x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 7 - KASAITA 3

  • 18001 words
  • 21000 words
  • Out of 27580 words

Category: Love Stories

Views 62

02 Jul 2025
Start ads
After Image Ads
shi fashi da makami.

Hajiya Asabe uwarsu kuwa an kamata da laifin yin zina kafin ta yi aure, da ta yi kuma tana shigo da wani namiji a cikin gida. Tuhumar ƙarshe kuma ta tabbatar cewa su Abdulrahman ba ƴaƴan Sarki ba ne, sakamakon faɗi da tayi da bakinta cewa ƴaƴan faranta ne.

Hadiza kuwa zaman kanta take yi yanzu haka, ban da gidanta ne matattarar ƴan duniya, ban da bin bokaye da take yi, wanda ya bayar da tabbacin har maƙabarta an taɓa kama ta tana tono wani sashi na jikin matacce. Wa'iyazubillah. Allah ka cikamu da imanin mu,masu yi Allah ya shirye su. Na faɗa a zuciyata.

An yi an gama, sai rigima ta dawo kan Yarima, wanda aka zaɓa a matsayin shi zai hau kujerar sarauta, amma ya ƙiya, ya ce shi da Jos har abada. Wannan al'amari ba ƙaramin tayar da hankalin jama'a ya yi ba. Har ya zama garin Kaduna ƴan garin sun zo, tunda kullum ma samu baƙi ƴan baiwa Yarima haƙuri, da ba shi baki akan ya koma gida. Amma maganar shi ɗaya ce Kaduna ta yi masa, shi hankalin shi a ƙwance yake.

Yau kuwa manyan baƙi ne, wato ƙungiyar su Waziri, amma Yarima ya ƙiya. Da na je gaishe su suka dinga roƙona a kan in ja hankalinsa in nuna masa muhimmancin mutanen da zasu zauna a ƙarƙashinsa. Na bisu da to. Amma na san ba zan iya tunkarar Yarima da wannan maganar ba.

Su Daddyna sun zo tare da Mamee, amma sai ya ce masu insha Allahu zai yi,su bashi lokacin ya yi tunani. Haka suka tafi suna murna. Amma suna tafiya ya ce ai shi sam,kunyar su tasa ya amsa masu. To ni kuwa dama da na ɗauko hanyar yi masa maganar, kallo ɗaya yake yi mani in yi shiru. Wani lokacin ma har in samu la'adar cewa ba ni da hankali.

Sarki Jafar Sada ne yau da kanshi da Iyalansa gaba ɗaya a gidan mu,Mama, Hajiya Kilishi, Ahmad,Yaya Salimat,Sauda, da Idris,Sarki ya yi gyaran muryar da dukkanmu sai da muka nutsu, sannan ya soma magana.

"Faysal my lovely son. Da farko zan fara da roƙon Allah ya raya maka zuri'arka, ya yi maka sakayya da aljannar fiddausi.

Faysal,sanin kanka ne ba mai raba ni da kai sai Allah, amma akasi ya faru tsakaninmu ta sanadiyyar yaudara da aka fara yi ta hanyar gaya mana aibunka da illolinka. Ban yarda ba da farko, sai da aka kawo mini shaida ta zahiri."

Ya buɗe wata ambulan ya miƙawa Yarima kaset da wasu hotuna.

"Duba!" Ya ajiye.

Ban kawowa raina komai ba. Ta haka ta fara yaudara ta. Ganin raina ya ɓaci matuƙa har na ɗan yi fushin ƙwanaki da kai,ai sai wannan hanyar ta ba shi damar shigo da abubuwan da na san sun daɗe yana tanadar su. Magana dai ni ke son ta wuce,a taƙaice ina neman a yi haƙuri a kan duk abubuwan da suka wuce,a taryi gaba,a kiyaye. Ko kana da magana?"

"Baba ni ban ce kayi mini laifi ba,ni ban riƙe kowa ba,ni dai nayi kokawar ƙwato maku ƴanci ne don kuna iyayena, amma ba don na hau gadon mulki ba. Na gode ƙwarai da ƙyautar da ka yi mini da nuna ƙauna, amma na barwa ɗaya daga cikin ƙannena,ai su ma sun girma. Amma ni Kaduna zan cigaba da zama, saboda hanyoyin cin....."

Ya miƙe ya je ya tsugunna ya kai gaisuwa. "Amma idan na ɓata muku rai ku gafarce ni." Ya miƙe ya shiga ciki.

Falon mu ya yi shiru har tsayin mintuna masu tsayi. Can Sarki ya nisa, "Yasmin, Hajiya Mariya, Hajiya Kilishi, aikin ku ne,kushawo kan ɗanku. Ke kuma mijinki. Koma in ce aikin ki ne. Yasmin ki taimaka ki shawo mana kan mijinki, ya taimaki jama'ar da ba mu san iyakacinta ba."

Ba ni da damar yin gardama, sai dai na bishi da, "To Baba, za'ayi ƙoƙari."

Ni kuwa har hantar cikina sai da ta kaɗa. Daga nan kuwa aka cigaba da ƴar hira, jin falon ya kaure da surutu yasa Yarima ya shigo shi ma ya zauna aka ci gaba da yi dashi.

Sai da suka ci abincin ranar mu, sannan suka tafi,mu kuwa rakiya har mota. Yau an samu shiga, bayan mun dawo hirar mu kawai muka cigaba har ya tafi gona.

Bayan mun shiga ɗaki ne har ma mun yi niyyar ƙwanciya kenan an gama duk wata hira. Na ɗauko Novelle Gelly ina shafawa a jikina, domin jikina ya ɗau ƙamshi gaba ɗayan shi. Gefen gado na zauna, amma gabana ke ta wani irin mummunan faɗuwa, saboda maganar da nake son ta fito daga bakina. Ban kashe fitila ba na hayo gado na zauna kusa da shi tare da robar man ƙamshin jikin nan a hannuna,sai kuwa kaɗawa take yi, da alama jikina ke rawa.

Sai da na karanta addu'a sannan na ambaci sunan shi.

_Ya waliyyan ni'imati,wa mallazi inda kurbati,ij'alni matahu bardan wasalam alayya kama ja'altana barda wassalamun ala Ibrahim (Ƙafa baƙwai).

"Honey." Na kira shi a sanyaye.

"Ina jin ki Sweetyna." Ya faɗa, har da ɗora hannunsa a saman cinyata.

"Magana nake son mu yi da kai mai mahimmanci."

"Ina jin ki. In kuma so ake in ƙara wani cikin, to ban manta ba." Ya faɗa har da ɗan taɓa mini gefen cikina. Na yi murmushin da yake haɗe da fargaba.

"Honey maganar sarau...." Wata tsawa da ya daka mini. Bani ba,na yi imani maigadi ma ya tsorata. Ni kuwa har na kai bakin gado, saboda na yi zaton duka ne zai biyo baya. Tun kuwa da na sauka, na durƙushe nake jin ɗan cikina na mutsulniya, tamkar ɗan kifi a ruwa.

Bai ƙara cewa ƙala ba daga wannan, sai ma ya juya min baya. Gaskiya na san na yi awa ɗaya durƙushen nan, ina saƙa hanyoyin da zan bi. Ganin ba shi da wani alamun motsi ballantana in san hanyar da zan bi, sai na ce, "Wash! Wash!! Wash!!! Cikina." Ina faɗar cikina na ga ya yi saurin saukowa.

Tun daga can na ji yana cewa, "Me ya samu cikin? Da ke nake,me ya samu cikin?"

"Ciwo yake. Marata!"

"Tashi mu gani."

Ya yi saurin isowa ya kama ni. Na lanƙwashe.

"Ba zan iya ba, ina jin ɓari zan yi."

"What? To kin ga ni ga irin ta nan,kin sawa ranki abin da ba ruwanki, ga shi nan za ki janyo mana asarar ƴaƴana. Taso mana mu tafi asibiti." Ya sake ni, ya tafi ya buɗe durowa ya ƙwaso mana kaya. Ya zo ya kama ni.

"Tashi, sannu." Ya yi alamar ɗaga ni. Na riƙe hannunsa.

"Yarima!”

"Ba na ce bana son kina kirana da wannan sunan ba?"

"Na sani,ka yi haƙuri, amma yau ne na ƙarshe, tunda ka nuna mini ba ni da amfanin komai a wajen ka. Yau zan haƙura da auranka,gara ka auro wacce take da muhimmanci da amfani a wajenka." Sannan nasa kuka.

Ina jin sa ya tsugunno. "Yasmin me ya faru? Me na yi miki? Ba ki taɓa gaya mini magana mai ɗaci ba sai yau."

"Yau ma kamawa ta yi." Ya ɗago kumatuna.

"Haba Yasmin, ya zaki tayar da hankalin mijinki...."

"Ba ka son a tayar da hankalin ka, amma kai zaka tayar da na mahaifinka?"

"Ba ruwan ki da maganar mu."

"Kenan ba ruwan ka da ni? Don Allah in tambaye ka?"

"Ina jin ki."

"Yanzu me ye nan cikina?"

"Ɗana ne."

"Kana son shi ko baka so?"


######
[2/28, 08:27] Ummi Tandama😇: *ƘASAITA BOOK 3*


*NA*

*MARYAM KABIR MASHI*


Page 10


"Wacce irin magana ce wannan Yasmin?"

"Ka ce mini eh ko a'a."

"Ina son shi mana."

"In ya zube za ka ji ciwo."

"Ƙwarai kuwa."

"To ka yi tunanin irin ciwon da za ka ji,ka ƙwatanta shi ga in ka rasa ɗan da ya girma za ka ji ciwo. To mahaifinka abin da yake ji a zuciyarshi ya linka naka dubu, kuma tunda ba ka jin ban haƙurin shi, to ni ma ba zan ji ban haƙurin ka ba, zan bar maka gidanka da ƴaƴanka, amma zan tafi da cikin jikina,in je Likita ya cire mini...."

"Ki rufa mini asiri Yasmin,duk wata taƙamata taki ce,kin zauna da ni a lokacin da na shiga babban tashin hankali, sai kuma yanzu a kan ƙanƙanin abu ki ce ba zaki zauna da ni ba."

"Kai ka ɗauke shi ƙarami."

"Yasmin ke nake ji, ina son ki,ina son zama da ke, muddin na karɓi sarautar nan sai ya zamo na yi miki amarya."

Ɗan cikina ya sake wajen ƙwanciya da saurin gaske, saboda tashin hankalin da maganar Yarima ta haifar. Jinyar sakan biyar na yi sannan na yi magana.

"Na amince ka yi idan dai har za ka bi maganar iyayenka."

"Yasmin kin kuwa ji abin da na faɗa?"

"Na ji, cewa ka yi zakayi min amarya,ko ba haka ka faɗa ba?"

"Haka na faɗa,kin amince?"

"Eh, amma kai ma in ka amince gobe da safe za mu je Jos,ka gayawa Sarki ka amince da abin da yake so, sannan za ka koma Jos da zama,in ba haka ba,yau ba zan ƙwana gidan ka ba."

"Wannan ma bata taso ba,dama na ga wata yarinya ɗazun da na dawo daga lambu, sai kallona take yi,kin ga shi kenan sai in koma in gani. "Ƴar gayu ce."

Na yi murmushi, "Ƙyan Namiji dama ya auri mace wacce ya gani da idonsa ya ji ta ƙwanta masa a zuciya, ba wai wani ya gane masa ba."

"Yasmin kenan, ba ki san cewa matar daraja da ɗaukaka ta bi bayan zaɓin Iyaye....."

"Ya isa,mu je mu ƙwanta."

"Cikin fa?"

"Ya lafa, zan iya kai wa safe." Ya kama ni muka je muka ƙwanta.


**** **** **** **

Taro kan ya haɗo jama'a, ta ko'ina, sai isowa suke yi. Manyan sarakuna na ƙasa, gwamnoni,kai har da shugabannin kasashe, duk sun iso filin jirgi na garin Jos. Mu kuwa muna gefen mata, wajen su Mama, amma ni ma da tawa gayyar a bayana.

Yarima na can daga sashen su Mai Martaba ya sha alkyabbar alfarma. Abin ka ga farin mutum, ya yi ƙyau, wanda ba ya misaltuwa. Ni kuwa ni da Aunty Salwa daga ni sai ita muna hirar jama'ar da ke wucewa.

Bayan kamar awa biyu kowa ya gama zama aka ce Sarkin Malaman Sarakuna ya zo ya buɗe filin taro da addu'a (Adalin Sarki kenan,Sarkin Musulmai Dr. Usman Nagwaggo) Sarkin Katsina kenan. Dattijo fari tas, mai ruwan matasan yara, jikinsa ba ya tsufa. Shi ya fito ya fara jero addu'o'in buɗe taro tamkar wanda ya girma a tsakiyar Larabawa, saboda harshen da ya karya tamkar na matashin Balarabe.

Tsayawa bayanin abubuwan da aka yi ma mun san ɓatawa kanmu lokaci ne, balle lissafa manyan da suka halarta. Amma mun san Sarkin Sarakuna na Nijeriya, manya ba wani a gabanka, shi ya yi naɗin sarautar,wato Mai Martaba Alhaji.Dr. Ado Bayero, wanda jama'a ke so kenan.


**** **** ****

Wani irin mahaukacin gida ne aka bai wa Yarima, har sai da ya ba ni tsoro. Na kalli gidan, daga ni sai ƴaƴana biyu, sai cikin da ke jikina wanda bai wuce wata baƙwai ba. Masu yi mana hidima kuwa ba su ƙirguwa, amma Mama ta ce in dinga yi wa mijina abinci da kaina. Haka kuwa aka yi, duk na ware ɗaki ɗaya na mayar da shi kicin ɗin kaina, wanda ni kaɗai ke shigarsa, sai kuwa ƴaƴana, amma ko jakadiya shakkun shigarta ciki nake yi.

Tsarin kundin littafin mulkin aka damƙawa Yarima domin ya yi nazarinsa, duk da ba wai shi kenan Mai Martaba ya daina aiki ba, a'a mulkin na ga hannun Mai Martaba, Yarima kamar ɗalibi ne da malami, wato ya koyi yanda ake yi, tun kafin Mai Martaba ya rasu ko kuwa ya yi tsufan da ko ya yi magana ma jama'arsa ba za su saurare shi ba,ko kuwa a dinga cewa ruɗin tsufa ne, amma yanzu da hankalinsa, duk abin da aka yi ba daidai ba zai tsawatar.

Dama su tsarin mulkinsu kenan, shi ne a baiwa wanda ake ganin ya cancanta a baiwa sarauta, tun Sarki na da rai, ba don komai ba sai don ya ga yanda zai tafiyar da nashi tsarin mulkin, saboda in ya yi kuskure a nuna masa hanyar gyara.

Shi kuwa Yarima, sabon tsari muka zauna muka gyarawa littafin nan, saboda wani al'amarin da ake yi yakan ɗan taɓa talakawa, sannan shi Addininmu ya nuna za'a tambayi duk wani mai mulki haƙƙin yanda ya tafiyar da talakawansa.

*** *** *** ***

Tsarin da Mai Martaba na biyu ya yi, ya burge kowa, ya kuma ƙara masa farin jini a wajen talakawansa. Tsarin kuwa shi ne da kansa ya zagaya garin Jos da kewayenta domin sanin halin da talakawansa ke ciki. Wasu lokutan kuwa ma ba a shigowa a mota sai a ƙafa, wasu kuwa ƙwatami ya yi yawa, wasu ƙauyukan kuma da ƙafa ake zuwansu.

Wannan rangadi ya ɗauke shi tsayin wata biyu har da ƙwanaki goma sha baƙwai,yana yin shi. Wata rana Yarima ya dawo da fara'a, wata rana kuwa da kuka yake iso mini,saboda irin ganin da idonsa ya yi na halin da talakawansa ke ciki.

Ni kuwa ciki ya tsufa, amma har yanzu haihuwa ta ƙi zuwa, wanda zan iya cewa na shanye watan haihuwata, ma'ana na wuce watan haihuwata. Wannan kuwa ya tayar da hankalin Mai Martaba na biyu, Yarima kenan.

Ƙarfe tara na dare shi ne ƙa'idar tashin Yarima daga fada, saboda ya samu lokacin hira da iyalinsa. Yau ma kuwa haka ya shigo gida, ya sameni ƙwance a ƙasan kafet ɗin da kusan launinsu ɗaya da katifa. Suhailat na ƙwance a gabana ta yi bacci. Yanayin yanda fuskarsa ta nuna shine yana tausaya mini. Yana isowa ya sunkuya ya ɗauki Suhailat ya kai ta ɗakinsu, sannan ya dawo ya durƙusa a gabana. Ya sunkuya ya sumbaci kumatuna.

"Sannu." Na ɗan yi fari da idanuwana

"Wallahi Yasmin ina tausaya miki."

*Ni kuma kai nake tausayawa, saboda aikin da ke gabanka na jagorantar mu. Ga ni da ƴaƴanka,iyayenka da nawa,ga jama'ar garin. Ga jama'ar garin nan ba ki ɗaya duk fa a ƙarƙashin ka muke. Yanzu in mutuwa ta kama ka ka ce da Allah me?"

"Wallahi kuwa,ai shi yasa nake son in ga kin haihu lafiya sai mu zauna mu yi shawarar ya zamu yi balle dama duk inda muka je an ɗaukar min shi a kaset, sai mu sa a tsanake mu ƙara gani."

"Honey,tunda haihuwar ta ƙi zuwa me zai hana a fara, tun da idona da bakina za su yi aikin ba cikina ba. Yanzu da ka ce a bari sai na haihu,to in na mutu wajen haihuwar fa..."

"Haba Yasmin ki daina irin wannan mummunar maganar ta ƙananan yara,me ki ke so na koma idan na rasa ki?"

"Baka zama komai."

"Na ji nidai ba na son ki dinga yi mini irin waɗannan maganganun marasa daɗi da ɗaci."

Ya juya har da ɓata rai sosai. Hannu na sa na juyo fuskarsa.

"Sorry, ba zan kuma ba na daina." Na faɗa cikin muryar nadama.

Ya ɗago fuskata ya ƙura mini ido, sai kawai na ga ya kai bakinsa ga nawa. Mun yi minti huɗu ya ɗago.

"Yasmin ni fa har yanzu son ki bai taɓa raguwa a zuciyata ba,kin san Allah duk every day, every time, every minute,every second,sai na ji sonki yana ƙaruwa a zuciyata. Ki daina gaya mini maganar da raina zai ɓaci,ki tayarwa da mijinki hankali,kin ji?" Na ɗaga kai alamar eh.

"To bari na ɗauko kaset ɗaya mu fara da shi."

Na yunƙura zan tashi ya yi saurin kama ni, na miƙe.

"Ina za ki?"

"Da abin hira zan ɗauko maka,in samu kuma in cire maka kayan jikinka."

Ya ja kunnena, har sai da na yi ƴar ƙara.

"Ke ɗin nan ba ki jin magana,sau nawa ina gaya miki cewa idan ina cikin gida kusa da ke na zama ɗan aiken ki.?"

Na narke na yi irin alamar kukan shagwaɓa, tare da maganar shagwaɓa.

"Ni Allah ban yarda ba,ni sai in dinga baka wahala."

"Wallahi na cije bakinki idan ya ƙara yi mini gardama."

"Ni! Ni! Dai...." Ya zare takalman ƙafarsa zai ƙwala mini cikin haushi. Na yi gaba da ɗan guduna, ina kiran.

"Na daina, na daina, Allah....."

Ya kamo ni saboda irin yanayin gudun mai ciki. Ya ɗaga takalman, na runtse idanuwana alamar tsoro, sai na ji ya zagayo ta bayana ya rungume ni yana dariya.

"Ga tsoro ga jan faɗa."

Dama yanda yake rungume ni kenan idan ina da tsohon cikin da zai hana masa sakewa ya rungume ni ta gaba. Ya sumbaci wuyana.

"To mu je in taya ki ɗaukowa."

"To tsaya in cire maka alkyabbar ko?"

Ya juya baya na zare masa alkyabbar jikinsa na ajiye saman kujera, sannan muka isa kicin.

Ba wani abu ba ne mai wahala ba abin hirar tamu. Tuwan abarba ne da inibi,an markaɗe su da ɗan kauri, tare da dabino wanda za'a jiƙa shi ya yi laushi, sai a ajiye ruwan gefe ɗaya, sannan a samu ƙwaƙwa ta ciki a goga ta da abin goga kuɓewa, bayan duk an wanke su kenan, sai a kawo ruwan abarbar da dabino da inibi a zuba a cikin ƙwaƙwar, sai a kawo madarar ruwa a zuba a ciki, ya danganta da yawansa, yawan madarar ga mai son suga ya zuba, ga mai son zaƙi sosai zai ji ya yi daidai. Amma ko ba inibi za'a iya yi, ana iya yi da madarar gari ma.

Cikin ɗan kofunan shan fruit salad ake shan shi, tare da ɗan ƙaramin cokali ana kiranshi da suna Appitizier (Coconut).

Mun kalli kasusuwan da dama a cikin ƙwara tara,babu abin da na lura a ciki wanda yake takurawa talakawa illa abubuwa baƙwai. Abin da muka zauna a yau juma'a muna tattaunawa da Yarima kenan.

"To ke yanzu me kika lura ya damu talakawana?"

"Ai ba talakawanka kaɗai ba, duk ƴan ƙasar Nijeriya."

To yanzu kamar me ye da meye ki ka lura da su?"

"Ruwa, rashin abin ƙonawa, itace ko kalanzir,ko gas,ga masu aiki da shi, ba wai babu ba, tsada ce ta yi masa yawa, suna buƙatar magudanan ruwa,takin noma, magunguna a asibitoci, hanyoyin mota, ballantana a cikin ƙauyuka, wutar lantarki,makarantun boko, Islamiyya tare da ilimintatun malamai,uwa-uba fetirin sawa motoci ko abin hawa ƙanana.

"Gaskiya na yarda. Ke kin ga wani ƙauye da muka je,kin ga ruwan da suke sha kuwa tamkar ruwan ƙwatami? To wai me ki ka ga ya janyo haka?"

"Rashin kulawa da sa ido, da zame hannu da ku sarakuna ku ka yi,ku ka bar wa gwamnati
End Ads