x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 7 - K'ADDARAR SO

  • 18001 words
  • 20867 words
  • Out of 20867 words

Category: Love Stories

Views 120

20 Jul 2025
Start ads
After Image Ads
bazan iya cin komai ba, garama na bari yunwar ta kashe ni da wa'innan kafuran Allah Ta'ala su kashe ni"

"A'a Fulani ki iya bakinki ki daina cewa haka please, karma suji ki kizo muce tare kawai idan ba haka ba nima ba ci zanyi ba"

Da sauri ta waiga inda Husaina take girgiza kai tayi ta matso tana cewa "shikenan mu ci tare"

Da kanta Fulanin tayi ta ba Husaina abincin a baki, wadda bata lura ba ita Husainar duk rabi ita ta ci sa, loma d'aya kawai Fulani tayi tabar mata sauran tana bata a baki, ko ruwan ma Fulani ba wani sha tayi ba.


Washe gari ma basu samu abinci ba, kusan kwanan su had'u yau kenan a wajan, a yanzu sun gane idan aka basu abinci yau to gobe fa babu maganar cin wani abincin.
Ko a ranar bazai wani wadace ka ba, abinci kamar wadda za'a ba kyanwa shi.


Wata irin kururuwa had'e ihu, su Fulani suka ji. Kai ba shiri suka zabura suna kallon inda ihun ke fitowa. Zare ido Fulani tayi gabanta na wata irin mummunar bugawa.


"Wayyo Allah na shiga uku ku taimaka min zai lalata min rayuwa, wayyo Allah ba wadda zai taimaka min ne?"

Fulani bata san sadda ta ce "Fyushind'o, Innallihi wa'inna alaihir raju'on, su kuma wa'innan harda fyad'e suke ma yara mun shiga uku, nan gaba muma zai iya zuwa kanmu"

Kwata-kwata duk mutanan dake wajan hankalin su yayi mummunan tashi ganin cewa su harda lalata yaran mutane suke, shi yasa kenan suka jido y'an mata, wadda suka kashe masu iyaye ba wadda zai kawo kud'in fassarsu, anfani zasuyi rink'a yi da su kenan?.

Wani kalar kuka Fulani ta saki tana shigewa jikin Husaina sosai kamar wacce zata koma ciki, Husainar ma hawaye take wadda tsabar tashin hankali da firgice har saida taji d'an cikinta ya mata wata irin juyawa, wadda har saida ta d'an saki y'ar k'ara. Ba shiri Fulani ta saketa tana dubanta hankali a tashe tana tab'a cikin tana cewa "Y'ar uwa ko haihuwa ce zakiyi muna cikin wannan tashin hankali?".
Girgiza mata kai kawai Husaina tayi, amma ita kad'ai tasan azabar da take ji a yanzu.

Ga Fyeshind'o dake kururuwar ihu, ba wadda yayi gangancin nufar inda aka aje Fyeshind'o y'an Ta'addar sun zagaye wajan da Bindigogi ga Ogan nasu wani rusheshe dasu yana niyar kwab'e wando, kai tsabar rashin kunya da rashin imani ma a gaban jama'a a bainar nasi yake shirin keta ma y'ar yarinya haddi.

Fulani ta kasa kallon inda abun ke faruwa, kuka take kawai jikinta na d'aukar wata irin kyarma, daga ita har Husainar hankalinsu a mugun tashe yake, da za'a auna su a wannan lokacin to za'a iya cewa jininsu yayi mugun hau sosai.

Wani tsoho ne wadda shi an dad'e da kawo shi wajan ya tashi yana isa inda Ogan ke shirin keta haddin baiwar Allah, ya d'uke k'asa yana rok'ar suyiwa Allah karsu lalata wannan y'ar k'aramar yarinya.

Wata hanb'ara da sukaima wannan tsoho ya tafi ya bugu da k'asa hancinsa ya fashe, kamin ma ya dawo hayyacinsa kawai suka ji saukar harsashi had'e da k'arar Bindiga. A saitin kansa suka halbesa ko shurawa baiyi ba.

Bakin Fulani bud'e yake kowa dake wajan yayi shuru kamar anyi ruwa an d'auke masu taya Fyeshind'o kuka, suma kukan ya yatsa cak yadda wajan ya d'auki shuru kai ka ce babu halittar dake rayuwa a wajan. Husaina kuwa d'an cikinta ne ya sake motsawa, had'e da naushinta, runtse idonta tayi da mugun sauri tana dafe mararta jikinta ya fara d'aukar kyarma, zufa ta fara keto mata. Ita kam yanzu tasan haihuwa ce tazo mata ba shiri tashin hankali yasa haihuwa zuwa a sadda lokacinta baiyi ba.

Wani d'an Ta'adda ne ya juyo inda suke cike da muryarsa marar dad'in ji ya ce "duk d'an iskan daya k'ara zuwa wajan nan da sunan ya rok'e mu idan muna aiwatar da abu, to zai tafi inda muka aika wannan tsohon".

Tsoro ne ya k'ara rufe su. Wadda suke kukan ma dole tasa suka toshe bakunansu, hawaye ne kawai kake iya gani na zuba a fuskokinsu.

Fulani hankalinta ya rabo kashi biyu, danta lura wallahi fa Husaina haihuwa ce tazo mata a wannan hali. Kamin su gama dawowa hankalinsu suka ji Fyeshind'o ta kwallara wata gigitacciyar k'ara had'e da cewa ta shiga uku ya kashe ta.

A sadda ya keta mata mutumcinta da rashin tausayi da rashin imani kuma, saboda da mugunta da k'arfi ya shigeta.


A dai-dai lokacin kuma Husaina ta saki wata irin gigitacciyar k'ara had'e da salati a bakinta.

Ba shiri wani daga cikin y'an Ta'addar ya ce "kai kardai waccar matar haihuwa zata mana a wajan nan?, Ai ko kuje ku tsaya inda take tana haihuwa ku amshe abunda ta haifa ku kashe shi, domin baza mu zauna da jariri yana damun mu da kuka ba"

Husaina da Fulani na jin wannan abu hankalisu ya k'ara tashi ainun, Husaina ta damk'e hannun Fulani tana girgiza kai cikin azabar ciwo ta ce "Fulani kiyi min al'k'awarin cewa duk wuya karki bari azzaluman can su kashe abunda na haifa, nabar miki komiye na haifa halak malak Fulani ni nasan mutuwa zanyi, Fulani ki ceci kanki da abunda na haifa dan Allah"
"Innallihi wa'inna alaihir raju'on" kawai Fulani ke iya cewa tana rik'e da hannun Husaina ta tare ko ina, ga y'an Ta'addar da suka zagaye su.





*FUNTUWA LOCAL GOVERNMENT KATSINA STATES NIGERIA*


"Ke Nana zaki fad'a mana, gidan ubanwa kika samo wannan kud'in, ko sai na mak'ure kin mutu kowa ma huta?, Ashe dama acan Abujar haka kike yi gidan mutane yawon bazan, da tsayawa da samarin banza?, Suke baki wa'innan kud'in ko kuwa?"
Cewar Inna Saude dake zaune a Babban parlon, gidan da take aiki. Da aka aika kiranta yau tazo an dawo mata da d'iyarta Nanah a bisa da bata jin magana ko kad'an, a can Abujar. Shi yasa tajawo Jafaru suka taho tare suna matsifa yarinya zata ja masu salalan tsiya, so take d'an arzik'in da suke ci a yanke masu cinsa.

Kawu Jafaru ne yayi kukan kura ya zafga mata marin daya sa ta wuntsila ta fad'i tana sakin kuka. Ya ce "kin ga y'ar banzar yarinya ana miki magana kina banza da mutane kaga y'ar iskar yarinya, y'ar bak'in ciki, so kike kiyi mana bak'in ciki kenan?"

"Ya isa haka Jafaru"

Cewar Mai gidan,

"Wallahi ranka ya dad'e daka barni na barta kwance dole ta sanar damu gidan ubanwa ta samo kud'in nan"

Kamin ma Jafaru ya rufe baki Inna Saude ta tashi haye ruwan cikin Nanah sai duka take kamar ta samu k'ato.

"Subhanallahi ke Saude miye hakan?"

Cewar Alhaji yana ma Inna Saude tsawa. Dakatawa tayi da dukan nata tana cewa "Alhaji daka rabu dani in kasheta kawai wallahi. Kuma zaki fad'a min gidan uwar da kike samu kud'in nan, ko ki bari idan muka koma gida, insa wuk'a in kashe ki kowa ya huta, ni daga baya an d'aure ni"


Kuka Nanah keyi harda majina tana cewa "wallahi Inna kud'in makaranta ne fa da suke bani nake tarawa suka zama haka"

"Rufe min baki munafuka, kud'in makarantar ne zasu zama haka, algunguma sababbin kud'in bugun Abujar da nake gani yanzu sune kud'in makarantar"


Jannat da ita ce akaba Nanah take zaune wajanta ta ce "ni dai Daddy daka bari munbar ta wajan iyayenta, domin kaga yanzu ma k'arya take gaya ma iyayen nata, mu da ba bata wasu kud'i muke ba, komai muna dashi a gida, idan zata tafi babu abunda bata dafawa domin tafiya dashi har biskit da alawa ina ajewa a gidana domin dai ita da Hana idan zasu school na basu. Na maida ita kamar fa ba y'ar aiki ba kamar y'ar uwata haka na d'auke ta"

Kamin ma Alhaji ya ya ce wani abu karaf Inna Saude ta amshe da cewa "kiyi ma Manzon Allah kuyi hakuri, kun san ka haife d'an yau ne kawai amma baka haifi halinsa ba"


Alhaji ya nisa ya ce "na sani Jannat zaku koma da ita, idan ta sake ni na ce ku dawo masu da d'iyarsu. Abunda yasa na ce haka shine, ba yadda za'ai ku dawo da ita a yanzu tunda kun rik'e ta tun tana y'ar yarinyarta yanzu kuma ta zama budurwa, kune keda alhakin yi mata kayan d'aki, kinga yanzu ba yadda za'ai ku dawo da ita salin alin haka nan kawai, hakan ba adalci bane"


"Daddy shi ai ya ce a gaya masu idan ta tashi auran a gaya masa zaiyi kayan d'akin da komai ba dole sai tana wajanmu zamuyi mata kayan d'aki ba"

"Nasan da hakan, nasan Sageer dama bazai k'i mata komai ba, amma ni na ari bakinsu na ci masu albasa, a bata dama ta biyu idan ta sake ku dawo da ita, ba maganar bada hakuri kuma"

"Ai insha Allahu Alhaji bazata sake ba, shegiyar yarinya kawai"

Cewar Inna Saude dake kallon Nanah tana banka mata harara

Alhaji ya ce "kuyi mata addu'ar shiriya shine kawai ba ku rink'a zaginta haka ba, saboda shi bakin iyaye dandanan yake kama yaro ku kiyaye ma yaranku baki"


"To to to Alhaji insha Allahu"
Cewar Jafaru yana zare ido yana kyaf-kyafta su.


Bayan an sallame su suka taho akan hanya ma sai zagin Nanah suke suna kwashe mata albarka.


A k'ofar gida, Jafaru ya iske Barau Mai Caca. Da zai juyo ya gudu ai ko Barau yayi kukan kura ya cafke sa. Yana zare mai ido ya ce "ka san Allah Jafaru na fika d'anyan kai, ko ka biya ni kud'in sadakin dana biyu, na al'k'awarin da kayi min zaka bani auran d'aya daga cikin y'ay'anka mata, ko nayi ma dukan da zaka kasa tashi. Kaje ka cinye su, ko kuma wallahi na kira maka y'an Sanda su zo su tafi da kai, kuma kasan wallahi har gidan yari sai kayi"


"Dan girman Allah ba sai ta kaimu da haka da kai ba, ai nayi ma al'k'awari zan baka Mafida in..... Wata irin ashar Inna Saude ta lailayo ta dank'ara tana cewa "kutumar Uba, ai wallahi baka isa ba, uban kuturo yayi kad'an bare na makaho, ai na rantse da sarkin da ke busan lumfashi, sai dai idan bana raye, zaka d'au y'ata kaba wannan tanbad'd'an mutunan, ai wallahi sai dai ka d'au d'iyar d'an uwanka Maryam ka basa, amma ba dai cikin Yara na ba wallahi"


A dai-dai lokacin da Maryam ke kawo kai zata fito daga cikin gidan, taji abunda Inna Saude ke fad'i. Gabanta yayi wata irin bugawa, har saida ta dafe k'irjinta tana kallon mutunan da ake son k'ak'uba mata shi yanzu. Miya kai Kawu Jafaru amsar kud'in sadaki a wajan Caca na Y'ay'ansa?, wannan wacce irin rayuwa ce suke haka?. Maryam ke fad'a a zuciyarta wasu hawaye taji suna zub'o mata a kumatu. Tabbas ko zata mutu wallahi bazata auri wannan mutunan ba.

Tunaninta ne ya tsinke jin a abunda Kawu Jafaru ya ce. Wadda yasa ma jinta da ganinta d'aukewa na wucin gadi tsabar tashin hankali da firgice...



*ARMAN HARUN'S HOSPITAL LOGAS NIGERIA*



Tsaye take tana share hawaye, tunda aka kwantar da Y Aliyu hawayenta suka k'asa tsayawa, gaba d'aya ahalinsu a tashe yake tashin hankalin da suke ciki yasa gaba d'aya komai nasu ya tsaya cakkk. Mimi kuwa canta baro ta d'akin da aka kwantar da Y Aliyun tana sallah tana rok'ar ma d'an nata samun lafiya da addu'ar kare sirikar tata a duk inda take.


K'amshin turaransa yayi mata sallama tun kamin ya iso wajan da take, ta waiga tana masa wani irin kallo mai wuyar fassarawa shima hakane, kallonta yake duk yadda lokaci d'aya ta rame ta fice daga yaccinta. Tunda suka zo asibiti shine ya amshi Y Aliyu. A sadda Lalaah ke mai jawabin abunda ya faru tana kuka, bai san sadda ya rungumeta yana lallashinta ba, a sannan ne kuma ya sanar da ita sirrin dake cikin zuciyarsa, da ya dad'e yana dako a kanta. Ta k'asa gasgata abunda take ji yana fitowa daga bakinsa, ga wata irin fargaba data tuna cewa fa shine Yayarta Lilaah take so kamar ranta. Kawai ta fito daga Office d'in tana rusar kuka kamar wacce akai ma mutuwa.


Har yanzu hawayen sunk'i tsaya mata, koda yazo saitin inda take ya mik'a mata wani kyalle mai taushi da k'amshi ta share hawayen dake zuba mata.

Amsa tayi kawaii can taji muryarsa yana cewa "please muje Office ki zauna ki samu natsuwa"

Bin bayansa kawai tayi kamar wata sakarai.



A dai-dai lokacin kuma Lilaah ta shawo kwana zata nufi Office d'in Arman d'in. Tana gaf bud'e Office d'in taji Bilkees na kwala mata kira. D'an dakatawa tayi da bud'e Office d'in.

A cikin Office d'in kuwa, Arman na k'ara jaddama Lalaah shifa auranta yake sonyi, kuma duk duniya ita ce kad'ai ta tab'a tasiri a zuciyarsa, ita ce kad'ai yake jin wani abu dangane da ita. Ita kuwa kallonsa kawai take hawaye na mata zuba. Tama rasa miye ya kamata ta ce "wai yau ita ce Arman Harun Maleek ke fad'a yana sonta haka?, so bana wasa ba, a yadda take ganin tsantsar sonta a cikin idonsa, anya ba mafarki take ba kuwa?, Arman dai wadda ta sani shahararran likitan nan mai ji da kyau da kud'i da iko kota ina, wai yau shine zaune a gabanta yana mata magiyar ta soshi, ita kam mi zata ce ma Ubangiji. Sai dai abu d'aya ke mugun bata tsoro da damunta, Lilaah fa? miya sa abun zaizo masu a haka?" abunda take cewa kenan a zuciyarta



"Ina ta kiranki tun d'azo wayarki bata shiga lafiya dai?, Kuma naga an kwantar da Y Aliyun ku a nan hospital d'in mi yake faruwa ne Lilaah?"

"Wallahi wai sumewa yayi saboda y'an Ta'addar da suka kira shi suna shaida masa idan aka sake sa Jami'an tsaro a ciki zasu kasheta ne"


"Subhanallahi ah ahh dole Y Aliyu ya suma, masu garkuwa da mutanan nan fa ba imani ne dasu ba"

"Hmm hakane kam"
Cewar Lilaah ko a jikinta, da kaga yarda take bata amsa zaka san ita abun bai wani dameta ba.

A tare suka nufi Office d'in domin shiga sun tura k'ofar kenan suka ji saukar muryar Arman yana cewa..........





*To laifin dad'i aka ce k'arewa a nan na kawo k'arshen Free pages. Game bukatar tafiyar nan dashi k'ofa a bud'e take*




Ina so na sanar daku cewa Free pages zai tsaya daga na 10 ne game bukatar TAFIYA dashi na wanga book d'in zai biya D'ARI BIYAR NE KACAL, ba sai na tsaya yin wani dogon jawabi ba, kun dai san wanga book akwai k'ura a cikin akwai matsaloli masu tarin yawa, akwai sirrikan dake binne wadda duk za'a warwaresu nan gaba*

Zaka iya turo kud'inka ta wannan account d'in 8130479973 Fatima Rabi'u Opay bank

Sai ka turo shedar biya ta wannan number d'in 👉 08130479973
Zaka iya turo kati MTN D'ari biyar ne kacal

An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels
End Ads