kuma yaji maganar ki" Hajiya tace "Okay, ina ji" Mummy ta gyara zama tace "Hajiya Kinga dai yaran nan duk kananu ne, sai kuma najimi wata magana, yanzu ace Baban su har zai yarda yaran nan su fara hira? Me makon ace karatu zasu sa a gaba" Hajiya tace "Toh ai naga aure ba wani abun ki bane " tace "Hajiya yanzu ace Leenan nan ace aure za'a mata? Ko fah yayun ta basu yi ba, kuma wannan ai beyi ba, dama ajira ace ba yanzu ba, sai ta kara girma" Hajiya ta gyara zama tace "toh me kike so ayi yanzu ?" Mummy tace "yauwa, Hajiya ki dakatar da Baban su akan wannan tsarin kawai, kice tayi karama kuma ma ai yayun ta basu yi ba, so ba wanda za'a aurar yanzu, kuma ya hana wannan saurayin da yake zuwa wajan ta saboda kar a fara zagin mu a unguwan ace yaran mu ba tarbiyya muna barin su suna fita hira" Hajiya tace "toh shikenan" Mummy tace "Kin san me, idan har Baban su yace A'a ki buɗa masa wuta ai kece kika haife sa, kuma yana jin maganar ki Nasan zai ɗauka" Hajiya tace "toh shikenan" Mummy na Murmushi ta tashi tace "Nagode, sai da safe" daga haka ta fita, Hajiya tayi murmushin Manya. Ta ɗau wayar ta takira Daddy tace "Ka shigo ina neman ka" daga haka ta kashe........
Kar a manta ayi min Voting, please.
[5/28, 7:39 PM] Jiddatulkhayr writes: *AGOLA (Behind the palace walls)*
Ko minti goma be yi ba sai ga Daddy yana sallama a kofar ɗakin Hajiya dama tana zaune awajen bata tashi ba ta amsa sallamar na sa sannan ya shigo bayan ya gaishe ta ta amsa yace "Gani Hajiya! Allah sa dai lafiya" tace "Lafiya klau, dama tambayar ka zanyi ya maganar yarinyar nan Leena baka kuma cewa komai ba" sai sannan Daddy yayi ajiyan zuciya yaji He feels relieved, yace "Eh yana nan, iyayen nasa ma sunce za su zo nema masa auren na ta a weekend ɗin nan" Hajiya ta gyara zama tace "Toh Alhamdulillah, Ni dai abinda zance maka shine kaji tsoron Allah kar wani ya canza maka ra'ayi akan wannan aikin lada da ka fara yi, sannan kayi ma yarinyar duk wani abu da kasan zaka ma Nisreen da Niswa, saboda itama ƴarka ce tunda kana auren Uwar ta, idan ta nice ma ba zan sa bikin ya ɗauki lokaci ba" yace "In shaa Allah Hajiya zanyi duk yadda zanyi, sannan kuma maganar sa rana ina tunanin zan bari naji ta bakin su farko tunkun nan" daga haka ya mata sallama. Leena da bacci ya fara daukar ta karan ringing ɗin da wayan ta yake yi ne ya farkar da ita with her sleepy voice, she answered the call and said ''Assalamu Alaikum'' in a voice that sounded golden, Muhammad be san sanda ya sauke wani ajiyan zuciya ba and couldn't help but smile and said, ''I can't wait to have you as my wife, Leena. I'll just wake you up whenever you're sleeping so I can hear this sweet, golden voice of yours" Leena ta turo baki taki cewa komai yace "Well, nasan ba zaki ce komai ba, so, How are you doing, today?" tace "I'm fine" yace "I'm calling you just to hear your voice before I sleep. Sorry for waking you up, baby. Good night, darling. Go back to sleep" Leena tsintan kanta tayi taji haushin hakan da yace kawai tace "Uhum" shi ya ɗauka duk a cikin baccin ne ya katse kiran and she feels somehow daga haka ta ajiye wayan ta a bedside table ta kwanta abinta. Mummy data ringa kiran aminiyarta Fatima baya shiga hakan yasa ta hakura har bacci ya fara satan ta, sai ga shi Fatima ta kira ta jawo wayan tayi ganin Fatima ne yasa ta tashi ta zauna sannan tayi picking call ɗin takai kunne da sallama a bakin ta Fatima ta amsa tace "naga alamun kinyi ta trying ɗina, wayan akashe" Mummy tace "ke de bari, dama fah na kira ki ne na sanar Miki yadda muka yi da Hajiya.." Fatima ta katse ta da wuri tace "Wai karde zaki ce min kin same ta akan wannan maganar ne?" Mummy tace "Ehem, na mata magana yadda zata fahimta kuma ta gamsu tace zata ma Baban nasu ma magana, Kinga wai har nine yau bacci ya fara ɗauka ta rabon da nayi tunda naji wai Saurayin Leena ne ya zo gidan nan" Fatima taja dogon tsaki tace "wallahi Ni ban san waya baki wannan gurɓataccen shawaran ba, matar da tunda ba shiri kuke yi ba, ita fah tasa ya aure uwar Agolan nan, matar da tasan baki son ta shine kike tunanin zata bi shawarar da kika batsa Mummy tayi shiru tana tunani Abin da Aminiyar ta tafada Fatima tace "Kuma duk abinda zakiyi gaba ko zai faru da yarinyar zata ce kina da hannu, musamman yadda muke da plan akan yarinyar" sai yanzu Mummy ta ga abinda tayi it sounds so dull tace "Toh yanzu ya kike gani zanyi?" Fatima tace "Matsala ta dake baki bin komai a sannu, Matar nan fa babban ce sab zata gane cewa haddasa kike wa yarinyar" Mummy tace "toh yanzu me mafita?" tace "ki bari zan shigo Kaduna gobe so jibi Saturday dan karaso" Mummy tace "Allah kaimu toh". Washe gari Friday, Leena bata da exams da safe sai bayan an taso a jumma'a, yau tunda ta tashi take taya Ammi aiki after some seconds sai ta duba wayan ta ko zata ga kira ko message idan ta duba taga babu sai ta cigaba da aikin da take yi duk Ammi na lura da ita, can Ammi tace "Leena je ki shirya Aydin Daddyn ku zai yi dropping ɗin sa" tace "toh" ta wuce ta shirya sa Ammi ta haɗa masa Golden morn dan su basu gama breakfast ɗin da suka ɗaura ba Leena na rike da hannun sa suka fita suna zuwa part ɗin Daddy ta tsaya daga waje tana sallama, bata manta lokacin da tazo ɗakin Daddy zata nuna masa JSCE result ɗinta ba Mummy ta kama ta a parlorn sai da ta fasa mata baki har da jini, jikin ta kuwa sai da yayi jaa dan duka akan haka sai da suka yi faɗa da Daddy wanda hakan ya kara mata bakin jini a wajan ta shiyasa tun daga ranan bata kara attempting shiga ba kullum a waje take tsaya wa, kara sallama tayi taji Daddy be Amsa mata ba Ayaan yace "Addah, just go, I'll enter. Maybe Daddy is in the bedroom, that's why he didn't hear us" Leena ta girgiza kai bata son tafiya ta barshi a wajen dan anything can happen after some minutes sai ga Daddy ya fito zai kulle kofar da mamaki yake kallon Leena, Ayaan yace "Daddy tun ɗazu muke ta sallama" ya karasa gun Daddy, Daddy ya ɗaga sa sama yana dariya, Leena tace "Ina kwana" yace "Ina baki jin magana ko, Leena? Didn't I tell you that whenever you come here, you can just come in?" ta sunkuyar da kai tana wasa da fingers dinta tace "Daddy I'm sorry" yace "It's Okay " Ayaan dake hannun Daddy yace "bye" Leena ta juya jikin ta yayi ta wuce ciki, tana shiga gun wayan ta ta wuce Ammi na kallon ta ta kunna wayan ta ganin ba missed call balle SMS ta wuce dinning Ammi tace "idan kin gama breakfast ɗin ki wanke plates ɗin" tace "toh Ammi" tana gama breakfast ta wuce kitchen before 9am ta gama ta wuce ɗakin ta sake duba wayan ta tayi taga shiru. Bayan ta fito a wanka tasa kaya hakanan taji hawaye ya gangaro mata ta share ta ɗauki Littafin ta ta fara duba abubuwan da ta karanta kafin Zahra ta zo. Da yamma bayan ta dawo daga school ta gaishe da Ammi, Ammi tace "Leena ko zaki je ki gaishe da Mami yanzu, amma karni daɗe, gobe kuma sai kuje shopping tunda Sunday zasu dawo" Leena tayi shiru Ammi tace "naga ba dadi kin mata alkawarin Saturday zaki je" tace "Toh, Ammi" daga haka ta wuce dakin ta ɗaukan wayan ta tayi tana expecting ganin call ɗin sa nanma shiru, ta wuce ta chanza kaya sai gashi ta fito tana kallon Ammi tace "Ammi ina Ayaan?, sai mu tafi da shi" Ammi tace "Daddyn ku ya fita da shi" tace "toh barin tafi" Leena ta kama hanyar fita a bakin gate tayi clashing da Rayyan shi da kannan sa ko kallon su bata yi ba tayi wucewar ta da kafa ta karasa gidan su Mami gatekeeper ya buɗe mata gate ta shiga parlorn da sallama Mami na zaune a sofa Sadeeq yana kwance a 3 seater yana kallo Sultan shima yana zaune yana ba Mami labari, ta karasa jikin parlorn Leena tayi hugging ɗinta Mami tace "Ai yanzu Leena kin daina sona ai" tace "Wallahi Mami ba haka bane" Sultan yace "Iyyee, Wato yau dan Kinga Mami shine ko magana babu ko?" tana murmushi tace "Ai zan gaishe ku, barin gama da Mami na" Mami tace "Ah toh" sai sannan tace "Uncle Sultan ina wuni" yace "Lafiya kau, ya exams ɗin" tace "Alhamdulillah" ta ɗan leka Sadeeq dake kwance tana murmushi tace "Uncle Sadeeq" Sadeeq yayi kamar be ji ba Sultan ya taɓa sa yace "baka ji ana maka magana bane" wani kallo ya masa yace "Waye?" Sultan yace "Leena mana" Sadeeq yace "Can you tell me who she is?" ba Leena ba har Sultan sai da ya buɗe baki yana kallon sa Mami tace "kyale sa abun ki" ko juyowa be yi ba balle ya kalli direction ɗin sa Leena ta harare sa. sai kusa da Magrib Leena ta fito a ɗakin Mami a parlorn ta haɗu da su Sadeeq ko kallon direction ɗin sa bata yi ba tace "Uncle Sultan barin tafi" yace "so soon?" tayi dariya tace "it's almost Magrib fah" ya gyaɗa kai yace"wait barin kai ki" sai sannan Sadeeq ya kalli Sultan, Sultan ya wuce sa ya ɗauki keyn motar sa. Da Daddare bayan Leena tana part ɗin Hajiya suna hira Hajiya na bata labarin daa Leena tana ta dariya wayan ta ne ya fara ringing kallon screen ɗin tayi ganin Muhammad yasa da sauri ta ɗauki wayan tace "Hajiya sai da safe" tayi receiving call ɗin ta kai kunne tana sauri ta wuce part ɗinsu ko gama buɗe labulan parlorn bata yi ba zata fita Rayyan da zai shiga parlorn Hajiya kenan Leena ta fada jikin sa rike ta yayi sai da ta tsaisaita kanta sannan ta wuce sa ko kallon sa bata yi ba waya kare a kunnen ta, binta yayi da kallo yaga still waya na kare a kunnan ta, kara sa cikin parlorn yayi, Hajiya tace "ka gane min yarinyar nan, tun ɗazu fa take nan muke labarin mu, shikenan saurayin ta na kiran ta shine fa ta rikice ko kallo na bata yi ba ta tashi wai sai da safe" ta karasa maganan tana rike haɓa Rayyan yafi minti biyar yana kallon Hajiya kamar wani statue Hajiya tace "ya zaka zo ka sani gaba kamar wata ƴar iska?" Sai sannan Rayyan yace "Hajiya ita Leenan ne take da saurayi?" Hajiya tace "Toh kar tayi? yarinya Ma-shaa-Allah so kake tayi ta zama mana haka ta buɗe ido" ya sauke idon sa kasa without saying anything sai can yace "Sai da safe" Hajiya tace "ikon Allah! Amma lafiya ko? Ka shigo ka sani a gaba da kallo sai kuma ka tashi kace zaka tafi?" ba kalli Hajiya ba ya fice abin sa. Leena da ta ɗauki wayan Muhammad shiru tayi taki ce masa komai tana karasa cikin ɗakin ta ta faɗa kan gado still wayan na kunnen ta ta fara sheshsheka Muhammad yace"SubhanAllah what's wrong dear" kana jin muryan sa kasan yayi maganar cikin damuwa tace "shine yau throughout baka kira Ni ba?" Muhammad yayi shiru yace "Baby na ɗauka ai kamar ina takura ki ne, kuma wallahi yau na wuni ina aiki ne gashi ni ne nayi organizing zuwan su Abba na jibi" tayi shiru itama tasan duk lokacin da suke waya bata basa attention sbd bata da interest, yace "Baby" tace "Uhm" yace "I'm so sorry" tace "it's Okayy" yace "ko sai gobe na biyo su Abba, na zo bada hakuri tukun" tace "Ai nayi hakuri" ba Leena ta kwanta ba sai pass 12am suna ta hira da Muhammad ita kanta tayi mamakin chanza wanta. Yau Saturday, Daddy ya hayo masu aiki suka gyara gidan tass duk wani lungu da sakon gidan sai da aka gyara flowers akayi streaming, masu paint suma suka zo da kayan aikin su. Kamar karfe 10am Mummy ta fito daga kitchen tana kallon Rayyan dake aiki a system ɗin sa tace "Ni kam Rayyan meke faruwa ne a gidan nan" yace "wallahi Nima Mummy ban sani ba, kawai dai naga Daddy yasa na kira masa masu paint zuwa na kuma naga anata sanitation" tayi shiru tace "kuma baka tambaye sa ba?" ya girgiza kansa yace "A'a ban tambaye sa ba" sai ga Nisreen ta shigo tace "Mummy wai yau muna da manyan baki?" Mummy dake kallon ta tace "waya fada Miki?" tace "Chap ai Mummy ki fita cikin compound ki ga yadda ake gyaran gidan nan, shine na tambaye Hajiya tace wai Abokanan Daddy ƴan siyasa ne zasu zo masa" Mummy tace"Ikon Allah, toh Daddyn naku be faɗa min ba" daga haka ta kama hanyar ɗakin ta at least taji hankalin ta ya ɗan kwanta akan da zu. Ammi ta mika wa Leena list ɗin hannun ta tace "ku fara zuwa wajen Chef Siyama ku bata list ɗin abinci da snacks ɗin da zata yi gobe, sannan sai ku wuce supermarket" Leena tace "toh Ammi" Ammi tace "kice mata na kira ta wayan akashe tana kunna wa ta kira Ni back" Leena tace "In shaa Allah" Leena na kallon Zahra tace "Mu tafi Zahra" Zahra ta tashi suka fita a compound suka haɗu da Rayyan da zai fita shima kallo daya Leena ta masa ta ɗauke kanta haɗa ido yayi da Zahra haka taji ba zata iya cin dry ba tace "Ina kwana " yace "Lafiya" daga haka ya wuce parking space. A bakin street ɗinsu suka tsaya suna jiran taxi sai ga Rayyan ya zo zai wuce sai kuma ya tsaya ya sauke glass ɗinsa yace "ina zaku" Zahra zata yi magana Leena ta riga ta tace "thank you, Muna jiran wani" kallon Leena yake ba kiftawa sai kuma yaja motar sa yayi gaba. A layin gidan abincin Chef Siyama taxi ya tsaya suka sauka suna kallon layin to figure out gidan nata opposite ɗin inda suka sauka su ka ga maza guda Uku kuma duk kallon Leena suke yi suna magana Zahra tace "Ke Leena kin san waɗannan mazan ne? Leena tace "dan Allah ki dena kallon su Zahra" dube duben gidan suka yi Zahra tace "karshe fa Leena sai mun tambaye mazan nan fah" Leena taja ta tsaya tace "sai dai ke ki tambaye su amma Ni ba zan tambaye su ba" Zahra ta karasa kusa da su tayi sallama suka amsa mata tace "Gidan abincin Chef Siyama muke nema Please" dayan yace ai next street ne ba wannan ba" sai sannan dayan yayi saurin cewa "Dan Allah wancan ƴar uwan ki ce" tace "Eh" yace "basu kama da wannan Malik ɗin" sai sannan Zahra ta kalle sa, ta sake baki with shock written all over her face, kallon sa take babu kiftawa da badan wannan na miji bane kuma dan babba bane zata iya rantse wa identical twin ɗin Leena ne, his eyebrows, lips ɗinsa, yadda idon sa yake, da yadda yake starring one place sak irin na Leena, bakin ta na shaking tace "Wallahi Allah kamar identical twin ɗin ta" sai sannan Malik ya ɗaga kai yana kallon Zahra......
[5/28, 7:39 PM] Jiddatulkhayr writes: *AGOLA (Behind the palace walls)*
17.........
Zahra bata taɓa shiga ruɗani irin na yau ba, ganin kallon da Malik ke mata yasa bakin ta na rawa tace "Ina wuni" ɗauke kansa yayi daga kallon ta kuma be amsa mata ba juyawa tayi ta koma inda Leena ke jiran ta, Leena tace "kinje kin sake musu fuska kuna magana, kawai ki tambaye abu shine zaki daɗe?" Zahra ta rike hannun Leena tace "Dan Allah kizo mu karasa wajan su kiga abin da yasa na ruɗe" Leena ta kwace hannun ta da karfi tace "Dan Allah muyi abinda ya kawo mu" Zahra tace "gidan na next line ne, Dan Allah Leena kizo muje ki gansa" Leena taja baya ta tsaya tana kallon ta da mamaki sai kuma ta kama tafiya Zahra ta bita tace "wani me kama da ke na gani" Leena ta harare ta Zahra tace "Wallahi Leena He's the spitting image of you" Leena ta tsaya tana kallon ta hangaga sai kuma tace "You must be joking, Allah ma ya sauwake" Zahra tace "toh kin gansa ne kike cewa hakan? Toh barin faɗa Miki in ba sai dana ruɗe ba, kin san Allah? Like two peas in a pod" Leena tayi dariya tace "A'a ki ma ce 1 pea muke" Zahra tace "Allah ya haɗa ku wata rana zaki yarda da abinda nake faɗa Miki" suna shiga next line suka hango signboard ɗin a kofar gidan abincin Chef Siyama suka shiga cikin babban gidan suka same ta tana koyawa student ɗinta abinci, tana kallon su ta basu kujera suka zauna bayan sun gaishe ta Leena ta mika mata list ɗin hannunta tace "Ammi na ta kira ki wayan ki akashe, wannan list ɗin ordern da tayi na gobe" Chef Siyama tace"Oh Okay, kar de ke ƴar sirbajo ce? Yanzu muka yi waya" Leena na Murmushi ta gyaɗa kai tace "ikon Allah, gashi ke ɗinma Ma shaa Allah sai dai baki kama da Ammin naki, ita ana ganin ta zaka gane buzuwace" Wata budurwa da tun shigowan Leena take kallon ta tace "Dan Allah amma ke kanwar Uncle Malik ne?" Leena ta