x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 16 - YAKANAH

  • 45001 words
  • 48000 words
  • Out of 84142 words

Category: Love Stories

Views 182

01 Aug 2025
Start ads
After Image Ads
juyo ba, ta ce,
"A haba Doctor! Wane ni in yi fushi? Mum dina aka kwantar a asibiti kuma ni nake jinyar ta sai jiya aka sallame mu".
Ya nuna tausayi tsantsa a kan kyakkyawar fuskarsa, a fili kuma ya ce,
" Am sorry….!"
Ta juyo don ta yi mishi murmushi, suka yi ido hudu da dan Inna Halima, wani chemistry yayi aiki cikin 'yan dakikai, ya kimsa wani al'amari mai GIRMA a zuciyoyinsu mai wuyar bayyanawa.

Gwiwoyinta suka yi sanyi, zuciyarta ta karye, duk wata soyayya da Allah ya halitta a zuciyarta ta hadu ta tattare ta dunkule a waje daya. To haka shi ma. Jikin shi ya ba shi wannan ita ce matar auren shi, wadda za ta samar mishi da 'ya'yan da zai yi alfaharin fitowar su daga tsatson ta. Ya ce.

"A bani address zan zo in duba Mamar mu".
Muryar Dr. Sulaiman har tsakar kan Hadiza.
Daga ita har Surayyah sai suka yi mutuwar tsaye, domin abune da ko da wasa basu taba kawowa ba. Kowa ya san shi da halin ko in kula da yake nunawa a kan mata, musamman dalibansa, wanda ke burge kowa. Don haka sun sha mamaki.
Ita Hadiza ta kasa magana, sai Surayyah ce ta rairayo mishi adireshin Hadiza. Ya ce,
"Idan na zo wa zan ce?"
Ta ce,
"Hadizah!".
Ya ce,
"Hadizahh, am I welcome?"
Ta yi murmushi ta ce, "
You are welcome, our humble consultant!!".


(The beginning of everything kenan ).

Tun daga wannan ranar kakkarfar soyayya ta kullu tsakanin Malamin da dalibarsa, kullum suna tare, a gida ne ko a ofis. Abin ya soma bayyana ga abokan aikin shi da abokan karatun ta, da manyan likitoci mata na bangarensa da ke yi mishi asirtacciyar soyayya.
Wannan ya janyo ma Hadiza hassada karara a wajen mafi yawan abokan karatun ta, to ita ma sai ta share su, saboda ta san Surayyah kadai ke kaunar ta saboda Allah.

***
10/15/21, 11:47 AM - Buhainat: Da wannan Sulaiman ya kashe bakin Hadiza da maganar ya kara aure, saboda ita ta nakasa. Don ta san cewa zai yi zai auri Dr. Surayyah, ita kuma in da abin da ta tsana ya fito daga bakin sa, to bai wuce wannan furucin ba.
Surayyar ba ta watsar da Hadiza ba, ta kan zo in ta samu sararin aiki kuma suna yawan yin waya. Tayi-tayi Hadiza ta koma aiki in ya so sai Fati ta dinga kula da zirga-zirgar ta amma ta ki. A ganin ta ita Fatin zaman ta kenan ba za ta yi nata auren ba? Ko ko haka za ta karar da rayuwar ta wajen hidimar ta alhalin bata kai ga cimma komai a rayuwa ba?
Gara ita ta kai ga matakin da duk dan adam ke burin samu; tayi ilmi, tanada kwali, tayi aure, ta hayayyafa. Don ta zauna gida a halin yanzu babu komi. Amma Fati fa?

Ta ce, "Surayyah mune bamu gane ba, ko da yake mu namu aikin mai tushe ne daga addini. Amma ba abin da ya kai mace ta zauna a dakin mijinta ta yi biyayyar aure dadi da kwanciyar hankali, amma ina amfanin da auren ki da mijin ki da 'ya'yan ki amma kin watsar dasu kin barwa mai aiki kullum kina titi, bayan mijin ya tsare miki dukkan bukatun ki na rayuwa?"
Surayyah ta ce, "Ke din ce dai kawai kin yi sa'a Hadiza, amma ba ko wadanne maza ne irin Dr. Sulaiman ba".
Kishi ya motsawa Hadiza ta hadiye shi mukut, amma ta san Surayya gaskiya ta fada, Sulaiman is unique, akwai wani simpleness a tare da shi wanda maza da yawa basu da shi.
Hadiza ba ta samu kwanciyar hankali ba sai da Dr. Surayyah Yahya ta kawo mata katin auren ta da Dr. Bashir Bunza, cike da shakiyanci ta nunawa Sulaiman. Ya karanta ya ciji yatsa,
"Shege Bunza, ya kasa ni!".
Ta kyalkyace da dariya ta ce, "Eh, to kai ne ka tsaya sanya".
Ya harare ta da idanun kauna, "Haka ma za ki ce? Bayan ke kika kashe min gwiwa, ai da tuni na karkata hula nasa kai, wallahi da ni zan kasa shi".
Ta sake yin dariya ta ce, "Oho dai, sai abi wani sarkin ba Ado ba".

****











Asabar ce sassanya mai dauke da wani irin lullumi mai sanya nishadi a zukatan dan adam, ana saura kwana biyar a kama azumin watan Ramadan, kamar kowacce asabar din karshen wata. Dr. Sulaiman ya zuba 'ya'yan shi a mota suka nufi Bakori ainihin gidan iyayen shi kamar yadda suka saba, can za su wuni, wani zubin har yamma ko dare. To yau ma hakan.
Gidan ya rage daga Hadiza sai Fati, don Alti ta je kauyen su Kukawa ganin gida za ta yi sati biyu tunda yaran ma cikin hutu suke. Fati ta tura Hadiza kitchen kamar yadda ta bukata, ita tana girki Hadiza na mata hira.
Ta ce, "Fati yau shekara guda cur da faruwar al'amarin nan, nayi-nayi ki kara neman wani admission din amma kin ki, kina nufin haka za ki yi ta zama kina yi min bauta ni da iyali na ba karatu ba aure? In don nice wallahi bana cikin matsala a halin yanzu I can take a good care of myself (zan iya kula da kaina) ko da a ce ni kadai ce a cikin gidan nan".
Fati ta sauke tukunya ta dora wata, ta yarfar da hannu don zafi. Sannan ta dubi 'yar uwarta,
"Yaya Hadiza ba zan iya barin ki ke kadai in tafi makaranta ba, ko na tafi tunanin halin da kike ciki ba zai barni in mai da hankali a kan karatun ba".
Ta yi murmushi, "Cewa nake watarana aure za ki yi Fati?"

Nan da nan Fati ta yi kicin-kicin da fuska, ta juya mata baya ba ta ce komi ba.
Hadiza ta ce, "Ko baki ji ni ba? Aure za ki yi Fati dole ba da jimawa ba, don haka ki tsaya ki gina rayuwar ki kamar yadda muka gina tamu, bana so saboda amfanin kaina ke in tauye ki. Don haka na baki kwana biyu ki yi tunani, an fara sai da JAMB na wannan shekarar, don haka ki nutsu ki kama abin da zai taimake ki ranar da bani.
Duk wata kauna da dan uwa na gari zai nuna wa dan uwansa kin nuna min ita, sakayyar ki na wajen Allah.
Sai dai ba zan bari ki kari rayuwar ki baki dandani zakin ilimin ko auren da na dandana ba, dole in samar miki future kafin Allah ya yi hukuncin da ya so a kaina....".

Fati ta yi saurin juyowa ta dubi Hadiza, domin a da ta bata baya ne. Ba ta gane abinda take nufi ba. Hadiza ta yi murmushin karfin hali ta ce,
"Fati zan gaya miki wani abu, amma bana so ki daga hankalin ki. Bani da lafiya Fati, amma don Allah ko Yaya ban yarda ki gayawa ba balle Sulaiman.
Fati na dade ina fama da ciwon kai wanda nake yi lokaci-lokaci, Sulaiman ya sani ina yawan fama da (migrain) amma bai taba zurfafa bincike ba, don ban taba gaya masa tsananin zahirin yadda nake jinsa ba.
Ba tare da sanin sa ba na je wajen Dr. Bunza mijin Surayyah, da ke likitan kwakwalwa ne, cikin sirri ya yi min bincike mai zurfi inda ya sanar dani ina fama da kansar kwakwalwa (brain cancer)".

Fati ta zazzaro ido ta sulale ta zauna a kasa, ta kai hannu ta dafe kirjinta, sai ga hawaye suna shatata! Hadiza ta yi murmushi ta matso da kujerar ta inda Fati take, ta dora hannu a kanta.
"A'a, Fati kada mu yi haka da ke, amanar rayuwata nake gaya miki, wadda bani da wanda zan bawa sai ke. Ba wanda zan iya gayama wa sai ke, ciwon bai yi tsanani ba, kuma ina shan magani a boye, ko Surayya ba ta sani ba.
Fati abin da ya sa na gaya miki don ki tallafa min ne, Sulaiman likita ne wanda ke bukatar kwanciyar hankali don samun (confidance) wajen gudanar da aikinsa na ceton rayuwar al'umma, idan ya ji wannan maganar ba zai taba samun kwanciyar hankali ba.
Fati Sulaiman yana sona, sosai, irin son da zai iya bani rayuwar shi, bana son abin da zai dagula masa lissafi, ki rike min amanata, ki rike min 'ya'yana, ki basu tarbiyya irin taki kada ki bari Sulaiman ya tagayyara a bayana. Ina son shi yadda yake so na, na so in ci gaba da rayuwa tare da shi, in ci gaba da haifa mishi 'ya'ya kamar yadda yake so, amma ban san ya ya Allah zai yi dani da rayuwata ba. Ki rike min Sulaiman Fati... bana so rashi na ya tagayyara shi........".
Zuwa wannan lokacin duka 'yan uwan biyu sharbe suke, na hawaye da majina.
Girki yana ta kauri, amma ba su kula ba. Fati ta rage sautin kukanta, ta ce,
"Shi brain cancer ba’a warkewa?"
Hadiza ta ce, "Ba a warkewa gaba daya, ko ya lafa zai tashi, amma ina kula da shan magani".
Fati ta yarfe hawaye ta ce, "Wannan ba abun boyewa bane Yaya Hadiza, ki daina fidda rai da rayuwa saboda ciwo. Insha Allah ke za ki aurar da Munib da Muniba, ya kamata ki sanar da Dr. domin ya taimaka miki da addu'a, duk wani hali da zai shiga ai shi musulmi ne ya san duk son da yake miki ya san bai kai wanda Ubangijin ki yake miki ba. If the condition become worse, ba tareda saninsa ba ba zai taba yafe miki ba.......!"

Hadiza ta yi shiru tana mamakin zurfin hankali irin na Fati, yarinya karama sai tunanin manya. Ta ce,
"Zan duba shawarar ki Fati, Allah ya kara min YAKANAH, ya bawa 'ya'yana tarbiyya irin taki. Ai dai za ki kula min dasu ko Fati?"
Cikin kuka ta ce,
"Yaya Hadiza ki daina yi min wannan maganar, bani da jarumtakar sauraron ta……".
Ta ce, "Na rantse da Allah idan baki yi min wannan alkawarin ba nima ba zan bi shawarar ki ba".
Cikin makyarkyatar murya ta ce, "Eh.......eh......na yi alkawarin zan kula dasu!!".
Ta ce, "To nima zan bi shawarar ki, amma ba yanzu ba. Tashi sauke tukunyar can tana kauri".
Ta share idonta ta mike ta sauke, ilahirin jikinta sai rawa yake. Ta kashe komi ta maido Hadiza falo, ta yi dakin su ta rufe ta fada kan gadon su ta soma girka kuka. Ta ga kukan ba zai amfane ta da komai ba, sai ta je bandaki ta dauro alwala, ta shimfida sallaya ta soma sallah, a kowacce sujjadarta tana yiwa Hadiza addu'ar Allah ya ba ta lafiya.
Wayar Hadiza ta yi kara, a lokacin tana bisa sallaya tana azkar, don haka ba ta daga ba har ta tsinke. Sai ya yo text, ta dauka ta duba.
Sulaiman ne yake gaya mata suna bisa hanya har da Inna Halima za ta zo ta duba ta kuma za ta ga likita, don haka a gyara mata daki don za ta kwana biyu.
Hadiza ta ji dadin zuwan Inna, domin Innar Sulaiman mutum ce har mutum, ma'abociyar raha da sanin mutunci. Don haka ta kira Fati a waya ta ce ta kara yawan abinci da ta aje a falo, ta kuma canza shimfidar gadon dakinta, don kullum a gyare yake Fati ba ta wasa da tsabtarsa.
Tara na dare dai-dai suka shigo, Inna dauke da Muniba da tayi barci a kafadunta. Hadiza da Fati suka yi mata sauka ta ban girma. Sai lokacin kwanciya ne aka kai ruwa rana da Inna, don ta ce ba za ta zaunawa Hadiza a daki ba, sai tare da 'yan jikokinta, dole suka kyale ta.

Duk juyin da Inna Halima ta yi a wannan dare, Fati take gani a kan sallaya, ta yi sallah, ta yi lazimi. Da asubahi kuwa ta soma rero (Suratul Yaseen) da sauti irin na Abdurrahman Sudaith. Kai ka ce daga masallacin Madinah aka kunno karatun. Saida tayi sallar asubah sannan ne ta dan samu barci.
Karfe shida ta fada kitchen ta soma aikace-aikace, Inna na hankalce da damuwar da yarinyar ke ciki, ta rasa abin da ke damun ta kankanuwa da ita haka. Bata uhm bata umhumh. Lokaci lokaci tana sanya gefen hijabinta tana dauke hawaye.
To haka a washegari ma, har cikin kitchen wannan yarinya ba ta rabo da hijabi da carbi, tun tana burge ta har ta koma bata tausayi.
Washegari litinin bayan sun yi kalaci, Inna da Sulaiman suka wuce asibiti in da za ta ga likitan ido (ophthalmologist), ba su dawo ba sai da rana ta take, yana sauke Inna ya juya ya koma ofis.

Sun fara cin abinci ita da Hadiza a kan darduma irin traditional carpet din nan na fata, an kuma shimfida ledar cin abinci. Don Fati ba ta cin abinci cikin mutane, loma ta farko, ta biyu, ta uku Hadiza ta soma kelayo amai kamar ta amayar da 'yan hanjinta.
Da sauri Fati ta shigo, Inna na rike da Hadiza, ita kuma ta kawo ruwa da roba Hadiza ta kuskure bakin ta. Fati ta sa moper ta gyare wajen, ta koma kitchen don hidimar abincin dare.
Ko me take yi cikin kitchen bakinta ba ya rabo da ambaton Allah, duk a kan lafiyar 'yar uwarta. Ita dai Inna haka nan ta ji Fati tana burge ta, tana bata sha'awa. Zahidah ce, babu duniya a gabanta, gata da dan banzan kyau da fata lafiyayya, amma ba sa gabanta, lahira take nema da harshen ta da goshin ta da gwiwoyin ta, ba ta furuci sai wanda ya zame mata dole, ko in an tambaye ta.
Amma a kwanaki bakwai da ta yi, Inna Halima babba ce mai cikakken hankali, ta lura Sulaiman ko ganin Fati a gidan shi ba ya son yi, don dai ba yadda zai yi ne, kuma bai son abin da zai bata ran Hadiza.
Suna falo ita da Sulaiman misalin karfe sha daya na dare suna hira a nutse irin ta da da mahaifi, ta ce, "Wai ni mai sunan Malam me yarinyar nan kanwar Hadiza ta yi maka ko kallon ta ba ka yi? Dazu da safe ina kallo tana gayas da kai ka dauke kai ka fita, haka tun zuwana ban taba ganin ka yi mata magana ba, balle wasan nan irin na mijin ya da kanwarta. In kana wuri ta shigo sai ka tashi, in kana falo ta ganka sai ta koma ta yi ta zaman daki. Ita da ganin 'yar uwarta sai in baka nan, mene ne manufar hakan?"
Ya juyo yana kallon Inna kasa-kasa, yace, "Wacce yarinya kike magana?"
Ta ce, "Fatima".
Ya ce, "Fati wai?"
"Eh, ita".
Ya yi shiru kamar bazaiyi magana ba yayinda Inna ta kura masa ido cikin tsananin son jin amsarsa, ya rausayar da kai ya ce,
"Raini ne bana so, kuma ni ban iya wani wasan kanin miji ko kanin mata ba".
Ta yi sakale tana jin sa, ta ce, "Hala wani laifi ta yi maka? Har Hadiza na lura ranta yana baci da irin halin ko in kulan da kake yiwa 'yar uwarta. Ban san ka da bakar zuciya ba, kada ka a fara a kan FATIMA, domin mutum ce cikin 'yammatan da babu irin su a yanzu, wannan yarinyar tana da halayen 'yan aljanna, ka yi a hankali baka sani ba ko waliyya ce".
Shi abin ma sai ya ba shi dariya, ya ce, "A wannan kalatacciyar duniyar tamu dama akwai sauran waliyyai Inna?"
Ta harare shi ganin ya bagarar da zancen cikin wata siga ta daban, ta cigaba da magana cikin kakkausar murya.
"Dariya ma kake min?”
Ya yi saurin cewa, "A'a, yi hakuri Inna ba dariya nayi ba".
Ta ce, "To ka gyara ma'amalar ku, zai fi kyau a ce akwai kyakkyawar alaka a tsakanin ku ko saboda Hadiza, in ta gaishe ka ka dinga amsawa cikin walwala da sakin fuska, wanda ya rike ibada ba ya wulakanta a duniya da lahira Ubangiji kansa girmama shi yake. Baka sani ba ko ta fi ka matsayi a wajen Allah, ka canza takun ka a kanta, rayuwa baa yi mata haka, don sauyawa take kamar WAHAINIYA ta inda bama tsammani. Ai ba haka na ga kana yiwa su Ruma ba, to matsayin ta daya dasu a gare ka, ka ji na gaya maka".
Bai ce komi ba ya jawo wata hirar, don dai a sauya wannan. He is not interested at all (Fati is not the kind of person he wanted to relate with), wato ba ta daga cikin irin mutanen da yake son yin mu'amala dasu akan dalilai masu yawa. Wadanda in aka ce ya zano akan karan- kansa sai ya ji su masu rauni da rangwamen muhimmanci (null and invalid ). Amma daga ciki ya san akwai gudun RAINI da rashin son sa da WASAN KANIN MIJI. Sauran hujjojinsa kuma ai a sarari suke; jinin su bai hadu ba, don yana son Ya, ba dole sai ya yi wata kakkarfar alaka da kanwar ta ba, bayan wadda musulunci ya ce, don haka ne baya damuwa ba ‘hypothesis’ din kowa akan ma'amalar sa da Fati, ai ba abokiyar wasan shi ba ce, kanwar shi ce.
****

Kwana bakwai din da Inna Halima ta yi jinyar Hadiza suke ita da Fati, komai ta ci sai ta amayar, ga zazzabi da ciwon kai mai zafi, sai ta rike kanta idan ciwon ya motsa mata tana wani irin kuka mai keta zuciyar duk mai imani.
Sulaiman da farko bai sani ba, don ya dauka laulayin ciki ne irin wanda ta saba, kuma ciwon baya tasar mata da daddare lokacin da suke tare kenan. Ita ma Inna ta lura ta san laulayi ne na sabon ciki, amma wannan buga kan da Hadiza take yi a jikin bango da kukan da take yi na azaba ta fahimci akwai dai wani abun, amma tana ganin dukkan su likitoci ne sun san abin da ke damun ta, kuma ta ga Hadiza tana shan magani, sai ba ta yi magana ba, amma dai ba ta taba ganin irin wannan laulayin cikin ba.
Don haka ta kara sati saboda lafiyar Hadiza wadda ta daina cin komai sai ruwan bakin lipton da ruwan tsamiya. Gaba daya ta rame ta fita hayyacin ta, ba ta taba yin cikin da yake wahalar da ita irin wannan ba.
Tun Sulaiman bai gane ba har ya fahimci Hadiza ba ta da lafiya sosai, wannan ya wuce laulayi kuma wannan (migrain) yana bukatar bincike.
A daren ya fito daga wanka yana tsane kanshi da dan kankanin towell, tana kwance rigingine a
End Ads