x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 1 - HIKAYOYIN ALAJABI Book 1

  • 1 words
  • 3000 words
  • Out of 11023 words

Category: Adventure Stories

Views 62

01 Aug 2025
Start ads
After Image Ads

An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

HIKAYOYIN AL’AJABI

MADAKI

HIKAYOYIN AL’AJABI

Abudulaziz Madakin Gini

1

HIKAYOYIN AL’AJABI

MADAKI

2

HIKAYOYIN AL’AJABI

A

MADAKI

BABI NA XAYA

wani zamani can baya mai tsawo an
yi wani mashahurin sarki a birnin
Hindu wanda Allah ya albakace shi da
tarin dukiya, tarin ‘ya ‘ya mata. Girman
qasa da qarfin mulki. Komai na jin
daxin duniya babu abinda wannan
sarki mai suna Ram ya rasa, a duniya
babu abinda wannan sarkin yake tsoro
sama da mutuwa, don haka wannan
zamani masana sun tabbatar da cewa
babu wani sarki da yake da tsoro sama
da shi a duniya.
A cikin gidan sarautarsa
dakaru na bil’adama miliyan xaya ne
ke gadinsa, gami da dakarun aljanu
guda miliyan biyu yana da likitoci
masu kula da lafiyarsa, guda ashirin da
uku, kuma duk abin da zai ci ko zai
3

HIKAYOYIN AL’AJABI

MADAKI

sha sai bokansa ya duba shi yayi
bincike ya tabbatar da cewa abin ba
zai tava cutar da shi ba.
Sarki Ram baya yarda yayi
tafiya da ta wuce tsawon rabin sa’a
kuma duk inda zai je komai rashin
nisan wajen sai dakaru tsoronsa sun
raka shi suna masu sashi a tsakiya,
aljanu na shawagi a samansa don
tabbatar da tsoro.
A rayuwar sarki Ram bai
yarda da kowa ba, hatta matarsa da
‘ya ‘yansa kuwa ko ruwan sha baya
yarda so bashi,yasha face bokansa ya
duba shi kuma ko jima’i zai yi da
matarsa sai bokansa na zaune a qofar
xakin saboda kada matar tasa ta cutar
dashi.
Ana cikin wannan halin ne
watarana kwatsam sai wata cuta ta
kama sarki Ram wadda shi kansa
4

HIKAYOYIN AL’AJABI

MADAKI

Bokan nasa ya kasa gano maqasudinta
da yanayinta, haka ma likitocinsa
yanayin cutar shi ne haka kawai sai
ransa ya vaci, ya zare takobi ya yi ta
saran hadimansa da dakarunsa,
tamkar wanda ya zautu.
Dole sai an riqe shi da qarfin
tsiya, an kwance takobi an bashi wani
magani yasha sannan hankalinsa ke
dawowa cikin jikinsa amma rabin sa’a
na yi sai ciwon haukan ya dawo.
Bisa dole aka hana matan
sarki da iyalinsa kusantarsa, amma
kuma a kullum a cikin rusa kuka yake
saboda an hana shi yin tarayya da
matan nasa, bisa wannan dalilin ne
Bokan ya matsa da bincike ya gano
cewa dole sai an samo wa sarki Ram
sabuwar amarya kuma kyakkyawar
budurwa masaniyar labarai na ban
al’ajabi, tana kusantarsa a kowane

5

HIKAYOYIN AL’AJABI

MADAKI

dare sannan sarki Ram zai daina
wannan cuta ta hauka.
Akan wannan dalilin ne aka
baza shela ana neman budurwa da
zata iya wannan aikin mai haxari
wanda ta san cewa idan ta kasa
gamsar da sarki Ram da dadaxan
labaranta kashe ta zai yi.
Nan fa aka yi ta cigiyar har
tsawon wata uku da qyar aka sami
wata budurwa mai suna Nasmirat tace
zata iya wannan aikin.
Nasmirat bata da uwa kuma
ubanta makaho ne kullum sai tayi
masa jagora sun yi bara a cikin gari
sannan suke samun abin da za su ci,
domin talakawa ne fitik! Maqasqanta
amma kuma ta kasance kyakkyawar
gaske, mahaifinnanta ba shi da kowa a
duniya sai ita kaxai,basu da gidan
kwana sai a runfunar kasuwa sai dai
su shiga daji.
6

HIKAYOYIN AL’AJABI

MADAKI

Lokaci da makaho Marhat
mahaifin Nasmira ya ji cewa ‘yarsa
zata auri sarki bisa wannan sharaxi sai
ya fashe da kuka ya ce “Idan kika je
mutuwa za ki yi, idan na rasaki wa zai
ci gaba da kula da ni?”
Koda jin haka sai hawaye ya
zubowa Nasmirat ta dafa kafaxarsa
“Ka kwantar da hankalinka ya kai
Abbana ka yi sani cewa ina da
waxansu labarai na hikayoyi masu ban
al’ajabi waxanda lallai za su iya
magance wannan cuta ta sarki, ka
tuna cewa idan na auri sarki zan siya
maka gida mai daraja da tsada, a
garin nan kuma shi ken an ka daina
bara, har abada abinda nake so da kai
kawai shi ne ka taya ni da addu’a”.
Koda jin haka sai marhat ya
rungume Nasmirat yace “Ya ke ‘yarta
ki yi sani cewa rayuwarki da farin
cikinki ya fiye mini komai a cikin
7

HIKAYOYIN AL’AJABI

MADAKI

wannan duniyar, da dai na samu gida
da dukiya koda ta kai cikin garin nan
gwara na ci gaba da kwana a kasuwa
ina bara a titi muddin za ki rasa
rayuwarki, ko farin cikinki ki tuna cewa
fa ni girma ya kamani, ina nufin tsufa
ya riske ni, abu ne mawuya ci na daxe
nan gaba, ke kuwa yanzu ne za ki fara
shirya rayuwarki ta gaba,idan kika
sami matsala tun a farko to fa abu ne
mawuyacin komai na ki ya tafi daidai.
Sa’adda Marhat ya zo nan a
zancensa sai Nasmirat ta janye jikinta
daga cikin nasa sannan ta ruqe
kafaxunsa da hannayenta biyu ta dube
shi cikin murmushi tace.
“Na yi maka alqawarin babu
abin da zai same ni kuma sai suna na
ya shahara sosai a wannan nahiya
gaba xaya, ba mai wai a garin nan ba”.
Koda jin haka sai marhat ya
gyaxa kai cikin alamun karayar zuciya
8

HIKAYOYIN AL’AJABI

MADAKI

yace “Haba yake ‘ya ta yaushe
wannan mafarkin na ki zai zama
gaskiya? Ni dai kawai bazan hanaki
jarraba sa’arki ba amma dai hankalina
ba zai tava kwanciya ba, face na ga
kin auri wannan sarki na mu da
tsawon watanni kin rayu”.
Koda jin haka sai Nasmirat ta
kama tsohon Marhat ta kwantar da shi
akan shimfixarsa a cikin rumfar
kasuwar sannan ta janyo mayafinsa ta
lulluve shi sakamakon sanyi da ake
busawa a cikin dare.
Gama haka ke da wuya sai
itama ta je ta kwanta a kan
shimfixarta ta janyo mayafi da nufin ta
lulluva sai ta hango dakarun gidan
sarki kimanin su goma gami da wata
kuyanga sun shigo cikin kasuwar kuma
sun durfafo inda suke.
A firgice Nasmirat ta miqe
tsaye, shi ma marhat ya miqe tsaye
9

HIKAYOYIN AL’AJABI

MADAKI

lokacin daya ji motsin takon sawayen
dakarun sai ya miqe zaune zumbur a
tsorace, ya fara kiran Nasmirat yana
cewa “Ya ta su waye suka durfafo mu
ina fatan dai ba irin ‘yan iskan nan ba
ne da suka tava zuwa domin su yi miki
fyaxe, masu gadin kasuwa nan suka
cece ki?”
Nasmirat tace “A’a Abba basu
bane waxannan dakarun gidan sarki
ne”.
Koda jin haka sai marhata ya
miqe tsaye a firgice ya kamo hannun
Nasmirat ya damqe da kyau, yace.
‘Ina fatan dai ba wani laifi
muka yi musu ba?”
Kafin Nasmirat ta qara cewa
wani abu tuni dakarun da wanan
kuyangar sun iso daf da su, kawai sai
kuyangar ta dubi Nasmirat cikin
murmushi tace.

10

HIKAYOYIN AL’AJABI

MADAKI

‘To yarinya mai sa’a ki yi sani
cewa gobe ne za a xaura aurenki da
sarki bisa wannan dalilin ne sarki ya
bayar da umarnin a xauke ku daga
nan akai ku can sabon gidan daya
baiwa mahaifinki kyauta”.
A cikin gidan akwai komai
babu abin da zaku buqata a can ne za
a yi miki kwaliyar amarya kuma da
magariba za a kai ki wajen angonki”.
Koda jin wannan batun sai
Nasmirat ta kamu da tsananin farin
ciki shi kuma Marhat sai hankalinsa ya
dugunzuma ainun fiye da koyaushe.
Nan da aka ga waxansu
haimai na gidan sarki sun qaraso da
keken doki batare da vata wani lokaci
ba aka sanya Nasmirat da mahaifinta a
cikin keken dokin aka tafi da su izuwa
wannan sabon gidan da sarki ya basu
dakaru na take musu baya tamkar sun
kasance jinin sarauta.
11

HIKAYOYIN AL’AJABI

MADAKI

Gaba xaya sauran almajirai
dake kwana a cikin rumfuna kasuwa
sai suka tashi daga barci suka bisu da
kallo kawai suna matuqar mamakin
yadda aka yi wannan xaukaka ta zowa
Nasmirat da mahaifinta a dare xaya.
Mutane da basu da kuxi siyan
doki su hau yau ga su a cikin keken
dokin ma sun kame ana jansu.
To dama masu iya magana
sun ce dare xaya Allah kan yi bature
wannan fa shi ne Allah ya yi aure da
mara kwabo.

12

HIKAYOYIN AL’AJABI

MADAKI

BABI NA BIYU
A she lokacin da wannan
kuyangar ke faxawa Nasmirat cewa
gobe ne za a xaura mata aure da sarki
wasu daga cikin ‘yan uwanta almajirai
sun ji nan da nan kuwa labari ya cika
birnin Hindu ya zamana cewa duk inda
ka gifta sai di ka ji ana tsagegumi ana
faxin cewa gobe sarki zai auri ‘yar
almajiri marhat.
Aikuwa sai kowa ya rinqa
faxin albarkacin bakinsa, wasu su
kushe wasu su yaba wasu ma sai suka
rinqa cewa ai talauci ne yasa Nasmirat
ta siyar da rayuwarta domin ubanta ya
amfana tunda dai ta tabbatar da cewa
ita mutuwa za ta yi.
Lokacin da keken dokin su
Nasmirat ya iso qofar gidan da aka
basu suka yi arba da gidan sai
13

HIKAYOYIN AL’AJABI

MADAKI

Nasmirat ta kamu da tsananin mamaki
domin gaba xaya birnin in banda gidan
sarauta babu wani gida mai kyansa.
Koda ganin haka sai hawaye
ya zubowa Nasirat saboda tsananin
farin ciki ta kama hannun mahaifinta
suka sauko daga cikin keken dokin a
ka yi musu jagora izuwa cikin gidan da
shigarsu cikin gidan sai Nasmirat taga
yadda aka qawata shi ainun aka shirya
aljannar duniya, a cikinsa sai ta sake
kamuwa da matuqar farin ciki mara
misaltuwa bata san sa’adda ta fashe
da kuka ba.
Al’amarin da ya razana
mahaifinta Marhat kenan ya damqe
hannunta da kyau kuma ya janyo ta
izuwa kan qirjinsa yace.
“Ki kwantar da hankalinki
yake ‘yata na sani cewa tsananin farin
ciki ne ya saki wannan kuka gami da
takaicin cewa ba ni da idanu bare
14

HIKAYOYIN AL’AJABI

MADAKI

naga wannan daula da muka samu
kanmu, to ki sani cewa ni farin cikina
guda xaya ne kawai cewa ko a yau na
mutu naga yadda qarshen ‘yarta ya yi
kyau.
Ko a mafarki ban tava zaton
cewa zamu tsinci kanmu a cikin irin
wannan daula ba, tabbas mai rai baya
fidda rabo.
Haka dai aka yi ta kewayawa
da su Nasirat a cikin gidan har sai da
suka gama ganin ko ina duk inda suka
shiga sai sun ga bayi, kuyangi da
hadimai suna ta gabatar da aikaceaikace su, tamkar a haka za su shuxe,
har izuwa qarshen rayuwarsu.
Bayan hadiman da suka kawo
su sun tafi sai hadiman gidan suka
kawo wa Nasmirat da mahaifinta
abinci mai rai da lafiya suka kimtsa
cikinsu suka yi hani’an da yake dare ne
sosai sai Nasmirat ta yi gyaran murya.
15

HIKAYOYIN AL’AJABI

MADAKI

Take wata kuyanga dake tsaye a bakin
qofar falon da suke ta rugo da gudu ta
zube a qasa gabanta bisa gwiyoyinta
tace.
“Ya shugabata me kike da
buqata?”
Koda jin wannan tambaya sai
Nasmirat ta ji kamar kanta zai fashe
wai yau ita ake kira da shugaba alhalin
ta kasance ‘yar almajiri mai bara a titi
kuma mai kwana a kasuwar rumfa.
Cikin murna da annushuwa
Nasmirat ta dubi kuyangarta tace.
“Ina son ki raka Abbana
izuwa xakin barcinsa, bayan nan kuma
ina so ki faxa wa gaba xaya hadiman
gidan nan su je su kwanta su yi barci
tunda yanzu mun gama samun
nutsuwa, ni da mahaifina sai gobe da
safe ku zo gaba xayan ku ina son yin
magana da ku”.

16

HIKAYOYIN AL’AJABI

MADAKI

Koda jin haka sai kuyangar
tace “An gama ya shugabata”.
Nan take kuyanga ta miqe
tsaye sannan ta kama hannun tsoho
marhat ya tashi tsaye sannan suka fice
daga falon.
Fitarsu ke da wuya sai
Nasmirat ta miqe tsaye ta shige cikin
qurya turakar inda tayi arba da wanni
fankacecen gado tun data ke a rayuwa
bata tava ganin shimfixa kamar
wannan ba tun tana qarama har kawo
yanzu data girma ta zama cikakkiyar
budurwa.
Samari da dama gami da
dattijan banza sun sha nuna mata kuxi
domin su yi lalata da ita amma bata
yarda, sau goma sha xaya ana
yinqurin yi mata fyaxe Allah na kareta,
wannan rayuwa da take ciki ta jefa ta
cikin matsanancin tsoro da damuwa,
don haka a yanzu da sarki yasa aka
17

HIKAYOYIN AL’AJABI

MADAKI

kilace su aka kawo su, cikin wannan
gidan sai ta tsinci kanta a cikin
nutsuwa da farin ciki mara misaltuwa.
Matsalarta kawai shi ne yadda
zata kare kanta a wajen sarki Ram ta
rinqa ba shi daddaxan labarai da za su
gusar masu da ciwonsa na hauka
batare da ya kashe taba.
Dogaron Nasmirat xaya ne,
akwai wata rana da ta shiga cikin daji
domin ta kawar da buqatarta a lokacin
dama sun zo giftawa ta bayan gari ita
da mahaifin nata marhat.
Koda ta ji bawali ya mats eta
sai ta sanar da shi, cikin kaxuwa yace.
“Yake ‘yarta kin gaya mini
cewa yanzu muna bayan gari
ne,vangaren dajin husur kin sani cewa
yaune ranar farko da muka tava zuwa
wannan vangaren a yawon bararmu
don haka ba mu san haxarin da ke
wajen ba kuma gashi nan inda muke
18

HIKAYOYIN AL’AJABI

MADAKI

tsaye kan hanya ne mutane na xan
giftawa lokaci bayan lokaci,kinga ashe
ba za ki iya kawar da laruraki ba anan
xin, ki shiga cikin wannan dajin ki
nemi inda ya dace amma dai ki yi taka
tsantsan kuma ki kula da kanki sosai
ko yaya kika ga wani abu wanda baki
yarda da shi ba ki juyo da baya da
gudu izuwa nan, inda nake mu gudu
tare.
Koda tsoho marhat ya zo nan
a zancensa sai Nasmirat tace “Babu
komai ya kai Abbana ka jira ni anan
kada ka damu koda ka ga na xan vata
lokaci saboda dole sai na ga inda ya
dace na kawar da buqatar tawa”.
Marhat yace “Babu komai kije
‘ya ta mai girma saljil zai kare ki”.
Saljin gunki ne na wata giwa
wanda shi ne abin bautar zuri’ar su
tsohon marhat wannan addini nasu

19

HIKAYOYIN AL’AJABI

MADAKI

yana daga cikin addinai na farko a
birnin Hindu.
Ba tare da vata wani lokaci
ba kuwa Nasmirat ta bar tsoho marhat
a bakin hanya ya sami wuri ya zauna,
ita kuma sai ta kunna kai izuwa cikin
daji.
Abin ka da wadda dama ta
saba shiga cikin daji ko alamar tsoro
babu a tare da ita har ta yi ‘yar
doguwar tafiya kaxan, kawai sai ta
hango wani qaton kogon dutse wanda
qofar shigarsa duk ta lulluve da yana
tamkar fiye shekaru arba’in ba wata
halitta bata shige shi ba.
Al’amarin da ya yi matuqar
baiwa Nasmirat mamaki ke nan tace a
cikin ranta “Mene ne dalilin da yasa
fatake ko dabobi ko waxansu
mugayen mutane basa shiga cikin
wannan kogon dutse don fakewa ko
vuya? Amsar ta kasa baiwa kanta ke
20

HIKAYOYIN AL’AJABI

MADAKI

nan kawai sai ta aiyana a cikin ranta
cewa za ta zagaya bayan wannan
kogon dutse domin ta yi bawalinta.
Koda ta zo giftawa tab akin
qofar kogon sai ta ji an kirawo sunanta
daga ciki. Take hantar cikin Nasmirat
ta kaxa, ta kamu da tsananin tsoro ta
yunqura da nufin ta falfala da gudu da
baya kawai sai ta ga an toshe hanyar
da qaton dutse.
A firgice ta sake juyowa da
baya don ta koma inda ta fito nan ma
sai taga an toshe hanyar da wani
dutse.
Kafin ta yi wani yunquri sai
taga gaba xaya yanar da ta lulluve
qofar gogon ta vace vat tamkar bata
tava wanzuwa ba a wajen sai ga wata
mace tsohuwa tukuf gashin kanta ya
zama fari sol saboda tsufa, kuma tana
sanyi da farare tufafi tana dogara farar
sanda ta fito daga cikin kogon dutsen.
21

HIKAYOYIN AL’AJABI

MADAKI

Koda Nasmirat ta yi arba da
wannan tsohuwar sai ta kamu da
tsananin mamaki, ba komai ne ya sata
wannan mamaki ba face ta san
wannan tsuhuwar sosai, ana kiran
wannan tsohuwar da suna jarisa,
kuma itama almajira ce wajen
kjwanansu xaya a kasuwa kuma duk
inda Nasmirat da mahaifinta suka je
bara sai sun ganta a wajen koda kuwa
sun baro ta a can baya.
Hakan tasa suka fara tsorata
da ita suna zargin ko aljana ce, amma
da yake tun kafin a haifi Nasmirat
tsohuwa jarisa ke rayuwa a cikin
almajiran kasuwa kuma ba a tava
ganinta cutar da wani ba sai ba a
damu ba duk da cewa kuwa babu
wanda yasan asalinta ko daga inda ta
fito.
Lokacin da Nasmirat ta yi
arba da tsohuwa jarisa sai jikinta ya
22

HIKAYOYIN AL’AJABI

MADAKI

kama tsuma saboda tsananin tsoro ta
qura mata idanu,kuma ta kasa
motsawa ko da taku guda, walau gaba
ko baya.
Koda ganin haka sai tsohuwa
jarisa ta dub eta cikin murmushi tace
“Haba yake Nasmirat tun fa kina cikin
mahaifiyarki nake tare dake, in da so
nake na cutar da ke ai da tun a
asannan zan cuce ki, a gaban idanuna
aka haife ki har kika girma a matsayin
marainiya mara uwa har kawo iyanzu
yau ne ranar da za ki san ko ni wacece,
da kuma dalilin da yasa nake ta
bibiyarku, tun kina cikin mahaifiyarki.
Ki kwantar da hankalinki na
rantse da darajar uwata da ubana ba
zan tava cutar da ke ba, ki sani cewa
sau goma sha huxu ina kare
mutuncinki daga sharrin mugayen
mazajen dake kawo miki harin fyaxe.

23

HIKAYOYIN AL’AJABI

MADAKI

Tun kina jaririya nake kare
lafiyarki da rayuwarki, idan baki manta
ba kimanin watanni shida baya kin yi
arba da wata qatuwar baqar macijiya a
bayan gonakin nan na cikin gari inda
macijiyar ta taso miki da nufin ta
kashe ki a bakin qoramar salbil amma
sai wani kada ya taso sama daga
qarqashin ruwa ya afka wa macijiyar
suka yi baqin gumurzu daga qarshe sai
kadar ya sami nasarar kashe macijiyar
to ba wani bane wannan face ni xin
nan”.
Koda jarisa ta zo nan a
zaucenta sai Nasmirat ta kamu da
tsananin mamaki kuma ta qara tsorata
ainun ta dubi jarisa tace “To wai shin
ke wacece? Shin kin kasance bil’adama
mai qarfin sihirin tsafi ko kuwa ke
aljana ce?”
Koda jin wannan tambaya sai
tsohuwa jarisa ta bushe da dariya
24

HIKAYOYIN AL’AJABI

MADAKI

sannan ta dubi Nasmirat tace “Biyo ni
muje cikin kogon dutsen nan na baki
ajiyar da kakarki ta wajen uwa ta
barmin domin ke kaxai jal”.
A cikin wannan duniya sai na
damqa miki wannan ajiya sannan zan
sanar dake komai akaina, da kuma
dangantakata da kakarta ki”.
Koda gama faxin hakan sai
tsohuwa jarisa ta juya ta nufi cikin
kogon dutsen tana dogara farar
sandarta, cikin alamun tsoro da xarixari Nasmirat ta bi jarisa a baya tana
kalle-kalle da waige-waige a cikin
kogon dutsen kamar kace kyat ta fita
da gudu.

25

HIKAYOYIN AL’AJABI

MADAKI

BABI NA UKU
Sai da suka yi doguwar tafiya
ta kimanin daqiqa xari tara da saba’in
da uku sannan
End Ads