x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 4 - HIKAYOYIN ALAJABI Book 1

  • 9001 words
  • 11023 words
  • Out of 11023 words

Category: Adventure Stories

Views 67

01 Aug 2025
Start ads
After Image Ads
nan fa
hankalinsa ya dugunzuma kuma ya
kamu da tsananin mamaki gami da
fushi, saboda wannan ne karo na farko
a rayuwarsa daya jarabawa yin wani
abu ya kasa.
Mu haxu a cikin littafi na biyu
daga Abdul’aziz Sani Madakin Gini.

84

HIKAYOYIN AL’AJABI



MADAKI

RAI DA SO

hankali kamar maciji wata baqar
mota ta sulalo ta samu matsuguni
a harabar farfajiyar asibitin, bayan
ta samu matsuguni tsayin wasu mintina kafin
qofar motar ta buxe a hankali, wani matashi xan
kwalisa ya sako qafafunsa waje kafin a hankali
shima ya qarasa fitowa.
Fuskarsa tana sanye da wani baqin
tabarau wanda ya taimaka wajen voye damuwar
dake shimfixe akan fuskarsa.
Kai tsaye ya wuce cikin asibitin, bai
tsaya a ko ina ba sai qofar ofishin likita, ya tura
haxi da sallama ya shiga.
Wani dogo siriri kamar takanxa ya xago
ya dube shi da motsatsiyar fuskarsa kamar an
taka tunfafiya, ganin shigar Bashir ya saka
bakinsa ya qara washe wa zuwa murmushi, kafin
ya amsa sallamar da ya yi tare da miqa masa
hannu suka gaisa cike da shauqin ganinsa.
“Kamar kasan kai nake zaman jira” Ya
faxa masa har lokacin hannun Bashir yana cikin
nasa.
85

HIKAYOYIN AL’AJABI
MADAKI
“Cinkoson ababen hawa ne ya hanani
qarasowa akan lokaci” Ya faxa yana zama.
Likitan ya gyaxa kai kamar qadangare
sannan ya jawo wata takarda yana dubawa bayan
wasu sakani ya xago qwayar idanunsa ya dubi
Bashir yana xan yamutsa fuska, kamar ba zai yi
magana ba.
“Har yanzu dai abinda muke son samu
bamu same shi ba” Ya xan yi shiru yana kallon
fuskar Bashir sannan ya miqa siraran ‘yan yatsun
hannunsa ya xauko biro yana juya shi a tsakanin
tsintsiyar hannunsa sannan ya ci gaba da magana.
“Yanzu ma kamar ko wane lokaci zan ci
gaba da faxa maka cewar, yana da kyau ka
sakawa zuciyarka dangana duk abinda Allah ya
qaddara zai faru ya riga ya faru, ita mutuwa xaya
ce kuma wanda ya mutu ba zai tava dawowa ba”
Bashir ya xago a hankali ya dubi likitan sannan
ya kauda kai zuwa gefe, idan da sabo wannan ba
shi ne karo na farko da wannan motsatsen likitan
ya ke faxa ma sa waxannan kalaman ba.
“Likita ba zan iya cire son Zainab daga
cikin raina ba” Ya faxa a taqaice, bayan xan
shiru ya ci gaba da magana cikin kwantar da
murya.
86

HIKAYOYIN AL’AJABI
MADAKI
“Bana iya barci sai na kuna kaset xin
bikin mu na kalla, haka nan dana tashi daga barci
bama samun nutsuwa sai na xauko kundin
hotunanta na kalla, sau nawa zan faxa maka ba
zan tava iya daina tunaninta ba” Dogon likitan
ya saukar da ajiyar zuciya.
“Nima ba cewa na yi ka daina tunaninta
ba, amman ka dubi irin halin daka shiga a
rashinta, wannan ciwon naka dole sai ka daina
sakawa ranka damuwa sannan za mu samu
nasara akan samun lafiyarka” Bashir ya yi
murmushi.
“Ba zan tava daina tunanin matata
zainab ba”. Ya faxa yana xan buga tebur xin da
xan yatsansa.
“Ni kaina nasan abu xaya ne zai saka na
daina damuwa” Ya kalli idon likitan shima ya
qura masa ido.
“Mene shi?” Likitan ya tambaya jin
shirun yana neman yin yawa.
“Idan zaka iya bani maganin da zai dawo
min da Zainab a raye” Cikin tsananin kaxuwa
likitan ya dube shi baki buxe.

87

HIKAYOYIN AL’AJABI
MADAKI
Cike da damuwa Bashir ya baro wajen
likitan ya na tafiya akan titi duk qwaqwalwarsa
ta cika da tunani kala-kala shi kansa yasan tuqin
kawai yake yi amman rabin hankalinsa baya kan
titin. A haka ya zo daidai hanyar da zata kai shi
unguwar Briged don haka sai ya saka sigina ya
shiga daidai kwanar ‘yan kaji Mariya dake tafe
hankalinta a tsananin tashe tafiya kawai take yi
sam bata san wajen da take saka qafarta ba har ta
hau tsakiyar titi sam bata sani ba.
Kamar daga sama Bashir yaga ta faxo
tsakiyar titi, cikin tsananin razana yaja wani birki
amman duk da haka sai daya xan tava ta, Mariya
ta xago kai ta dube shi, shima yana daga cikin
motar ya dubeta.
Kallon xaya daya yi mata yasan tana
cikin tsananin tashin hankali, bata kuma bi ta
kanshi ba sai ta yi gaba abinta.
Bashir ya bita da kallo cike da mamaki,
ko ita kuma me yake damunta? Yasan dai banza
bata kai zomo kasuwa, da ganinta tana cikin
tashin hankali.
Bai kuma bi ta kanta ba ya sakawa motar
giya ya soma tafiya yana yiwa Allah godiya da
bai qaddara tsautsayin a kan shi yake ba. A haka
88

HIKAYOYIN AL’AJABI
MADAKI
har ya qaraso inda ya nufa wajen malaminsa da
yake ba shi taimako game da harkokin
kasuwancin sa.
A shagonsa ya same shi malam Yusuf
matashin gardine xan kimanin shekara talatin,
tun sanda matar Bashir ta rasu yake qoqari
wajen yi masa rubutu yana ba shi duk a cikin
qoqarin ganin ya mance da marigarya.
Amman duk da wannan qoqarin da yake
yi sam babu wani ci gaba, domin kullum ta Allah
akwai wani abu na daban da Bashir xin yake
zuwar masa da shi.
A lokacin da Bashir xin ya qarasa qofar
shagon ya samu waje ya yi fakin xin motar ya yi
shiru yana kallon qofar shiga cikin shagon nan
take wani tunani ya ziyarci zuciyarsa.
Wata rana sun tava zuwa wajen malam
Yusuf da Zainab saboda matsala aljanu da suke
damunta tana yawan fama da wasu munanan
mafarke-mafarke harma ta riqa zabura a cikin
barci, sai kuma wani tsananin ciwon kai mara
sauka daya adabeta.

89

HIKAYOYIN AL’AJABI
MADAKI
Hakan ya saka ya xaukota takanas ta
kano ya kawota wajensa, lokacin da suka zo
layin sai ta dubeshi cikin damuwa.
“Ni bana son unguwar nan”
Bashir ya dubeta da murmushi.
“Me yasa?” Ta xan kalli gefe.
“Shi kenan dai”.
“Da kin faxi abinda yake ranki dai”.
“Ni dai kawai mu koma gida, kaina ya
daina ciwon” Suka qarasa cikin layin ya tsaya a
qofar shiga shagon.
“Sai da muka zo sannan za ki ce kin fasa,
ki daure dai mu shiga kawai addu’a zai yi miki
shi kenan” Zainab ta yi murmushi.
“Mijina kenan, ai tunda na faxa maka ba
zan shiga ba kasan ba zan tava shiga ba” Bashir
ya xan yi shiru na taqin lokaci sannan ya ce mata.
“To bari na shiga wajensa na fito”.
“Dama hakan ya fi maka, ni dai ina nan
zaune ina jiranka idan kuma ka daxe zaka dawo
ka samu bana nan” Cikin sauri ya buxe motar ya
fita.
Ko daya shiga wajen malam Yusuf sai
ya same shi a zaune yana zane-zane akan rairayi,

90

HIKAYOYIN AL’AJABI
MADAKI
bayan sun gaisa sai ya dube shi ya yi murmushi
tare da faxin.
“Ina uwar gidan kuma?” Bashir ya dube
shi cike da mamaki domin bai faxa masa cewar
za su zo ba, ganin ya na yi masa kallon mamaki
sai ya qara cewa da shi.
“Ko ba kwana tayi tana ciwon kai ba?”
Cikin sanyi jiki Bashir ya ba shi amsa.
“Haka ne”.
Sai ya qara yin murmushi ya ci gaba da
zane-zanen shi sannan ya qara cewa da shi.
“Yanzu ma da kuka zo ai cewa tayi
dakai ba zata shigo nan ba, daman ai ba za su
barta ta shigo ba” Bashir ya dube shi cikin
kaxuwa.
“Saboda me?”
“Aljanun ne suka hanata…”
Bashir ya saukar da ajiyar zuciya, bayan
ya dawo daga duniyar tunanin daya shiga sannan
a hankali ya buxe qofar motar ya zuro qafafunsa
waje, ya jima a zaune qafarsa a qasa kafin ya fito
daga cikin motar.
Ya nufi qofar shiga cikin shagon yana
zuwa ya qwanqwasa tare da yin sallama, daga
91

HIKAYOYIN AL’AJABI
MADAKI
cikin shagon aka amsa masa tare da bashi izinin
shiga cikin shagon, Bashir ya shiga tare da qara
yin sallama ya samu Malam Yusuf a zaune akan
wani buzu yana jan carbi.
Ya miqa masa hannu suka gaisa fuskarsa
cike da fara’a ya samu waje ya zauna, malam
Yusuf ya qarasa janye sauran ‘ya ‘yan carbin da
suka rage sannan ya ajiye carbin.
“Malam Bashir ya qarin haquri?”
“Haquri sai ma’aiki”.
“Allah ya ji qansa”.
“Allahuma amin” Suka yi shiru na taqin
lokaci.
“Ya kasuwar taka kuma?” Bashir ya
gyara zama.
“Kasuwa mun gode Allah, harkoki suna
tafiya yadda ake so” Malam Yusuf ya jinjina kai.
“Haka ake so” Ya xan yi shiru sannan ya
kuma xauko carbinsa yana xan juyawa a
hannunsa sannan ya ci gaba da magana.
“Kana dai shan rubutun nan da nake
bayarwa a kawo maka?” Bashir ya gyaxa kai.
“Eh ina sha amman har yanzu ban daina
ganin zainab ba, har yanzu duk lokacin dana
shiga falon mu sai naganta a zaune tana yi mun
92

HIKAYOYIN AL’AJABI
MADAKI
murmushi, haka ma idan na shiga wanka sai ta
zo ta tayani, hakan nan tana zuwa ta tayani
kwana” Malam Yusuf ya yi shiru kawai yana
kallonsa cike da mamaki.
“Duka marigayar kake gani tana yi maka
waxannan abubuwan?”
“Eh”
Malam Yusuf ya yi murmushi, tare da
dafa hannun Bashir.
“Bashir wanda ya mutu ai ya riga ya
mutu baya tava dawowa”.
“Nasan da haka, amman wallahi Zainab
nake gani”.
Malam Yusuf ya kalle shi cikin
tausayawa, sannan cikin kwantar da murya ya ce
masa.
“Bashir kana yin addu’o’in dana baka
kuwa?”.
“Wane kenan?” Shima ya mayar masa
da tambayar.
“Wacce da wacce na baka ma tukuna?”.
“Dana kwanciya barci dana tashi daga
barci dana fita daga gida dana shiga abin hawa
dana saka kaya da…” Ya xaga masa hannu.

93

HIKAYOYIN AL’AJABI
MADAKI
“Ya isa haka” Ya faxa yana sauke wani
numfashi.
“Amman kuma duk da haka baka daina
gane-ganen marigaya ba?”
“Shakka-babu” Malam Yusuf ya miqa
hannu ya jawo wani allo dake xauke da rairayi
ya xan soma zane-zane zuwa wani xan sakani
sannan ya furza da wani huci ya xago kai ya
dubi Bashir.
“Kafin ka zo nan kun haxu da wata?”
Bashir ya dubeshi cikin mamaki.
“Ban haxu da wata mace ba”.
Malam Yusuf ya yi murmushi, tare da ci
gaba da zane-zanensa yana yin murmushi ya
qara cewa da shi.
“Tuna dai tabbas kun haxu da wata,
kamar tana cikin tashin hankali…” Bashir ya
katse masa magana cikin sauri.
“Eh na kusa buge wata da mota, ga
alama tana cikin tashin hankali”.
Malam Yusuf ya dakata da dubansa.
“Wannan ita ce maganin matsalar ka, ita
zata saka mancewa da marigarya, sai dai
matsalar xaya” Ya xago cikin jimami yana

94

HIKAYOYIN AL’AJABI
MADAKI
kallon fuskar Bashir sannan ya ci gaba da
magana.
“Ta yi aure-aure har guda huxu”.
“Huxu!” Cikin ruxani Bashir ya tambaya.
“Eh” Ya tsuke fuska kamar an matse
lemon tsami.
“Bashir an camfata da cewar farar qafa
gareta”.
“Mene kuma farar qafa?” Ya tambaya
cike da damuwa.
Ya xan yi murmushin gefen fuska “Baka
san abinda ake nufi da cewar mace tana da farar
qafa ba?” Ya xauki carbinsa yaci gaba da ja.
“Idan aka ce mace tana da farar qafa
ma’ana duk wanda ta aura duk yawan dukiyarsa
sai ya tsiyace ya koma kamar veran masalaci”.
Cike da damuwa Bashir ya dube shi.
“Malam mene maganin faruwar hakan?”
“Abu xaya ne zai hana faruwar hakan,
ace ka koma cikin mahaifiyarka”.
Bashir ya yi mutuwar tsaye.
Kadan kenan daga cikin littafi me suna

RAI DA SO

NEMI NAKA A KASUWA
95

HIKAYOYIN AL’AJABI

MADAKI

Domin neman qarin bayani
tuntuvi lambar waya 09050063882

96


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels
End Ads