x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 27 - YAKANAH

  • 78001 words
  • 81000 words
  • Out of 84142 words

Category: Love Stories

Views 194

01 Aug 2025
Start ads
After Image Ads
sa, amma ni ko ya ya dai?”
Idan kuwa ka yi karo da jahili, sai ka ce, “Dubi wani yana sabon Allah cikin rashin sani, ni kuma ina yi cikin sani. Ga shi kuma ban san yanda karshen sa zai kasance ba, kuma ban san nawa karshen ba. Ko me zai zama a nan gaba? Allah shi ya fi kowa sani”.
Idan kuwa ka gamu da kafiri, sai ka ce da kanka, “Wa ya sani? Watakila nan gaba ya musulunta kafin ya mutu, kuma wa ya sani ko ni kuma in mutu a kafirce?”
Ire-iren wadannan maganganun gaba daya suna nuni da halin mutumin da YAKANAH da tawali’u suka baibaye shi, yake kuma cikin hali na binciken kansa a koyaushe.
Dalilin irin wannan tunani a zuciyar wannan bawan Allah shi ne, yana cikin yanayi na rashin yarda da kansa. Tare da rashin tabbas game da abin da zai abku wajen haduwar sa da Allah.
Ire-iren wadannan tunani kuwa suna nuna karfin imani ne da dogaro da Allah madaukakin sarki wanda shi ne tushen kaskantar da kai.
A kowanne lokaci idan bawa ya kaskantar da kansa, Allah zai kare shi daga masifu, kuma ya ba shi sirrin “Ikhlasi” Wato nacewa da son bin hakikar gaskiya a dukkannin al’amuransa na yau da kullum. Daga wannan mataki ne mutum zai kasance cikin mutane ‘yan kadan wadanda suka samu yardar Allah tare da kusanci da shi.
YAKANAH ita ce kofar da ake bi ta cikinta zuwa wurin da baiwar Allah da rahamar sa suke muhimmancin YAKANAH ga musulmi kamar kwatankwacin bargo ne a cikin kashi.
YAKANAH tana a matsayin bargo na Ibadah, kuma sauran ayyuka suna a matsayi na kashi. Bayin Allah wadanda ake kira ‘zahideen’ masu cike da da’a da tsantsenin duniya, tare da ‘nasiqeen’ masu sadaukar da rayuwar su domin bautar Ubangiji, dukkannin su suna ji da wannan baiwa ta YAKANAH.
Bayin Allah masu YAKANAH basa yin maganganu barkatai, basa yin tsegumi ko wata muguwar magana a game da wani a bayan idanun sa, su kan fadi abin alheri ne a game da shi. Ba sa shiga sharo ba shanu, kuma zuciyar su fes take. Ta kuma nisanta da miyagun dabi’u, kamar hargowa da JI DA KAI. Wato kirjin irin wadannan bayin Allah garau yake.
Duk maganar da irin wadannan bayin Allah masu YAKANAH suka fadi, ta dace dai-dai da abin da suka yi, suka kuma yi imani da shi.
Basu da wani abu da za su boye a zuciyar su domin kada wani ya sani, wato basu da wani mummunan abu a tare dasu.
Bayin Allah ne masu zallar gaskiya da rikon ta, wanda duk ya yi hulda da irin su zai ga cewa basa fafutukar neman kuskure a kan wani, maimakon haka, a shirye suke wajen neman kuskure daga wajen su, wato a kan kansu.
Basa yarda su zauna tare da (marada) (masu kawo tsegumi). Don haka ‘yan uwa musulmi mu yi damara da kokarin kasancewa cikin bayi masu YAKANAH, mu rike addininmu, mu kama Alqur’anin mu, mu suturce jikinmu, mu tsayar da sallah domin samun dacewa a duniya da lahira. Kamar jarumar wannan littafi, Allah ya bamu iko amin summa amin.
Takori
10/15/21, 11:47 AM - Buhainat: Yakanah
10/15/21, 11:47 AM - Buhainat: Tana ganin sanda sulaiman ya saki wata boyayyar ajiyar zuciya.
Inna ta ce, “To Allah ya yi muku albarka”.
Ya gyara zamansa cikin nutsuwa yace,
“Inna dama na zo in yi muku sallama ne….”.
Cikin mamaki ita da Malam suka hada baki suka ce, “Zuwa ina?”
Fati kuwa zuciyar ta ce ta buga, irin bugun da ba ta taba yi ba. Ya soma yi musu bayanin course din da aka zabe su su goma shi da abokan aikinsa na shekaru biyu a cikin jami’ar Chicago din Amurka.`
“Amma tare za ku tafi da iyalinka bakidaya ko?” Malam ya tambaya.

Ya ce a ransa, “An yi ba’a yi ba kenan! Fatin yake gudu, Fati yake son tserewa, Fatin yake so yayi nisa da ita, Fatin yake son yiwa kandagarki daga son kutsowa cikin rayuwarsa da karfin gaske, bai shiryawa hakan ba, bai taba mafarkin kasancewar hakan ba, kada ta rushe masa plan din rayuwa, in ya dauke ta suka tafi me aka yi ke nan? Bonono rufe kofar da barawo?
Duk da shi ma ya soma kalubalantar kansa da ganin wautar sa na tsallake abinda rai da zuciya suka soma so da gangan, wai don kada GIRMA YA FADI!”.
Ya ce, “A’a, za su zauna ita da Alti saboda yara suna zuwa makaranta”.
Malam ya ce, “Kun yi shawara ne ta yarda za ta zauna?”
Bai iya karya ba, kai tsaye ya ce, “A’a, bamu yi zancen ba”.
Ya ce, “To sai ku yi shawara a tsakanin ku can, in ta yarda za ta zauna din shikenan, mu ‘yan sanya albarka ne”.

Ba su taho ba sai yamma lis, kamin su iso gida har an yi kiran isha’i, kasancewar duk a koshe suke, Inna ta cika musu ciki da dambun shinkafar ta mai dadi, basu shiga kicin ba kowacce ta nemi makwancin ta, yaran ma sun nabba’a a dakin su, shi kuma ya juya asibiti.

Fati tana shiga daki ta kwanta rub da ciki, da filo a karkashin ta cikin wani mawuyacin hali na soyayyar Baban Munib da ke cin zuciyarta. Ta kai hannu ta dafe kirjin ta wanda ke bugawa da-sauri-da-sauri da haruffan SU-LAI-MAN a kowacce dakika, zai tafi ya barta, bayan ya gama da farauto zuciyarta, ya kimsa mata soyayyar da ba ta san iyakacin ta a zuciyar ta ba.
Ya warware duk wata nutsuwa da tunanin da ke tare da ita, ya mamaye 80% na zuciyarta. Ya haifar da wasu al’amura masu girma a gare ta da ba ta san ya ya za ta yi dasu ba.
Jin tafiyar shi take har ruhi da bargon jikinta, Fati tace wai maiyasa wasu mazajen suke haka ne? Idan sun san sun kimsa maka soyayyarsu, sai su nemi gudu su barka da jibgin abar ka?
Wasu hawaye suka zubo, maimakon ta share sai ta tara hannu tana tarar saukar su a kan tafukan ta. Ba ta ji motsin bude kofa ba sai alamar zaman mutum a gefen ta, kafadunsu suka gogi na juna, ta yi hanzarin juyawa, Dr. Sulaiman ke kallon ta da murmushi.
Ya sanya hannu cikin aljihun bakin jeans da ke jikinsa, ya zaro hankicin sa ya mika mata, ta jima ba ta karba ba, daga karshe ta karba ta share ambaliyar hawayen ta.
Ya mika mata hannu alamar ta ba shi abinsa, sai ta kalle shi sannan ta sunkuyar da kai ba tareda ta bashi ba.
Ya ce, “Bani mana? Ko kukan bai kare bane?”
Ta tsuke fuska, ta tsuke baki, ta hade girar sama da ta kasa.
Ya yi murmushi ya sa hannu cikin hannunta ya dauke hankicin sa, kadan ya rage ta sume da hucin sassanyan numfashin sa ya doki fuskar ta, kamshin jikin sa na fizgar ta, da wata itin fizga mai karfi, kamin ta farfado daga shidewar da ta yi na wucin gadi ya fice a dakin.

Zuwa can kuma ya dawo da takardu a hannun sa, sai dai wannan karon ya janye murmushin da ke kan fuskar shi, ya zauna dab da ita cikin kakkausar murya ya ce,
“Me ya sa ki kuka?”
Shiru ta yi masa ba ta amsa ba, zuciyarta na ci gaba da azalzala da azabar soyayya, wadda ke linkuwa a bayan kowacce dakika. Jikinta ya soma rawa, tana son cewa ya tashi ya ba ta waje ta samu iska amma ta kasa. Kallon ta yake yana (observing) da ido, da zuciya. Gaba daya yanayin ta ya sauya, ya nuna wata mace da ke azabtuwa da soyayya da sha’awar mijinta mai yawa.
Amma kawaici da kau da kai ya rinjayi komi, ya tabbata idan ya tafi ya bar ta cikin wannan halin, Allah ba zai yafe mishi ba, amma tunanin Hadiza ya danne komi. Tattalin girmansa da mutuncinsa a idanun yarinyar ba zai bar shi ya aiwatar da abinda zuciyoyin su da gangar jikin su ke so ba, idanun shi a juye yake kallon ta, gangar jikin shi babu inda bai kaduwa. Ya soma kokarin saisaita kansa, in azabar soyayya ce ai ya fita dandana, ba tun yau ba.
Ya janyo brief case ya fiddo daurin kudi masu tudu ‘yan awolawo ya ajiye a gefen ta, sannan ya mika mata form din JAMB Online.
Ta dan ware ido tana kallon sa da alamar jin dadin hakan sosai a kwayan idanun ta, ya kawar da fuskar shi gefe ya ce,
“Zan bude maku account da skyeBank in Allah ya kai mu gobe, in na wajen ki sun kare kuna da bukata sai ku je ku diba. Akwai sabon direba na aje muku duk inda kuke son zuwa ki kira shi a waya ki gaya masa, ni zan tafi jibi insha Allahu sai Allah ya nufe mu da dawowa.
To amma Fati, ba zan samu ko da kalmar Allah kiyaye hanya ba, daga Fatin da ba zan kara gani ba, sai bayan wasu shekaru har guda biyu?”

Hawayen ya kara zubo mata, ta yi saurin sharewa da bayan hannun ta. Ya tsura mata ido analytically, can kuma ya ce,
“Girl, ina so in san damuwar ki….., Akalla ko ban yi miki maganin ta ba, ina da shekarun da zan ba ki shawara a kanta. Ta bangare na dai duk hanyar da nasan zan bi in gyara kuskure na nabi, amma kin ki bani hadin kai I do not your thoughts. Not even a single word from you, you are indeed a nice person! Duk wanda ya zauna da ke na lokaci kankani, zai so ci gaba da zama da ke muddin rayuwar shi!!”

Ta yi hanzarin dagowa ta dube shi, kallon ta yake ta cikin kwayar idon shi, da wani lallausar murmushi makale a gefen bakin shi.
“Gaya min mene ne damuwar ki Fatima?”
A hankali ta ce,
“Babu”.
“Ba kya bukatar komai?”
Nan ma ta ce,
“Eh, Allah ya kai ku lafiya!”.

Ya ji dadin addu’ar da ta yi mishi, sai dai ba irin wannan rabuwar yake so su yi ba, ta rashin dadin zuciya. Ta ki sakin jiki dashi ko yaya ne.
Ya kama tafin hannun ta ya rike cikin nashi, “Ba za ki gaya min abin da ke sanya ki kukan ba?”
Ta ce a ranta, “Za ka yi min magani ne?”
Magana ta yi a zuci, ba ta san ta fito, ta shiga kunnuwan sa ba.
“Idan ina da shi me zai hana in yi miki?”
Ta ce, “Bani da damuwa, ba sai mutum yana da damuwa yake yin kuka ba, wani zubin mutum yana yin kukan, don ya ji dadin ransa”.
Ya yi murmushi a kaikaice ya lakaci kuncin ta da dan alinsa,
وتتاىاMu kwana lafiya, amma ina rokon ki duk wasu inconveniences ki yafe min su!!!”.
Ta lumshe ido kafin ta ce, “Babu wani inconvenience game da kai a tare dani, kada ka manta ka ce ni kanwar ka ce. Idan Yaya Mukhtar ya yi min laifi zan kullace shi ne, ko zan kasa yafe mishi?”
Ya yi kirr! Da ido yana duban ta da wani irin sassanyan kallo. Kalmar “Yayan” sai yau bata yi mishi dadi ba kamar ba shi ya jaddada ta ba. Tattausar muryar ta da nutsuwar ta na burge shi har bai son a daina hirar, ita kuma so take a gama, saboda yadda yake kara ruruta wutar son shi a zuciyarta
Nana ta yi motsi za ta soma kuka, dukkan su suka juya gare ta, suka mika hannu a tare don su dauke ta, nata hannun ya riga sauka a kan Nana, don haka nashin sai ya sauka a kan nata. Dukkan su babu wanda bai ji a jikin shi ba. Ta yi saurin sakar mishi Babyn, ta dunkule hannun ta.
Ya dauke ta ya kai kafadun shi ya mike tsaye yana safa da marwa da ita a dakin don ta koma barci, ya kasa fita a dakin Fati, mai wani irin sihirtaccen kamshi da ba zai ce na kowanne turaren wuta ne ba, haka nan gauraye da rabar A.C mai kwantar da hankali. Dakinta ko tsinke babu saboda masifar tsafta. Bai ki ba su kwana a hakan, yana jin sassanyan sautin ta mai motsa zuciya, ta yi mata rahma ko da ba da son ran mutum ba.
Ya kwantar da Nana cikin dan gadon ta dake kan gadon Fati, ya mika mata hannun daman shi, cikin sigar son a yi hannu ya ce,
“Can we be friends apart from Yayan?”
Murmushi ta yi, ta sarke hannuwan ta a baya, “A’a, ai ka ce ni kanwar ka ce wadda take zaman lalata kuruciya........”.

Daga yadda take furta maganar za ka karanci (bitterness) wato dacin da maganar ta yi mata a kan harshen ta da zuciyarta.
Ya ce a ransa, “Baki shi ke yanka wuya….”. Yana da tabo mai yawa a zuciyar yarinyar, wanda ke dakusar da karfin soyayyar sa da ta soma shigar ta. Dole ya wanke kanshi, domin karfi da yaj Fati na neman zamowa wani bangare na zuciyar sa cikin dan kankanin lokaci.
Ya ce,

“Mun yi magana a kan ALL the inconveniences, not SOME of the inconveniences, kin ce kin yafe su, amma why kike maida hannun agogo baya?”

Sai ta yi murmushi, ita ma ta mika mishi tattausan hannun daman ta, suka sarke su cikin na juna. Kowanne siririyar fatar bakin shi dauke da murmushi.

Dai-dai lokacin da suka ji kiran sallar asubahi a cikin kunnuwan su, a sannan ne suka mike domin haramar sallah cike da mamakin tsayin lokacin da suka bata suna hirar zuciya da zuciya (heart to heart talk).
Washegari ma bai samu zama ba, suna ta zirga-zirga a airport na booking jirgin tashin su. Bai dawo ba sai dare, lokacin kafatanin mutanen gidan sun yi barci.
Bai nemi kowa ba shi ma ya ci abincin da suka aje masa ya yi wanka ya shirya ya kwanta, amma tunanin Fati ya hana zuciyar shi sukuni, yana so ya san halin da take ciki, yana so ya sake jin sassanyar muryarta da ke yi mishi yawo a kwanya, yana so ya sake jin taushin hannun ta, yana so....... yana so…... Kai yana son komi nata! She is indeed a blessing cikin gidansa da rayuwarsa…. She is also a DARLING (abar so) farin cikin kowanne da namijin da ya san ciwon kansa.
Amma ba za a gane hakan ba farat daya, sai wanda ya yi zama da ita na tsayin lokaci ya nazarce ta, amma a fuska za a fassara ta da mutum mara son magana, kidahuma mai takurawa rayuwarta. Sai an fahimce ta a hankali za a fuskanci halitta ce, wato nature.
Ya so ya je gare ta a wannan daren da ya zamo na karshe da zai dade bai ganta ba, su raya shi da hira ta fahimta kamar yadda suka raya shi jiya.
Wata zuciyar ta ce, “A kul! Kama girman ka ka rike tsam-tsam kada ta ga weakness din ka”.
To kamun girman har yaushe ne? Shi ma ya tambayi zuciyar tasa. Tunda dai ba za a dauwama a haka ba, kuma ba zai taba sakin Fati ko ya yi mata kishiya ba, don bai da ra’ayin zama da mace sama da guda daya.
In haka ne dole watarana za’a aje girman a gefe a ranar da Allah ya nufa. Shin ko yaushe ce wannan ranar? Bai sani ba! Fati ta riga ta kama zuciyar shi fiye da yadda biro zai iya rubutawa.

Tana shirya masa kalaci a dining ya fito, cikin shirin tafiya, duk ta yi sanyi ta zama cool. Kodayake dama haka halittar ta take, amma na yau na daban ne, komai cikin sanyi take yin sa, amma na yau ya fi na kullum.
Ya tokare hannun shi jikin kofar dakin shi, dayan na zube cikin aljihu, ya langabar da kai yana kallon ta. Jikinta ne ya ba ta ana kallon ta, don haka ta dago kai ta dube shi, sai ta yi murmushi ta sunkuyar da kanta,

“…Morning friend Fatima!!”

Ya fada. Tare da miko mata hannu, tana murmushi ta mika masa nata. Ji take kamar in ya tafi shikenan ba za ta kara ganin shi ba.
Daga gaisuwar bai cika ta ba ya janyo ta a hankali ya rungume ta, ya sumbaci goshinta sannan ya cika ta.
Ta lumshe ido a hankali tana daidaita tunanin ta. Wani abu na zarya a dukkan ilahirin jikinta. Ya iso ga tebir ta karaso da sauri ta yi serving din sa, ya kama kasan hijabinta ya cire ya ajiye a kan daya daga cikin kujerun, ya ce,
“A dinga ajiye shi a cikin gida, don a sha iska”.
Wata muhimmiyar kunya ta kama ta, saboda ‘yan kananan kayan da ke jikinta. Kukan Nana ne ya cece ta daga kaifafan idon Sulaiman, don haka ta garzaya shi kuma ya fara cin abincin kamar bai taba cin abinci mai dadi irin shi ba.
Har karfe goma ya kasa fita, yana tare da ‘ya’yan shi da Nana a cinyar shi suna ta bashi sautun abin da zai sayo musu yana murmushi yana rubutawa.
Abokan tafiyar shi sun yi waya har sun gaji, yana cewa, “I am coming….. (gani nan)”. Sai da Dr. Khalil ya biyo bayan shi sannan ya mike, ya mika wa Fati Nana wadda kanta ke sunkuye.
Ya dago habarta da hannun sa, ta lumshe ido sai hawaye ya balle. Ba sai ta fada ba ya san ko na mene ne, Fati ta kamu da ciwon da shi ma yake fama da shi, amma kawaici da alkunyar ta ya sa take boyewa.
Yatsun shi biyu ya sa yana goge mata hawayen, kararrawar da Dr. Khalil ke dannawa ta sa dole ya amshi brief case din shi a hannun ta. Da sassarfa ya juya ba tare da ya kara waiwayowa ba, da sanyin ido ta bishi har ya fice a falon. Nana da ke hannun ta na ta kuka amma ba ta san tana yi ba, yara na ta yi mata magana, suma ba ta ji me suke cewa ba, ta tafi cikin duniyar kewa, shauki, bege da soyayya…… mai wuyar fassarawa.
Idan wannan ita ce soyayya da Sulaiman ya dandana ta Hadiza, sai ba ta ga laifin shi ba na wulakanta ta a farko, don ba ta jin in ita ce ya mutu a yanzu za ta yarda ta kara yin wani aure a rayuwar ta, ko zata kara son wani, kwatankwacin wannan son na Sulaiman da take ji a zuciyarta, ruhi da bargon jikinta.
Ta kara tausaya mishi kwarai game da yadda ya jure da rashin
End Ads