x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 6 - SHEIKH HEESHAM

  • 15001 words
  • 16100 words
  • Out of 16100 words

Category: Comedy Stories

Views 252

28 May 2025
Start ads
After Image Ads
isa gidan




Kallonta ya yi ya ce" ki shiga Heeshama zani unguwa?" kallonsa ta yi sai kuma ta kwaɓe fuska ta ce" Abba zan bika" girgiza mata kai ya yi ya ce" kije gida kinji Allah ya Albarkaci rayuwarki" murmushi ta yi ta ce" Ameen Abba na, Allah ya dawo dakai lafiya" "Ameen" ya furta da kyar, a hankali ta sauka tana tafe tana waigowa taga shima kallonta yake har ta shige parlon.



"Ina zamuje Sir?"

"Airport" Sheikh ya furta yana lumshe idanunsa shi kaɗai yake furta

"Ya Allahu Ya Rahmanu, Ya Zul-Jalalu wal ikhram".




"Mami banfa gansa ba" harararta Mami ta yi ta ce "wlh idan naje na ɗaukoshi sai ranki ya ɓaci" gyaɗa mata kai Shareefa ta yi sannan ta zauna suna hira da Nihal.



Duba sosai Mami ta yi amma bataga gold ɗin ba, sosai kuma abun ya ɗaure mata kai dan tasan babu kowa a gidan idan ba itaba, Shareefa, Nihal a parlon. Sakkowa ta yi tana kallonsu ta ce" bakuga inda na ajiyesa ba jiya ko na canza masa waje ne?" da mamaki suka ce "wai kema baki ganshiba Mami?" gyaɗa musu kai tayi Shareefa ta ce

"Kuma naga babu wanda ya shigo gidan nan jiya"


"Nima abunda yake bani mamaki kenan" Mami ta faɗa. Shuru suka yi sai kuma Nihal ta ce

"To ko za'a tambayi Jiddah ne ko ta gansa?" da sauri Shareefa ta ce" a ina Jiddah ta ganshi batama san mene gold ba bare ta ɗauka".


"Nifa cewa nayi a tambayeta ko ta ganshi, ko ya kika ce Mami?"


Da sauri Mami ta yi hanyar ɗakin Jiddah ba tareda ta sake yiwa koma magana ba.



"Mu koma gida i forget something"

Sheikh ya faɗa lokacin sun kusa kaiwa Airport ɗin, okay kawai drivern ya ce sannaa ya yiwa sauran motocin umarnin dasu koma suka kama hanyar gida.



Bata cikin ɗakin amma ruwa na zuba a banɗaki alamar wanka take, dube-dube Mami ta hau yi a ɗakin, time ɗin Shareefa suka shigo da Nihal da sauri Nihal ta ce" lemme help you Mami" daga nan ta fara bincike duka cikin ɗakin ita kuwa Shareefa sai binsu da kallo take.



"Mami i got it"

Nihal ta faɗa da ƙarfi, da sauri duka suka juyo suka kallonta tana riƙeda sarƙar gold ɗin a hannunta, tsabar shock sun kasa rufe bakinsu hatta Shareefa kallon sarƙar take da sauri Mami ta karɓa tana cewa


"Ina kika ganta Nihal?"

Daidai nan Jiddah ta fito daga banɗakin tana kallonsu da mamaki

"A cikin wasu kayanta ta ɓoye Mami"

Iyaka ɓacin rai ran Mami ya ɓaci ita kuwa Jiddah kallonsu take da rashin fahimta da sauri Shareefa ta shaƙe mata wuya ta figeta har parlon tana mata wani shegen kallo ta ce

"Ɓarauniya kawai, kin bani mamaki Jiddah ki rasa me zaki sata sai gold wlh kinyi asara daman ance tsintacciyar mage bata mage, no wonder Mami ta tsaneki ashe ɓarauniya ce bamu sani ba wlh kin yi asara banza kawai ƴar matsiyata"



Allah sarki Jiddah kallonta kawai take tama kasa magana ko kuka dan batasan akanme take mata magana ba, Mami ce ta fito tana kallonsu ta ce

"Shiyasa tun zuwanta nace bana sonta daman wlh ni nasan tabbas tanada wani mugun hali da take aikatawa yasa naji na tsaneta Heesham ya kawo mana masifa"


Da mamaki ya ce"what's wrong Mami?" kallonsa ta yi sai kawai ta fashe da kuka ta ce" Heesham sanda nake faɗa ai ƙarya kuke ɗauka nace na tsani yarinyar nan amma kuna min kallon mara imani" da rashin fahimta ya ce" Shareefa meya faru?" da sauri ta ce masa "yaya Jiddah ce ta satarwa Mami gold ɗinta data siyo jiya"

"Sata?"

Ya maimata kalmar a fili sai kuma ya kalli Jiddah wacce ta fashe da wani raunataccen kuka dan sai a sannan tak abinda ake zargin ta aikata, girgiza kansa kawai ya yi sai kuma ya juya ya fita daga parlon ta bisa da kallon amma ta kasa magana



Babu irin tijarar dasu Mami da Shareefa basu yimata amma duk wannan abun da ake Nihal bata saka baki ba tayi shuru abinta har suka gama maganarsu suka shige sama.




Zaune ta tarar da ita gefen wata flower sai kuka take kamar ranta zai fita

"Jiddah"

Ta kira sunanta, da sauri Jiddah ta ɗago tana kallonta sai kuma ta sunkuyar da kanta tana share hawayen fuskarta, zama ta yi gefenta ta ce" kiyi haƙuri Jiddah ki ɗauka hakan ƙaddararki ce, amma ina son baki wata shawara"

Da sauri ta kalleta ta ce cikin kuka "dan Allah wace shawara zaki bani?" numfasawa Nihal ta yi sannan ta ce" tunda kikaga Sheikh ya fita bai kula ki ba toh yan sanda zai kirawo su kama ki, kuma yanzu na baro su Mami suna faɗawa Dad kuma bai kamata ace Dad ya ganki da wannna laifi ba" hankali Jiddah idan ya yi dubu to ya tashi ta ce" dan Allah ki bani shawara"


"Shawara ɗaya zan baki shine ki gudu kafin su dawo kiyi tafiyar ki garinku" da sauri ta kalleta ta ce" ni bansan hanya ba kuma banida kuɗi" kuɗaɗe ta zaro wajen bandir ɗaya na ƴan dubu ta ce" ungo kiyi tafiyar ki idan kika fita saiki tambayi tasha idan aka kaiki sai ki hau motar garinku" goge hawayen fuskarta ta yi sannan ta ce" nagode" murmushi Nihal tayi mata sannan ta mike jiki a sanyaye ta fara tafiya har ta fita daga cikin gidan daga ita sai hijab har ƙasa ajikinta wata ƙaramar riga ce. Ajiyar zuciya Nihal ta sauke sannan ta tashi ta koma gidan.



Allah sarki rayuwa tafiya kawai Jiddah take yi batareda tasan inda zata ba, murmushi ɗauke a fuskarsa ya ce" dallah ka daina min ko bakaga tuƙi nake ba?" dariya Ajmal ya yi ya ce" wato bakason ka mutu yaya Sultan bakai aure ba?" kafin ya bashi amsa ya sake kai hannu zai taɓashi da sauri ya kalli gabansa amma kafin ya tsaya har ya rigada ya kaɗeta, cikin tashin hankali suka fito daga motar, kwance suka tadda ita dukda basu wani bigeta sosai ba amma ta suma, ɗukanta Sultan ya yi ya saka a mota suka cigaba da tafiya. Basuda ishashen lokacin da zai ishesu su kaita asibiti anan garin hakan yasa kawai suka hau private jet ɗin da aka kawo musu zuwa garin bauchi.......



*Shin wace irin ƙaddarace ta raba Jiddah da Abbanta?*
*Shin da gaske Jiddah itace wacce ta saci gold ɗin ko A'a?*
*Shin da gaske Sheikh yan sanda ya tafi ɗebowa Heeshamarsa?*
*Shin meyasa Jiddah tabar garinsu kuma suwane Ajmal da Sultan?*
*Shin ya Heesham zai ji idan ya dawo ya tarar babu Heeshamarsa?*


*Duka zaku samu amsoshin tambayoyinku a yayinda kuka biya kuɗin littafin Sheikh Heesham 500# via 9086030007 evidence via 09086030007 or contact me direct via 09086030007 whatsapp only*



*Taku har kullum Nanameera sai mun haɗu a paid group*
End Ads