x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 6 - JIKI MAGAYI

  • 15001 words
  • 18000 words
  • Out of 18490 words

Category: Adabin Hausa

Views 61

09 Jul 2025
Start ads
After Image Ads
kyar ya ciwo kanta ta yarda. Amma ya fada mata zai gaya wa jama'a zai tafi hajji ne, don kada a gane Za Su Bar Garin

Sai ran nan ya tara matansa duka, ya ce musu, "Na yi niyya zan tafi hajji, amma da Zainabu kadai zan tafi. Ku kuwa ku yi hakuri, har Allah ya sake tara mu."Ya kawo kudi mai yawa da abinci ya bar musu. Ya kira babban baransa ya danka masa dukan sha'anin gidansa. Ya yi sallama da sarki. Duk cikin yaransa bai tafi da kowa ba. Ya debi guzuri ya labta wa jaki, ya dauki rakumi daya ya aza Zainabu. Ya tashi, mutanen gari suka yi masa rakiya, suna mamakin irin fitar da ya yi.

Suka yi ta tafiya, kwanci tashi kwanci tashi, misalin wata biyu. Da ya ga dai ya rabu da inda aka san shi sarai, sai ya sauka a wani babban gari ana kiransa GARUJE. garin kuwa masafarta ne Kwarai. Ya tafi wurin sarkin, ya ce shi bako ne, yana so sarki ya ba shi wurin zama ya zauna, domin ya ga garin wurin ciniki ne.

Sarki ya yi murna da shi kwarai ya ce, "Ina sunanka?" Ya ce, "Malam Usman."

"Daga wane gari ka fito."

Sai ya nemi wani sunan gari wanda sarkin ma bai taba jin sunansa ba ya fadi.

Sarki ya kawo gida ya ba shi. Ya yi zamansa, yana ta sana'ar sa ta ciniki har ya tara dukiya da dama, ya gyara gidansa ya yi kyau. A hankali a hankali har arzikin Malam Usuman ya kasaita, ya zama shi ya ke tashen doki a garin.

KWATSAM....JIKI MAGAYI-08

Ana nan wata rana Kyauta da abokinsa Dogon Yaro suna cikin yawace-yawacensu sai suka zo wani kauye kusa da Garuje, suka sauka. Rannan suka shiga yawo cikin gari. Sai suka gamu da wani mutum, suka shiga zance da shi suka ce, "Kai, wannan gari yana cike da masu arziki, ba kamar garimmu ba!" Ya ce. "Ai wannan gari dai Alhamudulillahi"

Suka ce masa. "Mun shige wata kofar gida can, munga gidan da doguwar katanga, an kewaye da gaude, sai ka ce gidan sarauta. Gidan wani hakimi ne?"

Ya ce, "Daga wane waje?" Suka nuna masa.

Ya ce, "A'a, ba gidan hakimi ba ne, na wani mai arziki ne bako, sunansa Malam Usuman, 'yan shekarunsa kadan ne cikin wannan gari, ga shi yanzu shi ya ke tashen doki." Suka ce. "Don me ya gyara gida haka, har ya kakkafa gaude? Mu a garimmu sai gidan sarki za ka ga gaude. Ko yana tsoron Barayi ne?"

Ya ce, "I, kun san shi mai arziki ne, na ji ma an ce wanda ya yi zancen Barawo cikin yaransa, ko masu zuwa gidansa, ba su ganin fuska a gare shi." Suke ce, "Watakila an taba yi masa sata ne. Za mu tafi mu yi sayayya."

Suka kama hanyarsu suka zaga suka koma ta gidan Malam Usman , suna ta shawagi suna duban gidan. Da suka zazzaga sai suka kama hanyarsu suka ce da junansu, "Kai, wannan gida idan Allah ya ba mu sa'a za mu kwashi dukiya. Idan dai barayi ya ke gudu ya sa ya gyara gidansa haka, ya kuwa gamu da su !"

Da dare ya yi, kafa duk ta dauke, suka tasam ma gidan nan da suka gani da rana, suna sando suna bin inuwar katanga. Da suka zo gidan suka zaga suna neman ta inda za su shiga, suka taba Kofrn suka ji kan kan, sai suka ce, "Mu zaga mu gani watakila za mu sami tsani. Suka kama hanya, sai suka hango kan tsani a wani gida. Suka tafi, Kyauta ya duka, Dogon Yaro ya hau bayansa ya kama katangar ya hau, ya dire. Ya dauko tsanin, ya jingina a katangar, ya hawo, ya dauko ya ba Kyauta. Suka dauka suka tafi da shi suka jingina a katangar Malam Usman. Suka hau suka jawo shi daga ciki suka sauka Suka duba gidan duka suka ga yadda ya ke, sa'an nan suka tinkari turakar mai gida. Suka kasa kunne a kofar dakinsa suka ji yana minshari. Kyauta ya ce wa Dogon Yaro ya tsaya a kofa, shi ya shiga domin in ya ji motsin wani ya sanar da shi, idan kuwa bai ji ba kome ya samo zai mika masa.

Kyauta ya tura kofa a hankali ya shiga, ya tsaya shiru, ya ji mai gida bai yi motsi ba, ya shiga ya labe. Sai ya ci karo da butar karfe ta fadi kwaram. Mai gida ya farka ya ce, "Kai, kai wane ne?" Kyauta ya make.

Sai mai gida ya hangi inuwarsa a kofa ya zaburo, sai Kyauta ya yi wuf ya ribce shi ya fyada shi da Rlkasa. Dogon Yaro kuma ya yi farat ya shiga, ya toshe bakinsa. Yana ta mutsuniya, sai Kyauta ya zare wuka ya daba masa a kafon zuci, ya ja. Suka taushe shi har suka ji jikinsa ya saki. Sai suka ji tari daga waje suka ji tsoro suka yiwo waje, sai suka ji wata mace tace "Mene ne a ke haka a gidan nan, lafiya

Kyauta ya amsa yaxe, "Ai babu kome, ni ne na kewaya" Ta ce, "Wai! Da ka yi magana har ka tuna mini da Abdullahi." Sai ta kyasta ashana ta ga danta ne, shi kuma ya gane uwarsa ce wadda ya rabu da ita shekaru da yawa.

Sai ta ce, "Abdullahi, ka komo?" Shi kuma ya kasa magana. Suka tsaya suna duban juna. Dogon Yaro yana make, ya gaji da jira, ya ce, "Kai, ba ka san muna cikin hadari ba na abin da muka yi, sai ka tsaya kana ta tadi da mace?" Amma shi bai kula ba. Sai Dogon Yaro ya yi fushi, ya ce, "To, tsaya abinka ni na tafi,"

Zainabu ta ce, "Me ya kawo ka cikin wannan gida da dare? Ya ce, "Kin manta ciniki na ne?"

Ta ce, "Ko kana sata ka shigo ka yi a gidan ubanka ?" Ya ce, "Ubana! Yaushe kuka taso daga Galma kuka komo nan ?

Ta ce "Ai mun yi shekaru da yawa a wannan gari."

Ya ce. "Wallahi tallahi ban san ko da mafarki wannan gidan ubana ba ne." Sa'an nan duk jikinsa ya dauki rawa.

Sai ita kuwa ta ji tsoro ta ce. "Me ya faru ?" Ya ce. "Ai mun shiga wani daki can don mu yi sata, sai wani mutum ya tasam mana, mun soke shi."

Zainabu ta ce, "Kun soki wani! Allahu Akbar! Yau Wane kwana sun yi! Maza mu je mu gani."

Suka tafi suka shiga cikin daki. Zainabu ta kyasta ashana, sai ga mutum rub da ciki cikin jini, gabanta ya fadi, ta ce, "Juya shi."

Kyauta ya juya shi, sai ya ga ubansa ne. Sai ta matso kusa ta girgiza shi, ta ga bai yi motsi ba. Sai ta fashe da kuka, ta tuna da maganar da Abubakar ya ce mata danta zai kashe ubansa.

Da Kyauta ya ga abin da ya yi hankalinsa ya tashi, ya zama kamar mahaukaci, ya zare wuka zai kashe kansa. Sai Zainabu ta kama hannunsa, ta ce, "tsaya, kada ka yi barna, ina da jawabi da kai tukuna." Ta gaya masa dukan abin da ke tsakaninsu da Abubakar da yadda shi ne ya la'anta shi ya lalace a duniya har ya kai ga kisan ubansa. Ta ce, "Ka gani dukan abin nan da ka yi tun daga farko ba laifinka ba ne, haka Allah ya kaddara, amma yanzu sai mu saurari gaba mu ga irin sakayyar da Allah zai yi mana."

Ta rufe baki ke nan sai suka ji kururuwa a bayan gida, "Barawo, Barawo!" Sai suka dubi juna, ta ce, "Ka ji an kama abokin tafiyarka ! Maza maza ka fita kada su same ka a nan." Sai ta kama hannunsa ta jawo shi, ta zaga da shi lungu, har suka zo kofa, ta bude masa ta tura shi waje. Ta koma ta rufe dakinta. Zuwa can jimawa sai aka ji kuwace-kuwacen mutane suna zuwa, har suka iso kofar gida. Suka kyankyasa, sai wani yaro ya bude ya aleka ya ga mutane, ya ce, "Me ya faru?"

Suka ce, "Barawo ne muka kamo, mun ga ya hauro daga katangar gidan nan muka bi shi muka kama. Tafi ka taso mai gida maza."

Sai yaro ya sheka a guje zuwa turakar mai gida, ya ga kofa a bude. Ya tsaya a kofa ya yi kira. "Mai gida, mai gida!" Shiru. Ya kara daga murya, shiru dai. Sai ya kutsa kai cikin daki, ya yi tuntube da mutum. Sai ya yi ihu ya ce. "Ku zo, ga wani Barawo!" Ya nufo Kofar gida a guje yana kururuwa. Sai mutane suka rugungunto cikin gida suka nufi turaka, aka rasa wanda zai shiga. Sai aka haska fitila aka hangi mutum yana mike shame- shame cikin jini. Aka shiga, aka ga mai gida ne.

Shi Ne! Shi Ne!

Duk aka fashe da salati, suka ce. Lalle Barawon nan shi ya yi wannan aiki. Sai suka rufe shi da duka, yana ta kuwwa, yana cewa, "Ku bari, jama'a! Ba ni ne na kashe shi ba, abokin tafiyata ne." Suka ce. "Karya ne, ina ya ke?"

Ya ce, "Ai ko yanzu ma yana cikin gida, bai fita ba. Gama da na fita na bar shi cikin gida."

Suka ce, "Karya ka ke yi, kaka mutum zai yi irin wannan aiki har ka fita shi kuwa ya tsaya a baya? Ka maida mu mahaukata ko?

Ya ce, "Wallahi tallahi kuwa gaskiya ne. Ku dai ku duba, lallai yana nan bai fita ba Sai aka watsu cikin gida, ba inda ba a duba bu, lungu lungu aka bi ana lekawa, ba a ga kowa ba. Aka tambayi matan gida ko akwai wadda ta fita cikinsu. Duk suka ce ba wanda ta fita, sai lokacin da suka ji ihu. Jama'a suka ce, "Ko da ma mun san lalle karya ya ke yi.

Sai suka tafi da shi gidan sarki, sarki ya sa aka kai shi kurkuku cikin daren nan. Aka komo aka yi suturar Malam Usman, kowa ya koma gidansa. Da gari ya waye aka fito da Dogon yaro daga kurkuku aka tambaye shi sunan wanda ya ce suna tare. ya ce. "Ina tsammanin sunansa Garba."

"Kai ma ba ka san sunansa ba?"

"Ina tsammani sunansa ke nan." "Mutumin wane gari ne?"

"Ban san sunan garinsu ba."

"Kai ina sunanka?"

"Dogon Yaro."

"Na wane gari?" "Ibu."

Ba Mu San Garin Ba

"Makaryaci! Wane gari ne cikin duniyar nan da suna ibu? A koma da shi har mu bi sawu."

Yana nan a kurkuku, ana ta bincike. A kurkukun kuwa akwai wata rijiya mai zurfi da gaske tana cike da ruwa, sai ran nan ya fito da la'asar ya zo diban ruwa, sai tsundun ya fada cikin rijiyar. Da aka zo aka tarar ya mutu. Aka fito da shi, aka tafi aka shaida wa sarki Dogon Yaro
ya mutu. Sarki ya ce, "Shi ke nan, gaskiya ta yi halinta!"

Amma Kyauta da ya fita daga cikin gida Can halin da muka fadi bai tsaya ko ina ba, ya ratsa gari ya fita ya kama hanyar Galma. Yana fita sai babban hadari ya taso, ruwa ya yi masa duka, amma duk bai kula ba, hankalinsa yana gaba. bai tsaya ba, bai waiwaya ba, sai ka ce mahaukacin kare. Yana juyayin abin da ya yi, yana zulumi a kan maganar da uwarsa ta gaya masa. Ya zama ba shi da wani muradi a duniya sai ya hadu da Abubakar, ya dauki fansar dukan abin da ya yi masa

Gari ya waye masa yana tafiya, har rana ta yi zafi, har azahar har almuru. Haka ya kwana biyu yana tafiya ba ci ba sha, sai in ya kai maciya in ya sami dan abin sayarwa ya saya, yana tafe yana ci. Idan barci yayi masa sai ya yi dan rurumi, ya tashi ya yi ta tafiya, da haka har ya kai Galma. Bai zame ko ina ba sai gidan makiyinsa Abubakar. Ya shiga gidan, bai yi ko sallama ba, sai ya gamu da wata mace. Ita kuwa ta gan shi kamar mahauci duk yayi gizo gwanin ban tsoro a fuska, da takobi zararre a hannunsa.

Ya daka mata tsawa ya ce, "Ke, ina Abubakar ?" Ta kidime, ta kasa magana saboda tsoro. Sai ya yi caf da wuyanta ya ce, "Ba ki ji ina tambayarki ba?"

Ta yi masa nuni da hannu da wani daki, tsoro ya hana ta magana. Sai ya yi jifa da ita, ya wuce zuwa dakin. Sai ta tashi, kafin ya iso ta tafi ta kare kofa, ta ce, "Kada ka shiga! Mai gida na fama da ciwo rai ga Allah." Ya ce, "Ban wuri, in riga Allah a kansa! Yau kwanansa sun kare." Sai ya ture ta ya shiga, ya ce, "Ina ka ke?" Bai ji motsinsa ba sai nishi.
Da idonsa ya waye a cikin dakin sai ya ga mutum a kwance akan gado, fuska tasa tana kallon bango. Ya matsa, ya dafa kafadarsa ya juya shi, ya ce, "Abubakar ke nan ?"

Sai ya bude baki da kyar ya ce, "Wane ne?" Ya ce, "Ni ne Kyauta dan Malam Shaihu, yau ranar sakayya ta zo a kanka!"

Da Abubakar ya ji wannan magana sai ya yunkura zai tashi, ya fadi rigingine jikinsa yana rawa. Duk maganar da ya gayawa Zainabu tun shekaru da yawa ta fado masa. Ya nutsa cikin tunani, yana batun zuci ya ce, "M, na san sai haka. Ko daman an gaya mini alhaki zai komo kaina." Sa'an nan ya zura Kyauta ido, ya ce, "Ka zo ka dauki fansa ko? Amma kaddarar Allah ta rigaya ta cika. Abin da na aikata maka ya faru, muradina kuwa ya biya." burina ya cika.

SAI KAWAI SUKAJI......JIKI MAGAYI-09

Burina ya cika akan ka Sa'an nan karfi ya komo masa, ya yi farat ya zauna, ya mika
hannu ya nune shi, ya daka tsawa ya ce. "Ka makara! Wata fansar sai gobe kiyama !" Sai ya tuntsure, rai ya fita. Sai Kyauta ya fita, babu wanda ya ganshi Yana tafiya
yana cewa a ransa, "Allahu Akbar! Allah Buwayi, mai yin yadda ya so da bayinsa!" Ya fita ke nan sai matan nan ta zo da makwabtansu suka ce, "Ina mutumin ?"

Ta ce "Yana cikin turakar mai gida."

Suka shiga suka iske mai gida matacce, shi kadai. Suka duba duk gida ba su ga kowa ba. Suka ce, "Wace irin kama ke gare shi?" Ta ce. "Ba zan iya sifanta shi ba, domin da ni gan shi, ko magana na kasa yi."

Sai suka ce. "Lalle ta-ga Azra'ilu ne!" Duk gida ya cika da koke-koke.

Sai Kyauta ya tafi ya zauna a gindin wata itaciya a bayan gari kusa da rafi, hankalinsa ya komo, yana ta nadamar dukan muguntar da ya yi tun yana yaro, har zuwa kisan ubansa, ya ga dukan wadannan kamar mugun mafarki ne. Ya ce, "Allah kai ne Sarki, ka yafe ni!"

Sai ya tashi ya tafi ya yi wanka, ya shiga gari ya yi aski, ya sayi riga ya sa, ya nufi gidan ubansa. Ya sami yaron da ubansa ya bari jiran gida duk shekarun nan, amma matan gida duk sun fashe. Ya buda masa shi ne Kyauta dan Malam Shaihu, ya gaya masa mai gida ya rasu. Baran ya yi mamaki, domin ya yanke ran zai sake jin labarinsa ko na dansa.

Daga nan baran ya dauke shi, suka tafi gidan sarki. Bayan da suka yi gaisuwa sarki ya tambaye shi daga na ya fito. Ya ce, "Daga wurin ubana."

Sarki ya ce, "Ashe yana da rai? Tun da muka rabu shekaru da yawa ba mu ji labarinsa ba."

Kyauta ya ce, "Da ya tashi daga nan ya tafi wani gari da a ke ce masa Garuje, can ya zauna duk shekarun nan. Amma yanzu ya mutu, shi ya sa na zo in duba yadda halin gida ya ke kafin in koma in zo da mahaifiyata Sarki ya ce, "Ka rabu da halinka ?" Ya ce, "Ranka ya dade, ba ni ko son a yi tadin wannan. Abin da ya wuce ya wuce."
Sarki Ya Sa Masa Albarka

Da sarki ya ji wannan ya yi murna, ya sa masa albarka, ya ce, "Idan abin da ka gaya mini gaskiya ne ina so ka komo ka zauna, don soyayyan da ta ke tsakanina da ubanka Kyauta ya ce Ranka ya dade, na gode. Amma ko na komo ba zan iya cin gadon ubana ba sai na biya dukan alhakin da na dauka nasa " Sai ya yi sallama, ya tashi. Bai dauki kome daga cikin gidan ubansa ba, ko guzuri, ya tafi. Kwanci tashi har ya kai Garuje. Ya tafi wurin uwarsa ya gaya mata dukan abin da ya faru. Ya ce, "Yanzu ya kamata in koma da ke ki yi zamanki can cikin danginki."

Ta ce, "Shi ke nan, kai ka sani ko da ma a kan tilas na ke zaune a nan." Ta tafi ta shaida wa sarki ga danta yazo. Sarki ya ce, "Ashe Malam Usman yana da ɗa? Zo da shi in gan shi." Ta tafi ta zo da shi.
Da ya shigo sarki ya dube shi ya ce, "Babu shakka dansa ne" Sai ya waiwayi Zainabu ya ce, "Shi ke nan? Ko yana da yan uwa ?"
Zainabu ta ce, "Shi ke nan tilo."

Sarki ya tambaye shi, "Ka zo ka zauna a Sanka ?" Ya ce, "A'a, na zo in tafi da tsohuwata ne." Sarki ya ce a tafi a nuna masa bakin duk kayan ubansa, a yi musu kimma, a cire ushura. Da aka tafi aka yi, aka danka masa dukan kome.

Sa'an nan ya ce a tara masa dukan malaman garin su yi wa ubansa addu'a. Aka taru tinjim a kofar gidan ubansa, ya fito da kaya ya yi ta raba musu har ya gama. Suka yi addu'a Allah ya jikan Malam Usuman. Kowa ya watse.

Kashegari ya ce a tara masa musakai duka. Da suka gama taruwa ya fitar da dukan abin da ya rage cikin gidan ubansa, ya yi ta ba su, har kudi suka kare ya shiga rabon tufafi, da tarkace da dabbobi. Saboda yawan dukiya duk garin babu wanda bai samu ba. Ya rabar da kayan sarai, ko allura bai dauka ba.

Da ya gama ya tafi ya sallami sarki. Duk gari suna ta mamaki, ba su taba ganin wanda ya yi haka ba. Ya sa uwa tasa a gaba, suka tafi har suka kai Galma. Ya sa ta a gidan ubansa. Ya shaida wa sarki. Aka
End Ads