bari yanda baiyi sahur ba, yayi buda baki a wahale. Shinkafa da miyar kifin zatayi, ta soya dankalin da wainar kwai, sai ta hada musu lemon citta, ta sauko wasu kulolinta da bata taba amfani dasu ba, a ciki zata shirya komai, haka wasu filet dinta masu kyau ta dauraye, ta fiddo robobin da taketa boyo don irin haka, Rufaida ce ta bata su guda goma, design dinsu yayi kyau matuka, shisa ma ta adana, yau ga ranar amfani dasu tazo, shawarwarin Rufaida na dazun suka dinga mata shawagi
Haka kawai da zata biyewa zuciyarta da bakin kishi taje ta illata mijinta, a yanzun dai in wani abin ya same shi ai ita da yaranta sune da asara ba AZ din ba
Sai dai a lokacin da Jamila take aikinta cike da nishadi da son farantawa Baffa
Haka a gefe daya Baffa yake cikin nishadi da dokin ganin Magriba tayi dan yaje yaga abinda Aziza take ta fadin ta tanadar masa...!
#LubnaSufyan ✨
#WomenOfWords
#09035723778
Littafin nan na kudine akan #1k kacal, zaizo a manhajar Telegram 10/12/2024 In Shaa Allaah, bayan mun kammala shafukan dandano.
9035723778
Opay
Lubabatu Sufyan
Saika turo shaidar biya ta lambar da take sama. Nagode da addu'a'inku, nagode kuma da kwarin gwiwar da bakwa gajiya da bani
*
Duka littafin nan sadaukarwa ne ga Marubuciya Aisha Shafi'i, idan kunci karo da littafin nan, kun nishadantu, kun karu ta kowacce irin fuska, ku rokawa mijinta Isma'il Rahmar Allaah, ku roka mata sauki da juriyar rashin shi, ku rokawa yarinyarta rayuwa mai albarka. Nagode
********************** **************************
********** Ai Hausa Novels ****************
************************* **********************
DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery, Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from our blog.
Visit > https://www.aihausanovels.com.ng
Ka tura mana sako ta adireshinmu na email, domin tuntubarmu ko turo mana hausa novel ko kuma post.
Email > aihausabooks@gmail.com
******* FOLLOW US ******
Facebook: Ai Hausa Novels
Twitter: Ai Hausa Novels
Telegram Channel: https://t.me/Aihausanovels
WhatsApp Number: 08138873799
Haka kuma domin shiga kowanne daga cikinsu za ku iya ziyartar shafinmu ku yi search na AI HAUSA NOVELS, hatta facebook group dinmu ma za ku samu.
Wannan shagon na yanzun, guda biyu ne ya siya, da 'yar karamar plaza ce, akace mai ita ya rasu, to cikin yaran bayan an raba gado sai wasu suka siyar da nasu kason, wajene mai kyau, kuma a bakin hanya. Bayan ya siya a hankali saiya rushe katangar data raba shagunan, aiki yayi masa sosai, kusan duk wani tari daya dingayi da nufin siyan mota a wajen gyaran shagon suka tafi. Aka fadada shi, akayi musu dan karamin bandaki a ciki, saboda yaran shagon nashi idan aiki ya kacame musu, sukan kwana, da yake Baffa mutum ne mai tsantsani, bayason amfani da bandakunan plaza din sam.
Har yar doguwar kujera aka saka a cikin shagon daga gefe. Da shigar kananun kaya ya fito daga gida, sai kawai cikin yaran shagon nashi, Isma'il da yanzun zaice ma yana neman finshi kwarewa a harkar dinkin nasu na maza, gashi shi harda na mata ma yakeyi, ya dauko masa yadin daya manta ya siye shi yana fadin
"Oga Baffa nafa gama maka dinkin nan"
Ya karba, yadine ruwan toka mai duhu, irin masu laushin nan, ba wani abu akayi a jikin dinkin ba, amman yayi kyau matuqa, hannun dogo mai links, sai maballai a jiki, yasha guga, sai kamshin turaren sa Isma'il din yake amfani dasu a jikin duk wani kaya da zai dinka sukeyi, sai yaji ai wannan kayan sune ma yakamata ace ya saka anjima in zaije wajen Aziza. Haka kuwa akayi, yana ganin shida tayi ya shiga bandakin nan, yayi amfani da soso da sabulun da suke dashi ya kara wanke kafafuwanshi da babu abinda sukayi, har fuska ya wanke, inda ace shi din ba kumama bane ba wanka zai karayi, to komin zafin da akeyi saiya sirka ruwa yake iya wanka. Haka ya dauki mai da yake ajiye a saman wata yar shelf din katako da akayi, ya murza a hannuwanshi da kuma kafafuwa, sauran ya murza fuska, ya daura alwala, tukunna ya dauki kayan ya saka a cikin bayin
Yana fitowa ana fara kiran sallar magriba, Usman ya mika masa ruwa mai sanyi da dabino, yayi Bismillah ya fara cin dabinon tukunna yasha ruwan
"Oga Allaah dai yasa ba zance zakaje ba, irin wannan shan wanka da magribar nan"
Cewar Rabi'u dayake mikewa daga kan kekenshi
"Kaga wani sa'ido ko?"
Baffa ya fadi yana murmushi
"Da gaskiyarshi fa Oga, ba zamu bari a hada baki damu ayiwa Maman Arif haka ba, kai Isma'il kaine kayi dinkin nan, kamar a kunnenta"
Dariya Isma'il yayi yana daga hannuwa sama alamar saranda
"Ku rufamun asiri, ni na dauka ma cikin kayan sallah ne wallahi"
Kai kawai Baffa ya jinjina
"Wato dai in na lura daku, kamar bayan Jamila zakubi"
A tare suka hada baki suka amsa, ciki kuwa harda Abbati da bai cika magana ba, dan shi saida ya dora da
"Nan Madam take shaqaro kuloli da abinci ana aiko mana, so kakeyi a janye mana tallafi?"
Maganar taba Baffa dariya sosai
"Ni sallah zanje, ku kuka sani"
Suma sallar suka wuce bayan sun rufe shagon, da yake akwai masallaci a nan gefensu. Ana idarwa Baffa ya fadawa Usman akwai inda zashi, in dai wani abin ya taso sai su kirashi a waya, ya dauki mashin dinshi bayan ya turawa Aziza sakon cewa yana hanya, sai lokacin ma ya kula da cajin wayarshi saura 2%. Tunda yaje shago da safe bai sakata a caji ba, daman kuma jiyama haka bacci ya dauke shi da dare suna chatting da Aziza bayan wayar da suka sha, wayar da itace ma tasa shi ya barowa Jamila dakin nashi ya dawo falo. Addu'a yakeyi kar wani ya kirashi wayar ta mutu kafin ya karasa, dan bayason saiya nemi wanda zai aika a kira masa Aziza, gara dai ya kirata a waya.
A ranshi ya dinga zabga tsaki, shifa abinda ya tsana da unguwar nan ta Rijiyar Lemo kenan, musamman wannan layin 'yan chanan, kamar babu layin daya kaishi yawan kwatoci, jiyan nan ya bada aka wanke masa mashin dinshi tas, wani lokacin har mamakin yanda za'ace yarinya kamar Aziza tana irin wannan unguwar yakeyi. Ko a cikin layin nasu ma gidansu ne kadai mai katoton gate. Sai dai bayan ya karasa, ya samu waje a gefe yayi parking din mashin dinshi yana kara kallon unguwar tasu, cike da mutane anata hada-hada, ga masu awara nan da dankali waje-waje, an zagaye su layi danqam. Baiyi mintina uku ba Aziza ta fito, kamshin da take zabgawa ya wanke masa duk wani takaicin bata mashin dinshi da yayi.
Daya kalleta kuwa saida ya tsinci kanshi da rokon Allaah daya hore masa halin karasa gininshi ko zai samu ya mallaki Aziza kafin wani yazo yayi masa shigar sauri, bakinta daya sha jambaki ja ya kara fito masa da hasken fatarta tar da kwan lantarki ya haske masa kamar don shi aka bar wuta
"Kinyi kyau"
Ya fadi yana mata murmushi, ta danyi far da ido kafin ta saukesu cikin kunya
"Zaka fara ko Habibi?"
Yanayin yanda tayi maganar yaji duk ya susuce, shifa wannan abubuwan, yanayin yanda take lankwasa murya in zatayi magana, 'yar shagwabar da takeyi masa, kwarkwasar nan, sai yaita kallon Jamila yana tunanin yanda akayi tun farko bai taba kula bata da wannan abubuwan ba, ya dinga zurfafa tunani, daman ko lokacin kafin suyi aure haka take? Ko kuma daga bayane ta canza tunda tanajin aita same shi bata bukatar ta dinga yi masa irin wannan abubuwan
"Kazo mu karasa ciki"
Cewar Aziza, bai kuma yi mata musu ba, yau ma kamar duk zuwan da zaiyi, ya shiga tunanin yanda za'ayi a shiga da mota gidan nasu Aziza. Inka shiga karamar kofar jikin gate din, baifi kayi taku hudu ba zaka samu katanga data raba gate din da cikin gidan nasu, sai kuma wata kofa da ba'a sakawa kyaure bama, nan zaka shiga, wani dan surkukin soro ne da su biyu ma in suka tsaya shi da Aziza a ciki tsaf yan hisba zasu samu sabon case, sai dai suji ana tambayar lambar wayar iyayensu, don da wahala jikinsu ba zai gogi na juna ba saboda kankantar shi, a gefe kofa ce da take a rufe, bai taba ganinta a bude ba, sai kuma dayar kofar da zata sadaka da wadataccen falon da suke zama suna zance a ciki.
Aziza ce a gaba yana biye da ita, tun daga bakin kofar kamshin turaren wuta yayi masa sallama kamar ya shiga Maiduguri. Yaji wani sanyi na ratsa shi, kasala da gajiya duk suka rufar masa, suna kara tuna masa da ya kamata shima yasa AC a gidanshi, ko da iya dakinshi ne kuwa. Ya zauna a daya daga cikin kujerun dakin da sallama a bakinshi yana ba Aziza dariya duk da ta amsa, ta dora da
"Ina wuni, an sha ruwa lafiya? Ya aiki?"
Ya sauke numfashi yana amsawa, hankalin shi yana kan kwanonin da aka shirya a tsakar dakin, bawai abinda ke ciki yake hasashe ba, kwanonin ne sukayi masa kyau matuka, dan bai taba ganin irinsu ba. Aziza ta sauko ta fara budewa, kamshi ya cika hancin shi, saida ta mike ta dauko wata darduma mai kyau, tukunna ta shimfida masa tana fadin
"Ka sauko Habibi, nasan bakaci komai ba"
Saukowar yayi ya zauna, yana kallon fararen yatsunta da jan lalle a jikin faratan, yayi saurin maida idanuwanshi kan farantin yana jan Istigfari saboda tunanin da yake neman kutso masa cikin kai
"Kice mun ba wahalar da kanki kikayi ba kika sake shirya wani abin, ai nace jiya ki sakamun a firij"
Saboda shifa wannan tortilla din data kirane a ranshi har yanzun, so yake kawai yaga daga inda zata bullo
"Ya zanyi dakai tunda baka zo ba? Kuma kasan Mummy ma zatayi mun fada tace ya za'ayi in baka abincin jiya"
Ta fara mika masa wani dan karamin kwano da wani abu a cikin narkakke da dan barbadin wani ganye-ganye a ciki. Ya karba yana kura masa ido na dan sakanni kafin ya duba sauran tarkacen da take ta kiciniyar dibar masa, shi dai baiga biredi ba, abinda yake hannun shi kuma yayi masa kama da butter
"Nasanka da son dankali, gashi anci maiko tunda azumi ne shine nace gara inyi maka mashed..."
Yaji kalmar, kuma yasan turanci ne, a dan abinda yakeji dai ya kasa fassara shi balle hadinshi da abinda yake hannunshi, ya dai karbi cokalin da ta mika masa ya dibo yana kaiwa bakinshi da Bismillah, ba don korar shaidan ba, don neman sa'a kar bakinshi ya kunyata shi yaki karbar wannan abin. Hakan kuwa ya faru, shi dai yaji galmi-galmi, amman baiyi masa yanayi da abinda zai iya ci ba. A yunwar da yakeji ai gara ma ta bashi kunu akan wannan mashed abin. Gudun karya bada kanshi ya dinga turawa yana hadiyewa yana rokon Allaah Ya kiyaye shi da bacin ciki, saboda cikinshi bai cika son bakon abu ba. Har wani numfashi ya sauke lokacin daya ajiye dan kwanon ta bashi filet
"Bari inzo Habibi, dan Allaah ka cinye komai"
Cewar Aziza tana tashi, yaji dadin bashi wajen da tayi, tana ficewa kan tsiren da yake ciki ya fara, yayi masa dadi sosai, yaso ace shine yafi komai yawa, sai kuma yaci samosa da spring rolls, shima sunyi masa fiye ma da tsiren, kamar ya bude sauran kwanonin ya kara haka yakeji, ya dauki lemon data tsiyaya masa ya kurba, akwai sanyi, amman dai bai gane ma dandanon lemon ba, yayi masa wani daci-daci saiya ajiye
"Sufa 'yan gayu harshensu ma kamar daban yake dana sauran mutane"
Ya raya ma ranshi, yanata barin abinda yake tunanin yamballs ne daga karshe saboda soyayyar da take tsakaninsu, idan Jamila tayi wuni yake yana ci, ya kudurce a ranshi zai siyi doya gobe tunda ta fada masa sauranta ne ta soya musu jiya, ya dan ajiye filet din yana, daya dauka dai sai yaji shi sakat a hannunshi, gashi da girma, amman baiyi masa nauyi kamar yanda ya sani ba. Sannan daya kalla da kyau ma, bayan abin kamar ba kwai bane ba, yadai yi kyan suya, sai kawai ya jefa shi a baki duka yana taunawa. Sai yaji kamar kubewa ce a tsakiyar, gabaki daya komai da yaci ya nemi dawo masa, ba arziki ya fito dashi daga bakinshi, sai kuma tunanin inda zai saka shi ya dinga masa yawo, cikin hanzari ya mike kamar zai kifa yana ficewa ya tura kyauren gidan ya jefa shi ya dawo ya zauna, lemon daya ajiye ya dauka ya kwankwade saboda zuciyarshi da taketa hargitsawa
Gabaki daya ba haka ya hango yau din ba, sai yakejin inama jiyan yazo, ya tabbata abinda ta shirya masa jiya yafi na yau nesa ba kusa ba, kawai dai ita din da kuma kwalliyarta ne suka danne masa rabin disappointment din, sai gata ta dawo dakin da sallamarta tana dorawa da
"Afuwan Habibi, kasan Matar Officer na gidan, yau nan tayi buda baki, nasan yanzun mijinta zaizo daukarta, akwai ajiyarta a wajena"
Matar Officer kamar yanda Aziza take kiran Yayarta Jalila dashi, daga Jalilar sai ita, tazarar shekaru biyu ce a tsakaninsu, sai dai Jalilar tayi aure da wuri, dan yanzun haka ma yaranta uku. Kuma daga yanda Aziza take yawan maganarta, akwai shakuwa mai karfi a tsakaninsu
"Haba ni da kin gama cikamun cikina, ga aiki na baro a shago, anya ma zan iya asham yau?"
Sai tayi dariya ta karasa cikin dakin sosai tana zama a gefenshi
"Baka cinye ba, ga cheese balls dinma baka cinye ba, kuma saboda kai nayi"
Ta karasa cike da rashin jin dadi a muryarta
"Cikina ya cikane sosai, naci daya dan yayimun kyau a ido"
Sai ta dan saki fuska
"Aikam sai in juye maka ka tafi dashi"
Baiyi musu ba, wannan ai mai sauki ne saiya cillar dashi a hanya koya samu wani almajiri ya bashi. Koma wanne abu dai, hira suka dingayi cikin nishadi. Ana fara kiran sallah yace mata
"An kiramu"
Ta turo baki
"Bangaji da ganinka ba"
Murmushi yayi
"Ni akace na gaji da ganinki ne? Gashi da wahala in sake samun damar zuwa kafin sallah idan Allaah Ya kaimu"
Aikuwa tayi kwal-kwal da idanuwa har yana hango kyallin hawaye a cikinsu, duk yaji ya susuce
"Kar muyi haka dake Babe, ga waya fa, ga video call"
Hawayen ta bari suka zubo
"Wanne video call? Abinda daka shiga gida baka yarda muyi saboda matarka, bayan nima yanzun ina da hakki akanka tunda ai aurena zakayi..."
Da sauri yace
"Inji wa ya gaya miki saboda ita ne? Nifa na isa da gidana, abinda nake so shi zanyi"
Aziza taja hanci tana kara narke masa
"To me yasa idan na kiraka baka dagawa? Aiko ba zakayi magana ba saika daga in ganka"
Ya jinjina kai
"Zan dauka, shikenan? Dan Allaah ki share hawayen nan bana sonsu"
Duk da haka saida ya kara bata lokaci yana lallashinta da yi mata alkawura kala-kala duk da yaji an tayar da sallah. Ya ajiye mata dubu goma cifa, sababbin yan dubu-dubu. Yaji dadin yanda ta manta da hadashi da wannan cheese ball din. Daya fito ne ma sukayi kicibis da Jalila tana tsaye, bayanta goye da karamin Jawad, sai Jabir da Jafar da suke gefenta, ga wata katuwar leda data ajiye a gabanta, zuciyar Aziza ta tsinke, kar dai har yanzun Balarabe baizo ya daukesu ba
"Habibi ga Adda Jalila ku gaisa"
Cewar Aziza cikin karfin hali ganin idanuwan Baffa akansu ya fara sauka, ta kalli Jalilan tana fadin
"Matar Officer ga Habibina"
Duk da Baffa yasan ya girmeta haka ya dan rage tsaho yana gaishe da ita, ta amsa shi fuska a sake
"Kinga kila ma ciki zan koma, yanzun Officer ya kirani wai kaman ya taka abune tayarshi tayi faci"
Jalila ta fadi
"Babur din Baba ne yayi faci?"
Jabir ya fadi yana kallonta cikin maganarshi da bakowa bane yake ganewa, Aziza tayi saurin kallon Baffa da alama baiji abinda akace bama, dan hankalinshi naga masallaci da har anyi raka'ar farko, tunda da alwalarshi yacewa Aziza
"Bari kiga inyi sallah kafin in wuce, lafiya kalau mashin dina idan na barshi anan?"
Kai ta daga masa da sauri, dan unguwarsu tana da tsaro sosai duk kuwa da yawansu, akwai karancin sace-sace musamman irin wannan lokacin ma da jama'a suke hada-hada. Baffa na shigewa tana juyo karar mashin din Balarabe tun daga kan kwanar layinsu kamar babu salansa a jiki, suka hada ido ita da Jalila cike da takaicin da har yau basu daina shakarshi akan wannan mashin din nashi ba. Saikuwa gashi nan ya karyo kwanar, kana hango sabon uniform dinshi shar
"Officer take aure ashe, soja ne ko dan sanda?"
Baffa ya taba tambayarta da tace masa tana gidan Jalila din tana kiranta da Matar Officer, farko-farkon haduwarsu, babu shiri ta katse hirar da fadin
"Minti daya Habibi"
Ta kashe wayar, tunda ai ba zata sharo masa karya ba, idan aurenta zaiyi dole wannan likon zai cire, ta ina zata fara ce masa Balarabe dan karota ne?. Ko gaisawa bata tsaya sunyi ba, dan kafin ya karaso ta cewa Jalila
"Adda sai munyi waya"
Ta shige gida abinta. Baffa kuwa ana sallar nan kamar an kara zazzage masa hanji haka yakeji, gashi limamin nan kamar ya zabi yayi tilawa ne a sallar asham din, kafafuwan Baffa har sanyi sukeyi kafin ayi ruku'u. So kawai yakeyi a idar ya karasa gida ya dirarwa koma menene Jamila ta tanadar masa, Allaah Yasa tayi zobo, dan yau jinshi yakeyi kamar baisha abinda ya kai masa inda ya kamata ba.
#LubnaSufyan ✨
#WomenOfWords
#09035723778
Littafin nan na kudine akan #1k kacal, zaizo a manhajar Telegram 10/12/2024 In Shaa Allaah, bayan mun kammala shafukan dandano.
9035723778
Opay
Lubabatu Sufyan
Saika turo shaidar biya ta lambar da take sama. Nagode da addu'a'inku, nagode kuma da kwarin gwiwar da bakwa gajiya da bani
*
Duka littafin nan sadaukarwa ne ga Marubuciya Aisha Shafi'i, idan kunci karo da littafin nan, kun nishadantu, kun karu ta kowacce irin fuska, ku rokawa mijinta Isma'il Rahmar Allaah, ku roka mata sauki da juriyar rashin shi, ku rokawa yarinyarta rayuwa mai albarka. Nagode
MATAR HABIBI
4
(Free page)
Adai-daita na ajiyeta, ta dauki katon kwandon data hada komai a ciki, don da taga almajiri ma shi zata ba ya dauka ya tsallakar mata dashi saita bashi ko Naira dari ne sadaka. Kwandon yayi mata nauyi, haka ta kinkima saboda wani mai mota daya gansu a tsaye, mata su wajen biyar saiya daga musu kafa suka samu suka tsallaka, sai nishi takeyi, ta ajiye kwandon a kasa dan ta numfasa. Ta godewa Allaah da