x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 2 - SHEIKH HEESHAM

  • 3001 words
  • 6000 words
  • Out of 16100 words

Category: Comedy Stories

Views 248

28 May 2025
Start ads
After Image Ads
wanda zai fara saina koma wajen zamana, cecekuce suka fara akan wanda zai zama na farko hakan yasa suka fara faɗa i junansu, fita sukayi daga cikin bukkar sunata faɗace-faɗace......


Zama tayi da farko sai kuma wata zuciya ta raya mata "ga dama kinsamu kawai kiyi guduwarki bai kamata ace a cikin nan kika mutu ba" da wannan tunanin ta fara kalle-kalle ai kuwa tayi sa'a daga can ƙarshen bukkar ta ɗan yage, da sauri ta ƙarasa wajen dukda batada wani kwari amma haka tayi jarumta tana zuwa ta saka kanta ciki amma inaaa bazata iya fita ta ciki ba. Fashewa tayi da kukan baƙin ciki ta haɗe hannanyenta biyu waje guda tana kuka ta ce

"Allah na roƙeka ka taimakeni nabar nan wajen da mutuncina dan darajar Annabi" ta ƙarasa maganar tana rushewa da kuka, har sannan kuma tana jiyo hayaniyarsu suna faɗa kamar ba dare ba.....


Sake gwada fita tayi amma still taji ta kasa, can wata dabara tazo mata ta zauna ta fara kakkarya karan jiki da hannunta kasancewar tsohuwar bukkah ce yasa duk inda ta karya yake karyuwa saida tayi hanya data tabbatar zata isheta ta fita sannan ta saurara. Tana ƙoƙorin zura kanta ciki suka shigo, da sauri ta ƙarasa fita suka biyota da gudu......




Gudu kawai take babu ƙaƙƙautawa kuma har sannan suma binta suke har ta fara galabaita, batasan sanda ta waɗi ƙasa sumammiya ba.........



Tsayawa Driven ya yi da tuƙun, ahankali ya ɗago idanunsa daga kan computern hannunsa juya idanunsa ya yi kamar zai yi magana sai kuma ya yi shuru da bakinsa kusan 2mins amma bai ce komai ba cikeda ladabi driven ya ce
"Sheikh motar ta samu matsala kuma gashi dare ya rigada ya yi saidai mu samu wani wajen mu zauna zuwa safiya"
Sai a sannan ya kalleshi da fararen idanunsa kuma manya, sunkuyar da kansa drivern ya yi domin duk rashin kunyarka baka isa ka haɗa idanu da Shaikh Heesham ba. A hankali ya buɗe bakinsa yana tasbihi ga ubangiji kusan mintuna biyar sannan ya ce cikin tsantar nutsuwar data gama ratsashi
"Allah ya kaimu"
Abinda kawai ya furta kenan bai kuma sake wata maganar ba ya lumshe idanunsa masu kyau. Sheikh Heesham Muhammad kenan babban malami a ƙasar saudia yankin larabawa, ya kasance kyakykyawa dan asalin balarabe ne mahaifinsa Alhaji Muhammd ɗan asalin ƙasar saudia ne amma bai rayu acan ba kasancewar duka danginsa mutanen Nigeria mahaifiyarsa ta haifeshine a ƙasar dalilin zuwa omrah. Sanda aka samu cikin Sheikh Heesham sai mahaifiyarsa Hajiya Amina ta tafi saudia dan rainon cikin jikimta har kuma ta haihu ƙasar hakan yasa shima ya kasance indigin na ƙasar saudia saboda haka sanda ya fara tasawa sai mahaifinsa ya kaishi karatu ƙasar, ya kasance ya rayu a ƙasar tun yana ɗan karamin yaro har girma shiɗin likitane gefe guda kuma babban malami a ƙasar. Wannan shine ƙadan daga tarihin rayuwarsa..

Ganin dare na ƙara yi yasa drivern ya ce
"Sheikh ko zamu samu wani gurin mu zauna?"
Ba zaka taɓa cewa da Sheikh Heesham ake magana ba dan ko kallonsa bai yiba bare ya saka ran zai bashi amsa saima cigaba da danna cazbahar hannusa da yayi..

Hadarine ya haɗo ganga-ganga kuma kana gani kasan ba ƙaramin ruwane zai sauka ba, ɗaya daga cikin securities ɗinsa dake ɗaya motar ne ya fito yana tafiya kamar wani zaki yazo gaban motar ya sunkuyar da kansa ya ce

"Sir wannan hadarin zai iya sakawa ayi ruwa mun samu wani waje zaka je ka zauna saboda lafiyarka"
Sai a sannan Sheikh ya kalleshi amma bai ce komai ba, buɗe masa motar ya yi yana kallonsa. A hankali kuma cikin nutsuwa ya zuro ƙafarsa waje sannan ya fito daga motar yana gyara zaman al-kyabbar jikinsa ya ce
"Ya Allahu"
Shine abinda ya furta yana sake kallon yanda garin ke yin duhu na haɗowar hadari sannan ya fara tafiya yana goya hannunsa a bayansa....

Wata bukkah ce suka nuna masa ya sunkuya domin kwata-kwata bukkar batayi rabinsa ba, zama ya yi kan carpet ɗin da suka shimfiɗa masa kamar kuwa jira ake ruwan ya fara sauka da ƙarfinsa...

Ba ƙaramin ruwa akayi a jimeta ba ko'ina ya yi daɗin gwanin ban sha'awa ganyayyaki da shuke-shuke duk sunyi kyau, yanayi ne wanda zai sanyaka cikin nishaɗi da annashuwa haka kuma har Allah ya wayi garinsa.....

Zaune yake inda ya yi sallar domin bai iya bacci ba yana azkar ɗinsa wani guard ya shigo ya sunkuya cikin girmamawa ya ce
"Barka da safiya Shaikh!"
Ba tareda ya kalleshi ba ya ce
"Barka"
Abinda kawai ya iya furtawa kenan, guard ɗin ya ce

"Sir ya kamata mu tafi dan jirgin ya kusa tashi"


Batareda ya yi magana ba ya miƙe yana ambaton sunayen Allah a ransa kamar koda yaushe ya yi waje.....




Sosai take mamakin inda taganta kwance, ahankali ta miƙe zaune tana kallon kusan duk mutanen rugar da suka zagayeta ana ƴan ƙananun maganganu, mai garin ne ya fito yana kallon kowa ya ce


"Ina fatan kowa ya shaida abinda wannan yarinya ta aikata?, saboda haka za'ayi mata hukunci daidai da laifinta saboda kada ƴan baya suce zasu kwaikwaya " gyaɗa kai duk suke alamar gamsuwa da abinda ake faɗa d'in ita kuwa sai idanuwa take binsu dashi dan bata gane inda zance ya dosa ba....



Wata zabgegiyar bulala aka ɗauko irin wacce suke amfani da'ita idan za'ayi shaɗi tasha manshanu sai kyalli take, kallon bulalar kawai take dan batasan me zasuyi da itaba, mai gari ne ya kalli mutumin ya ce


"Zaka yi mata bulala 80 shine hukuncinta da kuma kora daga cikin garin nan".


Karɓar bulalar ya yi yana sake gyara zamanta a hannunsa ya ce"za'a riƙetane saboda kar ta wahalar dani?"

Girgiza kai ya yi ya ce
" Ai bata isaba dole ta tsaya ayi mata hukunci tunda shi ya zama ɗan iska"


Allah sarki Jiddah banda kallo babu abinda take amma zuwa lokacin ta gane inda maganar tasu ta dosa, wasu zafafan hawaye ne suka zubo mata ta saka hannunta tana sharewa Allah ya sani bata aikata komai ba kuma batasan ya akayi ta zo wajen nan ba amma wa zata faɗawa ya yarda da ita?!, babu..........




Tafiya kawai suke acikin motar, idanunsa a lumshe suke dan wani azabbaben ciwon kai yake ji, ji yayi zuciyarsa tayi wani kyakyawan bugu ya buɗe idanuwansa yana kallon garin daidai nan kuma ya hango wasu cuncurundon mutane kuma fulani ya yinda har sannan yake jin bugun zuciyar na sake tsananta.

"Stop the car"

Ya faɗa ba tareda ya kalli drivern ba cak kuwa ya tsaya yana juyowa dan yasan ba ƙaramin abune zai sa Sheikh ya magantuba. Kamar wanda akama tilas haka ya kama murfin motar ya fito, nan take duk guards ɗinsa suka fito kowanne ya yi cirko-cirko dashi...



Tafiya ya fara yi torward direction ɗin da yake hango mutanen, yana kusantar wajen yanajin bugun zuciyar na ƙaruwa fiyeda na baya a haka har ya ƙaraso.....




Ganin balaraben mutum yasa duka suka dare masa hanya, a hankali ya matsa har inda yarinyar ke kwance sai zabga mata bulalar ake, duk jikinta jini ne kana gani kasan ba ƙaramin duka suka mata ba..


Ba tareda ya yi magana ba ya ƙarasa wajenta yana kkallon mutumin, ahankali kuma ya zare bulalar daga hannunsa cikin yanayinsa nason kamewa ya ce


"Ka bari babu kyau zalunci"

Sakar baki sukai dan basu ɗauka ya iya hausaba, mai garin ne ya ƙaraso gabansa wani guard ya daka masa tsawa

"leave that place"

Zabura ya yi Sheikh Heesham ya riƙoshi yana kallonsa ya ce

"Mene?"

Cikin inda-inda ya fara faɗin

"Daman..Dama..Daman wannan yaron ya mana laifi ne an kamashi da maza da daddare kuma hukuncinsa shine bulala 80 sannan a koreshi daga garin"


Kamar bazai magana ba sai kuma ya ce

"Ku rabu da'ita"


Girgiza kai ya yi ya ce "ai saidai ka tafi da'ita dan indai tana garin nan to sai angama mata bulalar nan kuma bulala 20 aka mata"


Shuru Sheikh Heesham ya yi sai kuma ya sakeshi ya juya dan komawa mota....



Da gudu arɗo ya bishi kafin ya isa motar ya cimma sa cikin magiya ya ce

"Dan Allah dan Annabi yaro ki taimaka ki tafi da Jiddoh ko zata samu rayuwa me kyau zata mutu anan aradu indai suka gama yi mata wannan bulalar to bazata tashi ba, ki taimaka yaro"

Ya ƙarashe maganar yana kuka...


A nutse ya saka tattausan hannunsa ya ɗago arɗo yana kallonsa sai kuma ya yi murmushi ya ce


"Shikenan zan kula da'ita"


Ajiyar zuciya arɗo ya sauke sannan ya ce

"Amma baza su barka ka tafi da'ita ba har sai ka aureta"

Da sauri ya kalleshi sai kuma ya girgiza kai alamar bai yarda ba.


Tsugunawa arɗo ya sakeyi ya ce
"taimakawa zakayi idan kuka bar garin nan sai ka saketa kaji yaro" shuru Heesham ya yi arɗo ya ce

"Naga kayi kalar taimako yaro ka taimakawa marainiyar nan batada kowa sai Allah sai kuma kai yanzu"


Bazai iya cewa A'a ba dukda yasan bazai zauna da ita matsayin mata ba amma zai taimaketa yayi jahadi.......


Murmushi ya yi yana kallon Arɗo ganin yanda yake kuka da idanunsa ya ce

"Shikenan na amince".......


Kama hannunsa arɗo ya yi jikinsa har rawa yake suka koma wajen....




Yana kallon mai gari ya ce

"Zai tafi da'ita"

"Amma yasan saidai ya aureta?"

Gyaɗa masa kai ya yi ya ce" shikenan"


Anan aka ɗaura auren Sheikh Heesham Muhd da Hauwa'u Ahmad sadakinma zoben hannunsa suka karɓa.......



Kallonsa Ardo ya yi ya ce
"Na yarda dakai yaro nasan zaka kula da rayuwar Hauwa'u kada ka barta ta yi kuka kaji"

Riƙe hannunsa Sheikh ya yi ya ce

"Har ƙarshen rayuwa"


Kwance take dan har sannan bata farfaɗoba ya saka tattausan hannunsa ya ɗauketa yana tafiya har suka isa cikin motar, tsayawa arɗo ya yi yana musu addu'a har suka ɓacewa ganinsa.........




Share it plx.


*Paid book #500.*

*SHEIYK HEESHAM*
[3/4, 22:15] 🥰Nanameera🥰: https://chat.whatsapp.com/LSYEkQgVkLKDQyheA6YWH4

*🌹SHEIKH HEESHAM🌹*


*🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*
{R.S.W.A}

https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c
*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_*
_(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_

*Alk’alaminmu ‘yancinmu*





Nanameera.



03.


Tafiya kawai suke inda shi kuma tunaninsa ya ke wani wajen daban,
"Ya Allahu, ya Rahmanu"
Shine kawai abinda bakinsa ke furtawa har suka ƙaraso filin jirgin....

A vip yake ya kishingiɗa da bayan kujera idanunsa a lumshe shi kaɗai yasan iya abunda ke damunsa gashi kuma ciwon kansa nason hargitsashi, ahaka yana wannan tunanin bai san bacci ya ɗaukeshiba dan baccin Sheikh sai dai ɓarawo......

A nutse yake tafiya guards ɗinsa na biye dashi har ya'isa gaban motar suka buɗe masa, zama ya yi yana kiran sunan Allah a cikin ransa kamar koda yaushe. Ganin drivern yaƙi tafiya yasa ya ce
"lpia?"
"Sheikh daman yarinyarce ba'a ɗauko ba"
Sai asannan ya tuna dan kwata-kwata ya manta da wata yarinya ya ce" ina take?" tana can kwance har yanzu bata farfado ba za'a saka guard ya ɗauketa ya kaita asibiti"
Bai ce komai ba ya sauka daga motar ya bisa da kallo yana daɗa jinjina hali irinna Sheikh Heesham.....

Kwance ya tarar da'ita har sannan kuma batada niyyar farfadowa, a hankali ya sanya hannayaensa duka biyun ya ɗauketa, ji yayi kamar bai ɗauki komai ba saboda rashin nauyinta ni kuwa nace ya za'ayi tayi nauyi??????..

Kai tsaye asibitin Abdullahi wase dake nassarawa ya kaita, sosai sukayi murna ganin babban malami a asibitin cikin mutuntawa kuma suka karɓeta shikuma ya shiga mota dan tafiya gida......

Tsaye take saman benen gidan taga motocin na reton shigowa, da gudu ta sauko ƙasa tana kallon Mami ta ce" Mami Sheikh"
Murmushi Mami ta yi ta ce" ai naji ajikina ya dawo tun ɗazu" bata rufe baki ba ya shigo parlon ɗaukeda sallama, da murmushi afuskarsu suka amsa masa sannan ya zauna kan kujerar yana kallonsu ya ce
"Mami ina yini"
"lpia lao Heesham ya hanya?"
Ya ce"lpia lao Alhamdulillah" da murmushi a fuskarta ta ce" yaya ina yini"
"lpia lao ya karatu?"
Shine abinda ya tambayeta sannan ya miƙe ya ce" zan watsa ruwa" daga haka ya shige apartment ɗinsa.......

Ajiyar zuciya ya sauke lokacin da hancinsa ya shaƙi daddaɗan ƙamshin airfreshner da akayi amfani da'ita a ɗakin, a hankali ya shige bedroom ɗinsa yana jan jiki dan ya gaji sosai........

Zama ya yi gefen royal bed ɗin dake ɗakin, ko ina tsaf yake gwanin sha'awa kuma yasan babu wanda zaiyi wannan aikin sai Mami dukda yasan wajen a gyare yake amma wannan sabon gyarane, ganin lokaci na shigewa yasa ta tashi yana sakin ajiyar zuciya a karo na babu adadi ya shiga banɗakin......

Fitowa ya yi jikinsa yana ɗiga alamun wanka sumar kansa ta zubo har fuskarsa, ga wani faffaɗan ƙirjinsa sai gashi da ya yi luf akai a hankali yake goge jikin nasa kamar wanda kwai ya fashewa ajiki har ya gama sannan ya sanya wasu riga da wando farare sol dasu ya shafawa sumar kansa mai sannan ya tufketa da ribon ta zubo har bayansa, sosai take damunsa kuma ahakama ana rage masa ita, ya taje gemunsa wanda yake dogo kuma atsaye irinna riƙaƙƙun malaman nan.
"Alhamdulillah"
Shine abinda ya furta sannan ya hau kan royal bed ɗin nashi ya kwanta nan da nan bacci ya yi awon gaba dashi.........


A hankali ta fara ƙoƙarin buɗe idanunta waɗanda suka mata nauyi sosai, sosai ta firgita ganin inda take dan bata taɓa ganin makamancin irin wannan waje ba a rayuwarta iya kacin abinda tasani bukka, sai kogi. Yunƙurin tashi tayi amma taji wata irin azaba ta ziyarci kwakwalwarta dole ta haƙura ta cigaba da kwanciya nan take kuma duk inda jikinta ya fara mata ciwo, batasan ina take ba kuma batasan dalilin kawota wajen ba duk zatonta ma ko siyar da'ita su Ammi sukai, wasu hawaye ne suka wanke mata fuskarta babu abinda take tunawa sai irin yanda aka dunga dukanta akan laifin da bata aikata ba, tunanin hakan yasa ta sake fashewa da kuka dan ita kaɗai tasan yanda takeji a zuciyarta......



Murmushi ta yi tana kallonsa ta ce
"Laaa yaya Bilal sai yau kazo?"

Fuskarsa a sake ya ce" Eh mana ina Sheikh?"

Dariya ta yi ta ce"daman nasan saboda Sheikh kazo wlh Mami tana ta zancenka amma gashi kanaji ance Sheikh ya dawo shine kazo, ai shikenan ina Junior?" Murmushi ya yi yana shafa kansa ya ce "wlh yana gida ina Mamin?"

"batanan taje gidansu Nihal"
Ta bashi amsa gaba ya yi yana cewa " ok ina nan har ta dawo ai".......


Zaune ya same shi yana danna system kana gani kasan abu mai muhimmanci yake yi, zama ya yi kan bedside drawer ɗin yana murmushi ya ce " su Sheikh manya wato shine sai yanzu kaga damar zuwa ƙasar ko?"

Shuru yayi masa kamar bdashi yake ba, girgiza kai Bilal yayi dan yasan hali ya ce

"Wai kai harnima ɗaukemin kan ka keyi?"
Shuru Shaikh ya yi kamar bazai magana ba sai kuma ya ce" amma kana sane da bakayi sallama ba"

Kwaɓe fuska ya yi ya ce" sorry i forget assalamu alaika"
"Wa alaika salam" Shaikh ya amsa masa, murmushi ya yi ya ce" yanzu sai a kulani ko?"

Murmushin sa mai kyau ya yi dan yana matuƙar girmama abotar dake tsakaninsu dukda cewa shiɗin ɗan uwansa ne dan ɗan ƙanwar Mami ne kuma bazai wuce shekara 35 ba dan kusan tare aka haifesu da Sheikh Heesham.........


Hira suka fara yi akan rayuwarsu amma duk rabin hirar Bilal ke yinta dan shi Sheikh sai Umh, un'un, har lokacin kiran sallah ya yi. Miƙewa Shaikh ya yi ya shiga toilet dan ɗauro alwala domin shine yake jan sallar masjid ɗin gidan nasu............



Zaune suka tadda Mami suna taɓa hira da Shareefat, Bilal ya ce "Mami ina yini" harararsa tayi ta ce" yana gidan biki, sai yau kaga damar zuwa?" shafa kansa ya yi yana murmushi ya ce" sorry Mami wlh abubuwane suke riƙeni" ta ce" amma ai dayake ɗan uwanka ya dawo gashi na ganka yanzu babu abinda ya riƙeka kenan" kasa magana ya yi sai sunkuyar da kansa ya ce banda dariya babu abida Shareefat ke yi ta ce

"Toh yanzu ba gashi yazo ba Mami?" ta ce" yimin shuru kina goyan bayan yayanki kawai"

"Sheikh akawo maka abinci?"

Girgiza kai ya yi ya ce "azumi" ta ce" toh Allah ya haɗamu a ladan"..........


Shigowa ya yi ya ce" Sir yarinyar ta farka"

"Wace yarinya?"
Mami ta tambaya, tashi Sheikh ya yi yay gaba batareda ya amsa tambayar Mami ba, Bilal ne yabi bayansa yana cewa

"Wai bazaka tsaya niba"

Driver sit ya zauna bakinsa ɗaukeda addu'a ya yiwa motar key ya fara tafiya cikin nutsuwa, ganin yanda yake tafe slowly yasa Bilal ya ce" wai dan Allah kayi sauri mana" kamar bazai magana ba sai kuma ya ce" so kake natafi da gudu wani ya mutu?" "wane zai mutu?" murmushi ya yi ya ce" ni mana" da mamaki Bilal ya ce" Eh lallai kaga kuwa bai kamata ka mutu ba bayan baka tara iyaliba, wai yaushe zakayi aure ne?" "sanda Allah ya yi" Sheikh ya bada amsa. Murmushi Bilal ya yi ya ce"wlh inada wata yarinya zan baka ka aura plx" girgaza kai Sheikh ya yi sanda yake parking ya ce" Allah ya tsare" dariya ya yi ya ce" au hakama zakace?" bai ce masa komai ba ya sauka daga motar shima ya fito.........

Tafiya kawai yake amma shi yasan yanda zuciyarsa ke wani irin bugawa ya ce" ya Allahu ya rahmanu" shine abinda yake furtawa har ya kai bakin ƙofar ward ɗin, a hankali kuma ya murɗa kofar bakinsa ɗauke da sallama........




*SHEYKH HEESHAM*

*Paid Book 500#*[3/4, 22:15] 🥰Nanameera🥰: https://chat.whatsapp.com/LSYEkQgVkLKDQyheA6YWH4

*🌹SHEIKH HEESHAM🌹*








*Nanameera*.


*🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*
{R.S.W.A}

https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c
*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_*
_(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_

*Alk’alaminmu ‘yancinmu*


*AMMEY LAYLERH DETA SERVICES*

*Azo asai DATA kan farashi mai sauqi, cikin rahusa👌🏻🤗*

*Data*
*Available*

*MTN*
*AIRTEL*
*GLO*
*9MOBILE*

*MTN*

500MB-175
1GB -350
2GB - 700
5GB - 1750
10GB -3500

*AIRTEL*

500MB - 175
1GB - 350
2GB - 700
5GB - 1750
10GB - 3500

*GLO*


500MB - 175
1GB - 350
2GB -700
5GB - 1750
10GB - 3500

*9MOBILE*

500 - 175
1GB -350
2GB - 700
5GB - 1750
10GB - 3500

Account number: 3206656358

Account name: Maryam Nasiru first Bank



*MORE Information 08104493215*




Paid book
Free page 4.

Kallonsa kawai take tunda ya shigo, da mamaki Bilal yake kallon yarinyar dan kwata-kwata bai taɓa ganin yarinyar ba kuma baisan inda Sheikh ya samo yarinya mace ba, murmushi ya yi mata ganin yanda take kallonsa ya ce
"Sannu ya jikin naki?"
Tana kallonsa ta ce" da sauƙi" Doctor ne ya shigo yana kallon Sheikh cikeda girmamawa ya ce " Sir za'a iya discharging nata saidai a dinga kula da lafiyarta" jinjina kai kawai Sheikh ya
End Ads