x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 2 - JIKI MAGAYI

  • 3001 words
  • 6000 words
  • Out of 18490 words

Category: Adabin Hausa

Views 56

09 Jul 2025
Start ads
After Image Ads
ta tafi.

Da ta shiga gida ta dauki turaren ta ba uwarta, ta ce, "Ga shi Abubakar ne ya ba ni. Karbi ki ajiye mini." Dazata bata ta lakuta kadan ta yi bille da shi.

Da gari ya waye Malam Shaihu ya aika aka kirawo masa Malam Sambo, ya fada masa dukan abin da suka yi da Zainabu. Sai Malam Sambo ya ce, "Tun da ya ke ka ba ta turaren shikenan, kada ka sake neman ganinta, su da kansu sa aiko a neme ka"

Malam Shaihu ya yi masa godiya, ya sake kawo kudi ya bashi

Da yamma Abubakar ya tafi gidan su Zainabu da kansa, ya sa aka kira ta. Ya tambaye ta, "Gaskiya ne kuwa jiya bayan rabuwarmu kin tafi gidan Malam Shehu ?"

Ta ce, La

Ya ce, "Yanzu na sani tsakanina da ke rufarufa ne. Ina so ki fada mini a sarari idan ba ki sona.

Ta ce, "Ai ka sani budurwa haja ce, kowa ya gani yana so, kowa kuwa da irin tayinsa, amma mai saye daya ne. Ko da ba a yi mini baiko da kai ba, kaidai kana tashina." Sai ya tashi da fushi ya tafi abinsa.

Da ya koma gida ya fada wa uwa tasa abin da ya ke tsakanin- sa da Zainabu. Uwar ta ce, "Ai ni ko da na sani ba za ka auri Zainabu ba, domin kuwa tana da masoya masu arziki, ka sani kuwa kome na duniyan nan ba duka a ke yi domin Allah ba, sai don dukiya. Hakura, ka nemi daidai da kai."

Ya ce mata, "Haba, iya idan dai ni dan mutum biyu ne, sai na rama. Zan shiga duniya, da ko wane hali na sani Allah zai taimake ni. Amma kada ki damu. Ga Audu nan da kanwata da kakarmu, sun ishe ki zaman duniya, ni kuwa idan da rai watarana za ki ga na komo. Da ta ji haka ranta ya baci Kwarai da gaske, ta rasa abin da za ta ce masa, domin ta sani idan hankalin Abubakar ya tashi ba mai ikon tausa shi.JIKI MAGAYI-02

Daga nan uwar ta ce, "Ai ka sani abin duniya ba a yinsa da karfi, sai da rarrashi da ban magana. Abin da na ke so da kai ka yi hakuri a rarrashe ta, watakila ta koma cikin hankalinta Amma yanzu idan ka ce za ka yi mata na karfi, ka san halin yaran zamani watakila wannan ya zama shi ne dalilin da zamu rasa ta dungurungum babu rai babu girma." Sa'an nan ya kwance ta
Yammar fari sai gidan Malam Shaihu. Ta ce masa, "Tunda ya ke Abubakar ya yi zafin zuciyar tasa ina so ka fito zancen neman aure."

Da gari ya waye, Malam Shaihu ya aika wurin Malam Audu a fada masa yana nan yana aikowa a kan maganar da suka yi Malam Audu ya aiko a fada masa ba shi ba dai, sai ko abayan ransa a daura musu, Aka yi jayayya kwanaki da yawa. Sa'an nan yan'uwa suka taru suka yi wa Malam Audu. Ya amsa tilas, ba da sonsa ba ko kadan. Malam Shaihu ya fito zancen neman aure, aka yi masa baiwa ya biya wadansu ramuwa wadanda yarinya ta ci. A ran nan aka sa ranar biki. Dukan mutanen gari suna ta yi da Malam Shaihu don rashin dattakun da ya yi.

Randa za a daura aure ya saki matar tasa daya. Da yamma aka kawo amarya. Kashegari aka yi kasaitaccen biki wanda ko sarkin Galma ba zai yi irinsa ba. Abokansa daga ko ina suka zo . Babu irin abin da ba a yi ba, kowa sai cewa ya ke yi, "Tubarkalla, lalle mai arziki yana biki!" Sai facaka da kudi a ke yi, aka kwana uku ana wasa. Sa'an nan aka yi budar kai aka kawo gara. Mutane kuwa suka watse.

SAURAYI YA SHIGA DUNIYA

ABUBAKAR ya fita gida, bai san inda za shi ba, yana ta yawo har ya zo wani gari wanda a ke ce masa ZAUNA-DA-SHIRINKA . Garin kuwa na wadanda suka yi ko sata, ko wani abin kunya ne, suka gudo daga garinsu suka zo suka kafa tasu tunga, basa yin kome sai masha'a. Duk garin daga 'yan bori sai kasaitattun Barayi, sai matsibbata, da karuwai mata, Abubakar ya iso garin sai ya rika jin yizga tana tashi, da wake- wake. Sai ya zauna a gindin wata itaciya, yana hutun gajiya, har barci yakwashe shi.
Sai wani mutum ya zo ya gan shi yana kwance, ya tashe shi ya ce masa, "Samari, daga ina ka fito?" Sai ya farka daga barci, suka yi gaisuwa, ya tambaye shi ko
garin nan da wani shahararren malami. Mutumin ya ce masa, "Ba ka ji sunan garin nan ba?"

Ya ce, "Na ji." Ya ce, "To, ka ga wane malamin kirki zai zauna cikin wannan gari? Mu nan bama sha'anin komai da malamai sai tsafi da bori
Sai yace toh dakyau nuna mini gidan BABBAN MATSAFINKU.

Sai ya tafi da shi gidan wani waishi
TAUSAYIN KA-DA-SAUKI Da aka kai shi gidan bashi nan, ya tafi garin wata al'ada kwanansa uku, amma ana tsammanin da yamma zai komo. Ya zauna yana jiransa, bai komo ba sai da tsakad dare. Da ya shiga gida ya kintsa, sai wani daga cikin yaransa ya shiga, ya fada masa ya yi bako, tun da hantsi. Daga can sai ya fito, ya sa aka yi kiran Abubakar, suka kadaice. Da dai Abubakar ya gan shi sai jikinsa ya dauki rawa saboda kwarjinin dake gare shi. Suka gaisa, ya tambaye shi abin da ya kawo shi. Abubakar ya ce, "Maganata da yawa, sai Allah ya kai mu gobe na warware maka zarena da abawata."

Da gari ya waye, Abubakar ya tafi ya gaida Tausayinka-da-sauki. Bayan da suka gama gaisuwa ya ce masa, "Abin da ya kawo ni gare ka, bacin rai ne. Ni ke da wata yarinya wadda na ke so, ita kuma tana sona gaba da komai, tun muna yara har muka yi girma, ina nan ina tashinta za mu yi aure. Ina cikin shawara ke nan zan sa uwata ta tafi a yi mini baiko, sai wani attajiri a garimniu ana kiransa Malam Shaihu ya ji labarinta. Domin kwadayi kawai ya kangarata, ko da ya ke yana da matansa hudu. Irin wannan mutum bai kamata ya zauna lafiya ba. Ba shi yiwuwa a gare ni in zauna cikin garin nan, in ji ya aure ta. Saboda haka ne na rasa abin da zan yi domin in fanshewa kaina takaici. Sai na shiga cikin duniya ina yawace-yawace har Allah ya kawo ni garin nan. Ina cikin tambaya har aka gaya mini babu wanda ya fi ka sanin magani cikin dukan kasar nan Saboda haka na zo gare ka, in ka yarda ka taimake ni in dauki fansa a kansu, raina ya huce."

Tausayinka-da-sauki ya ce, "To, madalla, ka kuwa kawo kuka inda za a share maka hawaye. Dukan abin nan da ya kawo ka kafin ka fadi na riga na san shi. Domin jiya bayan da muka rabu Doguwa ta zo ta bayyana mini dukan abin nan da ya ke tafe da kai. Amma yadda ka ke tsammani ba haka ba ne. Domin ba kwadayi kadai ne ya sa attajirin nan ya yi maka wannan abun ba. Dalili dai yana son ɗa ne, an kuwa gaya masa Idan ya auri yarinyan nan zai samu."

Sa'an nan Abubakar ya ce, "Ashe hakanan ne?" Yace, kwarai

Abubakar ya ce, "To, zai kuwa samu ?" Ya ce, "Lalle zai samu, domin wannan magana ba nufin mutum ba ce, ikon Allah ne."Sai Abubakar ya yi shiru, ya nutsa dikin zurfin tunani. Sa'an nan ya ce, "To, tun da ya ke kwadayin ɗa ne ya sa ya yi mini wannan abu, abu daya ne kadai zai faranta mini zuciya, shi ne albarkan nan da ya ke nema ta zama masa la'ana."

Sai Tausayinka-da-sauki ya yi shiru, sa'an nan ya ce, "Wannan abu zai yiwu, amma da wuya. Ka yarda in na yi maka dukan hakinsa yana kanka?"

Abubakar ya ce, Na yarda. abin da duk Allah ya so ya yi da ni a kan wannan abu na dauka ni dai bukatata ta biya." Ya sake cewa, "Idan ka yi mini wannan me zan biya?""

Tausayinka-da-sauki ya yi dariya, ya ce, "Ni ba zan karbi kome daga gare ka ba, domin dukan abu kai zakayi da kanka. Ka iya ka jure ka samo abin da zan gaya maka?"

Ya ce. "Da ikon Allah zan iya."

Tausayinka-da-sauki ya ce, "Ina so ka samo mini KARON
KALGO." Ya ce "A ina zan sami wannan? Ban taba ganin wanda ya same shi ba."

Ya ce, "Ba shi a kasar nan, amma zan gaya maka inda idan ka tafi, ka samu. Ka san ba a kasan nan aka haife ni ba, ni mutumin Yale ne. Na bar gida tun ina yaro, sabo da shedancin neman asiri. Na ji kuwa har yanzu ubana yana da rai, yana kuwa begen ganina kullum, domin ni ne babban dansa. Zan aike ka wurinsa shi zai gaya maka inda za ka samu, domin na tuna tun ina yaro na kan ji yana ba da labarinsa."

Abubakar ya ce, "Kaka zai yiwu? Ko na tafi ba zai san daga wurinka na fito ba, gama ka shi rabuwarka da gida shekaru da yawa ke nan."

Sai ya sa hannu cikin ratayensa, ya kwance wata laya, ya ce, "Ga wannan ka kai masa, da ganinta ya sani. In ka tafi ka gaya masa dukan labarinka ka ce ina gaishe shi ina kuwa da rai Ina kuwa so ya yafe mini dukan irin dangin abin da na yi masa. Idan ya huce ya aiko mini sa'ad da ka ke komowa, na koma gida. Idan ka cika abin nan da na umurce ka ka biya hakin dukan taimakon da zan yi maka ke nan.

Da gari ya waye, Abubakar ya danki hanya yana ta tafiya, kwana wannan gari, tashi kwana wancan. Wani wuri ya sami abinci, wani wuri kuwa sai ya yi bara sa'an nan ya samu da kyar. Da haka da haka bayan wata biyu ya kai garin da aka aike shi.

Da ya shiga Yale tun wajen azahar yana ta yawo yana ta tambayar gidan uban Tausayinka-da-sauki. Ko ina ya tafi sai a ce, "Ba mu taba jin mai suna haka ba, balle mu san ubansa." Da ya gaji da tambaya sai ya yi zaune a gindin wata itaciya. Can sai ga wani dattijo zai wuce, ya tashi ya tare shi, ya fadi ya gaishe shi, ya ce, "Tambaya na ke yi. Ni bako ne daga wani gari ana ce masa Zauna-da-shirinka, wani babban boka ne ya aiko ni wurin tsohonsa. Shi kuwa tun yana karami ya dora, yana can yanzu ya yi arziki. Ni kuwa domin ragon azancina da zam fito na manta in tambaye shi sunan ubansa. Shi kuma bai gaya mini ba. Ko Allah ya sa ka san shi?"

Dattijon ya tsaya shiru, ya sunkuyar da kai, ya dade bai yi magana ba. Sa'an nan Abubakar ya ce, "Me ya same ka? Domin na tambaye ka kawai, wannan ya isa ya ɓata maka zuciya?"

Dattijon ya ce, "I, wannan magana da ka fadi ta tuna mini da abin da ko da ya ke cikin raina." Abubakar ya ce, "Sannu baba, da na san wannan magana
za ta Bata maka rai da ban tambaye ka ba." Sai tsoho ya ce, Babu kome, Allah shi ne Sarki."

Sa'an nan da Abubakar ya ga dai hankalin tsoho bai kwanta ba ya ce, "Baba, don Allah ka fada mini abin da ya Bata ranka."

Tsoho ya ce, "Ka ji, dana, ina da wani ɗa kamar yadda ka fadi, yau shekaru da yawa ya dora, amma ya mutu. Shi ne abin da na ke tunawa kullum, da ka yi mini magana kuma ya sake fado mini a rai."

Abubakar ya ce, "Yaya ka tabbata ya mutu?" Tsoho ya ce, "Tun shekarun nan da ya fita gida ban ga wanda ya gan shi ba, ban kuwa ji labarinsa ba. Shi ne ya sa na tabbata."

Abubakar ya ce, "Yaya kamar danka?"

Sai tsoho ya sifanta masa shi, ya ce amma wannan tun yana yaro ne, ba wanda zai gane shi yanzu. Sa'annan ne Abubaka: yace, "Kada ranka ya Baci, watakila
Allah ya kawo ni nan domin ka sami labarin danka ne." Tsoho ya ce, "Wannan ba shi yiwuwa, abin da aka yi she- karu da yawa. Ko yana da rai ma yaya zan tabbatar"

Daga nan Abubakar ya sa hannu a aljihu yafito da laya, ya ce, "Duba wannan abu ka gani, ko ka san shi?" Sai dattijon ya karba ya duba da kyau, ya ce, "Daga ina ka sami wannan?"

Ya ce, "Shi ne mutumin da na gaya maka ya ba ni in kai wa ubansa domin shaida."

Dattijon ya ce, "A! Allah Sarki, shi ne mai aikata abin da ya ga dama. Babu kuwa abin da ba shi yiwuwa a gare shi. Babu shakka ZAKARI yana da rai." Daga nan ya ce, "Zo mu tafi gidana, na kosa in ji dukkan labarinsa."

Sai suka tafi gida, ya saukar da shi, aka ba shi abinci ya ci, ya huta, sa'ar nan ya gaya masa dukan labarin dansa. Dattijon ya ce, "Da ikon Allah sai na aika masa ya komo
gida."

Ya sake ce masa, "Kai kuwa menene gaminka da shi, har zai aiko ka tafiya mai nisa haka, da wahala, da rashin sanin wuri?"

NAZO NEMAN KARON KALGO NEJIKI MAGAYI-03

Abubakar ya ce, "Dalilin saduwata da danka, wani abin bakin ciki ne ya same ni a garimmu wanda na kasa daurewa, na yi fushi na fita gida neman sakayyar abin nan da aka yi mini Ina cikin yawace-yawacena har Allah ya kai ni garin da ya ke, aka gaya min shi kadai ne zai iya fashe min wannan takaicin. Dana, tafi na shaida masa, ya ce zai bani, amma sai na samo masa karon kalgo tukunna. Da ya fada mini haka, na ce masa bansan inda zan same shi ba. Shiyasa ya aiko ni gare ka, ya ce
domin sa'ar da ya ke yaro ya kan ji kana ba su labarin inda a ke samu."

Dattijon ya ce, "Wane abu aka yi maka da zafi haka har da za ka yarda ka sayar da ranka? Domin samun wannan abu sai wanda Allah ya nufe shi da ganinsa."

Ya ce, "Aure na nema a garimmu, wani attajiri ya kwace ta ba girma ba arziki, ni da azatona kwadayi ne kawai da alfarmar dukiya. Amma da na zo na gaya wa danka ya kauda ni cikin wannan jahilci, ya ce dalili dai sabo da an gaya masa sai ya aure ta, sa'an nan zai ga ƙwan sa shi kuwa bukatarsa ke nan gaba da kome cikin duniya, domin bai taba samun ɗa ba. Sa'an nan na nemi taimako wurin danka, abin nan da za'a haifa masa maimakon albarka ya zama kasaitaccen lalatacce a duniya wanda zai jawo masa ko wace irin masifa, ya zama ya gwammace ya mutu ba shi da ɗa. Ya ce zai bani, amma sai na kawo masa ƙaron kalgo."

Dattijon ya ce, "Samari, abin da ya fi kyau ka hakura, ka bar shi ga Allah ya saka maka, domin wannan abin da kake nema ba abin kirki ba ne. Bai kamata ka saka mugunta da mugunta ba, ka bari Allah shi ne mai hukunci tsakaninku."

Tsohon ya yi ta rarrashinsa. Da dai ya ga bai ciwo kansa ba; ya ce, "Wannan abu da ka gaya min ban ji dadinsa ba. Amma tun da yake dalilinka ne na sami labarin dana, lalle ba zan iya kin taimakonka ba, ko da ya ke abin da ka ke bukata ba mai kyau ba ne. Amma ka sani da wahala mai yawa a gabanka, ko rabin tafiyarka ma ba ka yi ba tukuna. Inda zaka samo abin nan, sai ka rabu da mutane, ka shiga can cikin Dawan rukuki, nan ne idan Allah ya yi maka katari, ya gajarta wahalarka, za ka samu, Amma fa, kai, samun abin nan sai namijin gaske! Idan ka ji maganar da na gaya maka, gwamma ka koma gida ka hakura, ka bar shi ga Allah."

Abubakar ya ce, "Komai wuya idan dai zan samu, ba ni komawa gida, na gwammace garin neman wannan abu in mutu da in koma gida in zauna ina ganin takaici kullum." Dattijon ya ga dai ya kwallafa ransa ga tafiyar ya ce "Ka
kwana biyu ka huta, sa'an nan inbaka guzuri ka tafi."

**************** *********** ******* ************

Ana nan Zainabu tana gidan mijinta suna zaman jin dadi da juna, ba ta fi wata biyu ko uku ba, sai ciki ya samu. Da lokaci ya yi ta haifi ɗa kyakkyawa. Aka gayawa Malam Shaihu matarsa ta haihu, sai ya yi farin ciki da murna mara iyaka, domin dama abin dayake nema kenan sama da komai a duniya.

Nan da nan aka fada wa sarkin Galma matar Malam Shaihu ta haihu. Sarkin Galma ya aiko da kaya da yawa, yana murna kwarai. Malam Shaihu ya sa aka aika ko ina a sanar da abokansa da yaransa matar sa ta haihu. Kowa kuwa sa'ar da yaji sai murna da farin ciki masoyinsa ya sami magaji.

Ranar rada suna aka yi babban taro, aka yanka shanu da raguna, aka yi gagarumin biki har ya fi na ranar da aka yi auren yarinyar. Aka sa wa yaron suna ABDULLAHI amma galibi suna kiransa KYAUTA. Aka yi kwanaki ana ta rigima. Manyan malamai da dattijai kowa ya yi masa addu'a, Allah ya rayashi ya zama yaron kirki cikin musulunci, ya rike su kamar yadda ubansa ya rike su.

Ana nan ana nan yaron ya yi girma, aka yi masa bante, aka sa shi a makaranta ya yi karatu, har ya kusan saukewa. Tun tasowarsa yaron kirki ne mai nagarta, abin so ga kowa. Kullum abin farin ciki ne ga ubansa, babu irin jin dadin da ba ya jiyar da shi. Kullum inda Kyauta ya raba baka raba shi da yara. Ubansa ya gina masa wani kyakkyawan daki a shamakinsa, nan ne ya ke kwana tare da sa'o'insa yara. Da shi da kowa a cikin gari sai ban girma da ladabi, baya raina kowa. Inda ya wuce duka sai sa masa albarka ake yi.

Amma Abubakar bayan ya kwana biyu Yaji ya huta, ran nan dattijon ya kawo doki wanda zai hau, ya kawo kudi da zai sayi abinci a hanya, ya
End Ads