x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 3 - HIKAYOYIN ALAJABI Book 1

  • 6001 words
  • 9000 words
  • Out of 11023 words

Category: Adventure Stories

Views 64

01 Aug 2025
Start ads
After Image Ads
Boka Aulad yaga
sarkin yaqi ya sha gabansa cikin fushi
Boka Aulad ya dube shi yace “Wane
irin shirme ne haka zaka zo kasha
gabana alhalin kasan cewa sarki baya
son na gusa daga kusa da shi daidai
da tsawon rabin sa’a”.
Koda jin haka sai sarkin yaqi
ya yi xan guntun murmushi yace.
“Ai wannan da ne, yanzu nan
sarki ya bani umarnin cewa kada na
sake barin kowa ya je inda yake, koda
kuwa kai ne”.
Koda jin haka sai ran Boka
Aulad ya vaci ainun ya dakawa sarkin
yaqi tsawa yace “Wai shin ni kakan ka

55

HIKAYOYIN AL’AJABI

MADAKI

ne har da zaka zo mini da maganar
wasa”.
Da jin haka sai sarkin yaqi ya
turvune fuskarsa yace “Na tava yi
maka wasa ne? ko kuwa zan yi wa
sarki qarya ne saboda kawai biyan
wata buqata tawa? Inda sarki bai
sauya ra’ayinsa ba ai babu yadda za a
yi ya tafi ya barka. Ni ina ganin sarki
yana zarginka da wani laifi don haka
kasan hanyar da zaka bi ka gyara
tsakaninka da shi”.
Koda sarkin yaqi ya zo nan a
zancensa sai hankali Boka Aulad ya
dugunzuma ainun fiye da koyaushe ya
dubi sarkin yaqi cikin alamun matuqar
damuwa yace.
“Dole ne naga sarki yanzu
domin na hana shi Tarawa da wannan
amaryar tasa domin kuwa akwai
babbar matsala, abin da nake so da

56

HIKAYOYIN AL’AJABI

MADAKI

kai shi ne ka yi min jagora izuwa ga
sarki yanzu nan kafin lokaci ya qure”.
Sarkin yaqi ya girgiza kai yace.
“Ba zan iya ba, domin ni ma
idan na kaika gare shi zan iya rasa
matsayina gaba xaya”.
Koda jin haka sai Boka Aulad
ya dakawa sarkin yaqi tsawa, a karo
na biyu yace.
‘Shin ka manta ne cewa ni da
kai duk munyi rantsuwa da girman
abin bautarmu cewa zamu sallama
rayuwarmu da komai na mu domin mu
kare wannan gidan sarauta na mu da
qasar gaba xaya.
Na rantse da girman iyayena
idan ban hana sarki taraiya da wannan
amarya tasa ba sai mulkin ya suvuce
masa gaba xaya domin ita amaryarce
zata haye karagarsa kuma ajalinsa a
hannunta yake, ta yaya muna ji muna
gani za mu bar ‘yar almajiri mara
57

HIKAYOYIN AL’AJABI

MADAKI

cikakken asali zata zo ta karvi mulkin
qasar nan dare xaya?
Sa’adda Boka Aulad ya zo nan
a zancensa sai hankalin sarkin yaqi ya
dugunzuma ainun ya yi shiru yana
tunani da nazari har izuwa tsawon yan
daqiqu ya rasa abin da zai ce daga can
sai ya xago kai ya dubi Boka Aulad
yace.
“Tabbas dole ne na baka
haxin kai xari bisa xari domin ganin
mun ceci rayuwar sarki da kuma
darajar qasar nan ta kowane hali,
amma ka sani cewa tsalle xaya shi ke
jefa mutum a cikin rijiya, gaggawa a
cikin wannan al’amari a gare ni yana
da matuqar haxari, ka tuna cewa kai
fa boka ne wanda babu kamarsa a
qasar nan don haka ka yi amfani da
qarfin
sihirinka
wajen
magance
wannan matsala”.

58

HIKAYOYIN AL’AJABI

MADAKI

Boka Aulad ya yi ajiyar zuciya
cikin alamun takaici yace “Ai in da zan
iya yin hakan da tuni na yi ba sai na
tuntuve ka ba, ai idan ka ji makaho
yace a yi wasan jifa to lallai ya taka
hoge, ka tuna cewa duk faxin qasar
nan ba a sami budurwa da ta amince
za ta auri sarki ba a cikin wannan
larura tasa face Nasmirat kasan kuma
lallai akwai abinda ta taka.
Bisa wannan binciken da na yi
a kanta na gano cewa akwai wani
babban sihirin tsafi a jikinta wanda
duk wanda ya tunkareta da nufin ya
hallakata mutuwa zai yi, maganinta
kawai shi ne sarki ya fasa aurenta
kuma ya nisanta da ita.
Tun da ba zamu iya tava
Nasmirat ba ai za mu iya raba sarki da
ita, ni yanzu ba ni da sauran aminci
sarki kai kuwa kana da shi, ka yi
amfani da wannan dama a yau xin nan
59

HIKAYOYIN AL’AJABI

MADAKI

kafin sarki ya shiga xakin amaryarsa
kasa a sace shi a sirrance mu fitar da
daga cikin gidan sarautar gaba xaya,
mu kaishi can gidana na bayan gari
mu voye shi.
A sannan ne zamu yi tunanin
hanyar da zamu bi mu fitar da
Nasmirat daga cikin gidan sarautar
gaba xaya a cikin ruwan sanyi”.
Lokacin da Boka Aulad ya zo
nan a zancensa sai hankalin sarkin
yaqi ya qara dugunzuma ya shiga cikin
halin wasi-wasi,zullumi, fargaba da
zargi kawai sai ya xago kai ya dubi
Boka Aulad cikin alamun rashin yadda
yace.
“Duk waxannan abubuwan da
ka shirya mini yanzu sunyi kama da
hanyoyin da ake bi a shirya juyin mulki,
da wace hujja zan yi amfani na gamsu
cewa ba juyin mulki kake shirin yiwa
sarki ba?”
60

HIKAYOYIN AL’AJABI

MADAKI

Boka Aulad ya dakawa sarkin
yaqi tsawa a karo na uku yace “Yau
shekara ta arba’in ina bauta a wannan
gidan na sarauta na yi bauta ga
mahaifin sarki Ram da kakansa duk
tsawon waxannan shekarun ba a tava
kamani da laifin cin amanarsu ba, duk
abinda nake nema na jin daxi duniya
ina da shi a can fada ta ina da dukiya
mai tsananin yawan da ban san iyakar
adadin yawanta ba, ina da matan aure
guda tamanin da xaya, ina da ‘ya ‘ya
arba’in da biyu fadata ta ginu kuma ta
qawatu fiye da wannan wacce muke
ciki ina da fadawa kuyangi,barori da
dakarun tsaro waxanda suka ninka na
wannan fadar sau uku, a kan wane
dalili zan yi sha’awar wannan fada ko
karagar cikinta?”.
Koda sarkin yaqi ya ji
waxannan tambayoyi da Boka Aulad
ya yi masa sai jikinsa ya yi sanyi
61

HIKAYOYIN AL’AJABI

MADAKI

matuqa ya rasa abin da zai ce daga
can sai ya xaga kai ya dubi Boka Aulad
yace.
“Kafin dare yayi akai amarya
xakin angonta zan san abin da zan yi
akai kuma zan nemeka na sanar da kai
komai”.
Koda jin haka sai Boka Aulad
yayi doguwar ajiyar zuciya, sannan
yace “Lallai ka tabbatar da cewa ka yi
duk motsinka kafin a kai amarya xakin
sarki”.
Koda gama faxin haka sai
Boka Aulad ya juya ya yafito wani
hadiminsa da hannu take hadimin ya
janyo dokin Boka Aulad da sauri ya
kawo masa.
Cikin alamun fushi Boka Aulad
ya kama dokin nasa yah aye ya
zabureshi da gudu ya nufi hanyar fita
daga cikin gidan sarautar gaba xaya,
aikuwa sai wasu dakarun Boka Aulad
62

HIKAYOYIN AL’AJABI

MADAKI

kimanin su arba’in bisa dawakai suka
rufa masa baya.
Koda jama’ar gari suka ga
Boka Aulad ya fice daga ciki gidan
sarautar gaba xaya sai suka cika da
tsananin mamaki saboda an san cewa
dare da rana yana tare da sarki baya
yarda ya yi nisanta da shi,shi ma
sarkin haka fa aka fara tsegumi, kowa
ya riqa faxin albarkacin bakinsa.

63

HIKAYOYIN AL’AJABI

MADAKI

BABI NA SHIDA
Al’amarin sarki Ram kuwa
lokacin daya kama hannun amaryarsa
Nasmirat ya yaja ta izuwa cikin gidan
sarauta bai zame ko ina ba sai cikin
wani babban falo wanda girmansa ya
kai na fadar gidan sarautar. Babu
komai a cikin wannan falo face kujeru
da tebura na cin abinci birjik da yawa
iya ganin mutum.
Suna shigowa cikin wannan
babban falon sai suka yi arba da gaba
xayan sarakunan nahiyar waxanda
suka zo taya sarki Ram murna wannan
aure nas kowane sarki yana tare da
matarsa a zaune ga kayan ciye-ciye
dana shaye-shaye, iri-iri babu adadi
akan teburin amma a saboda girmama
64

HIKAYOYIN AL’AJABI

MADAKI

sarki Ram ko ruwansha babu wanda
ya xauka ya kai bakinsa sai ya iso
tukuna.
Koda sarakuna da matayensu
suka ga sarki Ram tare da amaryarsa
sun shigo cikin falon sai gaba xayansu
suka miqe tsaye suna kama yi masa
tafi ya yin da waxannan sarakunan
suka yi arba da amaryar Nasmirat a
cikin gagarumin ado da aka cava mata
sai dukkaninsu suka ximauce bisa
ganin irin tsananin kyawun da Allah ya
bata.
Nan fa wasun su suka fara
munafunci da tsegumi ga ‘yan uwansu
sarakuna.
Sarkin birnin kirishna ne ya
dubi sarkin birnin lamras ya yi masa
raxa a kunne yace “Tabbas banga
laifin sarki Ram ba da ya auri wannan
yarinyar ‘yar almajiri saboda ko ni ne
ba zan bari ta wuce ni ba”.
65

HIKAYOYIN AL’AJABI

MADAKI

Koda jin haka sai sarki lamras
ya yi murmushi yace “Amma ba don
kyaunta ya aure ta ba an ce saboda
kawai zata iya bashi labaru ne masu
daxi waxanda za su sa hankalinsa ya
kwanta ya daina hauka da shirme,
abin tambaya a nan shi ne a ina
wannan yarinya zata iya samo labarai
masu daxi, kuma masu ban al’ajabin
da za su iya saita wannan mahaukacin
sarki?”
Koda gama faxin hakan sai ga
sarki Ram tare da amaryarsa sun iso
daf da sarki lamras,kawai sai sarki
Ram ya dubi sarki Lamras yace.
“Na yi murna da ganinka a
wannan biki a zatona ba zaka zo ba
saboda laifin da na yi maka sa’adda
muka haxu a bikin naxin sarautar
birnin sin”.

66

HIKAYOYIN AL’AJABI

MADAKI

Koda jin haka sai sarki lamras
ya kama yaqe gami da murmushin
dole muryarsa na rawa yace.
“Haba ya kai sarkin sarakuna
ai ban isa na qi amsa gaiyatar bikinka
ba”.
Ita kuwa Nasmirat sai ta dube
shi tace “Zaka sha mamaki idan ka ji
irin labarum da zan baiwa sarki daga
daren yau, zaka ji daga bakinsa”.
Koda jin wannan batu sai jikin
sarki lamras ya kama tsuma saboda
tsananin mamaki gami da razana.
Daga nan suka yi gaba abinsu
haka dai aka ci gaba da gudanar
liyafar bikin na su.
Har tsawon wani lokaci kafin
aka kammala sarki Ram da amaryasa
suka wuce cikin.
Da shigarsu sai ta fahimci kan
sarki ya fara ciwo nan da nan
idanunsa suka juye ya fara tangaxi.
67

HIKAYOYIN AL’AJABI

MADAKI

Koda ganin haka sai ta
fahimci cewa lallai ciwon sarki ne zai
tashi a daidai wannan lokacin
maimakon ta ji tsoro ta nisanta da shi
sai ta janyo shi jikinta ta shiga yi masa
raxa a kunne tana mai cewa.
“Ya kai wannan sarki mai
daraja ka yi sani cewa an tava yin
wani gagarumin sarki a birnin kisra
wanda ya shekara xari da ashirin akan
karagar mulki batare da ya tava
fuskantar
wata
matsala
ba
a
rayuwarsa amma a karon banza aka
rabashi da mulki yana ji yana gani da
qarfinsa da lafiyarsa ya dawo bawan
sarkin da ya hau karagar alhalin da shi
sabon sarkin ya kasance bawansa
kuma ko kaxan ba shi da wata alaqa
da gidan sarautar”.
Koda jin wannan batu sai
sarki Ram ya ji kansa ya wattsake take
kuma ya ji kansa ya daina ciwo don
68

HIKAYOYIN AL’AJABI

MADAKI

haka sai ya dubi Nasmirat cikin
tsananin zaquwa yace, ta yaya wannan
al’amari ya faru, maza ki bani wannan
labari yake tauraruwar taurari.
Sa’adda Nasmirat taga sarki
Ram ya zaqu da son jin wannan
labarin sai ta qyalqyale da dariya tace.
“Ai kuwa akwai xinbin darasi
a cikin wannan labarin kuma gashi
yanzu dare ya soma yi, ina ganin har
gari ya waye ba zan iya gama baka shi
ba”.
Da jin haka sai jikin sarki Ram
ya kama tsuma zuciyarsa ta kama
tafarfasa kamar zata qone, kawai sai
ya zare takobinsa ya dakawa Nasmirat
tsawa yace.
“Maza ki ci gaba da ba ni
labarin da kika soma ko kuma yanzun
na sare miki kai”.
Koda jin haka sai Nasmirat ta
dubi sarki Ram cikin alamun tsoro tace.
69

HIKAYOYIN AL’AJABI

MADAKI

“Kwantar da hankalinka ya kai
mijina ai yanzu nan zan ci gaba da
baka wannan labarin” Nasmirat ta yi
doguwar ajiyar numfashi sannan tace.

70

HIKAYOYIN AL’AJABI

MADAKI

BABI NA BAKWAI
Kimanin shekaru xari da huxu
da suka shuxe anyi wani gawurtaccen
sarki a birnin kisira mai suna lafayis,
sarki lafayis ya kasance shahararren
mayaqi kuma babban sadauki mai
tarwatsa maza a filin daga.
Sarki lafayis ya kasance
azzalumin gaske domin bai xauki ran
xan adam a bakin komai ba, zalunci
kwace gami da fyaxe su ne al’adarsa
ta kullum da koyaushe rashin imaninsa
bai tsaya akan mazaje ba, hatta mata
da qananan yara bai qyale ba, sai da
takai cewa gaba xaya qasashen dake
makwabtaka da birnin qisra ana tsoron
sarki lafayis don haka duk qarshen
wata sai kowane sarki ya kawo masa
kuxi da bayi kyauta, domin gudun

71

HIKAYOYIN AL’AJABI

MADAKI

kada a kawo musu harin bazato, ko
ace za a yaqe su.
Haka dai sarki lafayis ya zama
alaqaqai kuma qadangaren bakin tulu
a nahiyar gaba xaya, ya adabi kowa
don haka duk sarkin da ya bashi
wannan cin hanci sai dai wani ba shi
ba, wato dai ataqaice sai da takai
cewa a fakaice sarki lafiyas ne ke
mulki gaba xaya qasashen dake
nahiyar saboda duk umarnin daya
baiwa sarakuna dole su bi kuma duk
abinda ya buqata daga gare su sai sun
kawo masa.
A rayuwar sarki lafayis babu
abinda ya tsana sama da ayi masa
gardama ko kuma ya bayar da umarni
aqi bi, duk wanda ya aikata xaya daga
cikin waxannan laifukan a gare shi to
sai ya kashe shi, ya qarar da dukkan
zuri’arsa domin ya zamo misali ga
wasu haka kuma a rayuwar sarki
72

HIKAYOYIN AL’AJABI

MADAKI

lafayis babu abin da yake so sama da
labaru da abubuwan ban dariya.
Don haka in dai mutum ya iya
barkwanci ko kuma ya iya abin dariya
to lallai zai samu kusanci sosai da sarki
lafayis kuma zai rinqa samun kyautar
dukiya mai yawan gaske.
Wata rana sai sarki lafayis ya
sami labarin wani gari da yake can
qarshen iyakar nahiyarsu da nahiyar
qasashen nasara wanda ake kira da
suna madhuzar.
Shi dai wannan birni na
madhuzar sabon birni ne wanda fatake
suka qiriqire shi asali ma ba a san ko a
qarqashin wacce qasa yake ba, akwai
ni’ima ta ruwa da yabanya a wajen shi
yasa fatake suka zavi wurin amatsayin
masauki rabin mutanen dake zaune a
birnin nasara ne rabin su kuma
larabawa saboda zaman lafiyan da ake
yi tsakanin qabilun biyu da kuma
73

HIKAYOYIN AL’AJABI

MADAKI

harkar cinikaiya sai aure ya rinqa
qulluwa a tsakaninsu suka rinqa
haihuwar kyawawan mata masu
kyawun launin fata gami da kwari da
kuma jarumta mazansu da matansu
duk kyawawa ne na gaban kwatance.
Babban abin da zai xaure wa
mutum kai shi ne babu wani bambanci
kowa yana da ikon yayi irin addininsa
da yake so babu mai hana shi,
shugabanci birnin a qarqashin qabilu
biyu yake babu sarki a garin amma
kowace qabila tana da wakili a
majalisar garin kuma wakilai a
majalisar garin kuma wakilai bakwai
ne sannan duk matsayinsu xaya babu
wanda yafi wani.
Kawai
dai
waxannan
shugabanin su goma sha huxu su ne
suke zartar da doka shari’a da kuma
umarnin a birnin wanda dole mutum
yabi ya yi biyayya a gare su.
74

HIKAYOYIN AL’AJABI

MADAKI

Akwai zaratan jarumai kuma
jatartun mayaqan samari a wannan
birni na hadhuzur waxanda suke kare
garin daga dukkan wani mugun abu ko
hari na bazata.
Bayan ga albarka noma ta
wannan
birni
akwai
arziqi
na
ma’adanan qasa a qarqashin wani
qaton tsauni dake tsakiyar wani qaton
kogi a na samun zinare da murjani a
wajen don haka kullum masu cinkin
zinare a cikin ziyarta birnin suke daga
ko ina cikin qasashen duniya.
Lokacin da sarki Lafayis ya
sami labarin wannan birni na
madhuzar ya ji irin arziqin dake cikinsa
sai ya ximauce, nan take yasa aka tara
masa dakarunsa na yaqi suka kaxaita
a cikin fadarsa inda ya dubi sarkin
yaqinsa yace.

75

HIKAYOYIN AL’AJABI

MADAKI

“Ya kai abu damrus wane
sakamako ka samo mini bisa binciken
da na ce ka yi a kan birnin madhuzar?”
Sa’adda sarkin yaqi abu
damrus ya ji wannan tambayar sai ya
yi ajiyar dogon numfashi ya dubi sarki
cikin alamun karayar zuciya yace.
“Ya shugabana bisa binciken
da na yi akwai manya qasashen kamar
guda uku a nahiyar nasarawa
waxanda suke baiwa birnin madhuzar
kariya da dakarunsa na yaqi, idan
muka ce za mu je mu yaqi birnin
madhuzar ba zamu sami nasara ba,
domin zamu tafi da gaba xayan
mayaqan mu za a kawo dakarun da
suka ninka namu sau xari, ka san
kuwa sarkin yawa yafi sarkin qarfi don
haka yanzu sai musan shawarar da za
mu yanke”.
Koda gama faxin haka sai
fada ta yi tsi! Akwa kama kallon-kallo
76

HIKAYOYIN AL’AJABI

MADAKI

juna aka rasa wanda zai ce qala da
ganin haka sai sarki lafayis yayi
murmushi yace.
“Aje a fara shiri gobe za mu
bar garin nan mu nufi birnin madhuzar
kuma dakaru dubu xaya kacal nake so
su yi mini rakiya”.
Sarki lafayis na gama faxin
hakan sai ya miqe tsaye ya fice daga
cikin fadar ya nufi hanyar da zata
kaishi cikin gidan sarauta.
Sai da aka ga sarki ya qule an
daina hangoshi sannan waziri ya dubi
sarki yaqi yace “Me ka fahimta
dangane da wannan hukunci da sarki
ya yanke?”
Sarkin yaqi ya yi murmushi
yace.
“Tabbas sarki ba zai yi
yunqurin yaqar birnin madhuzar ba so
yake mu je a matsayin fatake”.

77

HIKAYOYIN AL’AJABI

MADAKI

Koda jin haka sai hankalin
gaba xayan ‘yan majalisar ya
dugunzuma ba don komai ba sai
saboda sun san halin sarki lafayis na
iya yaudara akan tafarkin neman biyan
buqatarsa akwai yayuwar ya je ma ya
zauna a cikin birnin na madhuzar ya
rinqa taimakonsa ya kwashe duk abin
da yake so a garin ya sulale ya gudo
kafin su Ankara.
Na dai ‘yan majalisar suka yi
ta kace na ce kowa na faxin albarkacin
bakinsa.
Lokacin da gari ya soma yin
duhu sarki lafiyis na zaune a cikin
babban falonsa yana nishaxi yana
shan giya, ga waxansu kyawawan
kuyangi su bakwai tsaye a gefe guda
suna ta faman tiqa rawa sai ga sarkin
yaqi abu Damrus ya shigo.
78

HIKAYOYIN AL’AJABI

MADAKI

Da isowarsa kusa da kujera
da sarki lafayis ke zaune sai ya zube
qasa ya gaisuwa, batare da ya xago
kai ya dubi sarki ba, sai yace.
“Ya shugabana an gama
shirin tafiya kai ake jira kawai”.
Koda jin haka sai sarki lafayis
ya yi murmushi kuma ya miqe tsaye
zumbur ya tafa hannayensa sau xaya
take ‘yan matan dake rawa da
waxanda suka fice daga falon shi
kuwa sarki lafayis sai ya wuce gaba ya
nufi hanyar fita daga falon yana mai
cewa da sarkin yaqi mu je can bakin
fadar.
Dakarun Rakiyar na tsaitsaye
bisa dawakai a gefe xaya kuma
kuyangin sarki ne su goma gami da
waxansu hadimai bakwai a kusa da
dakarun kuma akwai raquma saba’in
xauke da guzuri da kuma keken dokin
sarki lafayis.
79

HIKAYOYIN AL’AJABI

MADAKI

Batare da vata lokaci ba sarki
ya shiga cikin keken dokin nasa ya
zauna,zamansa ke da wuya sai
dakarun rakiyar suka rabu gida biyu,
kaso xaya suka wuce gaban keken
dokin sarki rabi kuma suka tsaya a
bayan keken dokin ma’ana dai suka sa
keken dokin a tsakiya.
Nan take aka fara tafiya aka
fice daga cikin birnin qisra gaba xaya
sai da wannan zuga ta sarki lafayis ta
shafe kwana uku cir! Tana keta
dazuzzuka batare da sun haxu da wani
mugun abu ba.
A ranar kwana na uku ne
suka yada zango a bakin wata qorama
nan da nan aka kafa sansani aka haxa
tantuna kuma aka kewaye sansanin da
itatuwa yadda babu wata dabba ko
mutum da zai iya shigo wa kai tsaye.
A wannan lokkaci da aka
kammala
kafa
sansanin
farkon
80

HIKAYOYIN AL’AJABI

MADAKI

yammaci ne don haka ana gama cin
abinci sai sarki ya dubi sarkin yaqi
yace.
‘Ka wakilceni akan komai ni
yanzu ina sha’awar shiga daji domin
yin farauta”.
Koda jin haka sai hankalin
kowa
ya
dugunzuma
ainun,
musamman sarkin yaqi don haka sai
ya dubi sarki lafayis cikin alamun firgici
yace.
“Ya shugabana kusa ni cewa
akwai abubuwa masu hatsari a cikin
wannan dazuzzuka da muke bai
kamata ka shiga yin farautana, kai
kaxai”.
Da jin haka sai sarki lafayis ya
yi murmushi yace.
‘Na gama yanke hukunci duk
wanda ya biyo ni a baya sai takobina
yasha jininsa”.

81

HIKAYOYIN AL’AJABI

MADAKI

Koda gama faxin haka sai
sarki lafiyas ya koma cikin tantinsa ya
xauko makamansa na yaqi ya kunna
kai izuwa cikin daji, kai tsaye batare
da shakkar komai bah aka dai su sarki
yaqi suka zubawa sarki lafayis idanu
har ya qule aka daina hango shi.
Haqiqa masu iya magana
sunce jiki magayi ne kuma wanda bai
ji bari ba zai ji woho.
Lokacin da sarki lafayis yaci
gaba da kutsawa cikin daji yana kallekalle da dube-dube sai jikinsa ya yi
sanyi ba komai ne ya hadasa hakan ba
face jin tsananin shirun da ya cika
wannan daji da ya shigo inka xauke
sautin takun sawayensa babu abinda
mutum ke iya ji face sautin iskar da
take kaxa ganyayen bishiyoyi da kuma
rigar jikinsa.
Duk da tsananin jarumtaka
irin ta sarki lafayis sai da zuciyarsa ta
82

HIKAYOYIN AL’AJABI

MADAKI

xan bugo da qarfi ya tambayi kansa
cikin zuciya yace mene ne dalilin da ya
hana mafarauta ko ‘yan fashi ratsowa
cikin wannan dajin? Mene ne yasa
babu dabbobin daji da manya
tsuntsaye alhalin akwai ni’imar ruwa
da tsirai haka dai sarki lafayis yaci
gaba da yiwa kansa waxannan
tambayoyin, batare da ya baiwa kansa
amsa ba har sake kutsawa cikin dajin
sosai bayan ya shafe tafiyar rabin sa’a
adaidai wannan lokacin ne ya iso
gaban wani qaramin kogi mai ruwa
garai-garai gwanin ban sha’awa yana
isowa gaban kogin sai ya hango
waxansu manya kifaye,kimanin guda
ashirin suna ta zullo gami da kai kawo
a waje xaya.
Koda ganin waxannan kifayen
sai sarki lafayis ya ji ya kamu da
tsananin sha’awarsu don haka sai ya
fara tunanin hanyar da zai bi yayi su.
83

HIKAYOYIN AL’AJABI

MADAKI

Kawai sai ya je ya xauko wani
dogon ice ya fiqe qarshensa ya rinqa
kaiwa kifayen suka da ice domin ya
kamo amma sai kifayen suka rinqa
zullewa baya samun nasara cake su.
Tsawon xan lokaci yana ta yin
hakan amma ko kifi xaya ya kasa
kamawa.
Al’amarin da ya fusata shi
kenan ya yi wurgi da icen hannunsa ya
fara amfani da qarfin sihirinsa domin
ya kamo kifayen gaba xaya, nan ma
sai sihirin tsafi yaqi ya yi tasiri
End Ads