mata saƙo. Saƙon kuwa bai wuce ta je ta cewa Yarima ga Antina ta zo in yana da dama za su gaisa.
Gudu nake kada in ce yazo Aunty ta yi mini faɗa,ni kuwa ba na fatan ƙara zuwa sashinsa,lallai zance,ko kuwa tabɗijan! Ganin Yarima a filin da muke wasa, shi kaɗai da silifas a ƙafarshi,shin ina aka ajiye girman kan da ƘASAITAR, koda yake na lura a cikin gidan shi sauƙin kai ne da shi, tunda har yana ƙwanciya ƙasa saman kafet,ko filo babu.
Cikin rawar jiki ƴan matan nan suka sunkuya suka gaishe shi. A idona cikin mintuna biyu na ga an kafa rumfar lema da kujerunta uku amma na (Cane) irin kan Nan mai lanƙwaso da tebir a tsakiya, wannan duk aikin wasu maza ne, waɗanda ban ga isowarsu ba, sai dai aikinsu kawai na gani. Mulki, na ce a zuciyata saboda ganin ga rumfar da aka tanada don hutawa, amma har sai da aka kafa masa wata.
Mamaki yasa na yi tsaye na riƙe ƙugu da hannuwana duk biyun, ganin yanda ya gaishe da Aunty har da ɗan russunawa alamar girmamawa, yasa na dinga tunanin anya kuwa Yarima Faysal ne kuwa? Tambayar da nayi wa kaina kenan a daidai lokacin da na ga sun jera da Aunty suna tafiya zuwa ƙarƙashin inuwar lemar nan.
Har sai da suka zauna, sannan Aunty ta yi mini maganar wai in zo,a lokacin ne ma hankalina ya dawo a jikina, na iso na zauna a tawa kujerar, wacce ke gefe ɗaya,hakan kuwa ya yi ɗaya da lokacin da wani mutum ya iso da farantin kayan sha,su lemo kenan, wanda gefensu kuma tufa ce (Apple)
Hira sosai shi da Aunty. A cikin hirar na ji tana cewa, "Wai ranar da ku ka je gida Mamee ta gaya mini,cewa kun biya ta gidana ba ku same ni ba." A zuciyata na ce, Au! Ashe har gidanmu ake zuwa ba a gaya mini ba,neman shiga.
Iska ta taso mai ƙarfin gaske, wanda zan iya kiranta da guguwa,jin yanayin wasu addu'o'i a bayyane yasa na yi mamaki, a inda ni kuma gashin kaina ya kaiwa gefen fuskarshi ziyara, yasa hannu ya cire shi a hankali,a inda ya ci gaba da magana da Aunty.
"Aunty ki yi mata faɗa, ba ta son ɗaura ɗanƙwali ƙwata-ƙwata, tunda ta zo gidan nan ni dai sau ɗaya na ganta da ɗankwali, shi ma na san don gidanmu za'a."
Ta juyo gare ni, "kin ji ki daina."
"Aunty ba fa kowa a inda nake sai yaran nan su Mansura fa."
"A yanda ki ke gani ba,ni ko jiya na ji cikin dogarawana wasu na yin fasalin ƙyan gashinki,kin ga kenan suna kallonki in kin fito."
Maganar da yake yi mini kuwa tana nuna cikin jin haushi yake yin ta, na kalli Aunty, "Sai kin shigo Aunty." Na miƙe a fusace.
"Yasmin zauna." Na ji ya faɗa. Na juyo na kalle shi sannan na kalli Aunty. Aunty ta daka mini harara na koma na zauna, amma sai na kawar da fuskata ɗayan gefen.
"Aunty kin ga matsalar da muke ciki kenan ni da Yasmin ba yanda za'ayi in ce tayi abu ta yi shi, alhalin ta hakan za mu samu jituwa, amma na yi iya ƙoƙarina ina ƙasƙantar da kaina ina bin abin da ta umarce ni, yanzun kin ga an kusa ƙwana ashirin da ce mata ta yanke farcinan hannunta, amma ban isa ba."
Aunty ta juyo ta kalleni, "Yasmin tashi ki shiga ciki ina zuwa."
Na tashi cikin fushi na yi gaba, har sai da na yi wanka na shirya sannan Aunty ta shigo a inda ta same ni falon sama.
"Yasmin,duk na fahimci matsalarku, ba ta wuce jiji da kai duk ya gaya mini irin yanda ku ke tafiyar da rayuwarku. Na ba shi haƙuri. Yasmin ya ce baki girmama shi,in ya aiko ki je, sai ki mayar da ɗan aiken da cewa ba ki zuwa.
Ya nuna mini kina kunyatashi a gaban barorinsa,a nan ma kuma na gaya masa kin gaya mini aiken jakadiya ne baƙya so, ya ce yayi alƙawarin ya daina, sai dai ko aike na hidimar gida, yanda yake nuna mini ke ce mai matsalar kin rigaya kin sanya tsanar shi a zuciyarki. Haba ƴar ƙanwata, yanzun daɗinmu ne a ce mu dinga ɓatawa iyayenmu rai, kiyi tunani mana, wallahi na san Dad na kuma fiki sanin halayyarsa,kin ga saboda wannan matsalar,za ku iya mugun ɓatawa.
Ba na mantawa akwai wata rana muka yi rigima ni da Abdulƙadir lokacin ina goyan Tahir kin ga bai fi shekara ɗaya da ƴan watanni ba kenan, rigima ta kai mu har gida,kin ga yanda Dad ya yi mini kuwa. Ke a takaice sai da na shekara uku Daddy baya amsa gaisuwata sosai,in ma na samu ya amsa, balle faɗan ni ce banida gaskiya. Kinga kuwa a nan ke ce ba ki da gaskiya, duk da nasan ba ƙya son shi, amma ai shi Dad gabansa kin nuna za ki zauna da mijinki lafiya."
Nasihohi da faɗa su Aunty ta dinga yi mini,a inda ni kuma ba ni da wata maganar mayar mata sai kuka. Kai a ƙarshe na ce mata.
"Aunty ba na son shi,bana son shi, shi ma fa baya sona, jiki na kawai yake wa ƙwadayin ya samu Aunty."
Cikin kukana da mayar da kaina saman kujera na ƙwanta, Aunty ta ɗago ni ta rungume a inda ta gaya mini maganganu masu ƙwantar da hankali, sai da taga na ɗan samu kaina sannan ta tashi ta shiga wanka,a inda sallar magriba ta kawo jiki.
Bayan sallar magriba ne, sai ga Uncle ya zo ɗaukar ta, sai dai kawai muka gansu sun shigo tare da Yarima,mu kanmu mun yi mamaki, sai dai kuma tunanin gidan da ake tsaron shi kamar wannan gida, dole ne a san mai shiga da fita, har mota muka raka su Aunty Salwa,ni da Yarima muna tsaye dakarunsa guda biyu suka buɗe but ɗinsu Aunty suka sa musu wasu kaya, ban san ko su meye ba.
A daren ba a ƙwana ba, na ga masu aiki na ta haɗa wata waya a cikin gidana, wacce na ga an liƙa wani ƙaramin jan abu a falon ƙasa, haka a falon sama. Ni dai iyakaci na idanuwa, sai da ma suka gama, ana gwadawa a ga in ya yi,jin ƙarar shi yasa na gane Inner caller abin da ake kiran mutum idan yana nesa.
Ƙarfe sha ɗaya saura ƙwata na dare na ji ƙararrawar nan ta yi ƙara, doguwar rigar bacci ce a jikina tare da ƴar samanta, mai ƙyan gaske, har na kallu ba zani ba, saboda na rigaya na yi shirin ƙwanciya, amma tunanin abin da muka yi da Aunty yasa na ɗauki doguwar alkyabba na ɗora ta sama, sai ɗanƙwalinta na rufa a kaina.
Gaskiya aƙwai tsoro fita a wannan lokacin, don dai ma ko'ina gidan fitila ce tamkar da rana ne, ƙasan falonshi ba kowa, sannan fitilu duk a kashe suke, sai ƙwaya ɗaya, wacce ta bayar da kalar duhuwar haske na mayar da ƙofa na rufe kamar yadda na ganta.
Falonshi na sama ba kowa, sai duhu ne a tare da shi, ba wata fitila ko ɗaya, cikin jin haushi na tura ɗakinsa na shiga, tare da sallamata. Fitilar gefen gado ce kawai a kunne, amma ban ga kowa ba a cikin ɗakin,sanin zuwan da nayi da rana na same shi ƙasa ƙwance, yasa na dinga kallon ƙasan ɗakin, amma ban ga kowa ba.
Wucewa na yi barandar shi inda na san ya cika zama, shi ma baya nan, na leƙa kaina ƙasan barandar, amma ban ga kowa ba, sai ma na ji tsoro ya kama ni da baya da baya na dinga tafiya,wai ni gudun kada in juya wani abu ya kama ni,banyi aune ba sai kawai na ji nayi karo da wani abu ta bayana, kafin in yi ƙoƙarin juyowa sai na ji an rungume ni gam,an sa gefen fuska a tawa fuskar.
"Yasmin gani nan." Ya faɗa cikin muryar raɗa a hankali na bi na zame jikina,a inda na bi ta gefensa na wuce na zauna kujerar kusa da ni, wucewa ya yi saman gado ya zauna, sannan na ga hasken fitila ya gauraye ɗakin.
Maganarsa a hankali take fita, "Dama kirawo ki na yi saboda ina jin yunwa, don Allah ki sama mini wani abu in ci, ko da shayi ne."
"Ina kicin ɗin?"
"Yana ƙasa."
Na miƙe na nufi ƙasa, lokacin da na ji jikina ya yi mini sanyi. Firji na gani, ina buɗashi na ga cike yake da kayan kicin,alayyahu ne,nama,salat,tumatirin gwangwani,kai tarkace na kicin dai gasu nan birjik.
A nan take na yi tunanin haɗa masa salat, na kuwa cire mayafin da na yafa a kaina na ajiye gefe ɗaya, haka alkyabbar saman kayan baccina, cikin ƙanƙanin lokaci na gama yanka salat ɗin,ƙwai kawai nake jira ya dafu, madadin in tsaya haka nan sai na yi tunanin haɗa masa matsatstsan lemo da abarba.
Miser ta matse lemo nasa na matse shi, abin ka ga na'urar bature, haka kuma injin ɗin markaɗe na bature ya markaɗe mini abarba (Blander), rashin sabo da dogayen kaya yasa na ji rigar saman na damuna, amma dole haka na haƙura da ita.
Bayan na tace su ne, na samo ƙanƙara na jefa a cikin ɗan siririn dogon kofin da na gani mai murfi yalo (jug), shuga ɗan kaɗan na saka masa na ga ƙatuwar ƙwalbar fulebo, ta sitirober (Strawberry).
"Sannu da aiki." Na ji an ce daga bayana.
*ƘASAITA BOOK 1*
*NA*
*MARYAM KABIR MASHI*
Page 13
Na yi saurin firgita na nufi inda alkyabbata take na ɗauka na saka ta.
Farar singilet ce a jikinsa da dogon wando, wannan yasa ban ƙara juyawa na kalle shi ba, duk da dama jingine yake a jikin ƙofar shigowa ya harɗe hannayensa saman ƙirjinsa.
"In kin gama ina sama."
Ban amsa ba ni dai na ƙagu in gama in koma in ƙwanta.
Ƙarfe sha biyu da mintuna goma na kammala komai, cikin tangarayen nan nasu na sarauta a ciki na haɗa masa haɗin salat ɗin, na jera a wani ƙyakƙyawan faranti.
Ina shiga ɗakin nasa yana ƙwance a ƙasa kamar yanda na same shi da rana, na iso kusa da shi na ajiye kayan, ya tashi zaune.
"Za ki ci?" Na girgiza kaina.
"To na gode, shi kenan dama,mu je in rakaki."
Na miƙe na fara yin gaba, zuciyata ta cika dam da daɗi. Ina tafe yana biye da ni har ƙofar gida ta ƙasa, na juya na kalle shi.
"Mu je in kai ki gida ko,ko baƙya jin tsoro?"
Ban dai samu yin magana ba.
Yana bakin ƙofata ya dafa ta,ni kuwa ina daga cikin gida na riƙe ƙofar alamar zan rufe, ganin yana murmushi yasa na tsaya ina kallonsa.
"Na gode Yasmin,sai da safe kin kawo mini karin kumallo (Break fast)."
"Nima ba ni nake yin karin kumallo ba, yi mini ake yi."
"Ina son ci haka nan." Sai naga yana leƙen bayana, na ga ya ƙara zare idanuwansa.
"Me ye?" Na tambaye shi da sauri.
"Kamar wani abu ne tafe a bayanki."
Sai na yi saurin sakin ƙofa na fito da niyyar in waiga in ga ko meye, sai na ga ya yi ƴar dariya.
"Ba komai zolayarki nake yi, saboda kin ƙi yin fara'a."
Na ɗan yi murmushin dole, na koma cikin gida, sannan ya juya ya tafi,ni kuwa na kasa rufe ƙofar da take riƙe a hannuna, ina ta bin shi da kallon mamaki.
Har sai da ya juyo ya ɗago mini hannu, sannan na mayar da ƙofa na kulle da gudu na haye sama saboda tsoro. Ina isa madadin in ƙwanta sai na cire kayan saman rigar baccina, na buɗe ƙofar gaban gidan na fita baranda na runtse idanuwana na ware hannayena duk biyun iska na ɗaukan gashina a hankali.
Babu wanda ke zuciyata sai Anwar,son shi da ƙaunarshi suka dawo mini sabo a wannan daren,shin ko dai dama yaudara ce Yarima ya yi mini yanzu gashi nan ya tunasar da ni masoyina. Na tuna wata rana da Anwar ya zo gidanmu zai tafi, na yi masa rakiya, har ya zauna kujerar motarsa sai na ga ya miƙe tsaye, mamadin ya yi magana, sai na ga ya matso kusa da ni sosai.
A hankali ya ce, "Kalli ki ga yanda bishiyoyin nan ke rausayar jin daɗi, saboda sun samu ni'imtaccen wajen ƙwanciya."
Ya kawo hancinsa gab da nawa, sai na ji ya ce, "Haka muma wani daren za mu samu ni'imtaccen maƙwanci."
Idanuwana a lumshe ina ji ya sumbaci wuyana, yanda tsigar jikina ta tashi a wancan lokacin, haka na ji ni a yanzu.
Mamadin inji farin ciki, sai na ji lemar hawaye na gangaro mini,saboda tunaninmu ya zama mafarki,ko a wane hali yake ciki yanzu? Tunanin da nake so in kawar a zuciyata,amma sai nema yake ya haye mini,wai tunanin Yariman da yake babban maƙiyina na yi tsaki a daidai lokacin da na tuno ni bayana ƙwance a ƙirjinsa.
"Allah ya saka mini." Na faɗa tare da buɗe idanuwana, na shige cikin gida, har na kama ƙofar gidan zan rufe, sai na hango Yarima a barandarsa yasa hannuwa a aljihu yana kallon sama, na yi saurin mayar da ƙofata na kulle. Abin ka ga ƙofa mai gilashi ce, sai na ɗaga labulan na leƙo yanda na barshi haka yake, na yi tsaki na wuce na yi ƙwanciyata.
Bacci zo mana, amma kamar an busar mini da idanuwana,ko me ye dalili? Oho, na mutstsuke idanuwana tare da runtse su na yi lamo, amma babu alamar bacci a idanuwana. Ni kuma na kasa sanin me ya hana ni yin sa,a zuciyata na ji ina so na ƙara leƙawa in ga yarima ya shiga ɗakinsa ko kuwa yana nan a tsaye.
Shin dama haka yake yi ko kuwa yau ne kawai? Na miƙe na je na ɗaga labulan ƙofata,yana nan a tsaye, amma yanzu ya ɗan sunkuya ya dafa ɗan abin barandar wato gilashi mai zagayen nan. Taɓe baki na yi na koma, meye dalilinsa na ƙurawa dakina idanuwa,ko yana nufin nima irin sa ce mai tsayuwar dare, haka na faɗa gadona na tura kaina a ƙarƙashin filo, sannan na ɗan samu nutsuwa.
Ƙarfe goma na safiya na samu na farka daga saman gadona. Baccin bayan sallar Asubahi da na samu na yi ta da ƙyar, shi ma na san saboda kiran sallar masallacin cikin gidan shi yasa, wanda ake yin shi tamkar a ƙofar taga ta.
Na samu tsayin awa ɗaya, sannan na fito falon ƙasa,wayata da ke rataye a hannuna ita ce ta ɗauki ƙara, ina karawa a kunnena, sai na ji an ce.
"Ina jiran Gimbiya in ta tashi,abincina nake son ci." Sai a lokacin na tuna da ya ce yana cin abincin gidan na safe, na taɓe baki a lokacin da na isa ɓangaren da nake yin karin kumallo.
Su Musulma na zazzaune suna jirana, da sauri suka miƙe suka miƙa gaisuwarsu,a inda na zauna na bubbuɗe abin da su Asiya suka girka mini,kunun gyaɗa ne mai ɗauke da lafiyayyar madara, tare da farfesun dagwargwajajjan naman kaza, wanda babu ƙashi ko ɗaya a jikinsa, gefe ɗaya kuma biredi ne wanda aka yi shi da faɗi, tamkar an yayyankashi.
Ban da kunun aya wanda mutumina ne,ni na ce kullum ina buƙatar a dinga yi mini shi, amma mai kaurin gaske, cikin wata tangaran doguwa kuma tsire ne ya sha kayan haɗinsa sai ɗaukan ido da hanci yake, gefe ɗaya kuwa sinasir ne shishshimfiɗe a ƙwanan tangaran.
Na umarci su Mansura da su samo farantai su shirya su,su kai gidan Yarima su ce ga ni nan zuwa, haka aka yi. Ina shiga na same shi a sashen cin abinci ya kishingiɗa,siket da riga ne na atamfa ƴar Holand a jikina, ɗinkin mai shaf ne (fitted), amma buɗaɗɗan wuya da dogon hannu ne, sai mayafi ƙarami da na lulluɓe kaina da shi.
Atamfar Koriya ce da ɗishi-ɗishin zane baki a jikinta, wanda takalma masu tsini ne a ƙafata,su kuma baƙaƙe, haka mayafin saman kaina. Daga kishingiɗan nan da yake bai tashi ba, har sai da na zauna tukunna ya tashi ya zauna.
"Barka da Asuba." Na ce masa.
"Kin tashi lafiya?"
Na yi murmushi, "ga ni kuwa kaga alama."
"Ya jikin naki?"
"Ya warware."
Na ɗan yi shiru, "Ka yi haƙuri don Allah na manta ne da tuni an kawo maka,ni kuma ban tashi da wuri ba."
"Ba damuwa,ni ma ban daɗe da tashi ba,yau da ƙyar na je masallaci sallah saboda bacci, throughout jiya ban samu bacci ba na rasa abin da ya hana ni bacci.
"Jin daɗi." Na bashi amsa. Ya yi ɗan murmushi, "ina fa jin daɗi ga wanda ba shi da mata." Ya faɗa a daidai lokacin da ya rage sautin muryarsa, na ɗago kai muka haɗa ido da shi, sai na ga ya yi murmushi tare da lumshe idanuwansa tare da buɗe su.
"Ko zaki amince ki zama matata,ki kawo mini jin daɗin?"
Na girgiza kaina tare da miƙewa tsaye. "Zan tafi ni." Na faɗa, amma sai na tsinci kaina da canjawar murya.
"Kayan abincin jiya na ɗaki,ko za ki fito da su,dama ni mai gata ne, da an gyara mini ɗakin nawa yau ɗaya dai."
Ban ce masa komai ba na wuce abina.
"Ɗinkin ya yi miki ƙyau." Na ji ya faɗa a lokacin da na juya na tafi,a zuciyata na ce ka ƙari kinibibinka ni dai ba zan taɓa zama tare da kai ba,mayaudari,in ji da kunnena ka ce ba ka sona, sai yanzun don an hana ka zuwa wajen ƴaƴan turawa, shi ne za ka dinga kashe mini muryar kinibibi. Na gangaro na ajiye kayan kicin na yi gaba, zuwa gidana.
An samu ƙwanaki shida kenan yanayi mini ire-iren waɗannan tsirfar, ban da kallo da yake bina da shi, idan ina zaune a saman dutsen da nake hutawa, amma ko da wasa ban damu da abubuwan da yake yi ba, wani lokacin ma haushinsa nake ji, sai dai kuma abu ɗaya da ban gane shi ba, shi ne idan ina tare da shi duk jikina sai ya yi sanyi,ko magana ba na son yi.
Kuma idan na san yana waje a zaune, zan ga ina yawaitar kallon wajen,ko me ye haka kuma? Ni dai na san ina yawan tunanin Anwar wanda nake ta mafarkin ya zama angona,shekaru huɗu kenan, amma yau rana ɗaya mafarkina ya zama dirama.
Na wayi gari da safe, ranar cikon kwanaki taƙwas, wanda ya zamo daran jiya muna tare da