x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 2 - NI DA FATALWA

  • 3001 words
  • 6000 words
  • Out of 10307 words

Category: Horror Stories

Views 63

02 Jul 2025
Start ads
After Image Ads
ta juyo fuskarta fari fat kamar wacce ta shafagari amma kuma idanunta ko kadan ba fari a ciki baki kirin da su ga wani irin gashin gira dogo da Aunty Hauwa bata taba ganin kalarsa ba tunda take. "Ni ce Fatalwa Indo". Abunda matar ta fada kenan. "Wayyo Allah na dan Allah dan annabi fatalwa kiyo hakuri ban san nan dakin ki bane. Na rantse yanzu zan fita". Kulululu cikin Aunty Hauwa ya kada sai zawo kafin kace me tuni ta jika zanin ta da fitsari. Ita sam ta kasa yin addu'ah kamar an mantar da ita kuma ta kasa bude dakin ta fito a guje. Kawai sai ihu take. Fatalwar nan kuwa ba abunda take sai kyalkyala dariya. Ni da Habib muna daki har barci ya fara daukar mu muka jiyo ihun Aunty Hauwa can kasa-kasa. Dake ni na fara tashi nayi sauri na tada Habib nace ihu nake ji. Yace "kwarai kuma kamar a gidan nan ma". Da sauri ya tashi ya yo falo ni ma da nake a tsorace a guje nabi bayansa. Mukaje kofar daki mukayi mukayi Aunty Hauwa ta bude amma ta ki budewa ihu take har muryar na shakewa. Da gudu Habib ya koma domin ya daukko makolin dakin nima kuwa na bishi dan bazan yarda ya barni ba wannan yanayi. Muna dawowa mukaji Aunty Hauwa ta daina ihu. Habib na budewa muka tarar da Aunty Hauwa bakin kofa a yashe a kasa ga dukan Alamu dai suma tayi Habib ya debo ruwa ya yayyafa mata ta farko. Hade da sakin razanannen kara. Sai kawai gani mukayi ta tashi ta baza a guje ta fito daga dakin tayi hanyar kofa. Da sauri Habib ya riko hannuta. "Ina zaki Ke Hauwa lafiya kuwa". Habib yake yake tambayar ta cikin tashin hankali. Ita kuwa kokarin kwacewa take kamar mai aljannu sai kuka take tana fadin "Wayyo Allah ka barni in tafi gida fatalwa wallahi bazan kwana a gidan nan ba". Nima tambaya nake lafiya lafiya amma ina hankalinta ya matukar tashi ga dukkan alamu dai tayi matukar razana ne. Habib ya juyo yana tambayana wai ko tana da iskokai ne ai kuwa ta gallamai cizo a hannu dan dole ya sake ta ta ruga da gudu waje na bita a guje ina fadin ta dawo. Kafin ta kai gate naga taja wani uban birki ta saki razanannen kara. Ta juyo a guje, Nima ihun na saki na juya a millon sakamakon ganin abunda ta gani. Fatalwar nan ce zaune cikin fararen kaya tasa wani abu wanda shima kamar gawa ce dai cikin likafani sai dariya take hasken glof din tsakar gida ya haska mana ita. Sai gamu muna tsere da Aunty Hauwa da da take niyar bude gida ta gudu. Ina zuwa na rukunkume Habib ina fadin "Fatalwa Fatalwa". Aunty Hauwa ma da gudu ta zo ta makalkale ni. Habib yace "Wai ku wane irin mutane ne in ma fatalwar ce ba zakuyi addu'ah ba sai ihu?. oya ku sake ni naje na ga miye". Ai maimakon in sake sa ma kara rukunkume shi nayi.Aunty Hauwa da sai maida numfashi take hauwaye kam sun cika fuskar share-share. itama kara matse ni tayi kam. Nace "Dan Allah karkaje Habib Fatalwa ce". Tsaki yayi yace "Oya to muje dakin iyayen tsoro ku kama karanta ayatul qursiyyu. Ai tun kafin ya rufe baki Aunty Hauwa kamar an kunnata ta fara karantawa. A haka muka tafi daki kamar yara Ni ina rike da Habib Aunty Hauwa kuwa na rike da ni. Mukaje wajen kwanciya aunty Hauwa ta kwanta a kasa tace Alquran ba mai raba ni da ita. Habib yace to mu kwanta a kan gadon shi zai kwanta a kasa. Ni ma nace wallahi ba zan rabu da kai ba, ni da Aunty Hauwa ai duk jirgi daya ya kwaso mu tunda itama fatalwar ta rainata. Ba yanda baiyi ba a kan shi ba zai kwanta gado daya ba da Aunty Hauwa Amma abu yaci tura domin nima nace bazan rabu da shi ba itama kuma bazata rabu dani ba. ganin muna shirin yin kwanan zaune ga barci a idanunmu sannan ya aminta ya kwanta can gefan ni kuma na rungume shi aunty Hauwa itama ta kankame ni. ya zmana ni ce a tsakiya. Aunty Hauwa a jike take sharaf da fitsari amma tsoro baza zai barta ta canza ko nawa ne bama. rokon Allah kawai take gari ya waye ta bar mana gidan. Cikinta ne yayi kara kulululuuuu "Aunty Hauwa lafiya kuwa". Tace "Wallahi zawo ne kuma bzan iya shiga toilet ba ni kadai wallahi tsoro nake ji. g zawan ya matse ni"..............


ZANCI GABA


https://www.facebook.com/groups/1232550283531628/



↫ NI DA FATALWA! ↬

{gajeran labari}

Part {4}

@KINGBOY ISAH


*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*

(*KUYI HAKURI JIYA KUN JINI SHIRU WAYA TA CE TA SA MAN HAWAN RUWA. HAR YANZU DAI BAI SAUKA BA*)

Nace "Aunty Hauwa ki daure ki matse shi wallahi ni dai in kika fita fatalwa ta kamaki ba ruwana" Karan tusa naji. Aunty Hauwa kaman tayi kuka "Wallahi ya matsen Dan Allah muje ki rakani na rantse in ba haka ba a wando zanyi". Da sauri Habib ya mike zaune yace "Khadija maza tashi ki raka ta". Na tashi zaune nace wallahi ni dai bazan iya zuwa ni kadai ba dole sai dai a tafi da kai domin nima tsoro nake ji". "Khadija kina da hankali bn dakin zan bi ku?. Dallah kinga ki tashi ki rakata muje na jira ku a kofa. Haka muka tashi a tsorace sai waige-waige muke. Aunty Hauwa na tura kofan ban dakin tayo baya da gudu. Habib yace "Miye kuma?" "Faa.... tall... wa". Ta fada cikin in'ina Habib da shima zuwa yanzu ya dan fara tsorata a hankali yaje ya tura ban dakin ya tura kafar haggun gaba ya dan like kamar marar gaskiya, ganin ba komai ya juyo yayi tsaki yace "Kawai tsorata kukayi amma ba komai a ciki". Da kyar aunty Hauwa ta shiga kusan sau uku tana shiga tana bazowa da gudu daga karshe dai tare muka shiga na juya baya nima tsorace tayi toilet din Habib na jiran mu a kofa sannan muk fito. Bayan mun kwanta wani irin kara muka ringa ji daga falo kamar kuka kamar dariya ba shiri na kara makalkale Habib Aunty Hauwa ta makalkale ni itama. A daren nan bamuyi barcin kirki ba. Kiran sallar fari Aunty Hauwa tace gida zata da kyar muka lalabata ta tsaya sai karfe shida Nima ban yarda an barni a gidan ba tare muka shigo mota aka kawo ta gida sannan muka koma. Wajejen karfe goma lokacin Habib tuni ya fita aikj zaune nake a Falo rike da waya ina chat da kawayena whatsapp amma sam ba a cikin natsuwa nake ba kallo daya zaka mun kq tabbar da hakan, "Salamu Alaikum" Naji ance durum! Gabana yayi mumunar faduwa Inna Indo ce ta shigo yau ma dai cikin dogon hijabinta fari har kasa. Fuskarta kam kallo daya nayi mata na kauda kai dan tsoro. Abun da ya dugunzuma hankalina shine ta ina matar nan ta ke shigowa bayan kuma yau ma na tabbata na makala kubabin gidan baki dayansu?. "Wa'alaiki salam" Na amsa sallamar hade da cewa ga waje zauna. Bayan ta zauna ne nace "Inna Indo naga na rufe gidan da kubobi ta ina kika shigo?". "Aa ni kuma ai a bude na ganshi leka ma ki gani a bude yake". Na tashi na dan rabe na wuce, abun mamaki kuma tabbas gidan a bude yake. bayan na dawo na zauna n naji tace "Ki daina barin gida a bude fatalwar nan da rana ma fa zata iya shigo miki gida". Nace "Wallahi nima na rufe". Sai ji nayi tace "Kin san me ya faru da matar da ta zauna a nan gidan ta biyu kuwa?". A dan tsorace nace "Aa". Nan take ta shiga bani labarin. "Bayan matar nan ta farko wacce aka tsorata ita da mijinta sun tashi. Sai wani mutum ya kama hayar gidan nan dan kasuwa ne shi sai karfe sha dayan dare yake dawowa gida. Yana da mata da yara biyu, Wata rana wajejen karfe sha dayan dare lokacin mijinta bai dawo gida ba yaranta kuwa tuni sunyi barci, Itama din ta kwanta har ta fara barci kawai sai taji kamar ana surutu a falo. To lokacin nepa basu kawo wuta ba. Fitila dayace kuma suke da babba. hakan yasa ta tashi ta sauko daga kan gadon ta dau fitilar nan ta nufi falo. Tana zuwa falo sai tayi curus sakamakon ganin wasu mutane biyu masu fararen kaya a zazzaune kan kujera sun juya mata baya wato bata ganin fuskarsu". Tuni tsoro ya rufe ni nace "Inna Indo kuma ba mijinta bane?". Tace "Tsaya kiji mana, Lokacin da ta gansu sai tsoro ya kamata cikin muryar tsoro tace "Su waye?". Maimakon taji an manta magana sai ji tayi su biyun sun gagabe da dariya, Tsoro ya rufe ta kamar zata ruga cikin daki a guje amma sai ta dake a tsorace ta kara furta "Su waye". Nan take taji sun kara fashewa da dariya kuma sai gani tayi su biyun sun mike tsaye a tare. Mata ne gashin kansu baki wul ya zuba kan bayansu kuma duk dogayen riguna ne farare ajikinsu. Matar nan taji sunyi shiru hakan yasa ta kara magana sai kawai gani tayi kawunan su sun juyo baya maimakon su waigo. Fuskokin su abun tsoro ba kyan gani domin sam ba irin fuskokin mutane ne da su ba. Wani irin dogon hanci ne lauyayye da shi bakin kuwa wangameme ga wasu hakora sun zuro daga ciki jini na zuba idanunsu kuwa jawur gasu da girma. Abun dai baya lissafuwa. ". Nace wayyo Allah na, basu kashe ta badai ko?". Tayi dariyar nan wacce tafi haushin kare ban tsoro hade da cewa "Ai tana ganin haka sai jikinta ya hau rawa ta koma daki a guje. Tana zuwa dakin ta iske wannan halittun a kan gado kusa da yaranta a kwance a nan wajen ta sulale kasa sumammiya. Lokacin da mijinta ya dawo ya tayarda ita kuwa ta hau rikici tace wallahi bazata kwana a gidan ba ta tashi. Ai kuwa haka akayi tun a daren ta kwashe yaranta suka bar gidan da safe sai canza gida mijinta yayi har yau bata ko yarda ta biyo ta nan kofar gida". Na sauke ajiyar zuciya hade da cewa "To ke kuma fa Inna Indo fatalwar bata taba tsorata ki bane halan". Tayi murmushi wanda ya karawa fuskar tata ban tsoro tace..................................

Zanci gaba

https://www.facebook.com/groups/1232550283531628/





↫ NI DA FATALWA! ↬

{gajeran labari}

Part {5}

@KINGBOY ISAH


*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*

(KU CI GABA DA HAKUR DA NI DAI. KUNSAN WAYATA BATA AMFANI SAI IN AKWAI NEPA. JIYA KUMA BA NEPA SHIYASA KUKA JINI SHIRU Autan writers ne)


Hade da cewa "Innah Indo ke kuma fa Fatalwar bata taba tsorata ki bane halan". Ta yi murmushi wanda ya fito da jajayen hakoranta waje, Fuskar ta wani yamutse abun tsoro sannan tace "Watarana ina zaune a tsakar gida bayan isha'i na gama tuwo na da miya ina jiran mai gidana kurum sai ji nayi an yi sallama. Lokacin na dai ji ana cewa akwai fatalwa a nan amma ban taba ganinta ba hakan ne ma yasa bani da tsoro a sannan. Na amsa sallama. amma sai naji shiru ba a shigo ba.Aka kara sallama na kara amsawa ba a shigo ba sai da akayi sau biyar ina tambaya wacece amma ba cikakkiyar amsa sai dai naji ance ni ce. hakan tasa na mike hade da daukar torchlight dita na nufi zaure na hahaska ko ina amma banga kowa ba har kofar gida na haska banga kowa ba. Kawai ina komawa sai naga wani abu fari kamar mutum a zaune wajen da na taso. Nan take jikina ya fara karkarwa domin nasan ba kowa a gidan kuma yanzu na ta so, Hakan tasa na bude baki a hankali nace "Mine ne a nan?". Sai ji nayi anyi wata yar guntuwar dariya. Na kara cewa miye a nan?. Sai gani nayi abu ya mike sama wai ashe fatalwar ce. Na juya a guje na shiga makwabta. Ina zuwa zauren gidan ta mukayi karo da ita itama ta fito a guje wai fatalwa ta je ta kwanta mata a kan gado. Ba shiri muka fito a guje. A ranar dai ba irin wahalar da fatalwar nan bata bamu ba tsoro kuwa har suma sai da nayi. Bayan wannan ma cikin dare in na fito fitsari na sha ganinta da fararren kaya a zaune ko a tsaye a tsakar gida. Ranar nan munje gidan biki mukayo dare wajen karfe sha daya muka taho ni da Makwabciyata muna tafe a kasai tsoro ya cika mu sai sauri muke a saitin makabartar nan a muka ga fatalwar da bakar doguwar riga abun tsoron babu kai a jikinta. Muka kara sauri ni kam dan tsoro kamar in tashi sama. lokacin fa ban tsufa sosai ba. Kawai sai ji mukayi fatalwar nan tace kai ku zo nan". Cikin duhun dare ai kuwa sai muka zabura da gudun bala'i ai kuwa fatalwar nan ta biyo mu. babu kai a jikinta tana kiran mu tana dariya". Wani motsi naji a bayana ai kuwa na daka tsalle hade da kwada ihu. domin nayi matukar tsorata. Inna Indo ta bushe da dariya ni kuwa ido wuri-wuri na kama kallonta. ji nayi tace naje na dan debo mata ruwa. nace to abun mamkin kafin naje kitchen na daukko mata ruwan ina zuwa sai tararwa nayi falon wayam. na leka waje naga gida a rufe. a guje na koma daki na kulle. Wayata na dauka na kira Aunty Hauwa duka daya ta dauka. "Hello lafiya dai Khadija ya naji kina huci? ko fatalwar ce?". Nace "Eh wallahi wata mata ce take zuwa gidana mai wani hijab fari dogo. in kin ganta abun tsoro ni wallahi inaga ma itae fatalwar saboda fa sai na kulle gida amma sai kawai na ganta a cikin gida, Kuma in ta zo ba labaran da take bani sai na fatalwa wallahi na fara gajiya". "Shegiya mahaukaciya maza dai ki tsaya a gidan nan naki fatalwa ta kashe ki. Ai ni wallahi ko a mafarki naga na sake bin hanyar gidan ki sai na tashi na yi addu'o'i da nafiloli. Wai ke me yasa ba zaki dawo gida bane? Ya zaki tsaya gida sai ke da Fatalwa". Nace "Aunty Hauwa ke kanki kinsan halin Abban mu wallahi in na zo gida a kan wannan dalilin dan banzan duka zai yi mun kuma ya koro ni. Gashi shi kuma Habib yaki fahimta ta ni wallahi addu'ah nake ma Allah yasa shima fatalwar nan ta tsorata shi nasan a lokacin zai gaskata ni". Karan kwankwasa gida naji da karfi hakan yasa na mike a firgice. daga can Aunty Hauwa tace "Miye akayi". Nace "Wallahi gida naji ana bugawa watakil ma fatalwar ce". Dull sai ji nayi wayar ta katse. Na sake kira na dauka network ne ke rawa wai ashe Jin nace ana knocking watakil ma fatalwa ce yasa auntu Hauwa ta kashe wayanta. A hankali na fito daga falo bayan na gama leke-leke kamar marar gaskiya. A lokacin dan kwakkwaran motsi zanji kawai in ara a na kare. daga bakin kofa na fara fadin "Waye? Waye?" Shiru naji ba ayi magana ba an kuma kara kwankwasa gidan. A zuciya nace yau na shiga uku wai ni me nayi wa fatalwr nan ne da bazata bar ni in zauna lafiya ba?". "Waye ne?". Na kara fada da karfi cikin fada naji Habib yace "Dallah can sarkij tsoro ki zo ki bude gida waye zai zo yanzu in ba ni ba?". Shima a tsorace na karasa a hankali na bude sai da na leka naga shin sannan na bude sauran kubobin. Dariya yayi hade da cewa "To sarkin tsoro ni wani abu na manta na zo dauka"? Nayi murmushi hade da cewa "Ba zaka gane bane habib sai ranar da fatalwar nan ta makure ka". Yayi murmushi hade da cewa "Malama ba wani fatalwa kawai dai tsoro ne irin naku in ma fatalwar ce ai ina da addu'ah". A zuciya nace "Baka san lokacin da abun tsoron ya zo ji zakayi kamar an mantar da kai duk addu'o'in ba kenan. In takaice muku labari sati daya nayi a gidan Habib cikin tsoro da fargaba wataran kullum kuma Innaa Indo sai ta zo gidan nan haka kuma kullum da kalar salon labarin tsoron da take zuwa da shi. Tsakar dare kuwa daga inga fatalwa a tsaye sai inga Fatalwa kusa dani a kwance. mafarkai kuwa gasu nan barkatai ba irin wanda banayi. na taba yin mafarkin munje cikin makabarta ni da Inna Indo wai tace in shiga cikin kabarinta ni kuwa naki shiga kawai sai ji nayi an tura ni ciki da karfi. Ni tsoro ba irin wanda ba a bani ba. Wataran inga bakar mage da jan ido tana kukan gadawaa wataran inga mage na tafiya ba kai. Yau ma kamar kullum Inna Indo ta zo ta gama zazzaga labaranta na abun tsoro ta tashi ta tafi. Ina zaune a Falo naji shigowar waya kawayena ne su uku suka ce gasu nan zuwa zasu kawo min ziyara ne.................

Hhhhh yan kawo ziyara, Allah yasa dai ku fice lafita.lol

https://www.facebook.com/groups/1232550283531628/








↫ NI DA FATALWA! ↬

{gajeran labari}

Part {8}

@KINGBOY ISAH


*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*


_GABA DAYA PAGE NAKU KYAUTA NA BAKU. INNA INDO ZATA ZO TAYA KU MURNA.LOL_

*✧✦✩UMMIEY ZEE✩✦✧*

*✧✦✩AUNTY ASY INDIMI ✩✦✧*
___________________________
Yanayin dariyar da take yayi matukar firgita ni bansan lokacin da n fara karkarwa ba bakina na rawa na fara ja da baya ina cewa. "Inna Indo dan Allah kiyi hakuri ki yafe mun".
End Ads