x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 6 - K'ADDARAR SO

  • 15001 words
  • 18000 words
  • Out of 20867 words

Category: Love Stories

Views 121

20 Jul 2025
Start ads
After Image Ads
ma"

Girgiza kanta kawaii Mimi tayi, har yanzu Abbie bai san suwaye y'an Bindiga ba, su da suke kamar aljanu idan aka ce yanzu haka sun san da Jami'an tsaron da akasa cikin lamarin ba'a gaddama, yanzu haka sun d'an dakata ne suga iya gudun ruwansu.


Sallama sukai kawaii inda take shaida mai ya tsaya ya idasa abubuwan dake gabansa, zata sa a ci gaba da addu'oi had'e da sauk'e al'qur'ani mai girma, su had'u kuma suyita mata addu'ar Allah ya k'are ta daga duk wani sharrinsu.

Bai wani yadda ba, shi dai yasan dole ne cikin satin ya duro Nigeria.........
*K'ADDARAR SO*
(Destiny Of Love)




*©ZAHRA ROYAL STAR*🌝
Share Fisbilillahi





*ROYAL STAR WRITERS ASSOCIATION*


Chapter 8


*ARMAN HARUN'S FAMILY HAUSE LOGAS NIGERIA*


Yau ta kama weekend ne, kowa yana gida. Safiya ce mai cike da nishad'i domin garin hadari ne ya had'u sosai ya saki wata irin ni'ima, garin yayi luf-luf dashi gwanin ban sha'awa.

Babban parlon gidan ko ta ina ma'aikata ne ke aikinsu, masu shirya darning table nayi, sunfi ba darning table d'in mahimmanci wajan jera abincin safen da masu gidan ke gaf sakkowa domin su ci. Kamin a shafe y'an mintoci, sun shirya kan darning table d'in, had'e da gyara parlon ya d'au wani k'amshi na daban.

A hankali a hankali mutanan nan gidan suka rink'a sakkowa suna zama kan darning table d'in. Ga wata ma'aikaciya tsaye kana zama ita ce mai tabbayar ka miye kake son ci, zata zubama abunda kake ra'ayi da son ci, wannan shine aikinta kawai.

Kowa ya sakkowa harda su Daddy amma banda Arman a wajan. Salma ce ta d'an duk'a dai-dai inda Haj Shuwa ke zaune suna kusa da juna ta ce "Umma ya banga Arman d'in ya fito ba, kowa kuma yana ya hallara?"

"Hmm rabu da miskilin banza, yanzu haka yana can ya tsaya yangarsa, shifa ba wani abinci yake ci sosai ba, bari kiga koda ya zo ba wani zama yake ya dad'e a cikinmu ba"

Tab'e baki Salma tayi tana d'aga k'afad'arta irin ko a jikinta d'in nan.


Haj Zulaihat ce nufo darning table d'in, itama fitowarta kenan Bilkees dake danna waya ko kallon su Salma batai ba, bare ta san miye suke ciki. Humaira ce ma dai da Sa'adha dake kusa da juna, suke duban Salma yadda ta wani hakimce kamar wata sarauniyar gidan, Sa'adha bata dad'e da dawowa gidan ba, tana k'asar India tana karatu tazo hutu ne, Humaira kuwa d'iyar k'anwar Momma ce, dama ita gidan take zaune tun asali tare suke da Sa'adha, Humaira tafi son karatun k'asarta ta haihuwa, ita ko Sa'adha tana da ra'ayin fita. Hakan yasa iyayen Humaira dake zaune k'asar India suka bata goyan baya, take zaune a gidansu ita kuma d'iyarsu Humaira dama can ba zama k'asar take ba, tunda wayonta ta baro India ta komo gidan Momma, baka tab'a gane cewa ba Momma ce ta haife ta ba, haka itama Sa'adha idan tana can India baka tab'a cewa ba Iyayen Humaira ne suka haife ta ba, haka suke rayuwarsu cike da tsananin son juna.

Salma kuwa da biyu tayi dama, duk tana sane dasu. Tana cikin tunani Arman k'amshinsa kawai ya fara masu maraba da cewa gashi nan isowa. Su Sa'adha murmushi suka saki a tare, suna waigawa, suna duban Yayan nasu. Kai ita kanta Salma sai da ta had'e abincin dake bakinta ba shiri. Wani mayen kallo take binsa dashi, yaushe rabon data sashi a idonta, gani tayi yayi mata wani mahaukacin kyau, ita kanta bata san sadda ta saki wani murmushin munafurci ba, a zuciyarta take cewa. Tabbas Arman ka cika Zakin Maza dole y'an mata zasu rink'a harinka kota ina, na samu na shiga gidanka dai, amma ni nayi daban da y'an matan dake hauka kanka, ni dukiyar taka muke da buk'ata, ko kwanciya kayi dani wannan ma kad'ai ya wadatar dani. Ta k'are maganar tana k'ara fad'ad'a murmushinta.

Kowa ya gaisar dashi, amsawa yayi a takaice, shi kuwa kai tsaye sai da ya fara zuwa kusa da Daddy da Abba, ya kwashi gaisuwa suna ta samai albarka. Kamin yaje kusa da Momma ya rungumeta yana mik'a gaisuwarsa, cike da k'auna take samai albarka. Wajan zamansa ya zauna, da kanta Momma ta tashi ta zuba mai abunda tasan yana yana so.

Haj Zulaihat ta zunguri Bilkees tana d'agowa ta banka mata harara, k'asa-k'asa ta ce "wato ke dai baza ki daina halinki ba ko?, wato ke ta danna waya ma kike, bana ce idan ya fito ki rink'a zuwa kina amsar Momma ki rink'a zuba mai abincin da kanki ba?, da haka zai saba dake har ki d'an samu matsagunni a zuciyarsa sakarai dake komai sai ance kiyi"

Turo baki Bilkees tayi bata ce komai, itafa gaskiya abunda Momy ke son ta had'a tasan ba mai yiwuwa bane.


Haj Shuwa k'asa k'asa itama yadda Haj Zulaihat zata jita ta ce "hmmm ayi dai mu gani idan tusa na hura wuta"

Wani kallo mai cike da takaici Haj Zulaihat ke aikama Haj Shuwa tana kama leb'enta na k'asa ta d'an ciza, kwafa tayi tana kallon Salma, wato kenan Haj Shuwa ta canza shawara itama, so take wannan d'iyar y'ar uwar tata itama ta samu shiga wajan Arman kenan?, kan uban nan kayyasa ai ko da sake wallahi, ita Haj Shuwa zatai ma haka?, dan taga tana so itama tata yarinyar ta samu shiga. Wani dogon tsaki Haj Zulaihat ta saki, wadda yaja hankalin gaba d'aya mutanan wajan, kallo ne ya dawo kanta, basarwa tayi tana tashi gaba d'aya daga kan darning table d'in, tana ma Bilkees inkiya da ido akan ta biyo ta d'aki yanzun nan. Domin idonta ne yayi mata tozali da yadda Salma ke bin Arman da mayen kallo, kuma tuni ta harbo jirginsu ita da Haj Shuwa.




Bilkees na shigowa part d'in nasu, Haj Zulaihat ta kalleta ta ce "wai ke sai yaushe zaki gane abunda nake hango miki dangane da auran Arman ne?, har yanzu baki da wayo wallahi Bilkisu"

"Momy please wallahi kwata-kwata bana son kina min maganar had'a ni aure da Arman, na k'ara gaya miki cewa K'awata ke sonshi kamar ranta, bana jin idan Lilaah ta rasa Arman zata iya rayuwa"

"Ke dalla rufe min baki, kona d'ora miki ashar yanzu nan, harni zaki tsaya kina cewa wai k'awar ki idan bata sameshi ba akwai matsala, to tama mutu mana, ina ruwana. Nidai na k'ara gaya miki ki maida hankalin ki wajan jawo hankalinsa gare ki, idan ba haka ba kuma, wallahi Bilkisu ranki zaiyi mummunan b'aci ne"

Shuru Bilkees tayi, wani haushin Momy na kamata, kallonta kawaii take, yadda take ta sako mata maganar Arman, komai Arman kowa Arman, ita fa bata ga abunda suka hango har suka rud'e sai shi ba.

Harta gama b'ab'atunta Bilkees bata ce komai ba, tana gamawa Bilkees ta juya ta fice daga d'akin.
Tana fita Haj Zulaihat ta jawo wayarta, ta dannama wata K'awarta kira, bugu d'aya kuwa aka d'auka. Kamin ta cikin wayar ta ce komai Haj Zulaihat ta ce "Luba akwai matsala fa"

"Wacce irin matsala kuma Haj Zulaihat?"

"Akan abunda tun yarinyar nan na k'arama nake so na had'a domin cikar burina, amma yarinyar nan tana son b'allo min ruwa fa"

"Ai kece tuni Haj Zulaihat na ce miki ki fara aiki da Malaman tsubbu da bokaye, kiga aiki kamar yankan wuk'a, kika wani tsaya ai kissa da dabara zata sa ta fahimce ki, yo hatta mijin naku, keda wannan mai kama da ifiritan farko Haj Shuwa da tuni kin gama da ita wallahi, da yanzu sai dai watanta ba dai ita ba, bata isa ta d'aga miki koda d'an yatsa bane"

"Kinga Luba, nifa gaskiya zan k'ara gaya miki ban yarda da Malaman tsubbu nan ba, abu d'aya na sani nayi yak'i da kaina na samu abu yafi, kuma ko yanzu Mijina yana sona na sani, kowa da matsayinsa"

"To kin san da haka mi kika bugo nayi miki?, Fisbilillahi nifa kin sani da Malaman tsubbu nan na dogara, su suke min aiki har nake janyo y'an samari na tatse su kud'i yadda nake so, tunda na kaso aure na nake cin kare na babu babbaka"

"Hmm Luba kenan yanzu ba shawarar da zaki bani, ko na d'au haske"

"Haj Zulaihat kenan, nifa bari na k'ara gaya miki ga abunda zakiyi kiga buk'ata yanzu yanzun nan, ba b'ata wani lokaci, idan kuwa na ce ga abunda zakiyi to nayi k'arya ni ban san wannan y'an dabarun ba da kissar nan, a'a ni Malamai kawai na sani. Idan kin shirya binsu to ina sauraran kiran ki".

Tana fad'ar haka ta tsinke kiran.

Wani tsaki Haj Zulaihat taja tana magana ita d'aya
"Shi yasa fa ban son kiran Luba, komai ita sai kabi wasu bokaye abunda aikinsu na d'an kwanaki ne, nida nake so nayi abun ya zama sai dai mutuwa zata raba".




Momma kuwa, duk tana ganin abunda ke wakana a tsakanin Matan K'anin mijinta, har tsakin da Haj Zulaihat ta saki tasan can tsakaninsu ne ita da Haj Shuwa. Wani murmushi ta saki tana k'ara sama d'an nata albarka.


Haj Shuwa ce itama tsaye tana waya da Binta. Salma ce ta shigo hakan yasa Haj Shuwa tsinke kiran.

"Umma wai baki ganin yadda waccan matar Haj Zulaihat ke miki tsaki ne?, mi yasa baki ci ubanta bane?, nifa wallahi Umma bana d'aukar raini, shi yasa zuwa na gidan nan, muka had'u da waccar Humairar ta nemi tayi min iskanci na ce ubanta gaban Momma wallahi"

"Kin yi min dai-dai ai, shegiya sai ka ce ita ba cin arzik'in take yi ba"

"Hmm kema kin fad'a Umma, ai ko taji magana wallahi"

"Ni yanzu waccar Haj Zulaihat d'in ke son bamu matsala, amma abu d'aya zai tsaida mu shigowar yarinyar da Boka ya ce ne, amma data gane shayi ruwa ne, data gane cewa ba'a buga wasa da Haj Shuwa bata cinye wasan ba, amma nan gaba kad'an zata ga sakamakon wasan".

Dariya suka saki a tare harda su tab'a hannu kamar wasu sa'annin juna.





*SURURE LAGOS NIGERIA*


Wayar dake manne a kunnansa ce ke shirin fad'uwa, tsabar yadda jikinsa ke kyarma. Ba shiri Mimi dake kusa dashi hankali a tashe ta tarbe wayar tana sata a amsa kuwwa yadda kowa zai ji. Miye ya tada hankalin Aliyu?. Sai tabbayarsa suke tun d'azo da ya amsa kiran, ya koma tashi a zabure amma yak'i basu amsa, gashi ya tsaya kamar wadda gangar jikinsa ta daina aiki.


Abunda suka ji ne suma ya kusa tarwatsa kwanyarsu da tunaninsu. Domin daka ji yadda ake magana da wata basamudiyar murya, irinta gaggan y'an Ta'adda zaka sheda wadda suka sace Husaina ne suka kira.
Suna cewa "da alama baka so matarka ta dawo da ranta, mundun kuka sake sa Jami'an tsaro a lamarin, to matarka zata iya mutuwa ako wane lokaci, a sadda kuka shirya ta dawo gare ku zamu neme ku, amma yanzu baka shirya ta dawo gare ka da wuri ba. Suna fad'in haka suka datse kiran. Wata irin hargowa Aliyu keyi yana amshe wayar daga hannun Mimi yana cewa "hello hello dan girman ku tsaya, wallahi na shirya amsar matata, ko nawa kuke so ku fad'a zan baku, kuma Jami'an tsaro za'a cire su daga zancan, baza mu sake sanar dasu abunda ake ciki ba, hello hello hello". Maganar yake cike da fitar hayyaci.


Mimi da ke hawaye ta ce "haba Aliyu sunfa katse kiran"

Wata irin zabura yayi sai gashi ya zube a k'asa a sume.

Wata irin kururuwa Lilaah ta saki had'e da salati........


*Ina so na sanar daku cewa Free pages zai tsaya daga na 10 ne game bukatar TAFIYA dashi na wanga book d'in zai biya D'ARI BIYAR NE KACAL, ba sai na tsaya yin wani dogon jawabi ba, kun dai san wanga book akwai k'ura a cikin akwai matsaloli masu tarin yawa, akwai sirrikan dake binne wadda duk za'a warwaresu nan gaba*

Zaka iya turo kud'inka ta wannan account d'in 8130479973 Fatima Rabi'u Opay bank

Sai ka turo shedar biya ta wannan number d'in 👉 08130479973
Zaka iya turo kati MTN D'ari biyar ne kacal
*K'ADDARAR SO*



*©ZAHRA ROYAL STAR*🌝
Share Fisbilillahi




*END OF FREE PAGES* Chapter 9-10



*SANSANIN Y'AN TA'ADDA*


Kwance Fulani take a k'asa cikin ciyayi, sai juyi take k'afarta na mata wani irin rad'ad'i mai shiga kwanya, duk da ta zare k'ayar data shige mata k'afa amma k'afar har yanzu zugi take mata.

Murk'ususun wata mata taji kusa da ita tana shashshakar kuka, ba shiri ta tashi a zabure tana duban matar dake d'an nesa da ita. Kallon ko ina tayi gasu nan an zube su a cikin rana ba abinci ba ruwa, rabonta data ce tasha wani abu tun kamin Inna Wuro ta bata labarin basu ne suka haifeta ba. Yanzun ma yunwa tayi mata mummunan kamu da kyar take had'e miyau, ga k'irjinta data ke ji yana mata zafi, kamar mai shirin kamuwa da cutar kwalsa.

Gabanta ne ya fad'i ganin yadda matar ke kallonta ko kyafta ido babu, kallon matar take itama, ganinta d'auke da k'aton ciki, haihuwa yau ko gobe. Gani tayi suna mugun kama, amma kamar bamai fisgar mutum bace kace nan take ai kamar ta b'ace ko kuma ace ai su iri d'aya ne, a'a kama ce wacce da an gani za'a ce ta jini d'aya ce amma game hankali da tunani.

Fulani bata san sadda ta rarrafo ta nufi matar dake rik'e da cikinta tana zubar da hawaye ba. Wani d'an Ta'adda ne ya kwasama Fulani tsawa da cewa "ke y'ar gidan matsiyata, koma ki zauna inda kika taso, kona fasa kanki da bindiga yanzu"

Ko kallonsa batai ba, domin ita yanzu mutuwar kawai take so, tazo ta d'auke ta ko kuma su su kasheta da kansu, ta gaji, ta gaji da wannan duniyar gaba d'aya.

Rai a b'ace d'an bindigar zai nufi inda Fulani take, da wannan matar, Ogansu ya dakatar dashi ya ce "rabo da ita, da alama yarinyar zatai taurin kai"
Shuru yayi sai can ya ce "yo Oga ba sai yanzu ka bani Okay na fasa kanta da bindigar nan ba, yanzun nan lahira tayi bak'o"

"Batta dai ba yanzu ba tukunna"

Fulani duk tana jin miye suke cewa, wasu hawaye ne keta zuba a idonta, ita wallahi da sun kasheta a yanzun da sun kyauta mata ma. Tana isa ga matar ta tallafo kanta suna kallon juna, lokaci d'aya suka ji gabansu ya fad'i. Sharewa Fulani tayi cike da tausayi ta ce "baiwar Allah kema sato ki suka yi ko?, ga ciki koma nak'uda kike yi naga kin rik'e cikin?"

."a'a y'ar uwa ba nak'uda bace, da sauran lokaci, amma ko yanzu zan iya haihuwa saboda tashin hankalin da nake ciki. Ni ba har gida suka je suka sace ni ba, akan hanyata ta zuwa garinmu Katsina, suka tare motar da nake ciki, suka kashe driver na suka taho dani"
"Innallihi wa'inna alaihir raju'on wai su wa'innan mutanan basu da imani ne ko kad'an kashe rai kai jama'a"

Fulani ta fad'a hawaye na mata zuba har yanzu. Matar ta sake damk'e hannun Fulani tana jin k'aunar yarinyar har cikin ranta duk da zasu zo sa'anni da juna, har shekaru sai dai ita zaka iya cewa nan take ta girmeta saboda auran data yi kuma ga ciki sai ya k'ara bud'ata ta koma kamar wata babbar mace.

Ta ce "ya sunanki?"

"Ni sunana Fulani"

"Fulani" ta mai-maita sunan, sai can ta sake cewa "ni kuma Husaina"

Fulani haka kawai data ji sunan ta sake jin wata fad'uwar gaba, had'e da k'ara jin matar a jikinta

"Amma mi yasa kike kuka tunda aka kawo ki jiya, kuma kina rik'e da cikinki?"

Murmushin daya fi kuka ciwo Husaina ta saki tana duban Fulani wacce kamar akwai sauran yarinyata har yanzu dabe sake ta ba, ta ce "hmm Fulani kenan, ya za'ai bazan kuka ba?, ina tuna halin da mijina zai shiga ne da sauran dangina shi yasa kika ga ina kukan nan. Rik'e ciki kuma ina tausayin abunda zan haifa ne a wajan nan, fatana ace sun sake ni kafin na haihu, to amma banga alamun hakan a tare su ba, kamar so suke suga baya na ne, bamu san mi muka tare ma mutanan nan ba, ji nake a jikina kamar bazan sake sa Mijina a idanuwana ba sabo...... Toshe mata baki Fulani tayi tana girgiza mata kai ta ce "ki daina fad'ar haka, ai gara ma ke ni kin ganni nan sai da suka kashe min kowa nawa, shi yasa banga anfanin su sake ni da raina ba ma, su kashe ni kawai na so ace tun can cikin y'an uwana nima sun had'a dani sun kashe, ban san miye hikimar tahowa dani da sukai ba"

Tashi Husaina tayi a zabure tana duban Fulani ta ce "wai kina nufin garinku suka je suka kashe maku kowa, hasbinallahu wa'imar wakil"

Cewar Husaina, bata san sadda ta rungume Fulani suka fashe da kuka a tare ba, kamar wasu wadda suka dad'e da sanin juna.

Wata tsawa aka daka masu wacce tasa ba shiri suka zabura, suna kallon d'an bindigar dake tsaye da bindiga a wajansu. Yana cewa "munafukan banza, idan muka sake ganinku kuna wa'innan maganganun wallahi sai mun kashe ku gaba d'ayanku"
Shuru su Fulani sukai suna k'ank'ame jikinsu waje d'aya.

Wani garin kwaki aka jefo masu cikin wani kwano, ba magi ba gishiri an dai jik'asa sai uban yaji da aka dank'ara mai, sai ruwa guda d'aya da aka jefo masu, su biyu kowa kwano mutum biyu, ga garin bai wuce kayi loma uku dashi ba.

Kamin ka ce mi wasu sun lashe nasu, suna tand'e hannu. Duk rashin dad'insa su kam ba wani ji sukai ba, ruwan ma haka suka d'an kurb'a badan an k'oshi ba.

Fulani ta kalli Husaina ta ce "y'ar uwa ki d'auka kici kawaii kinga ke kina da ciki, bai kamata ki zauna da yinwa ba"

"To ke kuma fa?"

"Ke dai kawai kici ni yanzu
End Ads