An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng
For feedback and support
Facebook : https://facebook.com/taskarnovels
Twitter : https://twitter.com/taskarnovels
Telegram : https://t.me/taskarnovels
ABOKAN GABA
MUKHTAR I. KWALISA
08069524699
G
imbiya Lusa tana gaba akan ingaraman
dokinta ta yi shiga ta bajinta cikin sulke
da aka yi masa ado da koren qyalqyali.
Daga nesa idan ka kalleta sai ka xauka wani barde
ne mai qarfin dantse amma idan ta matso kusa sai
kaga ashe mace ce.
Sai tauri a duniyar sadaukai idan suka ganta
suna saurin rainata, amma abinda ba su sani ba shi
ne da mutum ya raina Gimbiya Lusa ya xauketa ba
wani abu ba gwara ya sha guba da za ta hallakar
da shi a sa’o’I uku domin Gimbiya lusa ta fi guba
saurin kisa. Ita xaya take faman kaiwa da komowa
a cikin duniya tana ta faman farauce rayukan
sadaukai da jarumai tun daga lokacin da aka bata
labarin cewar wani sadauki zai bayyana ya sace
ruhin mahaifinta wato sarkin aljanu mai girman
daraja sarki Gamsu.
A duk duniya babu wanda gimbiya lusa take
matuqar qauna kamar mahaifinta sarkin aljanu
gamsu duk da zamtowar ita ba aljana bace ta
kasance mutum bil’adama amma mahaifinta aljani
ne. Gimbiya lusa ta kasace mace ma’abociyar
kyau da a faxin duniya babu tamkarta a zamanin.
Ta kasance doguwar mace mai yalwar jiki ba wai
sosai ba tana da faffaxaar fuska mai xauke da
fararen idanuwa. Tafi iya murmushi fiye da komai.
A duk lokacin daka ganota daga nesa gani za ka yi
har wani xaukar idanu take yi, tana da qirar
jarumta tana da ruwan tausayi, kyawunta yafi
jarumtakarta.
A yanzu Gimbiya lusa tana tsaye a gaban
wani saurayin namiji mai cike da yalwar kyawu da
cikar zati, mai kwarjinin fuska da jarumta.
Wannan saurayin da yake tsaye a gabanta shi
kaxai ne jarumin da ya yi saura wanda bata
farauce ransa ba, a cikin mutanen da take
tsammanin za su iya zuwa har fadar sarkin aljanu
domin sato ruhinsa. A duk jaruman da su ka yi
gwagwaarmaya da ita wannan shi ne kaxai
jarumin da kwarjinsa ya cika mata fuska.
Suka jima a tsaye suna kallon junansu, a
hankali ya dubeta yace mata.
“Tun da nake a rayuwata ban tava ganin
mace da kyawunta ya girgiza mun ruhi ba sai ke…
na yi matuqar baqin ciki da kika zamo mace mai
yin hidima ga aljanu, kike farauce rayukan ‘yan
uwanki mutane akan kare ruhin wani tsohon aljani
don gudun sace shi”.Ya yi maganar yana mai
dubanta kafin ya ci gaba da magana cikin isa da
izza.
“Kar ki mance duniya tana da yawa kuma
qaddara ta riga fata” Gimbiya lusa ta yi murmushi
kafin ta mayar masa da martani cikin wani irin
sautin murya.
“Ina da tabbacin idan na farauce rayuwarka
zan kawo qarshen matsalar dake shirin faruwa ga
mahaifina zai zamo cikin walwala da nishaxi, don
haka yanzu zan kawo qarshen numfashinka kamar
yadda na aikata ga sauran jarumai ‘yan uwanka”
Da muryar jarumta tace masa.
Cike da jimami yace mata “Duniya ta zamo
mafaka ta mutane daban-daban ina fatan baki
mance da yanki baqar fata ba?”
Yana mai tsareta da idanu.
Ta yi murmushi.
“Baqar fata ba su da wayewar da har za su
san amfanin ruhin mahaifina a garesu, mutanen da
ba su fahimci kansu ba, taya za su fahimci amfanin
wani abu” Ya girgiza kai.
“Xan hakin daka raina shi ke tsone maka
ido”. suka yi shiru su duka suna kallon juna na
tsawon lokaci daga bisani ya qara dubanta sannan
cikin isa da taqama yace mata.
“Lallai ina mai tabbatar miki ruhina yafi
qarfin ki farauce shi don ba za ki tava samun
nasara akai na ba”.
Maganarshi ta zamto tamkar wuta ya watsa
mata, ta dube shi da qunar rai da tafarshashiyar
zuciya tace masa.
“Babu wani jarumi a duniya da ba zan sami
nasara akan shi ba, domin na farauce rayukan
sadaukai irinka waxanda suka fika jarumta da
nuna bajinta a duniya, don haka kaima lallai ina
baka tabbacin zan kawo qarshen numfashinka ka
zamto kamar ba a yi ka ba”.Gimbiya Lusa ta
tabbatar masa.
Ya girgiza kanshi sannan lokaci xaya ya
gyara ruqon da ya yiwa takobinshi ya kalleta sosai
a hankali yace mata.
“Bana buqatar ki zamto abokiyar gabata” Ya
yi shiru yana kallonta a hankali ya kuma ce mata.
“Kinyi gaggawa wurin yarda da cewar wani
aljani ne mahaifinki,bayan aljani bai isa ya haifi
halitta kamar ki kyakkyawa mai kyawun fuska da
kyawun idanu da kyawun shataccen baki ja”.
“Bana buqatar yawan surutu don haka ka
shirya tarata gani nan tafe zuwa gareka” ta ce
masa cikin tsawar murya, sannan lokaci xaya tayi
xauki zuwa gareshi shima ya taso ma ta lokci xaya
suka gamu da juna a tsakiyar fili, su ka kaiwa
junansu sara da takubbansu, makamansu suka
gamu wuri xaya, qarar haxuwar makaman ta cika
wurin suka gauraye wuri xaya suka soma qoqarin
farautar rayuwar juna, suka dinga kai sara ga
junansu. Gimbiya Lusa t sami sadaukin ba yadda
ta tsammace shi ba. Lokaci xaya suka yi jina-jina
duk jikinsu idan ka duba jikinsu ya yi kaca-kaca
da ciwuka. Haa suka ci gaba da saran juna kafin
daga bisani suka yanke jiki suka faxi suka yi
kare-jini-biri-jini.
“Ba za ki tava samun nasara a kaina ba,
domin ina son ki sani Ubangiji da nake bautawa,
wato Ubangijin da ya yi horo da bin addinin
musulunci wanda shi ne ya hanaki samun nasara a
kaina”
Ya tabbatar mata.
Gimbiya Lusa ta girgiza kanta cike da
gamsuwa domin ta tabbata bata samu nasara ba ga
wannan jarumin. Ta xago kanta a hankali ta dube
shi taga yadda jini yake malalowa daga jikin
raunukan da tayi msa. A hankali itama ta dubi
jikinta taga yadda itama jini yake ta faman xuba
daga jikinta ta girgiza kanta.
‘Babu makawa ba za ta iya samun nasara ba
akan wannan jarumin sai dai su yi Mutuwar kasko,
tun da suka yi kare-jini-biri-jini”
Gimbiya Lusa ta zuba masa idanuwa tana
kallonsa shima ya zuba mata idanuwa yana
kallonta.
Kowa ya ajiye makamin shi a gefe xaya.
Wannan ita ce rana ta farko da Gimbiya Lusa
ta tava ganin jarumin da jarumtarsa ta birgeta,
wannan rana ita ce rana ta farko da Gimbiya Lusa
ta ji tana son wani sadauki mutum kamarta a cikin
ranta.
Amma ta fidda rai, raunukan da yake a
jikinta da jikinshi ba za su barsu su ci gaba da
rayuwa ba.
Ta lumshe idanuwanta sunan shi ya dawo
mata a cikin zuciyarta.
“Ansar”.
A dai-dai lokacin da ta furta hakan a cikin
ranta, a dai-dai lokacin wani mummmunan aljani
mafi girma ya sauka a gabanta, yana sauka ya
suretaa da hannunsa ya juya ya yi sama da ita a
guje, tamkar an harba kibiya.
Gimbiya Lusa ta buxe idanuwanta a hankali
ta kuma kallon Ansar da yake kwance a wurin. Ta
mayar da idanuwanta ta lumshe su.
Ungulaye suka ci gba da yin shawagi, suna
jiran Ansar ya qarasa mutuwa su sami damar yin
kalaci da namanshi.
NAHIYAR BAQAR FATA
Nahiya ce data yi fice ta kuma shahara
wajen siye da siyarwa ta bayi. Don haka baqar fata
ba shi da wata daraja a wajen larabawa da
nasarawa, domin suna masa kallon ba shi da wani
amfani idan ba bautarwa ba.
Farsu ya kasance baqar fata mai kaifin
basira da dabara. Ya zamto jarumi mai yawan
bajinta, farsu ya kasance bawa ne ga bokanya
Namsu wacce ta kasance baqar fatar bokanya data
shahara a fagen sihiri, don haka a cikin tsafinta ta
gano amfanin ruhin sarkin aljanu Gamsu a gareta.
Domin ya bayyanar mata matuqar tana son ta
mulki duniyar bokanci ya zamo duk duniya babu
kamarta to sai ta mallaki ruhin sarkin aljanu hakan
yasa ta bazama duniyar tsafi da bincike akan
yadda zata mallaki ruhin, amma sai ta gano qarfi
sihirin tsafi ba zai tava sakawa ta mallake shi ba.
Haka ma tsananin jarumta.
Wanan lamarin ya matuqar tayarwa da
bokanya Namsu hankali ta rasa meye yake mata
daxi, tayi ta nazari ta rasa samun mafita. Sai daga
baya tayi tunanin tura bawanta Farsu yaje ya
gwada sato mata shi. Tunda shi Farsu gwani ne
wajen iya sata kamar sidabaru haka yake iya sace
abu. Tana gama tunanin ta nufi inda yake ta same
shi a zaune yana gyara makaminsa. Ta dube shi
ido cikin ido.
Farsu ya yi gaggawar zubewa a gabanta
domin girmamawa Bokanya Namsu a hankali ta
soma yi masa magana.
“Lokaci ya yi daya kamaya ka yi mun
bauta ta qarshe daya kamata na ‘yanta ka” Ta
saurara tana kallonsa sannan ta ci gaba da magana.
“Samun nasaraka a wannan karon tamkar
ka sami ‘yanci ne, don haka wannan damace
gareka ta barin qangi na bauta” Ta basa tabbaci.
Farsu ya xago idanu yana duban bokanya
Namsu, wannan shi ne zance mafi daxin ji daya
tava ji daga bakinta a iya zamanshi a qarqashinta.
Don haka cike da qwarin gwiwa yace mata.
“Wannan wane irin aikine haka?”
Bokanya Namsu tayi murmushi domin ganin
tarkonta ya kamar kurciya, a hankali tace masa
“Ruhin sarkin aljanu Gamsu nake son ka sato
mun”. Maganar ta zo masa a bazata ya sauke wani
gwauron numfashi kafin yace mata.
“Zan sato miki shi matuqar zan samu
‘yanci na kuvuta daga qangin bauta” Ya tabbatar
mata.
Ta dube shi cike da jin daxi tace masa.
“Wannan itace bauta ta qarshe da za ka yi
mun a rayuwarka, don haka idan ka sami nasara ka
zamto kuvutacce, ‘yantace. Yanzu zan haxaka da
aljanin da zai xaukeka ya kaika har cikin fadar
sarkin aljanu Gamsu” Ta kammala maganar tana
dubanshi kafin ta qara cewa da shi.
“Ko kan da wata buqatar ta yin shiri?” Ya
girgiza kai gami da faxin.
“Bana buqatar yin ko wanne shiri ya
shugabar bokaye”.
Bokanya Namsu ta yi dariya jin sunan
daya kirata, take ta shafi xamararta kamar qiftawar
ido wata jibgegeyar halitta ta bayyana mai
tsananin girma da tsananin muni. Tana da dogon
wuya kamar raqumin dawa da manya-manya
kunuwa farakam-farakam sun lanqwasa kamar
alamar tambaya(?) yana da fuka-fukai kimanin
guda ashirin da bakwi.
Bokanya Namsu ta dube shi tace masa.
“Maza ka xauki bawana Farsu ka kai shi
fadar sarkin aljanu Gamsu” Take aljanin ya girgiza
kai cike da girmamawa, Bokanya Namsu ta dubi
Farsu tace masa “Idan ka shirya kuna iya tafiya”.
Farsu ya dubi bayan aljanin ya dubi
kayan makamansa ya sunkuya ya xebesu ya
naxesu a cikin wata rigar fatarsa da yake amfani
da ita a lokacin tsananin sanyi, ya daka tsalle ya
haye bayan aljanin kafin yace masa.
“Muna iya tafiya”.
Bokanya Namsu ta dube shi gami da
xauko wani makami ta cilla mishi kafin tace masa.
“Ga wannan zai taimake ka” Farsu ya
zuba mata ido yana dubanta, a daidai lokacin
aljanin ya buxe fuka-fukanshi ya soma tashi cikin
sararin samaniya suka luluqa suka nutse a cikin
gajimare.
Haka suka xaui tsawon wata xaya da sati
xaya suna tafiya sannan suka qaraso fadar sarkin
aljanu Gamsu, wanda tun daga nesa farsu ya ga
rundunar aljanu tsaitsaye cikin shirin yaqi ko ina
ka duba sune. An qawata fadar da ado mai jan
hankali da zane-zane abubuwa masu matuqar kyau
da ban sha’awa.
A hankali aljanin ya yo qasa-qasa ya
shiga ciki fadar, ga matuqar mamakin farsu sai
yaga babu wani aljani daya damu da shi, ko wanne
sabgogin gabanshi yake yi a haka suka dangana
har cikin fadar, wanda a can ciki ne suka samu
wasu zaratan aljanu tsaitsaye suna ta faman
muzurai ko wanne aljani yana cikin shiga irin ta
yaqi irin wacce farsu bai tava ganin irinta ba. A
zaue akan wata kujera ta farin qarfe wani dattijon
aljani ne xan kimanin shekara dubu takwas yana
zaune cikin isa da taqama.
Aljanin daya xauko shi ya sauke shi,
kafin ya matsa zuwa ga sarkin aljanu ya faxi ya yi
gaisuwa, sarkin aljanu ya dubi Farsu dake zaune a
bayan aljanin xan tsurut! Da shi kamar ruwan aski
yace masa.
“Kai bil’adama mai ya kawo ka cikin
babbar fadar duniya ta sarkin aljanu Gamsu?”
Farsu ya sauko daga bayan aljanin ya
dubi sarkin aljanu Gamsu cike da girmamawa
sannan ya zube a gabanshi ya yi gaisuwa a hankali
yace masa.
“Ya mai darja mai girman daraja wanda
sarakunan mutane suke shayi, kayi sani cewar na
zo ne gareka domin ganewa idanuna wani abu da
ake gayaa mani ban aminta ba wanda aka ce duk
duniya kai kaxai ne a duniyar mutum da aljan
kake da ikon haka” sarkin aljanu gamsu ya dubi
Farsu da duban nutsuwa sannan yace masa.
‘Wannan wane abune haka da har duniyar
mutane suke girmamani dominsa? Na kuma zamto
ni kaxai ne mai iko da shi?” Ya tambayi farsu
yana duban shi da idanunsa farsu ya sunkuyar da
kansa qasa domin gudun kar sarkin aljanu ya gano
qaryar da yake shirin yi masa sannan yace masa.
“An ce a duk duniya mutum da aljan kai
xaya ne ruhinka yake a cikin kwlba, ma’ana kana
iya cireshi daga jikinka idan ka so ka kan ajiye shi
a gefe xaya gangar jikinka ta zamo babu ruhi ka
zamto tamkar matacce har sai an mayar da ruhin.
Don haka na zo domin ganewa idanuwana wannan
abin mamakin, wanda ya gagari duniyar sarakunan
mutane” Sarki aljanu Gamsu ya dubi farsu da
idanunshi da duban nutsuwa ya xauki tsawon
lokaci yana dubanshi daga bisani ya nisa a hankali
yace masa.
“Ina fatan kana da masaniyar domin
‘yarta Gimbiya Lusa ta samu labarin cewar wani
jarumi zai zo domin sace ruhina shi yasa ta sauka
duniyar mutane domin halaka duk wani jarumi?’
Ya tambaye shi yana tsare shi da idanuwanshi,
farsu ya kuma sunkuayar da kansa cikin ladabi
sannan yace masa.
“Ni ban zamto jarumi ba, face na shahara
a wajen zuwa ganin duk wani abun mamaki da
bajinta wanda hakan shi yasa da na samu labarin
irin wannan bajinta taka ta cire ruhina daga jikinka
ya sani na taho domin na ganewa idanuwana. In
fatan zan sami biyan buqatar ta a nuna mun
wannan abin mamakin” Farsu yace masa.
Sarin aljanu Gamsu ya dube shi ya yi
murmushi wani turiri ya fita ta cikin qofofin
kunuwanshi, sannan a hankali ya cewa farsu. “Tun
kafin sarakunan mutane su farka daga bacci mu
muka rigaya muka je inda zamu. Don haka
bajintata ta yi nisa a duniya ta kuma gagari duk
wani bil’adama sai mu gagararun aljanu.don haka
zan nuna maka ruhina domin na san ko kayi
yunqurin guduwa ba za ka iya kai labari ba, domin
rundunar aljanu tafi qarfin duk wani bil’adama”
Sarki aljanu Gamsu ya tabbatar masa sannan ya ci
gaba da ce masa.
“Kayi sani cewar ruhina ya zamto a cikin
kwalbar tsafi wanda idan babu shi a jikina zan
zamto tamkar matacce har sai an dawo mun da shi
jikina an saka mun shi a qirjina yadda yake, don
haka ka yi sani cewar za ka zamto xan Adam na
farko daya soma ganinsa wanda a duk faxin
duniya babu wani mutum ko aljani daya tava
ganinsa sai kai, amma idan ka gansa hukunci na
gareka shi ne zan halakaka” Da murmushin
mugunta ya faxa.
Farsu ya yi shiru yana kallon tsohon
aljanin da yake gabanshi mai kama da siffar
bididigin kwaxo sannan da murya jarumtaka yace
masa.
“Na amince matuqar burina zai cika na
ganin wannan babbar bajinta da wani mahaluki bai
tava yinta ba. Kuma na tabbatar zan zama mutum
na farko da duniya zata riqa tunawa da shi a
matsayin wanda ya tava ganin wannan ruhin naka”
Ya kammala maganar yana mai duban fuskar
sarkin Aljanu wanda yake dubanshi da haxaxxiyar
fuskar data tattare kamar busashiyar fata sannan ya
yi dariya yace.
“Haka nake son naga mutum ya zamto
mai zuciyar jarumta da rashin tsoro, don haka
maza ka shirya ganin ruhina yanzu nan” Yace
masa yana dubanshi sannan a hankali ya miqe
tsaye ya yi wata irin girgiza da ta haddasa tashin
wata maxaukakiyar guguwa. A sannu a hankali
guguwar ta soma yayewa sannan wasu fuka-fukai
suka fito a jikin shi daga bisani suka soma
bubuxewa a tsakiyar qirjinshi wata kwalba ta
bayyana. Ya dubi Farsu sannan yace “Matso ka ga
ruhina”.
Cikin jarumta ya tunkareshi ya qarasa
gabanshi ya tsaya yana zubawa ruhin na shi da
yake cikin kwalba idanu yana kallonshi cike da
mamaki. A hankali ruhin yake motsi a cikin
kwalba. Cikin tsananin zafin nama na bazata Farsu
ya miqa hannu ya cafi ruhin sannan ya fisgoshi
daga cikin inda yake.
Sarkin aljanu Gamsu ya qwarara wata
qara a razane, sannan lokaci xaya ya soma
bushewa yana komawa kamar busashen karmami,
a haka ya gama bushewa ya zama kamar gunki.
Farsu ya dubi ruhin dake hannunsa ya dubi
busashiyar gangar jikin sarkin aljanu Gamsu yace
masa “Baka san hikimar mutane bane shi yasa ka
yi gaggawar amincewa da ni”. Yana gama
maganar ya buxe jakarsa da ya yi xamara da ita ya
cilla ruhin a ciki sannan ya juya. A lokacin
rundunar aljanun da suke a fadar suka zaburo masa
domin amsar ruhin sarki aljanu Gamsu.
Farsu ya zare takobinsa ya jinjina ta a
hannunsa ya dubi yawan rundunar aljannun ya
lumshe idanunshi ya buxe ya kuma gyara riqon da
ya yi wa takobinsa. Adadin rundunar suka matso
ganin sun kusa zuwa gareshi ya sa shima ya nufe
su a guje suka gamu a wuri xaya, kasuwar yaqi ta
soma ci rayuka suka soma salwanta, mutuwa ta
soma shawagi tana farauce rayuka, jini ya soma
fantsama kawuna suka dinga yawo a sama kamar
tsintsaye makamai suka riqa zubewa qasa daga
hannun mariqansu.
Yawan adadin rundunar aljanun ya dinga
raguwa domin irin yadda Farsu yake farauce
ruhinsu yaqi ya ci gaba da tsawaita a garesu
mutuwa ta ci gaba da shawagi a tsakaninsu duk
wurin daya saka gaba sai dai