x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 12 - AGOLA Behind the palace walls

  • 33001 words
  • 36000 words
  • Out of 196927 words

Category: Love Stories

Views 532

22 Aug 2025
Start ads
After Image Ads
Ammi tace "ina kika je?" tace "Uncle sadeeq ne ya kawomin wannan saboda exams Dina" Ammi tace "kun sake waya da Muhammad din ne?" ta sunkuyar da kanta tana wasa da fingers dinta ta gyada mata kai Ammi tace "zuwan nasa yana nan?" Nan ma ta gyada kai Ammi tace "toh Allah kawo sa lafiya?" daga haka ta wuce ciki abin ta. Washe gari, tunda Leena ta tashi taji jikin ta amace ta rasa me yake mata dadi. Bayan sun gama breakfast taga Ammin ta tana ordern snacks Ammi na gama waya tace "Ammi snacks name kuma?" Ammi tace "ma bakon ki mana" Leena ta Turo baki bata kara cewa komai ba Ammi tace "kin ma kira sa kinji ko ya zuwan nasa?" ta girgiza kai tace "Amma dai jiya yace min karfe biyu ne Flight ɗin nasu zai tashi" Ammi tace "Allah kawo sa lafiya toh" Leena tace "Ammi Ni wallahi bana son yazo, kawai ace nine wanda wani zai fara zuwa wajen ta a gidan nan, ki kalla ko Niswa fah bata fara kawo wani ba" Ammi ta sake baki tana kallon ta sai kuma tace "Toh ke ina ruwan ki da Niswa? Ina anan uwarta ta saki a gaba? Baki da sakat a cikin gidan nan, ko fa friends dinki ne basu isa su zo nan gidan nan ba, dama Fata na kenan Leena ki fita ki bar mata gidan ba shikenan" Leena de hankalin ta be kwanta ba. Da yamma wajajen karfe huɗu Muhammad ya kira Leena a waya kamar zata yi kuka tayi picking call ɗinsa yace "Baby gamu a baki gate ɗin naku" tace "toh ku shigo, Ayaan zai karaso gate ɗin sai ya karaso da ku part ɗin namu" yace "toh" Leena ta ta fito ta karasa ɗakin Ammi tace "Ammi wai gashi a bakin gate" Ammi tace "toh kice su shigo mana" tace "na faɗa musu" tace "Ayaan zo" ya karasa inda take yana kallon ta tace "jeka bakin gate zaka shigo da wasu Uncles ko? Karfa ka tsaya shirme" ya gyada mata kai, ya karasa gate ya same su suna gaisawa da masu gadi, Muhammad na akallon Ayaan yace "Little boy" Ayaan na dariya ya mika masa hannu Ayaan ya karasa da su har parlorn su yana musu shirme, da sallama suka shiga parlorn wanda banda kamshi ba abinda yake yi Ayaan ya wuce ɗakin Leena yace "Addah suna parlorn" Leena sai da ta tsaya tayi ta addu'a sannan ta samu strength ɗin fitowa, kanta a kasa ta karasa cikin parlorn ta ɗan zauna nesa da su sannan ta gaishe su, Abokin sa ne kaɗai ya amsa banda Muhammad hakan yasa ta daga kai ta lalle sa sai kuma taga kallon ta yake da murmushi shinfiɗe a fuskar sa ta sauke idon ta kasa, tashi tayi ta wuce kitchen ta kawo musu abinci da aka girma musu, da snacks ɗin da Ammi ta musu order takai musu parlorn ta sake komawa kitchen ta ɗauko musu da drinks da ruwa, sai ta zauna tana kallon wani direction taji yace "ya exams ɗin? Hope basu wahalar min da ke" murmushi kawai tayi ta gyaɗa masa sai kuma tace "ku ci abinci" Muhammad yace "sai da muka ci a hotel ɗin da muka sauka kafin muka zo nan" tace "wannan da wancan ba iri daya bane" tana kallon Abokin sa tace "kai kam kaci dan Allah" murmushi kawai ya mata, Muhammad yace "kima Ammi magana zamu gaishe ta" tashi tayi ta wuce dakin Ammi ta faɗa mata sai da Leena ta fito sannan Ammi ta fito suna gaishe ta ta wuce ciki abin ta yace "Daddyn ku fah?" tace "me zaka masa?" yace "Oh baki so na gaishe sa kenan ko". Daddy daya zo da mota yana son shiga ciki da shi yaga anyi parking mota a bakin gate ba ta yadda zaiyi ya shiga da nasa hakan yasa ya hakura yayi parking a waje kawai ya shiga, ganin bakin a sashen Ammi ne kawai ya wuce ɗakin sa, Rayyan ma da ya dawo shima kawai sai yayi parking a waje ganin harda motar Daddy a parke. Bayan su Muhammad sunce zasu tafi Leena ta tafi kitchen tayi packaging snacks ɗin ta fito musu da shi Muhammad na rike da hannun Ayaan suka fito yayi daidai da fitowan Daddy a part ɗinsa Leena tayi sauri ta sauke kanta kasa Ayaan ya kwace hannun sa acikin na Muhammad ya tafi da gudu yana kira Daddy, Daddy na dariya ya sunkuya Ayaan yana zuwa Daddy ya daga sa sama yana masa wasa Muhammad ya juya yana kallon Leena yace "Daddyn mu ne ko?" Kai kawai ta gyaɗa masa shi da abokin sa suka karasa inda Daddy yake, Daddy ganin sun karasa yasa ya tsaya da wasan da yake ma Ayaan, Leena ganin sun nufi Daddy yasa da sauri ta juya ta koma ciki. Daddy yace toh mu karasa ciki mana ba musu suka bisa, suka sake gaishe da Daddy kansu a kasa, Muhammad ya taba abokin sa, sannan abokin nasa yana sosa keya yace "Um dama..dama." Daddy yace "Look! Just go straight to the point, Karka damu, ajiye wannan kunyan a gefe, bani da masala" ya karasa maganan in funny tongue, Abokin Muhammad yace "Daman yazo ne neman izini, sannan wai yana son kuma zai Turo magabatan sa" Daddy yayi murmushi yace "it's Okay, but I would love to know more about you, before then" in briefly yama Daddy bayanin komai game da shi, Daddy yace "it's okay, Allah yayi jagora, duk lokacin da kuka shirya sai ka fada ma yarinyar ta sanar mana" suna tayi wa Daddy godiya, suna fita suka kusan cin karo da Mummy dake kokarin shiga Rayyan yana biye a bayan ta, ja baya tayi suka gaishe ta ta amsa musu suka gaisa da Rayyan sannan suka fita...

Kar a manta ayi following ɗina, sannan a danna min star please...
*AGOLA (Behind the palace walls)*🫧


14....
Muhammad ya kira Leena a waya yace "ki fito muyi sallama dear" tace "Um, bakomai ai" yace "C'mon baby, taya zan tafi without saying Adios" kamar zata yi kuka tace "I'm coming toh" Dama tunda ta ga sun nufi wajan Daddy tana komawa ciki ɗakin ta ta wuce ko hijab ɗin jikin ta takasa cirewa ga kuma bugun da zuciyan ta ya keyi, suna gama waya ta tashi duk jikin ta ba karfi ta fito tana tafiya a hanaki kanta a kasa har ta karasa bakin gate ta gaida masu gadi ya buɗe mata kofar ta fita taga abokin sa na gaban motar Muhammad ne kaɗai ke tsaye a jikin motan ta karasa inda yake tsaye kanta a kasa tace "Gani" yana murmushi yace "wai duk wannan kunya ne Leena?, ko fa kallo na biki yi ba" bata ce masa komai ba sai wasa ma da take yi da yatsun yace "shikenan tunda ma ba zaki kalle Ni ba, I love you, but you don't feel the same. Is this an unrequited love, Leena?" kai kawai ta girgiza masa yace "well" daga haka ya buɗe booth ɗinsa ya ciro siyayyan da ya mata yana kallon ta yace "Baby zaki iya ɗauka kuwa?" ta kalle sa sai kuma ta kalli manyan Ledojin hannun sa tace "Na mene?" yace "Is a little something I got for you, baby" ta girgiza masa kai, ita ta kagu ta koma ciki saboda she's uncomfortable yace "Why are you acting like this?" Bata ce komai ba ya wuce ta yayi Sallama Mai gadi ganin sa  yasa ya taso ya karaso da sauri Muhammad ya mika masa Ledan hannayen sa yace "Dan Allah kaɗan karasa da su part ɗin su Leena" ya karɓa yace "Toh Alhaji" dama da zai fita sai da ya musu kyauta, ya koma yana kallon Leena yace "it's Okay, baby, thank you" ta ɗan kalle sa sai kuma ta sauke idon ta kasa tace "Thank you and I wish you safe trip" yace "thank you, Baby" daga haka ta wuce ciki tun kafin ta karasa taga Mummy ta sayar da mai gadi tana masa magana hakan yasa Leena bata yi attempting mata magana ba tayi wucewar ta, a bakin kofar parlorn ta samu ya ajiye kayan. Mummy tace "kana nufin dama ba bakin Alhaji ba ne?" yace "Toh gaskiya Hajiya bana ce ba, amma sun fara zuwa kafin ya zo" tace "kayan da ka shigar kuma fah?" yace "Eh shi mutumin ne yace na kaima Leena ciki" Mummy ta gyada kai sannan ta wuce bangaren ta. Da Daddare Leena na ɗakin Ammi Ayaan na game da wayan ta Ammi na mata wani kallo tace "toh yanzu da kika zo kika sani gaba me kike nufi?" tace "Ammi nifa bakomai nake nufi ba, kawai dai naga I'm still young, kuma na tambaye sa me yayi discussing da Daddy yaki faɗa min" Ammi tace "Toh akan me ze faɗa Miki? Ai gani yayi wasa kike son masa da hankali, kiga yadda matan nan tasan yadda tayi, tayi convincing Daddy haka kina gani duk sonki da international ya chanza Miki makaranta, amma ba zaki wa kanki fatan Alheri ba" Leena ta mike kamar zata yi kuka Ammi tace "Oho, ke kika sani kuma bari Daddyn naku ya shigo zanji yadda suka yi inhar da gaske yake wallahi sai dai kice ba zaki min biyayya ba" Leena ta fice a dakin ta wuce nata. Mummy na ta zaune tana jiran Daddy dake wanka, duk da ya shiga girkin Ammi amma haka ta sare ta kasa bayan ya gama shiryawa ya fito yana kallonta yace "Lafiya kuwa?" tace "kalau, kawai dai tambayar ka zanyi" ya zauna yace "Menene kuma?" tace "Dama bakin da kayi ɗazu ne nace Allah sa lafiya" yace "Lafiya sai Alkhairi ma" tace "toh ai nagan su matasa ne, and kaman nasan ɗayan, na ɗauka ai abokanan Rayyan ne sai naga basu ma san juna ba" yace "well, manemin Leena ne" wani zabura tayi da kyar ta'iya daidai ta kanta tana kallon sa tayi faking murmushi tace "Aure zaku ma Leenan kenan, ikon Allah naga ai yarinya ce ga yayun ta ma ba suyi ba, sai ita?" Daddy yace "that doesn't matter, kowa da lokacin sa, kuma ai idan har yarinyar da mahaifiyar ta basu son auren yanzu da ba zasu bari yazo nan gidan ba har ya nemi ya gana dani, so as her father zan mata abinda take so, period" wani shaking taji take yi ga zufa da suka fara zarya a jikin ta Daddy na kallon ta yace "Idan babu wani abu ina so zan wuce" ta tashi tana murmushi suka fita tare ya karasa sashen Ammi. Har Mummy ta koma ɗakin ta wani ɓari jikin ta yake yi, Leena ta fara aure? Ƴar da take fatan har ta mutu karta samu wanda zaice yana son ta, tafi son ta karasa rayuwn ta a haka. Wannan daren bacci ya kauracewa Mummy. Bayan Daddy ya dawo a sallahn Asuba Ammi na kallon sa tace "Baka ce min komai ba game da maganar wannan yaron?" yace "Oh well, I thought ai ya sanar da ku" tace "No" yace "Okay, wai dama izni yazo nema sannan yana son a basa daman zai Turo" Ammi tace "Toh me kace masa, dear?" yace "Tambayar sa nayi yayi min bayanin kansa, so yanzu nake son amin bincike akan sa, idan na gari ne fine, sai ya Turo su ɗin" Ammi ta gyaɗa kai tace "hakan yayi, Allah ya tabbatar mana da Alkhairi" yace "Amin". Ammi ta leka ɗakin Leena taga har yanzu tana kwance tace "wato breakfast ɗinma ba zaki fito kiyi ba ko? Kuma kinsan yau ma kina da paper ko?" Leena tace "kai Ammi jiya fa banyi bacci bane kuma papern mu sai karfe 2pm ne zuwa 9am naso tashi" Ammi tace "wato saboda maganar da na miki ne jiya ko?" Sai sannan ta tashi tana kallon Ammi tace "wallahi Ammi Ni karatu na kwana yi, amma ba wai naki bacci bane haka kawai" daga haka Ammi ta bar bakin kofar Leena ta tashi shiga toilet tayi brush sannan ta fito parlor, tana gama breakfast Leena ta wuce part ɗin Hajiya tana zuwa ta samu Mummy ma ta fito kenan Leena ta sauke kanta kasa tace "Ina kwana Mummy" Mummy ta share ta tayi kamar bata ji ba sai kuma ta rike baki tace "Eh lalle Leena, wato har zaki iya zuwa ki shige Ni dan rashin kunya ba zaki gaishe Ni ba, wato uwar ki ne ta hana ki" Leena ta buɗe baki tana kallon ta, dan zata iya cewa tunda take bata taɓa gaishe ta ta amsa ba kuma hakan baya sa taki gaishe ta ko da zata ki Ammi ba zata barta ba, Mummy tace "tabbas dole ki gwada min kin girma, ba kinga kin kamo Ni a tsayi ba? Kina sa duk wani abu da nake sawa, yanzu kuma aure kike so ba, dole ki ga mun zama daya mana" Leena that was totally speechless bata san sanda ta buɗe baki ba, wanke ta da mari Mummy tayi tace "wato saboda ni mahaukaciya ce ko kuma makaryaciya shine har zanyi magana ki wangale min baki saboda ga ƴar iska "Leena ta riƙe kuncin ta tana sauraron ta, ta daka mata tsawa tace "ki ɓace min Shegiya" Leena ta karasa ɗakin Hajiya da sallama a bakin ta tana rike kukan da taji ya zo mata dan karta fashe da kuka, Hajiya ta fito a kitchen tana kallon Leena tace "Yanzu kuma me ya haɗa ki da wancan matar take ta zuɓa mana ihu a gida?" Leena tace "Ba a bin da na mata" Hajiya tace "Allah zai saka Miki" sai kuma ta washe baki tace "ke da zaki bar mata gidan ma, ɗazu Baban ku daya shigo nan yake faɗa min wai na taya ki da addu'a, kuma wai a Habuja yake ko?" Leena na kallon wani wajan ta ɓata fuska Hajiya tayi kasa da murya tace "Gaskiya Khadijan nan munafuka ce, kila fah shigowa nan da tayi ko so take taji nace wani abu akai sai kuma taji nayi shiru, toh kema Leena ki fita harkan ta kawai kinsan ba zata so ki riga ƴarta aure ba" Leena ta mike Hajiya ta sake baki tana kallon ta tace "kai ƴar nan akwai ki da abun haushi, Khadija ne kawai daidan ki a gidan nan" Leena tace "sai anjima Hajiya, ina da exams ma anjima" Hajiya tace "ba dan halin ki ba Allah bada sa'a" Leena ta wuce sashin su tana shiga taga Ammi na parlor tana kallo, Leena ta karasa ciki sannan ta fara hawaye, Ammi na kallon ta tace "ke kuma Lafiya?" Leena tace "Ba Mummyy bane, ba abinda na mata shine ta mare Ni" Ammi tace "Toh me na gaya min? naje na rama Miki ko me? Ai kinji, kin gani zaki iya cigaba da zama haka a gidan nan da ita, so it's Okay" Leena ta wuce ɗakin ta kawai. Sha biyu saura Zahra tayi sallama"Ammi dake jera kuloli a dinning tazo ta buɗe mata kofa ta gaida Mummy, Mummy ta amsa da fara'a tace "ki shiga tana ciki" Zahra ta karasa ta samu Leena na waya ganin ta yasa tace "yanzu zamu tafi, I'll get back to you when I'm back" suka gaisa sai sannan ta ɗauki jakkan ta suka ma Ammi sallama suka fita, driver da zai fita zaije ɗauko Nisreen dake yanzu Leena ta wuce ta a aji yasa ita bata WAEC ɗin, Leena ta ɗaga masa hannu har suka karasa tace "zaka fita ne Yaya" yace "Eh zanje ɗauko Nisreen ne" tace "wai da zaka kaimu ne amma shikenan kaje" yace "toh ku shiga mana tunda har sai na wuce makarantar su Nisreen ɗin idan yaso dan kar tayi ta zama zan fara biya ta chan inna ɗauke ta sai na karasa da ku" Leena tayi godiya suka shiga ita da Zahra. A daidai bakin gate ɗin su Nisreen yayi parking, fitowar Nisreen daga cikin school ɗin kenan tana hango sa ta karasa jikin motar ta ɓude back seat to her surprise taga Leena and her friend taja wani dogon tsaki sannan ta buga kofar, ta ɗayan site ɗin ta buɗe front seat ta shiga ko gaida drivern bata yi ba, driver kam yaja mota ya kama hanyar makarantar su Leena, Nisreen tace "Wait, wai ina zaka kaini ne Malam?" yace "Hajiya zan sauke su ne a makarantar su, inajin jarabawar tasu karfe biyu ne" wani dogon tsaki Nisreen taja tace "ai wannan wulakanci ne, taya Zaka ɗauki ni ka kama yawo dani a cikin gari? Sai kace banda wani abin yi a gidan?" Leena ta kalli Zahra, driver yace "kinyi hakuri naga idan na fara kai su kafin na zo ɗaukan ki zaki daɗe a waje ne shiyasa nayi wannan dabara, amma kiyi hakuri" tace "Dalla kamin shiru, taya Zaka ɗauko Agola ina ƴar mai gidan ka mayar dani bakomai ba, irin haka da kuke yi ne yasa take jin kanta, who is she even da har zata na shiga Mota ana tuka ta?" Zahra tace "Oops! Do you want to know her? Well, go to any website and just type her name. You'll know her better, okay?" Nisreen ta juyo a tsawace tace "Who the hell do you think you are? Dake nake magana da zaki tsoma min baki a ciki?" Leena ta rike hannun Zahra tace "Please don't say anything" Zahra ta kwace hannun ta tana kallon Nisreen da ta juyo itama cikin tsawa tace "Don't think I'm Leena and that I'll mute for you. I'm Fatima Zahra, and we're two different people, wallahi cin uwarki zanyi kuma na kwana lafiya, idiot" ta karasa maganar tana hararan Leena da take cewa tayi shiru, Nisreen ta ɗanji tsoro ganin yadda Zahra ta hayyako mata ta buɗe baki tace "Enough, tho" Zahra tace "better!! Suit yourself" Nisreen tace "ƴar talakawa kawai, daman haka kuke" Zahra tayi dariya me isarta tace "A haka kuma Leena ta zama muku karfen wiya, Ni kuma wallahi baki isa kiyi da Ni ba, idan har kin isa kibari mu samu waje na gwada Miki Ni ba sa'ar ki ba
End Ads