lokaci guda ta d'aure fuska ganin Al-ameen ya bud'e 'kofa ya fita ta fashe da wani irin kuka tare da kwanciya a 'kasa tana birgima kamar wacce taji wani mummunan labari, lokaci guda hankalin Kaka ya tashi dan a tunanin wani abu ya faru da Ameenatoun.
Hajiya Babba dake tsaye a gefe ma ta matsu kusa tana 'kokarin ta'ba Ameenatou, da sauri Kaka ta karasa kusa ta bige hannun Hajiya Babban ta fara magana cikin kuka tana fadin "Ba ga irinta nan ba anyiwa yarinya mugunta, yanzu haka ma mayu suka kamata dama tunda muka shigo gidannan na ga ana nuna alamun ba'ayi murna da zuwarmu ba, wayyo ni Indo na shiga uku ya zanyi da ha'k'kin marainiya"
Gefen zani ta saka ta fyace majina ta cigaba da cewa''Kin tsaya kina kallona ne ba zaki wuce ki kiramin d'ana ba yazo asan wacce za'ayi dan ni ba zan lamunce haka ba."
Jiki a sanyaye Hajiya Babba ta mi'ke za ta fita sai dai kafin ta 'karasa ta jiyo murya Ameenatou tana magana cikin shesshe'ka ta ce" Ni fa Kaka ba abinda aka yi kawai yunwa ce inaji yasin kamar hanjin cikina zasu tsinke na mutu haka nakeji."
Kaka ce ta mi'kar da ita zauna ta ce" Bayani zakiyi ai 'yar lelena ga abinci maza kici a 'karo miki dan wannan ba isarki zaiyi ba nasani."
Kuka Ameenatou ta fashe da shi tana fad'in" Ni wallahi ba zanci ba tare da Onkul Al-ameen za mu ci ya dinga bani a baki."
Shiru Kaka tayi kafin ta ce'' Yo ai wannan ba wata matsala bace bari a kirashi ya baki ai kema 'kanwarsa ce"
Kallon Hajiya Babba tayi wacce ke tsaye tana kallon sangarta irin na Ameenatou, Kaka tace"Ke Mero maza je ki kiramin yaron nan Ameenu ya zo ya baiwa 'yar uwarsa abinci a baki."
Cike da ladabi Hajiya Babba ta ce" Mama yanzu kamar Ameenatou ace sai Al-ameen ya bata abinci a baki saboda sangarta ina gani hakan kamar bai dace bawai dan wani abu ba sai dan saboda girmanta yanzu ai abun kunya ne wani ba'ko ya shigo ya tarar ana bata a abinci a baki ba ciwo ba komai kawai dan shagwaba."
Aikuwa me neman kuka an jefe shi da kashin awakai, nan Kaka ta fara surfa bala'i tana fad'in Hajiya Babba ta raina ta daga zuwa gidan d'anta zata fara zaginta, hakuri Hajiyar ke bata amma Kaka ta runtse ido sai masifa take yi.
"Yoo zan ga yau ni da ke wayafi wani mahimmaci awajen Audu in kuma ke kika bani Nonon da na shayar da shi sai ki fadamun."
Ameenatou dake gefe ganin fad'an Kaka ba tsayawa zaiyi ba ya sa ta isa ga plate din abinci ta fara ci hannu baka hannu kwarya dan abincin ya mata dad'i sosai farar shinkaface da miya wacce taji had'i ga nama, hakan yasa bata ko 'kara kallon inda Kaka ke tsaye ba bare tasan me take fad'a.
Hayaniyar da Kaka ke yi ne ya fito da Hajiya 'Karama, ta taho tana rangaji kamar wata matashiyar budurwa dan ita irin matan nan ne ta suke wayayyu, batare da ta kula Kaka ba take tambayar abinda ya faru ko da Hajiya Babba ta fad'a mata yadda akayi sai ta ta'be baki ta fara magana cikin isa ta ce" Banda abinki Mama ta ina Al-ameen zai fara bawa wannan 'kazamar abinci a baki ai hakanma ba zai yiwu ba gaskiya dan idan ya taba wannan kazantar kila kwana zaiyi a asibiti dan kwalera ce zata kama shi."
Ameenatou ta kwalara ihu da sai da ya karade ilahirin gidan.
Kaka ta...................
*Zan ci gaba in sha Allah in ga ruwan comments*
_LITTAFINA NA KUDINE DUK MAI SO ZATA TURO DA KATIN 300 TA WANNAN NUMBER 08103080717 SANNAN TA MUN MAGANA AWATSP TA NUMBER KO KUMA ATURA TA ACCOUNT 1453215759 Aisha Abdullahi Sani Acess Bank, THANK YOU OLL,SHARE& COMMENTS FISABILLAH🥰_
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.```
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
*https://www.facebook.com/106494781436168/*
_RUBUTAWA_
_*Xayyeesherthul-humaerath*_
_SADAUKARWA_
_*Nura Sada Nasimat, Allah ƙara Daukaka Oga.*_
_*Domin Farincikin ki kawar arziki irin albarka Ameena Abubakar*_
_NOBLE WRITERS ASSOCIATION ABAR ALFAHARI NA,NA GAIDAKU DUKA,SON SO FISABILLAH🤍_
_*LITTAFINA NA KUDINE NAIRA DARI UKU⚠️*_
*FREE PAGE-12*
_*KALAMAN SOYAYYA🤍*_
_Ba kyau ko dukiya zan so ba zan sokana saboda ka daukeni tamkar sarauniya, hakan na bani tabbacin cewa babu wata da zata iya kasancewa acikin zuciyarka bayan ni, ina sonka ina kaunar aduk inda kake ka tuna cewa kai ne farincikina_
_*Oyoyo Harbeebbty Zeey Er Mutan Zazzau🥰🥰🥰💃💃💃 Tabbas ina cikin farincikin dawowarki*_
_*🎂🎂🎂Appy bornday Anty Zee (African Black Coffe) admins din Shahararrun Novel Allah ya karawa rayuwa albarka)*_
___________
Tuni Ameenatou ta hau birgima ta jefar da plate ɗin abinci, ta fara kakkafe ido tamkar wata mai aljanu tana faɗin, "Wayyo Allah Kaka wallahi yasin wannan Ƙaraman Hajiya ce ko wace suke kiranta Mayya ce ta kamani, Wayyo zata kashe ni."
Ameeenatou ta kwallara wani gigitaccen ƙara dai dai lokacin da Daddy ya shigo gate ɗin gidan, domin ya fita ya ɗan siyo musu yan kayayyakin da zasu bukata kafin gobe in Allah ya kaimu, ko gama gyara parking baiyi ba ya fito daga motar yayi cikin gida da gudu.
Dai dai lokacin da Kaka ke saka na ta ihun ta nufi Ameenatou tana faɗin, "Wallahi Zulai kike ko waye sai kin sakamun kurwan jikata, dama ai na ji tarihin dangin ku an ce kaf Mayu ne saboda Maitanku ma kuka ƙi Auruwa shine aka laƙaba ma Ɗa na, to wallahi jikata ta fi ƙarfin ki kurwan ta kur, ki zo kawai ki tsallaka ta tashi."
Daddy ne da Al'ameeen suka shigo a ruɗe suna tanbayar lafiya.
"Yauwa gara da Allah ya kawo ka Audu."
Kaka ta faɗa ta kakalo wasu hawayen, tana face majina.
Gaba ɗaya Daddy ya ruɗe ya isa gurin kaka da Ameenatou yana tambayar kaka lafiya.
"Ina fa lafiya Audu garin jajibe-jajibe irin naka kaje ka Auro mana Mayya, gashinan ta kama Ameenatou."
Kaka ta ƙarasa maganar tana fashewa da kuka tana cigaba da jijjiga Ameenatou.
Ita ko Hajiya ƙarama bata taɓa zaton sharin su kaka da wannan figigiyar yarinyar ya kai haka ba, Tabbas sai ta yi maganin su kuwa.
Gaba ɗaya Hajiya Babba ta kasa motsi saboda da ganin sharri irin na Ameeenatou ƙiri-ƙiri domun ganin idon ta ta ga Ameeenatou na ma Hajiya Ƙarama gwalo da dariyar mugunta.
"Wai Audu tsayawa kayi kana kallon ta ba zaka ɗauki mataki ba har sai jikata marainiyar Allah ta mutu ne."
Kaka ta ƙarra saka kuka tana sallallami wai matan Audu sun asire mata yaro dole ta zo ta neman mai taimako tun wuri tun kafin su rabata da shi.
"Ba dan na tuba ba tabbas yau da kunga asirin asali mu da muke mai da mutane kashi ma, to wallahi ahir dinku."
Gaba ɗaya sun ishi Al'ameen ji yake kamar ya kwashe su ya mai da ƙauye, don shi irin mutanen nan ne da bai son hayaniya ya dawo ko hutawa bai yi ba ya haɗu da jaraban su kaka, tsaki ya yi ya juya zai fita, Kaka ta wuf ta sha gabanshi.
"Ka ga wanda kayi ma tsaki nan gasunan tsaye da Audu da Mero, saboda baƙin hali an tsotsa a Nonon Uwa kana ganin ƴar uwar ka rai a hannun Allah Matar Uban ka ta kama mata kurwa Amma kake tsaki zaka fita to ba in da zaka sai Ameeenatou ta tashi eheee."
Kaka ta ƙarisa maganar tana fiki-fiki da ido.
"Audu in har na isa da kai ka sa Zulai ta tsallake Ameenatou, bayan ta tsallake ta kuma ta tashi sai ka rubuta mata takardar saki ta ƙara gaba don ba zamu zauna sa zuri'ar mayu ba, in kuma kaki ni yau a matsayina na uwar ka sai na ɗaga ma Nono kabi duniya eheee."
Gaba ɗaya yan falon sai da suka razana da batun kaka, ban da Ameenatou da ita matuƙar murna tayi, maganar kaka kuma yayi dai dai da shigowar Hassana da Hussaina ƴaƴan Hajiya ƙarama sun dawo daga makaranta, sosai suka razana suma da maganar kaka.
*************************
*ƘAUYE*
"Wallahi Furera ina ta kewar guggo Ameenatou, ita ko tana can Binni tana cin daɗin ta."
"Ke dai bari kawai Lantana ai ji nake kamar nima nayi tsuntsuwa in ganni a Binni ɗin nan."
"Waya ga Fure a Binnni, Tab."
Lantana ta faɗa tana kwashewa da dariya.
"Ki ce dai waya ganmu a Binni ni da ke, kin ji ta shi mu shiga gari muga ina muka nufa ni duk zaman ma ya isheni fa."
"Uhmmm ki bari kawai ai Ameenatou ta fara bamu kewa tun yanzu, na san da tana nan da tuni mun shiga gari.
*************************
"Audu baka ji mai na ce ba ne wai."?
"Naji Inna Amma don Allah ki soke maganar sakin nan zata tsallaka Ameeenatou, insha Allah zata tashi."
Daddy ya ƙarasa maganar ya na mai durkusawa a gaban Inna.
Gaba ɗaya yaran gidan sai suka ji sun tsani Ameeenatou don duk ita ce silar komai.
"Kai Auduuuu Alllah............!
*in ga ruwan comment sai ku ga ruwan typing*.
*TEAM ƊIN AMEEENATOU GAFA AMEEENATOU TA ISO BINNI DAGA ZUWA TA FARA DA MATAN GIDA.*🤣🤣🤣
LITTAFINA NA KUƊI NE DUK MAI SO ZATA TURO DA KATIN 300 TA WANNAN NUMBER 08103080717 SANNAN TA MAGANA TA WHATSAAP TA NUMBER, KO KUMA A TURA TA ACCOUNT 1453215759 Aisha Abbdullahi Sani Acess Bank, THANK YOU ALL, SHARE&COMMENT FISABILILLAH🥰
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.```
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
*https://www.facebook.com/106494781436168/*
_RUBUTAWA_
_*Xayyeesherthul-humaerath*_
_SADAUKARWA_
_*Nura Sada Nasimat, Allah ƙara Daukaka Oga.*_
_*Domin Farincikin ki kawar arziki irin albarka Ameena Abubakar*_
_NOBLE WRITERS ASSOCIATION ABAR ALFAHARI NA,NA GAIDAKU DUKA,SON SO FISABILLAH🤍_
_*LITTAFINA NA KUDINE NAIRA DARI UKU⚠️*_
*FREE PAGE-13*
_*KALAMAN SOYAYYA🤍*_
_Zan So mukasance tare ne kawai da son ranka inko baka bukata na zabi bawa zuciyata hakuri duk radadin ko kunar da za ta ji,amman ina so ka sani,kar ka manta ina kaunarka har cikin raina._
_*TEAM AMEENATOU AYI KARO-KARO ASIYA MATA ABUNNAN FA🤭KO CIKO NE SAI AYI*_
_*MY GROUP MEMBERS ANTIES MASU SHARHI BARKA 😁SU GOGGOS MASU ƊUMAMA GROUP DAN ALLAH ABAMU WAJE MU SARARA😒✋*_
"Aradun Allah ko da Malam ne zai dawo yau ba Zan Yarda Zulai ta ci gaba da zama agidannan ba." Cewar Kaka tana fiki-fiki da ido kamar jinjirar munafika.
Dady ya rasa abun fadi kawai yana kallon ikon Allah duk anyi shiru a falon.
Kaka ta numfasa kan ta ce, "Ince so kake sai ta gama tsotse mata jinin bata tsallaketa ba? To maza ki tsallake mun jika komai ma ya biyo daga baya."
Dady ya kalli Hajiya Karama kan ta ce, "ki tsallaketa dan Allah."
Kamar ba za ta yi ba can kuma ta tuna abun da bata zato ma kaka zata iya abu mafiyin tunanin kowa.
Hakan yasa ta tsallake Ameenatou.
Tana tsallake ta kuwa ta ta shi tana attishawa tana, "Kaka, Kaka ki zo ta sakeni,Wallahi ta sake ni, Wayo kwakwalwar wuyana zafi anan ta shakeni kaka mutuwa zan yi shikenan wuyane ina jin ta kwashe hanjin wuyan."
Riketa Kaka tayi tana hawaye da shekan majina, "Yi Hakuri Ameenatou na kin warke ba za ta kara kamaki ba kin san bana son maganar mutuwannan na fada miki ban so wallahi Ba za ki mutu ki barni ba aradu da ki mutu gwanda mun Audu ya mutu ma."
Ta juya tana kallon Dady "Ka na gani kana kallo Matarka zata cinye mun jika? 'Yar 'Yar Uwarka amman ko ajikinka an riga an shanyeka ko? To ahir na ce rubuta mata takarda saki Hamsin dan uku ya yi kadan ina kallo."
Dady ya kalli Kaka araunace yake fadin, "Inna Dan Allah kiyi hakuri bana so kiyi fushi ki bata dama zata gyara kuskurenta."
"Iyeeee, na ce Iyeee Ashe ma ban isa da kai ba,yoo ko Malam Mahaifinka kafin ya bar duniya bana fada ya ja bare kai na ce ka saketa tun kafin in tarwatsa gidannan."
Ameenatou ce ta ce, "Umm Kaka Kin san miye? Kin ga ita ta girka abincin can kuma ya yi dadi abarta tana mana girki irin wannan in ta kuma kamani sai mu korata ko?"
Kaka ta ce, "kun ga 'Yar Albarka an cuceta kuma ta yafe dake batai gadon bakin hali ba, tabbas yau kun ci sa'ar Ameenatou ne amman da yau sai Dai ka zaɓa ko zulai ko ni Indo."
Ficewa Al-ameen ya yi, ya yin da Hassana da Hussaina su ma suka nufi dakinsu.
Kowa ya watse afalon anbar daga Ameenatou sai kaka.
Kaka ta ce, "Yoo ni naga gyatumar fitina wato duk kowa ya yi daki anbarmu afalo gamu filajin ko? To ba a isa ba, ina kike Mero,mero,mero na ce ki fito nan."
Hajiya Babba ta fito tana, "Inna Gani." Ta karasa maganar tana durkusawa gabanta.
Kaka ta ce, "Ince mu anan kukeso mu dawwama Bama da dakin zamane?"
"Aa Inna ga daki can angyara har kayan ku ma ankai can."
Kaka ta ce, "To maza amun iso ga dakin nima inje in kwanta a kushin kamar kowa."
Sai da Hajiya ta kaisu kan ta dawo dakinta.
Ameenatou tsalle ta fara kan gadon tana waƙa, "Tab Kaka Ai bani ba kauye yasin kin ga gadon nan da di inaga irinsu ne a aljanna."
Kaka ta latsa katifar , "Ba Shakka wannan abu kwai dadin zama kana lumewa kamar ka samu naman dawisu."
A dakin suka hini har dare sai kai masu abinci aka yi, ban da tabe-tabe ba abun da Ameenatou take yi.
Washegari.
Ameenatou ta fita tana zagawa wani daki ta hango.
Dakin Nauwara da Nusaiba, dake Nusaiba na bording bata gidan ita ko Nauwara tana aiki sai dare take dawowa in ta fita tun safe.
Nauwara ta shiga wanka ta ciro kayan da zata sa harda su bra da pant Ameenatou ta shige dakin ba abun da idonta ya fara kaiwa sai kan bra din.
Dauka tayi tana dariya sannan ta daura kan kirjinta , "Aradun Allah zan nunawa Onkul Al-ameen ya siyamun wannan abun saka Nonon ai nima na girma jibeshi ba laushi harda kushin aciki."
Nauwara na fitowa da Mamakinta ta tsaya kallon Ameenatou tana, "Lafiya? meya kawoki dakinnan?"
Washe baki tayi tana, "Ni ce Ameenatou da Kaka mu ka zo kuma."
Murmushi Nauwara tai kam ta ce, "Welcome Ameenatou ta ajiyamun kayan in sa ko?"
Ameenatou ta ce, "Aa ina Zuwa bara inje inunawa Onkul nima ya siya mun ina sa Nono ciki."
Kallonta tai sama da kasa bata ga kirjin da za asawa bra ba kawai ta kyalkyale da dariya.
Ita ko Ameenatou ko ajikinta yafawa tai a kirjinta tana tafiya tana kallo har ta isa bangaren Al-ameen.
Kwance yake yana sharbam barci hankalinsa kwance.
Dukansa ta fara yi tana, "Onkul tashi ka siyamun wannan ka tashi ka siyamun."
Yana bude ido.....
*Zan ci gaba in sha Allah in ga ruwan comments*
_LITTAFINA NA KUDINE DUK MAI SO ZATA TURO DA KATIN 300 TA WANNAN NUMBER 08103080717 SANNAN TA MUN MAGANA AWATSP TA NUMBER KO KUMA ATURA TA ACCOUNT 1453215759 Aisha Abdullahi Sani Acess Bank, THANK YOU OLL,SHARE& COMMENTS FISABILLAH🥰_
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.```
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
*https://www.facebook.com/106494781436168/*
_RUBUTAWA_
_*Xayyeesherthul-humaerath*_
_SADAUKARWA_
_*Nura Sada Nasimat, Allah ƙara Daukaka Oga.*_
_*Domin Farincikin ki kawar arziki irin albarka Ameena Abubakar*_
_NOBLE WRITERS ASSOCIATION ABAR ALFAHARI NA,NA GAIDAKU DUKA,SON SO FISABILLAH🤍_
_*LITTAFINA NA KUDINE NAIRA DARI UKU⚠️*_
*FREE PAGE-13*
*MY GROUP XAYYEESHERTHOU FANS CLUB TABBAS INA YINKU OVER🥰🔥TEAM AMEENATOU ANTIES MASU SHARHI BAN DA GOGGOS YAN ƊUMAMA GROUP*
______
Mai zai gani?
Bra ce sanye a kirjin Ameenatou tana nuna masa.
"Onkul ka siyamun nima wannan ka ji, ka ga ya mun kyau ina so nima in fara sawa."
Wani irin hamshakin Tsaki Al-ameen ya yi bai san lokacin da ya figi Ameenatou ya jafa waje tare da kulle kofarsa ba.
Dafa kan sa ya yi, "Oh My God, Na tsani yarinyar nan amman tana neman takurawa rayuwata."
Ameenatou kuwa bajewa tai tana bori da ihu, "Onkul wallahi ka fita sai ka siyamun aradun Allah ba inda zanje in baka siyamun ba, Kaka ki zo ki ce Onkul ya siyamun abun saka Nono nima zan sa nawa." Tuni kurarin Ameenatou ya baza gidan aka firfito.
Kaka ce ta fara karasawa tana, "Meya Faru kuma Ameenatou kar dai waccen Zulai Mayyar ba ta barki ba har yanzu?"
Kuka ta fara tana, "Kaka Onkul wai naje ina nuna masa ya siyamun wannan abun saka nonon shine ya koroni waje kuma ya kulle kofa, Kaka ki ce ya bude kuma ya siyamun ni."
Kaka ta tashi tsaye da rike kugu kai ka ce Budurwa ƙauye, "Iyeee ai lallai Ameenu ka isa lallai ne tashen balagar tsuntsayen naka har ya kai haka da zaka jefomin Jika waje ba gaira ba dalili to ni da kai ne maza ka bude kofar nan kuma ka ɗauke ta kuje ku siyo in ba haka ba sai na tsinewa shegen goshinnan naka mai kama da albasar turawa."
Nauwara ce ta karaso ta dafa Ameenatou tana, "Ameenatou ina wannan kikeso? To na bar miki kuma Uncle zai fito ya siyo miki wasu ma akasuwa amman yanzu ki fara sa wannan tashi ki daina kukan kinji."
Share hawayen "tau Antu Naura kuma ki ce ya siyamun masu kyau."
Hajiya Karama ta kallesu ta ce, "Oh Allah Gidadanci da ƙauyenci dai bai yi ba Arayuwa, ina brest din da za asawa bran ma kirji kamar kan giginya." Ta na karasa maganar ta juya ta tafi