Hadiza. Idan haka rabuwa da masoyi yake, tana addu’ar Allah ya sa ita ma ya so ta ko da rabin-rabin yadda yake son Hadiza ne”.
****
BAYAN TAFIYAR SULAIMAN
Rayuwa ta yi zafi ga Fati, komi na yanayin rayuwarta ya sauya, ta zama calm mai yin komi cikin kokari, juriya, karfin zuciya da dauriya. Soyayyar mijinta ta hana ta sukuni, hatta ‘ya’yanta sun san Auntyn su ta sauya, ta rage zama da su, ta rage walwala, sai dai Nana kullum tana jikinta.
Ta sakar ma Alti ragamar komi na gidan, ta fiya kwanciya tsakiyar gado, rigingine da Nana a kan ruwan cikinta. Ta rasa walwala da kazarniyar ta, komi ya fice mata a rai, mijinta kawai take so, wanda kuma ya yi mata nisan da ba za ta kamo shi a nan kusa ba.
Ita Alti sai ta yi zaton ciki ne, don haka take bata kulawa ta musamman. Misali da yake ta rage cin abincin gidan, sai lemu da ruwa, sai take tambayar ta ko da wani abu da kike marmari in yi miki?
A lokuta da dama cewa take babu, in kuma akwai sai ta fada mata.
A daddafe ta zana jarrabawar JAMB. Ba jimawa ta sake samun admission inda za ta karanci fannin da take so, wato Islamic Studies.
Idan direban yara ya kai su da motar da Dr. Sulaiman ya bar musu, sai itama ya sauke ta a makaranta.
Kullum cikin zumbulelen hijabin ta har kasa, Alti kan zauna a kofar aji ta rike mata Nana, ko su zauna masallacin Ramat su jira ta ta fito lacca. Karatun na taimakawa dari bisa dari wajen debe mata kewa da rage mata tunanin Dr. Sulaiman din da take zaton zuwa lokacin ya manta da ita.
Don har yau da ya cika watanni biyar da tafiya, ko sau daya bai kira ta ba. Kai tana jin ma ba shi da nomba din ta.
Duk sanda suka yi waya da Inna tana tambayar ta lafiyar ta da ta ‘yan jikokin ta, ba ta yin zancen Sulaiman, tana so ta tambayi Inna ko yana yi musu waya, tana kuma tsoron kada su yana yi musu ita ce ba ya nema, Inna ta yi mishi magana ya ce ta kai karar shi. Don haka ta ci gaba da jurewa ba ta yiwa Inna zancen ba.
Shekarar farko ta kare cike da dimbin nasarori a gare ta, domin duk jarrabawar da ta zana ba ta faduwa. Ta kare shekarar da maki mai daraja.
Nana ta yi bul tana gudun ta ko ina, ba ta taba sanin ba Fati ce mahaifiyar ta ba. Ta shiga 200 level cike da karfin gwiwa, tun Alti na zuba idon ganin ciki ya bullo mata har ta gaji ta gane ba ciki bane.
A yau da suka tashi Karkasara suka wuce domin duba jikin Baban su da bai ji dadi ba. Yaya ta ji dadin ganin su, fes dasu cikin koshin lafiya, wanda ke nuni da cewa babu abin da suka nema suka rasa. Dr. Sulaiman ya tsaya musu a kan komi.
Alti na tsakar gida, ita da Yaya suna daki suna hira irin ta da da mahaifi, ta ce, “Dazun nan nake ce da Sulaiman kun kwana biyu baku zo ba, ya ce karatu ne ya yi miki zafi ashe kuna tafe”.
Mamaki da haushi suka kama ta, wato yana kiran kowa har ‘ya’yan shi yana kira a makaranta ofishin malaman su su yi hira ya ji lafiyar su, ita ce dai ba ya kira don har yanzu yana kin ta, don rannan Munib yake gaya mata wai Daddy yana gaishe ta.
Ta ce, “A ina ka ganshi?” Ya ce, “Waya muka yi a school”.
Sannan ga shi yau Yaya ma ta ce yana yi musu waya. Duk inda ranta yake in ya yi dubu to ya baci, har Yaya ta lura kamar ta yi shiru tana tunani.
Ta ce, “Lafiya ko?” Ta yi saurin girgiza kai, “Babu komi”.
A dakin Baban su bayan sun gaisa, ta tambaye shi jiki ya ce ya ji sauki alhamdulillahi.
Sannan ya ce, “Fati har gobe ba zan daina sanya miki albarka ba, saboda yadda ki kai mana biyayya kika zauna lafiya a dakin mijin ki, duk da na san ba da son ranki aka yi auren nan ba. Biyayyar ki da YAKANAH…. ni na gaya miki ba za su tashi a banza ba!
Allah ya baki ‘ya’yan da za su yi miki biyayya fiye da yadda ki kai mana”.
Idanun ta suka cicciko, kamar ta gaya mishi cewa har yanzu Sulaiman ba ya son ta, da yana son ta da ya damu da lafiyar ta. Amma ko ya take tsayin shekara guda bai taba cewa ba.
Idan kuma ta yi tunanin sauyikan da ta gani a tare da shi kafin ya tafi, sai ta samu kanta cikin rudu a kan al’amuran Dr. Sulaiman, ta kasa tantance cewa yanzun yana son ta ko ba ya son ta?
“You are darling! Duk wanda ya zauna da ke na lokaci kankani, zai so ci gaba da zama da ke muddin rayuwar shi”.
Ta tuno kalaman shi ana i gobe zai tafi. Gaba daya maganganun da suka yi a ranar take tunawa filla-filla, wadanda in aka auna su a ma’auni na hankali da tunani suna nufin Dr. Sulaiman ya sauya muguwar fahimta da akidar shi a kanta.
To amma why yake kin neman ta a waya ko common gaisuwa ce su yi? Me hakan ke nufi? Babu wanda zai amsa mata tambayoyin ta sai shi. To ina za ta gan shi? Ta MAIRON HURE da ta ce,
“He is far away.....’ (Ya yi nisa).
****
Da la’asar sakaliya suka yi shiri suka nufi Bakori dukkannin su, za su yiwa Inna week end (hutun karshen sati).
Direba Malam Habu ne ke jan su, zuwa karfe shida na yamma suna cikin garin Bakori. An yi sa’a Saude, Ruma da Anti Ramatu kannen Sulaiman duk suna gidan sun je biki sun dawo suka zarto wajen Inna.
Don haka falon Inna yau ya yi albarka, ya kauraye da hira. Ita dai Fati ba ta magana illa in anyi abin dariya ta yi murmushi, suna son yarinyar sosai saboda sanyin ranta.
Anti Ramatu da yake sarkin barkwanci ce, ta ce, “Fati sai yaushe za mu zo suna ne? Mun kosa fa Nana ta samu kani ko kanwa”.
Kunya ta kama ta, musamman da yake Inna tana wurin. Ta rufe fuska da mayafinta, haka suka yi ta tsokanar ta su lallai suna jiran baby da Yayansu ya dawo.
Wayar Inna ta yi kidi tana neman agaji, Inna ta amsa cikin nutsuwa don ta gane lambar ta Sulaiman ce.
Bayan sun gaisa ya ce, “Hirarrakin me nake ta ji haka?”
Ta ce, “Su Ruma mana, sun sanya Fati gaba duk sun hanata sukuni, gasu nan sun zo dukkannin su baka ga yadda Nana ta yi wayo ba”.
Ya lumshe ido yana sauraron Inna, amma bai ce ta ba shi Fati ba sai ‘ya’yansa. Sun dade suna ta shirmen su kamar ba kudi suke narkarwa ba, har gwalantun Nana an sanya mishi ya ji, sannan suka shiga gaisawa da kannen shi.
Ya ce, “Ina Khalid?”
Inna ta ce ya je Malumfashi ta aike shi wajen Inna Atika kanwar ta.
Cike da kewa ya yi sallama da su, ya koma ya kwanta ya ta da kai da hannayen shi a rest chair irin kujerar nan da turawa ke sakawa da zaren roba da katako.
Ya mika hannu ga zungureriyar robar coca-cola ya daga, ya tashi zaune yana daddaka. Sanyin lemon da karfin ‘gass’ din shi na soya mishi makoshi, amma bai kula ba.
Ga wanda duk ya san Dr. Sulaiman-Sulaiman a da, lokacin Hadiza, ya kuma gan shi a yanzu, to ba zai gane shi ba.
Gaba daya ya rame, ya kara yin duhu, sai dai hakan bai boye zahirin kyawun halittar sa ba. Ba abin da ya sa gaba sai abin da ya kawo shi, sai dai hakan bai sa tunanin yarinyar ya barshi ya huta ko na second daya ba, kamar yadda ya yi tsammanin nisa da ita shi ne hanya mafi sauki da zai yaki kutsowar soyayyarta.
Ashe hakan tamkar zubawa wuta fetur ne? Tunanin sa na cewa yin nisa da Fati shi ne babban makamin yaki da farmakin data kawowa rayuwarsa ashe ba shi ne maslaha ba.
Abinda bai sani ba sai bayan tahowarsa Fati ta riga ta yiwa zuciyar shi kamun kazar kuku, ta yadda dai-dai da rana daya tun tahowar sa zuciyar sa ba ta taba hutawa ko na dakika da tunanin ta ba.
Dr. Smith ya iske shi a hakan, ya dade yana magana bai san yana yi ba. Kafin dan lokaci ciwon ciki ya turnike shi, ya kama cikin ya soma juyi, sai ya fado bisa kilishin dake shimfide a farfajiyar wajen.
Da sauri Dr. Smith baturen Chicago ne na asali, ya kama shi ya soma binciken abin da ke damun shi, tare da ba shi taimakon gaggawar duk da ya dace.
Bai samu kansa ba sai bayan awanni biyu, lokacin ciwon cikin ya lafa. Ya sa ido yana kallon Dr. Smith wanda ke shan lemo a gefen shi, shi ma kallon shi yake amma bai fasa shan lemon sa ba. Ya mike zaune a hankali suna kallon-kallo.
Dr. Smith ya dauke kansa ya ce,
“A lokuta da dama bakar fata ku kan birge ni wajen rike amanar matan ku, mazanku da matan ku, da wuya daya ya ci amanar daya a cikin aure. Wannan dabi’a ce mai kyau, in ka san ba za ka iya zina ba, me ya hanaka tahowa da matar auren ka? Sai ka zauna kana tara abu har sai ya kashe ka a banza?”
Ya aje tambulan din hannunsa ya dubi Dr. Sulaiman sosai, ya ce,
“Don me baka taho da matarka ba, alhalin gidan da aka baka yalwatacce ne? Sannan dai-dai gwargwado ba za ka kasa rike ta a nan ba.
Tun wancan karon na gaya maka abinnan yana barazanar kwantar da kai, wanda in ka ci gaba da tara shi zuwa wani lokaci sai anyi maka aiki. Duk me ya yi zafi? Ka aika matar ka ta zo, mene ne wahala a ciki?”
A sanyaye ya ce da shi,
“Hadizah ta rasu!”
Dr. Smith ya ce, “Oh dear! Tun yaushe ne?”
Ya rausayar da kai ya ce, “For almost a year and a half kenan”.
Smith ya ce, “Why not ka kara yin wani auren Dr. Sulaiman?”
Ya yi shiru kamar ba zai yi magana ba, har Smith ya kara maimaitawa. Ya dago idanun shi da suka shagide ya dube shi.
“Ina da wata matar Smith”.
“To me ya sa baka taho da ita ba?”
Ya yi murmushi ya ce, “Ba zan iya bane, saboda kanwar mata ta ce, auren hadin iyaye aka yi mana”.
“Which means….. baka son ta….?”
“Ko ina son ta ba zan iya hada jiki da ita ba! Idan na yi hakan GIRMA NA ZAI FADI A IDANUN TA. Ka gane, ina tattalin mutunci na ne, duk da Hadiza da kanta hakan take so kamin ta rasu, wato ‘yar uwarta ta maye gurbin ta, amma ni ba zan iya ba!”
Smith ya ce, “Wannan shirme ne, baka da hujja kwakkwara. Idan har kana son matarka ka aje girman kan nan ka daidaita da ita, domin kana zalintar ta. Kana zalintar kanka.
Dubi yadda kake suffering (wahala) baka tunanin ita ma haka take, sai dai ta nuna kawaici? In kuma baka son ta ne ka sahile mata ka ba wa iyayen ku hakuri, ba za ta rasa mai son ta ba, kai ma ba za ka rasa samun wadda za ka so ba.......”
Ya yi saurin katse shi da cewa, “Babu saki tsakani na da Fati, har abada, babu. Ko bana son ta balle halayen ta da nagartar ta sun sayo mata soyayya mai yawa a gare ni.
Hujjar nan dai da na gaya maka ita ce, wato tana ganin girmana bana so ta raina ni, bana so GIRMA NA YA FADI a idanun ta”.
Abin ma sai ya baiwa Smith dariya, ya murmusa ya ce, “Babu zancen raini a harkar aure, ka yarda dani Dr. Sulaiman, ka daidaita da matarka don samun lafiyar ka da nutsuwar dukkanin ku, sannan da albarkatun da ke cikin aure.
Poor Fati! Na tausaya mata, aure kusan shekara biyu ba ta san albarkar da ke cikin shi ba. Wallahi ka yi a hankali, tun hakki bai kama ka ba”.
Da maganganun Dr. Smith ya kwana, yana cizawa yana busawa. Ta yaya zai doshi Fati da bukatar aure? Gaskiyar Hadiza ne he is not taking things easy (ba ya daukar abubuwa da sauki). Fati yarinya ce mai hankali da zuzzurfan sani a addini, mawuyaci ne ta raina shi don ya gyara rayuwar auren su.
Ya juya a hankali ya rungume filo, ya samu kanshi da flashing no Fati, cikin shekara daya da rabi da ya yi bai taba kiran ta ba, don ko abin ya ciyo shi ya dauko wayar zai neme ta fasawa yake yi.
Yau dai ya tabbatarwa kanshi Fati ta ci kwallon, ta yi winning a kansa, ta kayar dashi warwas, duk da tana kidahumar ta. Kenan a so mutum, soyayya ta gaskiya ba ya nufin a nuna tsiraici, ko abubuwa na jan hankali. Halin mutum shi ne jarinsa, ‘yammata sai ayi hattara!
****
T
ana kwance a gadon bonon Inna, lokacin da wasu lambobi rankacau suka shigo cikin wayar ta. Ba a jima ba sako ya shigo.
“Ni na san ni mai laifi ne, amm ina neman afuwar ki kamar kullum. Fati, zan samu?”
Ta maimaita sakon ya fi sau hamsin, babu wanda ta sani a kasar waje sai mijinta Dr. Sulaiman. Ta mike ta yi sujjada ga Allah da ya karkato mata da zuciyar abin sonta, cikin addu’o’in da take kwana da yini tana yi.
Amma ba ta ba shi amsa ba, don ta dade da sanin shi hawainiya ne canza kala yake yi. Tana tsoron kar ta kara sakin jiki da shi ya zo ya sake guje mata kamar baya, bayan ta sakankance da shi ta amshi ban hakurin sa da soyayyar sa.
Tun yana sauraron amsa har ya koma ya jingina da balcony na harabar flat din shi. Ya kira wayar har ta gaji ta tsinke ba ta daga ba.
Ya san Fati ta yi fushi! Haba!! Ai ko shi ne, shekara guda da rabi ba kwana guda da rabi ba. Sai dai ya san sanyin halinta, da wuya su yi arba ya ba ta hakuri ba ta hakura ba.
Hankalin sa ya tashi sosai,
“Wallahi ka yi a hankali tun hakki bai kama ka ba”.
Ya tuno kalaman Smith, kirista ma kenan, balle shi da yake a cikin musuluncin sa.
Inna na tuyar masa, Fati na wankin kayan Nana a jikin famfo, sanye take da riga da zani na atamfa (super) ruwan ganye. Ta makala dan karamin hijabi iya kafadun ta. Babu wani make up a fuskarta, sai tsabar kyawun halittar tsurar sa.
Nana na gefe ta yi fes cikin fararen suwaita da (mini skirt) kanta ya sha ribbons da rufaffen takalmi da socks a kafarta, tana ta wasa da Saddika ‘yar Anti Ramatu.
Khalid ya soma shigowa da wasu firda-firdan jakunkuna, can kuma sai wani kamshi da ta dade da sani na turaren ‘Chris Adams’ ya bakunci hancinta, kamin ta gama tantance abin da ke faruwa ta jiyo ‘husky’ muryar Dr. na Hadiza suna gaisawa da Malam a soro.
Ranta ya yi fari, duk wani kunci da ke cikin zuciyar ta sai ya yaye, ta tabbata ya kasa hakuri ne da yin biris din da ta yi da shi, shi ne ya taho, ba zato ba tsammani.
Ba ta fasa aikinta ba amma kar ki so ki tona zuciyar ta, da soyayya ta yiwa illa mai yawa. Ji ta yi kamar an dauke numfashinta, tana shirin faduwa a gindin famfon, ta yi sauri ta kama kan famfon, harshen ta na addu’ar neman nutsuwa daga rabbil izzati.
Karasowa ya yi gindin famfon ya yi tsuguno a gaban ta, ya leka fuskar ta yana murmushi. Ta gan shi ya yi kyau, amma ya rame, fatar shi ta kara taushin gani a ido, ya zama cool kamar ba shi ba.
Ta yiwa Allah tazbihin kasancewar ta matar Dr. Sulaiman-Sulaiman Bakori, domin ba ba kowadanne maza ne irin Sulaiman ba, ko da ba ya son ta ai ya damu da ita, tunda fushin ta ya tunkudo shi har inda take.
Ya mika hannu ya dauki Nana yana sumbatar ta, fuskarta babu fara’a ta ce mashi,
“Sannu da zuwa”.
Hararar ta ya yi,
“Bana son sannun ki, rike abin ki”.
Inna ta fito daga cikin kitchen bakinta ya kasa rufo, suka wuce dakin ta yana dauke da Nana wadda ke ta kukan ya sauke ta don ba ta san shi ba.
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services