x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 8 - AMEENATOU YAR KAKA

  • 21001 words
  • 23210 words
  • Out of 23210 words

Category: Romance Story +18

Views 67

30 Jun 2025
Start ads
After Image Ads
ce adaura Auren Ameenatou da Ameenu gobe in dai ni ce uwar da na haifeka."


Cikin firgici Dady ya ce, "Inna ki mun wannan alfarmar Dan Allah."


Kara fashewa da Sabon kuka kaka tai tana yi Ameenatou na tayata.

"Yanzu ni ban isa da kai ba kenan ko Audu? Matan ka sun shanyeka sun baka Nono ka sha ince bani ba?

Ta janyo zani tare da face majina.

"To na rantse sau saba'in da bakwai harda digo biyar in baka Aurawa Ameenatoun dan uwanta ba,bani ba kai ."


Dady ya ce, "Abun bai kai ga haka ba Inna,In Sha Allah za a yi yadda ki ka ce."


Ba tare da ya jira maganar Kaka ba ya tashi kawai cikin sarkakiya ya nufi ɗakin Hajiya Babba.


Dafa kansa ya yi tare da zama agefen gado .


Karasowa Hajiya Karama tai ta dafasa tare da fadin, "Alhaji lafiya kuwa? Ka san dai ba cikakkiyar lafiya gareka ba,kada ka daurawa kan ka damuwa dan Allah,komai ya yi zafi maganinsa Allah."


"Maryam ya Inna take so inyi da rayuwata Don Allah? Ina zan sa kaina, yanzu Al-ameen ya zai yi da Ameenatou wai cewa take fa Gobe adaurawa Al-ameen Aure da Ameenatou."


Duk da kasancewar abun ya taɓa ta har cikin ranta amman sam bata nuna ba.

Zama tai daf da shi tare da sake masa murmushi, "Wannan sam ba abun damuwa bane Dadyn Al-ameen ni duk tunanina ma wani abune, Ameenatou da Al-ameen duk ɗayane awajen mu,miye laifi dan Inna ta ce a haɗasu aure? Jifan tsuntsu biyu zamu yi da dutse daya,mu taimaketa na maraici sannan mu zaba mata miji wanda ba zai cutar da ita ba,ko ma ya Ameenatou take dole haka Al-ameen zai yi hakuri Yar uwar shi ce ba yadda zai yi."



Dady ya gyara zama "Hmm Maryam! Al-ameen bai kula matan nan bama sai Ameenatou? Kuma wai aure a gobe? Ni na ce ma ta bari zuwa karshen wata a hada dana Nauwara amman sam taki na rasa ina zan sa kaina zuciyata zafi take mun."


Hannunsa ta rike tana, "ka nutsu dadyn Al-ameen akwai lokacin da komai zai sauya,yanzu ba duk wannan ba biyayya ga Inna shine farko,ka kirawo Alhaji Adam anjima ka sanar da shi komai, gobe a daura auren, Al-ameen kuma in sha Allah zan kirasa cikin darennan mu tattauna ,ni dai kawai ayiwa Inna biyayya duk sauran abubuwan masu sauki ne, kuma dama ga gidan cen naka an kammala komai ina jin har kaya ansa so ba ma da wata matsala mu mu zauna anan ba sai mun koma ba shi Al-ameen da Ameenatou su koma,ina fatan watarana muyi alfahari da biyayyar da mukai wa Inna."




Ɗagowan da Dady ya yi ya sake wa Hajiya Karama Murmushi, "Maddala da samun mace ta gari mai son farinciki da inganta rayuwar Ahalinta,yanzu bara naje na dubo Alhaji Adam mu tattauna in sha Allah hakan za ayi."


Yana fita Hajiya ta kira Al-ameen a waya nan take kuwa ya xo.


"Al-ameen na san ka fiye da kowa na san wanene kai da kuma kudirin ranka amman ka da ka manta farincikin iyayenka a kullum shine gaba domin inganta rayuwarka cikin aminci, ka da ka bijire mana,kuma ka da ka ce mun zalinceka kamar yadda Inna ta bukata gobe in sha Allah za adaura ma Aure da Ameenatou."


Wani irin faduwar gaba Al-ameen ya ji wanda sai da hanjin cikin sa suka haɗe waje guda.



"Momy! Me ki ke fada? Aure ni? Aure ni fa? Kuma Ameenatou Momy wallahi bana da buƙatar auren kowacce mace a duniyar nan bare Ameenatou, Momy me na maku kuke son hukunta ni da auren yarinyar nan." Karasa maganar ya yi hawaye na zubowa daga idanunsa.



"Al-ameen ban san ka da bijirewa umarni na ko na Dadyn ku ba, ina so kasa aranka wannan kaddara ce da muke fatan kasancewar ta mai kyau,dole sai kayi hakuri ka yi hakuri Al-ameen."




Share hawayen ya yi kan ya ƙaƙulo murmushin dole wanda azuciyarsa yana tuna yadda zai ladaftar da Ameenatou ne kawai,"In sha Allah da kanta zata gudu ta barni."

A zahiri kuma ya ce, "Bakomai Momy."


Murmushin ita ma ta bisa da shi, "Allah ya yi maka albarka."


Da Ameen ya amsa kan ya tashi ya fice ba tare da ya ce komai ba.



Yana fita ya nufi ɗakinsa kwanciya ya yi kawai ban da saƙe-saƙe ba abun da yake,babban tashin hankalinsa yadda ya ga da gaske safiyar nan fa yi take kuma wai aure za a daura masa da yar ƙauyen cen.





Washegari


Da sassafe Kaka ta fito tana kwaleleto , "Audu na ce za ka fito Aɗaura Auren Ameenu da Yar Uwarsa ko kuwa ?"



Dady ne ya fito yana, "Inna Gani za adaura in sha Allah,jiran Alhaji Adam nake zai tawo da goro."


Kan Kaka tai magana kuwa sai ga sallamar Alhaji Adam.

Amsawa sukai a tare Kaka ta ce, "Yawwa Dan albarka in ce kaine Waliyin Ameenu ko?"


Murmushi ya yi, "Eh in sha Allah Inna."



Kaka ta washe baki, "Yawwa to maza adaura zam zam."



Dadyne yasa Al-ameen ya kirawo masa wasu daga cikin makotansu domin sheda daurin Auren.

Haka Al-ameen ya kasance sam ba kumahari da ka gansa za ka san takaici fal cikin ransa amman abun mamaki wani lokacin sai ya sake murmushin da shi kadai ya san ma'anarsa.


Ameenatou kuwa na ɗaki ban da tsalle tsalle da murna ba abun da take taso fitowa Kaka ta hanata wai ai ita Amaryace kuma boye amare ake hakan ya bata damar tiƙan rawa tana murna aɗaki yau tayi aure.



A gaban Kaka aka daura auren Al-ameen da Ameenatou abisa sadaki Dubu ɗari da Alhaji Adam abokin Dady ya bada.


Ana daurawa wata irin guɗa da Kaka ta yi saida ya zagaye illahirin gidan.


"Alhamdulillah Alhamdulillah Alhamdulillah an daura Auren Ameenatou da Al-ameen yan bakin ciki sai dai su mutu."



Nan take Dady suka fice da abokansa.


Ita kuwa Ameeenatou ta fito da gudu ta rungumi Kaka tana, "Kaka da gaske wai yanzu ni matar aure ce kuma Matar Unkle Al-ameen?"


Kaka ta ce, "Eh mana yan bakin ciki kam sai dai su mutu."


Hajiya karama ce ta fito tana, "Cab Lallai Al-ameen ya shiga kaddarar rayuwa wayaga kwaila wannan kam fanko aka aura masa."



Kaka ta ce, "me kika ce? Na ce kin ci gidanku da shegen baki kamar an taune gafiya bani waje ni."

*****

Ranar ko zuwa breakfast Al-ameen bai yi ba.

Bayan an gama kowa na hutawa Kaka ta ce, "Audu ince yaushe za a kai Ameenatou gidanta dana Al-ameen ne?"


Dady ya ce, "Inna na ce ko za abari ayi mata siyayya kafin lokacin bikin Nauwara sai akaisu duka."


"Aa aa na ce maka Audu haka kawai yara da aurensu kuma suna zumudin juna ace za arabasu? Sam ban lamunci daukan hakki haka ba,in ma za ka sani ka sani daren yau za akai Ameenatou gidan Al-ameen eheee."


Dady zai yi magana
Hajiya Babba tayi saurin fadin, "Bakomai Inna Yanzu zan bincika mata sabin kayan Nusaiba a hada mata kawai su tafi zuwa lokacin bikin in aka hada wasu sai akai mata."



Kaka ta ce, "To Uwar azagwaigwai yau kam kinyi hankali ba shakka har kin fi mijin naki, hakan zai fi daren yau akai yara gidansu na sunnah."




Hajiya karama ta ce, "Hmm akwai kallo,wayaga zumuɗin juna."


Dady ya ce, "Nauwara ki kira mun Al-ameen awaya ya zo ɗaki ya sameni."

Yana fada ya tashi awajen.


*****

Jiki sam ba kwari Al-ameen ya nufi ɗakin Dady.

Da sallamarsa Dady ya amsa.


"Yawwwa Ameenu ga Keyn gidan cen nan domin a ciki zaku tare zuwa dare in sha Allah na san baku da bukatar komai hatta kayan abinci akwai sai dai inyi maku fatan alkairi,kayi hakuri da halin Yar Uwarka ka yi hakuri ka danne zuciya Al-ameen watarana sai labari, sannan maganar skul dinta kuma kaje ka karbo mata uniform din ta fara zuwa ranar Monday in sha Allah, Allah ya yi maka albarka."



Al-ameen ya amsa da Ameen kawai kan ya fice batare da fadin komai ba.



Dare na yi Ameenatou ta tsalla kwalliya,jan baki har kasan labba,girar kuwa har kunne,kamar dodonniya, ta zauna gefen gadon Kaka ana jira atafi.


Aiko Dadyne ya yi sallama yana , "Inna in kun shirya ku fito,ga su Hajiya ma,mu rakata sai mu dawo ko?"


Kaka ta ce, "To, to to gamu nan yanzun nan ma kuwa kasan amare sai da rarrashi ga mu nan tafe."


A motar Dady suka je aka kai Ameenatou har gidanta ban da kalle-kalle da tabe-tabe ba abun da take,domin a kyau da komai wannan gidan ya ninka na Dady kai ka ce Aljanar duniya.


Ba ka ce Amarya aka kawo ba domin tuni ta ware tana zagaye gidan.


Hajiya Babba ta nuna mata wasu ɗakuna biyu masu kallon juna.

"Yawwa Ameenatou wannan shine ɗakinki,wancen kuma na Al-ameen."


Kaka tai karaf ta ce, "Au har raba masu ɗaki ake? To ahir irin haka ke janyo kishiya a banza baku iya tattalin miji ba, Ameenatou kar ki kuskura ki kwana ɗaki daban maza kuna kwana ɗaki daya,haka kawai acuceku to ban lamunta ba."



Hajiya karama ban da ummm ba abun da ta iya furtawa.



Dady ya ce, "to mun rakota,Inna ku zo mu tafi gida."


Ameenatou ta washe baki "to Kaka da Hajiya, Baba Audu sai da safenku ban da waccer hajiya karamar kuma karta kara zuwamun gida ma."



Kaka ta ce, "kar ki ji komai maza nemi waje ki zauna, Yanzu Ameenu zai shigo kin san dai me na fada ko? To a kiyaye sai mun zo zaman jego kuma."


Ameenatou ta sheƙe da dariya.


Kaka ta fita tana, "yanzu nan da wata tara za amun kawa Ah Alhamdulillah yo ai wannan aure ni akawa."



Dady ne ya kira Al-ameen ya sanar da shi sun kai Ameenatou ya je gidan kar abarta ita ɗaya.



Ita ko tanan ta ɗane kan kujera ban da tsalle-tsalle ba abun da take yi.



Al-ameen na sallama taje da gudu oyoyo uncle ta rungumesa.


Tsaki ya yi kan ya finciketa gefe.

Dakinsa ya nufa kawai.


Da gudu ta bisa ɗakin ya kara cillota waje.


"Unkle Wallahi Kaka ta ce tare zamuna kwana ta ce kar in barka."


Ko kulata bai yi ba ya share.


Can ya shiga har ya fara barci Kasancewar ya gaji Ameenatou ta lallaɓa taje ta kwanta kusa da shi ji ya yi kawai ana taba masa baki.

"Ji bikin unkle dinnan mai kyau kamar irin na yan tv da muke kallo gidan Baba Audu,bari in masa yadda suke."


Ta kai bakinta za tai kissing na shi kenan kawai........




*😹💔 Ameenatou za tai kissing unkle ya kuke ganin rayuwar Auren Al-ameen da Ameenatou xai kasance? Maza ku hanzarta biya domin karanta naku cikin sauki yanzu aka fara ko ince har yanzu ma da sauki akan na gaba*


Littafaina na kudi ga duk mai bukata

Matar Police 200
Ashe haka so yake 300
Jameel 200
Ameenatou 300


Duk mai son duka hudun 800 maimakon 10000


_LITTAFINA NA KUDINE DUK MAI SO ZATA TURO DA KATIN 300 TA WANNAN NUMBER 08103080717 SANNAN TA MUN MAGANA AWATSP TA NUMBER KO KUMA ATURA TA ACCOUNT 1453215759 Aisha Abdullahi Sani Acess Bank, THANK YOU OLL,SHARE& COMMENTS FISABILLAH🥰_

_*Urs Xayyeesherthuo🤍*_o🤍*_huo🤍*_

An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels
End Ads