ba abinda taci, kafin su isa yar kasuwa tuni na faɗima ya kusa karewa saura kaɗan, isa sukai ta zauna gabanta sai dukan uku yake, lah shatu ga yayanki shi da wasu, ɗago kai tayi karaf muka haɗa ido da shi...
Cikin dari dari ta buɗe baki zata mai magana taga ya haɗe rai, ai kuwa taja bakinta ta tsuke
ta mai da idanuwanta wani gurin daban, jin muryar wani tayi yace "sannu yan mata nawa ne nono ƙwarya ɗaya....?,
ɗagowa tayi ashe wanda suke tare da ya Usman ne tare, nace " dubu daya da dari biyar...,
buɗewa yayi ya duba sannan ya rufe, ya kalli faɗima yace "ke nawa ne naki....?,
Duk kuɗi ɗaya ne ta bashi amsa, ciro kudin yayi ya bata ta zuba mai a leda me zane zane, kallan Usman yayi yace "haidar zaka rakani na hau mota ko daga nan gida za ka tafi....?,
yace muje na raka ka sai na tafi nima
tashi faɗima tayi tace " shatu sai mun haɗu a dandali...,
Tace to sai anjima.
Ta tafi suma suka tafi aka barta nan sai raba idanu take, ganin sai zama take ko anzo an taya ba'a saye yasa taji kamar tasa kuka, duk wanda yasan nono me kyau to bai iya siyen nata, ga kuma rana tazo inda take, tashi tayi ta dauki kwaryar nonon da botikin ta koma inuwa ta zauna, tana zaune sai zabga hamma take ya Usman ya dawo, da sauri ta dauke kanta dan kadama su hada ido, har karfe shida tana nan zaune ba wanda ya siya.....
lokacin ta galaɓaita da yunwa sosai, wata mata ce tazo tace ta bata na dari bakwai, ta karbi kudin hannunta na rawa na bata ta tafi, kai har magariba tana kasuwar nan, ganin ana ƙoƙarin rufe kasuwar ne ta tashi, tafiya take tamkar zata faɗi, hanjin cikinta har curewa suke gu ɗaya saboda tsabar yunwa, dakyar ta ƙarasa gida ga ciyayi ga duhu, tayi sallama innai tayi banza da ita kuma ba wanda ya amsa, ashe adda Binta tazo ta ganta zaune da ɗanta, ta ajiye kwaryar nonon tace adda Binta dama zaki zo yau?
toshe hancinta tayi tace "da hallacan matsa sai warin rana kike....,
jikin shatu yayi sanyi ta miƙe, sai taji ance kee....
gabanta ne ya faɗi tace innai ga kudin,
amsar kuɗin tayi ta soma kirgawa, sannan ta buɗe kwaryar ta duba sai kuwa ta ɗauki sanda ta fara bugun shatu da ita, sosai take kuka tana neman dauki amma ko a jikin adda Binta, sai ma danna waya da take abunta ga danta gefe, ganin ba me cetonta yasa ta shige bukkar ya Usman da kullum sai ta gyara mishi, duk kuwa da baya nan, a gigice ta faɗawa kansa ashe yana nan, ya ja da baya cikin faɗa yace "ke wacce mara hankali ce zaki faɗo kai na...?,
tayi ƙasa da kanta tace kayi hakuri dan Allah hawaye nabin kuncinta......
YAR LAGOS
Episode 16-17
Yace Dalla Zo ki fita kin wani tsaya kin tsare mutane da ido, kuma fa ba kallonshi take ba,
hannuwanta ta haɗa waje daya tare da ɗurƙusawa tace "Dan Allah ka temake ni, wallahi ina fita dukana zata ci gaba da yi....,
be ce mata komai ba ya koma ya kwanta, adda Binta ce ta shigo hannunta riƙe da yaronta tace "dan uwarki zo ki fita, banda uban gantali ba abinda kika aje, gidan ubanwa kika tsaya har kikakai dare a waje? kin tsaya rabawa yan tasha gindi ko?...,
Jikinta na rawa ta tashi ta soma bin bango, a lokacin shekarunta 15 bata ma san me take nufi ba, bata da wayewar da zata fahimci ina zancen ta ya dosa, ganin ta kasa fita tace "Usman rikemun yaron nan yau sai naci uban yarinyar nan, sai ta jawo mana abin magana da alama...,
yayi tsaki ya amshe shi yana fadin shegiyar ba, ganin tayo kanta ta ɗurƙusa ai kuwa ta shiga dukanta ta ko ina har ta gaji, komawa tayi ta takure jikin bango ta kasa fita, ɗaukan yaronta adda Binta tayi ta fita ranta a ɓace, ganin ta fita ta koma gefe ta haɗa kai da gwuiwa tana kuka, batasan lokacin da bacci yayi awan gaba da ita ba.
azaɓa ce ta farkar da ita ya Usman ne taji yana daure mata hannuwa ta baya, sannan ya sa mata wani tsumma a baki ya toshe ta yanda kar aji ihunta, ya daga rigarta ya kurawa yan kananan nonuwanta ido, shafarsu ya fara yi gashi ko wani fitowar kirki basuyi ba, ba kunya ba tsoran Allah be dubi yarintar ta ba balle maraicinta ya fara tsotsarsu tamkar ba gobe, sai zogi suke mata shi kuma ba ruwanshi, bata ƙara shiga wani tashin hankalin ba sai da ya cire mata kayan jikinta, a karshe dai sai daya rabata da mutuncinta, tayi kuka sosai har hawayen sun bushe a fuskarta, yace "saura inji kin fadawa wani, wallahi saina ɓatar dake.....,
ta daga kai da kyar alamar bazata fada ba, domin ba ƙaramar a zaba nate ji ba ta ko ina, ya cire mata tsumman daya tusa mata a baki sannan ya kwanceta, ya wurgo mata kayanta ta sa da kyar, be mata Magana ba ya nuna mata hanyar fita ba shiri ta fita jikinta na rawa, bukkarta ta shiga ta kwanta akan tabarmar kaba, ta buɗe kafarta saboda data hade cinyoyinta azaba takeji, har asuba tayi tana cikin wannan hali, gari ya waye innai ce ta shiga kwaɗa mata kira, da kyar ta iya fitowa ta ɗurƙusa cikin dashashshiyar murya tace "gani....,
dan ubanki yau wani salon iskanci kika fito dashi...?, gari ya waye ba ruwan da za'a dora abin kari amma kin kwanta gaki yar hutu ko?
ƙasa tayi da kanta dake tsananin sara mata murya na rawa tace 'innai yau bani da lafiya...,
au ta haka kika biyo? to jeki, Usman Binta ku fito suka fito suna mamakin kiran innai, tace "ku zame min sheda tun da bata ɗebo ruwan da za'ayi amfani dashi a gida nan ba, to wallahi daga safiya har dare bazan bata abinci ba....,
okay kawai ya usaman yace ya koma, ta fita tayi kofar gida da kyar take tafiya, kallo adda Binta ta bita dashi ta ankara da jinin daya bushe a kafarta, ga kuma wani na gangarowa, dariya ta sheƙe da ita tace "innai yarinyar nan ta girma ba mashin shine...,?
kamar ta yanzu wasu ana shirin aurar dasu wasu kuma har da ya'ya
ita dai batace ƙala ba tacigaba da tafiya har ta isa bukkarta, ta kwanta jikinta na mata matsanancin ciwo musamman ma kirjinta da gabanta, a haka har baccin wahala ya ɗauke ta, jin maganar baffa suna hira dasu adda Binta tasan karfe uku tayi, dakyar ta tashi farin ciki ya kamata jin sallamar faɗima, baffa ya amsa tace "innai shatu na nan...,
Eh kawai tace mata, wucewa tayi ta shiga bukkarta da sauri taso tace "faɗima a galabaice
Cikin mamaki fadima take kallonta tace "shatu me ke damun ki? baki da lafiya ne? wannan jinin fa daya ɓata miki kaya da kafa...?,
da kyar ta tashi ta zauna tace eh wallahi bani da lafiya fadima, bakona ne yazo kuma ba ruwan da zan wanke jikina
cikin tausayawa tace "to Bara na ɗauki tulu na ɗebo miki ruwa...,
kamo hannunta tayi tace harda abinci fadima ina buƙata dan Allah, banci komai ba tun jiya
riƙe hannunta tayi gam tace" karki damu kawata, zan damo miki kindirmo amma bamu da siga,
HALEEMATOU YAR LAGOS
EPISODE 17-18
Eh zan iya sha haka ta fada a galabaice kamar kuma zatayi kuka, fatima ta fita cike da tausaya mata tunda dama tasan irin zaman datake a gidan, bata dade ba ta dawo da ruwa da kwaryar nono, lokacin ya Usman ne kaɗai a tsakar gidan, ta ajiye kayan gefe sannan ta zuba ruwa a cikin kwarya ta kai bayi, shiga ta taso ta shatu ta kaita bayi ta fito, ya Usman kuwa fita yayi ya zauna ya zuba tagumi yana danasanin abinda yayiwa shatu, musamman ma daya ga yadda ta koma, to wai ma meya sa ya aikata haka?
bayan wannan abun daya faru kwanan sa ɗaya ya koma makaranta, haka ta dinga rayuwa ba dadi, kwatsam rana ɗaya ciki ya fito ba ƙaramin tozarci taci ba, a gaban ya Usman innai ta watso mata kayanta tabar gidan,
abin ka da ruga tuni kowa ya fito ana kallona, yara suka rakota har tasha suna yi mata ihu, haka ta hau mota bata da kuɗi, da kyar aka samu wanda ya biya mata kuɗin mota zuwa lagos, haka ta dinga fadi tashi a Lagos har ta samu wajen zama, Allah ya taimaketa ta samu aiki a shagon linda tana biyanta duk wata,
shine fa har ta haifi haleemo, taci gaba da rainonta da dadi ba dadi, wannan dalilin ne yasa bata son komawa garinsu, amma sau tari ta kanyi tunani musamman da Haleemo tayi wayo take yawan tambayar mahaifinta, komai na ya Usman haleemo bata bari ba, abu kaɗan ne ta dauko nata, dan haka tafi kama dashi sosai tamkar an tsaga kara,
ɗa sauri haleema ta ɗago jikinta na ɓari, kenan ta wannan hanyar aka sameta innalillahi wa'inana'ilaihir raji'un, ta fara kuka kamar ranta zai fita daman ita ba kowan kowa bace? ga wannan mummunan tabon da har abada ba zai gogu ba, cikin rawar baki tace umma... maganar dataso tayi ta kakare sai kawai ta kifa Kanta a cinyar mahaifiyarta ta tana kuka, bata hana ta ba domin tasan wannan kukan shine samun sa'ida a ranta,
Wannan kenan Kano
Daddy daddy tun daga kan bene take magana, cikin tsawa ammee tace "amra anya kuwa kina da hankali? me makon ki sauko ki sameshi ki mishi magana sai kace wanda zai gudu,
ƙarasa saukowa tayi tace "daddy Dan Allah yau tun da kana gida zaka kai mu shopping, idan kace yaya ya kai mu ba kai mu zai ba....,
ɗagowa yayi ya goge bakinsa da tissue yace 'amra kiyi hakuri yanzu zan tafi office...,
zunɓuru baki tayi ta kalli ammee tace "dan Allah to ki kai mu gidan aunty Farida....,
ammee ta harareta tace ba inda zani, ke kin fiye son yawo habaa, ta sa kuka ta hau sama daddy yayi dariya yace "amrah a kwai rigima....ba kamar momyna ba da ba runwanta....,
briefcase ɗinsa ya ɗauka yace Allah ya shirya mana su, ammee tace ameen amma amra sai addu'a lokaci daya ta birkice, Allah ya shirya mana baki daya
Amin ya Allah ya faɗa yana rataya briefcase dinsa, ya fita tayi mai Allah ya tsare ya buɗe motarsa ya shiga, tare da yiwa mai gadi horn ya buɗe mai ya fita, kiran mansur ne ya soma shigo mai a waya, amma sanin dokar tuki ya faka gefe ya ɗaga wayar, tare da karawa a kunne ya amsa sallamar'sa, gaisawa sukai mansur yace " yau naga ikon Allah daddy Faisal....,
takaici ne ya kama daddy yace"kai daman ba wata magana ce me mahimmanci ba ka kirani....?,
wallahi abokina ina cikin al'ajabi yanzu nan ina wani shago naga wata yarinya wallahi kamar ku ai kafin ya karasa ya kashe wayar ci gaba yayi da tukinsa wajan wasu masu sai da nono ya je ya tsaya siyan fura yayi zai buɗe motar sa yaji ance ya Usman da sauri ya jiyo ƙarasuwa faɗima tayi tace "ya Usman ina huni ko kun kara jin labarin shatu kuwa.....?,
lafiya qalau ya iyalin naki
Alhamdullahi kasan yanzu a kano nake aure unguwar daɓai
to Allah ya bada zaman lafiya
amin ya Allah dan Allah ko kaji labarin'ta
dan jim yayi yace "a'a bamu ji ba...,
gefen mayafin'ta ta saka ta share hawaye tace"Allah ya bayyana'ta in a raye take in kuma ta mutu ya jikan'ta....,
amin ya Allah miƙo mata kuɗi tayi tace baza ta amsa ba sai da ya matsa ta amsa shiga mota yayi zuciyarsa ba dadi tunani ya ishe shi har ya isa office be de tunani ba
shima yanzu ya fara zargin anya kuwa tana darai har ta kai wannan shekarun ba ta waiwayo gida ba parking yayi ya fito ma'aikatan Company ne suka shiga girmama shi cikin mutuntawa yake gaishe shi har ya buɗe office ɗin'sa be dade da zama ba Faisal ya shigo gaishe shi yayi yace "daddy ina huni....,
lafiya qalau Faisal daman baka gida
zama yayi yace"eh ina nan...,
to Allah yayi albarka
amin ya Allah
shirune ya biyo baya file ɗin da aka tara mai tun safe ya shiga dubawa Faisal na taya shi Faisal dole kai zan tura Lagos ka tawo da wannan order da mukai in jinan sun zo
To Allah ya kai mu ya faɗa yana ci gaba da duba file ɗin
Wannan kenan Lagos
Haka rayuwa ta ci gaba da gudana yayin da haleema ta zama cikin damuwa saidai kullum umma na yi mata na siha da wa'azi amma kam zuciyar ta ta bushe idan ta tuna rashin imanin da mahaifin nata yayi mata har ya zaɓi ta zo ta wannan kazamar hanyar da take tsanar zina ashe zina ce tayi ta jin sallamar aunty zulfa'u da sauri ta ɗago tace
"Aunty zulfa'u sai yanzu kika dawo...,
zama tayi ta cire mayafin da ta rayata tace "wallahi kuwa kin ganni nan shegen mutumin nan ya ɓata min rai wallahi har na gama zamana wai be zo ba wani meeting ya tsare shi....,
dariya halee tayi tace"wallahi ki gane ba wani meeting matar'sa dai ta riƙe shi...,
pillow ta hulla mata dariya tayi tace "wallahi gaskiya nake faɗa miki...,
wallahi halee kin raina ni ina umma
yau ta tafi aiki
ke me ya hanaki zuwa...?,
hmmm bakomai
tabe baki zulfa'u tayi tace "ta nuna miki halinta ko..?,
au kin san halin nata
wallahi na sani yar iska ce neman mata take ni kuwa me zanyi da yar uwata mace ga namiji hajiyata
to Allah ya shirye ki kema daman zaki aure wallahi
halee kenan ta faɗa tana tashi tsaye cire kayan'ta tayi,
ta ɗauki
towel ta daura ta fita suka gaisawa da iya aliya, shiga bayi za tayi taga da mutum ciki, taja wani dogon tsaki tana cewa kai Allah ya yaye mana zama a wannan gidan, wannan wacce irin jaraba ce haka? ace mutum ya rasa inda zai yi iskancinsa sai a bayi, kai dan kuttumar ubanka ka fito,
dayake kusan rabin yan gidan suna jin hausa, gida ne me face me face you, ɗakuna goma sha biyar ne ban daki ɗaya, kuma kullum baki zuwa suke suna fita, ko da sunday yaji zagin da zulfa'u tayi masa shima sai ya rama, yace "kai ma kuttumur uban ka shege....,
dai dai lokacin haleema ta fito taji yana zagin zulfa'u, tace lallai ta samu damar da za tayi maganin dan iskan mutumin nan, cikin ɗaga murya tace "Wallahi ka fito kona janyo ka ɗan wahala kawai..,
buɗe kofar bayin yayi yace shigo idan kin isa, da sauri haleema ta dauke ido gabanta na faɗuwa, domin haka ya fito baya kaya jikinsa haihuwar uwarsa ko kunya, ita kuwa zulfa'u ko a jikinta tace "wallahi kasan halina sarai, saina shigo wallahi na kuma ci mutuncin ka....,
fitowa yayi gaba daya ashe bashi kaɗai bane shida kartuwarsa ne
salati halee tayi tace "tab amma wannan anyi dan iska wallahi...,
yace ko kema kina ciki ne
tace Allah ya kiyaye
shigewa daki sukai zulfa'u tace "kinga sunday yadda kika san gindin ayu ne dashi, kullum kana nan kana can shege a haka zai kare
kinga aunty zulfau shiga bayi dai kafin wani ya fito, kafin haleematu ta rufe bakinta tuni maman tobi ta shiga, da sauri halee ta tashi taje ta fusgota, kifa mata mari mamman tobi tayi kafin ta sauke hannunta itama ta rama tace "ke wacce irin jaka ce kina jin abin da ake, amma saboda dudewar basira kika banza kamar baki ji ba zaki shiga...,
maman tobi tace ni kika mara?
ko zaki rama ne?
zulfa'u ta fito ta shiga ta barsu nan suna fada, matan gidan ne suka taru aka bawa maman tobi rashin gaskiya...
ganin kowa ya bata rashin gaskiya ta ja matattun ƙafafuwanta ta shiga daki, zalfau ta fito haleematu ta shiga wankan itama tayi ta fito, shiga daki tayi ta ɗauki wayarta tana game batare data saka kaya ba, dama daurin gaba ne jikinta, ajiye wayar tayi ta fara wani tunani dole fa ta zama fitsararriya idan tana so mahaifiyarta da ita su zauna lafiya a gidan nan..
ba wanda ya isa ya taka su, zalfau ce ta shigo ta zauna take cewa halee tunanin me kike...?,
tace na samun mafitar zama a gidan nan ne
ta faɗa kanta tsaye batare da shakka ba ko shayi,
good girl abin da tun farko ya kamata kiyi kenan, kin ga ana yi min abin da ake yi muku....?,
ta kalleta tace a'a
to saboda an san ni ga abin da nake kuma bani da kunya, tunda har na iya baro garin mu na taho nan karuwanci, bance ki zubar da mutuncin ki ba amma ki tashi tsaye ba dan iska ko shegiyar da zaya kawo miki wargi,
halimatu kam ta dauki hudubar nan, ta kwanta rub da ciki tace "Insha Allahu daga yau sai na gyarawa ko wanne shege zama a gidan nan,
Well-done yarinya haka nakeso
sallamar ra'isa ce ta tayar da halee da take kwance, da bacci har ya dan fara dibarta, tace" ra'isa ke nake gani haka ko me?
dariya ra'isa tayi ta cire katon glass din dake fuskarta daya kusa cinye rabin fuskar, sai zabga kamshi take kamar an yi ɓarin turare, zama tayi tace sannun ku ina umma....?,
amsa wa zulfau tayi ta fita halee tace tana wajan aiki...,
to Allah ya temaka
amin ya allah ya akai ki ka gane gidan mu?
dariya tayi sosai tace " ke ma dai tun ina primary school nake biyowa ta nan fa kafin mu tashi....,
Allah sarki to ya karatu halee ta tambaye tana tana ƙoƙarin tashi
rike ta tayi tace " ina zaki kuma...,
tace zan samo miki ruwa da biscuit ne,
wallahi karki damu kafin na fito sai da naci abinci
halimatu ta koma ta zauna, daman biscuits din bashi zata karbo, Ra'isa ta kalli haleematu sosai tace kin yi kyau abinki haly, komai naki ya ƙara fitowa,
ta faɗa tana kallon shatin kan nonuwanta daya fito
dan murmushi halee tayi tace hmmm ina wani kyau, duk rayuwa ta tasa mu a gaba, ke dai Allah ya kyauta,
ayya Allah ya kawo muku mafita kawata