suka iso wata qatuwar
fada wacce kana ganinta kasan cewa
ba fada bace irin ta mutane sai dai
aljanu domin komai na cikinta
girmansa ya wuce na bil’adama haka
ma kamaninsa da yanayinsa.
Babu komai a cikin fadar face
wata qatuwar karagar mulki sai
gumaka na dakarun yaqi masu siffofin
iri-iri na ban al’ajabi da ban tsoro wasu
dakarun jikinsu na za ki ne, amma
kawunansu da hannayensu na aljanu
wasu kuma sai ka ga rabinsu
bil’adama rabinsu kuma na aljanu
sama da qasa.
26
HIKAYOYIN AL’AJABI
MADAKI
Kai wasu ma tsagin rabin
jikinsu ne daban-daban wasu kuma
jikinsu na bil’adama ne amma
kawunansu na dabbobi, dukkaninsu
suna riqe da muggan kayan yaqi kuma
sun kewaye qatuwar karagar mulkin
dake fadar.
A gaban karagar mulkin akwai
wata farar akwatin qarfe wacce ke rufe
kuma babu alamar murfi a jikinta ko
kuba wacce za a iya buxe ta.
Tsohuwa jarisa ta ci gaba da
tafiya tana ratsa wa ta tsakiyar
miliyoyin waxannan dakarun yaqin ta
tunkari inda wannan farar akwatin
take cikin tsananin firgici Nasmirat ta
bi bayan jarisa tana kallon dakarun a
firgice saboda gani take kamar a
koyaushe za su iya zama masu rai su
halakata.
Koda jarisa tai so inda farar
akwatin take ta dafata da sandarta sai
27
HIKAYOYIN AL’AJABI
MADAKI
gaba xaya dakarun tsaron suka zama
masu rai kowannansu ya yunqura ya
zare takobinsa.
Sai suka yi ca izuwa kan
tsohuwa jarisa za su ragargazata sai ta
yi wuf ta xauke sandarta daga kan
akwatin take gaba xayan dakarun suka
koma da baya kowannansu ya tsaya
cak! A inda yake da ya zama gunki.
A daidai wannan lokaci ne
tsohuwa jarisa ta waigo ta dubi
Nasmirat tace duk faxin duniyar nan
kece kaxai za ki iya buxe wannan
akwatin ki xauko ajiyar ciki wacce
kakarki ta bar miki duk wanda yayi
gangancin buxewa savanin ke ko da ni
ce kuwa sai waxannan dakarun sun
hallaka shi.
Da farko yanzu sai ki je ki
buxe akwatin ki xauko abin dake ciki
sannan na yi miki bayanin komai.
28
HIKAYOYIN AL’AJABI
MADAKI
Koda jin wannan batu sai
Nasmirat ta dubi tsohuwa jarisa cikin
alamun fushi tace “Ta yaya za ki ce na
je na buxe akwatin da bata da murfin
ko mabuxi”.
Koda jin wannan tambaya sai
jarisa ta yi murmushi cikin lokaci guda
kuma sai ta murtuke fuskarta ta
dubeta a fusace tace “Xiga xigon
jininki akan akwatin”.
Koda jin wannan batu sai
Nasmirat ta rikice kuma ta ximauce ta
kasa koda motsawa daga inda take
koda ganin haka sai tsohuwa jarisa ta
yi wuf ta kamo hannu Nasmirat tasa
farce hannunta ta yanke xanyatsanta
guda sannan ta jata izuwa kan akwatin.
Koda jinin Nasmirat ya xaga
akan wannan farar akwatin sai akwatin
ta buxe tamkar an buxe tsakiya littafi
babu komai a cikin akwatin face wani
xanqaramin jan littafi akan bangon
29
HIKAYOYIN AL’AJABI
MADAKI
littafin an yi rubutu da baqar tawada
mai kauri kamar haka HIKAYOYIN
AL’AJABI shi dai wannan bango littafin
an yi shi ne daga dutsen zinare,
rubutun kuwa da baqin dutsen lu’u lu’u
aka yi shi sai sheqi da walwali littafin
yake yi.
Nasmirat bata san sa’adda
sha’awar littafin ta kamata ba ta zura
hannayenta biyu cikin akwatin ta
xauko littafin.
Koda ta fito da littafin daga
cikin wannan farar akwatin sai gaba
xaya gumakan dakarun suka kama
tsattsewa suna rushewa tamkar an
tsoma alli a cikin ruwa.
Nan da nan gaba xayansu
suka rugurguje xayansu bai tsira ba.
Al’amarin da ya matuqar
baiwa Nasmirat mamaki kenan ita
kuwa tsohuwa jarisa sai ta bushe da
dariya farin ciki har da qyaqyatawa
30
HIKAYOYIN AL’AJABI
MADAKI
kuma nan take ta rikixe ainahin
sufarta ta aljana ta buxe fukafukanta
ta tashi sama tana shawagi a sama
Nasmirat tana mai ci gaba da
qyalqyala dariyar murna daga can
kuma sai ta sauko qasa ta fuskanci
Nasmirat har a sannan bata daina
kallon littafin dake hannunta ba cikin
matuqar al’ajabi.
Koda taga jarisa ta dira a
gabanta sai tax ago kai ta dubeta tace
“Yake wannan aljana mene ne dalilin
wannan farin ciki naki haka? Me
ximbin yawa?”
Koda jin wannan tambaya sai
aljana jarisa tace “Ba komai ne ya jefa
ni cikin wannan farin ciki ba face sai
yanzun nan na sami ‘yanci da zan
daina zama tare dake, da kuma tsare
wannan littafi na tsawon shekaru
ashirin tun kafin a haife ki,kamar
31
HIKAYOYIN AL’AJABI
MADAKI
yadda na gaya miki da farko zan yi
miki bayanin komai yanzu.
Kakanki na wajen uwa shi ne
mutumin da yafi kowa sanin labarai na
ban al’ajabi waxanda suka faru a ko
ina cikin wannan duniya, domin sai da
ya yi shekaru xari da biyar yana
binciko ire-iren waxannan labarai a
cikin madubin tsafinsa.
Don haka duk inda wani abin
al’ajabi ya faru a duniya a ko ina sai ya
ganshi sannan ya zauna ya rubuce
labaran da qarfin sihirin tsafi a cikin
kwanaki casa’in da tara da ya
kammala wannan aikin ne ya gyara
littafin sosai ya san ya shi a cikin
wannan bangon na zinare da lu’u lu’u
ya kawoshi nan kogon dutsen ya
adana a cikin akwatin nan.
Bisa binciken daya yi duk
wanda ya karance gaba xaya labaran
dake cikin wannan littafin walau a fili
32
HIKAYOYIN AL’AJABI
MADAKI
ko a cikin ransa sai ya samu mulki
gami da xaukaka da babu wani
mahaluki da zai iya samun kamarsa
face shi xin ya bar duniya.
Koda ya gano hakan sai ya
sana’anta wannan farar akwatin wacce
bata da murfi ko mabuxi yayi ta yadda
babu abinda zai iya buxeta face xigon
jininsa ko na zuri’arsa.
Ya sani cewa kece kaxai kika
rage a cikin zuri’arsa don haka saboda
ke kaxai ya adana wannan littafin. Ya
ke wannan yarinya me sa’a kiyi sani
cewa akwai labarai na ban al’ajabi
guda dubu biyu da xari biyu da ashirin
a cikin wannan littafin kuma a kullum
za ki iya karanta kowane labari kina
gama karance labaran su zauna a cikin
qwaqwalwarki tamkar akan takarda
aka rubuta da alqalami.
Karanta sun kuwa zai xauke
tsawon daqiqa casa’in da tara ne kacal
33
HIKAYOYIN AL’AJABI
MADAKI
idan kina shakka ko yanzu za ki iya
jarrabawa.
Koda jin wannan batu sai
Nasimat ta qyalqyale da dariya tace,
“Ai kuwa in dai haka ne wannan kakan
nawa ya cika babban matsafin da babu
kamarsa a wannan zamani.
Aljana jarisa tace “Ai dama
hakanne kuma kece kaxai za ki iya
gadarsa sirrin wannan littafi shi ne
kada ki kuskura ki karanta shi a gaban
wani mahaluki face idan kin kaxaita ke
kaxai a cikin xakin ki na barci, don
haka dole ne ki kasance kina mai ci
gaba da voye littafi a cikin wannan
akwati ya zamana cewa kullum kina
karantashi sau xaya har sai kin shafe
kwanaki xari uku da sittin kullum kina
karanta labarai bakwai sannan ki
kammala shi.
34
HIKAYOYIN AL’AJABI
MADAKI
Koda jin wannan batu sai
hankalin Nasmirat ya dugunzuma
ainun tace.
“Ta yaya zan iya voye
wannan littafi da wannan akwatin ba
tare da kowa ya gani ba, kuma yanzu
kina nufin cewa kullum idan ina son na
buxe wannan akwatin sai na yanke
jikina jikina na xiga jinina a kanta?”.
Aljana jarisa tace “Shakka
babu sai kin yi haka amma akwai abin
da za ki iya ki sami babban sirri a cikin
al’amarin yadda babu wani mahaluki
walau mutum ko aljan da zai tava
sirrinki,sirrin kuma shi ne za ki iya
mayar da akwatin nan ta zama xan
qarami guri da zaki xaure shi a
qugunki ya kasance dare da rana yana
jikin ki, duk sa’adda kika kaxaita a
cikin xakinki ya zamana cewa kina son
ki karanta littafin al’ajabi sai ki kwance
35
HIKAYOYIN AL’AJABI
MADAKI
gurin ki ajiye shi a gabanki ki xiga
masa jini.
Take gurin zai zama kawai sai
ke kaxai kuma akwatin zata buxe
kanta ki xauko littafin ki karanta da
zarar kin kammala kin mayar da littafin
cikin akwatin za ki ga ta rufe kanta,
kuma ta sake rikixewa ta zama
qaramin gurin.
Haka za ki yi ta yi har ki samu
nasarar kammala karanta littafi a cikin
kwanaki xari uku a da sittin ki sani
cewa daga yau ba ni da sauran alaqa
da ke koda wannan littafi domin dama
nib a waiwar kakanki ce na fi shekara
saba’in ina yi masa bauta bai ‘yanta ni
ba albashir xin ‘yanta shi ne na kare
wanna littafi har izuwa lokacin da
hannunki zai kai kansa, gashi kuwa
yanzu lokacin ya yi.
Da wannan furuci nake yi miki
bankwana yanzu nan zan tafi izuwa
36
HIKAYOYIN AL’AJABI
MADAKI
can qarshen duniya vangaren bangon
arewa zan qarasa sauran rayuwata
tare da mijina wanda tun da aka raba
mu tsawon shekaru yake zaune yana
faman sharar kuka, idan na koma gare
shin a sami ‘yancina babu wani boka
da ya isa ya sake tsare ni na yi masa
bauta, kuma har izuwa qarshen
rayuwata bazan sake rabuwa da mijina
ba, daidai da tsawon kwana xaya”.
Koda gama faxin hakan sai
Aljana jarisa ta yunqura zata tashi
sama, amma sai Nasmirat ta yi wuf ta
roqo fukafukinta guda xaya tace “Ya
za ki tafi baki gaya mini yadda zan
mayar da wannan akwati xan qaramin
guru ba?”
Koda jin wannan tambaya sai
aljana jarisa ta qyalqyale da dariya
tace “Ai na gaya miki tun xazu tun da
dai yanzu kece kaxai a cikin wannan
kogon dutse babu wata halitta mai
37
HIKAYOYIN AL’AJABI
MADAKI
raid a ke ganinki ko sauraronki,kawai
ki buxe littafin ki karanta labarai
bakwai kina kammala wa sai ki mayar
da littafin cikin akwatin ki rufe za ki ga
akwatin da kanta ta rikixe ta zama
gurun.
Gama faxin hakan ke da
wuya sai aljana jarisa ta buxe
fukafukanta ta yi sama tana ta
qyalqyala dariya farin ciki kuma ta
buxe muryarta da qarfi tana faxin na
sami ‘yanci na samu ‘yanci.
Kafin cikin daqiqa biyar aljana
jarisa ta luluqa a cikin gajimare ta vace
vat tamkar bata tava wanzuwa ba a
wajen.
Koda ganin abinda ya faru sai
Nasmirat ta dubi gabas da yamma
kudu da arewa a cikin kogon dutsen
kuma ta kasa kunnuwa har sai data
tabbatar da cewar babu wnai mahaluki
mai rai a cikin kogon sannan ta buxe
38
HIKAYOYIN AL’AJABI
MADAKI
littafin na hikayoyin aljabi ya fara
karanta labarin farko.
Koda ta ji irin tsananin daxin
labarin da kuma abubuwan al’ajabin
dake cikinsa sai ta ji cewa ai idan
kwana zata yi a tsaye tana karanta shi
ba zata gaji ba.
Nan da nan a cikin daqiqa
kaxan ta gama karanta labaru bakwai.
Tana gama karanta labari na
bakwai sai littafin ya rufe kansa,
Nasmirat ta yunqura da nufin ta sake
buxe littafin domin ta ci gaba da
karanta shi amma sai ta ji littafin ya
vame! Tamkar qusa aka kafe shi.
Nan fa ta dage iya qarfinta
domin ta buxe amma sai ta kasa, bisa
dole ta haqura ta mayar da littafin
cikin akwatin.
Faruwa haka keda wuya sai
farar akwatin ta rufe kanta sannan ta
qanqance ta zama guru xaya xan
39
HIKAYOYIN AL’AJABI
MADAKI
qarami cikin farin ciki Nasmirat ta
xauko gurun sannan ta xaure shi a
qugunta sannna ta ruga da gudu ta
fice daga cikin kogon dutsen.
Daga wannan rana kullum da
daddare sai Nasmirat ta shiga cikin
wani shago kasuwa wanda babu wani
a cikinsa ta kulle kanta ta kwance
wannan guru daga qugunta ta ajiye shi
a gabanta sannan tasa zabira ta xan
yanki xanyatsanta ta xigawa gurin jini.
Take yake zama wannan farar
akwatin ya buxe ita kuma sai ta xauko
littafi hikayoyin al’ajabi ta karance
labarai bakwai a cikinsa. Tana gamawa
sai ta mayar da littafin cikin akwatin
kuwa sai ta zama guru, Nasmirat ta
xauke abinta tax aura shi a qugunta.
40
HIKAYOYIN AL’AJABI
MADAKI
BABI NA HUXU
Yau kwana bakwai ke nan
Nasmirat tana yin wannan abun cikin
sirri ba tare da kowa ya gani ba, ko ya
ji hatta mahaifinta nata kuwa amma
kawai ranar daya tava hannunta ya ji
alamun yanka ya tambaye ta yadda
aka yi ta sami wannan raunika sai tace
da shi ai ta je aikin aikatau ne a wani
gidan attajiri aka sata ferayar kabewa
shi ne ta samu wannan raunika.
Koda jin haka sai makaho
marhat yayi ajiyar zuciya, cikin alamun
rashin gamsuwa amma sai ya yi shiru
bai sake tanka mata ba.
41
HIKAYOYIN AL’AJABI
MADAKI
A wanna rana ta bakwai ne
aka je aka xauko Nasmirat da
mahaifinta aka kai su cikin wannan
qerarren gida da shirin cewa kashe
gari za a yi bikin aurenta da sarki Ram.
A can gidan sarki Ram kuwa
tuni an fara shirye-shiryen bikin
aurensa ana ta shirya abinci da za a ci
gobe manya baqi kuwa tuni sun fara
hallara
daga
sauran
qasashen
makwabtaka
birni
da
qauye,
hadimai,barori da kuyangi kuwa sai kai
kawo suke yi suna ta yin ayyuka nag
yare-gyare ado da shirya qawa a
wurare da yake na cikin gidan sarautar.
Su kuwa matan sarki Ram su
goma sha xaya sun taru gaba xayansu
a cikin xakin uwargidansu suna
shiryawa kansu wata ‘yar qaramar
walima sai ciye-ciye da shaye-shaye
suke yi, suna ta qyalqyala dariya
42
HIKAYOYIN AL’AJABI
MADAKI
mugunta suna cewa za su ga yanda
wannan budurwa zata iya tsallake
kaifin takobin sarki Ram yaya suma
suka kasance matan sarki na tsawon
shekaru sun haqura da zuwa turakarsa
sai kamar budurwa yar shekara sha
takwas ce zata iya da shi?
Me ta sani a rayuwar duniya
ma bare ta bashi labarum da za su
kwantar masa da hankali su hana shi
hauka.
A can vangaren turakar sarki
kuma a wannan rana wani abin
mamaki ne ya faru, domin a ranar
gaba xaya ciwon sarki bai tashi ba ko
sau xaya ba, kuma sai ya kasance a
cikin tsananin farin ciki ya yi ta rabon
kuxi da kayayyaki ya zamana cewa
babu abinda yake son a faxa masa
face a ambaci sunan amaryarsa
Nasmirat, shi kansa Boka Aulad
makusancin sarki Ram sai da ya yi
43
HIKAYOYIN AL’AJABI
MADAKI
matuqar mamakin yadda aka yi sarki
Ram bai yi cutarsa ta hauka ba a
wannan rana, kuma har sai da dare ya
raba sarki Ram bai daina nishaxi da
farin ciki ba, babu shiri a lokacin Boka
Aulad yasa aka baiwa sarki Ram
maganin barci yasha sannan ya vingire
akan gado ya kama sharar barci hard
a minshari rabon da sarki Ram ya sami
irin wannan barci mai nauyi tun kafin
ya haxu da lalurar wannan cuta.
Kashe gari kuwa da sassafe
aka fara shagalin biki gaba xaya birnin
ya ruxe da kaxe-kaxe gami da bushebushe sarakuna da ‘ya ‘yansu attajirai
da masu faxa aji suka yi ta tururwa
izuwa cikin birnin suna rinqa shiga
gidan sarautar,masana tarihin birnin
said a suka tabbatar da cewa ba a
tava yin gagarumin taro da ya kai na
bikin auren sarki Ram da Nasmirat ba,
44
HIKAYOYIN AL’AJABI
MADAKI
tun daga farkon kafuwar qasar kuwa
izuwa yanzu.
Bisa al’adar auren a qasar
Hindu a wannan lokacin dole ne ango
da amarya su tsaya a gaban
masoyansu ‘yan uwansu da dukkan
zuri’arsu a kwara musu ruwan madarar
shanu akansu sannan kowannensu ya
zo gaban gunkin da suke bautawa ya
yi sujjada ya dangwali wani jan zabibi
da xanyatsansa na hagu yayi fashin
goshi a kansa da goshin gunkin,
sannan kuma ango ya shafawa
amaryarsa jan zabibin akan goshinta,
hakan na faruwa sun tabbata miji da
mata kuma sun sami albarkar gunki.
Bayan taro y agama cika, duk
inda mutum ya hanga gabas da
yamma kudu da arewa sai dai yaga
kowannan bil’adama rubutu batutu
babu masaka tsinke, a cikin tsakiyar
filin gidan sarautar ne aka yi wannan
45
HIKAYOYIN AL’AJABI
MADAKI
gangami sai ga sarki Ram tare da
amaryarsa sun fito daga cikin gidan
sarautar sun fito daga cikin gidan
sarauta.
Dukkaninsu sun cava ado na
gaban kwatance suna tafiya a kan
wani jan kishi wanda ya nufo wajen da
gunki yake, dakaru da kuyangi na take
musu baya.
Koda ganin fitowar sarki da
amaryarsa sai mutane suka ruxe da
shewa suka kama yi musu jinjina gami
da kirari.
Sai da sarki Ram da amaryasa
Nasmirat suka yi taku sittin sannan
suka iso gaban gunki suka tsaya
tsayuwarsu keda wuya sai aka zo da
madarar guda biyu a cikin gorar ruwa
aka kwararaa sarki da Nasmirat a
kansu suka jiqe sharkaf kaico, kaji
wata al’adar banza duk wannan
46
HIKAYOYIN AL’AJABI
MADAKI
kwalliya da ma’auratan suka yi an
vatata.
Nan take sarki Ram ya
dangwali jan zabibi ya yiwa kan fashin
goshin kuma ya yiwa gunki ya koma
gefe xaya ya tsaya.
Ita ma Nasmirat sai ta
dangwali zabibin ta shafawa kanta a
goshin.
Koda ta durfafi gunki da nufin
ta shafa masa zabibin akan goshinsa
sai kawai aka ji an zabga wata irin
tsawa mai qarfin gaske mai tsananin
ban tsoro wacce ta razana kowa
alhalin babu alamar hadari a garin.
Ita kanta Nasmirat bata san
sa’adda ta faxi qas saboda tsananin
firgita da tayi, amma sai ta miqe tsaye
zumbur taje ta shafawa gunki zabibin
sannnan ta shafawa kanta.
Koda ganin haka sai murna ta
kama sarki Ram don haka sai shima ya
47
HIKAYOYIN AL’AJABI
MADAKI
dangwali zabibin ya shafawa Nasmirat
a goshinta suka rungume juna a
lokacin da jama’a suka kaure da shewa
gami da tafi alamar aure ya tabbata a
lokacin da jama’a suka kaure da
wannan shewa ana ta murna gaba
xaya bokayen qasar kuwa hankalinsu a
dugunzume
yake
bisa
wannan
muguwar tsawa da aka tafka.
A lokacin da Nasimarat ta je
zata shafawa abin bautarsu zabibi a
goshi.
Hakan bai tava faruwa ba
kuma yana yi musu nuni ne da cewa
lallai akwai wani babban sauyi da yake
shirin zuwa, amma ta hannu wannan
budurwa amarya sarki.
Nan da nan Bokayen suka bar
filin gidan sarautar gaba xayansu suka
tafi izuwa can wani xakin bauta dake
bayan gari suka kulle qofarsa.
48
HIKAYOYIN AL’AJABI
MADAKI
49
HIKAYOYIN AL’AJABI
MADAKI
BABI NA BIYAR
Boka
Aulad
shi
ne
shugabansu don haka sai ya dube su
gaba xayansu yace da su “Abin da
nake so da ku shi ne kowannenku yayi
mana bincike yanzu a cikin madubin
tsafinsa ya gano mana ma’anar
wannan tsawa mai ban tsoro da aka
tafka sakamakon zuwan Nasmirat
gaban abin bautarmu da nufin shafa
masa zabibi bisa al’adar aure.
Koda jin wannan umarni sai
gaba xaya bokayen suka fiddo
madubinsu na tsafi suka duqufa shima
Boka Aulad xin ba a barshi a baya ba
sai ya taya su jim kaxan sai kowa ya
xago kai suka rinqa kallon-kallo a
junansu cikin matuqar al’ajabi aka rasa
wanda zai ce qala har shi kansa Boka
Aulad xin.
50
HIKAYOYIN AL’AJABI
MADAKI
Daga can sai boka Aulad ya
dube su yace.
“Na sani cewa duk abu guda
muka gani a cikin bincikenmu don
haka ba sai na tambayi xayanku ba.
Tabbas wannan bil al’ajabi ne
baba kuma abin tsoro don haka ya
zama wajibi musan matakan da zamu
xauka, wannan tsawa da aka tafka
ashe ba komai bace face gargaxi a
gare mu gaba xayan mutanen Hindu
cewar mai girma abin bautarmu bai yi
amana da wannan auren ba na sarki
saboda ita wannan yarinya Nasmirat
tana da wani babban sirri wanda nan
gaba zata kai ga samun babban
matsayi da xaukaka a birninmu. Ga
dukkan alamu ma sai ta mulke mu ta
zama sarauniyarmu idan kuma hakan
ta faru, mun tafka babban abin kunya
da ba a tava yin kamarsa ba.
51
HIKAYOYIN AL’AJABI
MADAKI
Ko ina a duniya ace ‘yar
almajiri mara cikaken asali ta zama
sarauniyar mu ya zama dole mu hana
sarki yin taraiya da wannan amarya
tasa a wannan daren na yau, kuma
musan hanyar da za mu bi mu
hallakata a sirrance batare da kowa ya
sani ba”.
Koda boka Aulad ya zo nan a
zancensa sai babban Boka na birnin
Kashmir ya miqe tsaye ya dube shi
cikin alamun girmamawa kuma ya
risina masa yace “Ya shugabana to
yanzu ya za mu yi da wannan cuta ta
sarki tunda ka san cewa abu ne
mawuyanci mu sake samun budurwar
da zata iya sai da ranta ta aure shi?”
Koda jin wannan tambaya sai
Boka Aulad ya ja numfashi ya ajiye
sannan yace “Ai har abada jarumai
basa qarewa a cikin duniya sai mu
lalubo wata, ina son ku barni mini
52
HIKAYOYIN AL’AJABI
MADAKI
komai a hannuna zan san abin da zan
yi.
A yau xin nan zan kawar da
wannan amarya ta sarki cire silin gashi
daga cikin tandun mai yafi wannan
aikin sauqi a wajena, tunda kun sani
cewa babu wani mahaluki daya fini
samun aminci a wajen sarki”.
Koda jin wannan batun sai
farin ciki ya lulluve dukanin bokayen
suka kama yiwa Boka Aulad jinjina
cikin farin ciki gami da samun nutsuwa.
A can filin gidan sarauta kuwa
bayan an gama xaura aure sarakai da
manya baqi suna zuwa su taya shi
murna, kuma suna bashi kyaututtuka a
lokacin da amaryarsa ke tsaye daf da
shi, sai ya lura babu boka Aulad a filin
gaba xaya.
Koda ya sake hangawa ko ina
sai yaga ashe gaba xaya bokayen
qasar ma basa nan, nan take hankalin
53
HIKAYOYIN AL’AJABI
MADAKI
sarki Ram ya dugunzuma ainun ya
aiyana a cikin ransa cewar lallai Boka
Aulad yaci amanarsa kuma akwai wata
maqarqashiya da yake shirin tafka
masa, shi da sauran bokayen.
Nan take sarki Ram ya kirawo
sarkin yaqinsa yace da shi, maza kasa
a rakani izuwa turakata kuma daga
yau kada a sake barin kowa ya shigo
inda nake ko a inda amaryata take
koda kuwa Boka Aulad ne, kai kaxai
na yarda da ka shigo turakar mu yi
magana.
Sarkin yaqi ya risina ya ce “An
gama ya shugabana”.
Nan take sarki Ram ya kama
hannun amaryasa Nasmirat suka nufi
cikin gidan sarauta dakaru sama da
miliyan xaya na mutane da aljanu na
take masa baya.
A daidai wannan lokacin ne
Bola Aulad da sauran bokayen suka
54
HIKAYOYIN AL’AJABI
MADAKI
dawo filin fadar koda Boka Aulad ya
hango sarki da amaryarsa za su shige
cikin gidan sarautar sai ya rugo da
gudu ya nufi inda sarki ya ke da nufin
ya shiga.
Kwatsam sai