x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 3 - ABOKAN GABA

  • 6001 words
  • 9000 words
  • Out of 11905 words

Category: Adventure Stories

Views 45

09 Aug 2025
Start ads
After Image Ads
magunar ruwa” Maganar ta zamto
tamkar ta watsawa sarauniyar aljanun cikin ruwa
wuta a zuciyarta cike da fusata ta dubeta.
“Lallai za ki yi nadamar wannan furucin
naki, domin sai na ladaftar dake bisa kuskuren da
kika yi” Tana rufe baki ta dubi yawan dakarunta
da suke mamaye da wajen cikin isa da qasaita tace
mu musu “Maza ku yi mun maganin waxannan
qananin halitar” tana rufe bakinta dakarun suka
zaburo a fusace makamansu a zare za su yi
sukuwar sallah akan su.

Hausa qarasowa zuwa garesu
suna
tsaye suna kallonsu, sai da ya zamto baifi sauran
taku goma ba sannan Ansar ya daka musu tsawa,
wanda hakan ya haddasa musu tsawa waj e xaya
lokaci guda yace wa sarauniyar aljanun cikin
ruwa.
“Kin yi babban kuskure wurin turo
dakarunki domin su yaqe mu, don haka ki saurara
kiga yadda za mu qare da su kafin mu qaraso
gareki” Yana gama maganar ya zare takobinsa
sannan cikin azama ta bazata ya yi xauki garesu,
ganin tahowarsa yasa suma dakarun suka kuma
zaburowa suka gamu a tsakiya kasuwar yaqi da
saye da sayarwa rayuka ta soma ci mutuwa ta
soma shawagi tana farauce ruhin aljanun cikin
ruwa.
Masifa irin ta yaqi ta dunga sauka a
wurin kai sara da kai suka ya yawaita zubar jini da
malalarsa ya wanzu a wurin qasan tekun ya
hautsine wanda hakan yasa ruwan tekun ya soma
tambal-tambal tamkar zai malalo cikin duniya.
Bawa Farsu ya zamo tamkar wata annoba ta wuta
a cikin tsakiyar gonar auduga domin duk wurin da
ya sa kai sai dfai ka ga kawuna suna yawo a sama
tamkar tsuntsaye, jikuna suna zubewa qasa babu

kawuna haka itama Gimbiya Lusa ta wanzu tana
saukar musu da azabar yaqi.
Kafin wani lokaci sun yiwa rundunar
fata-fata sai tsirarun xaixaikun dakarun suka rage
ganin sun zama tsiraru ya saka sauran suka yadda
makamansu suka yi mubaya’a. ganin haka ya sa
ran sarauniyar aljanun cikin ruwa ya matuqar
dugunzuma ta dube su cikin tsawa tace musu
“Qasqanci ya tabbata a gareku halaka ta zama dole
a gareku” Tana gama maganar ta zare takobinta
dake xaure a xamarata sannan lokaci xaya ta
tunkaresu da zumar ta yaqe su ganin irin wannan
tahowar da ta yi ya sa bawa Farsu ya taryeta tun
kafin ta qaraso suka yi wata muguwar haxuwa
takubbansu suka gamu a wuri xaya, wata qara mai
qarfi ta cika wurin sannan wata wuta ta buga ta yi
sama, suka soma musayar sara da suka a
tsakaninsu zuwa tsawon lokaci, ganin lokaci yana
tafiya a banza ya sa bawa Farsu ya tunzura ya qara
qaimi wurin kai sara da suka gareta can ya xauki
numnfashinta ya kai mata wani kaitattacen sara a
wuya da zumar tsinke mata kai.
Ganin tahowar saran ya sa sarauniyar
aljanun cikin ruwa yin qoqarin kaucewa domin kar
saran ya sameta amman ta makara domin sai da

saran ya sameta kaxan a wuyanta. Ba don wata
sarqa da take rateye a wuyanta ba wacce saran ya
tsaya akanta, amman banda haka da saran ya yi
tasiri akanta da tuni wani labarin ake yi ba nata ba.
Sarqa ta zamo daga wuyanta ta sulmiyo ta yo qasa.
Bawa Farsu ya ga tahowarta ya miqa hannunsa ya
taryota ya riqeta a cikin tafin hannunsa ya yi
zamiya yana kallonta.
Ita ma ta dube shi na wani lokaci, a
tsawon rayuwarta yau ita ce ranar farko da wani
sadauki ya tava wanzuwa a gabanta tsawon lokaci
har ya ke qoqarin samun nasara akanta, a
rayuwarta bata xaukar wani tsawon lokaci suna
fafatawa da wani sadauki, sai ta farauce rayuwarsa
amma ga mamakinta sai ga baqar fata ya zamar
mata ciwon ido. Suka zubawa junansu idanu suna
kallon juna bawa Farsu ya dubi sarauniyar aljanun
cikin ruwa ya dubi sarqa da take riqe a hannunsa
ya xagata sama ya nuna mata ita ta bi sarqa da
kallo cike da mamaki da baqin cikin ganin ya
qwace ta daga gareta annurin da ya yi saura akan
fuskarta ya soma narkewa daga kan fuskarta. Tana
gama kallon sarqa da Bawa Farsu ya xaga mata
akan fuskarta sai ta juya ta dubi hanya sosai
sannan tace masa “Wannan sarqa da ka xagata

akan idanuna dole na gudu tunda ka xagata na
ganta da idanuna, domin sirrin tsafin dake jikinta,
amman ba don haka ba da yau sai na halakar da
ruhinka, don haka ka jirani a haxuwa ta gaba da za
mu yi”. Tana qarasa faxar haka ta dubi hanya ya
falfala da wani azababben gudu kafin su farga har
ta vace musu daga gani.
Bawa Farsu ya bi sarqa da kallo cike da
mamaki ya juya ta zuwa ga su Gimbiya Lusa da
sadauki Ansar ya fuskance su sosai yana kallonsu
cike da mamaki ita kuma sarqa sai qyalqyali take
tana xaukar idanu Gimbiya Lusa ta miqa hannu
zata amsa Bawa Farsu yace mata.
“Dakata” Ga matuqar mamakinsa sai
yaga ta qame tamkar gunki ya dubeta sosai ya yi
murmushi ya nuna sadauki Ansar da ita shima
yace masa “Qame!” Take Ansar ya maqale shi ma
tamkar busashen itace. Bawa Farsu ya dube shi a
qame kamar busasun itatuwa ya qyalqyale da
dariya cike da gamsuwa ya matsa gaban Gimbiya
Lusa ya shafi fuskarta a hankali yace mata.
“Qaramar mara kunya”.
**
Bokanya Namsu ta dubu xayar da take
tsaye a kusa da ita da duban matuqar mamaki mai

matuqar yawa domin ganin matuqar kama da su
ka yi da junansu. Ta yi murmushi akan faffaxar
fuskarta sannan cikin murya fushi tace.
“Ka yi mana asara biyu, dukkanmu mun
rasa abin don haka kakan iya dawowa sufaffarka ta
ainahi kafin na halakaka bisa wannan zunibin da
ka aikata mun” tana gama maganar tana duban
xayar da ke tsaye a gabanta, aka yi wata dariya
mai xauke da isgilanci sannan cikin taqama aka ce
mata “BOKA SHARBANGA shi kaxai ne wanda
ya kamata ya mallaki ruhin sarkin Aljanu Gamsu
domin na fi kowa sanin muhimmancinsa a duniyar
mutane, domin haka kafin ki halakani ni yanzu zan
salwantar da ruhinki domin ke kaxaice bokanya da
za ki iya bani matsala a cikin lamarina’.
Ya gama maganar yana mai yin wata
girgiza tamkar tsuntswa nan take duk kayan da
suke sanye a jikinsa suka zube a qasa, ya komo
ainahin surarshi ta ainahi, wato namiji basamuden
qato mai mummunan kama ya dubi Bokaya
Namsu ya yi murmushi.
Ta dubeshi itama cikin tsananin fushi mai
tarin yawa tace masa.

“A yau bokanya xaya a tsakiyar mazaje
zata daka maka gumba a hannunka, ta nuna maka
cewar akwai bambanci tsakanin aya da tsakuwa”
Ta gama maganar tata tana mai miqa
hannunta cikin gashin kanta ta zaro wani xan
guntun itace ta cilla masa shi, take wuta ta kama
itacen ta soma ci ganga-ganga lokaci xaya aljanin
da suke kai ya kurma wani ihu mai tunzura zuciya
sannan lokaci xaya wutar ya narkashi ya narke
tamkar ruwa, ya riqa xiga yana zagwanyewa
lokaci guda wutar ta doshi Boka sharbanga.
Bokanya Namsu ta miqe ta yi sama tamkar
wata tsuntsuwa ta tsaya akan iska ta bi wutar da
kallo tana da tabbacin ta gama halaka boka
sharbanga.
Wutar tana zuwa wurin da boka sharbanga
yake tsaye ya narke ya zama ruwa wutar ta ratsa ta
cikinsa, wuta da ruwa suka bada wata qara sannan
lokaci xaya wutar ta mutu boka sharbanga ya yi
dariya yana kallonta yace mata.
“Ke qaramar mara kunya maza bisa kanki”
Yana rufe bakinsa ya yi wata fitar burtu ya tasar
mata yana zuwa kusa da ita suka sake tashi a sama
kamar tsuntsaye, nan take ya buxe qirjinsa suka
taso suka qaxa qirji da qirji nan take suka yi baya

kamar an watsa yakuwa a cikin teku, suka sake
tasowa juna a guje suka yi suka yiwa juna karo
kamar raguna suka yi baya taga-taga.
Wajen da suka yi gware take ya fashe jini
ya soma zuba boka sharbanga ya miqa hannunsa
sama take wata takobi ta bayyana ya yi xauki akan
bokanya Namsu kafin ya qarasa gareta itama ta
miqa hannu cikin iska, lokaci guda wata takobi ta
bayyana a hannunta itama tayi xauki kansa suka yi
wata gamuwa mai muni suka soma kaiwa junansu
sara da suka ko wanne yana qoqarin farauce
rayuwar xan uwansa duk wanda ya sari wani a
cikinsu sai dai kaji kamar wani qarfe da qarfe ne
suka gamu a waje guda.
Haka suka tafiyar da tsawon lokaci suna
faman fafatawa a tsakaninsu ba tare da wani a
cikinsu ya sami nasara akan xan uwansa ba, can
suna cikin wannan gumurzun sai Boka sharbanga
ya faki numfashin bokanya Namsu ya zaro wata
farar hoda daga cikin jakarsa ta bokanci ya watsa
mata.
Hodar tana sauka a jikinta nan take ta soma
jin jikinta duk ya saki, ta saki makamin da yake
hannunta sannan lokaci guda ta zube a qasa, ya

dubeta a wulaqance sannan ya qyalqyale da
dariya.
“Wanda ya fiki himma ya riga ya sha kanki,
don haka yanzunnan zan halaka ki”. Yana gama
maganar shi ya buxe jakar bokancinsa ya xauko
wata wuqa da aka yi da qashin haqarqarin mutum
ua xago da idanunshi ya kalleta gami da
qyaqyacewa da dariya kafin ya sake cewa da ita.
“Duk duniya babu wani mai sihiri da
wannan wuqar ba zata huda shi ba, don haka
yanzunnan zan halakar da ruhinki, ki zamto
tamkar ba a tava yinki na doron qasa ba” Yana
gama maganar tashi lokaci xaya ya xaga wuqar a
sama ya dubi qirjinta daidai inda zai luma wuqar
sannan yace mata.
“Sai wata rana ABOKIYAR GABATA,
Bokanya Namsu” Yana gama maganar ya nufi
qirjinta cikin sauri da zumar soka wuqar a gaban
qirjinta.
**
Sarauniyar aljanun cikin ruwa ta wanzu
tsawon lokaci tana tafiya babu qaqautawa ita da
kanta tana da masaniyar duk duniya babu wani
mahaluki da yake da gaggawar da zai iya biyo
bayanta har ya cimmata don haka ganin ta yi nisa

da wurin su bawa Farsu sai ta rage gaggawar da
take yi ta samu wuri ta tsaya.
A hankali ta miqa hannunta ta shafi
wuyanta cike da takaici da baqin ciki domin rasa
sarqarta da ta yi. Duk duniya babu abinda tafi
qauna a rayuwarta kamar sarqa domin duk wani
sirri nata ya ta’allaqa a jikinta. Duk abubuwan duk
abubuwan ba su ne vacin ranta ba, babban vacin
ranta na rashin samun damar buxe jakar da ta saka
ruhin sarkin aljanu Gamsu wanda dole sai ta yi
amfani da sarqa ta zata buxe jakar. Wannan abun
shi ne abu mai muni da sarauniyar aljanun cikin
ruwa ta tava cin karo da shi a tsawon shekarunta
da ta yi a duniya.
Ta xaga kanta sama ta soma qoqarin tunani
da zumar ta tunano hanyar da zata bi domin ganin
ta samo mafita akan abinda ya dameta.
Abubuwa da yawa suka yi ta zuwar mata
cikin ranta, amma duk ba su haska mata tunanin
yadda zata dawo da sarqarta ba. Haka sa’o’i masu
dama suka wuce tana faman tunane-tunane bayan
tsawon lokaci wata dabara ta faxo mata, wannan
dabarar ba qaramun faranta mata rai tayi ba,
domin ta yi imani itace hanya guda da zata dawo
da sarqarta gareta cikin ruwan sanyi.

Don haka cikin gaggawa ta miqe tsaye ta
lalubi gefen qungunta ta xauko wani madubin tsafi
ta dubi kanta a ciki ta yi murmushi sannu a hankali
ta soma karanto wasu xalasimai na tsafi tana
duban kanta a jikin madubin, bata xauki wani
lokaci a haka ba take kamaninta suka soma juyewa
zuwa na bil’adama.
A hankali ta juya kama zuwa ga surar mace
baqar fata mai kyawun gaske, yadda duk wani
namiji idan ya kalleta sai ya yi mafarkin kyawunta,
ta dubi kanta a jikin madubin har sheqi take yi
tamkar ta shafa shuni a jikin fatarta, ga manyan
fararen idanu da jan shacin bakinta tayi wa kanta
tattausan murmushi a hankali tace.
“Wannan surar Gimbiya Zailu na aro, duk
duniyar baqaqe babu mai kyawunta zan yaudari
baqar fatar nan na amshi sarqata daga hannunsa
kafin na halakar da ruhinsa ya zamto na shafe shi
daga doron qasa” Ta qarasa magana tana
qyaqyacewa da dariya kafin lokaci guda ta nufi
wajen teku ta wajen da tana da tabbacin tanan su
Bawa Farsu za su fito.
Iska teku ta ci gaba da kaxawa a hankali.
**

Tsawon lokaci suka xauka a tsaye a wurin
bawa farsu yana kallonsu yana yi musu dariya.
Kafin ya miqa hannu ya xauki sadauki Ansar ya
mayar da shi can wani wuri yua ajiye shi, ya
xauko wasu sassa na gawarwaki halittun da suka
yi yaqi da su ya xoxxora masa a jikinsa. Ya dawo
itama Gimbiya Lusa ya zuba mata idanu yana
kallonta ya qare mata kallo a hankali.
Ban tava tsayawa na qare miki kallo ba sai
yau, ashe daman haka kike da tsantsar kyau, ya
saurara yana dubanta ya dubi idanunta da suke a
buxe manya da su, farare qal. “Tunda nake a
rayuwata ban tava ganin kyawawan qwayar
idanuwa kamar naki ba, surarki zata xauki
hankalin sarakuna da attajirai ma su ji da kansu”
Ya kammala maganar yana dubanta. Ya juya ga
sadauki Ansar yace masa “Ka koma yadda kake”
Yana faxar haka sai sadauki Ansar ya ci
gaba da motsi kamar yadda ya ke a baya, ya tsaya
yana duban kansa cike da mamaki ya mayar da
kallonsa ga Bawa Farsu yaga yadda ya tsaya a
gaban Gimbiya Lusa cikin tsawa yace masa.
“Meye haka? Maza ka matsa daga wajenta”
Ya juyo yana dubansa fuskarsa xauke da
murmushi.

“Kana da alaqa da ita ne?” Ya jefa masa
tambayar sadauki Ansar shima ya tsare sa da ido.
“Wanne sihiri ka samo kake aikatawa a
gare mu, don haka ina mai sanar maka lallai kayi
gaggawar rabuwa da shi, idan kuma ba haka ba
zan amshe shi da qarfin tsiya na lalatashi”
Kalamansa ya baiwa bawa Farsu dariya ya
fuskance shi sosai sannan yace masa.
“Bana jin akwai wani sadauki da zai iya
amsar wannan abun daga hannuna da zunzurutun
jarumtaka don haka idan kana ganin cewar za ka
iya to ga fili ga mai doki, daga ni sai kai sai kuma
Gimbiya Lusa” Ya gama maganar yana mai
dubanta “Ci gaba da rayuwarki” yana rufe bakinsa
itama ta dawo yadda take ta dubi kanta cike da
mamaki, ta mayar da kallonta ga sadauki Ansar
cikin mamaki ta tambaye shi.
“Kaima abinda ya faru da ni ya sameka?”
ya gyaxa kai.
“Ga wanda ya aikata mana sihirin tsafi,
kuma yanzu nan zan ladaftar da shi akan wannan
laifin daya aikata mana. Domin zan amshi sihirin
na lalata shi”.
Gimbiya Lusa ta juya ta dubi Bawa Farsu a
fusace tace masa gwara tun cikin ruwan sanyi ka

bamu sihirin da ka aikata akanmu mu lalatashi
domin idan ba haka ba zamu amshe shi da qarfin
tsiya, sannan mu mayar da shi kanka” Bawa farsu
ya dubeta ya yi murmushi kafin yace mata.
“Ba irin mu ake yiwa barazana ba domin
mun sha jarumtaka a nono, mun zama dutsen dake
cikin ruwa bamu san ana rana ba. Saboda haka duk
wanda yake ganin zai iya amsa da qarfin damtse to
ga fili ga mai doki” Ya gama magana yana
dubansu.
Sadauki Anwar ya miqa hannunsa ya zaro
takubinsa ya riqeta sosai a hannunsa ya dubi Bawa
Farsu ganin haka shima ya zare nasa makamin ya
dubi sadauki Anwar suka fuskanci juna ko wanne
a cikinsu yana jujjuya makaminsa. Tsawon lokaci
suna tsaye carko-carko kamar zakaru kafin daga
bisani Anwar ya yi xauki ga bawa Farsu da zumar
ya yi tafiyar guguwa da shi,ganin tahowarsa ya
saka shima bawa Farsu ya tare shi suka yi wata
qazamar gamuwa data girgiza qasan tekun,
makamansu suka bayar da wata maxaukakiyar
qara, su ka yi zamiya suka kuma juyowa suka
gauraya suka soma musayar sara da suka a
tsakaninsu.

A haka suka xauki tsawon lokaci suna
faman fafatawa bayan tsawon wani lokaci sannan
bawa Farsu ya sauya salon yaqinsa nan take ya
takura Sadauki Ansar duk da irin tsananin jarumtar
da yake da ita. Wannan shi ne salon yaqi xaya da
aka tava sauya masa a tsawon rayuwarshi ta
duniya bai san ta yadda zai qare kanshi ba a ‘yan
lokuta kaxan bawa Farsu ya gajiyar da shi ainun!
Ganin abinda yake shirin faruwa ya sa Gimbiya
Lusa itama ta zare makaminta ta yi xauki akansa
da wata irin zuciya mai kama da dutse, jin
motsinta ya saka ya yi saurin juyawa tana zuwa ta
kai masa wani sara a kaikace cikin zafin nama ya
kaucewa saran, nan suka soma kai sara da suka ya
zamana su biyu wato Gimbiya Lusa da sadauki
Ansar sun rufarwa Bawa Farsu a tsakiya.
Qura ta turniqe a wurin babu abunda zaka
dunga juyowa sai qarar haxuwar makamansu da
gilmawar kai sara da suka a tsakaninsu walqiya da
motsin wucewar makamansu ya karaxe ilahirin
wurin. Kai komo da sintiri suka rika yi a wajen ko
wanne a cikinsu yana burin ganin ya samu galaba
akan xan uwansa. Su Gimbiya Lusa suka kasa
samun nasara akan Bawa Farsu haka shima ya
kasa samun nasara akan su, har suka gaji dukansu

suka zame qasa a jigace numfashinsu yana fita da
sauri da sauri.
A daidai lokacin wani aljani ya keto qasa
ya fito ya tsaya a gaban Gimbiya Lusa ya yi
gaisuwa a gareta ta dubeshi sannan ta ce masa
cikin muryar gajiya “Maza ka xauke mu ka fitar
da mu gavar teku” Bata gama rufe bakinta ba ya
sunkuya ya xaukesu ya ajiye su a bayansa sannan
lokaci xaya ya vace daga wurin. Ilahirin wajen ya
zamto tamkar wata halitta mai rai bata tava
wanzuwa ba, babu komai a wurin da ya yi saura,
sai gawarwakin matattun dakarun sarauniyar
aljanun cikin ruwa.
**
Bokanya Namsu tana kwance ta na kallon
tsinin wuqar boka sharbanga ta tunkaro qirjinta ta
ta lumshe idanunta tana da tabbacin yau itace ranar
mutuwarta, domin babu wani mahaluki da zai iya
zuwa domin ya ceci rayuwarta daga halakar da
take ciki.
Duk da runtse idanunta da tayi hakan bai
hanata ganin kakkaifar wuqar boka sharbanga ba,
haka ya sa ta yi gaggawar buxe idanunta a lokacin
ya nufo qirjinta da wuqar da zumar ya soka mata

Bokanya Namsu ta runtse idanunta karo na biyu
wannan karon ta fi tsorata fiye da kowanne lokaci.
Kafin kaifin wuqar ya qarasa qirjin
bokanya Namsu, wata kibiya ta qaraso ta samu
matsuguni a hannun Boka Sharbanga ya qwala
wata razananniyar qara da amonta ya watsu ko ina
da ina na illahirin sararin samaniyar tekun. Hakan
ya sa Bokanya Namsu ta yi gaggawar buxe
idanunta domin ganin abunda ya sa Boka
Sharbanga qwala ihu. Tana buxewa ta ga Boka
Sharbanga ya yi tsalle gefe xaya yana qoqarin zare
kibiyar da ta samu matsuguni a jikin hannunsa.
A lokacin wani saurayin aljani ya qaraso
wurin wata budurwa mai kyawun fuska ta sako
daga kansa ta tsaya gaban Boka Sharbanga ta tsaya
a hannunta riqe da wata kwari da baka qirar
mutanen nahiyar baqaqen fata.
Wannan budurwa dake tsaye akan Boka
Sharbanga itama baqar fata ce kamar Bokanya
Namsu, sai dai ita yarince xanya domin du-du-du
shekarunta ba su fi goma sha tara ba, tana da qirar
cika na mace ta tattare gashinta a wuri xaya, tana
sanye da kayan yaqi koraye, waxanda suka
matuqar yi mata kyawu a bayanta tana rataye da
wata takobi mai koren mariqi da aka yi mata ado

da farin qyalqyali, akwai alamomin jarumtaka a
jikinta.
Ta sunkuya ta buxe gefen takalminta ta
xauko wata hoda ta watsata a jikin Bokanya
Namsu nan take ta ji duk kuzarinta da ta rasa ya
dawo, cikin sauri ta miqe ta tsaya gaban budurwa
tana dubanta, a lokacin Boka Sharbanga ya zare
kibiyar daga hannunsa ya miqe tsaye a fusace ya
dubi budurwa da fushin murya yace mata.
“Wacce ce ke da har kika aikata wannan
laifin a gareni?” Budurwa ta dubeshi fuska da
fuska kana ta ba shi amsa da cewar.
“Ni ce Sultan”.
Boka sharbanga ya zuba mata idanu cikin
tsananin mamaki, yana da labarinya ya santa a
matsayin jaruma mai tsananin jarumtaka duk
wajen dataje a rayuwarta sai anyi tsananin zubar
da jini, bata zuwa wani waje ba tare da wani ya
mutu ba, wannan shi ne abinda kawai ya sani
akanta. Ya juma yana kallonta, sannan cikin
xaukar numfashi ya shammaceta ya yi wuf! Ya
zare takobinsa ya afka mata suka gauraya a wuri
xaya suka soma musayar kai wa juna sara da suka
mutuwa ta soma shawagi a tsakaninsu musayar kai

sara da suka ya karaxe wurin suka xauki tsawon
lokaci suna fafatawa.
Ganin lokaci yana tafiya ya sa Sultan ta
sauya salon fafatawar bayan wasu
End Ads