x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 3 - JIKI MAGAYI

  • 6001 words
  • 9000 words
  • Out of 18490 words

Category: Adabin Hausa

Views 59

09 Jul 2025
Start ads
After Image Ads
kawo tufafin sawa da na rufa, ya ba shi, ya sa shi a hanya, ya ce masa, "In ka fita daga nan kada ka ratse ko ina sai ka kai wani gari da a ke ce masa SANGA. Daga nan idan ka huta ka tashi ka yi arewa tafiyar kwana kamar bakwai, kana ta tambayar Dawan Rukuki, in ka bi ga ka yi ta yawo, watakila Allah ya yi maka gamon katar. Ka san irin abin da za ka nema abu ne mai sihiri, ba shi da wuyar bacewa, har wani lokaci ya kan yi wa mutum kwari ya haukace ko ya mutu.

Ya ce, "Ban taba ganin irinsa da idona ba tun da na fito duniya."

Dattijon ya ce, "Idan Allah ya gwada maka shi, za ka ga wurin da ya ke ya dauki haske sai ka ce rana. Shi kuwa dan rankafen abu ne. Amma galibi idan ka je za ka dauka, ya kan Bace. Idan ka shiga Sanga ka sami batta, ka shafe ta da kitse, a ciki za ka saka in ka samu."

Suka yi sallama da juna, dattijon ya ce, "Allah yabaka sa'a, ya gajarta wahalarka!" Ya ce, "Amin."

Abubakar ya shirya 'yan kayansa ya daure, ya taka dokinsa ya hau. Ya yi ta tafiya cikin kungurmin daji. Tun da ya tashi bai gamu da kowa ba sai mutum guda kusa da Yale. Mutumin ya ce masa, kai kuwa Wannan mutum, ina za ka cikin wannan kungurmin daji kai kadai sai doki da wannan kaya haka a sarari? Ba ka tsoron hadari? Da alama dai kai bako ne, ba ka san hanyan nan ba."

Abubakar ya ce masa, "Za ni Sanga ne." "Sanga Amma wannan mutum da wargi ka ke, kodayake ban san irin shirinka ba. Je ka, Allah ya fisshe ka " Yace, "Amin."

Tun daga nan Abubakar ya soma jan Li'ilafi, yana ta tafiya har rana ta take: Yana dai ta yi, har shi da dokinsa suka tarke don yunwa da tsananin kishinwa.

Ya ciccije, suka isa wani babban rafi mai kwazazzabo da kyar. Da zuwansa sai ya sauka ya kowance wa dokinsa sirdi, ya debi 'yan kayansa ya kai inuwa, yaja dokin ya gangara da shi yasha ruwa ya yi wanka a rairayi.

Sa'an nan ya jawo shi tudu ya yi masa tarnaki, yana cin ciyawa a bakin ran. Shi kuwa ya gangara, ya tube ya yi wanka. Ya sa tufafinsa, ya debo ruwa, ya hayo ya zauna a inuwar da kayansa da dan guzurinsa yana ci. Babu zato Babu tsammani.....JIKI MAGAYI-04

Babu zato Babu tsammani ya duba bayansa sai ya hango mutum biyu suna zuwa, ko wanne da kwari cike da kibau, da baka da wata kibiya a zare, sun nufo shi. Shi dai a lokacin nan zaune ya ke kamar wanda ya mutu don tsoro. Da zuwansu sai daya ya yi sallama, Abubakar ya amsa "Kai, ina za ka?" da rawar jiki,
"Barawon ya ce, Ya ce, "Sanga."

"Kai bako ne ba ka taba bin wannan hanya ba ?"

Ya ce, "Tun da na ke ma ban taba zuwa kasar nan ba." Sai dayan ya ce da dan uwansa, "Kai wane irin mutumin banza ne, mun zo mu yi hira ne? Mu yi abin da ya kawo mu mana, mu tafi."

Ya ce. "Kai, da ranka da kayanka ka zabi na zaba"

Abubakar ya ce, "Na zabi raina."

Ya ce, "Tube riga da wandon da ke jikinka ka dora bisa kayan nan naka." Ya tube, ya dora, Sai dayan ya tafi garin ya kwanto doki. Da doki ya ga ba ubangijinsa ba ne, ya dinga harbe-harbe da cije-cije. Sai ya ce, "Zo mana, kana ganin dokinka zai cije ni!"

Sai Abubakar ya yanka a guje, ya kama doki, yasa masa linzami ya jawo, ya daura sirdi. Suka ce, "Je ka abinka!" Sai ya kama hanya tik sai turen bante. Da dai suka ga ya fara tafiya sai daya ya ce, "Tsaya nan!"
Abubakar ya tsaya cif, ko daga kafa bai yi ba, jiki duk na rawa. Da zuwan dam fashin sai ya kife shi da mari ya kife, ya zare wuka ya yanke masa rabin kunne, ya bar shi nan. Su kuwa suka tsere da kayan. Abubakar yana nan kwance sai kururuwa ya ke yi, ga zafin mari ga kunne yana ciwo, ga takaicin kayansa duk an kwace. Zuwa can sai ya farfado, ya ja jiki duk jini, ya kama hanya ya yi ta yi har la'asar, bai gamu da kowa ba, babu kuwa wanda ya cim masa. Sai da la'asar sannan ya ji maganar mutane suna zuwa a bayansa, tsammaninsa wadansu yan fashi ne, sai ya shige daji kadan, ya rabuke a jikin wata itaciya. Ashe masu jakuna ne su ke zuwa. Da ya ga haka,
sai ya fito ya tsuguna a hanya. Da suka zo suka ce, "Kai, me ya same ka?" Yace. "Daga Yale na fito za ni Sanga, 'yan fashi suka tare ni a hanya suka kwace min dukan abin da na ke da shi, suka bubbge ni, kun gani har kunnena ma sun datse don keta"

Da suka Ji dukan abin da ya gaya musu suka ce, "Lalle hakanan ne, gama jinin ga alama a hanya. Suka yi masa juyayi, wani daga cikinsu ya kawo 'yar taguwa ya ba shi. Suka dora shi a kan jaki, suka kai shi wani gari, suka wuce. Ranar dai kam ya rasa gidan sauka ya kwana da yunwa a kasuwa. Da gari ya waye babu abin karin kumallo, sai bara, wanda ya ga Allah ya ba shi sadaka. Kwana da kwanaki yana kwana a kasuwa. Ran nan sai wani mutum ya gan shi ya tambaye shi inda ya fito. Ya gaya masa dukan hadarin da ya same shi. Ya, ji tausayinsa ya karbe shi a cikin gidansa, har ya huta karfinsa ya komo. Da ya yi 'yan kwanaki ya huta sarai, ran nan sai ya ba shi guzuri, suka yi sallama, ya dauki hanya.

Kwanci tashi yana ta tafiya har ya kai wani gari ana ce masa RIMI da lisha. Ya nemi masauki, ko ina ya tafi sai a kore shi. Da dai ya ga babu wurin kwana, sai ya tafi kasuwar garin, ya nemi wata rumfa ya shiga ya kwanta. Ya yi barci kai daya sai ya ji ana cewa, "Barawo! Barawo!" Aka nufo kasuwa. Shi kuwa don ragon azanci, ga shi bako ba wanda ya san shi, sai ya fito ya tsaya a kofar rumfar. Sai wani mutum ya ga baki baki ya ce, "Gudummawa jama'a! Ai ga shi nan!" Nan da nan aka yi masa caa, aka rufe shi da duka, yana cewa, "Ku tsaya, ku tsaya, ni ba Barawo ba ne! Ni bako ne yau na sauka, na nemi wurin kwana ko ina a cikin gari ban samu ba, shi ya sa na komo kasuwa na kwanta. Gama kayana can a rumfa". Mutane suka ce, "Karya ya ke yi, lalle shi ne Barawon da aka
koro yanzu
Aka daure shi tam, sai gidan sarkin Rimi. Da gari ya waye aka kai shi gidan alkali, aka tambaye shi garin da ya fito, ya ce daga GALMA ne.

Suka ce, "Ba mu taba jin wani gari da suna haka ba. Lalle Karya ya ke yi, Barawo ne". Alkali ya ce a yi masa bulala, hamsin, a daure shi wata uku. Aka gwada masa azaba mai yawa.

Bayan ya gama wata uku aka kwance shi, aka kore shi daga garin. Ya kama hanya tasa. Duk wahalan nan da ya sha zuciyarsa ba ta girgiza ba, sai dada kekashewa ta yi, duk hankalinsa yana kan rama muguntar da aka yi masa.

Yana ta tafiya, kwance tashi har ya kai Sanga. Kullum a zuciyarsa ya kan ce, "Ba ni dai komawa gide komai wahala, sai na samo Karon kalgon nan, bisa ikon Allah

Da ya tuna da wuyar da ya sha a Rimi yana zuwa garin sai ya nu fi gidan sarki, ya ce shi bako ne zai wuce, amma yana neman masauki. Sarki ya tambaye shi daga inda ya fito, ya fada masa. Ya sa aka ka shi bakin kasuwa, aka saukad da shi a gidan wani mutum mai samu, ga shi kuma mutumin kirki. Yana nan zaune gidan da sarki ya saukar da shi, babu abin da ya rasa na wajen abinci.

Ran nan suna zance da mai gidansa sai ya ce masa, Zaman nan ba zai yi mini ba, ka ji ka ji abin da ya ke tafe da ni, an yi mini kwatanci ne da dajin can na Rukuki, an ce sai a can zan sami abunda na zo ne nema

Mutumin yace masa, "Lalle kuwa sai can, domin kuwa akwai daji, babu irin abin da ba za a samu a ciki ba. Amma ya kamata ka zauna kwana biyu ka huta sarai, gama ka gaji da wahala. Sa'ad da ka huta sa'an nan na ba ka dan guzuri ka tafi". Abubakar ya yarda da magana tasa, ya yi zamansa, yana dako yana samun 'yan kudinsa yana kullewa har ya tara guzuri.

Ran nan ya ce wa mai gidansa yana so zai tafi. Ya kawo guzuri mai yawa ya ba shi. Abubakar ya kintsa kayansa har ya sami battar da dattijon nan ya ce masa ya nema, inda zai jefa Karon kalgon idan ya samu. Sai ya mika, ya kwana wannan gari, ya tashi ya kwana wancan, har ya zo wani gari ya kwana, aka ce masa babu wani gari a gaba.

Ya tambayi labarin Dawan Rukuki, amma bai sami tartibi ba, domin kowa ya tambaya sai ya ce bai taba zuwa ba. Amma,. kowa ya sani mugun daji ne da gaske, ba su ma taba jin labarin wanda ya je ya komo ba. Ya zauna nan ya fara shiri don wahalar da ke gabansa. Da ya gama shiri sarai sai ya tashi ya kama hanya, har ya wuce karkara, tungana ganin kauyuka daya daya har ya komo kuma ba ya gani sai makiyaya. Bayan kwana da kwanaki su ma ya daina ganinsu. Bai dai fasa ba yana ta tafiya, har ya sami gidan wani maharbi can cikin kungurmin daji. Sai ya ratse gidansa, ya yi sallama, mai gida ya fito ya tambaye shi abin da ya kawo shi cikin wannan daji. Da ya gaya masa ya yi mamaki, ya ce, "Da za ka ji shawarata da sai ka koma tun kana da sauran sukuni, in ka ki tawa ka wuce, lalle ba za ka komo ba. Domin wannan ba karamin daji ba ne, ko ni da ya ke daji ne gidana, iyakata nan, na kan kuma yi wata uku ban ga wani mahaluki ba."

Abubakar ya ce, "Na ji na gode, amma tun da na rigaya na yi niyya babu abin da za ka gaya mini wanda zai kaushe ni daga nufina. In yi tafiya irin wannan mai dadewa, ga hadari da wahala, sa'an nan in koma hannun wofi ?"

Sai maharbi ya ce, "Kome hadari da wahala da ka sha kadan ne bisa ga wadanda za ka sha gaba nan." Daga nan ya shiga ba shi labarin abin da ya sani na dajin nan na wajen ban tsoro da mugunta da aljannu da ke ciki. Da ya ga dukan abin da ya gaya masa ba su razana shi ba, bai kuwa kauda shi daga nufinsa ba, sai ya kyale shi, ya ce, "Amma gobe zan raka ka har dutsen can, a nan zan nuna maka inda za ka nufa."

Da gari ya waye suka kama hanya da shi da maharbi har suka kai dutsen da ya fadi, suka hau. Daga can Abubakar ya duba, iyakacin ganinsa babu komai sai kungurmin daji baki kirin, gwanin ban tsoro. Sai maharbin ya ce, "Ka ga dutsen can dushi-dushi, ta nan za ka raba. In ka kai ka mike sosai, ina tsammani in ka yi ta tafiya kwana da kwanaki za ka fara shiga cikin dajin Inda abin da ka ke nema ya ke."

Abubakar ya yi masa godiya, sukayi sallama da juna, suka ce, "Allah ya sake gama fuskokin mu." Maharbin ya koma da baya, Abubakar ya wuce. Abubakar ya tafi kwana da kwanaki har ya shige dutsen. Ya yi ta tafiya har yatsammaci ya kai inda aka ce ya soma nema. Sai ya sami wani kogon dutse ya ajiye kayansa. Idan almuru tayi ya shiga nema, ba ya komowa sai gari ya waye. Haka ya yi wata da watanni, har guzurinsa ya kare. Sai ya shiga cin 'ya'yan itace da saiwoyi da kwari. Dukan lokacin nan bai ga kome ba, har ya soma fid da zuciya.

Sai ya tashi ya fara gaba yana ta nema. Da rana ya sami kogon dutse ko na itace ya shiga ya yi barci. Da haka da haka har ya manta da lissafin shekarun da ya yi..

Ana nan ana nan wata rana yana yawo cikin daji sai ya hango wani abu yana kalkali kamar rana a jikin wani kalgo, duk murna ta kama shi, jikinsa ya dauki rawa, ya katsa a guje don ya ciro. Cikin gudu sai ya ci karo da wani kututture ya fadi, hakoransa suka fita. Da ya tashi bai ga kome ba, wuri ya yi dudum kamar da. Ya yi ta duba ko ina, duk ya tattake kewayensa, yana dubawa har gari ya waye. Sa'an nan zafin hakora ya tashi, ya rasa abin da ya ke masa dadi nan duniya. Ya zauna, nan ya ke yini da kwana, amma bai sake ganin kome ba. Ya cika da bakin ciki. Sai ya tashi daga wurin, ya yi ta nema. Ya dade da gaske bai sake gani ba.

Wata rana sai babban hadari ya taso, aka tsunke da ruwa. Amma a wannan lokacin ba ya kula da zafin rana ko ruwa kome tsananinsu, sai ya yi ta yawo yana nema. Yana cikin tafiya sai aka yi babbar walkiya da tsawa gaba daya, idonsa ya dushe, bayan haka sai dudum, ba motsi. Can sai ya daga kai ya hango haske kal. Bai yi wata-wata ba sai ya yanka a guje ya nufi can, sai ga kalgo shirim a gabansa kamar zai ci karo da shi, abin na walwal a jikinsa. Ya yi tsalle zai ciro. Kwaram sai aradu ta fada wa itacen ta tsaga shi biyu, ya fadi kasa tija! Tuni an yi jifa da Abubakar, yana can kwance bai san abin da aka yi ba. Bai farka ba sai can gari ya yi sha. Ya ga itacen ya bushe, babu alamar abin da ya gani da dare. Ya tashi jikinsa na nauyi, ya yi kwanaki kafin ya murmure ya iya yawo.

Ba'a dade ba da yawa ya sake ganinsa, gani na uku,, Ya kwana yana yawo ya gaji, sai ya juya zuwa mahutarsa, gari ya kusan wayewa. Ya duba gabansa, sai ya ga haske kamar hudowar alfijir, ya ce, "Ashe gari ya waye." Ya waiwaya, ashe abin da ya ke nema ne, haskensa kuwa ya fi dukan na sauran da ya gani. Nan da nan ya manta da gajiya, sai ya sheka a guje da bakin karfinsa don kada ya sake bace masa, kafin ya kai. Da ya mika hannu har ya taba shi sai ga katon kumurci ya tashi tsakaninsa da gindin itacen bakikirin, kaurinsa kamar cinya, bai ga iyakar tsawonsa ba. Sai ya fadi da baya, kumurcin ya fasa kai yana dubansa, idanunsa kamar garwashin wuta, yana fitar da harshe jawur kamar tartsatsi. Abubakar ya rufe idonsa ya ba da rai ga mutuwa.

Sai ya ji tsawa ana cewa, "Kai mutum, wane karambani ne ya kawo ka nan? Hadarin da ka shiga sau biyu ba su ishe ka ba

Cikin tsoro ya ce, "Wane ne?"
"Ni ne wanda sarkin aljanu ya mallaka mini dukan Karon kalgo. Babu kuwa wata halitta da za ta iya kwace shi daga hannuna sai wanda na ga dama in ba shi. Kai kuwa yau shishshiginka ya kawo ka ga halaka.

Abubakar ya ce, "Ranka ya dade, wallahi ban sani ba. Ba shisshigi ne ya kawo ni ba." Ya fada masa dukan dalilin abin da ya kawo shi.

Sai ya ji ya kyalkyace da dariya, ya ce, "Samari, ko da mu ba domin alheri a ke neman mu ba sai don mugunta. Da ka zo gare ni tun da fari da dukan wannan wahala ba ta same ka ba. Dukan muguntar da ka ke so na taimake ka da ita, amma ban da alheri, domin mugunta ita ce halina, wanda kuma ya yi nufin yinta shi ne abokina."

Daga nan ya suma, bai san komai ba. Da ya bude ido sai ya ga rana ta fito, shi kuwa yana kwance a gindin kalgo daidai inda ya fadi. Ya dubi nan ya dubi can, bai ga kumurcin ba, sai ya tsammaci ya yi mafarki ne. Sai ya duba ya ga battarsa, ashe ya yar da ita sa'ad da ya fadi. Ya mifa hannu ya dauka, sai ya ji wani abu yana rawa, ya bude sai ya ga haske kal, ko da ya ke da rana. Ya yi maza ya rufe, ya yi hamdala. Ya kunshe a jikinsa, ya tashi ya tafi, bai san abin da ya ke ciki ba, duk ya rude saboda murna da farin ciki. Sai ya kama hanya ya tasam ma wajen mutane. Ya yi ta tafiya yau da gobe, har ya fita daji ya shiga karkara, da haka da haka har ya kai SANGA.

SAIDAI FA KASH.....JIKI MAGAYI-05

ABUBAKAR ya yi kwanaki a Sanga ya sami abokan tafiya sa'an nan ya shiga cikin ayari, ga su nan ga su nan sai Yale. Da shigarsa bai zame ko ina ba sai gidan dattijon nan, uban Tausayinka-da-saufi. Da ya tafi tsohon ya gan shi bai gane shi ba. Ya ce shi ne Abubakar. "Tsohon ya ce, "Wane Abubakar ?" Ya ce wanda aka aiko shi daga Zauna-da-shirinka.

Tsoho ya ce, "Karya ka ke yi. Domin ka ji labarin wani yaro sunansa Abubakar ya zo nan na yi masa goma sha biyu na arziki, shi ya sa kai kuma ka zo."
Abubakar ya ce, "Wallahi, ni ne." Tsoho ya ce, "Ni ban yarda ba. Abubakar wanda ya zo daga Zauna-da-shirinka kyakkyawan yaro ba inda ya ragu, ga shi kai kuwa mummuna, baki, babu hakora, sai gizo kamar Barawo. Abubakar ya ce, "Abin da ya sa ka ga na fita kamata yunwa
ce, da wahalar tafiya. Ka ga tabban nan na jikina, bulala ne hamsin da aka yi mini
End Ads