dan haka dole yayi abinda bayaso, aiki da keken dinki wanda bana wuta ba.
Zuwa la'asar duk ya zazzage dan abinda yayi saura a cikinshi, ga ciwon cinyoyi da yakeji duk sun rike, kwata-kwata baima samu natsuwar danna waya ba, yama manta a silent ya sakata har sai bayan ya dawo daha Tarawih din nan, sai abin ya fado masa, ya riga yasan dole zai sha mita wajen Aziza. Yana duba wayar kuwa ya samu ta kirashi babu adadi, ga sakonni ta text da WhatsApp ta bar masa har yana rasa ta inda zai fara karantasu, sai kawai ya fara da tura mata da gajeran sako
"Ayimun hakuri Babe, yau abubuwane suka rincabemun a shago, wayar kuma tana silent. Nayi missing dinki da yawa"
Saida ya tura ya fara bin nata sakonnin, sai kuma zuciyarshi ta buga daya tuna yau yayi mata alkawarin zuwa yayi buda baki a wajenta, tun kwanaki biyar da suka wuce sukayi wannan tsarin, ya tabbata ta shirya masa shagali, lokaci daya yaji ranshi ya baci, musamman ma da ta dawo masa da sakon daya tura da
"Ka kusa? Inata jiranka tun dazun. Gashi har tara saura"
Yana shirin kiranta ne Jamila ta shigo, shisa ya tashi ya shiga dakinshi yana addu'ar Allaah Yasa karta biyo bayanshi, yasan halinta da naci wani zubin
"Dan Allaah kiyi mun hakuri Aziza, dan Allaah..."
Yake fadi cikin magiya da kwantar da kai saboda yanda Aziza ta birkice masa, kamar ma kuka takeyi
"Ni ba sai kaci anan ba, kazo ka dauka kawai dan bansan yanda zanyi da abubuwan nan dana shirya maka ba"
Muryarshi ya karayin kasa da ita
"Na fada miki da zazzabi na dawo, yanzun haka ina cikin bargo a kwance, dan Allaah kiyi hakuri, ki sakamun komai a firij, na miki alkawari gobe In Shaa Allaah zanzo da wuri ma"
Wani shiru ya ratsa a tsakaninsu kafin tace
"Hmmm..."
Gabaki daya a gajiye yake jinshi, bayajin ma yana da cikakke karfin fita da mashin din daya riga ya shigo dashi, balle harya falla unguwarsu Aziza
"Ke kinsan babu yanda za'ayi haka kawai da gangan inyi missing din abubuwan da nasan kin shiryamun, kinsan yaushe rabon da inji wani abu mai dadi a bakina?"
Cike da shagwabarta da take kara narkar dashi tace masa
"Habibi saboda zuwanka fa nace yau 'yan gidama suci albarkacinka nayi tortilla da sauce din kwai"
Duk da in za'a tsire shi baisan meye tortilla din ba, amman yanda ta fade shi tanayi kamar zata taune harshenta yasa Baffa hasaso wani abu da yaji naman kaza a cikin kanshi, ga kuma kwai data kira
"Duk ki ajiyemun dan Allaah..."
Bai sauke wayar ba saida ya tabbata Aziza ta hakura, musamman daya fara dauko mata hirar daya kula tafi faranta mata rai akan komai, hirar yanda in ta shigo gidanshi zata wanke masa takaicin rashin iya girkin Jamila, za kuma ta zame masa fitilar daya jima yana nema, a takaice dai, Baffa yace mata
"Kina saka inaji kamar sai yanzun zanyi aure Aziza, kamar banma san iya abubuwan da na rasa ba sai yanzun da kika shigo rayuwata..."
*
Maza nawa ne irin Baffa?
Mata nawa ne irin Jamila?
'Yan mata nawa ne irin Aziza?
Kun shiryawa wannan tafiyar kuwa?
#LubnaSufyan ✨
#WomenOfWords
#09035723778
Littafin nan na kudine akan #1k kacal, zaizo a manhajar Telegram 10/12/2024 In Shaa Allaah, bayan mun kammala shafukan dandano.
9035723778
Opay
Lubabatu Sufyan
Saika turo shaidar biya ta lambar da take sama. Nagode da addu'a'inku, nagode kuma da kwarin gwiwar da bakwa gajiya da bani
*
Duka littafin nan sadaukarwa ne ga Marubuciya Aisha Shafi'i, idan kunci karo da littafin nan, kun nishadantu, kun karu ta kowacce irin fuska, ku rokawa mijinta Isma'il Rahmar Allaah, ku roka mata sauki da juriyar rashin shi, ku rokawa yarinyarta rayuwa mai albarka. Nagode
MATAR HABIBI
2
(Free page)
Yau kam fuskarshi ta nuna rashin jin dadinshi sosai
"Nifa naji wani Malami na wa'azi in dai har sallar dare zatasa ka makara gara ka hakura da ita"
A nutse take kallonshi
"Babansu ai ana maganar sallar asuba ne, yau kuma bamu makara ba yanzun ma ake shirin tayarwa"
A hasale ya amsa ta da
"Amman ai mun makara sahur ko? Kinsan irin wahalar da na sha jiya kuwa Jamila? Gaskiya kisa alarm a wayarki yau"
Kai ta jinjina masa
"Kaje karka makara sallah"
Kamar ba zai tafi ba sai kuma ya wuce, ta tabe baki, jiya bayan ta kwantar da Nana tayi mata addu'a sosai, da batayi niyyar zuwa dakinshi bama, sai kuma ta sake kayan jikinta zuwa doguwar rigar bacci da ta wuce har kwaurinta, ta kara goga humra, ta nemi hula ta saka a kanta sannan ta tafi, a kwance ta sameshi yana danna waya, da yake wutar dakin a kunne take saita kashe, tabi hasken wayarshi har zuwa kan gadon, kafin ma ta gyara kwanciyarta yace
"Nifa a gajiye nake ba wani abu zan iya yi miki ba"
Maganar tayi mata bambarakwai, a lokaci daya kuma wani abu yazo yayi mata tsaye a makoshi, tasan shi din ba wani mabukaci bane ta wannan fannin, saboda kaso tamanin cikin dari na lokutta itace take binshi, kuma tasan tana iya kokarinta wajen yin gyara, shi ba ma'abocin bada kudi bane ba, sai ayi watanni kyautar kudi bata gifta a tsakaninsu ba, ko roka tayi kuwa bako da yaushe yake bata ba, saima kaji yana mitar
"Kin cika kashe kudi Jamila, meye zaki siya da baki dashi a gida?"
Amman kyautar da 'yan uwanta suke mata lokaci zuwa lokaci tunda sun san ba sana'a takeyi ba, a ciki take dauka tana siyan magungunan mata, maganin sanyi kam wannan baya yanke mata sam ko dan yanda ake kara jaddada amfanin yawan shanshi ga mace ko da bata da aure balle kuma mai aure. Da kanta a WhatsApp ta fice daga cikin groups da dama na matan aure saboda yanda in an samu wata mai maganin matan, suka siya aka gwada za'azo ayita sharhi, kaji wasu suna bada labarin yanda miji ya manne musu, wata ma zatace
"Nifa da niyyar kwana biyu yazo, amman kinganshi nan yana maganar ya kamata ace wannan komawar dani ya koma"
To ita kuwa duk wani doki da rawar kai a wannan harkar Baffa yayi mata itane a cikin watanni ukunsu na farkon aure kafin ta fara laulayin cikin Arif da yazo mata da zafi, daga baya kuma sai taga kamar abin koya fita daga ranshine, yanayin wannan hirar da take gani tsakanin mata, ita kuma inta siya tayi amfani dashi sai taga dai babu wani canji ta bangaren Baffa, saima ita da wasu magungunan zata ga kyansu, wasu kuma inta sha idan sun cika bauri ta wuni cikinta na murdawa. Sai kuma takeji kamar ta daina burgeshi yanzun, wannan soyayyar duk ta disashe. Amman duk da haka kai tsaye bai taba bude baki ya fada mata magana mai zafin ta yau ba. Idan ma gajiyar yayi to zai kyaleta ne ta shige jikinshi sosai ta kwanta.
Yanda gwiwoyinta sukayi mata sanyi yasa ta kasa tashi tabar masa dakin, zuciyarta ta dinga mata zafi, musmaman ma data ga ya juya kwanciyar shi yana matsawa ya bada tazara a tsakaninsu. Ta rufe idanuwanta da sukeyi mata yaji-yaji, bata kasance cikin mata masu saurin kuka ba, asalima abinda zai saka hawayenta zuba ba karami bane ba, ta dinga jero duk wata addu'a da tazo bakinta ko zata samu saukin zafin da kirjinta yakeyi, ashe bacci ne ya dauketa a haka, bata sani ba sai data fitsari ya tasheta tunda ta daddaki zobon da tayi babu laifi. Bataga alamar Baffa a kusa da ita ba, saita dauka ya shiga bayi, shisa ta nufi kofa ta bude da nufin tafiya dakinta, kuma har zata wuce saita dinga juyo karar kiran wayarshi daga falo.
Da mamaki ta nufi falon, yana kwance kan doguwar kujera yana bacci, ga wayar nan a kasa da alama subuce masa tayi bai sani ba, daman Baffa da bacci, sau nawa ko kiranshi akayi ita kiran saiya tasheta shi yana baccinshi. Ta karasa ta dauki wayar, sai dai tana dauka kiran na yankewa, zata ajiye masa a gefenshi sako ya shigo, kuma da yake ko a mukulli take zaka iya karanta sakon ta saman inka dan taba, haka kawai taji tanaso ta karanta, anyi saving din lambar da "AZ" kawai.
"Habibi bacci kayi ko? To bari in tashi inyi sallah in rokar mana Allaah Yasa next azumi kana gefena zakayi baccin nan"
Wani duhu-duhu ya nemi rufe mata ido, musamman da wani sakon ya kara shigowa
"Ina sonka sosai. Allaah Ya kulamun da kai Habibi Na, sai anjima In Shaa Allaah dan yau gara na kwana a zaune da in bari kayi dorere"
Daman haka kishin yake? Duk wanda take zato tanaji a baya karya ne, yanzun ne tasan yanda yake. To taya mata suke iya danne shi? Ya suke kallon mijinsu ya ketare ya tafi dakin wata matar batare da zuciyarsu ta kama da wuta ta kone ba? Ita gata, sako kawai tagani amman zuciyarta kamar tana gab da zama toka saboda yanda takejin tana ci da wuta. Sai gashi tanajin alamar hawaye suna neman zubo mata, ta ajiye masa wayarshi inda ta ganta a kasa, ta wuce dakinta da kudiri daya. In Shaa Allaah har a karasa azumi nan da kwanaki bakwai ko takwas ta gama tashin shi Sahur, ita AZ din saita tashe shi kafin azumi na gaba din da zasuyi tare saita dora daga inda ta tsaya a wannan din.
Yau ko dar bataji bama, dan daya shigo dakinta bankan-bankan lokacin ma da hijabinta a hannu
"Ke Jamila wai wanne irin abune ya sameki yau ma?"
Ya fadi bayan ya turo kofar
"Kasan goman karshen nan, sallah jima inayi, sai na dan kishingida sai yanzun na tashi naji anata kiraye-kirayen sallah, to alwala nayi ma yanzun nake shirin zuwa in tasheka"
Taji ranta yayi mata sanyi-sanyi ganin nashi ran a bace, a nutse tayi sallarta ta idar tana zaman Azkar. Tana idarwa ta koma tayi kwanciyarta.
*
Wajen Azahar tana zaune tana firar dankali, Nana kuma ta gama kukan faduwar da tayi da keken Arif ta buge bakinta har saida yayi jini, shine ta samu take baccin wahala, tayi mata shimfida anan tsakar gidan. Da yake gidan inka shigo gate, akwai wata yar haraba da har mota ma za'a iya parking dinta kuma a samu waje, sai ka kara shigowa wata kofa da zata hadaka da cikin gidan, daka shigo kofar akwai dan filin tsakar gida da ba wani girma ne dashi ba, daga gefe kitchen ne wadatacce anyi masa kanta mai kyau daga ciki, da yake itama ba wani tarkace ne da ita ba sai tsarin kitchen din yayi kyau. Akwai karamin bandaki a tsakar gidan, sai kuma wata kofa da inka shiga itace zata sadaka da falon Jamila, a cikin falon akwai daki daga hannun dama, inda ta mayar dashi dakin yaran, sai kuma daga hannun haggu dan dogon corridor ne da zai sadaka da dakuna guda biyu da suke kallon juna, daya na Jamila, dayan kuma na Baffa, kowanne daki kuma da bayi a ciki.
Tsarin gidan yayi kyau, dai-dai na masu rufin asiri. Sai dai yanda Baffa yake gaya mata tsarin saman ne yasa taji son wajen ya kara kamata, tunda yace a falon har wajen dining za'a fitar, sannan kuma kitchen a ciki za'ayi shi shima, ba kamar na kasan da yake a waje ba. Irin dai tsarin gidajen 'yan gayu. Abinda kawai take so da kasan shine tsakar gida, dan ita tanaso ta fito taga sararin samaniya lokaci zuwa lokaci, bawai kullum kana cikin daki ba. Har mamakin irin gidajen da basu da tsakar gida kwata-kwata takeyi.
"Mami waken duka zan tsince? Akwai yawa fa"
Asaad ya fadi cike da kosawa, tayi 'yar dariya. Shi Arif in dai akwai kallo tofa bashi da lokacin komai tunda yarone marar hayaniya, komai nashi da sanyi-sanyi yakeyi. Asaad kuwa irin yaran nan ne masu kulafacin uwa. Baiki duk inda tasa kafarta ya mayar da tashi ba, gashi da son aiki, shisa bata rasa abinda zata bashi ya tayata ko danma ya zauna waje daya
"Duka zaka tsince dan albarka, kayi maza kagama in baka ka dakamun maggi"
Aikuwa saiya kara maida hankali, dan yanason ta bashi dakan abu a karamin turminta, kwankwasa gidan da akayi yasa ta ajiye firar dankalin taje ta bude, tun daga kofar suka fara gaisawa da Rufaida. Wata mata guda daya da tun ranar da suka dawo unguwar suka fara mutunci saboda kirkinta, itama tace basu fi shekara biyu da dawowa unguwar ba, tana da yaranta hudu
"Dan Allaah ki taimako mun da flavor in kina da milk zansa a kunun aya, ragowar Intee ta mungular mun dashi"
Cewar Rufaida bayan sun gaisa da Jamila
"Allaah Ya shirya mana yaran nan, gashi kai ba abin ka jibgi kudinka ba"
Kai Rufaida ta jinjina
"Inka biye musu ai karyasu zakayi 'yan albarkar"
Daki Jamila ta shiga tana barin Rufaida da Asaad da yake gaishe da ita, tunda dan karamin firij din nata a falo yake, data ajiye shi nan tsakar gida rana ta hanashi abin kirki, a kitchen kuma ya cike mata waje, saita mayar dashi falo tayi masa waje tunda falon wadatacce ne. Data fito ta kawo mata ne take ce mata
"Kinga wata gumba ce aka kawomun naji dadinta wallahi, kin aiko Arif ya karbar miki na manta dana fito miki da ita"
Tabe baki Jamila tayi
"Dan Allaah ki rabani da 'yan shaye-shayen nan ina azumina"
Hararta Rufaida tayi
"Wannan gumbar yanda kikasan kina shan madara da kantu haka zakijita, kefa mazan yanzun saida gyara"
Yanayin fuskar Jamila dai inka gani kasan yau zancen bai zauna mata ba sam, saima yake tuno mata da wulakancin da Baffa yayi mata jiya
"Wannan duk baya hanasu karo aurensu insun tashi"
Dariya Rufaida tayi sosai
"Allaah Ya shiryaki wallahi, to ke ina ruwanki da karo aurenshi? Daman ai bawai zaki gyara bane dan karya karo aure, a'a taki mafitar zaki duba, ki gyara dan ki samu naki matsayin a wajen shi, in kika tsaya wallahi 'yan matan nan na yanzun da suke da ido a tsakar kai sai su sa kwabarki tayi ruwa"
Dan jim Jamila tayi tana tauna maganganun Rufaida din, wata irin shakuwa ce ta shiga tsakaninsu kamar sunyi shekaru tare, dan Jamila zatace ita dai a yanzun bata da kawa kamar Rufaida, kuma sukan tattauna matsalolin da ba'a rasa duk wata mace dashi, musamman ta maza, su ba juna shawara
"Hmmm..."
Jamila ta iya fadi, kuma yanayinta yasa Rufaida ta fahimci cewa tana da damuwar da bataso ta fito fili ta fadi
"Karki yarda ki bar mijinki a hannun wata, musamman ma yarinyar da duk wani feleqe da takeyi kokarinta ta taddoki ne, kibari inta shigo sai kiyi lokacinta, amman yanzun kam ki kara rike mijinki"
Haka Rufaida ta dinga bata shawarwari kala-kala har saida taga tana aminta da maganganunta, ta kuma kira Arif tace ya bita ya karbo mata gumbar. Rufaida na fita bata jima ba, dan dawowar Arif kenan shima ya ruga daki dan ya cigaba da kallon shi, taji wayarta na ringing, ta dauka tunda tana nan ajiye a kusa da ita. Baffa ne, ta daga tasa a kunne hadi dayin sallama
"Mamin yara"
Ya fadi daga dayan bangaren yanasa tayi murmushi, kafin kuma ta amsa ya dora da
"Daman zanji ya kuka wuni ne? Ina yaran? Kinata aiki halan?"
Sai taji wani sanyi ya ratsa zuciyarta, akace abubuwan da mata suke so daga wajen mazajensu ba masu yawa bane ba, kulawa komin kankantarta na daga cikin wannan abubuwan, ta manta rabon da haka kawai Baffa ya kirata a waya. In kuwa ya kira to sako zai bata, ayi masa wani abin, ko ita ta kirashi suna bukatar wani abu, da takan kira inya tafi dan taji ya ya isa shagon sai yace mata
"Daman shikenan abinda zaki fada? Kai kema dai kina da rigima, sai kace wanda zai bace a hanya"
Irin wannan sage gwiwar da yakeyi mata kan abubuwa da yawa yasa ta hakura ta yakicewa kanta yi masa su tunda basa burgeshi. Ko kuma ita dince ta daina burgeshi ba zata iya cewa ba
"Bama aikin da nakeyi, dankali ne nake ferewa"
Ta fadi muryarta cike da annashuwa
"Akwai saura ne har yanzun? Ko in bada a karo sai a kawo muku?"
Kai ta girgiza tanata murmushi
"Akwai fa, kasan shi saurin lalacewa yakeyi, kuma azumin ma yazo gangara"
Tunda ita dankalinma baya cikin abubuwan da suke burgeta, saita soya shi sau nawa bataci ba
"To shikenan, kinga dinkunan nan da yawa, daman ince miki karki wahalar da kanki yau ba zan dawo gida da wuri ba, mun nemi wani abin muci anan. Kiyi abinci mai sauki kawai na sahur"
Lokaci daya taji wani abu ya haska cikin kanta
"Me kake so a dafa maka?"
Dariya yayi
"Kome kika dafa ai kinsan zanci"
Saita jinjina kai
"Zan dan fita anjima to tunda ba zaka dawo da wuri ba"
Dariyar ya sakeyi
"Kafarki ce take kaikayi daman, Allaah Ya tsare, ki dauki dubu biyu a dakina inda nake ajiye kudi saikiyi kudin mota..."
Ta fara jera masa godiya
"Wai ina ma zakije matar nan?"
Saita kama dariya
"Badai kace kabarni ba?"
Shima dariyar yakeyi
"Bazan biye miki ba, bari inyi aikina koma ina ne a dawo lafiya. Ki kula da kanki dai, kar kuma ki dade"
Ta jinjina kai, saida tasa hannu tana share wata yar kwallar farin ciki, yaushe rabon data jita cikin nishadi haka? Yaushe rabon da Baffa ya biye mata suyi hira cike da kulawa irin wannan? Harta manta, waya kuwa ko history ta duba na shekara daya basuyi wayar data wuce yan sakanni ba dashi, tunda yana gama fadar abinda zai fada yake kashewa batare ma daya jira tace wani abu ba, hira kuwa tunda ya gane mayi da 'yan matanshi inya dawo ta yanke a tsakaninsu, saita kirga magana nawa take hadasu inya dawo gidan kafin su kwanta.
"Asaad ajiye tsintar waken nan haka..."
Tace tana tsame hannunta daga cikin dankalik ta tafi ta dibo cefane ta hau gyarawa, bayan ta wankesu, ta dauko wani kwali da busashen kifi yake a ciki, Yayanta Kabiru ne ya kawo musu tsarabar shi daga Jos inda yake aiki, da yawa ta diba ta zuba a wata tukunya ta yanka albasa ta zuba citta da tafarnuwa, dan Allaah Yayita da jin karni matuqa, in zatayi amfani da kifin saita fara tafasa shi haka ta zubar da ruwan, tukunna ta zauna ta gyara shi ta cire kan da kaya. Cikin wani lokaci sai gashi ta gama miyarta mai yawa. Yau kam yanda ya faranta mata rai, itama saita faranta mishi.
Zata bashi mamaki, kayan buda baki zataje ta kai masa har shago, yaran shagon nashi ma sai bakinsu ya canza yau, ba zata