x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 5 - JIKI MAGAYI

  • 12001 words
  • 15000 words
  • Out of 18490 words

Category: Adabin Hausa

Views 58

09 Jul 2025
Start ads
After Image Ads
wahalar da shari'a ba, bazan daure ka ba,"

Sa'an nan Kyauta ya ce, "Ni ne na dauka." Alkali ya tambayi bakon, "Kudinka nawa ne?"

Ya ce, "Fam uku da sule goma." Alkali ya ce, "Kyauta kaji" Ya ce, "Haka su ke."

"Ina su ke ?"

"Na kashe saura fam piyu." "Kawo fam biyun
"Suna can, na haka rami na binne." Alkali ya hada shi da yaro, suka tafi, ya tone ya kawo
Alkali ya ce a tafi akira ubansa maza. Nan da nan nan aka tafi aka kirawo Malam Shaihu. Da ya zo alkali ya mayar masa da jawabi yace "Ga shi danka bai isa shari'a ta daure shi ba, sai ka biya, ka tafi da danka ka san dabarar da za ka yi da shi, domin kuwa gaba a ke duba. Ka san da ya isa shari'a da an daure shi."
Malam Shaihu ya fitar da kudi, ya biya, ya yi wa alkali godiya Ya tafi da Kyauta,

Da ya komo gida la'asar ta yi sosai, rana ta kusa faduwa Ya shiga da Kyauta gida, ya kulle shi. Daren nan ko abinci ya hana masa. Gari na wayewa ya sa yarensa ya tafi ya kira Malam Sambo. Da ya zo ya shiga gida ya taso Kyauta a gaba ya kawo shi wurin malam. ya ce, "Ga shi nan, ni dai ya gagare ni. Idan na bar shi tare da ni wata rana zafin rai zai sa in kashe shi. Tafi da shi kasa shi a mari, kada a kwance shi sai ya sauke. Kai, ko ya sauke ma sai na ga halinsa ya sake. Kada ka raga masa kome.. abin da duk yara ke yi sa shi, kada ka dubi wai don yana dana." Malam ya ce, "To, abin dai ya ba da mamaki, yaro wanda da babu wanda a ke so da gani kamar sa, ga shi da karatu, ga ladabi ga kowa, sa'a daya ya lalace. Allah ya yi mana taimako."

Ya tafi da Kyauta ya buga masa mari. Yana nan yana karatu, ya dami dukan 'yan makaranta da malamin, ba su da iko su ajiye kome sai ya kawar. Haka dai misalin shekara guda, har ya kusa saukewa. Rannan Malam Sambo ya ce su tafi su yiwo ciyawar jinka. Suka tafi, ana tafe yara suna ta yi masa shakiyanci da ba'a. Da suka kai kowa yana ta yankar ciyawa. Sai Kyauta ya rabu da sauran yara ya tafi can, ya dauki laujensa da duwatsu, ya dubi mari ya yi ta bugawa har ya bude. Ya share wuri ya yi rubutu da hannu ya ce,
"MALAM GA KARAFANKA NAN KA SAN WANDA ZAKA SAKA MASA, BA NI BA.
Ya kawo mari da lauje ya ajiye ya yi tafiyarsa.

Yara suka gama ciyawa, kowa ya daura, ba a ga Kyauta ba. Babbansu ya zuba yara suka watsu cikin jeji suna nemansa, ba su gan shi ba. Sai wai yaro ya zo ya ga mari da lauje a kai Ya dauka, ya karanta abin da aka rubuta. Ya mayar da su ya ajiye , ya karawo sauran yaran suka gani Aka komo aka gayawa Malam Sambo,

Nan da nan ya tafi wurin Malam Shaihu da bacin rai, ya ce, "Na zo ne in shaida maka yaro na aike su ciyawa tare da yara, ya gudu."

Malam Shaihu yayi Shiru, abin da a ke gudu ya auku, Malam. Yanzu na rabu da yaron nan kenan. Na sani ko da Allah zai yi nufin in ganshi, sai da bakin ciki da kunya.
Yaya ke nan?"

KYAUTA kuwa ya mika cikin duniya abinsa. Uban ya sa aka yi ta nemansa, ko labari ba a ji ba. Sai ya hakura, ya ce, "Na sani lalle idan ba mutuwa ya yi ba, ina zaune za'a zo mini da labarin wani mugun abu da ya yi."

Kyauta ya yi ta yawace-yawacensa, har rannan Allah ya kai shi wani gari babba kamar Galma, tsakanin garin kuwa yar jirgi bai cika nisa ba. Da ya tafi, ya sami 'yar kwarya, idan yamma ta yi ya shiga gari yana bara, da safe idan ya sami aiki ya yi, in ya tafi wani lokaci ya cinye kudin a kamo shi a bubbuge shi a sake shi.

Ran nan ya tafi wurin akawun kanti, ya ce masa yana so ya zauna tare da shi ya rika diba wa matarsa ruwa, ya yi masa aiki. Akawun da ya gan shi wayayyen yaro ne, ga shi kuma da kyau, ya ce zai yi shawara da uwargida, idan ta yarda zai dauke shi. Kullum kullum ya zo, ran nan sai akawu ya ce, "Shikenan, ka komo gidana ka zauna."

Akawun ya tambaye shi. "Ina garinku?" Ya ce. "Garimmu da nisa, ni ma ban sani ba, gama ni tun ina Karami iyayena suka mutu, aka ba da ni goyo ga kakata, ita kuma ta mutu a wani gari, shi ya sa na ke yawace-yawacena." Yana nan gidan akawu, matarsa da shi duk suka amince da shi, sai ya shiga kanti lokacin da ya ke so Idan akawu za shi gida cin binci sai ya bar shi tsaron kanti. Kyauta kuma sai ya taba halinsa, amma da wayo ba yadda za a gane ba....JIKI MAGAYI-07

Ana nan ana nan, sai ya ce da akawu, "Na ji barguna da yan basuma suna ciwuwa a Samu, ya kamata ka ba ni in tafi, watakila ma Karu, Idan na sayar kuma inyiwo gyada."

Akawu ya ce, "To, gobe idan jirgi ya zo zan auna maka wadansu hajojji ka tafi, zan kuma ba ka kudi." Ya yi ta murna.

Tun da yamma ya shirya masa kaya na wajen fam ashirin

Da safe ya kawo kudi fam goma ya ba shi, ya ce ya rika sayen gyada da su kafin ya sayar da hajjar. Ya sa masa kaya a jirgi. Da fitar Kyauta kudin nan fam goma su ya fara sa musu sanda ya rabke, wadanda kuma ya samu na hajja ya kashe, bai sayi kome ba. Shiru shiru akawu baiji motsinsa ba. Sai ya ta da wani yaronsa ya tafi ya ga abin da Kyauta ya ke ciki. Ka san duniya idan mutum yana da samu ba ya rasa masoya sai wani ya riga yaron akawu ya tafi ya gaya wa Kyauta akawu yana aikowa a caje kaya. Da Kyauta ya ji hakanan sauran kudaden da ke tare da shi sai ya Boye, ya sa wa dakin da ya ke kwana wuta, ya koma ya yi tulu.
Da yaron akawu ya zo ya iske Kyauta ba shi da kome ko riga ma sai 'yar tsumma. Ya tambaye shi, "Ina kaya?"
Ya ce. "Kaya wuta ta cinye, kudi kuma an mini sata. Yaron akawu bai ce masa kome ba, sai ya koma ya shaida wa mai gidansa. Nan da nan akawu ya sake aikawa a yi rahotonsa, aka ji kudi ya kashe ne, daki kuma shi ya sa wuta da hannunsa. Da yaro ya sake komowa ya shaida masa, sai ya yi karar Kyauta gidan sarki, aka sa nan da nan aka tafi aka zo da shi. Sarki ya bi maganar duka, ya iske Kyauta ya tabbata mugun yaro, Ya tambaye shi garinsu, ya ce shi mutumin Galma ne. cikin Galma kuwa dam Malam Shehu.

Sarki ya ce, "Allan wadanka! Kazama dan banza, ko da na sami labarinka." Nan da nan ya rubuta takarda ya aika Galma ya shaida wa ubansa ga dansa an kama shi ya yi zamba, ya zo.

Da aka zo da takarda Malam Shaihu ya karanta, sai ya fada cikin gida da hasala da bacin rai, ya ce, "Ko da ma na sani ba zan ga yaron nan ba sai da wai bakin ciki.

Ran nan ya yi shiri ya dauki kudin da zai biya, da kuma tufafi da kudi domin ya rarrashe shi ya komo gida. Kwanci tashi har suka kai garin. Sarki ya sa aka saukar da shi. Da gari ya waye aka fito da Kyauta daga matsara. Malam Shaihu ya tafi, aka mayar da magana. Sa'an nan sarki ya ce. "To, Malam Shaihu, shekarun danka nawa ""

Ya ce, "Ran sarki ya dade, yau shekarunsa goma sha hudu da wata uku". Sarki ya ce, "Bisa ga shari'a bai balaga ba, shari'a ba ta daure shi ba amma kai ne mai lamuninsa. Kudin nan da ya ci na akawu za ka biya. Bayan ka biya, za mu ba ka danka, za ka tafi da shi gida ka lura da shi, domin kuwa idan ba ka iya ba, wahala ba ta kare tare da kai ba." Malam Shaihu ya biya, ya yi wa sarki godiya, ya tashi da Kyauta, suka koma masauki.

Ya Kwana yana rarrashinsa ya daina halinsa, ba irin abin da bai ce zai ba shi ba idan sun koma gida ya sake halinsa. Cikin daren nan ya kawo girken Nufe da wandon zina da rawani ya ba shi. Kyauta ya yi masa alkawari idan sun koma gida zai zama yaron kirki, ba zai kara halinsa ba.

Gari ya waye Malam Shaihu ya tafi ya sallami sarki, suki mika da shi da yaransa da dansa. Kwanci tashi sai da ya rage zango daya su kai Galma, can dare ya yi, Raba duk ta dauke suna kwance, sai Kyauta ya shiga dakin da ubansa ya ke kwance, ya dauke masa kudi da tufafi ya gudu.

Da gari ya waye shiru shiru bai ga Kyauta ba, ya duba babu riguna babu kudi. Ya kira yaronsa ya ce masa, "An yi mini sata. Ina yaron nan ?"

Ya ce, "Tun dare rabuwarmu da shi ya fada mini za shi yawo cikin gari, muka tafi tare, amma ni na rigaye shi komowa." Malam Shaihu ya yi salati, ya sanar da Ubangiji, ya rasa abin da zai ce. Aka nemi yaro Kasa da bisa cikin gari, ba a gan shi ba. Malam Shaihu ya hau ya koma gida cikin bakin ciki. duk ya rude ya rasa abin da ya ke ciki. Ya baza yaransa ko ina suna neman Kyauta wata da watanni ba su ji labarinsa ba, suka komo.

Ashe da Kyauta ya gudu bai zame ko ina ba sai Kano, ya kadar da abin da ya kwashe na ubansa sarai, ya sayar da rigar da ubansa ya ba shi da wandon, ya taushe kudin, ya yi zamansa, ya yi ta sace-sace, har aka dade Wara rana da daddare bayan duk an yi barci. Ya zo wani gida ya shiga ke nan, ashe yan gadi suna ganinsa. Sai da suka bari ya shiga, sa'an nan suka tafi suka kirawo wadansu mutum biyu, suka yi su biyar, kowane daya ya tsaya a kusurwa. "Daya ya shiga gida ya ta da yaron mai gida, ya ce, "Yanzu muka ga barawo ya shiga gidan nan, shiga ka ta da mai gidan."

Yaro ya shiga ke nan sai suka yi karo da Kyauta ya yayo kayan mata da zannuwa ya daure cikin zane ya dauko. Sai yaron ya kama shi, ya ce, "Barawo, Barawo!" Kyauta ya jefar da kaya. Nan da nan 'yan gadi suka shigo suka kama shi. Cikin dare aka tafi da shi gidan sarkin gadi da kayansa, ya kwana.

Da gari ya waye aka kai shi gidan alkali, aka daure shi shekara biyu.

A KWANA a tashi rannan wani Bakano ya zo da kaya ya sauka gidan Malam Shaihu. Ana cikin tade-tade sai ya ce, "Kano dai Barayi sun tasar mana. Bai fi wata shida ba aka kama wani yaro mai kama kaza, mai kama kaza, ya shiga gidan wani ya kwaso kayan matansa. Aka ba shi odar shekara biyu."

Da Malam Shaibu ya ji irin kwatancin da Bakano ya yi a ransa ya ce, "Lalle yaron nan da kyar zai rasa kasancewa dana ne." Sai ya kira wani daga cikin yaransa wanda ya yarda da shi ya ce masa, "Ka gani yanzu tsakanina da mutanen gari sai ta fatar baki kadai, ka ga na zama abin dariya da ba'a ga kowa sabili da yaron nan. Ina so ka zo ka tafi Kano, zam ba ka kayan sayarwa, ka tafi ka zauna can. Ka rika lura da kyau da kuma tambaya a hankali, watakila Allah zai sa ka ga yaron nan cikin fursuna. Da ka ganshi ka niko mini da takarda in sani."

Yaron ya ce, "To, Allah-ya sa in gan shi." Malam Shaihu ya ba shi kaya. Ya sayi doya buhu talatin, ya auna masa a jirgi, ya tashi. Ya tafi ya zauna a cikin gari, yana sayar da kaya yana tambayar labari. Doya ta kare, ya aiko masa har yanzu dai bai ga yaro ba, amma ya aika da wata doyar. Aka sake aika masa da buhu hamsin. Ran nan ya fita garin ya dauko doya a tasha, sai suka hadu da Kyauta cikin fursuna za su ta aiki. Da dai Kyauta ya gan shi sai ya dauke kansa. Sai yaron ya yi magana da ganduroban suka gaisa, ya fada masa ya ga daya daga cikin fursunan can dan mai gidansa ne a Galma, ya rabu da gida shekaru da yawa. Ganduroba ya kira Kyauta ya ce, "Ga yaron ubanka" Ya zo suka yi gaisuwa ya tambaye shi labarin gida da uwa tasa.

Yaron ya ce masa, "Sauran watanka nawa?" Ya ce, "Saura shida." Ashe sauran watansa daya kadai yafita. Yaron ya kawo 'yan kudi ya sunna wa ganduroban, ya kawo kuma ya ba Kyauta. Suka tafi wurin aiki. Yaron kuma ya tafi tasha ya dauko doya.

Ko yaushe idan ya so ganin Kyauta, sai ya zo hanya ya tsaya, in za su wuce su yi gaisuwa. Sai ya rubuta takarda ya aika wa Malam Shaihu ya ga Kyauta shi da shi, har sun yi magana, sauran watansa shida a kwance shi. Ashe yaron bai san an kwance Kyauta ba, sai ran nan ya tafi hanya inda ya saba ganinsa. Da ya ga duroban ya ce, "Ina Kyauta yau? An yi canjinsa a nan ne?"

Duba ya ce, "Ai an sake shi jiya Ni ma ca na ke ya nemi inda ka ke ya zo. Ya ce, "Wallahi, ban gan ski ba."

Nan da nan ya koma gida, ya shirya kayansa ya koma Galma, ya fada wa mai gidansa irin batar da sawu da ya yi masa. An sake shi, amma ba wanda ya san inda ya yi.

Kyauta da fitarsa daga fursuna, sai ya hadu da wani barawo sunansa DOGON YARO ya ce zai shiga jirgi zuwa. Ikko, domin kuwa shi can ya ke zama. Kyauta ya ce ya yi masa dalili su tafi tare ya ga wuri, gama bai taba zuwa can ba sai dai labari. Barawon ya biya masa kudi, suka shiga jirgi sai Ikko. Suka Dogon Yaro ya ba Kyauta ya kawo tudu ya Batar da shi ya yi zamanu a kawo masa kudi. Haka dai su ke yi, har Kyauta da kansa ya Ikko, idan Allah ya yi musu sa'a suka yi sata. zama kuntukurmin Barawo, ya shiga tambaye-tambayen magunguna na sata, har kuwa ya samu. Su biyu suka zama mashahuran barayi a Ikko, da kuma a ketare.Wata rana daga Ankara suka runkuma kasaitacciyar sata, suka gudo, aka neme su ba a same shi ba, suka nufo tudu. Suka zauna, suna ta nasu nishadi. Aka yi ta nemansu ko ina ba wanda ya ji labarinsu. Su kuwa da suka yi zana akin ko wane gari, sai suka tafi suka sami wani kungurmin daji suka zauna can, sai su kwarari gari su yiwo sata su komo su yi zamansu, ba abin da ya sha musu kai.

Da dai abu ya dami Malam Shaihu, ya rasa yadda zai yi zuciyarsa ta huce. Yana zaman bakin ciki da faduwar gaba ko wace sa'a, domin bai san labarin da watarana za'a kawo masa ba. Ga shi cikin gari yana ma kunyar fita waje, in ga mutane sun hada kai sai ya zaci zancen dansa su ke yi. Kuma idan ya wuce za shi wani wuri ya ga taron yara sai ya kaddara zundensa su ke yi suna cewa, "Ga uban barawon nan yana zuwa!" Idan ya gamu da wani mutum a hanya wanda ya san labarin dansa sai ya kauda fuska, ba ya yarda su hada ido. Har ya zama dai ya daina fita waje saboda kunya, yana zaune cikin gida kurum sai zullumi

Zainabu kuma a cikin gida ba ta da kwanciyar rai, domin idan magana ko ta zafi ko ba ta zafi ba ta hada ta da kishiyoyinta sai su rika yi mata gori da habaice habaice cewa, "Irin aure auren kenan, har a je a auro wadda za ta haifi mugun da! Da haihuwar Barawo gwamma Bari." Kullum sai ta bingire da kuka ta rasa abin da ke mata dadi, duk ta kare. Har rannan ta je wurin mai gidanta, tace masa, "Irinta kenan dai, ina zaman zamana ka tilasta mini, to, ga abin da ya jawo mana. Da na tara sani da Allah in na aure ka haka al'amari zai juya, ko da wasa ba na fara ba, ba gwamma in fada a ruwa na mutu ba? Raina me ya dada mini? Shehu Allah ne mai sakayya tsakanina da kai."

Wannan magana ta dada bata wa Malam Shaihu zuciya, har ya zama babban muradinita ne ya bar garinsa da gidansa da dukan abin da ya mallaka, ya tafi wata kasa inda ba a san shi ba, ya yi zamansa da rai a kwance.

Sai ran nan ya kirawo Zainabu su biyu, ya ce mata, "Abin da ya sa na yi kiranki irin maganganun nan da ki ke yi mini sun shiga raina. Ke a ganinki abin nan da mutane su ke fadi kammu bai dame ni ba ko To, zan gaya miki na yi shawara a raina zan fita wannan gari, in bar kome da kome in yi tafiyata wata kasa inda ba a san ni ba, in zauna lafiya, Za ki ?" Ta ce, "Ni Zainabu ba zan bar mahaifata ba. in tafi wani wuri in zauna. Idan kai dai za ka, sai wata rana."

Ya ce, "Ashe watau har zaman garin nan dadi ya ke miki da ba ki son barinsa? Ba ki sani ba idan na tashi dukan surutun nan da a ke mana a kanki kadai za su kare? Har ma a rika kiranki mai bakin kashi, sabo da ke mijinki ya dora ya bar dukiyarsa da gidansa?"

Ta ce, "Kome aka so a kira ni kai ka jawo mini." Ya yi ya yi da ita, da
End Ads