x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 3 - NI DA FATALWA

  • 6001 words
  • 9000 words
  • Out of 10307 words

Category: Horror Stories

Views 64

02 Jul 2025
Start ads
After Image Ads
Wata gigitacciyar dariya ta daga kai sama tanayi jini ya fara zuba daga cikin idanunta. yayin da ni kuma naje karshen bango a lokacin da nake ja da baya din. Sai ji nayi ta daka mun tsawq duk falon ya dauka
nan take sai gani nayi ta zama hayaki al'amarin da ya kara rudani kenan, hayakin nan ya baje a tsorace na tashi na fara kokarin bude kofar falo domin dawowa tayi ta rufe da karfi. Ina cikin jan kofar da nufin in bude in gudu sai ji naji an kyalkyalewa da dariya na juyo amm banga ta ina ake dariyan ba domin ko'ina a cikin falon amsawa yake sama kasa da ma ko'ina Tsulum sai ganin Inna Indo nayi a sama kan iska kusa da fankar dake sama, cikin wata irin bakar riga mai baza hayaki na fita a karkashinta. gashin kanta ma ya mike tsaye wani irin bakin hayaki ke fita a ciki. Fuskar ta bakyan gani abun tsoro domin idanunta jawur suke kamar danja haka suke fito da wani haske ja. Hakoran ta kuwa sun kara tsayi da tsini gasu suma bakakke fuskar ta jagule ta zama abun tsoro. Magana ta fara da wata irin murya mai tsananin kara da ban tsoro "Hahahahaha Tabbas kin aikata babban kuskure Khadija da kikayi kokarin kona ni Indo Fatalwa. Kin aikata zunubin da ba zan taba raga miki ba bazan kuma taba ragawa duk wani wanda yace zai zauna a gidan nan ba". Cikin firgin ina kukan tsoro sai karkawa nake nace "Dan Allah Inna Indo ki yafe mun zan bar miki gidan yanzu". "Hahahaha kinyi kadan domin nan gida na ne dama baki isa ki fita a cikinsa ba yau sai na kashe ki. A nan aka binne gawata sadda na mutu ana cikin haka kuka zo kuka gina gida a wajen kabarina. Da kun samu ina raga muku shine har kika sama damar yunkurin kashe ni? hahahaha ko kin manta dama can ni matatta ce? Kin taba ganin gawa ta mutu? to bazan mutu ba. kuma daga yanzu ba wanda ya isa ya kara zama a cikin gidan nan ko na minti biyar gida ya zama mallaki na. don haka yanzu zan hallaka ki kamar yanda kikayi yunkurin hallakani". Tana fadar haka sai kawai gani nayi ta bace tsulum ta bayyana a gabana da hannu daya ta shake mun wuya ta daga ni sama a haka, harbe harbe na fara ina buge bug hannuwan n kokarin banbare hannunta daga wuyana amm ina kamar karfe hannun nata. In banda wata mahaukaciyar dariya ba abunda take. ni kuwa tuni lumfashina ya fara kokarin daukewa. A zuciya na yanke shawarr yin kalmar shahada domin dai yau na tabbata kwana na y kare. Nan take na fara karanto kalmar shahada tun sannan naji Inna Indo ta kwalla uban ihu. Ta kalle ni hade da kara zazzare mun jajayen idanunta. "Kiii... daki.... na... kar.. karatun... nan". Haka ta fada cikin in ina tana kara shake wuyana ni kuwa tuni idanuna sunyi jawur lumfashi ya fara daukwa. Nan take na tuno ayyutul kursiyyo. Ina fara karantawa sai ji nayi Inna Indo ta kwalla gigitaccen ihu ba shiri ta sake ni ta fadi kasa. Ina ganin hka cikin juriya da karfin hali na juya na bude kofa falo na fito a million har sannan da karfi nake karanta ayyatul kursiyyu. Na jigata sosai amma ganin na fito daga wannan gida baisa na fasa gudu ba. kafafuna ba takalmi ko dan kwali babu shi a kaina balle hijab. Ko da naga nazo saitin makabarta sai na kara kaimi wajn karatun kamar dalibar da aka karawa karatu take yi dan karta manta.
Ina karasawa bakin titi Allah ya taimake ni wani mai napep ya kawo kai na tsaida shi tun kafin ya karasa tsayawa na hau da sauri ina cewa muje muje. shima dai ya fahimci ba lafiya ba saboda irin figar napep din da yayi a guje. Muna cikin tafiya yace "Hajiya ina za'a kai ki? Da alama dai ba lafiya ba?". nace muje tawalala zaka kai ni. har a lokacin lekowa nake baya dan kar inje Inna Indo ta biyo mu. Muna karasawa tawalala a kofar gida ya faka a guje na fito na fada gida. Umma na zaune a bakin kitchen Aunty Hauwa kuma na cikin kitchen tana juya abinci. Ita ta fara ganina na shigo a guje na fada daki. Haba ai itama ihu ta kwala ta wullar da ludayin hannun ta ta fito dag kitchen din a guje kadan ta hana ta bige Umma dake zaune. Ina ban tsaya falo ba na tsallake sai dakin umm can kuryan gado na haye naja blanket na shiga. Aunty Hauwa ma na ihu ta fado ta shige cikin bargon. Banda haki ba abund nake. Umma ta fado dakin a rude "Kai miye wai? Khadija Lafiya". "Indo Fatalwa, Indo Fatalwa zata kashe ni Umma". Tambya take amma banda haka ba abunda nake cewa. kuma ban yarda na fito daga bargo ba. Aunty Hauwa kuw kar kudundunewa take. Umma ta fara addu'ah tana tofa mun da kyau na dai-daita na dawo normal. ina ji mi napep ya aiko aka karba masa kudinsa. Zaune nake gefan gado Umma a gefan damana tana mun addu'ah Aunty Hauwa a gefan hagun wai itama addu'ah tak na kuwa tabbata banda miyau ba abunda take watsa mun domin kuwa itama a firgice take. Kuka na fashe da shi na kwashe labarin duk abunda ya faru na gayawa Umma. Umma ta tafa hannu hade da yin salati. Na kara da cewa wllahi bazan koma gidan nan ba. Umma ta goyi bayan haka sai dai dady na take ji. Nima shi nak ji domin mutum ne mai tsatsauran ra'ayi. Har dare ba wani bayni bana rabuwa da Umma duk inda tayi ina biye da ita ina kuma karanta Ayyatul Qursiyyu dan ba dan itab da yau an kashe ni. Ina jin shigowar dady amma naki yardq ya ganni. haka mukaita wasan buya Umma ma bata gaya masa ba domin zai iya cewa sai na koma gidan Habib.
Misalin karfe biyar na asuba na farka sakamakon mummunar mafarki da nayi wai ga Inna Indo nan zata kashe ni ni da Habib. A gigice na tashi na yo falo a nan fa mukayi kicibus da Dady ya fito zai tafi masallaci. Salati yayi sannan ya kwalawa Umma mu kira. Tana fitowa yace "Me wannan ta zo yi gida naga alama ma a nan ta kwana da izinin wa? Mijinta ne ya kawo ta?". Cikin tsoro nace "Aa dady gidan ne da mtsala fatalwa ce a gidan shiyasa gudu zata kashe...". Tass! naji saukar mari ba shiri na hadiye maganar da ban karasa ba. Marar hankali da tunani kin dauka aure wasa ne da zaki fito daga gidan miji har ki kwana a wani waje bai sani ba? Oya shige muje ko masallaci bazan je ba sai na maidaki gida tukun kuma wallahi ki kuka da kanki in har na iske ran Habib a bace"..................................


_Kutt! Khadija ana maidaki Inna Indo zata sheke ki. Ko dan ai yanzu kin tuno da addu'ah_

https://www.facebook.com/groups/1232550283531628/



↫ NI DA FATALWA! ↬

{gajeran labari}

Part {9} *Last page*

@KINGBOY ISAH


*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*

_GABA DAYA PAGE NAKU KYAUTA NA BAKU. INNA INDO ZATA ZO TAYA KU MURNA.LOL_

*♡❥❥PHATEEMA ALIYU♡♡*

*♡❥❥AUNTY ZEETY♡♡*
_____________________________
Kuka na farayi ina rokon Abba yayi hakuri ya bar ni. Haka itama Umman mu tana masa magana amma kunnuwan shi kamar an toshe. Ya kama hannuna har cikin motar sa dake waje dama nan take kwana. Muna shiga yaja motar yayi gaba, Titin fayau mutane jefi jefi suke tucewa masu zuwa masallaci. Cikin dan kankanin lokaci sai gamu a kofar gida. A matukar tsorace nake har lokacin ban daina kuka ba domin nasan ba makawa Inna Indo ba zata kyale ni ba. Addu'ah na farayi yayin da dadi ya fara kwankwasa gida ya dan dade yanayi yaji shuru yana dan tura kyauren sai yaga ya bude ba a kulle yake ba. Bugon zuciyata ya karu tuni nq fara karkarwq a lokacin da Abban mu yace in shiga. Ayyatul kursiyyu na fara karantawa sannan na dan sama kwarin gwiwar shiga. Cikin sanda kamar barauniya haka nake tafe Abba na bina a baya. har muka isa falo. Abba yayi sallama kusan biyar amma ba muji an amsa ba. hakan tasa yace in je inga ko Habib din barci yake in taso shi. Tsuru nayi ina kallon dakin ina kallan dadi yayin da na fara in ina ina shirin yin kuka domin tsoron shiga nake. Sai da Abba ya daka mun tsawa sannan naci gaba da karatu na nufi dakin kirjina na dukan tara tara. tsoro ya dabai baye ni. Rufe idanuna nayi domin kar in bude dakin inga Inna Indo hankali na dora hannuna jikin kofar na murda a hade da tura kofar jin shiru yasa na bude idona ihu na kwalla da karfi na fara kiran Abba domin abunda na gani yayi matukar girgiza ni. Habib ne kwace cikin jini kamar matacce kanshi jini ke zuba haka jikinsa duk raunuka ne. Cikin hanzari Abba ya karaso da sauri ya karasa wajen shi. Kara kunnensa yayi a kirjin Habib din yaji zuciyarsa na bugawa. da sauri ya cicibe sa yayo waje ni kuwa banda ihu ba abunda nake zundumawa na bi bayan Abba. Ni na bude bayan motar ya saka shi sannan na shiga, cikin hanzari ya figi motar sai General hospital A nan Habib yake aiki Muna zuwa akayi gagawar yi da shi Emergency shi.Nan na durkushe a kofar banda kuka ba abunda nake. Abba kuwa ya rasa me ma zaiyi, Sai sintiri yake a kofar wajen da aka shiga da Habib din. Likitoci kuwa sai kai komo suke domin wasu duk abokan shi ne na aiki. Wajejen karfe shida da rabi wani dan gajeran doctor ya fito. Ni da Abba mukayi saurin tarbarsa dan jin ya jikin Habib. Ajiyar zuciya yayi sanan yace "To Alhamdulillah a gaskiya da ace kun yi jinkiri wajen kawo Dr Habib da an rasa shi. Amma yanzu masha Allah mun yi masa aiki in sha Allah ba wata matsala babban ciwon da yaji a kai ne sai dai anci sa'a abun bai taba kwakwalwarsa ba". Cikin kuka nace "Dan Allah ina so in ganshi". Dr din yace a yanzu ba halin ganin shi domin har yanzu akwai sauran likitoci a kanshi
sai nan da wani lokaci sannan. Ni da Abba mukayi sallah sannan ya kira Abban su Habib ya shaida masa suzo asbiti ba lafiya". Cikin kankanin lokaci sai gasu sun karaso a firgice Abban Habib sai Mamanshi da kuma Ibrahim kaninsa. Abban Habib ya fara tambayar Abban mu lafiya kuwa?. Abban mu ya kwashe duk abunda ya faru ya gaya masa.Da jin haka Umman Habib ta hau kuka. tana leka ciki inda Habib yake. Abban mu ya kira gida ya fadawa Umman mu sannan yace ta taho mana da kayan kari nan asibitin. Bayan mun kakarya har lokacin ba abada damar shiga wajen Habib ba. Ina jin su Umma suna hira wai a zargin su Yan fashine suka wa Habib haka.Ni kuwa ban kawo kowa a zuciya ta ba sai Inna Indo domin na tabbata ikirarin da tayi ba karya bane don nima kadan ta hana ta hallaka ni. Wajejen karfe biyu da rabi likitocin suka bada damar shiga. Muka shiga kowa kuka yake ganin irin mawuyacin halin da Habib yake ciki. Har lokacin bai farka ba balle mu san me ya faru da shi. A takaice Habib bai farka ba sai bayan kwana uku da faruwar abun. Ina zaune a gefansa Umman sa da Bintu kanwar shi suna zaune a kujeru banda tagumi ba abunda mukayi. "Wayyo Allah fatalwa". Abunda ya fara tashi da shi kenan. a gigice. ganin yana neman zare karin ruwan dake hannunsa yasa na fita a guje na kira wo doctor. har lokacin da na dawo ihu yake yana fadin fatalwa tayi hakuri karta kashe shi. Abun ya daure wa su Umma kai amma banda ni domin ni nasan komai. Allurar bacci akayi masa ba wuya ya koma barci doctor yace Insha Allah nan da awa biyu zai tashi. kuma zai farka ne cikin natsuwa. Sai a lokacin muka dan kwantar da hankali. Umma ta kira Abban shi ta gaya masa ya farka haka nima na kira gida na fada musu ance nan da awa biyu Habib zai farka. Kafin lokacin tuni Family din biyu an hallara. Kamar yanda doctor ya fada awa biyu na cika Habib ya fara bude ido a hankali. Sannan ya yunkurq a gajiya ya tashi zaune. yayin da su Abba suke taimaka masa. Waige-waige ya hau yi yana cewa bata nan karfa ta zo ta kashe ni". Abban shi yace "Wace ce kuma zata kashe ka din". Habib yace "Indo Fatalwa mana dan Allah kar ku bari ta zo". Abban mu yace "Fatalwa kuma? Habib lafiyan ka kuwa". Yace "Eh Abba a hayyacina nake da idona na ganta duk ciwukan jikina ita taji mun wallahi bata da imani". Kallon kallo mutanen wajen aka shiga yi kafin Habib ya fara bada labari yace........,..............


Koma dai me yace ni kam na gaji yaseen a nan zan tsaya. Tunda Habib aka sambada bani ba.lol


https://www.facebook.com/groups/1232550283531628/







↫ NI DA FATALWA! ↬

{gajeran labari}

Part {10} *The end*

@KINGBOY ISAH


*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*

♥♡❥ ALFAHARI DAKU NAKE MASOYAN LITTAFAINA A DUK INDA KUKE. NA GAIDA MASOYAN ALJANA KURIYYA DA KANWARTA MARIYYA NA LITTAFIN MIJIN ALJANA. DA KUMA MASOYAN ALJANA SAFURATU TA LITTAFINA ALJANAR FATIMA. BAN MANTA DAKU BA MASOYAN SMASHER NA LABARIN ALJANA CE. GA KUMA MASOYAN FATALWA INNA INDO GAISUWA NAKE. KU KASANCE DA NAKU KING BOY ISAH MAI GURIN NISHADANTARWA FADAKARWA AND WA`AZANTAR DA KU A KO DA YAUSHE.❥♡♥

Habib ya fara da cewa. "Karfe shida da rabi na dawo daga wajen aiki. Abun mamaki ina zuwa kofar gida sai naga gidan a bude. bayan kuwa nasan Khadija da tsoro ba zata iya barin gida a bude ba. Bayan na saka mota cikin gida sai na shiga falo inata sallama amma shiru ba khadija. Hakan yasa na shiga cikin daki a zatona ko tana ciki ne amma sai ban ganta ba. Na tura ban daki naga nan ma a bud bata nan. Nan take zuciyata ta hau suya. Wato khadija har tana da ikon fita daga gidan nan ba tare da izinina ba? Lalai zata dawo ta same ni. A zuciya na fadi haka cike da kunar rai. Na ajiye jakar dake hannuna bayan nayi wanka na dawo falo Abun haushi har lokacin Khadija bata dawo ba dare kuma ya farari domin bakwai da rabi. Na fiddo wayata na kira number khadija amma sai ji nayi waya tayi ringing a kusa dani wato a nan ta bar wayar. na dauka hade da yin tsaki a zuciya nace yaushe Khadija ta fara bin gidaje yawo gashj har dare yayi bata dawo ba? Ni a zatona batayi nisa ba tundq ta bar gida a bude kuma ga wayarta ma a gida. Haushi da takaici suka ishe ni jira nake kawai Khadija ta dawo domin ta karbi hukunci. Dan kwanciyar da nayi ne barci yayi gaba dani. Ina fara barcin nan Kuwa na fara mafarka na abu tsoro kala kala. Ji nayi ana daddabata ana kiran sunana alamun tashina ake daga barci. Bude ido da zanyi sai ganin wata mumunar fuska nayi mai ban tsoro wata mace mai sanyi da bakakke kaya doguwar riga. hakan yasa na kwalla ihu kafin in tashi zaune na nema matar sama da kasa na rasa. Lokacin na lura da an kawo wuta. Kirjina yana bugawa domin na tsorata sai dai ina tantama matar nan a mafarki ne na ganta ko a farke. lokacin na kara kiran khadija amma sai ji nayi shiru kamar maye yaci shirwa. Na lashe wayata karfe tara da rabi. nan take haushi yq kara rufe ni. wato Khadija bata dawo ba har yanzu
Tashi nayi naje kitchen na dakko bredi da juice na zo na kunna kallo na fara ci. Ana cikin haka naji an bude kofar kitchen da karfi ina waigawa naga wani bakin abu ya shiga kitchen din a guje ya rufe kofar. Cikin gaggawa na tashi na bude kitchen din na leka ko'inq Amma banga kowa ba. Na fito yayin da na dawo sai gani nayi babu biredin da nake ci juice din dake cikin jug ma babu an dauke sannan na duba ni da nake kallon MBC 2 sai gani nayi an maida ni mbc Bollywood abun ya ban mamaki sosai. zaunawa nayi naci gaba da kallo ko minti biyu ba ayi da zamana ba naji ana kwankwasa gida da karfi. tun daga falo na fara fadin waye? waye jira a bude ma?. Ina zuwa na bude sai gani nayi wajen wayam ba kowa. Ana cikin haka naga wani abu baki kamar doki ya nufo ni a guje. ba shiri na mayar da gidan na kulle na koma ciki a razani. Naje wucewa kawai naji an tada mota ta ina lekawa naga wani a ciki na dauka barawo ne hakan yasa na dauki wani icce dake kusa dani kafin in zagaya na bude motar sai gani nayi ba kowa kuma motar ta kashe kanta. Ana cikin haka sai ji nayi an kure volume kallo da nake yi a falo da gudu na karasa ciki amma sai banga kowa ba. Na dauki remote na rage. Lokacin fa abun ya fara bani tsoro. Ina cikin kallo naji an dungure ni ta baya na juya da sauri banga kowa ba. Nan take kuma sai naji wani iska mai karfi ya shigo cikin falon ina jiyawa naga fankoki ne suke gudu kamar zasu cire. na tashi a rikice nakashe su. Kukan dan jariri naji a cikin dakin da muke kwana tsoro ya fara ziyarta ta a lokacin a hankali na nufi dakin ina
End Ads