domin yan fashin wani irin salon yaki suke ,sannan
gasu da juriya dacin rai da naci, don sai kaga badakare ya zabga
masu sara a jikinsu jini yayi fallatsi, amma sabida tsabar naci
haka zasu cigaba da yakin
.
A yayin da dakarun sarki suka fahimci muddin akaci gaba da
wannan gumurzu toh yan fashin na iya karar da su gaba daya,
hakan tasa wani badakare mai matukar girman jiki ya falfala da
gudu izuwa wani bangare na gidan,
Koda ya je wajenda yake son zuwa . Wata irin dogon ginice mai
tsayi wacce a samarta akayi mata rumfa,
Irin wannan ginin ana amfani da sune ta hanyar ganin wanda
yake wajen gidan sarki ko ta hanyar sada wani sako, ajikin
ginin da kwaita iriyar matattakala ta katako, da isan wannan
badakare sai ya kama wannan matattakala ta katako, ya fara
hayewa izuwa saman birnin ko da yakai ga karshen ginin sai, ya
dauki wata makekiyar mabushi, yana dauka ya kafata abakinsa
sannan ya ringa busawa har tsawon wasu dakiku sannan ya
saurara.
.
A yayin da ake tsaka da gumurzu lokacinda su kallabu suka fara
cin karfin dakarun sarki hinzur
Suna kara kusantar asalin babban kofan da zata sada mutum
izuwa cikin falon gidan sarautar,
,
Alokacinne suka ji wata irin busa na tashi,koda kallabu ya
saurari wannan busa sai zuciyarsa ta bashi lallai ba lafiya ba,
hakan tasa ya ayyana aransa ya kamata suyi sauri su aikata
abinda zasu aikata su wuce abinsu,
Rashin sani tafi dare duhu, lallai da yanfashinnan sun san abin
da zai biyo baya toh da sun gaggauta barin wannan gidan
sarautar don ceton rayukansu,
.
Wannan busar bana komai bani illa busan Yaki, kuma sanar da
mutane cewa gari babu lafiya.
.
Kwance yake bisa shimfidarsa daga shi sai gajeran wando, duba
daya zakai mai kagane cewa yana jin dadin wannan baccin da
yake
Gabjejen katone baki amma bakinsa bawai irin baki kirin nan
bane,
,
Ba kyakkyawa bane amma kuma ba a kirashi da mummuna ba,
Yana da tarin damatsa, jikinsa a cure take a waje daya ,
Kamar acikin mafarki sai yaji wannan busa , zumbur ya mike
sannan ya natsu don kara sauraron busar tabbas wannan busace
dake tabbatarda cewa birnin nan na cikin tashin hankali, nan da
nan ya sanya kaya ajinkinsa, sannan ya sanya sulken yakinsa,
Ya daoki takobin sa ya rataya , sannan ya fito farfajiyar gidan
Nan da nan ya nufi turkin dawakansa da zuwa ya haye kan wata
bakar doki
Take dokin tai rimi sannan ta fice daga cikin gidan.
Wannan gabjejen mayaki ba kowa bane face sarkin yakin
birnin Tehran mai suna ZABBAGI bin SHARMIL
.
Abin da su kallabu basu sani ba shine A lokacinda suka isa
gidan sarki hinzur Dakarun da suke fada dasu dakarune masu
kare lafiyan sarki su dubu daya,
.
Su wayannan dakaru basa rabuwa da wannan gidan sarautar sai
sati yadda za'a canja da wasu su wayannan suje su huta
.
Acikin gari kuwa koda Mayaka da dakaru suka ji wannan busa ,
Nan da nan duk wani mayaki kuma dakare na wannan birni yayi
shirin yaki sannan aka tasamma gidan sarki,
Sabida karan busar daga cikin gidan take fitowa,
Sarki hinzur na turakansa sai sharbar barci yake kwatsam sai
yaji karar wannan busar acikin kunnuwansa
Nan take ya mike daga kwancen daya ke ,
Koda ya fahimci busar na fitowa daga cikin gidansa ne sai ransa
ya baci,
Cikin kankanin lokaci gagarumin shigar yaki irin ta sarakai, ya
dora takobin sa akan kafadarsa
Cikin hasala da zafin rai ya bangaje kofan turakanshi take
kofan ta fadi kasa shirim,
Kofar na faduwa ya fito ya fara tafiya cikin izza koda yaga yayi
tafiya mai dan tsayi amma bai hadu da dakarunsa ba, sabanin
da, sai ya kara fusata nan da nan ya falfala da azabaBben gudu
Cikin kankanin lokaci ya iso bakin babban kofan da zata
sadashi da farfajiyar gidan,
Cikin kunan rai ya daki kofan da kafansa take kofan ta fadi
rikica ,
Kofan na budewa sarki hinzur yai arba da wayannan yan fashin
sai ratattakan dakarunsa suke.
Nan take ya kwala wata irin kara wacce tasa gabadaya mayakan
suka tsaida yakin sannan sukai dubi izuwa wajen da yake tsaye
.
Yanfashin naganin haka sai suka falfalo da gudun tsiya don su
afka ma sarki hinzur
Sarki hinzur na ganin haka sai shima ya ruga da gudu don ya
tarbesu,
Koda ya rage baifi saura taku kadan ba tsakaninsa da yanfashin
sai ya daka tsalle yai sama , a saman ne cikin zafin nama ya
shafttare,
Makogwaron yanfashinnan da sukai kansa su biyar.
.
Nan fa sarki hinzur ya cigaba da sara da suka baji ba gani duk
inda ya nufa sai de kaga sassan jikin mutun na yawo bisa
sararin samaniya, yadda kasan ana sassabe a gona, tabbas
masifa ba' a samata rana lallai da mutum yana wajen yana ganin
irin yanda sarki hinzur ke yiwa wayannan yanfashi kisan gilla
toh daya tabbata lallai sarki hinzur ya cika NAMIJIN GASKE
duk girman kato sai dai kaga yayi tsalle ya saka takobinsa ya
farke masa ciki take zakaga jini yayi tsartuwa, cikin kankanin
lokaci sarki hinzur ya kashe kasu biyu cikin kaso uku na
yanfashin
.
Koda yan fashin suka fuskanci muddin aka cigaba da wannan
yakin a haka toh tabbas nan da wasu yan dakiku za'a karar da su
Ai nan take yanfashinnan suka fara neman hanyar tsira, cikin
masifaffen gudu suka tasamma kofan fita daga gidan da nufin
su fice daga gidan sarautar,
Bazato sai gani sukai kofan gidan ta bude da kanta
Budewar kofan keda wuya sai ga sarkin yaki zabbagu ibn
sharmil da mayaka abayansa kimanin milyan daya ,
Nan fa sarkin yaki ya cigaba da fille kawunan yanfashinnan shi
kallabu koda ganin haka sai ya hankalinsa yayi matukar
dugunzuma take ya sadakar cewa ya rigaya ya mutu,
Tsulum sai ganin Kamsas yayi ya bayyana agabansa yana
baiyana ya kama hannun kallabu yana shirin furta kalmomin
dazu kenan kawai sai gani sukai sarki hinzur ya baiyana a
gabansu
Cikin matukar hassala sarki hinzur ya daga takobinsa sama da
nufin ya fille kan shugaban yan fashi kallabu da kuma kamsas ,
Koda Takobin tazo daidai saitin wuyan kallabu
Sai........
.
SAI ME
SHIN AGANINKU KALLABU ZAI TSIRA DAGA KAIFIN
TAKOBIN SARKI HINZUR KUWA
.
Namijin gaske 1
Part 1D
(c)shuraih Usman
@shuraih 99%
NAMIJIN GASKE
Littafina daya 1
Marubuci:- Shuraih Usman
Typing:- Shuraih Usman
Tel. 08133209890
Part D
.
Doka, banyarda wani yayi copy ko ya sarrafa wannan labari ta
ko wace hanya batare da izni na ba. Dafatan za'a kiyaye
Copyright
Shuraih Usman
.
Koda Takobin tazo daidai saitin wuyan kallabu
Sai wata iriyar guguwa mai karfin tsiya ta bayyana
cikin kankanin lokaci guguwar ta zuke kallabu da
kamsas.
.
Koda ganin haka sai ran sarki hinzur yai matukar baci
nan da nan ya auka wa sauran yanfashin da suka
rage,
Cikin kankanin lokaci aka karkashe dukkan yan
fashinnan,
A sannan ne sarki hinzur ya dubi sarkin yaki zabbagu
yace da shi
"Ya kai sarkin yaki birnin tehran shin ta ina wayannan
runduna suka bi har suka shigo cikin wannan fadan"
.
Sarkin yaki yace " ranka shi dade ina kwance bisa
shimfidata naji sautin busa toh a sannan ne nasan an
kawo mana harine ,"
Wani badakare dake gefe yazo ya durkusa agaban
sarki hinzur yace"ya shugabana muna cikin aikinmu
na bada tsaro , kwatsam sai gani mukayi sun bayyana
rike da makamai a hannuwansu"
.
Koda sarki yaji haka sai ya bada umarnin a kwashe
gawarwakinsu a tafi a kona, nan ya wuce zuwa
turakarsa ,
Washe gari kuwa afada sarki hinzur ya nuna tamkar
bai damu da al'amarin daya faru jiya da dare ba
.
Amma a boye ya saka wani bokansa mai suna
KAMSUSULJANI yayi masa bincike
.
Kwanaki suka ringa ja harzuwa watanni biyu acikin
watanni biyunnan abubuwa da yawa sun faru ciki
kuwa har da aurena da sarki hinzur,
Al'amarin ya kasance ne wata rana sarki hinzur na
zazzagaya gari yana duba yanda talakawansa suke
kamar yadda ya saba aduk karshen shekara
.
Ni kuma alokacin banfi shekaru goma sha tara ba ,
nazo kasuwa zan siya kallabi, kawai sai ganin
cincirindon jama-a nayi a waje guda dana tambaya
kome ke faruwa sai aka sanar dani cewa sarki hinzur
ya kawo ziyara , kawai sai na tsinci kaina ina mai
karissawa. Wajen,
Don nasha jin labarinsa da kuma irin yabonsa da
jama'a keyi, amma ban taba ganinsa ba
.
Ashe dai kyaututtuka yake rabawa wa jama'a ,
Dogon layi akayi a yayin da shi kuma sarki hinzur
yake gaban wata rumfa dankarere ,agabansa wani
makeken teburine akan teburin kuwa kyaututtukane
kala kala ,
Banyi kasa a guiwa ba nima nabi layi , har layi yazo
kaina ,
Kaina na sunkuye ina dago kaina nai arba da
kyakkyawar fuskarsa ma'abociyar murmushi , nan
take naji zuciyata ta buga,
Maimakon sarki hinzur ya miko mani kyautar dake
hannunsa sai ya kura mini ido kaman yana nzarin
wani abu a tattare dani ,koda naga haka sai na
sunkuyar da kaina kasa,
Ina sunkuyar da kaina kas ne idanuwa suka ci karo da
abin da ya tayarmin da hankali
Bakomai bane illa wata zabgegiyar macijiya baka
kirin, jelar macijiyar da sauran jikinta yana kasan
teburin a yayin da kan macijiyar ya leko ta saman
teburin daidai saitin hannun sarki hinzur,
Nan take macijiyar ta fiddo da harshenta , ai koda
naga haka sai nayi wuf cikin zafin nama na bangaje
hannun sarki hinzur ,da hannuna kafin na kauce da
hannuna sai wannan macijiyar ta dankara mani cizo a
hannu, nana na kwala ihu daga nan ban san meya
faru gareni ba.
.
$ai farkawa nayi na ganni acikin wata kimtsastsiyar
turaka bisa wata luntsumemiyan katifa na alfarma
wannan turaka ta isa daular duniya don kayan dake
cikinta yayi hannun jarin wani attajirin.
.na mike zaune
Kofan dakinne ya bude sannan wata kuyanga ta shigo
, koda wannan kuyanga taga na farka sai ta washe
baki sannan tamin sannu na amsa mata cikin boye
murya ,
Fitan kuyangan keda wuya sai naji takun sahun
mutun yana nufo dakin , ya bude kofa ya shigo ya
kariso har inda nake zaune bisa katifa ,
Bakowa bane face sarki hinzur , yai mani sannu da
jiki sannan ya fice,
Ficewarsa keda wuya
Sai wasu kuyangi suka shigo nan suka tasar dani sannan suka shiga bayi sukai mani wanka bayan mun fito daga bayine suka zaunar dani bisa wata kujera,
.
Anan sukai mani kwalliya sannan suka sanya mani wani tufafi na yadin alharini. Sannan suka ce dani naje sarki naso yayi magana dani.
.
Acikin wata turaka na sameshi kai alokacin in ka ganni kace sarauniyar duniyace , doguwar rigace sanye a jikina rigar an yimata ado da duwatsun lu'u lu'u sannan na yafa wata mayafi wadda akayi mata cin baki da zubar jadi, wannan mayafi ya rufe mani ilahirin fuskata
.
Bayan na zaune a daya daga cikin kujerun dake cikin turakar sai na yaye mayafin dana rufe. Fuskata da shi , koda sarki hinzur yai arba da fuskata sai ya mike tsaye yana mai cewa " tsarki ya tabbata ga wanda ya kagi wannan kyakkyawan halittar"
.
Koda naji sai na sun kuyar da kaina kasa cikin jin kunya
Sarki hinzur yacigaba da cewa " ya ke wannan sarauniyar kyawawan duniya kiyisani a lokacin dana dora idanuwana akanki tunanina,hankalina,dakuma natsuwata duk sun guje daga gareni,
Banki nayi shekaru ina kallon wannan kyakkyawan fuskar taki ba,
Kiyi sani yake wannan kyakkyawa wannan sarki yazo da kogon barar sa gareki da jin cewa zaki amshi tayin soyayyarsa"
.
Koda naji yayi shiru sai na dago kai na dubeshi nace
"Yakai wannan sarki ma'aboci a dalci, kayisani cewa babu wata ya mace da zatayi arba da kai sonka bai shigeta ba,
Kasani tun alokacin dana fara ganin ka naji ina matukar kaunarka,"nayi shiru cikin kunya
Anan dai mukai ta hira cikin nishadi
In ka ganmu sai ka rantse munfi shekaru muna tare
.
Aranar sarki bai fita fada ba
Bayan kwana uku aka daura aurena da sarki hinzur sai da aka kwashe kwanaki goma ana ta shagulgulan bikinmu
Abun babu kama hannun yaro
.******* **
Al'amarin waziri humaiz kuwa tun dayaga shirin daya shirya na halaka dan'uwansa baiyi tasiri ba sai ya shiga kulle-kulle ya kulla wannan ya kwance wannan har dai daga karshe wata dabara ta fado masa.
****** **
Al'amarin boka kamsusulajani kuwa bayan yayi bincike a hallaran tsafinsa sai ya gano cewa waziri humaiz ne keson kashe sarki hinzur
Sai yaki fada ma sarki gaskiyan Al'amarin
.
****** **
Sarki hinzur kuwa yayi tacin amarcinsa ya kasance baya zuwa fada sosai kuma kullum cikin farinciki yake
Wata rana a fada ana cikin fadanci sai ga wani badakare yazo gaban sarki ya tsuguna yace
"Ranka shidade wani bakone akofa yace wai daga birnin KuFA yake kuma yazo ya isar da sakone,
Nan sarki yace abarshi ya kariso
Koda zuwan wannan manzo sai ya zube kasa ya kwashi gaisuwa wajen sarki sannan ya fidda wata takarda ya mika ma wani badakare,
Take maga takarda ya karbi takardan yafara karantawa kamar haka
.
Sako daga sarki hurshad bin harush mai mulkin birnin kufa zuwa ga aminina sarki hinzur bin humas, dafatan kuna cikin koshin lafiya kai da al'ummarka kayi sani cewa ban rubuta wannan wasikar don komai ba face don na sanar da kai cewa, matata kuma abar begena ta haifa mani santalelen yaro ayanzu haka dai na zama baba, sannan ina gaiyatarka walimar radin suna , dagamai mulkin birnin kufa sarki hurshad bin harush,
.
Koda magatakarda ya idda karatunsa sai sarki ya dubi dan sakon cikin murmushi yace "kagayawa aminina ina nan tafe nan da kwanaki biyar
.
Marubuci:- Shuraih Usman
Hakkin mallaka (m) Shuraih Usman
Company:- Shuraih 99%
(c) shuraih Usman 2017
Typing:- shuraih 99%
Namijin gaske 1
Part 1E
(c) shuraih Usman
@shuraih 99%
NAMIJIN GASKE
Littafina daya 1
Marubuci:- Shuraih Usman
Typing:- Shuraih Usman
Tel. 08133209890
Part E
.
Doka, banyarda wani yayi copy ko ya sarrafa
wannan labari ta
ko wace hanya batare da izni na ba. Dafatan
za'a kiyaye
Copyright
Shuraih Usman
.
Koda magatakarda ya idda karatunsa sai sarki ya dubi dan sakon cikin murmushi yace "kagayawa aminina ina nan tafe nan da kwanaki biyar
.
A washe garin ranar ne sarki hinzur ya shirya nima ya sanar dani, na shirya muka tasamma birnin kufa dagani sai sarki hinzur da kuma dakaru goma kacal,
.
A tarihin sarki hinzur baya tafiya da dakaru masu tsaron lafiyashi, don wani sa'in ma shi kadanshi yake shiri ya tafi rangadi,
Koda yan fashi, ko wasu muggan dabbobi sun tareshi kuwa, take yake tarwatsa su duk yawansu,
Muna tafe bisa dawakai nida mahaifinka a cikin wata daji mai dogayen itatuwa .
Kwatsam ba zato ba tsammani sai gani nayi sarki hinzur ya dakata,
Nima sai na dakata na dubeshi nace
"Yakai mijina kuma abin kaunata shin ina dalilin tsayuwarka acikin wannan dokar daji mai mugun yanayi" murmushi kawai yayi sannan ya bingiro kasa, yafado daga kan dokinsa,
Toh anan ne naga abin daya tayar mani da hankali, acaccake a bayansa kibau ne har guda biyar,
Koda ganin haka sai na sauko bisa dokina , sannan na karisa wajen dayake kwance bakinsa sai aman jini yake,
Na tallafo kansa ina mai fashewa da kuka, su ko dakarun da muka fito da su suna zazzaune bisa dawakansu.
Nan na daka musu tsawa kan cewa su fara binciken wanda yayi wa sarki haka.
Wani daga cikinsu ya bushe da dariya sai da yayi mai isarsa sannan ya dubemu yace
"Kusani yaku wayannan sarakan yau kam kun gamu da ajalinku"
Sarki hinzur najin haka sai yayi wuf ya mike yayi tsayuwa irin ta manyan sadaukai tamkar babu abinda ya sameshi, sannan ya zaro takobinsa yace da wayannan dakarun
"Ai NAMIJIN GASKE baya faduwa kasa banza, shin kuna tsammanin wayannan kibau din da kuka harbeni da su zasu illata nine hakika kunyi babbar kuskure domin kuwa jinake tamkar Allurai kuka sossaka mini"
Yana gama fadin hakan ya falfala da azababben gudu don ya isa wajen da suke, ai koda ya rage baifi saura taku biyu ba tsakaninsa da su sai ya daka tsalle sama , ya sanya kafafuwansa ya doki dakaru biyu dake kan doki , take suka fado kasa daga kan dawakansu.
Cikin zafin nama ya sanya takobinsa ya guntule kawunansu.
.
Koda sauran dakarun suka ga haka sai suka ruga aguje don su tsira da rayuwarsu, duk sun kasance suna kan doki shi kuwa sarki hinzur bisa kafafuwansa ya falfala aguje don ya cimmusu,
Nan dai aka kasa tsere tsakanin dakarun da kuma sarki hinzur
Cikin kankanin lokaci ya cimmusu, nan take ya daka tsalle sama a samanne tun kafin ya sauko kasa ya sanya takobinsa ya shaftare makwogaron dakaru uku nan suka fadi matattu.
.
Koda ganin haka sai sauran dakarun suka zage damtse sai gudu suke a yayin da shi kuma sarki hinzur ke biye da su abaya, koda sarki hinzur yafara jin gajiya , sai ya yar da takobinsa sannan ya kwala ihu wanda ta haddasa karamar girgizar kasa,
Take tsuntsaye suka ringa canja sheka,
Take dawakan da dakarun suke kai suka firgita ainun da wannan ihu, nan suka tsaya cak suka ki gaba sannan suka ki baya, a haka sarki hinzur ya kariso ,
Koda zuwansa sai dunkula hannu yaiwa doki daya naushi take dokin ta fadi akas sumammiya
Cikin zafin nama ya cafe wuyan badakaren daya ke kai sannan ya murde
.
Cikin kankanin lokaci duk ya karkashe wayannan dakaru
,
Koda yagama kashe su sai yazo inda nake a durkushe ina kuka
Ya mika mani hannu don na mike tsaye
Kawai sai gani nayi kibau ta hudo ta gadon bayansa ta fasa kirjinsa cikin azama na mike na tallafeshi ina mai kiran sunansa cikin karaji,
.
Ya lumshe idanuwa sannan yace " yake abar kaunata hakika naji bakin cikin rabuwar da zamuyi na umarceki daki gudu don ki tsira da rayuwanki"
Cikin sheshshekan kuka nace mai"yakai miijina alfaharin qalbina,kayisani babu abinda zaisa na rabu dakai a kowanni hali ka tsinci kanka aciki duk rintsi duk wuya ina tare da kai ,
Ko mutuwace ta zo daukarka toh sai dai ta dauke mu gaba daya "
Ina gama fadin hakanne sai muka ji an bushe da dariya a bayanmu, koda muka juya sai mukayi arba da waziri humaiz shi da dan fashi kallabu sai kyakyata dariya suke,
.
Nan take hawayen bakin ciki ya zubowa sarki hinzur ya dubeni yace
"Na rokeki da ki gudu don ki tsira da rayuwarki..." Maganar tasa ta katse a daidai lokacin da wata kibau ta cake sa acinya
Nan take ya fadi kasa yana mai aman jini,
Yasake cewa " ki gudu ki tafi ki barni"
Ba don son raina ba haka na falfala da gudu nayi cikin dokar daji, koda kallabu yaga na ruga sai shima ya biyoni,
Koda ya zo wucewa ta gefen sarki hinzur sai sarki hinzur ya gabza mai wata naushi a yayan marenansa, take kallabu ya durkusa sannan ya kama wajen da hannayensa bisa jin wata muguwar zogi,
Damar da sarki hinzur ya samu kenan cikin zafin nama ya zare takobin kallabu a kugunsa,
Sannan ya fille mai kai take dungulmin kan tayi tsalle ta fado a gaban waziri humaiz,
.
A lokacin waziri humaiz na rike da kibau a hannunsa , cikin har zuka ya yarda kibau din gefe,
Sannan ya zaro takobinsa ya fuskanci sarki hinzur,
Nan fa suka rugunzume da azababben yake, nan fa waziri humaiz ya wanzu yana kai ma sarki hinzur sara da suka, shi kuma sarki hinzur ya wanzu yana mai karewa, sannan kuma yana maida martani, sai da aka shafe kimanin sa'a biyu ana wannan gwagwarmayar toh a sannan ne waziri humaiz ya tuna cewa ya riga daya illata sarki hinzur koda gama aiyana hakan aransa sai ya yarda takobinsa sannan ya yage rigan dake jikinsa,
Lallai shima waziri humaiz ba karamin kato bane don kuwa jikinsa a mummurde suke,
Faruwan keda wuya shima sarki hinzur ya yar da takobinsa ya