x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 3 - ASHPA KO ASHNA

  • 6001 words
  • 9000 words
  • Out of 15220 words

Category: Love Stories

Views 46

02 Jul 2025
Start ads
After Image Ads
suka damu ƙawata gata nan malam wuni daya dk ta rame idan babu damuwa ko za a taimaka mata ",da to ta dnga amsawa har suka gama wayar sannan ta dubi momy tace an gama ƙawata malam zai zo idan anjima kadan.

A tare suka dnga sauke aiyar zuciya ita da ƴaƴan ta, ranar dai sai hajiya maryam ce ta shga kitchen dan kowa na gidan tsoron matsawa yake yi musamma Bash da meerah da suka San abnda suka ji.


Sai wajan yamma malam yazo ya kira hajiya Maryam ya sanar da ita tayi masa iso ya shigo.


Jinjina kai oga Jibo yayi sannan Ashpa ta maida masa kayan sa da idon ta tmkar ma baa cire su ba, izinin zama ta basu a hanzar ce kowa ya zauna ya sunkuyar da kansa ƙasa suna jiran umar ni.

Rintse idon ta tayi tayi shiru wajan minti biyu kafin ta bude ta saki murmushi ta dubi Jibo tace"" daga nan zuwa titin Allu evenue zai ɗauke ku mnti hamsin idan kuka yi sauri, Alh jibril Mato zai ƙaraso wajan a lokacin zai ci abinci a seven therty restaurant, ku shiga cikin gurds ɗn sa ku ɗakko shi babu wanda zai ganku "".

jinjina kai sukayi babu ɓata lokaci suka tashi suka bar wajan suka dauki motoci suka hau titi.

Kmr ana tura su haka suka dnga gudu a titi har suka iso wajan, kmr yanda ta faɗa kuwa haka abn yake dk yanda tace suyi haka sukayi har Alh ya gama cin abnci ya tashi ya nufi wajan mota.

jibo ne ya buɗe masa ya shiga gurds ɗn suna tsaye sun ƙame basu san meke faruwa ba, sai PA ɗn sa wanda yake tare da alh koda yaushe aiko suka taso su gaba ɗaya.

A cikin dajin Ashpa ta tashi wasu securities ɗn suka fitar da waɗanda aka kama.


Tana nan zaune tana saƙawa da warware wa motar su Jibo ta dawo, tn daga bakin hanya ta hango su ta ƙara gyara zamn ta tana sakin wani killer smile.

Alh bai fahimci komai ba saida aka zo bakin dajin sannan ya gane batare da gurds ɗnsa yake ba.

juye juye ta fara yi yana shirin magana ya ji an ɗaga shi sama.

Ja da baya PA ya fara ganin oga a sama ba a hannun ko wa ba, wata irin damƙa jibo yayi masa ya ja baki yayi shiru yana wurga Ido.



Jinsa a sama ya sa ya waiga don ganin wanda ya ɗaga shi, saidai ba kowa shi kaɗai yake tafiya cikin iska, wani uban ihu ya kurma da ƙarfi yana wurgar Ido yace "" wayyo Allah na wayyo na ga ta kaina haba boka ya zaka mn haka ka rufa mn asiri ta kara ta ban yanka jariran ba saura kaɗan ka rufa mn a siri kar ka kashe ni ban cika buri na ba innahumin sulaimanu wa innahu wainnahu "".

wainnahu yake ta maimaitawa ya kasa kamo ƙarshen har aka sauke shi gaban Ashna, ya bude baki zaiyi mgana a ka daki bakin yaja yayi shiru, kallon kowa na wajan Ashna tayi suka watse aka barta daga ita sai Alh, kallon sa Ashna tayi fuskar ta babu annuri tace """ Faɗi abnda zaka fada"" jikin sa na rawa yake kallon fuskar ta yace "' babu abnda zance nidai kimn rai karki kashe ni takara ta dn Allah ki barni ban gama cika buri ka na ba.

da karfi Ashna ta kaiwa bakin sa bugu ya sake kurma ihu ganin haƙorin sa guda ɗaya a hannun sa, kafin yayi magana dajin ya fara rawa wasu ƴananun yara suka zagaye shi suna tsalle suna rawa, babu abnda suke furtawa face"" jini"".

wani irin numfashi alh ya fara ja mai cike da wàhala da tashin hankali.

yana cikin hakan ya sake ji anyi sama dashi ana jujjuya shi, zuwa yanzu muryar sa ta fara dashewa, banda gunji babu abnda yakeyi idon sa a rufe yake fadin"" wayyo ni wayyo rayuwa na shiga uku dn Allah ki yi haƙuri ki yafe mn kaico kan mu kaico abnda zai ƙarar damu, kaico na na shi ga uku na lalace innahu"" bai ƙarasa faɗar innahu ɗn ba aka sake kaiwa bakin sa bugu yayi shiru wani gurnani yake kmr zaki yace"" nayi shiru nayu shiru madam bazan sake ba wllh na tuba kimn rai nayi shiru "".


nayi shiru yake ta maimaitawa yana gunji yana tuba sannan Ashna ta kalle shi ya sakko ƙasa

harisu (PA) dake gefe ya ƙunshe dariya ganin wandon oga jiƙe kashi.

bai yi aune ba yaji an ɗaga shi sama kansa a ƙasa ƙafar sa a sama yana lilo, nan fa ido ya raina fata ya fasa ihu yana cewa""" na tuba anty na wllh bazan sake dariya har abada nida dariya bazan sake ba dn Allah kar ki bari na mutu wllh ni kaɗai iyaye na suka haifa kuma tnda na samu aiki suna ƙauye banje wajan su ba dn Allah ki bari naje su ganni ko sau ɗaya ne, dn Allah ki mn rai ko auren farin banyi ba na shiga uku na, dn Allah ki yafe mn oga ka yafe mn na cuce ka abubuwa da yawa dn Allah kowa ya yafe mn niko tawa ta ƙare



Hajiya maryam ce tace wa malam ya shigo, ga mamaki na wani baƙin mutum ba gani jikin sanye da rigar fatar kura hannayen sa ɗaure da guraye ya ɗaura wata fatar a ƙugun sa, hannun da rike da wani gashi irin na inyamurai da ƙoƙo a ɗaya hannun nasa.


Babu ko sallama ya shigo cikin falon yana raba idanu, ya kalli hajiya maryam yace"" daga ina ne shaiɗanun suke? hajiya maryam ta kalli momy tace"" to ƙawata faɗa masa"" nan da nan jikin momy na rawa ta kwashe dk abnda y faru ta faɗawa malam.

Yana gama ji ya fara zuwa kusurwa kusurwa na palourn yana tsoma wannan gashin cikin ƙoƙon hannun sa sai ya yarfa ruwan dake ciki a jikin bangon kusurwar.

saida yayi dka kusurwar sannan ya dawo tsakiyar palourn ya tsaya cak ya ɗaga ƙoƙon sama ya fara magana da wata irin murya mara daɗin ji yace """ Kuna ina ! Kuna ina kananun marasa kunya!! kuzo ku shiga nan ya faɗa yana nuna ƙoƙon dake hannun sa, shiru babu wanda ya amsa haka yayi ta kururuwa shiru.

wata yar dariya yayi ya dubi hajiya Maryam yace "" an gama sunji tsoro ba zasu iya komai ba ƙananun ƙwari ne"" bai ƙarasa faɗa ba aka zabga masa wani gigitaccen mari saida yayi tagaltangal saboda tsabar zafi amma haka ya dake ya tsaya ya cigaba ya murmushin yaƙe.

wani marin aka sake zabga masa ya sa hannu ya sosa kumatun sa yayi shiru.

zuwa yanzu jikin sa ya fara rawa wani gumi ne yake karyo masa gashi baya so a gane, can dai aka sake zabga wani marin ai da ƙarfi ya buɗe baki yace ""kaaaaaiiiiiiiiiiiiii"" yana faɗa ya yadda ƙoƙon da gashin yayi hanyar ƙofa a guje, ai kafin yaje aka rufe ƙofar ji kake garam, nan take kuma wani duhu ya mamaye Palourn Wanda ko tafin hannu baa iya gani...


Oum sharifat ce.
Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/LWo0GX36DMiJAdHiIcVwrl



ASHPA KO ASHNA

11-12
JARUMAI WRITTERS ASSOCIATION TAKEN MU ALKALAMI YAFI TAKOBI
NA
KHADIJA UMAR ABDULLAHI)GARKUWAR JARUMAI CE) 💪🏽
بسم الله الرحمن الرحيم



Momy da ƴaƴan ta suka ƙanƙame jikin junan su suna wani kuka mai tsuma zuciya, ita kam hajiya maryam bayan kujera ta samu ta laɓe, shi kansa malam neman wajan laɓewar yakeyi amma ya rasa.

Yana nan tsaye ya ƙanƙame jikin sa yaji an ɗauke shi cak aka ɗaga shi sama ka buga shi da ƙasa wai uban ihu ya kurma cike da nadamar zuwa gidan, wutar ɗakin ce ta fara kawowa tana ɗauke wa aka dnga jijjiga dakin, wasu muryoyi mara sa daɗin ji suka fara dariya suna jan ɗafar malam.
zuwa yanzu malam yayi suman wucin gadi saida aka zabga masa mari sannan ya farfaɗo, wata doguwar mace ya gani tsaye a gaban sa fuskar ta na kallon bayan ta tana zaro harshen ta gajin kanta ya rufe idon ta ta na yo kansa da wata sharbebiyar wuƙa, ja da baya malam ya fara yi tana ƙara biyo shi.

saida ya kai ƙarshen bango sannan ta tsaya.
ya rintse idon sa gaba ɗaya ya gama sallama rayuwar sa yaji an ja ƙafar sa kmar ana jan kayan wanki aka kaishi tsakiyar palourn, a lokacin kuma hasken palourn ya dawo.

ganin wannan matar ba ƙaramin tada hankalin su Bash yayi ba haka suka sake maƴale juna shida kb, cikin rashin saa Bash ya kai idon sa jikin tv da sauri ya rintse idon sa sakamakon matar da ya gani cikin tvn tana zaro masa ido, ta cikin tvn ya ga ta miƙo hannu yayi saurin ɓoye kansa jikin momy Amma saida hannun yazo inda yake ya shaƙe shi ya ɗaga shi sama aka haɗa shi da bango.

cikin wata kakkausar murya aka daka masa tsawar da saida jikin sa ya fara karkarwa aka ce ""malami kuka samo ko? wanda zai cire mu ko""?

Jiki na ɓari Bash ya ce ""wllh anty ba ni bane nifa banma san inda malamai suke ba wllh momy ce da ƴawar ta dn Allah kiyi hakuri ni wllh ma ƙasar zan bari"""

"" kaje ka cigaba da lala ta ƴaƴan mutane ko ?ido wuri wuri bash yace ""ni?!! aa wllh ni ko aure ma bazanyi ba babu abnda zan ƙara nida mata har a bada"" wani zazzafan mari aka zabga masa aka ce"" sunnar manzon Allah (saw) ce ba zakayi ba? wato ka fi son na yan iska ko? .

bash ya fashe da kuka yace. Aa wllh zanyi a satin nan ma zan yi anty wllh zanyi aure da kanki ma kinemo min matar ko kuturwa ce wllh Ina so dariya ta sake kecewa da ita sannan ta watsar da bash gefe

Yanda ta juyo kan malam tana wata irin tafiya yasa gaban malam ya cigaba da bugu kmr gangar coci , ƙura idon ta tayi a kan malam kmr daga sama malam ya fara jin duka ta ko ina kafin ya sosa wannan an sake zabga masa wani tsuguna wa malam yayi a gaban ta yace "" kiyi mn rai dan gausin dan giyasin"" ƙafa ta sa hankaɗa shi baya.

cikin wata karairaya da yauƙi ta ƙarasa gaban sa tace ""kai fa malami ne kuma kace mnji tsoro kai kukan me kake yanzu? kawai ka fitar da mu daga gidan nan.

tana faɗa gabaaya palourn ya lauka da hayaniya wasu muryoyi mara sa daɗi suna sudai a fitar da su daga gidan.

idon malam pa sunyi wuƙi wuƙi kamar shege a rabon gado yace ""wayyo ni ni na isa na kore ku bazan iya ba wllh ba aiki na bane ni ɗin banza ai nan gidan ku ne dole a tafi a barku"".

"" zaka iya" yaji wata murya mai kama da ta ƙaton gardi ya faɗa, ja da baya malama ya farayi yana kuka yace ""wllh bazan iya ba ki rufa mn asiri wllh ban iya ba bansan komai ba kawai damfara ce irin tamu ta ƴan bariki "" zafafan maruka aka shiga zabga masa cikin muryar jarirai aka ce da gaske kai ɗan bariki ne "?
jikin malam na rawa yana jijjiga kai ya ce"" ƙwarai kuwa tantirin ɗn iska ne ni bansan komai ba jahili ne ni wllh kina saki na islamiyya zan koma, na rantse da Allah na dena duba.

wata dariyar aka sake sheƙewa da ita sannan aka shiga dukan gaba ɗaya mutanen palourn tako ina ba ji ba gani.

momy da ta gama jin duka tayi lilis ta ce"" Allah ya isa hajiya Maryam babu ni babu ke Allah ya tsine miki""

hajiya Maryam dake sosa jikin ta dk inda aka daka tana jin kamr ranta zai fita cikin kuka tace ""saima kin faɗa? aini yakamata in faɗa babu ni babu ke har abada gayyar tsiya kawai"" a tare aka zabga musu mari suka ja baki sukayi tsit sai gurnani suke kamer zaku na

KADUNA

Gyaran murya akayi tare da sallama , Abubakar da Umar suka juya suka kalli ƙofa, wani dattijo ne ya shigo wanda kallo ɗaya zaka yi masa ka ga tsananin kamar sake tsakanin sa da su.
da sauri kuwa Umar yayi bayan sa ya tsaya yana dariya, jawo shi mtmn yayi kmr wani ƙaramin yaro yace"" aa ni fa Umar bana goyon bayan wannan halin naka nasan dai tsokana ce kayi dama Ammin ku ce ke goyin bayan ka Amma banda ni""
turo baki Umar yayi kamr zaiyi kuka ya koma kusa da Ammi ya zauna Yana kumbura, murmushi Ammi tayi tana shafa kansa tace"" ka rabu dasu kaji ni Ina bayan ka ai " ɗn murmushi yayi yana yiwa Abubakar gwalo .

Zama dattijon yayi suka fara yi masa sannu da zuwa yana amsawa.

Ammi ce ta dube shi cike da kulawa tace "" to Alh muje kayi wanka ko? sai ka ci abnci ""

aa ba yan zu ba sai na huta cewar daddy yana gyara zamn sa kan sopa.

sannan ya dubi Abubakar da Umar yace"" dama Ina so muyi wata magana da ku in sha Allah ranar week end zamuje daku Kano zaku ga ƴaƴan gwaggon ku Ashpa da Ashna kowa zai auri ɗaya.

Wani kallo Umar ya yi wa daddyn cike da damuwa yace ""wai daddy kana nufin wannan yaran masu kama da aljanu?
fuskar Daddy ta zanja zuwa b
ɓacin rai yace"" Umar ƴannen naka ne masu kama da aljanu? ashe ba zaka iya tsayawa kan rayuwar su ba? ashe ba zaka iya yin yaƙi da dk wanda zai aibata su ba? to su nake nufi kuma su zaku aura idan har na isa

Kayi haƴuri daddy Allah yasa haka shi yafi alkairi cewar Abubakar yana zabgawa Umar harara.

haƙuri shima Umar ɗn ya bawa daddy a ransa kuwa yana lissafa irin azabar sa zai yiwa dk wacce aka aura masa a cikin su ( nidai nace Anya kuwa? Readers kowa ta zaɓi team ɗn ta nidai ina bayan Umar yanzu za a fara wasan).


Bayan sun gama shan dukan palourn yayi tsit matar ta ɓace komai ya dawo yanda yake kamr ba ayi komai ba.

malam da bai san inda kayan sa suke ba daga shi sai gajeren wando ya tashi a guje ya fice daga palourn yana tsinewa hajiya maryam.

mai gadi na banɗaki malam yana ta kira azo a buɗe masa amma shiru ganin bazai iya jira ba ya daka wani wawan tsalle ya haura katanga ya dira ta baya ya zuba a guje

Ranar dai Babu wanda ya haura upstairs anan palourn suka kwana baccin dai ba wani isasshe ba, kashe gari da safe daƙyar suka yi wanka ranar dai da kansu suka shiga kitchen suka dafa shayi suka sha

Suna cikin yin breakfast suka jiyo wata murya daga bakin ƙofa wacce na kasa banbance macece ko namiji ne.

nidai naji ance ""Salam wa'alam"" gaba ɗaya suka juyo dn ganin mai wannan sallamar sn San dai mtm ɗaya ne mai yi wato sai autan momy .

Wani matashi ne wanda bazai wuce shekara ashirin da biyu ba sanye da farar jallabiyya ya ɗaura zanin atamfa a ƙugun sa sannan ya ɗaura wani ɗankwalin atamfar a kansa.

a haka ya karaso cikin palourn yana karairaya shi a dole ga mace, girgiza kai meerah tayi ta dube shi tace"" yanzu kai Aliyu ba zaka dawowa daidai ba kai fa .. Bata ƙarasa ba wanda aka kira da Aliyu yaja da baya ya taɓe baki cike da yauƙi yace ""keee dakata ƙaramar yar iska Aliya nake kar ki sake jefa ni cikin ƙattai ni jinsin ki ce ehe "" ya ƙarasa faɗa yana buga cinya. Kb da zuwa yanzu ya fara sabawa da masifa yayi wata ƴar dariya yana hango irin masifar da Aliyu zai jefa kansa cikin gidan.

Oum sharifat ce..


Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/LWo0GX36DMiJAdHiIcVwrl



ASHPA KO ASHNA


13-14

JARUMAI WRITTERS ASSOCIATION TAKEN MU ALKALAMI YAFI TAKOBI

NA
KHADIJA UMAR ABDULLAHI (GARKUWAR JARUMAI CE)

بسم الله الرحمن الرحيم

Kowa komawa yayi ya jingina da kujerar zuciyoyin su Banda lugude babu abnda sukeyi, tnani fal ransu yadda Aliyu ke Shirin jefa su cikin masifa.

Kb ne ya taso yazo kusa da Aliyu ya kai hannu da nufin taɓa shi, da sauri Aliyu yaja baya yana gyara ɗaurin ƙirjin sa yanatafa hannu "" yace na shiga uku an fasa aure na, kai yanzu saboda ka cika ƙaton gardi ɗn iska ni zaka taɓa me kake son ji a jiki na? shege kwarto, to wllh a hir ɗn ka ƙwalelen kare da hantar kura ya ƙarasa faɗa yana murguda baki kmr karuwar ƙauye.


Tsananin mamaki ya hana Kb magana haka ya koma gefe ya zauna ba tare da yace komai ba.

cike da rangwaɗa Aliyu ya fara taku cikin palourn ya ƙaraso gaban momy ya kai hannu ya rike ƙafar ta, yana shirin yin mgna da sauri momy ta ɗaga masa hannu tace "haba Aliyu menene yake burgeka a cikin wannan rayuwar ? Me kake nema wanda Allah bai maka ba ? Baka ga kowa na gidan nan alamun yana cikin damuwa ba? haba Aliyu ka dawo yadda kake kaji Aliyu na.

Maimakon Aliyu ya canja sai ma ƙara miƙewa yayi yana yarfa hannu yana kashe ido yace ""yo ni fa momy nasan dama ba ƙaunata ake a gidan nan ba, dk yadda nake taka tsantsan da rayuwa ta nake jan jiki saboda gudun raini amma bakwa gani, kuma ma idan naƙi shiga a gidan aure ai ba zan ƙi shiga a tasha ba a hayyye ya kara fada yana bugun cinya tare da cewa sawaaaa.

Bai kai ga gama faɗar sawaa ɗn ba yaji saukar zazzafan mari a fuskar sa, a hasale ya ɗago kai ya kalli Kb wanda ke kusa da shi ya buɗe baki da shirin magana aka kaiwa bakin sa bugu, zaro Ido Aliyu ya fara yi
End Ads