasu zakaru cikin murya tsawa-tsawa tace
musu.
“Kai baqar fata wanne irin shisshigine ya
kawoka cikin fadata” Farsu ya dubeta cikin
nutsuwa kafin ya bata amsa. “Ni ne baqar fata
Farsu na zo ne domin amsar Ruhin da yake
hannunki domin bai dace da ke ba” Maganarshi ta
zamto tamkar sukar kibiya a cikin zuciyar
sarauniyar aljanun cikin ruwa, ta yi zaman shekara
xari uku tana jiran abu yau ta same shi sannan
wasu za su ce sun zo domin su rabata da shi? Ta
dube shi sheqeqe.
“Babu makawa duk duniya babu wani
wanda yake da jarumtar da zai iya amsar wannan
Ruhin daga hannuna, idan kuma akwai jarumi to
yana iya gwadawa” Cikin izza ta faxa.
Gimbiya Lusa ta dubeta sannan cikin
xaga murya tace mata “Na yi zaton mutane ne
kawai suke son sace ruhin mahaifina sarkin aljanu
Gamsu, ashe ba haka bane a cikin duniyar aljanu
ma akwai masu buqatar shi, don haka ina mai

tabbatar miki cewar za ki zamto aljana ta farko da
zan soma sadarwa zuwa ga ajalinta” Jin haka yasa
sarauniyar aljanun cikin ruwa ta yi dariya sannan
ta nunata da yatsa tace mata.
“Duniya ta daxe da wayewa Gimbiya
Lusa don haka na gaba ya yi gaba” Gimbniya Lusa
itama ta xaga hannu ta nunata. “Babu makawa zan
dawo da na gaba baya, domin duk tsohon da bai ji
kunyar hawa jaki ba to shima jaki ba zai ji kunyar
kayar da shi ba. Da mai jini a jika shi ne wanda
zamani yake tafiya da shi, don haka ke mai tashe
ce ni kuma mai zamani, saboda haka za ki bani ta
lumana ko kuwa sai kin ga jinin sadaukanki yana
malala tamkar
End Ads