x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 16 - AGOLA Behind the palace walls

  • 45001 words
  • 48000 words
  • Out of 196927 words

Category: Love Stories

Views 529

22 Aug 2025
Start ads
After Image Ads
"You barin faɗa mata, ashe bai da lafiya" Hajiya tace "Eh wallahi, kuma yaki faɗa wa kowa rai a hannun Allah aka same sa" Ammi tace "Toh Allah yaye masa, idan kuka dawo ko da yamma sai na leka su" Leena ta fito daga kitchen tana kwalawa Ayaan kira yazo yayi breakfast Hajiya tace "Yauwa Lina sai ki shirya zaki raka Ni asibiti" Leena tace "toh" daga haka Hajiya tayi ma Ammi sallama. Leena na rike da hannun Ayaan ta kasai gun driver gaishe su tayi suka amsa mata tace "ga Ayaan Daddy baya nan zaka kaisa makaranta inji Ammi na" yace "Toh ba damuwa Hajiya Leena" daga haka Ayaan yayi kissing hannun ta yace "bye Addah" Leena na shiga Ammi tace "Toh ai saiki je ki shirya kafin Hajiyan ta gama shiryawa" Leena tace "toh barin yi breakfast, dan banyi ba" ta wuce dinning. Hajiya ke doka sallama Ammi ta fito tace Hajiya ki shigo Hajiya tace "Leenan ta gama kuwa?" Ammi tace "Leena ki fito ga Hajiya tana jiran ki" Leena dake ciki tace "Toh Ammi ta ɗan ban 2 minutes gani fitowa" Ammi na kallon Hajiya tace "Hajiya ki shigo kar kkyi ta tsayuwa da gajjiya ai" Hajiya ta shiga parlorn tana jiran Leena taga har tayi wajan minti 5 tace "ikon Allah! Yanzu haka zaki je Habujan kina yi sai miji yace dake ki shirya sai ki kyale sa?" Ammi ta kara kwala mata kira tace "wai Leena baza ki fito bane?" Leena tace "Ammi gani fitowa fah" Hajiya tace "ko nayi tafiya ta ne? Yaro yana can yunwa sai tayi masa illa ne? da nice ba lafiya da yanzu ya gama daga hankalin sa" sai sannan Leena ta fito tana turo baki tace "Na gama" Hajiya tace "ba shakka kice kwalliya kika tsaya yi?" Leena tace "Ba kwalliyan da nayi fah" bayan sun fita Hajiya na kallon Leena tace ta ɗauko basket ɗin Abinci sai sannan Leena taga inda ta ajiye ta ɗauka suka karasa parking space Driver ya budewa Hajiya backseat Leena ta wuce front seat daga haka ya kama hanyar asibitin da Rayyan yake bayan sun isa suka sauka suka kira Daddy ya faɗawa Leena inda suke, su ka karasa har ward ɗin da aka kwantar da shi samun su Daddy sukayi a waje Mummy ta gaishe da Hajiya, Leena ta gaishe da Mummy duk da bata yi sammanin jin ta amsa mata ba hakan kuwa akayi ta gaishe da Daddy ya amsa tace "ya me jiki?" yace "Da sauki Daughter" Hajiya tace "toh Ni kam ba zaku kaimu muga Rayyan ɗin ba?" Daddy yace "tun ɗazu be farfarɗo bane so an rufe ɗakin sai zuwa anjima za'a shiga amma for now sunce ayi Hakuri" Hajiya ta rike haɓa tace "dama jikin haka yayi" Daddy yace "shi ba yaro ba, ace ma'aikacin asibiti wai yana jin bai da lafiya sai ya kulle kansa a ɗaki? Da ace banyi noticing hakan ba fah? This is rubbish ai" Hajiya tace "yanzu fatan mu Allah basa lafiya" Wayan Leena ne ya fara ringing da sauri ta kalli me kiran sai kuma tayi silencing wayan Daddy na kallon ta yace "yau baku da paper ne" ta gyaɗa masa kai tace "sai gobe Daddy" yace "success dear" tace "Amin, thank you" daga haka Daddy yace bari zai je ya dawo in banda Hajiya da ke ɗan hira da Leena to duk sunyi shiru kana ganin Mummy kasan tana cikin mugun damuwa can Hajiya tace "bari toh mu tafi" daga haka suka bar asibiti. Leena da ke kwance kan kujerar Hajiya tana waya da Muhammad Hajiya ta shigo parlorn tana masifa Leena tayi saurin ɗaura yatsan ta a bakin ta alamar tayi shiru Hajiya tace "bazan yi ba, idan kika shigo banda aiki ba abinda kike sani, ko ɗan tattare waje baki wa mutun, ji yadda kika bata min kitchen" Leena tayi saurin cewa "Hajiya gashi za'a gaishe ki" Hajiya ta washe baki ta karɓi wayan ta kai kunne tace "Wa'alaikumus salaam, wallahi lafiya kalau" daga haka Leena ta bar Hajiya da wayan kan fridge ɗin Hajiya ta tafi ta ɗauke mata soyayyen naman da ta ajiye ta karasa cikin parlorn suna gama waya ta mikawa Leena wayan Leena ta karɓa ta bar part ɗin Hajiya. Da yamma Hajiya ta gama girka abincin da zata kai wa Rayyan a kofar ɗakin Ammi tayi sallama Ammi ta amsa tace "ki shigo mana Hajiya" Hajiya ta girgiza kai tace "in shiga yanzu ma Lina ta shanya ni? Ai ina tsaye anan" Leena na dariya tace "toh ai yanzu na shirya" daga haka ta fito Ammi na kallon Hajiya tace "Hajiya ko na sa hijabi na biku ne?" Hajiya tace "wallahi da kin kyauta kiyi saboda Allah ba dan matar can ba" daga haka Ammi ta wuce ɗakin ta ta ɗauki Hijab Ayaan dake bacci ta ɗauke sa ya buɗe ido ta sauke shi tana rike da shi suka fito, karasa parking space sukayi. Bayan sun isa asibitin yanzu jikin nashi da ɗan sauki hakan yasa duk suna ciki, bayan sun sauka a motar suka karasa ɗakin da sallama Hajiya tace "A'a toh Alhamdulillah tunda yanzu ana iya shiga" Ammi ta gaishe da Mummy, Mummy ta ɗauke kai daga Rayyan har Daddy ba wanda abin yayi wa daɗi, Ayaan ya gudu ya tafi jikin Daddy, Rayyan ya sauke idon sa kasa yace "ina wuni Ammi" Ammi tace "Lafiya kalau, ya jikin naka Rayyan?" yace "da sauki" tace "Allah baka lafiya yasa ƙaffara ne" Ayaan ya karasa wajan Rayyan yana masa dariya Daddy strictly yake kallon Niswa da Nisreen yace "ko baku iya gaisuwa ba ne" sai sannan suka gaida Ammi, Ammi ta amsa musu Hajiya tace "Ai yaran nan basu da kunya! To nima yaushe suka gama gaishe ni balle sirbajo da suka raina, ai dama me biyayyan kenan daga Rayyan sai Leena" Mummy ta kalli direction ɗin Hajiya tayi suka ciki ciki, Leena na wasa da fingers ɗinta daga kanta tayi taga sun haɗa ido da Rayyan ta sauke idon ta kasa, kuma ɗagawa tayi taga har sannan kallon ta yake yi tace "ina wuni" yace "lafiya Leena" tace "ya jikin kuma?" yace "Alhamdulillah!" tace "Allah kara sauki "yace "Amin, thank you Leena" har sannan be daina kallon ta ba Leena ta zama uncomfortable saboda every now and then sai dai bata ɗaga ido ba sai taga ita yake kallo, wayan ta ne ya fara ringing da sauri ta tashi ta fita dama hakan take so Mummy ta bita da kallo har ta fita. Bayan sun koma gida Leena na kallon Ammi tace "Ammi wallahi ke kike sa nake gaishe da matan can, ni kuma wallahi daga yau na daina, naga dan rashin kunya yaran ta basu gaishe ki ba au" Ammi tace "ai idan kika gaishe ta kin nuna mata ke kina da tarbiyya ne" Leena ta ɗauke kai a ranta tana kudirin ba zata kara gaishe da Mummy ba ai uwa bata fi uwa ba. Da Daddare Daddy yace duk su tafi shi zai kwana da Rayyan a asibiti Mummy na kallon sa tace "ka bari kawai ni zan zauna da shi karka damu" yace "ki tafi kawai, naga kina bukata rest ne ai" daga haka ita da yaranta mata suka fita dama Daddy na neman space da zaiyi magana da Rayyan ne baya son ya gaskata abinda yake tunani bayan tafiyarsu da kamar 10 minutes Daddy yana kallon Rayyan yace "Son" sai sannan Rayyan ya ɗaga jajayan idon sa yana kallon Daddy Daddy yace "Son hawaye nake gani a idon ka?" sai sannan Rayyan ya girgiza kai Daddy yace "well, ina kasan ni mahaifin ka ne ko?" Rayyan ya gyaɗa kai" Daddy yace "Ina son ka faɗa min damuwar ka Karka ɓoye min komai Rayyan, na maka alkawarin idan har be fi karfi na ba toh tabbata zan tai maka maka wajan ganin damuwar nan ta washe" Rayyan ya sauke idon sa kasa ta'ina ma zai fara? yayi shiru for almost 5 minutes yana tunani still Daddy be ɗauke idon da ya zuba masa ba ya ɗaga idon sa yaga still Daddy kallon sa ya ke yi ya tashi daga kwance da yake yi yayi shiru still Daddy na studying ɗinsa yace "say out your mind son" Rayyan ya sauke idon sa yace "Daddy Nasan I'll sounds so dull, bana son barin selfishness ɗina ya ruguza farin cikin wasu, idan naji kamar zan iya daurewa sai na gagara nasa ba zan iya ba" ya kare maganar hawaye na gangaro masa Daddy yaji tausayin ɗan sa yana jiran yaji me ze ce Rayyan ya ɗan kalli Daddyn nasa yace "Daddy Leena nake so, ba zan iya ganin wani ne zai aure ta bani ba" ya karasa maganar yana me rufe idon sa while hannun sa na kan kirjin sa Daddy yayi shiru yama rasa ta ina zai fara yace "Rayyan kayi bacci, zamu yi magana gobe kaji?" sai sannan Rayyan ya buɗe ido ya kalli Baban nasa Daddy ya gyaɗa masa kai yace "ba maganar da zamu yi yanzu bane" gyaɗa masa kai yayi ya rufe idon sa yana ji a kashi dari na damuwan sa kashi ishirin sun tafi. Leena tayi tagumi tayi shiru Ammi har ta gama abinda zata yi zata shiga ta kwanta taga still Leena a yanda ta barta tun ɗazu haka take ta karasa har inda take tace "Leena Lafiyan ki?" Sai sannan Leena ta kalli Ammi ta cire tagumin da tayi tace "bakomai Ammi" Ammi tace "toh tunanin me kike yi haka?" tace "Ammi baki ga yadda Ya Rain ya koma ba? Duk ya rame a cikin ɗan kankanin lokaci" ta karasa maganar hawaye ya gangaro mata Ammi ta tsaya kallon ta sai kuma tace "Addu'a zaki masa Allah basa lafiya" tace "Amin" Ammi na kallon ta tace "toh yau anan zaki kwana kenan dana ga kin zauna kina tunani" ta girgiza kai ta tashi zata shiga ɗaki Ammi tace "shine dalilin daya sa yau kika ki yin wayan daren kenan? Shiyasa yana ta kira kika ki ɗauka kenan ko?" Leena ta buɗe ido tace "A'a Ammi be kira bane kuma ba dan haka bane" Ammi ta harare ta ta wuce ɗakin ta. Baya Leena ta shiga ɗaki kayan bacci tasa ta ɗauki wayan ta da niyyar zata masa text taga har wajan 5 missed ya mata ta buɗe ido da mamaki dan ita bata ji bama kiran sai yanzu ta fahimci me Ammi take nufi da tace shiyasa taki ɗaukan kiran sa ganin text ɗinsa tayi bayan ta karanta tajii jikin ta yayi sanyi ta kashe wayan sannan ta kwanta abunta....
*AGOLA (Behind the palace walls)*




19.....
Washe gari, Mummy bayan tayi alwala ta fito a toilet wajan wayan ta ta nufa kiran Aminiyarta Fatima tayi har ya katse bata ɗauka ba ta kuma kira still bata ɗauka ba ta zauna a bakin gado tayi tagumi duk ta rame a cikin kwana biyu nan jin har an idar da Sallah a masallaci yasa ta tashi ta hau kan sallaya. Bayan Leena ta idar da Morning zikr ɗinta ta wuce part ɗin Hajiya da sallama ta shiga ta zauna akan kujera Hajiya ta fito tana cewa "Yar halak kinki ambato yanzu nake taɗi a raina zanje na tambaye ki ko kuna da makaranta da safe?" Leena na kallon Hajiya tace "Eh ina da shi karfe 9 ma, amma yaushe zaki je asibiti duba Yayan?" Hajiya tace "Lala tafiyan mu zaiyi da ban danni gaskiya karin kumollo zan kai masa toh Kinga da safe zan tafi" Leena tace "zaki je dubo sa da yamma ne?" Hajiya tace "Gaskiya ban sani ba sai naga yanayin jikin nasa tukun nan" Leena ta gyada kai tace "Na san dai in shaa Allah ba zamu wuce 12 ban dawo gida ba, idan na dawo in har zaki koma da yamma zan bi ki" Hajiya tace "Toh, Allah nuna mana" daga haka Leena ta wuce sashen su tana shiga ta hau dafa couscous tasa enough hanta dayan kan gas ɗin kuma ta ɗaura ruwan tea kuma at same time tana soya doya, Ammi ta leko ta sai sannan ta gaishe da Ammi Ammi ta amsa tace "Karfe nawa zaki tafi?" tace tunda papern 9 ne Zahra tace Mu tafi tun 8" Ammi tace "idan ta zo da wuri kawai ku tafi kafin 8 ɗin saboda Kinga ba Daddyn ku a gida yau, toh bansan wa zai kai Ayaan ba" tace "Toh shikenan" daga haka Ammi ta wuce don shirya Ayaan, Leena kuma couscous ɗinta yana gama dafuwa ta sauke ta juye a wani warmer ta ajiye akan cabinet breakfast kuma ta kai dinning tunanin ta tsaya yi sai kuma da sauri ta ɗebo raguwar bawun pineapple tayi blending tare da su citta, kananfari ta juye a pot bayan ya tafasa ta tace da zuba sugar ta ɗauko kankara ta sa acikin ta haɗa sai ta juye a jug daga haka ta ɗauki warmern couscous ɗin da jug ɗin juice ɗin da ta haɗa ta karasa sashen Hajiya ta shiga da sallama Hajiya dake cikin kitchen tana ma Rayyan kunu ta fito tana kallon Leena, Leena ta karasa tace "Hajiya dan Allah gashi ki kaiwa yaya" Hajiya tace "Toh shikenan, zan faɗa masa" Leena tace "Allah basa lafiya" Hajiya ta amsa da Amin daga haka ta fice tana shiga parlorn su taga Zahra har ta zo Leena na dariya tace "Amarya" Leena ta nuna mata ɗakin Ammi daga haka ta wuce kitchen Ganin Ammi tayi a kitchen ɗin Ammi na mata wani kallo tace "me kika yi min a kitchen haka?" Leena ta sauke idon ta kasa tace "breakfast nayi Wa Yaya" wani kallo Ammi ta jefa mata tace "wa kuma kika tambaya?" tayi shiru Ammi tace "Toh wallahi sai kin gyara min kitchen kafin ki tafi exams, ba kin saba ɓata wa ni na gyara ba, toh yanzu ya wuce" daga haka Ammi ta fice a kitchen ɗin Leena ta tsaya tana bin ko ina da kallon kamar zata yi kuka fitowa tayi a kitchen ɗin ta wuce ɗakin Ammi taga har ta gama shirya Ayaan tace "Ammi toh makarantar Ayan ɗin fah, kar kuma yayi latti" Ammi tace "Daddyn ku ya dawo gida zai sa driver ya kaishi tunda shi zai dan huta ne" daga haka Leena ta bar kitchen ɗin Zahra tace "Leena ba zaki je ki shirya ba? Ko kin manta yau practical ne kar muje latti a fara arranging a lab mu rasa kujeran zama?" Leena tace "haka ne fa! Yau Lab zamu yi toh dan Allah Zahra ki taimake mu ki tattara min kitchen mana kafin nasa kaya" Zahra tace "toh amma Kiyi sauri" daga haka Zahra ta wuce kitchen tana tattare tattaren inda Leena ta ɓata Ammi ta shigo kitchen ɗin ta sake baki tana kallon Zahra tace "Wato aiki ta saki kenan? Sai kuma kika biye mata ko?" tana murmushi tace "A'a Ammi dan kar muyi latti ne" Ammi tace "bari abin ki idan masu aiki sun zo za suyi Leenan ne bata son aiki wallahi" Zahra tace "ai na kusan gamawa ma" Ammi ta hana ta Zahra na dawowa parlorn ta sami Leena ta fito tace "ke banyi breakfast ba, barin juye mana a kula sai mu tafi da shi" daga haka ta wuce kitchen ta ɗauki kula ta juye musu. Hajiya ba ita ta gama shiri ba sai wajajen 8:30 ta fito lokacin har Daddy ya gama shiri yana jiran ta a parlorn Ammi Hajiya ta doka sallama yace "Hajiya kin gama ne?" Yana fitowa a ɗakin ne yake mata wannan tambayar tace "Eh, gani nan" Daddy ya karɓa baske ɗin hannun ta ya wuce da shi parking space tana biye da shi a baya ya buɗe mata kofar motar ta shiga. Bayan sun shiga ɗakin da Rayyan ya ke daga Mummy sai abokin sa Fu'ad ne kaɗai a ɗakin Hajiya ta fara shiga Daddy na biye da ita a baya Fu'ad ya tashi a kujeran da yake ya ajiye mata yana gaishe ta Hajiya ta riƙe haɓa tace "wa ido na yake nuna min? Eh lalle Fu'adu laifi muka maka ka daina zuwa gaishe mu" Fu'ad na sosai kan shi yace "wallahi ba haka bane Hajiya abun ne yanzu sai a hankali da ke kuma yanzu aikin nawa ba anan nake yi bane" sai sannan Mummy ta gaishe da Hajiya, Hajiya ta amsa tana tambayar ta ya me jiki Rayyan yana kokarin tashi ya zauna Fu'ad ya taimaka masa ya zauna ya gaishe da Hajiya Hajiya tace "ya karfin jikin kuma dai?" yace "Alhamdulillah" Daddy ya karasa da basket ɗin abinci kusa da Rayyan yana kallon sa Rayyan ya sauke idon sa kasa saboda wani nawin Daddy da yake ji yanzu Hajiya tace "Ai ni zaka bawa na zuba masa amma shi ai ba zai iya ba" Hajiya ta ciro couscous da jug ɗin Juice tace "Allah sarki Leena, wallahi tun da asuba ta gama maka girki ta bani wai na kawo maka ita tana da jarabawa da safe ba zata zo ba" wuff Mummy ta tashi ta tsaya sai kuma bata karasa wajan ba Rayyan zai buɗe kulan Mummy tace "ba kace baza ka iya cin abincin ba?" yace "Mummy yanzu kuma naji ina jin yunwa ne" bayan ya buɗe kulan yayi shiru yana kallon abincin wato Leena tasan favorite food ɗinsa kenan Mummy tace "Toh ka ajiye wannan a gefe sai kaci alalen mana" Yace "Favorite food ɗina ta dafa min kuma tun jiya nake sha'awan ci" Mummy sai hararan sa take yi shi kuma yaki yarda ya kalli direction ɗin ta dan ya san zata hana sa da ido Daddy yace "Ƴar uwar sa ce fah ta kawo masa abincin ba wata ba" Hajiya tace "Ahtoh shine Nima nagani, amma tana son ta hana sa cin abincin da wayo sai kace nan yara ne da ba zamu fahimci me take nufi ba" Hajiya ta karɓi kulan ta zuba masa abincin ta mika masa pineapple juice ɗin ma ta zuba masa, rabon da Rayyan yaci abincin har ya koshi shi kansa ya manta Mummy ta dinga hararan Hajiya ta gefe,
End Ads