x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 25 - AGOLA Behind the palace walls

  • 72001 words
  • 75000 words
  • Out of 196927 words

Category: Love Stories

Views 530

22 Aug 2025
Start ads
After Image Ads
ne, kana ganin yaron nan kasan baya hayyacin sa, idan bamu tausaya masa ba wa zai tausaya masa fisabilillah?" Yace "Ai ya iya furta cewa zai bar gida yaje inda ba zamu taɓa ganin sa ba, so irin wannan kuma ai baya neman taimakon iyayen sa, tunda ya gina kansa ai" daga haka ya shige cikin dakin sa saboda yadda zuciyarsa yake wani tururi. Ummi ganin haka ta fita da sauri tunawa da tayi da friend dinsa dake can main parlor ta kira sa da taimakon driver suka taimaka aka kaisa asibiti, suna zuwa aka masa allura nan da nan bacci ya ɗauke sa. Walima aka yi kamar yadda dama Ammi ta shirya amma Leena taki fita daga karshe ma bacci ne ya ɗauke ta a dakin Ammi. Bayan ya farka a bacci kallon agogon dake manne a bangon dakin yayi ganin la'asar ta kusa yasa ya mike da kyar ya wuce toilet yayi wanka sannan ya dauro alwala bayan ya fito ya tsaya yana tunanin wani kaya zai sa, duk da yamma yayi haka nan yaji yasa kaya mai kyau ya dauki wani Farar kaftan dinsa ya sa, ya feshe jikin sa da favorite perfume ɗinsa, Subtly scenting the air, ya dau prayer mat ya shimfiɗa sannan ya fara Sallah yana idar wa ko tashi akan dadduman be yi ba sai ga Sultan ya buɗe dakin, Sadeeq ya daga kai ya masa kallo ɗaya sannan ya cigaba da tabihn da yake Sultan ya karasa ya zauna a wani resting chairn Sadeeq da ke ɗakin, yana kallon sa yace "Ya jikin, bro?" A takaice Sadeeq yace "Alhamdulillah" ya mike ya nannaɗe dadduman Sultan yace "wannan wanka haka? Ko dai zaka zance ne?" Sadeeq ko kallon direction ɗin sa be yi ba balle yasa ran zai basa amsa Sultan ya dinga kunshe dariyar sa shi rayuwar Sadeeq mamaki yake ba shi dan shi be ga zai iya wannan rayuwar ba, ya kuma cewa "Toh ni kam wannan rashin lafiyar ta ka ko dai saboda Leena zata yi aure ne?" Sai sannan Sadeeq ya juyo yana kallon sa yace "Waye ita kuma?" Sultan na dariya ya mike yace"ai kafi ni sannin ta mana" Sadeeq ya ɗauke kansa daga haka Sultan ya kama hanyar fita yace "dama na shigo ne naji ya jikin naka sai naga ashe zance ma zaka tafi" Sadeeq ko kara kallon direction dinsa be yi ba. Da Daddare bayan yawanci wanda suka zo bikin su wase Anty Binta da Mairamah suna ta jan Leena da hira dan ta sake ga Ayaan dake manne da ita yana game da Wayan ta Ammi ta shigo da sallama duk suna kallon ta ta zauna gefen Leena tace "kina son wani abu ne?" Leena ta sauke kanta kasa tana girgiza kai Ammi tace "Amma yanzu ciwon kan da sauki?" Leena tace "Eh, Alhamdulillah"Ammi ta mike dakin Daddy ta wuce tayi knocking sannan ta buɗe ta shiga ta same sa zuwan sa kenan daga masallaci ta zauna kasan carpet kusa da kafafun sa ta daura kanta akai, ta gaishe sa ya amsa mata tayi kasa da murya tace "Dear kayi hakuri da abinda a faru da zu, na san ban kyauta ba, kuma bana son kayi tunanin kamar baka da Say ne akan Leena, A'a wallahi, kayi ma Leena abinda ko mahaifin ta ne iya ka, kuma ba wai bana son jinin ka bane, dan Allah ka fahimce ni" ta karasa maganar muryan ta ya fara canzawa, Daddy yace "Bakomai Sirbajo, na fahimce ki, kuma Hajiya ma sai da ta min magana da yamma nan, wallahi komai ya wuce Allah basu zaman lafiya, Rayyan kuma ba mijin ta ba ne, haka Allah ya tsara" Ammi ta gagara magana Daddy yayi mamaki jin kamar hawaye ne ke zuba a kafan sa yace "kuka kuma Sirbajo?" ta girgiza masa kai, ta share hawayen ta sannan ta ɗago tana kallon sa tace "ban san yadda Leena zata ɗauki wannan lamarin ba dan har yanzu bata sani ba, so dan Allah kai ka mata magana kaji?" yace "shikenan, ki kira min ita ɗin amma ki dawo ke ɗin ma" Ammi ta mike tana kallon sa tace "Nagode" daga haka ta wuce. Sadeeq be taɓa shiga shock irin na wannan lokacin ba, Mami's words left him speechless, his eyes locked on hers as he struggled process what she she had just said, Mami smiled reassuringly at him, as if to say "Ka daina mamaki, da gaske ne" Sadeeq yaji wani hawayen da be san na menene ba ya kama kafafun Mami ya daura kansa akai yace "Mami bansan me zan ce Miki ba, thank you so much, I love you so very much , Mami" Mami tace "Say 'Alhamdulillah' first then thank Sultan, shi ne tsilan everything, Dan sun so a ɗaura da Yayan ta" Sadeeq ya ɗago kansa yana kallon Mami ba ko kiftawa Sultan kuma ? wani Sultan din kuma? kuma ai dazu da yamma ya shigo har yake tsokanan sa amma be ce masa komai ba, ya maida kansa kafafun nata yana ji kamar wadda aka zarewa dukkan wani damuwa Mami tace "tashi muje muyi dinner" ba musu ya mike tana gaba yana biye da ita, suka samu already Sultan da Jidda suna dining din da alama gulman suke dan sai dariya su ke yi suna ganin Mami da Sadeeq duk sukayi shiru. Daddy na kallon Leena ya daura da cewa "so, Kinga ba wanda zai canza ƙaddaran sa, Shine dama nake son sanar da ke shi Muhammad ya janye sai aka daura auren ki da Sadeeq" tsinbul Leena ta mike tana kallon Ammi tace "Ammi waye kuma Sadeeq?" ganin yanayin ta kamar ma bata hayyacin ta yasa Ammi ta mike ta rike ta tace "ke ba musulma ba ce Leena?, kamata yayi ki godewa Allah, ki rungumi ƙaddarar ki, kuma ai shi ya bukaci hakan" tana girgiza kai tace "Ammi wani sadeeq kuma? Ki taimaka ki faɗa min" Ammi tace "Uncle Sadeeq ɗinki mana, Yayan Jiddah" Leena tace "Wallahi bana son shi Ammi, ki taimaka min" da iya karfin ta take ihu kamar ma bata san me take yi ba, and she passed out, Ammi ta ruɗe ganin Leena ta zube kasa ta fara kiran sunan ta da karfi Daddy ya karasa wajan yace "Is Okay Sirbajo, kar kiyi calling attention din mutane" yasa hannu ya daga ta sama yace "bani makullin motar ta" Ammi na mika masa suka fita without anyone noticed them, Ammi sai kuka take ita gani take kamar Leena ba ta nunfashi, duk da gudun da Daddy keyi gani take kamar baya tafiya suna isa da ita ciki Nurse suka karbe ta aka kwnatar da ita akan gado wani Nurse na miji ne ke tsaye a kanta kafin sauran su shigo duba ta ya ɗan yayyafa mata ruwa nan take Leena ta ja wani dogon numfashi sai kuma ta farka ta fara bin ko ina da kallo Suna haɗa ido da Ammi ta fara recalling abubuwan da suka faru zata yi magana Nurse biyu mata suka shigo hakan yasa tayi shiru amma kuma har sannan hawaye na sauka daga idon ta. Daddy yaso kwana da ita a asibitin amma Ammi taki ganin ma ba ranar girkin ta bane gwara kawai ya tafi, kuma ita hankalin ta Zai fi kwanciya ace tana ganin ta. Bayan likitan da ke kansa ya zare masa drip din hannun sa zuwa yanzu ya daina jin ciwon kan da dazu ya keji , ga kuma malamin da ya gama masa addu'a ya tabbatar musu asiri ne dama ba su zo asibitin ba, bin dakin da aka yi admitting ɗinsa yake yi da kallo, lokaci ɗaya komai ya dawo masa kwakwalwar sa a mugun razane ya mike ba Ummi kadai ba hatta Abbah dake jin tausayin ɗan nasa ynz, da sisters dinsa da suke dakin duk tsorata sukayi suna kallon sa yana kallon kanwar sa yace "ke, karfe nawa?" tace "passed 8 pm" ya fara Salati ya zauna bakin gadon asibitin ya dafe kansa da hannu bibbiyu yace "Ummi meya same ni ne?" Duk kallon sa suke da mamaki ya mike ya ya taɓa aljihun sa ko zai ga wayan sa yaji babu yayi kasa da murya yace "Nawaal please ki duba min available flight yanzu" Abba na kallon sa yace "ina kuma zaka?" yace "Abbah Kaduna mana, Kaduna zani" sai kuma ya karasa ya rike Abbah yace "Abbah Meyasa baka je ba? Meya faru dani naki Leena? ya durkusa kan gwiwowin sa yace "wallahi I'm not myself, bansan komai ba" sai kuma ya daga kai yana kallon su yace "toh ko mafarki nake yi ne?" ganin yadda yake abubuwa Ummi ta karasa ta rungume sa tana me jin tausayin sa, tace "ka bari sai ka natsu, kaji? duk zamu tafi tare" Yayi shiru a jikin Ummi baya son believing abinda yake ta yawo masa a kwakwalwar. Da safe su anty Binta suka gama breakfast tun wajajan 7am, ta fita da niyyar zuwa sashen Daddy tace masa ta gama sai kuma suka haɗu a compound tana kallon sa tace "yanzu dama nake shirin zuwa ce maka mun gama" yace "Okay, ki same ni a parking space" daga haka ta koma ciki ta dauko basket ta fito. Daddy ne ya fara shiga dakin da akayi admitting ɗin Leena, ga Ammi da ke zaune kan dadduman har sannan bata tashi ba tana ta addu'a, kana ganin ta kasan bata yi bacci ba, ganin su yasa ta shafa addu'an sannan ta gaishe da Daddy, ya amsa yana tambayar ya me jiki, Anty Binta ta gaishe ta ta amsa, Daddy sai kallon Mummy yake wanda kana ganin ta kasan bata yi bacci ba, Anty Binta tace "Yaya, ki koma gida ki huta dan Allah, stress karya kwantar da ke" Ammi ta kirkira murmushi tace "karni damu Binta, I'm okay" Daddy yace "ai gaskiya ta faɗa Miki, kina bukatar hutu" tayi shiru saboda bata son musu da shi, can yana kallon ta yace tashi na kaki gida, ba musu ta mike amma ita hankalin ta zai fi kwanciya idan tana tare da Leena sai de bata ce masa komai ba, Daddy dake kallon Binta yace "idan ana bukatar wani abu kafin na dawo ki kira ni Please" tace "in shaa Allah". Ammi na shiga parlorn ta Ayaan da gudu yazo ya rungume ta tana rike da shi ta karasa ciki, Anty Mairamah tazo tana gaishe ta tana tambayar ta me jiki tace da sauki. Sultan ya lura tun jiya da Daddare Sadeeq ke avoiding ɗin sa, gashi kamar yadda suka saba su tafi Gym tare amma sai yau Sadeeq yayi tafiyar sa ba tare da ya jira Sultan ba, kuma ko haduwa ba suyi ba bayan a masallaci da asuba kuma ana idar wa Sultan ya nemi Sadeeq ya rasa, shi abin ma dariya yake basa, bayan ya dawo Sadeeq nata sauri ya gama breakfast kafin Sultan ya dawo sai kuma be kai ka ya gama ba sai ga Sultan ya dawo yana shiga tun da ya hango Sadeeq na breakfast ya fasa haurawa sama ya wuce dinning kawai ya ja kujera daya baya sannan ya zauna yana kallon Sadeeq da ko sau ɗaya be kalle sa ba, Sultan yace "Hey! Yau ba magana ne?" sai sannan Sadeeq ya kalle sa yace "How are you doing?" Sultan yace "I'm great, avoiding dina ka ke yi?" Sadeeq ya ware ido yace "Saboda me kuma?" A takaice Sultan yace "ka fini sani ai" yayi maganar yadda shima Sadeeq yake wa mutane, sai sannan Sadeeq yace "Thank you, bro. I do really appreciate your effort, I love you" ya karasa maganar yana danna wayan sa Sultan ya masa wani kallo yace "For?" sai sannan Sadeeq ya kalle sa yace "for Everything" Sultan ya mike yace "ka canza rayuwar ka ko zaka ji dadi, kana so ka na kai kasuwa, wai har ce min kayi 'who is she?' imagine fah" Sadeeq ya fara sosai kai yana murmushi ya mike yace "anyway tunda ka gama studying dina is Okay". Tunda Ammi ta dawo gida ta samu bacci har sannan bata farka ba, Hajiya da taji labari tayi ta faɗa wai ba'a gaya mata ba. Mami dake kallon sa tace "Baka ce komai ba?" yace "Duk yadda kuka ce is Okay, Mami" Jiddah tace "well, ni a gani na Mami tunda an daura auren kuma ai su Kinga ba wai wani shiri za suyi ba gidan, already sun gama biki kawai ta tare a cikin satin nan" Mami na kallon sa tace "Hakan ya maka?" yace "duk yadda kuka ce" Jiddah na kallon sa tace "sai ka kira masu paint su sake tunda za'a kai amarya" ta karasa tana dariya ko kallon ta be yi ba, Mami tace "Maganar akwati kuma baka da matsala tunda dama can ka haɗa sai dai dole zaka sake haɗa mata wasu kayan, kawai kudi ne zasu yi magana". Anty Binta sai kallon Leena da take ta surutai ita kaɗai tace "Leena kin ban mamaki, ban ɗauka zaki ki zabin Ammi ki ba, ji yadda matan nan ke wahala akan ki, amma kika rufe ido kice baki son sa? da yanzu ta bari da tuni Daddy ya aurawa dan sa ke kuma kinsan uwar sa azabtar da ke kawai za suyi, ke ba zaki dubi mahaifiyarki ki amsa auren hannu bibbiyu ba?" Leena na share hawaye dake sauka fuskar ta da hannun ta dake makale da drip tace "Anty Binta ba wai bana son zaɓin ta bane, kawai lokaci ɗaya ace wanda kake so ba shi ka aura ba wani daban dole na shiga shock" ta share hawayen da ya gangaro mata tace "kuma fah wanda aka daura min aure da shi bana son sa, yana feeling kansa arrogant ne" tace "zaki so sa Leena, komai ai sai a hankali ne". Bayan Mami taji labari ba yadda bata yi da Sadeeq su je duba Leena a asibiti ba amma fir yaki daga karshe hakura tayi suka tafi ita da Jiddah sai Sultan dake driving ɗin su. Ba su dade da zuwa ba aka sallame Leena ganin yanzu zazzaɓin nata ya sauka sosai. Mummy da ta zuba wa Aminiyarta ido tana sauraron ta gaba daya taji kamar duk duniyan nan itace mara Sa'a, Aminiyarta ta tace "Aikan gwara ki daina murna, an dai gudu ba'a tsira ba ne, yaro dai ance shi daya ne ɗa namiji a gun ubansa wannan ɗayan cousin dinsa ne, sannan uban sa ne me wannan Late kadafur, me wannan gidajen man fetur da ke garuruwan arewacin kasar nan" Mummy ta share zufan goshin ta tana kallon Aminiyarta ɗin, Fatima ta daura da cewa "wallahi kinyi rashin dabara, da hakura kikayi ta aura Rayyan ɗin sai bayan kwana biyu kisa ya rabu da ita, Kinga tana bazawara ba lalle ta kuma auran saurayi ba, kuma idan ta ga ita karamar bazawara ce sai ta iya fara yawo gani zata yi ai yanzu ta bar tsawon yara" Mummy ta share hawayen bakin ciki tace "Toh ni ina Nasan yaron? Kuma ai ita uwar Tata ma bata son a haɗa ta da Rayyan ɗin" tace "ke ba mace bane ? gwadawa zaki yi yanzu ba da bane ? So zaki amshe ta matsayin surka" Mummy tace "yanzu kuma me abun yi?" Tace "ai aikin gama ya gama kuma yanzu, Rayuwar jin dadi zata fara nake gaya Miki"

*I dedicate this to Sadeeq and Leena's Fans*💗🤗

30.....
Leena na zaune a kan prayer mat a dakin Ammi, tana morning azkar ɗinta, ta jin gina da gadon Ammi har ta gama, tayi nisa cikin Thoughts, ta rasa what exactly take ji, ta share hawayen da ya gangaro mata, Sallaman Hajiya ne ya dawo da ita daga tunanin da ta faɗa ta daga kai ta kalle ta har ta shigo a hankali tace "ina kwana Hajiya" Hajiya tace "Lafiya, ya jikin naki kuma" tace "Da sauki" Hajiya ta ajiye mata bowl ɗin hannunta sai ga Ammi ta shigo da sallama Leena ta gaida Ammi, Ammi ta amsa tana tambayar ta ya jiki, mikawa Hajiya cup din hannun ta tayi sannan ta bar dakin Hajiya ta ajiye a gaban Leena tana kallon ta tace "Toh dau ki cinye, ga tea din ma Amin ki ta haɗa" Leena tace "Hajiya ki bari zuba ɗan anjima zan yi kafin nan gari ya fara waye wa" Hajiya ta sake baki tana kallon ta tace "wani gari kuma ya waye bayan karfe 7am yanzu" Leena ta daga kai da sauri ta kalli agogo sai yanzu tayi realizing ashe ta dade zaune a wajan, bata ma san haka ta jima a wajan ba. Ummi tayi knocking kofar Muhammad sannan ta murɗa handle ɗin ta shiga, to her surprise bata gansa a dakin ba kiran sa tayi ko yana toilet amma taji shiru, ta fita ta ja masa kofan, anan corridor ta haɗu da Nawaal da itama dakin zata shiga duba sa tace "Nawaal Yayan ku ya fita ne?" Nawaal tace "baya dakin sa ne?" Ummu tace "Eh, na shiga duba sa sai kuma naga baya nan" Nawaal tayi shiru tana tunani. Bayan Mami ta ajiye spoon ɗin hannun ta ta goge bakin ta da tissue alamar dai ita ta gama breakfast din ta, tana kallon su ta mike tace "See yah later" A dawo lafiya su ka ma Mami da zata office sbd yau Monday ne, Jiddah na kallon Sadeeq da ya maida hankalin sa akan abincin gaban sa tace "Ya Sadeeq kaje ka duba jikin Leena kuwa?" sai sannan ya kalle ta, Sultan ya ɗaura "kema kin san ba inda ya je, kuma ya kama ta kaje, Sadeeq ka ajiye wannan i don't care attitude din na ka aside, to be sincere Family membern ta za suyi magana, tun ba'a je ko ina ba baka damu da health matter din 'yar su ba" Sadeeq yace "then, how is it going to be?" Sultan yace "Duk yadda ka gani ɗan rainin hankali" yana kallon Jiddah alamar jiran amsar ta ya ke yi tace "then, sai kaje gidan nasu mana, atleast za su san Yes zaka iya rike musu ita" Sadeeq na sosa kan sa yace
End Ads