Yau ma Yarima na ƙwance a doguwar kujera daga shi sai singileti fara da dogon wando,ni kuwa ina ƙwance,wato saman jikinsa,muna ta hirarmu ta yaushe zan je Jos, saboda na samu shekara kenan har da wata biyu ban je ba. Na fahimci Yarima yanzu ba ya son ana yi masa hirar Jos, amma ni a wajena ta zama dole. Bai kai ga bani amsa ba muka ji sallama.
Na ɗan yi gaggawar tashi zaune, sannan na ce, "A shigo." Sa'a mai rainon Suhailat ce ta shigo ɗauke da Suhailat yarinyar da ta shekara ɗaya da wata huɗu kenan. Ta durƙusa har ƙasa sannan ta ce, "An yi baƙuwa tana waje. Na tambaye ta sunan ta domin inzo in gaya maku, amma ta ce ace baƙuwa ce daga Jos."
Nan take Yarima ya ɓata rai, "Ki ce mata ta koma can Jos ɗin, nan gidan duk ƴan Kaduna ne ba ƴan Jos."
"A yi haƙuri Yarima." Ya juyo da saurin gaske, ya kira sunana. "A yi haƙuri kuskure ne,je ki kice ta shigo." Ta tashi ta fita.
Kafin ta shigo na yi saurin miƙa masa doguwar rigarsa ta shan iska. Ya karɓa tare da yi mini ƙorafin kada in ƙara kiransa da Yarima, baya so. Na bishi da na daina.
Wata fuska na gani, wacce da gani na san fuskar, sai dai ganin ta yi mini tsufa, ta rame,ko ince ma ba tsoka ko ɗaya a jikin fuskar.
Dattijuwar da ta shigo, ta zauna ƙasa tana gaishe mu.
######
[2/25, 16:04] Ummi Tandama😇: *ƘASAITA BOOK 3*
*NA*
*MARYAM KABIR MASHI*
Page 8
"Sannu Inna,ban gane ki ba, na so dai in ga kamar na taɓa ganin ki, amma na kasa tunano a ina na taɓa ganin ki."
Sai na ji ta saka kuka tana cewa, "Ai dama na san da wuya ki gane ni Gimbiya ni ce jakadiya."
Kafin ta ƙarasa daga ni har Yarima mun miƙe tsaye tare da kiran Innalillahi wa'inna ilaihir'raji'un! Kamar haɗa baki muka ƙara cewa, "Jakadiya me ya same ki haka?"
"Ai Gimbiya Allah ya yi da ragowar shan ruwana gaba, da tuni da sai dai in kun tunano ni ku ce Allah ya ji ƙaina. Yanzu mu ai mulkin kama karya ake yi mana a Jos, saboda azzalumin Sarkin da aka baiwa sarauta."
"Wa aka ba sarautar?" Yarima ya yi tambayar.
"Wani ne wai shi Abdulrahman, wai ɗan Sarki ne, shi ne yanzu duk abin da ake yi sama da shekara uku duk baku da labari?"
"Ba mu da labari, wajen wa zamu ji?"
"Wajen Mama."
"In ta zo mu bata gaya mana komai. Ni kuma ko na je Jos ba na zuwa ko'ina sai gidanmu,ni kuwa ban taɓa ji ba,mun san dai ance an yi naɗin sarauta a Jos, amma ba mu san me aka naɗa ba."
"Ai abin ba daɗin faɗa,kin gan mu nan jiya muka gudo daga gidan yari. Wahala ta duniya ba wacce ba mu gani ba...." Tasa kuka.
"Ke har da fyaɗe an yi mini, tsofai-tsofai da ni. Ke yanzu dai Allah ya yaye mana masifa kawai."
"Ina su Mansura." Na tambaya cikin sigar tashin hankali.
"Sun gudu su duka waɗanda ki ka sani, maza da mata, saboda kamo su kawai aka dinga yi ana yi masu fyaɗe kullum. Maza kuma a kaiwa shugaban nasu, shi kuma aikinsa kenan amfani da maza. Gimbiya ƙartin mutane ya zo da su sune dogarawansa, sun kai ɗari biyu, ban da ƴan iskan ƴan mata." Ta sake fashewa da kuka.
"Dole ne in neme ku in sanar daku yanda ƙasarku ta koma. Ku yi mana arziƙi ku je ku taimakawa al'ummarku."
"Ina Mai Martaba yake ne ake yin irin wannan abubuwan kafirci?" Yarima ya tambaya.
"Yana nan,ai ya riga ya tsafe shi, sai yanda ya ga damar yi da shi. Waziri da manyan mabiyansa fa an neme su an rasa."
"Wasu ne ya kawo ya zuba masa. Kai bacin su Ahmad fa da ƙila ma an gama da su Mama, to su ke tsaye a kan iyayensu, duk sun ajiye karatunsu, sun zama masu gadin iyayensu."
"Yanzu ke ya aka yi kika gane nan gidan?"
"Gidan su Gimbiya na je na samu maigadinsu, shi ne ya yi min ƙwatancen nan gidan. Shi ya gaya mini ma kuna nan garin, da duk abin da ya faru a baya, saboda mu bamu sani ba. An dai taɓa jin labarin kuna ƴar takun saƙa da Sarki, har na cewa Gimbiya ta tashi tsaye,sa hannu aka yi maku kai da mahaifinka."
"Me ye sa hannu kuma?"
"A je mugayen matsafa su shiga tsakanin masoya biyu."
"Allah ya kiyaye. Yanzu ki tashi kiyi tafiyarki,ni yanzu hankalina a ƙwance ya ke ni da iyalina, saboda haka ba na fatan abin da zai zo ya dagula mini lissafi. Sarauta kuma Allah ya tayashi riƙonta. Amma ni yanzu ko ma sha'awarta ba ma yi, ballantana inji ina sonta."
"Amma Allah ya ja da rai kayi kuskure babba, saboda iyayen ka na cikin bala'i, amma sai ka ce ba ruwanka, yanzu haka fa Sarki ya auri matar nan uwarsu shi wanda aka naɗa, sai fa yanda ta yi da shi. Mama kuwa in zata fita sai dai fa ta fita ta ƙofar nan ɓoyayyiya ta je duk inda zata ta dawo."
"Ban yarda ba, saboda da Mama ta gaya mini. Kin ga tashi ki tafi. Honey ba ta dubu goma ta sha ruwa a hanya, kada ki ƙara dawowa gidana,kina jina?"
"Allah ya ja da...." Ya daka mata tsawa. Nan take na ce, "ya isa. Tashi mu je waje,ki jira ni." Na shiga ɗaki, ita kuma ta tafi waje.
Ina fita na ja ta zuwa bayan gida, na tara masu aikinmu na ja masu kunne a kan kada su sake su faɗa cewar akwai baƙuwa a gidan nan . Na ba ta ɗaki na ɗiba mata sabulu, sannan na bayar a sayo mata kayan sawa.
Satin jakadiya shida kenan a gidanmu, ta yi ƙyau, ta mayar da jikinta tamkar ba ita ba. Yanzu abin da ya rage ƙoƙarin shawo kan Yarima. Jakadiya ta ce mini babu wata hanyar da zamu bi mushawo kan shi illa mu jira zuwan Mama,idan har muka samu Mama ta gaya masa halin da ake ciki baki da baki,wata ƙila ya amince ya tashi tsaye ya nemawa al'ummar da ke ƙarƙashinsa yanci.
Ikon Allah! Yau kuwa safiyar Laraba sai ga Mama ta zo, ganin ta sake lafiya ƙalau kamar yanda take yi mana kenan, ta nuna ba a cikin wata matsala take ba. Dalili ne ma yasa na ɗan tambaye ta ina su Mansura da jakadiya, sai na ji Mama ta ce.
"Lafiyar su ƙalau." Kan ganin bata da niyyar cewa komai yasa na aiki ɗaya daga cikin masu aikina na ce a kira mini baƙuwar nan.
Shigowar jakadiya za ta yi daidai da ɗaga gwangwanin lemon da Mama ta yi. A madadin ta ci gaba da sha, sai aka samu akasin hakan, saboda firgitar da ta yi.
Gaskiya dai ta bayyana daga bakin Mama, wanda Mama har da kukanta take faɗar wasu abubuwan. Hankalin Yarima kam ya tashi. Cikin sakan ɗaya jinin sarautar sa ya gudanyo jikinsa, saboda har wata rawar jiki na ga yana yi. Sai da ya nisa ya kai sau baƙwai, sannan ya miƙe yana cewa.
"Zan je sai na kashe su."
Mama ta yi saurin riƙe shi tare da zaunar da shi, ta koma ta zauna ita ma. Ya dube ta ya ce, "ina nan zuwa da bindigata, sai na kashe shi."
Mama ta yi murmushi, sannan ta yi kirarinsu na manya, shi ne "Ta yaro ƙyau take yi, amma ba ta ƙarko. Ai Yarima duk yanda ka ke tunanin mutanan nan sun riga sun wuce mu. Abin da ya kamata mu yi kawai shi ne mu ma mu dage da roƙon Allah ba dare ba rana. Na farko jakadiya kin fi mu sanin hanyoyin da za'a bi a karyawa Sarki abin da ke jikinsa."
Nan take na ji Yarima ya ce, "Aƙwai wasu addu'o'i da ayoyi ina da su na karya sammu ko wani mugun baki. Ban da ayoyin da Manzon Allah (S.A.W) ya ce mana, tare da koyar da mu yanda zamu aikata su."
Zan sa a yi saukar Alƙur'ani mai girma,sau sittin da baƙwai, wanda kowanne daga ciki za'a tofa a ruwa a yarfawa wanda ake tunanin an yi masa sammu, ba wata hanya da zamu bi illa wannan. Sannan mu duka mu dinga tashi cikin dare muna gabatar da wannan nafilar, da kuma wacce Allah ya hore mana. In zamu iya kuma mu ma muyi sauka da kanmu. Ga addu'o'in da sallar nafila.
Nafila ce raka'a huɗu, kowacce nafila da Ayatul kursiyu ƙafa baƙwai 7, dukkansu bayan ka yi sujjadar ƙarshe sai ka karanta wannan addu'ar. _Wallahu galibun ala amrih,walakin na akasaran nasi la ya'alamun (7),_ Idan mun sallame sai mu karanta wannan addu'ar.
_Allahumma wahastu nafsi wa irdilaka_ sau baƙwai(7), sai mu karanta Laƙada ja'akum, ita ma sau baƙwai(7).
Manzonmu Annabi Muhammad (S.A.W), ya ce wanda yake karanta waɗannan kalmomi guda goma, Allah zai kare shi daga sharri biyar a duniya,biyar a lahira. Ga su nan kamar haka:---
_1) Hasbunallahu liddini_
_2) Hasbunallahu liman ahamman_
_3) Hasbunallahu liman hasadani_
_4) Hasbunallahu liman kadani bi su'in._
_5) Hasbunallahu indal masala fil ƙabar._
_6) Hasbunallahu indal mizan_
_7) Hasbunallahu indal masala fil ƙabar_
_8) Hasbunallahu la'ila ha'ildalaihi tawakkaltu wahuwa Rabbul Arshir azim._
Allah yasa mu dace.
Cikakken bayanin maganin sammu,wato yanda za'a bi a karya sihiri,ko wani mugun Aljani mai taurin kai,ko sanin me mutum ya kamata ya yi,mata ko maza. Ana iya neman littafin nan kantin Al'Ameen Bookshop GUZURIN MATA MUSULMAI IZUWA ƊAKIN AURE. Wanda Malam Bashir Aliyu (Bashir) ya wallafa. Za'a samu duk wani ƙarin bayani a ciki.
Cikin wata ɗaya da ƙwana biyu muka gama duk wani tsarin da muke son muyi. Ta hanyar Mama kuma muka samu ta baiwa Mai Martaba maganin da yarfa masa wannan ruwan sauka. Ban da masallatai da Yarima ya dinga bi yana cewa a tayamu roƙon Allah.
Ba na mantawa da duk zuwa Makka da zan yi,wato aikin Hajji,ko Umarah, sai na yi roƙon Allah ya daidaita tsakanin Yarima da Mai Martaba.
Yau ga shi zan iya cewa Allah ya amsa roƙona,dama kuwa faɗa ce ta malamai, cewa duk muminin ƙwarai ba zai ziyarci ɗakin Allah da buƙatunsa ba face Allah ya biya masa buƙatunsa. Sai dai zasu iya ɗaukar ƴan lokuta, wasu kuma sha yanzu magani yanzu ne. Ko dai ka dawo ka ga alherin abun,ko kuma ma kana can kana dawowa ka samu abin da ka roƙa ya faru.
Mu kanmu ba mu san lokacin da Yarima ya je ga hukumar ƙwantar da tarzoma ta ƙasa ba (Mobile) bayan ya samo taimakon gaggawa, sai dai yau muka wayi gari muka ji an kama Sarkin ƙarya Abdulrahman da mahaifiyarsa, da Yayarsa Hadiza da duk mabiyansu.
Allahu Akbar! Yau ba wanda bai yi wa Mai Martaba kuka ba, shi da ɗan sa Yarima, wanda suka samu shekara ta biyar ba su ga juna ba.
Gaban bainar jama'a Mai Martaba Sarki Jafar ya rungume ɗansa, wanda ya ɗauki sama da mintuna goma, ya ɗagoshi ya kalle shi, sai kuma ya mayar da shi jikinsa ya ƙwantar. Daga baya ne yake tambayar ina jikansa Ammar. Yaro ɗan shekara biyar da wata huɗu ne kawai babu. Amma har ya zama ɗan saurayi saboda girman jiki da yake da shi.
Bayan ya ganshi ne aka miƙa masa Suhailat. Abin ka ga rashin sani, ta ƙi zuwa wajen Sarki. Da yake Allah yasa ta yi saurin tafiya da gudunta, ta iso wajena ta riƙe ni gam tana nuna mini Mai Martaba.
Hankalin Mai Martaba ya dawo jikinsa sosai, saboda duk ya ruɗe wajen neman su Waziri. To aikin da ya ragewa Yarima kenan, neman dattawan da suka rufa mana asiri da yanzu an hallaka mu. Bayan komai ya lafa ne muka ɗauko hanyar dawowa Kaduna. A hanya ne na ji zazzaɓi ya saukar mini,ga shi ko mun isa gida Yarima ba zama zai yi ba, zai tafi yawon neman su Waziri. Wannan shi ne dalilin da yasa muna isowa Kaduna na ce mu biya asibiti in ga Likita, saboda zazzaɓin da ya rufe ni cikin ƙanƙanin lokaci, wanda ni na san hayaniya ce kawai ta yi mini yawa.
Ina zaune a mota da yara da mai rainonsu a baya. Ni kuwa ina mazaunin kusa da direba, ina jiran in ga inda Yarima zai fito, saboda ba zan iya zirga-zirgar cikin asibitin Arewa Clinic ba. Ganin shi ya taho yana washe baki kamar na yi masa albishir ɗin daɗi, duk da na san yau farin ciki yake. Sai da ya iso ya buɗe mota sannan na ga ya ɗaure fuskarshi.
Ni dai ban ce komai ba, amma ina mamakin ganinsa hannu biyu da wata ƴar farar takarda a hannunsa. Abin da ya sa ban yi magana ba, tunanin ko biyawa za mu yi ƙyamus a siyi magani, amma har muka wuce duk inda za'a samu magani ban ga ya tsaya ba.
Ɗaki na nufa kaina tsaye, saboda yanda nake rawar sanyin zazzaɓi. Ina ƙwance Yarima ya shigo ya zauna kusa da ni.
"Tashi ki karɓi takardunki." Gabana kam ya faɗi, amma na yi saurin tashi na karɓa saboda ganewa idanuwana abin da ke ciki.
Positive (Pregnancy test) . Na ga an rubuta a jikin takardar. Na yi saurin dafe cikina.
"Ciki! Haba." Ya harare ni.
"To me kike nufi?"
"Haba Yarima ciki fa?"
"Kina ko ƙwanto ne?"
"Haba gani na yi duka yaushe na haihu?"
"Ko kina nufin ciki ɗaya ya yi kaɗan? Da gaskiyar ki,ƙato kamar ni a ce ciki ɗaya na yi. Tsaya ki gani in dage in yi na biyu yanzu."
Ya taho da sauri zai hayeni, na yi ɗan hanzarin sauka.
######
[2/25, 21:47] Ummi Tandama😇: *ƘASAITA BOOK 3*
*NA*
*MARYAM KABIR MASHI*
Page 9
"Na tuba wallahi,ɗayan ma ya isa."
"A'a da sauran Waziri da yake gadin ƙofa, tsaya dai ki ga,ke kin ɗauka abin da wasa ne."
Saboda rashin lafiyar da ke jikina yasa na kasa gudu sosai, har sai da ya kamo ni ya ɗauko ni cak, ya ɗora saman gado.
"Yau Celebration (murna) ɗin shiryawa da Mai Martaba zan yi."
Yana magana yana tuɓe rigar yana cillarwa. Ga shi saman cinyoyina zaune,ni kuwa sai dariyar kukan shagwaɓa nake yi, ina haɗa shi da Allah.
Ya yi saurin sumbatar bakina, ya tsotsa, sannan ya ɗago ni ya tattara gashina da ya baje saman gado, ya riƙe da hannu ɗaya.
"Yasmin na gode miki da ki ka taimaka mini da rayuwa mai ƙyau, ingantacciya. Ga shi kina haifa mini ingantattun yara. Na gode Allah da....."
Muryar Ammar ce ta nufo ɗakin mu. Da ji da gudu yake yana kiran.
"Dady ka yi baƙi masu kayan soja, ga su can a get a tsaye."
Cikin gaggawa ya miƙe tsaye yana kokawar mayar da rigarshi jikinsa. Ni kuwa dariyar ƙeta kawai nake daga ƙwance, har Ammar ya shigo, amma riga ta ƙi sanyuwa,dan ma Allah ya taimaka da wandonsa a jikinshi. Ammar na shigowa sai na ji yana cewa.
"Tsaya Daddy kada ka sa rigar."
Yarima ya yi tsaye da riga a hannu.
"Daddy tsugunna ka gani."
Yarima ya tsugunna, Ammar ya taɓa damtsan cinyar hannun Yarima.
"Wai Daddy ka ajiye chuka,ka fita haka,kai ma sojojin su ji tsoron ka,ka bibbige mana su,nima in na girma zan chuka haka."
"Za kayi amma daga yau tsoka ake cewa."
Ya dafa wajen ƙirjinsa,in tuɓe riga in ga ina da wannan."
"Amma ba yanzu za kayi wannan ba, sai kana cin abinci ka girma,ka zama babba kamar ni."
"Mama wai haka?"
"Kai fita ka barwa mutane waje. Ba na hana ka shigowa ɗaki ba sallama ba da irin wannan surutun naka. Fita mana."
Ya juya tare da cewa, "Ki yi haƙuri Mama." Yana fita na taso na ja kunnan Yarima.
"Kai ma ba na hana ka biyewa surutun Ammar ba? Wata rana sai ya baka kunya a gaban jama'a."
"Sorry Mamo." Na ƙara shan kunu na juya. Ya yi saurin fizgo ni jikinsa.
"Sorry Mamo, ina son in na dawo inga an yi mani fara'a."
"To je ka an yi haƙurin, kada a daɗe a zo a bani magani insha."
"Pracetamol ne kawai za ki sha. Bari in ɗauko miki."
"Ni dai gaskiya mai ƙarfi wanda zai hana komai zama cikina."
"Kada ki damu, ba mantawa na yi ba. Kin ga ko Ammar ya ce zan iya faɗa da sojoji,kin ga kuwa ƙyau na ace ciki bibbiyu nake yi." Na ture shi.
"Ni dai je ka."
Ya yi dariya ya saka riga ya fice. Sai da sha ɗaya na dare ta wuce, sannan ya dawo. Da ganinsa kuwa a gajiye yake. Ya zauna kusa da ni cikin cewa.
"Wash!"
"Sannu."
"Ke dai bari wallahi, na gaji sosai, ta so muje ɗaki,dama dai ni ake jira, bari in ɗan watsa ruwa in ji sanyi."
"Abincin fa?"
"Zan ci, bari dai in samu kaina tukunna."
Bayan ya fito ne yake ba ni labarin cewa wajen su Sarkin ƙarya Abdulrahman ya je, saboda yasa a tuhume shi inda ya kai su Waziri. Da ƙyar ya faɗa, shi ma gani ya yi za'a kashe shi a banza. Kin san inda ya kai su?" Na girgiza kai, tare da matsowa irin na mai ɗokin a gaya masa.
"Suna babban gidan yarin Legos,ƙiri-ƙiri Prison."
"To ya za'ayi yanzu?"
"Sai gobe zamu je mu taho da su. Kai Allah dai ya kusan raba mu da ƙajaga."
Haka dai muka dinga tattaunawa har muka ƙwanta.
N.T.A Kaduna, gidan talabijin na ƙasa, shi muke kallo. Inda muka ga su Yarima na saukowa daga jirgi da su Waziri a bayanshi, sun kai su talatin, dukkansu kamar za su kife ƙasa saboda rama, ga tsufa,ko kuwa in ce yunwa. Amma kaya ne masu ƙyau a jikinsu, ga shi sun sha aski. Jakadiya kuwa, sai kuka take yi,wai tunanin wahalar da ta sha take yi.
**** **** **** **
Wata ɗaya kenan da sati uku da dawowar su Waziri wanda ya yi daidai da yau aka yankewa su Abdulrahman da Yayarsa Hadiza da uwarsu Asabe da sauran muƙarrabansu hukunci a babbar kotu ta jaha, wacce ta yanke masu hukuncin ɗaurin rai da rai, saboda bincike ya nuna Abdulrahman da mabiyansa an kama su da laifin fyaɗe, aikata aikin alfasha da maza, shaye-shaye,kisan kai. Ga shi dama wai sana'ar