Asabe tana Ibadan tana auran wani mai kuɗi Alhaji Alabi.
Shi kuwa Abdul Rahman yana Scotland zaune da matarsa baturiya (Vivian), yanda Mama take nuna mini kamar Sarki ya yafe su ƙwata-ƙwata, kenan ya barwa uwarsu su, sai dai ta ce ya kan aika masu da kuɗin makaranta da na abinci da suna yara, yanzun kuwa ko maganarsu ma baya son a tayar.
Asalinsu Mama kuma iyayenta ƴan barikin Ladi ta nan Jahar Plateau,tun da daɗewa a garin Jos,ƴan ƙauyukan garin ke zuwa karatu, wato Makarantar ƙwana ta gaba da Primary,anan suka haɗe da Sarki a lokacin bai ma hau gadon sarauta ba, daga baya ne ma da ya hau mulki ya ƙara auran Hajiya Kilishi.
Yanzun haka iyayen Mama suna nan da ransu a garin Aboko, da sauran danginta. Yarima kuwa shi ne ɗan ta na farko, sai Salimat, sannan Idris, daga su kuwa ba ta ƙara ba. Hajiya Kilishi kuwa anan Jos ya aure ta,ɗiyar hakimin Bukuro ce ta nan ƙaramar hukumar Plateau.
Saboda rashin ganin hanya a ranar da muka zo gaishe da iyayen Yarima, shi yasa ban gane cikin gari suke zaune ba,a unguwar Dogon Agogo,wai wannan rukunin da nake gani har wajen baƙwai a gidan Yarima,wai na farko fada ce in Sarki ya zo kenan dai gidansa ne na hutawa,ko kawo baƙi na musamman.
Sai masallaci a liƙe da shi, ragowar rukunin kuwa kamar namu ne,gidana da na Yarima, sai na su Idris da Ahmad,wai in sun yi aure, amma kowanne da kalar yanda aka tsara nasa ginin, amma tsananin kowanne gida zuwa wani gida, sai an shiga mota,in ba motsa jini za'a yi ba, saboda ko da Asuba ko ragowar sallolin nan an kai Yarima a mota.
*** **** ****
Tsugunne muke gaban Sarki ni da Yarima a ƙaton falonsa, na cikin gida,kawunanmu kuwa a sunkuye suke da gani ka san gaban manya muke.
"Yau ne matarka za ta koma gidanta wacce ta samu tsayin ƙwanaki arba'in da biyu a hannunmu, dalilin da sakacin da ka yi da ita har ta faɗa haɗarin saran maciji.
Bayani ya same ni na irin zaman da ka yi da ita a baya, zaman ko in kula da banzatar da ita. Wannan dalili ne ma ya janyo mata faɗawa rayuwa ƙuntatacciya, na gode,ka yi mini daidai ashe ni ina taƙama da ina da ɗa mai biyayya, ashe ban sani ba,ƙarya zuciyata ke gaya mini.
Ka bani mamaki,a ce ita mace na je na nemo auranta ga iyayenta, suka amince suka ba ka ita, alhalin ba ta san ka ba, kuma suna da wanda ke jiransu su aura masa ƴarsu, ita ma tana da wanda zuciyarta ke so, amma ta haƙura ta yi biyayya ga iyayenta, kai kuwa ban isa ba."
"Baba...." Yarima ya faɗa cikin sanyin murya.
"Kada ka ce mini komai, kai ne da bakin ka ka gaya mini da ka amince in zaɓa maka wacce na ga ta dace da kai, tun daga ranar na baza mutane a kan su gano mini matar da ta dace da ɗana wanda nake mugun ƙauna a zuciyata, Allah ya ba ni ya kuma ba da sa'ar aka samu ƴar gidan manyan mutane masu mutunci.
Ka tuna,bakina da naka muka yi wannan maganar ba fa aike na yi maka ba,ka tuna,kiranka na yi ka faɗa mini wacce yarinya ka gani ta ƙwanta maka a yi maganar auranku,ka tuna, kai da bakinka ka ce mini babu.
Yanzun na yanke hukunci zan raba auranku, amma na baka tsayin ƙwanaki biyar ka zo mini da rubutacciyar takardar sakinta...."
"Baba...."
"Bana son jin komai daga gare ka,ka bani haushi,ka ɓata mini raina matuƙa."
Ya miƙe tsaye, "Ɗiyata ina ƙaunarki da ɗana, amma ki je kiyi haƙuri, sannan ki yafe ni da na sa aka raba ki da wanda ke son ki,saboda son kai irin nawa. Zan aiko a yi kiranki." Ya juya ya tafi.
Yana ƙulewa a inda har ya ƙule, Yarima na Baba,Baba cikin girmamawa, amma bai ko juyo ba,ni kuwa na waigo a sanyaye na kalli Yarima inda ya koma ya ƙarasa zama a ƙasa.
"Tashi mu tafi." Na faɗa cikin muryar da zata ƙara karyar da zuciya.
"Kin ji abin da Sarki ya ce fa Yasmin."
Na ɗan yi murmushin da ƙago shi kawai na yi.
"Kana da magani?" Ya girgiza kai. Na miƙe na bar shi a wajen zaune,gudun kada ya karyar mini da zuciyata.
Ina jiyo su daga falo,suna cikin ɗakin Mama yana gaya mata, amsar da ta bashi ce nima ta ɗan firgita ni.
"Gara haka,ai ni har naji daɗi, tun da baka son ƴar mutane a dinga ajiyarta a gidanka,ƙwanaki nawa kuka ɗauka da ita ba ka ji kana son ta ba,sai yanzu....?"
"Mama zan iya yi miki rantsuwa da Alƙur'ani akan ina son ta, Mama duk laifinta ne...."
"Laifintan wa? Kusan kullum sai mun yi waya in har baka zo ba,in dinga ƙwatanta maka cewa don tana mace,kai ya kamata ka dinga shishshige mata,yau da gobe za ta saki jiki da kai."
"Wallahi Mama, ina yi mata, ita da wanda take so,wai shi ANWAR."
"Shi kenan ka ga yanzu ka yi wa kanka, ita kuwa tana da wani."
"Mama yanzu ya zan yi? Wallahi ina son Yasmin,ni dama can ina son ta."
"Ƙarya ka ke yi, da kana son ta da baka tsaya yi mata mulki da kuma ƘASAITA ba, haka ka ga muna zaune da mahaifinka?
Mulkinsa da ƙasaitarsa a waje suke, sai kuwa idan ya shigo gida ya ga barorinsa, wannan dole ya yi,kana kallo wata rana da kansa zai leƙo ya kira wacce yake son yin magana da ita a cikinmu.
Ko an ce maka jakadiyar da aka sa a tsakaninku, Addini ne ya shinfiɗa ta?"
"Mama matsalar, Mama, Yasmin ba ta sona ƙwata-ƙwata,ni kawai ke sonta."
"A yanzu ko kai ma?"
"Mama ki tuna ranar da na fara ganinta daga can sai nan fa nazo na gaya miki na ga yarinyar da nake so,amma ban san ko ƴar waye ba, har ki ka ce sai in je in ta nema, wallahi Mama ita ce nake gaya miki, don dai haɗuwarmu ta zo ne da saɓani shi ya sanya...."
"Saɓani ko dai ka nuna mata kai ka isa, dole ne ta ji tsoron zama da kai yanzun."
"Mama duk ki bar wannan maganar,a yanzu na ajiye duk wata ƘASAITA in dai ina tare da Yasmin kamar yanda nake miki Mama."
"Yanzun ko?"
"Mama,ki taimaka,in Sarki ya haƙura ma zamu Greece Honeymoon da ita."
"In tana son ka ko, na san zai sa a tambaye ta,in ta nuna a'a, to kai ka sani."
"Mama zan yi ƙoƙarin da Yasmin zata so ni, wallahi na yi miki rantsuwa da Allah."
"To na ji kayi ta addu'a ka san halin Sarki, baya tayar da magana in dai har ya furta ta da bakinsa,ka san dai ba sabon abu ba ne ba wannan. Yanzun da ƙafar ƴar mutane ta lalace ya za mu cewa iyayenta?"
"Mama shi kenan mu zamu tafi, zan dinga zuwa."
Ta yi dariya, "Dama ni ce Yasmin in ce sai Anwar " Ta cigaba da dariya. Suka fito,ni kuwa sai ma na nuna ban san abin da suke yi ba.
"Ƴan gidan tun daga nesa na hango su tsaye ana ta murna,kai har da mazajen sashen gidan Yarima, Allah Sarki, Mansura har da kuka,yarinyar nan ta shiga raina nima,ko don yadda take nuna mini ƙauna,wai sai da muka kusan wajen sannan aka ƙara sakin labulan nan baƙi, duk da dama gilashin motar ma baƙi ne, sai dai ka ga mutum amma shi baya ganin ka.
Ya juyo sosai ya riƙe hannuna, "A tanadar mini abinci,yau gidanki zan yi hira, saboda in taya ki zama." Na rausayar da idanuwana na yi murmushin da na san gefen kumatuna suna lotsawa.
"Ka fi ƙarfina." Ya yi saurin matsowa. "Kada ki ƙara faɗar haka, har kin janyo ma ba zan iya wucewa gidana ba,naki gidan zan sauka."
Ka rufa mini asiri."
Sai na ga ya yi saurin sakin hannuna ya matsa baya, wacce ta yi daidai da buɗe ƙofar motar da muke ciki. Mun gaisa da jama'a da dama, sannan muka haye sama ɗakina, sai na ji na kasa komai. Wannan yasa na dinga haɗa shi da Allah ya tafi ɗakinsa,an jima da dare ya dawo hirar sannan ya amince.
Ƙwana uku yana zuwa taya ni hira, sai sha biyun dare yake tafiya, a ranar na huɗun da goma na dare na ji wayar hannuna ta yi ƙara, na ɗauka a tunanina Aunty ce, sai na ji muryar Yariman da na gaji da jira, na yi ƙwalliyata mai ƙyau, saboda shi amma shiru, wanda na kasa zaune na kasa tsaye saboda rashin zuwansa,ni kuma na kasa zuwa inda yake in dubo ko lafiya.
A hankali yake magana cikin muryar da zata iya tayar maka da hankali, idan ka ji ta, saboda tafi yanayi da ta marasa lafiya,a take kuwa na ji hankalina ya tashi.
"Yasmin na kasa zuwa wajanki."
Cikin yanayin tashin hankali na tambaye shi, "Ba ka da lafiya ne?"
"Eh, to ni ya zan ce miki, zaki iya zuwa gare ni yanzu? Yasmin forget the fast please."
"Zan yi tunani."
"Please Yasmin."
"Okey,na ji."
Ya kashe wayar, na miƙe tsaye daga zaunawar da na yi a gado, na nufi madubina, na ƙara feshe jikina da turare, na kalli kaina irin kayan da ke jikina, riga da siket ne na Turawa amma buɗaɗɗen siket ne, ga shi da tsayi har zuwa ƙwaurina,bulu ne mai haske (light blue).
Sai ruwan ja amma mai haske light pink mai dogon hannuwa ce, amma daga ƙarshen hannun buɗaɗɗu ne, sai buɗaɗɗan wuya, wanda ya nuna sashen bayana a buɗe yake, haka gaban rigar (roundneck) , zagayayyen wuya ne, da wasu zarirrika biyu a gaban rigar waɗanda an yi su don ƙwalliya kawai.
Takalmin ƙafata masu ɗan tsini ne,kalar rigar jikina, amma ɗan mayafin da aka sakowa kayan irinsu ɗaya da siket ɗin,bulu mai haske kenan, sai da na feshe gashin kaina da turaran shi, sannan na mayar da mayafi na yafa kalar rigar jikina,alkyabbar da na rufa a sama, ita ma pink ce, sai da na kuskura man ƙamshin baki mai ƙamshin (mouth wash,rinse), sannan na rataye wayata mai ruwan alkyabbar a hannuna.
Na murɗa ƙofa na shiga,ƙasan ba kowa sai fitilar nan ɗaya da aka saba bari duk dare na Ubangiji, na haye matattakalar bene,domin in isa ɗakinsa.
Falon sama na same shi ƙwance cikin kujerar hutawa farar shirt ce da wando a jikinsa, amma ya ɓalle maɓallan gaban rigar, sai farar singilet ce ta rufe fatar naman jikinsa.
Wayar hannu ita ce a saman ƙirjinsa, wacce kalar jikinta fari ne daga ƙwancen ya juyo ya kalleni.
"Yasmin."
Shi kaɗai ya faɗa, amma bai tashi ba, na iso na tsugunna gabansa.
"Ba ka da lafiya ne?" Na dafa saman goshinsa, ya lumshe idanuwansa.
"A'a."
"Yana ga jikinka ya yi laushi?"
"Ke ce."
"Me ya faru kuma?"
"Gobe ne fa Sarki ya yanka mini."
Ya yi shiru nima sai na ji gabana ya faɗi. "Na yi waya da Mama yanzun kafin in yi miki, amma ta ce Sarki yana nan a kan abin da ya faɗa."
*ƘASAITA BOOK 2*
*NA*
*MARYAM KABIR MASHI*
Page 3
"To me ye na damuwa?"
"Na san halin Sarki ba tayar da magana."
"Shi ne na ce me ye na damuwa? Iyaka ka auro wacce ka ke so,dama ni ma takura ka aka yi ka au...."
Ya tashi zaune tamkar tashin wanda ba shi da lafiya.
"Me ye abin damuwa Yasmin? Ni ke ce abin damuwata."
Na miƙe tsaye na ja baya tare da dafa goshina, na juya kamar zan tafi.
"Yasmin,No! No!! No!!! I love you. Na juyo da kaina na gan shi a tsaye yana kallona, na girgiza kaina na juya zan tafi.
"Please, Yasmin."
Na tsaya cak a lokacin da na ji wani abu yana yi mini yawo a cikin jikina, wanda ba zan iya faɗar yanda yake ba, na mayar da idanuwana na lumshe tare da fitar da numfashi sama-sama,shin me ye wannan? Ban kai ga tunanin amsar ba, na ji an rungume ni ta baya.
Ajiyar zuciya uku ce ta fito gaba ɗaya a cikin sakan ɗaya, kafin in yi tunanin ya zan yi in ƙwace jikina daga Yarima, sai na ji ya zame alkyabbar da ke sanye a jikina zuwa bayana, madadin buɗe bakin da na yi inyi magana, sai dai bakin ne ya tsaya a buɗe sakamakon sumbata da ya kai a buɗaɗɗan bayana, wanda riga ba ta ƙarasa rufe shi ba.
Madadin inji ya sake ni, sai na ji ya cigaba da sumbatar wuyana zuwa bayana. Me ye wannan ke yi mini yawo a jikina? Lallai ba zan iya gano ko me ye ba,saboda ya fi ƙarfin in iya faɗarsa, jin alkyabbata ta faɗi ƙasa, ita ta dawo da hankalina a jikina, wanda na ji sam ba shi da ƙarfin komai.
Ba zan iya wata magana ba, sai dai na yi ɗan ƙoƙarin da bai wuce na mirginawar marar lafiya ba, na zame jikina, ina girgiza kaina, idanuwansa a lumshe suke inda yake saukar da numfashi sama-sama kamar mai asma farkon tashi.
Numfashin haɗe yake da faɗar, "No! No!! No!!!" Wacce ba zan iya ƙirga ko nawa ce take fita daga bakinsa ba, wannan ne ya ba ni damar jan jikina in tafi gidana, wanda ko alkyabbar ban tsaya ɗauka ba.
Sai da na tsaya jikin ƙarfen matattakalar bene na ɗan huta,don ƙarfi ya samu a jikina, sannan na samu na iya gangarewa ƙasa, har na kai ƙofa na murɗa na juyo muryarshi.
"Yasmin." Na waigo na kalleshi tsaye yake a ƙofar benen riƙe da alkyabbata a hannunsa, na mayar da kaina na sunkuya a inda ya iso, ya tsaya gabana tare da miƙo mini alkyabbata,na karɓa muna kallon-kallo da shi.
Sannan na murɗa ƙofa zan fita, ya juyar da kai tare da ɗan asirtaccen murmushi, wanda da gani tare yake da takaici, saboda fitowar da ya yi tare da numfashi, sai da ya yi irinsa ya kai sau baƙwai, sannan ya ja baya na buɗe ƙofar, ya yi saurin riƙo hannuna.
"Yasmin stay with me." Na girgiza kai, na saɓula hannuna na yi gaba, sai dai na jiyo shi yana kiran. No! No!! No!!!" Ɗinsa da ya saba kira,ko waigowa ban yi ba.
Da gudu na haye saman ɗakina, ina zuwa na faɗa gadona, sai da na mayar da numfashi ya fi talatin kamar wacce asma ta taso mata, ga idanuwana a lumshe, sannan na ji tunani ya zo mini.
Shin ko wannan shi ne SO? Na girgiza kai,ba zan so Yarima ba. To me ye wannan? Oho, abin da zuciyata ke faɗa kenan,nan take ta juya linzamin tunaninta ga abin da ya faru ƴan mintuna da ba su wuce goma ba da suka wuce.
Jikina na ji ya kama rawa shi kaɗai, na yi sauri na miƙe tsaye, sai na ji kamar jiri na shirin kada ni, na yi saurin zama, na cire mayafin kaina na jefar da shi ƙasa, na juyar da kaina, kamar wacce ta rasa abin da ke yi mata ciwo a jikinta, na sunkuyar da kaina, gashin kaina ya zubo a fuskata,a inda na tura hannuwana duk biyun cikin gashina.
Na samu mintuna goma sha biyu a haka, sannan na ji kamar an sumbaci bayana, na yi saurin ɗagowa, amma ban ga kowa ba, na yi murmushi na miƙe na nufi banɗaki. A banɗaki na cire kayana duka na shiga ruwan wanka mai ɗumin gaske,wai ko abin da nake ji ya sake ni. Tsayin mintuna biyar na yi kawai na miƙe da sauri, saboda tunanin da ya faɗo mini a lokaci ɗaya.
Na ɗaura tawul na fito da saurina,wai ji nayi kamar an bugo mini waya,ba abin da ya faɗo mini kuwa sai maganar Sarki.
"Zan turo a kira mini ke kin ji."
Hankalina ya tashi matuƙa, gobe, gobe lallai zan shiga damuwa kenan in an rabani da Yarima.
Na yi saurin tunano Anwar a zuciyata, take sai na ji bana son tunaninsa,na fi son tunanin Yarima,shin ina son Yarima? Ba amsa, na ɗauki rigar bacci ta da su Mansura suka ajiye mini na zura a jikina, da ƙyar na iya ɗaga ƙafata na zura ɗan diras ɗin da ke kusa da ita, na isa ga madubi na taje kaina tare da ƙara gyare shi.
Rigar baccin doguwar shimi ce har ƙasa, orange colour da ƴan hannuwanta guda bibbiyu a kowanne ɓangare sai ɗan leshi da ya ratsa saman ƙirjinta, ruwan lemo ce mai santsin gaske. Na feshe jikina da turare madadin in haye gadona sai na ji na kasa, buɗe ƙofar barandar gaban gidan na yi na fita.
Kamar yanda na saba a kullum yau ma haka na yi, shi ne in ware hannayena duk biyun,yau ma kuwa na samu sa'ar garin yana fitar da iska mai sanyin gaske, wadda ta taimaka da wasa da gashin kaina, idanuwana kuwa a lumshe suke, amma na kasa tunanin komai a yau.
Cikin wani sanyin jiki da sanyin zuciya, na ji tunanin Yarima ya faɗo mini a zuciyata a iya nawa tunanin, sai na ji dama Yarima ya iso yanzu,can ɗayan gefen na zuciyata kuwa, sai ya dinga karanto ni a jikin Yarima,a cikin tunanina ne na ji kamar an bi nawa hannayen a hankali, wani daɗi ya dirar mini a zuciya.
Cikin tunanin kuwa na ji an haɗe ƴan yatsun hannuna da nashi waje ɗaya an runtse su, cikin ƙwanciyar hankali ya rungume bayana a ƙirjinsa, sumbatar da ya kaiwa wuyana shi yasa na saukar da ajiyar zuciya mai fitar da sauti.
Hankalina gaba ɗaya na ji ya ɗauke har ya zamo na manta mai nake ji a jikina, ƙwaƙwalwata ta fara karanto mini da in buɗe idanuwana da suka yi nauyi in ga ko zan ga Yarima a barandarsa.
Cikin sakan biyar na ji hankalina ya dawo a jikina, madadin in jini ni kaɗai ina tunanina, sai kawai na tsinci kaina da jin ɗumin mutum a jikina, gaske ne,ko dai har yanzun mafarkin tunanin ne nake yi,jin sautin numfashi na tashi a kunnuwana yasa na buɗe idanuwana da sauri.
Na razana, na tsorata, duk a lokaci ɗaya da na ji bakina ana Yarima, na yi ɗan gaggawar fizge jikina na ja baya, kenan mafarkin tunanin da nake yi da gaske ne, na girgiza kai tare da ɓata fuska.
"Me ke damun ka haka? Bana son abin da ka ke yi mini,ba na..."
"Yasmin ya isa haka nan,don Allah, na san na yi miki laifi a baya, ya kamata ki zamo