x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 15 - SIRRIN DAUKAKA

  • 42001 words
  • 45000 words
  • Out of 82078 words

Category: Romance Story +18

Views 132

30 Jun 2025
Start ads
After Image Ads
Ciki Kuma?" Nafisa tace. "insha Allahu kuwa wata hud'u kenan" wani i'rin hawayen dad'ine Ya sauko fiskanta “Alhamdulillahi Allah kai mai kub'utarwa ne Ya Arrahimu yah maliku ya ƙuddusu Yah hayyu, Yah Kayyumu, Yah Allah kaman yadda ka kub'utar dani Allah ka kub'utar da abinda ke cikina lafiya Allah ka saukaka Al'amura na ubangiji ka karamin Hakuri juriya da Dangana.." wani i'rin tausayinta ne ke sake samun matsunguni cikin zuciyar Nafisa, “Ameen” Nafisa tace sannan ta riketa a hankali take tafiya har suka shiga Bayin wanka da wanke baki tayi sannan ta d'auro Alwala A zaune ta ringa jiro sallolin dake k'anta tanayi tana Hutawa , Bai zoba har ta cika kwana Goma Nafisa ta biya komai ta kula da lafiyarta sosai bata da abinda zata biya matar domin ta sota , tamkar d'iyar cikinta haka ta d'auketa Bata rik'eta kishiya ba, randa ta cika kwana Goma Sha biyu suka dawo Gida, Jumana ce ta Gyara mata shashinta Haka ta cigaba da Mika Al'amuranta ga Allah Bata wasa da Sallah sadaka, da taimakon Gajiyayyu Har ta shafe wata Uku Gidan bai leko inda take ba, Abin na damunta Amma ta barwa ranta ta mayar da komai ba komai ba, tana masa Girki kuma Yana ci , Ganinsa ne de batayi,


Seda cikinta ya shiga wata Bakwai Ran Nan da dare inna Zaune saman kujera domin Cikin kwanakin nan inna fama da yawan fad'uwan gaba da ciwon kai Gefe d'aya da ya sarƙafeni Hannuna rik'e da Hisnul-Muslim inna duba adduo'i kaman wani munafiki Haka ya shigo kallon tsaf na masa duk ya susuce Hasken ma ya dushe D'auke kanta tayi daga kallonsa Bai lura da cikin Jikinki, dayafara turowa ba ya zauna kusa da i'ta tare da d'aura kanshi saman kafad'arta.


"Yallaɓai sai yau aka sako min kai kenan?” ta fad'a tana shafa Kanshi daya Tara Gashi duk da shi ba ma'abocin tarawa bane, mamaki ne ya kamata sosai.. d'agowa yayi cikin Sanyin murya yace “Dan Allah dan Annabi kiyi hakuri"


“Ni? Me kamin da kake bani Hakuri?" Ta fad'a tana sakin murmushi tare da Jan Karan hancinsa. Wani i'rin sanyi jikinsa yayi Allah ne ya bashi Jiddah Amatsayin mata i'rinta ne matan da ake musu lakabi da mar'atu-Swahliha Yana kallonta ta d'auko abinda yake aske Gashi ta joya tare da ajiye kujerar Tsunguno Zama tayi ta aske mishi Tass tare da Gyara mishi fuska kallon kansa yayi a madubi tare da kallonta Kaman yayi kuka Haka yake ji kawaicinta yayi yawa.


Komawa kujera tayi ta zauna tana sauke Numfashi tare da Rik'e Bayanta domin ya rik'e, biyota yayi tare da Zame Himar d'in da tun d'azun take sanye dashi Mutuwar Zaune yayi lokacin da idanunsa ya sauka , bisa cikinta “Hasbunallahu Yanzun kina da ciki shine ko ki sanar mu HAUWA?" Murmushi ta sakar masa “Tunda idanunka sun gane maka ai shike Nan."


Cikin wani i'rin Jin dad'i ya d'aura hannunshi saman cikinta Yana shafawa "Ubangiji ya raba lafiya Allah yasa ki Haifa min 'Yan biyu kaman yadda Halima ta Haifa" shekara d'aya kenan da haihuwar Halimatu ta haifi Aalik da Aaleen. Murmushi tayi Sannan ta kwanta cikin Kujera d'agota yayi "a a taso Yunwa nake ji wallahi..” dakyar ta Mike tana rik'e Baya a Haka cikin Daren ta d'aura Girki bata fito ba sai da ta kammala sannan ta had'a mishi saman tire a hankali take takowa har ta shigo d'akin a saman darduman carpet ta ajiye mishi Saukowa yai tare da Zama, Zuba mishi tayi zata mike yace "Zauna muci.." kawad da kanta tayi domin bata K'aunar Kallon shi bata ce mishi komai ba ta Mike ta Nufi Band'aki wanka tayi da ruwan sanyi tana zubawa jikinta tana sauke numfashi domin zafi take ji sosai tana Fitowa ta kunna Fankan dake fuskantar Gadonta ƙure gudunshi tayi sosai d'aure da zani ta kwanta tana jin yadda cikinta ke Juyawa.


Yana Kammalawa ya kwashe kayan hayewa yayi saman Gadon har Ga Allah Bata so ya tab'a jikinta daurewa kawai tayi harya nutse ga gajiyar da take fama dashi rik'e shi tayi sosai “Wai Allah bayana!" A hankali yake bi da i'ta “Banji yadda nake so Kiyi wani Abu Mana Wallahi ƙam kike Babu ruwa a Jikinki.." lumshe i'do tayi hawaye na sauka mata har yanzun Yana jikinta Amma magana yake fad'a mata tana jinshi ya gama fad'anshi "Baki da dad'i Wallahi nifa na gaji bazan iya wannan rayuwar ba, ki binciki Jikin ki" sauka yayi a jikinta tare da mirginawa Gefe, kukan zuci take, i'ta lokacin da yake da lalularsa bata tab'a fad'a mishi wani magana ba, sai ma, damuwa data daurawa kanta, Ɗan Adam kenan mai wiyar Sha'ani tana ta kokarin mikewa domin taje ta tsarkake jikinta ta kasa i'ta bata i'ya kwanciya da najasa ba. "Temaka min na mike bayana ya rik'e.." tsaki yaja tare da Juyawa Yana Gyara kwanciyarshi "Magana nake maka Yallaɓai.."


"Dalla malama ki ƙyale ni haba! nagaji bazan i'ya wani temaka miki ba, aikin me kikayi da bayanki yake ciwo in Zaki tashi ma ki tashi" shuru tayi tare da ƙurawa Bayanshi i'do i'ta bata son fad'a da masifa, Sunan Allah kawai take ambata domin zuciyarta zafi yake mata muddin tace Zatayi magana inna ga saiya kusan kifa mata mari, ranta ya Bala'i b'aci tsaki taja da karfi ta mike Zaune haureta yayi da kafa tare da mikewa Zaune "Ke har kin isa kimin tsaki Yar iska kawai" wani i'rin Kallo take jifanshi dashi mai cik'e da ma'anoni Da sauri ta Mike ta Nufi Band'aki jingina tayi da kofar ta fasa wani i'rin kuka mai tab'a zuciya Ya Zatayi ne? Wannan wacce i'rin jarabawa ce, wani i'rin rayuwa take fusk'anta haka.


"Allah Nagode maka Ubangiji ka karamin Hakuri da juriya!" Ta fad'a Haka tare da cire zanin jikinta a hankali take wanka tana kuka k'asa k'asa ..


Fitowa tayi ta sameshi har yayi barci sallaya ta shimfid'a ta hau nafiffilu Ranan ko barci batayi ba ta kwana saman Sallaya a lokacin da kowa ke barci i'ta Kuma tana kaima Allah kukanta Biyar da minta Goma ya farka tare da barin d'akin tana idar da sallah ta Gyara d'akinta kichin ta shiga ta fara had'a mishi abun Kari tana Kammala komai ta wanke kwanunka da yaci abinci jiya da Wanda ta b'ata Gyara gurin tayi sannan ta jera mishi abincin a falonta wanka ta shiga tana Fitowa ta fara jin Hayaniyar Fure da Zaina a falonta wadda rabon data ga d'ayansu tun lokacin da abinnan ya faru , a gurguje ta shirya tare da saka Himar ta fito ta samesu Kan abincin data dafa mishi sunyi Kaca Kaca da Falon wani i'rin dogon tsaki taja a zuciye tayi Gurin. Allah ya gani tana Hakuri dasu, Halinsu ya i'sheta.


“in ma Mijina Girki kuzo har cikin falona ku cinye sannan ku b'ata min Gurin banson damuwa fa meyasa ku, kullun in baku tada husuma ba bakwa jin dad'i haba wani i'rin ibilis ne ke kanku?.." Fure ce ta mike tare da shaketa da Himar d'in, “Dan Ubanki waye iblis shegiya ke kika sai abincin?.." tureta Jiddah tayi tana haki ranta a b'ace tace. “Bade ubana ba, Wallahi.." fincike Himar d'in jikinta Fure tayi tare da Wurgi dashi "Au ni kike zagi Aiko zaki ci Kan uwarki Yau, daman ban tab'a shiga Jikinki ba" a razane Zaina ta mike ganin cikin jikin Jiddah ya girma “Na shiga uku ni Abu ke dan Ubanki daman cikin nan Bai fita ba, durun Uwa! aiku ki Haifa in gani.." tana fad'in Haka takaima cikin duka lilis suka mata Fure na dukanta Zaina na kaima cikinta Tun tana i'ya Kare Kanta Har ta kasa ta galabaita ga jini daya tsinke mata ganin Haka yasa suka fita da gudu Karo sukaci dashi Baya yayi Yana kallon yadda suka fito a hargitsa da sauri ko wacce tayi d'akinta Yana shigowa yace “innalillahi ke Meya had'aku suka Miki Haka, wai bana ce ki daina shiga sha'aninsu bane? Allah yasa nide karsu tab'a lafiyan abinda ke ciki.."


Cije baki tayi tana kuka abinda zaice mata kenan wato i'tace ma ta jawosu ma, Yana korin tab'a ta saiga Nafisa ta shigo da Gudu domin karaman Yar Zaina sajida a Kan idonta akayi komai shiyasa taje ta sanar mata “Kai...! Karka yarda ka tab'a ta azzalimi solob’iyo Kana cikin Gida kana ji Amma dake kana tsoron Zaina ka kasa komai kalli yadda take fitar da Jini Allah Yana nan Muazzan Allah baya barci" Durkusawa tayi ta Kama hannun Jiddah "Jumanah..!" Ta kwala mata Kira da sauri tazo ta kamata suka fita.


Binsu Yayi da motar shi tsaban ta galabaita ko idanunta Bata iya bud'ewa ‘Dakin taimakon Gaggawa akayi da i'ta Kasa komai Nafisa tayi domin ta tsorata da lamarin sosai likitoci ne suka rufu a kanta Fitowa tayi tare da zama a kujeran Reception d'in Tafukan hannayenta tasa a fusk'anta tana kuka Yana tsaye Yana kallonta Hankalinshi a tashe wayarta ta d'auka tare da Kiran iyanmu ta sanar mata, kasa Kiran Ummi tayi sai sako data tura mata da Gmail d'inta Halimatu ta kira, ta sanar mata kashe wayarta tayi tana Zaune d'aya daga cikin likitocin ya fito, Mikewa tayi cikin rawan murya tace. “Dr Aliyu lafiya ya take..?" Dr Aliyu yace “Kai Dr Nafisa Gaskiya ana zalunci Yanzun su waye kuka daki cikinta haka..?" Nafisa tace. "Sanin wannan lamarin sai Allah ni dai ya Lafiyar ta dana cikin?" Dr Aliyu yace "Za'a mata C's domin alamu sun nuna tun jiya take nakuda" tafiya yayi da sauri ya d'ibi kayan aiki Suna Tsaye gurin aka fito da i'ta tare da Nufar wani D'aki kimanin awa d'aya da rabi wata Nurse tazo ta kirata tana shiga d'akinta ta sameta kwance kaman Gawa kafin tayi magana wayarta yayi Kara.


"Kuna wani asibiti?" Cewar ummi da i'sowarta Kenan daga Kaduna Nafisa tace "Muna asibiti na Harkun karaso kenan" kashe wayar Ummi tayi sannan ta fad'awa iyanmu wadda kusan lokaci d'aya suka i'so "Barka da arziki An samu maza biyu mace d'aya sai dai biyu ba lafiya macen ta samu karaya sosai a jikinta namijin dai hannun d'aya ne ya karye sai na ukun Sabida mace ce farko ga yaran can" ya nuna mata inda aka sanyasu a kwalba, kallon gurin tayi taga su ƙananu Jiddah ta kalla tare da kallon shi tana jiran Karin bayani "Kwankwasonta ya Goce dole in d'inkin ya warke
za'a kifata a mata aiki"


Fita tayi a d'akin.


Saida ta kwashe sati Uku a kwance kafin ta farka da dare, Sai dai Bata i'ya komai tana kwance Ummi na Gurinta da iyanmu ga Nafisa ma dake tsaye kanta , sai washe gari ta ganshi da sassafe ya shigo Ko kallon inda yake batayi ba, “Sannu Allah ya Kara lafiya" sanin ummi da Mahaifiyarshi na gurin ne yasa ta amsa domin bata so su fahimci halin da take ciki dashi , Bata samu Ganin yaran ba domin suna kwalba Dole sai sun cika adadin kwanakin ,


Alhamdulillah Bayan kwana Goma aka d'aurata Kan magani komai na tafiya dai-dai da taimakon Allah Dana Nafisa sai Ummi domin Iyanmu ta koma sai an kwana biyu zata dawo A hankali lafiya yake samuwa Har ta fara mikewa sai dai Bata mikewa duka Zuwa lokacin an Ciro mata yaran wadda tana ganinsu Allah ya d'ora mata masifar K'aunarsu tayi kuka sosai Ganin yadda saura suke ba lafiya, Macen taci Suna Sanah Mazan Kuma Aakif da Aaki Bayan kwana Biyar Macen da da Aaki suka koma Ranan kaman zata mutu Dan kuka domin yaran sunki Kama nono Aakif ne kawai ke Sha seda aka kara Mata ruwa domin zazzab'i ya rufeta Ummi ke rarrashinta da nasihohi Tana samun karfin jiki suka dawo Gida Zaina da Fure ba wadda ya lek'o ta, makota nata shigowa Suna mata Barka, Zaina bakin ciki kaman ta mutu Ganin Jiddah na raye har da D'a , lallai da sauran Aiki gabanta , Ummi ce ke lura da lafiyarta dana Aakif duk da ba wankan jego take ba Amma tana Amfani da ruwan zafi sosai tsakaninta da Arab sai dai kallo domin ko zai shekara Mata magana Bata kallon shi sai dai in ummi na Gurin ne take sakewa Suyi magana in Kuma Bata Nan sai dai ya d'auki 'Danshi in ya gama kallonshi ya tashi ya tafi Ta samu arziki sosai a haihuwar domin ta ko'ina samu take costumes d'inta sun mata alheri da makota shima yayi rawan Gani sai da ta samu wata Biyar Ummi ta koma Bayan ta mata nasihohi sosai domin tafahimci Yadda suke Zaune ba me shiga harkan wani, a hankali take Renon Yaronta tare bashi kulawan daya dace Shekaran shi d'aya ya bar nono batare data yaye shi ba, bata fita tunda ta dawo,


A hankali take fuskanta yadda matan ubanshi suka tsane shi shiyasa bata barin shi ya fita sajida na shigo Mata jefi jefi, domin saita faki idon uwarta take zuwa, Ranan daya cika shekara biyu da wata Uku inna kichin inna girki na fara jin kukan shi domin na barshi kwance Yana barci D'aki na shigo Naga baya Nan da sauri na fita inna Kiran sunanshi “Aakif Aakif.." dakatawa nayi Ganin Zaina da bulala Yaron na ganin uwarshi da sauri yazo Yana makalewa bayanta “Yanzun me wannan yaron ya Miki da zaki mishi wannan dukan?" Ta fad'a hawaye na zubo Mata ganin i'rin dukan data mishi sai Ajiyan zuciya yake tsaki Zaina tayi sannan tace "ba duka ba wata rana saina kashe shi" tana fad'in Haka tabar Gurin jikina na rawa na d'auke shi inna kuka nayi d'akina dashi Wayata na d'auka tare da Kiran Abbanshi ba b'ata lokaci yazo,


Ya sameta Zaune ta tasa yaro gaba tana kuka Zama yayi tare da cewa "Meya Faru?" Tura mishi yaron nayi "Tsakani da Allah na gaji Yanzun wannan karamin Yaron ya chanchanchi Haka! Mena tsarewa Zaina meyasa ta tsaneni haka" tana kuka tana fad'a mishi yadda Zaina ta Zane mata yaro Gashi har yanzun yaki daina kuka, d'aukar shi yai ya kaishi d'akin Nafisa tana wanka ya zauna jiranta , k'aurin Girki yasani mikewa da sauri domin na ma manta da inna girki saukewa nayi, na kashe gas din sannan na biyoshi d'akin. Na samesu tana dubashi Magani ta rubuta mishi “Ki ringa lura da lafiyan d'anki" Gyad'a Mata Kai nayi, sannan na d'auke shi na fita.


inna Zaune shuru shuru bai dawo ba na Miki na dawo falo Bayan na Goya Aakif dake kuka inna jijjigashi kiranshi nayi a waya, Yana d'auka yace “Kinga banson damuwa gani zuwa" kafin tayi magana ya kashe wayar sai Tara ya shigo Mata da maganin zuwa lokaci yaron yayi barci , Karb'a tayi batare da tace mishi komai ba ta nufi d'akinta ajiye magungunan tayi tare da shimfid'e yaron ta kwanta biyota yayi Bata hanashi abinda yake so ba, Yana Gamawa ya mike Yana Jan tsaki, fita yayi i'tama taje tayi wanka halinshi sai shi,


Washe gari tana Zaune da safe Aakif na cinyarta har yanzun zazzab'i yaki barinsa Tana jin hayaniya na tashin cikin Gidan Amma taki Fitowa tana Zaune suka shigo shida Gimbiyar shi hotuna ya watsa mata “Shegiya karuwan banza" Zaina tace tana jifanta da Mugun kallo fiska k'unshe da murmushi kallon Hoton tayi taga i'tace da Sir Nabil, lokacin da suka fita da Ummi tayi tuntub'e ya tare ta sai d'ayar lokacin da suka fita da Yamma dashi maganarshi ne ya katseta “Nagode da abinda kika min Jiddah da Aurena kike cin amanata nagode kije nagaji Allah ya had'a kowa da rabonsa..." 'Dagowa nayi inna murmushi "Toh sai me inka sake ni? Ance maka zanji haushi ne ko Zan kurma ihu ne! Alhamdulillah Allah Nagode maka daka rabani da wannan Qangin Yah Allah sharrin Zina da ake bina dashi Ubangiji Allah ka yafe min Allah kasa su gane"


"Wake Miki sharri Bayan ga zahiri kece fa kwance jikin wani Kato da Aurena Amma kin cuce ni Allah ya i'sa!"


"Na sake ki saki uku ki fito ki barmin Gidana!"


Murmushi ta sake yi "insha Allahu Yanzun kuwa Mena tsinta a gidana banda bak'in ciki da masifu Allah Yana kallo zaluncin da kamin kaida matanka Allah baya barci seya saka min Wallahi bazan tab'a Yafewa Rayunkan 'Ya'yana biyu da nake jin K'aunarsu ba" Fita yayi a d'akin Takowa Zaina tayi Gabanta "Ya kika ga wasan? Nayi Cari up, abin wani sarkin Kuma gwara ki sake hawayen ki daina matsewa.."


Kallon sama da K'asa na mata “insha Allahu bazaki tab'a ganin Kukana ba, Duniyace Zainab ta i'shi kowa Riga da wando bare mu da muke cikinta Na barki da Allah na barki Kuma da fitowar Rana da fad'uwarsa Hakk'i na bazai tab'a barin ki ba" Kayanta ta had'a na sawa tare Dana Aakif dake Zaune Yana Kallon maman shi na kwashe kaya Tana Gamawa ta kashe duk wani kayan wutan d'akin tare da Goyashi, Fitowa tayi tana jan jaka zata fita ya kwance Goyan tare da karb'an Jakan kayanshi “d'a nawane bashi kika Zo ba, Zaki iya tafiya"


"Wannan ne Kuma baka i'sa ba Wallahi..! Ka bani d'ana" ta fad'a tare da Kai hannu zata karb'i yaron Mari ya kifa mata tare da Bawa Zaina yaron "Tashi ki barmin Gida 'Yar iska kawai.." janta yayi da jakar Kayanta har waje tare da Kullo kofar Falon wani i'rin kuka ta sake tare da buga kofar “Ka bani ‘DANA lbrahim..!" Kuka take sosai Ganin yaki bud'ewa yasa ta shiga motar ta a guje tabar Gidan ikon Allah ne kawai ya kaita Kaduna Da karfi take danna horn ba shiri me Gadi ya bud'e mata tun kafin ya gama bud'ewa ta danno hancin motarta da gudu ya matsa ko gama dai-daita tsayuwar motar batayi ba ta fito a guje tayi cikin Gidan, ummi na Zaune taga mutum ya fad'o tana shirin magana taga Jiddah ce “Ke Lafiyar ki kuwa?!" Zubewa tayi a kasa tare da Rik'e Ƙirjinta tana Jan numfashi da sauri Ummi tayi Kanta..




Maman Faruq
12/26/23, 9:03 AM - UMMI JB: ♡SIRRIN ƊAUKAKA..!♡*


Farin Jini Writer's Association


Page22.


"Dan Allah kice ya bani Yarona Wallahi bazan iya barin shi cikin wannan Gidan ba, Ummi Yarona.."
Gyatsa mai had'e da Aman jini tayi cikin tashin hankali ummi ta qwalawa Yahgana Kira da sauri ta
End Ads