halinta. Ji ta yi kamar an kawo ta kabarin ta, ta yi kuka ta yi kuka har ta gode Allah. A karshe ta tattara komi ta mikawa Allah, ta jawo kular da Inna ta ajiye mata ta debi abinci tana ci.
Ai ba ta tashi jin tsoro ba, sai da karfe tara na dare ya yi, Fati ba ta taba kwana a gidan da babu mutane ba, ta tabbatar ita kadai za ta kwana a wannan katon gida, don tuni ta san Dr. Sulaiman ya saba aikin kwana.
Jikinta ya soma mazari kamar ana kada mata gangi, ta daddage ta takure a can karshen katifa ta kudundune cikin bargo tana dakacen ina ma ita ce ta tafi, Hadiza ta zauna, ko babu komai Hadiza ta fita bukatar rayuwar.
Na farko tana aikin lada, ta hanyar ceton rayuwar mata ‘yan uwanta. Na biyu tana da 'ya'ya tana kula da tarbiyyar su da rayuwar su, na uku tana da mijin da ke son ta suke rayuwa cikin so da kaunar juna.
To amma ita fa? Babu sidi babu sadada. Ba ta kai karshen tunanin ta ba ta ji karar fashewar tangaran a kitchen, wannan ya tabbatar mata ba ita kadai ce a gidan ba, to wane ne? Ta san dai ba maigidan bane, don shi in ya dawo karfe shida ba ya kara fita sai takwas, ba kuma zai dawo ba sai past ten sai dai in yana da aikin kwana.
Ta ji dan tsoron ya ragu, ko ba komi tana da confidence na cewa akwai mutum cikin gidan ba ita kadai ba ce. Ta mike ta fito ta nufi kitchen, wanda ba ta zata ba shi din ta gani, ya tara hannu cikin famfon sink yana wanke jinin da ke bulbula daga hannun sa, ga kuma kwai yana ta kauri a kan cooker.
Ta karasa da sauri ta sauke, ta kashe gass din. Ta dauki tsintsiyar laushi ta soma tattare fasashshen tangaran din, kafin ta farga ya fice a kitchen din yana ta disar da jini a kan tiles.
A take ta hada wani kwan ta soya masa, ta juye a farantin tangaran ta debi ‘cake’ samosa da spring roll cikin firji ta dumama a microwave , ta tafasa ruwa nan da nan ta juye a karamin tea flask ta kwasa ta yo falo don ta bashi.
Ya tada kai da karamin filo yana kwance a tsakiyar kilishi, sanye da fararen riga da wando na barci marasa nauyi, har yanzu dan yatsansa bulbular da jinni yake, amma bai damu ba, kamar ba jikinsa ba, ta zo gaban shi ta russuna ta aje mishi, sannan ta sanyaya murya ta ce,
"I'm sorry!".
Bai kalle ta ba, haka bai amsa ba kamar bai san Allah ya yi ruwan tsirar ta a gun ba. Kai bangaren data ke ma bai kalla ba. Ta mike za ta koma daki cike da tunanin hannun shi da ke ta kwararar da jini, amma matsayin shi na likita bai yi wani kokari ba ko yaya ne don dakatar da gudun jinin ba.
Ta san da Hadiza tana nan Allah kadai ya san irin gigicewar da za ta yi, sannan za ta sa mishi magani ne ta daure, sannan ta yi ta jinyar ciwon har sai ya warke.
Hakan ya taba faruwa da ya sharce babban dan yatsan sa garin ferar tuffaha, irin wannan kulawar kenan Hadiza ke nufi ta yiwa mijinta? Da kamar wuya wai gurguwa da auren nesa.
Aka ce wargi ma wuri shika samu; ko fuska babu, ba ta son tuno yadda ya yi da fuska kaman an aiko mishi da manzon mutuwa lokacin da ta shiga kitchen din.
Ba ta kai ga shiga daki ba ya yi mata wata irin tsawa wadda ta gigita ta, ya ce,
"Ke!"
Ta juyo da sauri. Ya ce,
"Zo ki batar min da wannan shirgin naki a nan, na ce da ke ina bukatar taimako ne?"
Jiki na rawa ta dawo ta russuna za ta dauke, ya kama fatar kunnuwan ta da riko mai karfi, ta sa kuka don azaba. Ya ce,
"Daga yau sai yau kada ki kara shiga shirgina, ko me za ki ji na yi kada ki zo inda nake, tunda ban neme ki ba. Na yi kama da saurayin ki ne? Be careful ni Yayanki ne, mijin Yayarki, Hadiza. Idan kin manta in tuna miki. Tun da kin yarda a kawo ki ki yi zaman 'ya'ya ki lalata kuruciyar ki a banza, to ki yi ta yi. Ranar da kika gaji, ki gaya min in maida ke gida, kina ji na?'
Cikin kuka ta daga mishi kai, ya saki kunnen ta ya ce, "To kwashe su a nan tun ban yi ball dasu ba, kema in babballaki". (Yana nuna wa da hannayen shi irin yadda zai babballa ta din).
Jikinta na kyarma ta kwashe ta yi kitchen dasu, ya ja tsaki "Tsuu…." A ranshi ya ce,
"Kai! Inna da Malam sun takaice ni wallahi, me zan diba a jikin wannan fingi-fingin?" Ya yi ball da filon da yake kwance ya mike ya nufi (exercise area) din sa.
Fati bata daddara ba, washegari tunda ta tashi da asuba ba ta koma ba, kitchen ta shiga ta shirya kalacin funkason alkama da miyar agushi. Wanda ta kwaba tun daren jiya. Ta kara da Quaker oat da plantain soyayya ta aza a ‘master dining’ din shi kamar yadda ta ga Hadiza na yi.
Da gudu ta koma daki ta kulle, yana fitowa zai fita rike da ‘brief case’ ya yi tozali da sabbin warmers, sai kamshi ke tashi bisa dining din shi. Da gaske yunwa ta gallabe shi, hanjin cikinsa har rawa yake. Sai dai yana ganin idan ya ci ya zama sakarai tunda ga abin da ya ce da ita jiya, kuma raini zai gitta.
Don haka ya hadiye azababbiyar yunwar shi ya fice. yana shiga AKTH ya nufi gun cin abincin manyan likitoci na asibitin, can ya yi kalacin sa. Sai dai a bakinsa babu dandano, don Hadiza ta riga ta sangarta shi da cimar Fati mai dadin da ba ya misaltuwa, ya kuma fi na Goggo Alti wadda a da yake ganin babu wadda ta kaita iya sarrafa abinci, musamman na Hausawa wanda ya fi kama mishi ciki kasancewar shi ma'abocin tara yunwa kafin ya yi quenching din ta.
Da ta tabbatar ya fita, ta fito ta bude ma’adanan abincin, babu abin da aka taba. Bata ji haushi ba, ta tattara ta mikawa Malam Ilu bayan ta dibi iya wanda take ganin za ta iya ci, ta koma daki ta yi wanka sannan ta zauna cin abinci.
Tana kammalawa wayarta da ta sa a caji ta yi kara, ta amsa cikin kamilalliyar muryar ta, Inna ce. Suka gaisa, sannan ta mikawa Malam Sulaiman shima suka gaisa.
Ya yi mata addu’a sosai, ya kara da cewa, ta jure duk wani rashin jin dadi da za ta fuskanta daga mai sunan shi, nature (halittar shi) kenan, fara nuna kiyayya ga abu kamin ya so shi. Da yardar Allah watarana za ta tashi da riba.
Ranta ya yi fari, zuciyarta ta yi haske, a kalla ta san ta samu surukai na gari da ke son ta. Ta kara jin karfin gwiwar son ci gaba da kyautatawa Sulaiman, ba don ya yabe ta ko ya so ta ba. Ita ma ba son na shi take yi ba, sai dai ba za ta iya yin watsi da al’amarin shi kamar yadda ya bukata ba, saboda alkawarin da ta daukar wa Hadiza, ta tabbata sakayyar ta na wurin Allah.
Don haka ta mike ta nufi dakin shi don ganin ko akwai gyararrakin da za ta iya, cikin sa’a rufe kofar kawai ya yi amma bai sa key ba.
Ta murda ta shiga cikin sallama duk da babu kowa, wannan tarbiyya ce mai kyau sabida mala’ikun rahma. Dakin babu kintsi, ko ina takardu baja-baja, gado a yamutse, kayan wanki a toilet fal cikin kwando.
A jikin bed side ta yi tozali da ‘yar uwarta tana murmushi. Ta karasa ta dauki ‘frame’ din hoton tana shafawa a hankali tana murmushi itama, hawaye fal idanun ta.
Ta maida shi mazaunin shi ta nade hannun riga ta soma gyara komai neatly, ta cire bed sheet ta canza wani. Ta kunna A.C don dakin ya yi sanyi.
Ta koma toilet ta hau wankin da ya dauke ta har zuwa azahar, ta fito da kayan inda suke shanya ta shanya, ta wanke bandakin sosai da parazone, sai daukar ido yake, ta jawo kofofin ta fito ta soma aikin falo wanda babu datti sosai don su Inna sun tsaftace ko ina kamin su tafi.
Zuwa la’asar kayan sun bushe, sai tashin kamshin Dr. Sulaiman suke kamar yanzu aka fesa turaren gidan (Chris Adams) ba’a sanya su a omo ba.
Ta yi shimfida a falo ta soma goge su da dutsen guga, ta kammala cikin dan lokaci, ta je ta jera mishi a wardrove ta kunna burner ta turare dakin da bandakin da touch me, sannan ta fita ta koma dakinta ta yi wanka ta kwanta tana hutawa.
Bai dawo gidan ba sai goma na dare, nan ya soma shakar daddadan kamshin amarcin da gidan ke yi, ya kara cin karo da sakon Fati a kan dining cikin wasu flasks din asu zabar kyau ba na dazu ba.
“Wato yarinyar nan ba ta jin magana”.
Ya fadi a zuci.
Ya danna kai dakin shi, kamar ya sume don daddadan kamshin da dakin ke yi, da wata ni’ima ta musamman dake fita, wanda ya gauraye da rabar split mai sanyaya zuciya da kasalantar da gangar jiki.
Ya bude wardrove don ya sauya kaya, nan ma ya cimma sakon Fatima Ja’afar Mai-Yadi. Ya girgiza kai ya ce,
“Na san maganin ki tunda baki da zuciya”.
Washegari ma Fati ta kara yin kalacin kunun tsamiya dan leda, da poncake ta aza dining. Yau ma da ya gani wucewa yayi yana girgiza kai, cikin ransa yake fadin.
“Lafiya ce ta yi miki yawa kike losing energy din ki a banza!”.
‘Surely’ yana bukatar abincin, amma girman sa da yake tattali a idanun ta ya hana shi. In ya ci girkin ta ashe tana da amfani cikin gidan kenan, shi kuma so yake ya nuna mata da ita da babu duk daya. Babu wani amfani da mace za ta yi masa tunda ya rasa wadda yake so, ya jure rashin Hadiza ma balle rashin cin abincin da yake so?
Haka suke ta gangarawa har tsayin sati guda. Ranar lahadi yana gida, Mukhtar ya yi sallama ta hanyar danna kararrawa.
Ya tashi daga kan computer ya je ya bude, Mukhtar Ja’afar ne rungume da Baby Nanah, Munib da Muniba na biye da shi, suka rangada da gudu suka rungume mahaifin su.
Shi ma ya rungume su yana bin kowannen su da sumba, idon shi a lumshe. Suka karasa cikin falon shi da Mukhtar, Mukhtar ya mika mishi Nana, ya karbe ta ya rungume yana sunsunar ta. Sannan ya tsaya yana kallon ta, kamannin shi da ita har sun yi yawa.
Suka yi musabiha da Mukhtar, yake gaya mishi Inna ce ta yi waya ta ce a kawo su wajen babar su. “Ina Fatin ne? Ko barci take?”
Cikin dauriya ya ce, “Bari in duba”.
Ta fito daga wanka ke nan tana rufe kofar bandaki, karamin towell ne ta daura daga kirji zuwa cinyoyin ta, kanta cikin hular wanka, tana jona hand dryer don busar da gashin kanta da ya jike.
Ya turo kofar ya shigo, idanun shi suka yi kyakkyawan gani, shi kadai ya san abin da ya tsirga daga yatsar kafa zuwa zuciya da kwakwalwar sa, ashe model yarinya ce a cikin HIJABI?
Kallon second biyu ya yi mata ya dauke kansa, sannan ya juya da sauri cikin kakkausar murya ya ce,
“Mukhtar ke kiran ki”.
Ta zubo doguwar rigar shadda ‘dark-bluesenegalese’ ta dora da matsakaicin hijabi, ta tadda su a falon.
Ai kuwa su Munib suka yo tsalle suka yo kanta, har suna kokarin kada ita. Itama ta rungume su, suka soma jero mata tambayoyi.
“Anti Fati, Mummy ba ta dawo ba har yanzu? Ina kika tafi muka daina ganin ki? Nana tana ta kuka idan bakya nan, don Allah kar ki kara tafiya ki barmu…..”.
Ta ce, “Ba zan kara ba”. Ta kamo hannun Muniba, “Ba inda zan je muna tare kun ji my kids?”
Suka yi murmushi sannan ta karasa ta russuna ta gai da Yayanta, wanda suke ta hirar su shi da Sulaiman, ta nufi firjin kitchen ta kawo mishi lemon (Donsimon) da gorar ruwan (Eva) mai rangwamen sanyi.
Mukhtar bai dade ba ya yi musu sallama ya tafi. Bayan ya karbi lambar Fati. Tana so ta karbi Nana amma tana bisa cinyoyin sa, ta fara kuka don ta dade ba ta sha madara ba.
Dole ya mika mata ita, hannuwan su suka saka kara gogewa dana juna. Wasu irin hannuwa gareta masu bala’in taushi kamar auduga, wadanda suka tada tsigogin jikinsa. Ita kuma suka haifar mata da kasala irin wadda ta ji a ranar da hannun ta ya fara shafar nasa.
A hanzarce ya mike, “Oya kids! Muje mu sha (Ice-cream)”.
Suka yi tsalle suka dane kafadun shi, Munib ya ce,
“Amma har da Anti Fati za mu je?”
Ya yi kamar bai ji shi ba, ita dai jakar kayan su ta dauka ta yi ciki da Nana a hannun ta. Ya sunkuci yaran shi duka biyun a kowanne hannu daya du girmansu, suka yi waje.
Dama tana da tafasasshen ruwa cikin filas a kitchen, nan da nan ta dama madara ta soma baiwa Nana bayan ta sha iska.
****
10/15/21, 11:47 AM - Buhainat: 2
Karfe goma sha dayan dare garin Kano ya yi tsit, sai iskar hunturu da ke kadawa. Malam Ja'afar ya dauko tabarmar sa ya shigo cikin gida daga soron kofar gida.
Zai gifta ta dakin Fati ya jiyo shesshekar kukan ta, ya dakata ya daga labulen yana kallon ta, tana zaune a kan darduma ta kunshe fuskar ta cikin hijabi sai kuka take.
Ya karasa shigowa cikin dakin ya ce,
"Fadimatu kukan me kike yi?"
A razane ta cira kai ta dube shi idanunta jawur, sun yi luhu-luhu alamar ta yi kuka har ta gode Allah. Malam Ja'afar ya zauna a wata 'yar kujera da ke dakin yana fuskantar diyar sa. Nanah ta soma motsi alamun za ta tashi daga barcinta, ta soma rirriga ta.
Ya jima bai yi magana ba sai da Nana ta koma barcin ta ya ce,
"Gaya min damuwar ki Fadimatu, ni mahaifin ki ne".
Ta share idon ta da hankici, ta ja shessheka kafin ta ce,
"Baba babu komi".
Ya jima yana kallon ta, sannan ya yi murmushi ya ce,
"Kina tuhumar mu da yi miki auren da baki so, auren mijin 'yar uwar ki. Ki yi hakuri, alheri muke nufin ku da shi, ba za ku gane ba sai nan gaba, idan kun gano gatan da muka yiwa rayuwar ku".
Fati ta yi shiru tana sauraron Baban su, ta ga cewa wannan ita ce damarta ta karshe, daga gobe za a zarga mata igiyoyin wanda ta tabbatar ba ya son ta. Ta kai kanta kasa tana kuka sosai, ta ce,
"Ku yi min alfarma Baba, Baba baka taba sani in yi wani abu na shallake maganar ka ba, amma a wannan karon, ina so ka duba hujjojina.
Baba Dr. Sulaiman ba ya sona, Baba Dr. Sulaiman ya fi karfina, bani da ilimin da zan jera da shi a matsayin matarsa. Baba Sulaiman ba zai taba son wata ba, bayan son da yake yiwa Yaya Hadiza. Baba kune baku sani ba, amma Dr. Sulaiman tun fil azal ya tsane ni, ban san laifin da na yi masa ba.
Ban taba gaishe shi ya amsa ba, haka bai taba duba na a matsayin jinin Hadiza ba, balle ya yi la'akari da wannan ya kaunace ni. In dai don 'ya'yan shi ne ai nima 'ya'yana ne, zan ci gaba da rike su ba sai na zama matarsa ba".
Ya ce,
"Amma za ki zama matar wani ko? Kuma babu wanda zai aure ki da zugar 'ya'yan Yayar ki? Da ‘yar uwarki ta damka miki amanarsu?
Na ji hujjojin ki Fati, na kuma yarda bazaki yi mun karya ba, amma nima ina so in tambaye ki.
Wane abu ne Hadiza take da shi wanda ya kaita ga matakin zama matar babban likita irin Sulaiman? Tana 'yar talakawa kuma mace kamar ki?"
Babu dogon tunani ta ce,
"Ilimi".
Ya ce,
"A ina ta samu?"
Ta ce,
"Fita ta yi ta nema".
Ya ce, "In haka ne ke mai zai hana kema ki fita ki nema?'
Ta ce,
"Ba zan iya irin nata ba!"
Ya yi murmushi ya ce,
"Duk ilimi sunan sa ilimi, balle ilimin ki ya fi na kowa, yafi na komai, ilimin Alkur'ani ne da ke wanda ya kunshi dukkan rayuwar duniya da lahira baki dayan ta, ke din nan ba abar wulakantawa ba ce 'yar baiwa ce, mahaddaciyar Alkur'ani, wallahi-wallahi a rayuwar duniya da lahira ba za ki tozarta ba.
Sannan don kina gaishe shi bai amsa ba, sai ki ce ba ya son ki? Me kika yi masa? Mutum ne mai kyakkyawar zuciya, shekaru dai-dai har bakwai da nayi tare da shi ban taba ganin wata halayya ta banza a tare da shi ba.
Tunda ya auri 'yar uwar ki ba’a taba jin kansu ba, ba ta taba yin yaji ba, ba ta taba kawo karar shi ba. Sai ki yi tunanin me Hadiza ta yi ta samu wannan mafificiyar soyayya a zuciyar mijinta, tunda kin zauna da ita, kema ki kwatanta ko ba duka ba, ki gani idan ba za ki samu ba?".
Ta share ido ta ce,
"Baba ai ni gani na yake 'yar kauye, ga shi ni kuma ba zan iya yin irin rayuwar su ba. Mai ya sa ba za ka gane ba? Banida abinda zan burge shi da shi. Don Allah Baba ka aura min ko wane ne, komi yawan matansa da yawan shekarun sa, na rantse zan zauna da shi, amma kada ka kai ni inda ba zan yi kwarjini ba, inda za a wulakanta ni, inda ba za a so ni ba….".
Ya yi murmushi ya ce, "Babu inda zan kai ki sai gidan SULAIMAN! Na kuma tabbatar miki ko a yanzu bai son ki, watarana na zuwa da za ya so ki. Kamar, ko ma fiye da yadda yake son 'yar uwarki.
Daina kukan nan kada ya haddasa miki ciwo, a duk sanda ki kai sujjada cikin sallolin farilla ki