x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 3 - SHEIKH HEESHAM

  • 6001 words
  • 9000 words
  • Out of 16100 words

Category: Comedy Stories

Views 250

28 May 2025
Start ads
After Image Ads
yi sannan ya ce" a fito da'ita ina jiranta " daga haka ya juya ya fita, da kallo kawai Bilal ya bisa har ya fita sannan ya kalli Jiddoh ya ce" taso mu tafi dear" batayi musu ba ta tashi tana tafiya ahankali saboda har sannan jikinta babu wani kwari ta bi bayansa suka fita.........


Zaune suka tadda shi cikin motar yana danna cazbahar hannunsa, kallonsu kawai ya yi har suka shiga motar sannan ya yi mata key ya cillata kan titi............


Murmushi Nihal ta yi ta ce" to ai naga bangansa ba ina ya tafi?" taɓe baki Shareefat ta yi ta ce" wlh dai karki zaƙe dan Sheikh halinsa sai shi" ta ce" nikam ko dukana zai dinga yi inasonsa haka"tashi Shareefat ta yi ta ce "aikuwa zakisha wahala" sannan ta shige toilet.......


Kallon makeken gidan kawai take dan gani take kamar ba'a duniya take ba, dan ko a mafarki bata taɓa ganin abu mai kyau irin wannan gidan ba, lura da hakan yasa Bilal ya yi murmushi ya ce" what's ur name?" kallonsa kawai tayi amma bata bashi amsaba dan batasan abinda ya faɗaba ma, ya ce" nace ya sunanki?" sai a sannan ta sunkuyar da kanta ta ce" Jiddah" murmushi ya yi ya ce "masha Allah Hauwa'u kenan?" gyaɗa masa kai kawai ta yi, girgiza kai kawai Sheikh ya yi ya buɗe ƙofar parlon bakinsa ɗauke da sallama...........




Murmushi ɗauke a fuskarsa ta ce" welcome back yaya" ba tareda ya kalleta ba ya ce" thank you", sannan ya zauna kan royal sofa ɗin dake zagaye a parlon
"Ya Allahu"
Shine abinda yake faɗa akaro na babu adadi, tsayawa tayi tana kallonsu ɗaya bayan ɗaya, Shareefat ta ce" yaya ina kasami ƴar fulani?" shuru ya mata kuma daman tasan bazai amsa mata ba yasa bata wani damu ba. Mami ce ta fito daga part ɗinta hannunta riƙe da waya tana dannawa da alama magana mai muhimmanci take, zama tayi kan kujerar batareda ta kallesu ba ta ɗaga kiran da ake mata.

Murmushi ta yi ta ce"ok kawai ki barta ta kwana gobe sai ta tafi makarantar tanan"
Daga ɗaya bangaren ta ce" tom shikenan Allah ya kaimu"
Ta ce" Ameen" sai a sannan ta kallesu kai tsaye kuma idanunta ya sauka akan Jiddarh wacce har sannan bata samu ta zauna ba, da mamaki Mami ta ce
"Wannan yarinyar fa?"
Kamar bazai magana ba sai kuma ya ce" idan anjima zan miki bayani in sha Allah" yana gama fadin hakan ya miƙe yana sake tattare al-kyabbar jikinsa ya shige ɗaki yana cewa
"Shareefat ki kaita ɗakinki ta yi wanka"......

Bai fito ba sai lokacin sallar magrib ya fito cikin wata shadda ash colour ya ɗora al-kyabba orange mara nauyi akai, zaune ya tadda ita kamar yanda ya barta ɗazu babu alamar tayi wankan ko ta sake kayan jikinta. Kallonta ya yi sai kuma ya kalli agogon hannunsa kawai ya yi waje.......


Yana shigowa gidan shi kuma ya fito daga masjid ɗin, murmushi ya yi yana zuwa ya shige jikinsa yana sauke wata nannauyar ajiyar zuciya a karo na babu adadi ya furta" Alhamdulillah" shafa bayansa Daddy ya yi yana murmushi ya ce" saukar yaushe Sheikh?"
Saida ya raba jikinsa da nasa sannan ya ce" ɗazu na sauka Daddy" murmushi Daddyn ya yi ya ce" sannunka da zuwa ya hanya?" "Alhamdulillah" shine kalmar daya furta yana sakin fuskarsa. Sosai suke kamada Daddynsa dan babu abunda ya raba su suka jera gwanin sha'awa suka shiga gidan.............

Zaune suka sake tadda ita amma wannan karan tayi tagumi ita kanta batasan kuka take yiba, da mamaki Daddy ya ce

"Wannan yarinyar wace?" murmushi Sheikh ya yi ya ce" zanyi muku bayani later" ok Daddy ya ce sannan ya shige part ɗinsa dan dawowarsa kenan.

Kallonta ya yi ya ce" keeee" ɗago kanta tayi tana kallonsa da dara-daran idanuwanta ta ce" dan Allah malam ka maidani rugarmu kaji" kamar bazai ce komai ba sai kuma ya kama hannunta cikin nutsuwa ya yi waje da'ita........



A bakin wani makeken shopping mall ya tsaya sannan ya sauka daga motar, shuru tayi ganin bai ce mata tafito ba kuma bai buɗe motar ba ta zauna kawai tana kalle-kalle..............


Bayani kawai ya gama yi mata sannan ya ce" plx pink, white, coffee colour" cikin girmamawa ta ce
"Okay Sir" sannan ta juya dan haɗa masa kayan.........


Kayane aka haɗa mata kamar hauka amma duk yawanci abayas ne sai inner wears kala-kala sai mayuka masu kyau da tsada irinna ƴaƴan manyan nan, ni kuma nace idan tana tareda Sheikh ai kuɗi ba'a magana.........


Suna tafiya a hanya yana tuƙinsa a hankali ya yinda ta shagalta da kallon kyakkyawar fuskarsa, ajikinsa yaji ana kallonsa ya juya suka haɗa idanu. Murmushi ta sakar masa ya ɗauke kai dan shikam bai shirya haka da'ita ba, ganin bai kalleta ba yasa ta ɗauke kanta tana kallon hanya har suka ƙarasa gidansu............


Banda ƙarar cokula babu abinda ke tashi a parlon kowa ya yi busy banda Sheikh Heesham wanda yake zaune ƙasan carpet yake cin nasa abincin, daga can gefe na hangota ta takure jikinta dan ko abinci takasa ci kuma daman babu wanda ya bata abincin sai Daddy. Kallonsa kawai take dan Allah ya gani wata irin yunwa takeji kamar ta mutu amma babu wanda zata iya tambaya abinci haka tana kallo suka cinye kuma bataci wanda Daddyn ya bata ba.........


Yana gamawa ya tashi a nutse ya shige apartment ɗinsa dan kwata-kwata bashida nutsuwa ji yake kamar ba shiba. Suna gamawa ta ce" nifa bangane wannan yarinya da Sheikh ya kawo ba, banson irin hakafa ka sani" murmushi irinna manya Daddy ya yi sannan ya ce" Amina kenan, kinsan ai tunda ya kawota dole akwai wani abu ko, kuma ai bacewa ya yi zata zauna a gidan nan ba bare kice" haɗe rai tayi dan ita arayuwarta ta tsani ganin wanda taba saniba a gidanta tunda wata ƴar aike ta taɓa cutarta, saboda haka bata yadda da duk wanda bata sani ba. Ganin kamar ta tafi tunani yasa ya ce" Aminaa!", a ɗan firgice ta kalleshi ta ce" na'am" "tunanin me kike?"
Ɗauke kai ta yi ta ce" nifa tunda ta shigo naji na tsani yarinyar kawai bata yimin ba wlh gwara yazo ya mayar da'ita inda ya ɗaukota" girgiza kai ya yi dan yasan halinta da kafiya ya miƙe ya ce" Allah ya kyauta" Ameen............

Yana gama shiryawa ya yi kwanciyarsa yana lumshe idanunsa dayake jin suna masa nauyi koda yaushe........

Ita kaɗai ce a parlon kuma har sannan batayi wankan ba shurun ne ya mata yawa ta miƙe a hankali tana tafiya a hankali har ta hau kan stairs ɗin benen, tafiya take a hankali dan a tsorace take da benen tunda ba taɓa hawa tayi ba har ta isa ɗakin Shareefat........

Tura ƙofar tayi a hankali, zaune suke suna hira da Nihal ta shigo da sallamarta cikin gurɓatacciyar hausarta ta ce" dan Allah in zauna anan tsoro inaji" ta yi maganar tana langwaɓar da kanta. Kallonta Shareefat ta yi sai kuma ta ce" A'a malama ɗan fita banda wari babu abinda ki keyi wlh bazaki zauna min ɗakiba kisa ya yita wari, sannan duk kayan da Sheikh ya kawo naki ki kwashe su muje na nuna miki ɗaki" tom ta ce sannan ta firfito mata da kayan ta ɗiba itama ta ɗibar mata wasu.............

Wani ɗakine a downstairs ɗin gidan wanda babu kowa aciki dan ɗakin ƴar aikinsu ne kuma ta tafi, shiga sukayi tana kallon Jiddarh ta ce" ki zauna anan, amma ki shiga banɗaki kiyi wanka" gyaɗa mata kai kawai tayi, ganin batasan yanda zatayi komai ba yasa ta shiga da ita banɗakin ta nuna mata yanda zatayi wankan da yanda zatayi brush, sannan ta fito.............

Kasancewar tanada saurin riƙe abu yasa batashi wahala ba tayi wanka ta fito tana tafiyar ta anutse kamar koda yaushe.......

Zama tayi gefen bed ɗin tana ƙarewa ɗakin kallo dan yanda aka gyara ɗakin bazaka taɓa cewa ba ɗakin ɗan gida bane, a hankali ta buɗe ɗaya daga cikin ledojin tana kallo. Rasa wane kaya zata saka tayi ta zaro wata riga dogowa amma batada nauyi pink colour. Sanya rigar tayi wacce tayi masifar yi mata kyau dan tabi jikinta sosai, turare ta gani ta ɗauka tana kallo dukda batasan mene ne ba amma kawai ta fara ƙoƙarin buɗewa,sauran ƙiris ta fasa shi Allah ya taimaka ta buɗe tana kallonsa a ɗan tsorace ta danna wajen fesawar. Ganin yanda yake fitowa yasa abun ya bata dariya ta buɗe baki tana dariya ta ce" lahhh kamar ruwa" ta faɗa tana faɗaɗa fuskarta har saida beauty point ɗinta ya loma. Sosai ta shafa turaren dan har yaso ya mata yawa sannan ta ajiye ta haɗe komai a gefe...........

A ɗan tsorace ta hau kan gadon daga gefe ta kwanta ta lumshe idonta nan da nan bacci ya ɗauketa.........


Wata irin azababbiyar yunwa ce ta tasheta, ta miƙe tana riƙe cikinta lokaci ɗaya kuma ta fashe da wani irin kuka tana sake riƙe jikin, a hankali ta sauko daga kan gadon ta fito daga ɗakin......

Tafiya kawai take ba tareda tasan inda zata ba, haka har tahau benen, tsayawa ta yi tana ƙarema ɗakunan kallo a hankali kuma ta fara tafiya zuwaga wanda yake kallonta. Riƙe numfashinta tayi saboda wani ƙamshi daya daki hancinta lokacin data buɗe ɗakin, babban parlon ne wanda ya wadatu da kayan more rayuwa, kalle-kalle tayi ta hango wata ƙofar kamar kuwa ana turata taje ta buɗe ƙofar...........

Bataga kowa ba sai ƙamshi lokaci ɗaya kuma idanunta ya sauka kansa, kwance yake ya rufe duka jikinsa da blanket dukda an kunna a.c.......
Ƙarasawa tayi gabansa ta tsuguna tana kallon fuskarsa wacce bai rufeta ba, wata kyakkyawar ƙara ta saki da tasa ya buɗe idanunsa bakinsa ɗauke da addu'a yana kallonta. Tashi ya yi zaune ganin yanda take kuka kamar ranta zai fita, tattausan hannunsa yasa ys ɗagota ya zaunar gefensa yana magana cikin sanyin jiki ya ce" lafiya?" sake fashewa ta yi da kuka ya kwaɓe fuska yana kallonta ya ce" ki yiwa Allah karki fasamin kai" shuru tayi da kukan tana sauke ajiyar zuciya, sai da yaga tayi shuru sosai sannan ya ce "ke dawa?" kwaɓe fuska ta yi ciki shagwaɓa ta ce" koba yunwa nake jiba" sakar baki ya yi yana kallonta jin akan yunwa take masa wannan kukan ya ce" to kiyi haƙuri saida safe ko" sake fashewa tayi da kuka ta ce" ni wlh zan mutu yunwa nake ji" dafe kansa ya yi dan nema take tasaka shi ciwon kai ya miƙe a nutse ya buɗe frigde ɗin ɗakin......

Babu komai aciki sai kayan marmari sai kuma fresh milk , fresh milk ɗin ya ɗauko mata har lokacin tana riƙeda cikinta. Miƙa mata ya yi shi kuma ya shige banɗaki.....

Kafa kanta tayi ta fara sha tana lumshe ido saboda garɗin madarar da yake zuwa har cikin kwakwalwarta, fitowa ya yi bayan ya ɗauro alwala ya kalli inda take, mamaki ya yi ganin ta kwanta tana bacci bayan ta yarda empty robar madarar girgiza kansa kawai ya yi sannan ya yi waje.......
Prayermat ya shimfida a parlon ya hau sallolinsa na nafila wanda ƙa'ida ce duk dare sai ya yi su.........
*SHEIKH HEESHAM*
*Paid Book 500#*
[3/4, 22:15] 🥰Nanameera🥰: https://chat.whatsapp.com/LSYEkQgVkLKDQyheA6YWH4


*🌹SHEIKH HEESHAM🌹*








*Nanameera*.


*🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*
{R.S.W.A}

https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c
*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_*
_(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_

*Alk’alaminmu ‘yancinmu*


*I Dedicated this book to yhu Aunty Sarauta my nimcyluv, much luv*

Paid book
Free page 5.
Sai wajen ƙarfe 6am sannan ya shigo gidan bayan ya gama wa'azi a masjid ɗin kamar yanda ya saba, kai tsaye ɗakinsa ya wuce yana kiran Allah aransa kamar koda yaushe............

Kwance ya tarar da'ita da alama har sannan bata tashi daga baccin ba, girgiza kansa kawai ya yi dan da alama yarinyar zata wahalar dashi. A nutse ya ƙarasa yana kallon fuskarta wacce ta kwaɓeta kamar zata yi kuka yake yi yana sake riƙe kansa akaro na babu adadi, ahankali ya ɗan bubbaga gefen pillow aukuwa ta buɗe ido kasancewar batada nauyin bacci. Kallonsa take tana murza idanunta dan ta manta inda ma tayi baccin,
"Tashi ki tafi"
Abinda ya furta kenan sannan ya juya ya shige toilet, shagwaɓe fuska ta yi sai kuma ta miƙe kamar mai tsoron tafiya haka tafara yinta.............


Fitowarta kenan daga ɗakin Shareefat ta kalleta da mamaki, ƙarasowa Jiddah ta yi ta mata murmushi, bata amsa mataba haka kuma bata daina kallonta ita dai ta ratsa ta gefenta ta sauka daga benen ahankali dan har sannan tsoronsa takeji.....


"lafiya?"
Shareefat ta tambaya ganin yanda ta tsaya, murmushi Nihal tayi ta ce" nothing kawai jiranki nake" daga nan ta sauka, ɗaga kafaɗa Shareefat tayi alamar bai dameta ba sai kuma tabi bayanta..............


Kallonsa take har ya gama shiryawa sannan ta ce" wai dan Allah ina zakaje da safen nan dear?" yana saka hularsa ya ce
" wajen Sheikh zani zamuje unguwa"
Murmushi ta yi ta ce"daman ai tunda Sheikh ya dawo shikenan yanzu ganinka zai mana wahala, to kace masa ina miƙo saƙon gaisuwa" light kiss ya mata a goshi sannan ya ce" in sha Allah, bye" ɗaga masa hannunta itama tayi sannan ya juya ya fita, ajiyar zuciya ta sauke sannan ta koma bedroom ɗinta...........


Zama tayi daga gefen kujera ta rakuɓe bayan ta gaida Daddy dan shine kawai ya amsa, kallonsa Daddy ya yi yace" Sheikh muna sauraronka ina kasamo yarinya?"

Ajiyar zuciya Sheikh Heesham ya sauke sannan ya ɗago yana kallon iyayen nasa wanda suma shi suke kallo. Ahankali kuma cikin nutsuwar da tagama ratsashi ya fara basu labari tun daga farko har ƙarshe, abu ɗayane bai faɗa musu ba shine an ɗaura masa aure da'ita......

Ajiyar zuciya Daddy ya sauke amma bai ce komai ba dan haƙiƙa yaji tausayin Jiddah,
"Allah ubangiji ya jiƙan iyayenta yasa sun huta, amma bari kaji bazai taɓa yiwuwa ba ta zauna agidan nan ka ɗauki ƴar mutane ka mayar da'ita cikin ƴan uwanta dan banjin zan iya zama da'ita cikin gidan nan"

Tunda ta fara magana yake kallonta bashi kaɗaiba harda Daddy, Shareefat, Nihal, Bilal sai kuma Jiddah. Hankalinsa a matuƙar tashe yake amma bazaka taɓa cewa shine ake yiwa maganar ba saboda iya riƙe kansa............

Girgiza kai Daddy ya yi cikin dattako ya ce
"Wannan wace irin magana ce Amina?, madadin ace kinji tausayinta kin jata ajiki kamar ƴar da kika haifa shine zakice bazata zauna tare dake ba, toh bari kiji gida dai gidana ne kuma ni nakeda iko da duk wanda yake cikin gidan nan saboda haka matuƙar ina raye to tabbas zan kulada rayuwarta kamar ƴar dana haifa kuma nasan ko bayan mutuwa ta Heesham zai ɗora daga inda na tsaya, kuma wannan umarni ne bawai shawara ba saboda haka take note" yana gama faɗin haka ya kalli Jiddah wacce tayi shuru kanta a ƙasa ya ce" ki saki jikin ki daughter ki ɗauka nima babanki ne da ya rasu, duk abinda kike buƙata ki sanar dani ko Heesham kinji" gyaɗa masa kai tayi sannan ya shige apartment ɗinsa........


Kowa na parlon ya yi shuru sai kallo da ido, ahankali ta miƙe tana kallonsa ta ce

"Bazan koreta daga gidan nan ba tunda ba gidana bane kamar yanda mahaifinka ya faɗa amma ka sani babu abinda ya haɗani da ita koda wasa karna kuskura naganta a inda nake idan ba haka ba ran kowa zai ɓaci" fuuuuu tayi benen gidan.......


Tashi sukai atare suka tafi ɗakinsu wajen ya rage daga Sheikh, Bilal sai Jiddah. Kuka kawai take a hankali, kallonta Bilal ya yi dan tabashi tausayi sosai yarinyar, kamo hannunta ya yi ya ce" ki daina kuka kinji Jiddah, zaki bini gidana?" gyaɗa masa kai ta yi ya ce" ok ɗauko hijab a ɗaki mu tafi" cikin sanyin jiki ta tashi ta shige ɗakin nata..........

Sai a sannan ya kalli Sheikh wanda zaka ɗauka baya wajen ya ce" zan tafi da'ita, can i?" tashi Sheikh ya yi daidai lokacin ta fito sanye da hijab ɗin yana batareda ya yi magana ba ya kama hannunta a hankali ya fara taka stairs ɗin benen tana biye dashi.............

Girgiza kai Bilal ya yi dan daman yasan da kyar ya barshi ya tafi da'ita, ya miƙe kawai ya ɗauki car keys ɗinsa ya yi waje....


Fitowa ya yi daga bedroom ɗin har sannan tana zaune kan kujerar da yabarta tana kuka, dafa kansa ya yi bai ce komai ba ya zauna kan kujerar dake facing ɗinta ya yi mata alama da tazo da hannunsa......

Cikin tafiyarta ta nutsuwa ta ƙaraso gabansa zata tsuguna ya kamo hannunta ya zaunar da'ita kan cinyarsa yana yin baya kaɗan ya ce
"kukan na mene?"
Turo baki ta yi sai kuma ta sake fashewa da wani sabon kukan, shuru ya yi yana sauraronta har wani runtse idanu yake sabida tsananin azabar ciwon kai. Saida tayi mai isarta da kanta tayi shuru tana sauke ajiyar zuciya, kallonta ya yi cikin kasala ya ce" kin gama?, kin kusa fasamin kai fulani" kwaɓe fuska tayi ta ce" toh ni kamayar dani rugarmu kaji" cikin son shawo kan rigimar da take masa ya ce" shikenan ki kwanta zuwa anjima zansa a maida ke" shuru ta yi ba tace masa komai ba wajen 2mins ya kalleta ta ɗauke kai, bai san sanda ya yi wani kyakkyawan murmushi ba amma bata gansa ba ya juyo da fuskarta yana ƙare mata kallo ya ce
"ki daina rigima zan saka ki makaranta"
Riƙe hannayensa ta yi da murna ta ce" irin wanda su Adda suke zuwa?" bai gane wace makaranta take nufi ba hakan yasa ya yi mata shuru, haɗe rai ta yi sai kuma ta ce" to wai kai bakayin magana ne?" buɗe gajiyyayun idanunsa ya yi ya sauke akanta tayi saurin ɗauke nata saboda wani kwarjini da ya yi mata. Sauketa ya yi daga jikinsa yana faɗin
"Astgfirullah"
leƙa fuskarsa ta yi ta ce" mene wannan ka faɗa?" kallonta ya yi da mamaki da alama dai batasan komai ba gameda addini, a ransa ya yi alƙawarin mayar da'ita cikakkiyar malama kuma mai tarin ilimi.............

Ganin lokaci na tafiya yasa ya ce" tashi kije"
Miƙewa tayi tana kallonsa ya nuna mata hanyar waje ta juya ta fita, a hankali ya furta
"Ya Allahu, Ya Rahmanu".

Da mamaki ta ce" to yanzu yarinyar tana gidan?"
Gyaɗa mata kai Nihal ta
End Ads