x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 1 - ASHPA KO ASHNA

  • 1 words
  • 3000 words
  • Out of 15220 words

Category: Love Stories

Views 39

02 Jul 2025
Start ads
After Image Ads

An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


ASHPA KO ASHNA

Episode 1

JARUMAI WRITTERS ASSOCIATION TAKEN MU ALKALAMI YAFI TAKOBI

STORY AND WRITING BY
KHADIJA UMAR ABDULLAHI (GARKUWAR JARUMAI CE)

بسم الله الرحمن الرحيم

Kyakykyawar budurwa ce fara sol doguwa, bata cikin sirara kamar yanda bata cikin basu ƙiba, tana da goguwar fuska da dogon hanci, mnyan idanuwa ma"abota gazar gazar ɗin gashin ido baƙiƙirin, gashin girar ta yana da yawa sosai saura kaɗan ya hade, ɗan ƙaramin baki gare ta tare da pink lips, tana da siririn wuya da cikakken dukiyar fulani, cikin ta a shafe kamar babu komai a ciki tana da hips madaidaici .

Baƙar doguwar riga ce a jikin ta ta yafa farin mayafi ɗn ƙarami a saman kanta, inda ta jawo mayafin ya rufe rabin fuskar ta, yanda take tafiya kaɗai kamar bata son taka ƙasa ya isa ya sanar da mutum ajin da take da shi.

A bakin titi take tafiya kan ta na kallon ƙasa, wata ƙatuwar baƙar mota ta taho da gudu a kan titin daga bayan ta, tn kafin su ƙasaro suka buɗe ƙofar motar, daidai inda take suka iso ɗaya daga cikin su ya zuro hannu ya ja hannun ta da ƙarfi ya jefa ta cikin motar suka ƙara gudu.

Daga cikin motar ta kalli gefen ta hagu da dama wasu ƙattai ne guda hudu suna ta muzurai kallo ɗaya zaka yi musu kaga tsantsar rashin imani a tare da su.


gefe wasu ƴammata ne guda biyu da tsohuwa ɗaya jikin su banda rawa babu abnda yake yi suna ta kuka, sosai suka bata tausayi ta maida kallon ta gaban motar, mutum ɗaya ne driver yana sanye da kayan sojoji sai wata mace a gefen sa cikin riga da wando da ƙatuwar gun a hannun ta.

Saida ta gama ƴare musu kallo tsaf sannan ta sauke ajiyar zuciya ta gyara zaman ta acikin motar.

Sosai suke sharara gudu a titin har suka iso wani daji ma'abocin dogayen bishiyoyi da duwatsu, akwai ƙarancin haske a wajan, wasu fararen ƙyallaye suka ɗakko suka ɗaure musu fuskokin su dashi sannan aka fito dasu, mutum biyu a gaban su biyu a bayan su suka nufi cikin jejin .


Tafiya sukeyi sosai cikin dajin sunyi nisa sosai wani ɗn ƙaramin dutse ya gangaro ya faɗo gaban su, cikin waɗanda ke gaban su wani yaji an jashi baya da mugun ƙarfi, saura kaɗan ya rusa ihu sai Kuma yaji an sake shi, da mamaki yake kallon hannun da yayi masa wannan ruƙon, yana shirin yin magana ta ɗaga masa hannu tare buɗe ɗn ƙaramin bakin ta fara motsa shi a hankali tace ""zakayi tuntuɓe da dutse ne shiyasa na jaka".


Zagaye ta sukayi gaba ɗayan su da bindugu wani daga cikin su ya cire ƙyallen dake fuskar ta ya ɗakko baƙi ya ɗaure mata fuskar sosai dashi sannan suka cigaba da tafiya, shidai wanda aka ja har yanzu jikin sa bai dawo daidai ba, tnda yake a rayuwar sa bai taɓa jin hannu mai ƙarfi irin wannan ba, har yanzu hankalin sa bai kwanta da yarintar ba haka ya dinga saƙe saƙe a zuciyar sa har suka iso saman ƙaton dutsen da ogan su yake suka dangwarar da waɗanda suka kamo a gaban wani dn siririn bafulatani.


Shima kayan sojoji ne ajikin yana tsaye ya jingina wata ƙatuwar bindiga a jikin ƙafar sa kansa da baƙar p cap baa ganin fuskar sa.


Wani uban ihu ogan ya kurma yana juyawa a wajan ya daga bindigar sama ya harba ta saboda tsabar murna, gaba ɗaya wajan sai da ya amsa sautin harbin, su dai ƴammatan da tsohuwar daga nan basu ƙara sanin inda kansu yake ba.


Su kansu waɗanda suka ɗakko su saida suka koma gefe saboda sun san babban burin oga Jibo shine ya kashe mutum lokacin da ya samu kansa cikin farin ciki sannan ne farin cikin sa yake cika.


Dawo da kallon sa yayi gare su dn ya tabbatar da yayi abnda yake so wato tsorata mutane, ja da baya yayi cike da mamakin kallon yarinya guda ɗaya a zaune ta tanƴwashe ƙafa idanun ta a rufe da baƙin ƙyalle, ""kodai kurma ce ya faɗa a zuciyar sa yana ƙara mamakin wannan halittar, matsowa kusa da ita yayi ya cire mata ƴyallen sannan ya ƙara ɗaga gun ɗn sama ya sake har bawa, yasan dole ta tsorata koda kurma ce ai idon ta yaga abnda ya faru, ƙara maido idon sa ƙasa yayi da mamakin sa still har yanzu tana zaune saima ƙara gyara zama da tayi tana kallon sa, dk da idon ta a lumshe suke amma yana hango ƙyallin ƙwayar idon ta wacce bazai iya tantance kowace colour bace.


Ransa ya ɓaci sosai ganin rashin tsoron yarinyar, cike da ɓacin rai ya dakawa yaran sa dake tsaye tsawa ya basu izinin kaisu masauki, Babu musu kuwa suka nufi inda suke a takure sakamakon ƙarar harbin gun na biyu daya farkar dasu daga suman da sukayi.

Yanda suka zo a tsakiya haka suka ƙara saka su tsakiya, ita dai banda kalle kalle ba abnda take yi.

ɗaya daga cikin wanda suke bayan su ya sa ƴasan gun ya zunguri kanta tare da daka mata wata razananniyar tsawa wacce tasa su juyo wa gaba ɗaya, wani irin kallo tayi masa tare da watsa basa kwala kwalan idanuwan ta, Damm ƙirjin sa ya buga ganin blue ƙwayar dake cikin idon ta, sai dai ya dake ya gyara tsayuwar sa yana muzurai shi kar a raina shi, ya sake tamke fuska ya dube ta yana wani ciccije leɓe yace "" ke!! baki san ina ne nan ba ko? To kibi a hankali idan kika yi wasa a take a nan zan tarwatsa kanki , ki mutu kowa ya huta "" dn ƙaramin murmushi tayi sannan ta dube shi a raine tace """ ka taɓa ganin an kashe gawa? wani irin juyi cikin sa yayi yayi baya zai faɗa ramin dake bayan sa, da sauri ta sa hannu ta shaƙo yuwan rigar sa ta dawo dashi ya tsaya ƙyam akan ƙafafun sa, ta sakar masa murmushi tare da ɗaga masa gida ɗaya ta juya ta fara tafiya, kamar wasu dolaye haka suka fara binta tana gaba har suka iso ɗakin da suke ajiye mutanen da suka kamo.




Ashna! Ashna!! Wata dattijuwa take take ta kira a tsakar gida, jin shiru yasa ta canja kiran zuwa Ashfa, daga cikin ɗakin wata bdrwa ta fito, (nidai bazance komai domin wacce na baro a daji kmr ita na gani anan) "" duba min yar uwarki tana ina? cewar dattijuwar tana kallon wacce ta kira da Ashpa, zoben dake hannun ta budurwar ta murza shi tare da kallon tafin hannun ta, a razane ta ɗago kanta sai kuma ta fashe da dariya ta fara rawa a tsakar gidan tana ""mai rabon ganin baɗi ya gani"" , rawa take sosai tana juyi, dattijuwar na kallon ta rai a ɓace ta daka mata tsawa tare da cewa ""kee Ashpa menene haka? Cewa nayi ina Ashna take""? sake sheƙewa da dariya Ashna tayi sannan tace "" wani mai rabon tsautsayin yayi kidnapping ɗn Ashna, kaiii Inna Ina ma nice akayi kidnapping ba ba Ashna ba ta ƙarasa faɗa tana sake cigaba da rawar ta tana mai rabon ganin baɗi ya gani.



Wani ƙayataccen palour ne wanda ya haɗu yaji kayan alatu da komai na more rayuwa, wasu manya manyan kujeru ne cikin palourn yayin da wasu ƙammata ke zaune a kai suna operating wayoyin su, daga upstairs wata dattijuwa fara mai ƙiba ta sakko tana shafa cikin ta, direct dianing ta nufa saidai ganin wayam ba komai yasa ta sautin juyowa tana kallon yammatan dake zaune kan kujera tace "" meenah ba dai wannan matsiyaciyar yarinyar har yanzu around 09: bata zo tayi mana breakfast ba"? ""Bata zo ba momy"" wacce aka kira da meenah ta faɗa ba tare da ta ɗago kan ta ba.

daɓas momy ta zauna kan kujera ranta a ɓace ta fara masifa"" Talaka !! Talaka!! hmm wato saboda taga idan nace zan kore ta dadyn ku yana hanawa shi gashi uban masu tausayi shine ta samu damar barin mu har yanzu ba breakfast to bari tazo zanga uban da ya tsaya mata...



OUM SHARIFAT CE IDAN NAGA COMMENTS ZAAGA TYPING...

IDAN KIN KARANTA KIYI SHARE PLEASE


ASHPA KO ASHNA
EPISODE 3-4

JARUMAI WRITTERS ASSOCIATION TAKEN MU ALKALAMI YAFI TAKOBI
NA
KHADIJA UMAR ABDULLAHI (GARKUWAR JARUMAI CE) 💪🏽

Ina matukar godiya ga masoya masu bibiya ta love you oll amma yau sai kunyi hkr da typing dn🙈🙈

بسم الله الرحمن الرحيم

Shiru mama tayi tana kallon yanda Ashpa ke rawa a tsakar gida kmar ba wani abu ne ke Shirin faruwa ba, ""Ashna"" mama tace tana zama kan kujera ƴar tsuguno, da sauri Ashna ta bar rawar ta dawo kusa da mama ta zauna har yanzu fuskr ta ɗauke da murmushi ta dubi mama tace ""gani mama na"" kallon Ashna mama tayi ta laure fuska tace""" ki tashi ki shirya kije gidan Alh yau tnda Asha bata nan ƙila a hanyar tafiya ne suka ɗauke ta"" da to Ashpa ta amsa ta tashi ta shiga ɗ,aki bata wani jima da shiga ba ta fito sak ciki shiga irin wacce Ashna ta fita da ita, tayi wa mama sallama ta yi hanyar waje, har ta kai soro mama ta ƙwalla mata kira wanda ya sa ta juyo wa ta ce "mama gani "".


gyara zama mama tayi ta dubi Ashpa tace "" Ashpa bana so kiyi wani abu wanda zai canja daga irin halin Ashna, koda wani yayi miki wani abu idan ba zaki iya haƙuri ba ki rama dai dai da ramuwar Ashna, kisa a ranki ke ba Ashpa bace ke Ashna ce, idan kikayi haka zanji dadi sosai kinji Ashpa ta""? badon Ashpa taso ba ta ce" tom" sannan ta miƙe ta fice daga gidan.


""Meenah zo ki ɗan dafa mn shayi mna in ɗan samu na sha wllh ciki na kamar anyi yasa"" da sauri meenah ta ɗago ta kalli momy tace ""wah ni wllh aa bazan iya ba ki dai jira ƴar wahalar tazo tayi miki"".

jingina momy tayi da jikin kujera ta lumshe idanun ta tana jin cikin ta yana wani irin kuka irin na waɗanda suka daɗe ba su ci abnci ba, bayan ko da asba saida tasha tea, ganin ba zata iya jurewa ba yasa ta ɗago ta kalli ɗayar tace ""meerah kefa? wani kallo meerah tayi wa momy ba tare da tayi magana ba ta cigaba da abnda takeyi, ita dai momy tasan ma"anar kallon don meerah ba zata yi mata ba koda kuwa zata mutu.


Asslam alaikum sallama ake tayi a ƙofar palourn shiru babu wanda ya amsa, haka ta kutsa kai cikin palourn, direct hanyar dianing ta nufa ""keh zo nan dan ubanki""cewar momy tana riƙe da cikin ta wanda yake kukna yunwa.

cak Ashna ta tsaya zuciyar ta na zafi, sai da ta sake kiran sannan ta tina kalaman mama sai juma ta juyo, tana sunkuyar da kanta ta ƙaraso kusa da kujerar da momy ke zaune ta tsuguna kanta a ƙasa .


Kamo gashin kanta momy tayi taja da ƙarfi har sai da Ashpa ta saki wata siriyar ƙara sannan tace"" ke dan uwarki dn ubanki saboda kin samu an ɗauke ki aiki shine kika samu damar da zaki barmu da yunwa? matsiyaciya kawai to wllh na baki minti talatin kisan yanda zakiyi damu nida ƴaƴa na.

Jin abnda momy tace yasa meenah da meerah miƙewa suka ƙaraso suka ja kujera suka zauna, meerah ta dubi Ashpa"" tace oya ki haɗa mana break cikin minti talatin kmar yanda momy tace shigiya mai suffar aljanu"", haka suka cigaba da zaginta suna zaune har momy a dianing suna jira ta basu break cikin minti talatin.


ƙarasowa kusa da su Ashpa tayi ta ƙurawa dianing ɗn ido nan take wasu manya manyan kuloli suka bayyana a kan dianing dn gaban su kuwa ƴaton plates wanda mutum biyar zasu iya ci su ƙoshi kowacce an cika mata nata da fridrice da coslow, ga naman kaji akai daga gefe ƙaton jug ne cike da tea mai kauri da ƙaton bread, kowacce haka aka shirya mata a gaban ta.


wani rin ja da baya suka fara suna waro idanuwa suna kallon abncin suna kallon Ashpa, cikin su kuwa Banda juyi babu abnda yakeyi gaba ɗaya suka mike tsaye, momy ta dubi Ashpa baki na rawa tace ""Kee me me"" ɗaga mata hannu Ashpa tayi tana zaro mnyan idanuwan ta tace"" matsiyaciya ƴar talakawa ta haɗa muku breakfast cikin minti biyu, kuma wllh dk wacce bata cinye abnda ke gaban ta ba sai na juya mata fuskar ta zuwa ƙeyar ta tana gama faɗa tayi wani tsalle sai gata zaune ta tankwashe ƙafa bata sama bata ƙasa.

Tnda aka kai su Ashna ba'a sake waiwayar su ba sai da aka kira sallar magrib sannan wani ya shigo ya ƙare musu kallo ya juya, zai fice Ashna ta miƙe ta biyo bayan sa, jin takun tafiya a bayan sa yasa shi saurin juyowa yana ɗana harsashin bindigar sa yace"" kee ya'akayi ne? bata kula shi ba ta zagaye shi tayi gaba, haka shima ya bita kmar yaro da uban gidan sa.

suna fita taga wasu securities ɗn su uku a wajan gaba ɗaya sukayi kanta da bindugu, ɗaga musu hannu Ashna tayi sannan ta maida fuskar ta alamar tsoro tace ""alwala zanyi ruwa nake so"" sheƙewa sukayi da dariya gaba ɗayan su, ɗaya daga cikin su yace ""Allah ta sallah to nan ba'a sallah sai ki jira idan iyayen ki sun fanshe ki kya yi ta a gida, suka ƙara sheƙewa da dariya suna kallon ta dayan ""yace yarinya ta haɗu fa kaya iya kaya yana faɗa yana matsowa kusa da ita yana lashe baki.

hannu yasa akan kafaɗar ta ya fara murza hannun ta, a hankali Ashna ta kai duban ta kan hannun sa da yake yawo dashi a kafaɗar ta, d sauri ta cafki ta murɗa saboda tsabar azaba saida ya kurma wani uban ihu wanda yasa gaba ɗaya dajin ya amsa, matse hannun ta ƙara yi sannan ta wurgashi can gefe ya faɗi yana haki riƙe da hannun da yake da tabbacin ya karye .

ranta yayi matuƙar ɓaci ta kalli inda yake saiga hannun ta yana ƙara tsaho ya iso har inda yake tasa hannun ta shaƙi wuyan sa ta ɗaga shi sama sai ga ƙafafuwan sa suna lilo idon sa ya firfito alamar wahala ga azabar shaƙa wanda yake gab da barin duniya...

OUM SHARIFAT CE
MORE COMMENT MORE TYPHING..

*ASHPA KO ASHNA*
5-6

JARUMAI WRITTERS ASSOCIATION TAKEN MU ALKALAMI YAFI TAKOBI

NA
KHADIJA UMAR ABDULLAHI (GARKUWAR JARUMAI CE 💪🏽)

بسم الله الرحمن الرحيم

Turawa suka farayi hanjin cikin kowannen su na kaɗaw, kallon idon ta kaɗai idan sukayi wata ƙatuwar macijiya suke hangowa a ciki, haka suka sunkuyar da kansu suna tura abncin wanda babu daɗi ko na sisi, ga ɗan banzan gishiri da yaji aciki.

haka suka dinga dannawa suna hawaye, suna ci suna amai har suka gama cinyewa suka fara kokarin tashi, nan fa jiki yaƙi motsi abnka da ajeboters anci ya wuce lissafi, momy dama ga ƙiba tamkar buhun masara haka ciki yayi ƙato
End Ads