x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 4 - SHEIKH HEESHAM

  • 9001 words
  • 12000 words
  • Out of 16100 words

Category: Comedy Stories

Views 251

28 May 2025
Start ads
After Image Ads
yi ta ce" wlh Daddy ne ya ce babu inda zata amma Mami sai faɗa take" ajiyar zuciya ta sauke ta ce" ina Heesham ɗin?" "yana gidan shima" ta bata amsa, shuru sukayi duka sai kuma Nihal ta ce" Mommy bari naje nayi wanka nikam" ok Mommyn ta ce sannan ta shige ciki.........


Zaune suke a company ɗin Bilal ya ce" yanzu ya zakayi da ita?" shuru ya yi masa ya ce" wai dan Allah bazaka daina wannan abunba kanaji ana maka magana kayi shuru" numfasawa Sheikh ya yi sai kuma ya ce" zan kaita makaranta ne saboda na fuskanci batasan mene ne karatu ba ma both boko da islamiyya tanada flaws sosai". Ajiyar zuciya Bilal ya sauke sannan ya ce" toh meyasa ka karɓo musu yarinya?" murmushi Sheikh ya yi amma bai bashi amsa ba, tashi sukayi dan daman magrib ya kusa kuma zasu tafi gida............


Sai wajen ƙarfe 10pm sannan yashigo gidan kai tsaye kuma apartment ɗinsa ya nufa dan ba ƙaramin gajiya ya yiba. Yana gama shiryawa ya yi kwanciyarsa dan sam ya manta da wata Jiddah..........

Washegari wajejen 9am kowa yana parlon suna breakfast Daddy ya ce" ina Hauwa'u naga bata fito ba?" kallonsa kawai Mami ta yi amma bata bashi amsa ba ya ce" Shareefat jeki kirawota" tashi tayi kawai ta shige ɗakinta dan kiranta kamar yanda ya umarceta.........


Zaune ta tadda ita tana kallon mudubi wanda azahiri bashi take kallo ba tunani kawai take ki, tsaki Shareefat ta yi sai kuma ta ce" keee" juyowa ta yi tana kallonta dan batasan tashigo bama, tana tattare fuska ta ce" ki zo ina kiranki" ta juya ta fita...........

Da sallama ta shigo parlon ta tsuguna ta gaishesu suka amsa banda Mami as usual, kallonta Daddy ya yi ganin yanda ta tsuguna ya ce" tashi ki zauna anan" ya nuna mata kusadashi, batayi musu ba ta zauna kamar yanda ya ce ya miƙa mata abincin yana kallonta. Ahankali take cin abincin saboda rashin sabo da cinsa, har tagama sannan ta tashi ta koma ɗakinta.........

Da daddare ya dawo gidan lokacin kusan ƙarfe 9pm shida Bilal, zaune suka tadda ita a parlon tana kallo a tv, murmushi Bilal ya yi ya ce" kallo ki keyi?" gyaɗa masa kai ta yi ta ce" ina kwana" cikin harshen fulatanci langwaɓar da kai ya yi ya ce" Ayya Hauwa'u ai ni ban'iya ba saidai ko Abbanki" juya fararen idanunta ta yi sai kuma ta ce
"Abba"
Murmushi ya yi ya ce" Eh mana ai Sheikh Abbanki ne, saboda haka daga yau Abba zaki dunga ce masa" murmushi tayi har saida fararen haƙoranta suka fito ta ce
"Abbana"
Ya gyaɗa mata kai yana murmushi shima ya ce" yees Abbanki". Kallonsu kawai Sheikh yake amma bai ce komai ba, Bilal ya miƙo mata wata takarda ya ce"admission later nki" kallonsa tayi da rashin fahimta ta ce" ni bangane ba" dafa kansa ya yi ya ce"ohh sorry, gobe zaki fara zuwa makaranta".dariya tayi ta ce" da gaske nima zan fara zuwa makaranta?" gyaɗa mata kai ya yi yana dariya ta ce" nagode" ya ce" Abbanki zaki yima godiya"................

Tashi ta yi ta ƙarasa gabansa ta tsuguna cikin harshen fulde ta ce" nagode Allah ya ƙara arziƙi" murmushi ya yi ya shafa kanta ya ce" Ameen Fulani"..........

*SHEIKH HEESHAM*
[3/4, 22:15] 🥰Nanameera🥰: https://chat.whatsapp.com/LSYEkQgVkLKDQyheA6YWH4
*🌹SHEIKH HEESHAM🌹*








*Nanameera*.


*🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*
{R.S.W.A}

https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c
*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_*
_(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_

*Alk’alaminmu ‘yancinmu*



*I Dedicated this book to yhu Aunty Sarauta my nimcyluv, much luv*

*Paid book*
*Free page 6*

Da sassafe ta farka saboda zumuɗin zata fara zuwa makaranta, ahankali take tafiya cikin sanyin jiki kamar batason taka ƙasar har ta ƙaraso ƙofar part ɗinsa. Tura ƙofar tayi bakinta ɗauke da sallama, zaune ta sameshi yana karatun al-qur'ani mai girma cikin daddaɗar muryasa mai tsinka zuciya, zama tayi gefen gadon tana sauraren karatun nasa har ya kammala sannan ya kalleta. Tsugunawa tayi cikin ladabi ta ce
"Abbana ina kwana"
"lafiya lao, kintashi lpia?"
Sheikh ya tambaya lokacin da yake miƙewa tsaye dan shiryawa, murmushi ɗauke a fuskarta ta ce" yau zan fara zuwa makarantar Abba?" gyaɗa mata kai kawai ya yi dan ya lura nema take ta sa kashi magana.

Shiryawa ya yi cikin wata dakakkiyar shadda ash colour ɗinkin jampa da babbar riga ya ɗora hirami akansa sannan ya fito, kallonsa kawai take dan sosai ya yi mata kyau

"Mefa?"
Ya faɗa ganin irin kallon da take masa, girgiza kai tayi ya miƙa mata hannunsa ta kama sannan sukai waje.



Mami ce zaune sai Daddy suna breakfast, da murmushi a fuskarsa ya ce" ƙaraso mana Hauwa'u" ahankali ta fara tafiya tana zuwa ta tsuguna gabansa ta ce" ina kwana?" kamo hannunta ya yi ya zaunar gefensa sannan ya ce" kintashi lafiya?" gyaɗa masa kai tayi saboda batason magana musamman ganin irin kallon da Mami ke mata. "Ina kwana?" ta faɗa tana kallon Mami, shuru Mami tayi dan bazama kace da'ita take ba sunkuyar da kanta tayi lokaci ɗaya hawaye ya fara zubuwa a fuskarta


Lura da hakan yasa Daddy ya ce" ci abinci kinji karki makara" "na ƙoshi" ta furta cikin sanyin jiki.

Girgiza kai Daddy ya yi ya ce" noo dole sai kinci abinci tukunna idan kingama sai akai ki makarantar kinji" batasan yin musu dashi yasa ta fara cin abincin wanda kwata-kwata baya yi mata daɗi


Bata wani ci dayawa ba ta ce" na ƙoshi" gudun karya takura mata yasa ya ce" shikenan ayi karatu dayawa dear" tashi tayi tana satar kallon Sheikh wanda ya zauna tun ɗazu akan kujera yana jiranta


Gaba yayi hakan yasa tabi bayansa tana sauri gudun karya tafi ya barta


A harabar gidan suka tadda Bilal wanda daman shine zai kaita makarantar, da murmushi a fuskarsa ya ce" ƴar makaranta" sai asannan tayi dariya tana rufe fuskarta ta ce" ina kwana?" "lafiya lao" ya amsa mata



Kallonta Sheikh ya yi sannan ya ce "akula banda wasa, kiyi karatu da kyau" gyaɗa masa kai tayi ya zaro wani abu a hannunsa, batace ga abinda ya zaro ba saida taga ya kama kafaɗunta a nutse kuma ya fara saura mata afuska


Kallonsa kawai Bilal yake har ya gama sanya mata niƙaf ɗin wanda yayi mata kyau sosai, murmushi tayi ta cikinsa ta.ce" laaa! Kamar dodo" girgiza kai kawai ya yi sannan ya juya ya fara tafiya hannunsa goye a bayansa kamar koda yaushe, guards ɗinsa ne suka fito suka buɗe masa motar ya shiga sannan suka bar harabar gidan.


Ajiyar zuciya ta sauke sannan ta kalli Bilal ya sakar mata murmushi ya ce" mu tafi ko?" ya kama hanyar wajen motarsa tana biye dashi.




A harabar makarantar Sheik Bashir dake cikin garin kano ya yi parking, sosai makarantar ta birgeta musamman daya kasance suna koyarda both boko nd islamiyya, a office ɗin principal suka zauna aka ƙarasa cike-ciken da za'ayi sannan suka bata aji Jss 1 domin acewarsu batasan komai ba a harkar karatun


Wata prefect akace ta kaita aji, suna fitowa ya ce" banda wasa kinji Jiddah" ɗaga masa kai tayi hawaye na taruwa a idanunta ya ce" mene ne?" "tafiya zakayi kuma?" ta faɗa da zallar gaskiyarta


Dariya ya yi sannan ya ce" to ai daman ke kaɗai za'a dinga kawowa idan antashi amaida ke gida, karkiyi kuka kinji" goge hawayen ta da yasamu damar zubowa ta yi ta ce" to ni dawa zan zauna?" dafa kansa ya yi ya ce" Jiddah ki daina rigima da akwai mutane a cikin ajin" bata kuma cewa komai ba ya ce"please ki riƙe hannunta" tom prefect ɗin tace sannan ta kama hannun Jiddah suka fara tafiya tana juyowa har suka bar section ɗin.




Fitowarsa kenan daga wanka ya tsaya yana ƙaremata kallo ganin yanda take bacci kamar jaka, tsaki kawai ya yi sannan ya girgiza kai yazo gabanta,

"Nabeela!!Nabeela!!Nabeela"

A firgice ta buɗe idanu tana mutstsiƙesu ta ce"please kabarni nayi bacci mana" sakar baki ya yi yana kallonta sai kuma ya ce" amma kinsan lokacin sallah ya yi ko?, kuma bakida alamar tashi kiyi" turo baki ta yi ta ce" to naga idan mutum bacci yake ai ba'a tashinsa saboda sallah ni gaskiya ka daina tashina haba" ta tashi ta shige toilet ɗin


Girgiza kai ya yi sannan ya ce" Allah ubangiji ka shiryi Nabeela"



Tana gama zuba masa abincin ta kallesa ta ce" Doctor nagama" murmushi ya yi ya ce" thank you dear Allah ya yi albarka" Ameen ta amsa sannan ta koma kitchen d'in dan ƙarasa abinda take




Murmushi ya yi yana kallon yanda yake zuba masifa ya ce" haba prince wannan fa ba girmanka bane" wanda aka cewa prince ɗin ya kallesa ya ce"ok haka ma zaka ce?, nayi ƙafa da ƙafa tun daga bauchi nazo wajenka amma shine zaka cemin haka babu komai thank you"


Murmushi Khalil ya yi sannan ya ce" ba haka nake nufiba Ajmal abinda nakeso ka gane ita rayuwa a hankali ake binta bada faɗa ba tunda kaji mai martaba ya ce haka dole akwai abinda ya faru dan Allah ka dinga yayyafawa zuciyarka ruwan sanyi".


Kallon kawai ya yi sannan ya ce" ni idanma ya yi haƙuri ƙasar zan barmasa sai ya ƙarata shida su, kuma fa wai har Fulani koyon bayansa take" murmushi ya yi ya ce" haƙuri zakayi friend karka ɗauki abin wani personal kaji, Allah ya yi mana jagora" ajiyar zuciya ya sauke sannan ya ce" Ameen, nagode amma wlh bazan koma yanzu ba" dariya Khalil ya yi ya ce"shikenan sai ka zauna gidana" da sauri ya kallesa sai kuma ya ce" waye zai zauna gidanka?, Allah ya tsare wannan ƙazamar matar taka tana gidan, tab" girgiza kai ya yi ya ce" tunda bazaka zauna ba karka zagarmin mata agaba ahaka ina sonta kuma itama tana sona" kallonsa ya yi sai kuma ya fashe da dariya ya ce"ina wata soyayya bayan babu tsafta?, kana dai fama" tada motar ya yi ya ce"E, naji".






Kallon motar da tashigo suke har tayi parking, fitowa tayi da niƙaf kamar yanda ta tafi sai kayan makarantar da suka bata a hannunta sai school bag ɗinta, murmushi ta sakar musu, haɗe rai Shareefat tayi Nihal ta ce" sannu dazuwa" "yawwa" Jiddah ta faɗa sannan ta shige gidan.



Harararta Shareefat ta yi ta ce" banza mene ne na gaisheta?, wlh wannan sai ta shiga tsakanin ki da Sheikh" murmushi Nihal ta yi sannan ta ce" ke bakida wayo idan muka nuna bama sonta ai za'a iya fahimta, amma idan mun sakar mata fuska ta saki jikinta damu sai mu rabata da gidan nan" dariya Shareefat ta yi ta ce" muguwa kawai" juya idanunta ta yi ta ce" nafi hakama"







Da sallama tashiga parlon nasa wanda banda ƙamshi babu abinda yake, zaune ta sameshi ya rufe idanunsa ya yi shuru. Zama tayi a ƙasansa ta ce" Abbana"

Buɗe gajiyyayun idanunsa ya yi akanta amma bai ce komai, littafin hannunta ta buɗe ta ce

"Abbana ka koyamin ban iyaba"

Kallonta ya yi sai kuma ya kalli littafin ya miƙa mata hannu, tagane abinda yake nufi hakan yasa ta miƙa masa littafin nata.


Ajiyewa ya yi agefensa sannan ya tashi ya shige bedroom ɗinsa


Not too long ya fito hannunsa riƙeda al-qur'ani ya zauna aƙasan carpet ya tankwashe ƙafafunsa

"Zo nan"

Ya furta a nutse.Tasowa tayi cikin sanyin jiki ta zauna gefensa tana kallon al-qur'anin

"Daga yau idan kindawo daga makaranta zamu dinga yin karatu" murmushi tayi sannan ta ce"tom, zaka koyamin Abbana?" gyaɗa mata kai kawai ya yi dan gudun kar taja maganar da tsayi. Sosai yayi mamakin ganin yanda take karatun kamar antaɓa biya mata kuma hadda bata yimata wahala duk abinda ya biya mata to haddacewa take, kuma yasa ya dinga godewa Allah.




Dariya tayi ta ce"ai naganesa shine wanda ya dinga liƙa dollar ranar bikinmu" "exactly ashe baki mance saba" murmushi Ajmal ya yi ya ce" ai nima ban mance amarya ba to ya gida?" "lpia lao Alhamdulillah" ta bashi amsa sannan ta miƙe tashiga kitchen.



Kallonsa ya yi ya ce"yanzu zaka kwana anan friend?" girgiza kai ya yi ya ce" nifa bazan kwana ba narigada na kama ɗaki tun da safe kuma anan zan dinga kwana period" girgiza ka Khalil ya yi ya ce" Allah ya rabaka da gaddama prince" harararsa ya yi ya ce" ba Ameen ba".



Kallonta kawai yake har tagama kwanciya akan gadon sannan ya ce

"Dare nayi aje akwanta"

Tura baki tayi ta ce" ni Abba ka barni anan" girgiza kai ya yi y ce" banson rigima" shuru tamasa tana sake rufe jikinta da blanket ɗinsa, ajiyar zuciya ya sauke sannan ya juya ya fita daga bedroom ɗin




Zaune suke acikin ajin kowa da ƙawarsa amma banda ita tayi shuru abinta, taɓata Hajar tayi ta ce" hyyyyy" shuru tayi mata dan batasan mene ne abinda ta faɗaba, bata kawo komai aranta ba ta ce" ya sunanki?" Hauwa'u Heesham ta bata amsa dan shine sunan da Bilal ya faɗa mata. Murmushi Hajar tayi ta ce" ni sunana Hajar inason ki zama ƙawata" batasan mene ne ƙawaba ta ce"tom" kamo hannunta ta yi ta ce" zo muje muyi break" bata mata musu ba suka jera tare abin su.



Buɗe ƙofar ɗakin akai ta ɗaga kanta tana kallonsu zama sukayi gefenta da murmushi a fuskarsu Nihal ta ce" karatu ki keyi?" gyaɗa mata kai Jiddah tayi har sannan tana riƙeda al-qur'anin ganin kamar bata saki jiki da suba yasa Shareefat ta ce" daman zuwa mukayi muganki taso muje ɗakina" murmushi ta sakar musu dan daman batason zamanta ita kaɗai indai ba Sheikh yana nan ba kamo hannunta Nihal ta yi tace"taso mana" tashi tayi cikin tafiyarta a nutse kamar koda yaushe ta ajiye al-qur'anin sannan suka fita daga ɗakin.





Ƙarar shigowar motoci taji yasa ta miƙe da mamaki Nihal ta ce" A'a Jiddah ina zakije?" gaba tayi tana faɗin "Abbana ya dawo zai min karatu" harararta Shareefat ta yi ta yi ta ce" kinji munafuka ko, daman ƴan fulani da tsafi wlh inaga ta tsaface Sheikh" tsaki Nihal ta yi ta ce"ni bari Mami ta fito kawai azo ayi maganar nan dan wlh jinake kamar zuciya ta zata fashe saboda baƙin ciki wlh na tsani yarinyar nan" dariya Shareefat ta yi ta ce"wlh kam idan kin aureshi shikenan kin huta da fargaba, yarinya ƴar ƙarama sai makirci" tashi sukayi saboda yin sallar isha'i.






Yaukam da wuri tayi karatunta yana jinta dan bai mata ƙari ba, tana gamawa ya ce

"Allah yayi miki Albarka Fulani"

Murmushi ta yi har saida beaty point ɗinta suka lotsa ta ce"Ameen Abba".



Kusan wata ɗaya kenan tana zuwa makaranta kuma sosai ta bawa kowa mamaki dan tanada saurin fahimtar duk abinda ka koya mata, har malaman makarantar sun fara saninta, yauma suna zaune da Hajar suna karatu dan indai ba lokacin wasaba to zaka samesu suna karatunsu abinsu. "Wai kee ina ne gidanku?" Hajar tatambayeta kwaɓe fuska ta yi ta ce" nima bansan sunan unguwar ba saidai na tambayi Abba idan na koma gida" dariya Hajar ta fara mata ta ce"yanzu bakisan unguwarkuba?" haɗe rai tayi ta ce" E, ɗin" shuru tayi saboda tasan next reaction ɗinta kukane ta ce"shikenan mu cigaba da karatunmu"..



Murmushi tayi ganin wanda yazo ɗaukanta bayan sun shiga mota ta ce" uncle ina Abbana?" yana kallon titi ya ce"bayanan yaje Abuja shine ya ce nazo na ɗauke ki" kwaɓe fuska ta yi ta ce"yaushe zai dawo?" dariya ya yi ganin yanda tayi da fuska ya ce"gobe" fashewa tayi da kuka ta ce"dan Allah kace masa ya dawo yau" dariya kawai yake saboda yanda take kukan ya ce"shikenan calm down dear anjima zai dawo yanzu gidana zamuje dake ki zauna ko bazaki ba?" ɗaga masa kai tayi ta ce"zani" ya ce" good gurl".



*SHEIKH HEESHAM*[3/5, 16:00] 🥰Nanameera🥰: https://chat.whatsapp.com/LSYEkQgVkLKDQyheA6YWH4
*I Dedicated this book to yhu Aunty Sarauta my nimcyluv, much luv*


*Paid book*
*Free page 7-8*


Murmushi Ameera ta yi ta ce"yau ɗiyar Sheikh ce a gidan namu?" zama Jiddah ta yi ta ce" ina yini y gd?" "lpia lao" kalle-kalle ta yi sai kuma ta ce

"Ina junior?"

"Yana makaranta maybe suna hanya"

Okay Jiddah ta ce sannan ta yi shuru dan damaan ita ba gwanar magana bace.




Har kusan isha'i tana gidan Bilal, dan tare suka dafa abinci da Ameera tana koya mata wasu abubuwan


"Mom"

Juyowa tayi tana kallon ɗan ƙaramin kyakkyawan yaron ta ce

"Toh sarkin tambaya yanzu kuma mene ne?"


Turo baki yaron ya yi sannan ya ce
"Dad ne ya ce wai aunty Jiddah tazo zai maida ita gida"


Kallonsa Jiddah ta yi ta ce"ka ce masa gani nan"

Juyawa yaron ya yi Ameera ta ce" bazaki kwana ba?"


Girgiza kai tayi ta ce" Abba zai min faɗa"

Murmushi Ameera ta yi ta ce

"Kaga ɗiyar Sheikh"

Rufe fuskarta ta yi da hannunta sannan ta ce"na tafi"

"Tom sai anjima "


Sannan ta fito parlon ta ɗauki school bag ɗinta sannan tayi waje.


Har suka isa gida ba tace dashi ƙala ba saboda kwata-kwata ta matsu taga Abbanta ji take kamar tayi shekara bata gansa ba



Tsaye ta tarar dasu a parlon kowa ya yi shuru, da mamaki take kallonsu dan ta ɗauka wani abunne ya faru


"Daughter me yasa kika bi Bilal baki sanarwa kowa ba?"


Rarraba idanu ta yi sai kuma ta ce" ai na ɗauka ya faɗa muku shiyasa Daddy kuma..



Wata kyakkyawar tsawa da Sheikh ya daka mata yasa ta yi shuru jikinta nata ɓari, lokaci ɗaya kuma ta fashe da kuka



"Idan baki yimin shuru ba i'll deal with you"


Tsit ta haɗiye kukan nata tana sauke ajiyar zuciya, ya juya yana tafiya dan dauriya kawai yake a haka har ya haura benen



Girgiza kai Daddy ya yi dan yasan halin Heesham kawai ya juya ta tafi, Shareefat ce ta ƙaraso gabanta ta dafata


"Kiyi haƙuri kinji Jiddah ki tashi ki tafi ɗaki gobe sai ki bashi haƙuri"


Ɗagowa tayi tana kallon Shareefat da idanuwanta da suka kumbara ta ce

"Wlh bansan bai faɗawa Abba ba da bazan bisa ba"


Gogo mata hawayen ta yi ta kama hannunta suka shiga ɗakinta



Saida ta tabbatar ta daina kukan sannan ta fito daga ɗakin lokacin ta shiga banɗaki



Juyi kawai take akan gadon amma kwata-kwata ta kasa bacci ko meyasa?????



Da wuri ta tashi kamar kullum ta gama shirin makarantar ta sannan ta fito, kallon ƙofar ɗakin kawai take tanajin kamar ta shiga kamar kuma karta shiga. Jiki asanyaye ta buɗe ƙofar bakinta da sallama ta shiga, zaune ta hangeshi kan carpet ya tankwashe ƙafafunsa ya yi shuru dan bazakace ga abinda yake ba.



Zama ta yi gefensa kanta ƙasa ta ce

"Abbana ina kwana?"

Shuru ya yi mata hakan yasa
End Ads