x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 2 - ALIYU HAIDAR

  • 3001 words
  • 6000 words
  • Out of 42137 words

Category: Romance Story +18

Views 126

18 Jun 2025
Start ads
After Image Ads
asma'u, kinji siyama wannan shine abunda yasa na tsaneshi, saboda da ba dan an haipieshi ba da banda damuwa"
Nana ta juya ta dubie siyama
"Kuma wallahi zan iya halaka aliyu akan hakan"
Siyama dake zaune da sauri ta tashi tsye tasa hannu ta dafa kafad'anta
"Nana kiyi hkuri ni banga wni abu gameda hakan ba tunda mahaipinku komai yanayi maki kuma shi ai namiji ne fa, dole ne ya rik'a daukanshi yana fita dashi"

Nana tai ajiyan zuciya
"Hmm siyama kenan kada ki manta a cikin Al_qur'ani mai girma Allah yana cewa "y'aku wad'anda kukayi imani kuji tsoron Allah kuma kuyi adalci a tsakanin "ya "yanku". Allah bai ban_bamta "ya "ya maza da "ya "ya mataba, dukkan mu "ya "yanshi ne da siyama...
Siyama ta nisa ta bude baki
"Buh amma...
Dea2 lokacin mai zuwa daukansu yazo hkn yasa siyama tai shiru, aliyu na hangoshi da gudu ya karaso inda suke
"Anty nana gashi mota tazo mu tafie gidah"
"Jeka gani nan zuwa" ta fad'a tare da watsa masa harara.
Jiki a sanyaye ya k'arasa cikin mortar ya bude gidan gaba ya shigah.
"Aliyuna har an tashi"?
"Eh an tashi kuma kasan next week zamu fara last exam dinmu a primary kaga sea in shiga secondary ko"?
Murmushi yay
"Allah ya bada sa'ah aliyu"
"Amin uncle" ya fad'a yana daria.

Nana tai d'an murmushin mugunta
"Yau aliyu ina fadamaki bazea kwana a duniya ba, ba dea ice cream yake shaa ba? Yui kuwa zaisha na ajalinshi, kada ki kashe wayanki dan zan kiraki in fadamaki cewan aliyu ya mutu"
Ta kyalkyale da daria ta kama hanya zuwa mota, yayinda siyama ta girgizah kai cike da tsoro take kiran sunanta, dan daukan take ta haukace.
Nana najin kiran da take mata tai banza da itah, hka ta shiga mota ta maida marfin motan ta rufe, kawu musa yaja motan suka karasa gidah.
®Kausar Luv💞
[11/15, 5:19 PM] Kausar~Luv: [7/30, 9:30 PM] Kausar Luv💞: *ALIYU_HAYDAR*
Page ((7))

©Kausar M Hassan

"Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un"
Siyama ta furta a fili, yayinda ta kira shafi'u ganin mai zuwa d'aukansu yazo.
Da gudu ya karaso suka shiga motan duk a gidan bayah, tunani ta hauyi na anya kuwa za'a samu irin wad'an nan mutanen a duniyah lallai kuwa nana ta tabbata batada hankali kuwa, amma ya zatayi tai saving din Aliyu gameda nana "?? Wannan shine tunanin data shigayi a hka har suka karasa gidah dukansu.
Suna isa aliyu da gudu yay kan abbi, abbi yaja hancinshi kad'an
"Ma boi an dawo skul ko"?
"Yes daddy and kasan kuma cewan ranar monday din nan zamu fara jarabawa, I need to read hard sannan kuma ynxn babu shan ice cream babu wasa, babu game"
Murmushi abbi yay
"Ma boi kenan, kaga kuwa abunda ya kamata ayi shine kana kammala primary dinka tunda akuy yaron abokina dake karatunshi a london shima secondary yake sea in had'aka dashi kaje chan ka kammala har degree dinka ka dawo ko"?
Aliyu daria yay
"Abbi ni bana son zuwa chann, America nakeso" ya fad'a cikin muryan shagwa6a.
Duk wannan abun dake faruwa a gaban idon nana akeyinshi, wani d'an guntun tsaki taja tukkuna ta haura sama tai d'akinta cike da takaici.
Abbi ya d'go kai ya dubie ummi dake tahowa
"Kinga d'anki nan wea nace na kaishi U.K yace U.S yakeso idan ya gama primary dinshi.
Ummi ta dafa kanshi tare da cire masa jakar makarantar dake goye a bayanshi.
"To alhj inda yakeso ba sea akaishi a chan ba, tunda dea d'ana ne, maza kaje kai wanka kazo kaci abunci sea driver ya kaika gurin mame ko".
Alhj shuraihu y d'ago kanshi
"Babu inda zashi yana nan tare damu"
Zatayi wata magana kawea ya haura sama yay d'akinshi, yayinda aliyu ya tafi ya aikata kaman yanda umme tace ya dawo da kanta take bashi abunci yana ci, har ya koshe ya tashi yay d'akinshi ya fara karatu kaman ynda ya fad'ah...
[7/30, 9:33 PM] Kausar Luv💞: *ALIYU_HAYDAR*
Page ((8))

©Kausar M Hassan

A chan bangaren siyama kuwa tun bayan komawarta gida tunani kawea takeyi, saboda tasan nana zata iya aikata abunda ya zarce wnda ta fad'a gameda duniyah.

Da wannan tunanin ta wuni har dare
Misalin karfe 8pm na dare, bayan sun kammala dinner d'insu, ummi taja hannun aliyu sukai d'akinta, tana zaune tana kallo, sea ga kira wayanta ya hau ruri.
Dauka tai ta kara a kunne tare dayin sallama
"Assalamu alaikum"
"Amin alaikum salam ummi, nice siyama kawar nana dan Allah aliyu nakeson yin magana dashi idan yana kusa"
Ummi ta kira aliyu, da sauri ya taso yazo
"Kar6a waya wea siyama kawar nana keson magana dakai, kayi magana ni zan tafie kasa in dauko maka lemo in dawo ko"?
Kai ya d'aga mata alamar to tare da amsan wayan ya kara a kunne.
Cikin muryanshi mai dadin sauraro ya fara magana
"Hello"
"Hy"
"Aliyu kana jina ko? Daga ynxn duk abunda nana zata baka kada kacishi"
"Saboda mi"? Ya fad'a a takaice.
"Saboda tace tana so ka rabaka da mame kaji ko"?
Kai ya girgizah tukkuna ya kara da cewa
"To anty siyama bazan ciba"
Ya maida wayan ya kashe.
Idonshi da zai d'ago sukayi ido 2 shida nana, ido ya ware, yayinda nana ta shigo a d'akin tana yimasa murmushi rike da ice cream a hannunta.
Da gudu ya hau kan kujera ya dauki remote ya chnza channel zuwa MBC 3 ya hade hannayenshi guri d'ayah.
Nana murmushi tai ta matsa kusa dashi ta zauna
"Aliyu na"
Ido ya d'ago
"Na'am anty nana"
"Ga ice cream na kawo maka, nasan kana son ice cream"
Kai ya girgizah
"Ni bazan sha ba anty nana, ummi tajie ta daukomin lemo"
Nana ta turnukie fuska
"Haba aliyu mai yasa bazaka shaa ba, kaga bazan kara dukan ka ba kaji ko"?

"Na fadamaki bana shaa ki kyaleni anty"
"Dan ubanka sea ka shashi ina maka magana kana kyaleni ko"?
A zuciye ta bud'e roban ice cream d'in ta d'ebo a cikin chokali ta fara mika mashi tare da murd'e masa baki, kokawa ta 6arke tsakaninsu.
"Hakan yayi dea2 da shigowan ummi

"Ke! Mai kike yine haka"?
Cikin rawar murya ta fara magana
"Ummie a'a... wea.. dama ice cream ne na bashi shine yace baya shaa"

"To ana dolene nana, tunda baya sha ki kyaleshi mana dan Allah, ki daukie kayanki ki shaa mana"
Ta karasa maganar da karasawa cikin d'aki taja hannu aliyu suka wuce ciki
A cikin zuciyanshi yake cewa
"Kin shiga 3 kuwa nana" yay mata gwallo😜
[7/30, 9:40 PM] Kausar Luv💞: *ALIYU_HAYDAR*
Page ((9))

©Kausar M Hassan

Washe garin ranar ta kama assabar tunda safe aliyu ya tashi ya tattaka zuwa kopar dakin nana, kasancewar masu aikin gidan da an kammala sallan asuba suke tsafatace ko ina da ko ina na gidan.
A hnkli ya daukie ruwa a cup, dea2 kopar d'akinta ya zubar dasu ya ruga a guje y koma d'aki ya kwanta.

Ba'a jima ba nana ta fitoh dga d'akin, taku 2 tai kajita kasa tim😂 kamar an zube kayan wanki, kugu ta rike ta fara waiyyo! Dkyar ta iya tashi tukkuna ta karasa d'akin aliyu ta kwankwas, tasowa yay ya bud'e tare da cewa
"Ina kwana anty nana"
"Lpy qlw aliyu, zo muje kitchen yau ni zan dafa maka abuncin daka fiso kaji ko"?
Murmushi yay suka kama hanya sukai down stairs, a kasan ta samu dogon towel ta d'aura ta cire kayan baccin ta shanya a igiyah suka shiga kitchen din, ta fara har_hada masa indomie, shidea yana zaune yana kallonta
Har ta kusan kammalawa ta dubie aliyu
"Jeka d'akina ka dauko min kaya na nan kan karamin drawer dina yi sauri"
Babu gardama ya haura saman, koda ya isa an goge ruwan, daria yay kad'an ya bud'e dakin ya shiga y dauko kayan kaman ynda tace ya dawo kasa.
Koda ya sauko ya tarar da ta had'a abuncin akan dinning.
"Yauwa aliyu kawo kayan nan zauna ga abuncinka nan na had'a maka"
Murmushi yay ya dubieta yaga tana yin yar daria
"Anty nana ina ruwa, kinsan bana cin abunci sea da ruwa fa".
Har ta bud'e baki zatayi masa fad'a sea ta fasa ta tashi ta koma kitchen, kapin ta dawo yay maza y chnza kwanon abuncin ya fara cin na gabanshi.
Tana dawowa ta tarar dashi yana cin abuncin, haka yasa tai murmushi ta ajiye masa ruwan kusa dashi, ta zauna ta fara cin nata, tana ci tana murmushin muguntah, shi kuwa aliyu sea cin nashi yakeyi.
Har taci abunda yafi rabin abunci sea taji cikinta ya fara murd'awah, da sauri ta rike cikinta, ta fara hawaye, aliyu ta kalla tagan lapiyanshi kalau, take ta kai k'asa, aliyu dake zaune da gudu ya haura sama ya kira ummi, tare suka dawo shida ummi a rud'e, da sauri tace "zubairu kiramana Dr bilal, haka kuwa akayi , kasancewar shi makocinsu da hanzari yazo gidan, yana ganin hakan yace "a bashi madara peak, da sauri aka shiga kitchen aka kawo masa, fasata yay yace "ummi ta rikata", haka ummi ta d'aga kanta ta bata madaran tasha, take sea amai, nan aka dauketa akai da ita d'aki, Dr bilal ya dubata bayan d'an lokaci kad'an ya dubie hajjah
"Hajja guoba ce taci a cikin abunci, Allah ma yayi mata arziki dan da ta kasheta"!

🙆🏾Nana u wan kill d lion😏?

Cike da mamaki hajjah ta amsa da
"Guoba kuma dr, kai aliyu waye y baku abuncin da kuke ci"?
Cikin sanyin murya y kalleta
"Ummi ita ta dafa fa kuma ita ta bani nawa da nata"
Ummi ta jinjina al'amarin
"Allah ya sauwaka, nan Dr ya basu tabbacin cewan zata farka zuwa wasu awowi, in shaa Allah kuma zata buqaci hutu sosai, ya kuma yi masu sallama.
Fitarsa keda wuya, ummi ta fitah ta bar aliyu a d'akin
Daria yay a fili ya furta
"Am back bakin samu na rika jin magana ba har ina jin tsoronki ba, to na dawo da asalin sunana na aliyu"
Dama chaan bana jin magana, haka nake wollah😂 sbd hka ki kuka da kanki... Nanuwa😏
®Kausar Luv💞
[11/15, 5:19 PM] Kausar~Luv: [7/31, 5:39 PM] Kausar Luv💞: *ALIYU_HAYDAR*
Page ((10))

©Kausar M Hassan

Nana bata farfado ba sea kusan la'asar tana nan tana bacci, yayinda Aliyu ya tafie makarantarsu ta islamiyya dake nan kusa da gidah.
Bayan nana ta farka dga bacci, a hnkli ta bu'de idonta chaan ta tuna abunda ya faru sea ta girgizah kai
"Yaro kaman aljani, nikam yau ai danayi mutuwan mazuru"
Tashi tai ta shiga toilet ta watsu ruwa, tare da d'aura alwala tai sallah.

Aliyu bai dawo ba sea karfe 6 dea2, yana shigowa sukayi arangama shida nana, jaa da baya yay kad'an tukkuna ya kalleta
"Anty nana ina kwana, ina wuni"?
Hannu tasa ta rike masa kunne
"Kai uban wa yace maka ka chnza kwanon abunci nan d'azu"?
Baki ya torou
"Nifa anty nana kinga ba ni naiba, kefa kika bani abuncin nan"
A kunne take fad'amasa
"To yayi aliyuna yi maza kaje d'akin ummi"
Murmushi yay
"Ok anty nana"
Kai tasa ta fita wajen gidan yayinda aliyu cikin sand'a yay dakin nana ya maida ya kulle. Kasancewar akuy wata kujera a d'akin da nana ke zama mai kamar ta karfe, kuma d'aurata akeyi mutum take zea iya kwance ta y kuma had'ata.
Aliyu daria yay, ya daukie kujeran ya kwance d'an abunda akasa aka d'aureta ya maida ya ajiye, ya lalla6a ya fitoh dga d'akin zuwa nashi d'akin ya cire kayanshi yay wanka ya chnza kayan jikinshi abunshi yasa takalminshi sandals ya fitoh.

Aliyu haydar kenan ba dea tsafta ba, ga son gayu kwata2 baya son k'azanta a rayuwnshi, gashi dea yaro amma kuma abokin manya sbd Kanshi na jaa...
Yana fitowa kai tsaye dakin ummi ya nufah, chaan ya tarar da abbi zaune kan carpet yana kallon CNN, yayinda ummi ke had'a lemun ginger.
"Assalamu alaikum" aliyu yay sallama
"Amin alaikum salam" abbi da ummi suka amsa
Da gudu yaje kusa da abbi ya zauna shima ya kurawa TV d'in idanu yana kallon news, duk da primary school yake amma yana jin turanci, irin wnda ba big2 grammars d'in nan ba.

Chaan kaman an ta6ashi ya dubie ummi
"Ummi ni gskya ki fad'awa abbi bana son america kuma, makkah nakeso"
Abbi dake zaune yay daria kad'an ya dafa kanshi
"Aliyu mai yasa kake son zuwa chaan Makkah"?
"Abbi saboda kaga chaan duk muslimi ne"

"Shekenan Alhj kaga d'ana yayi zabi mai kyau sea akai shi a chaan"
"Allah y kaimu lokacin"
Ummi ta amsa da
"Amin"
Yayinda Aliyu yay murmushi abunshi wnda ya k'ara masa kyau..
[7/31, 5:57 PM] Kausar Luv💞: *ALIYU_HAYDAR*
Page ((11)

©Kausar M Hassan

Karfe shida da rabi nana ta dawo dga inda ta'je, kai tsaye dakinta ta nupa, taja kujera ta zauna, zaunawan da zatayi kajita kasa rum,
"Waiyh Allah"
A daddafe ta tashi ta koma kan gado ta zauna, tana mamakin abunda ke faruwa, sea kuma ta tuna da cewan Aliyu fane, chaab!

Hka sukai spending ranakun karshen makon, tskanin aliyu da nana kuwah, duk tarkon data had'a masa sea ya ketareshi abun y koma kanta.

Yau ranar ta kama monday, sbd hka Aliyu da nana suka shirya zuwa makaranta, kasancewar yau itace ranar dasu zasu fara jarabawa yasa shi natuswa, hka suka shiga class din, da uniform din makarantar dark blue din wando da farar riga, da abun wuya shima dark blue, na matan kuwa duk hkne dfrnce din shine bbu abun wuya, sea farin hijab..
Hka sukai exams d'insu har ta tsawon sati 2 suka kammala.
Ranar da suka kammala akai hotona na bankwana, tare da malamai da kuma d'aliban makarantar.

Akuy wata yarinya a ajinsu aliyu mai suna Nadiya, ita dea aliyu yana matuqar burgeta, hakan yasa tai duk ynda tai sukai hoto su 2, sannan sukai tare da shafi'u..

Bayan kammala exams d'inshi, ya rage dagashi sea ummi ke zama a gidan, kasancewar nana tana zuwa makaranta yin waec, rayuwarsu sukeyi cikin jin dadi yayinda abbi yasa aka fara nemawa aliyu admission dinshi a wata makaranta dake nan gaein madina birinin manzo, brinin karamchi....
[7/31, 6:15 PM] Kausar Luv💞: *ALIYU_HAYDAR*
Page ((12))

©Kausar M Hassan

Bayan wata 3!
Yau ranar ta kama ranar juma'ah, yayinda ummi keta faman had'awa aliyu kayanshi na wucewa makarantar da aka sama mashi admission din a kasar madina.
Bayan ta kammala hada masa kayanshi tsaf, ta dubie abbi dake zaune yana kallonta yana murmushi,
Cike da tsoro da kuma fargabar abunda zai biyo baya ta fara magana.
"Alhj dama cewa nai mai zai hana akai yaron nan yaga mame dinshi kapin ya wuce makaranta, tunda yanzu idan ya tafie kuma sea ya jima bai dawo ba"?
Abbi dake gincire y tashi tsaye ya dubie ummi
"Ina wasa dake irin wannan ne? Kada ki koma yimin wannan maganar idan ba haka ba ranki zai bace a gidan nan"
Yana kammala fadar haka ya tashi ya zarce d'akinshi

Ummi binshi tai da kallon mamaki, a zuciyanta ta furta
"Ikon Allah ikon gskya, ynxn ni daga magana sea abu y dawo kaina? Ni ina laipiena dan kawea inaso kayi abunda yakamata, wannan ai baso bane kana kokarin raba uwa da d'anta, Allah ya sauwaqa"
Washe garin ranar ta kama assabar, ummi ta shirya ta fitah bikin wata yar kawarta da akeyi, aka bar nana da aliyu a gidan
Nana ce zaune a babban falo, tai zaune kan kujera, aliyu ne ya fara saukowa dga d'akinshi, idanunta da zata d'aga tagan shi yana kokarin yayou downstairs.
Cikin kakkausar murya ta kira sunanshi
"Aliyu kai"
D'agowa yay ya dubeta dan bashida idea akan abunda zata iya yi masa yasa ya sakko k'asan, kusa da ita yaje ya rage tsayenshi ya kafeta da idanunshi, hannu tasa ta zungureshi akai, ya dago idanunshi da sukai narai2 ya dubeta

"Kai zaka tafie saudi karatu ko"?
Ta d'aga hannu kenan zata mareshi sea ga sallama
Wadda wannan ba sallaman kuwa bane face na Anty zaliha, kanwar mamansu, tare da nafisa kanwar nana.
Hakan yasa ta fasa niyyan abunda zatai, da gudu nafisa ta rugu, duk daukan nana gurinta zatai sea taga tayi gurin aliyu.
"Yaa aliyu i miss u"
Murmushi yay kad'an
"Kanwata inace kin dawo gidah dea sbd nima a rika cemin yaya"
Nafisa ta d'aga masa kai
Aliyu yaja hannunta suka haura saman d'akinshi yayinda anty zaliha ta zauna kan kujera, suka fara tadie da nana, nan ta dauko mata ruwa da lemo ta kawo mata tare da kiran zubairu daya sanarwa ladidi mai aiki ta dora girki anyi bakuwa.

Zubairu! Shine babban yaron gidan Alhj, shine ya zaama tamkar d'an uwansu na jini da tsoka jiki da jijiya. Yazama kamar sarkin gidan, duk abunda ake a gidan yana sane, haka ya daukie aliyu tamkr d'an daya haifah..
Haka kuwa ya fice ya aikata kaman ynda ta fad'ah.

Ba ummi ta dawo ba sea bayan la'asar lis tukunna, nan suka gaggaisa da kanwarta ta kuma shaidamata cewan nafisa ce tace tana son dawowa gidah shine tace bara ta kawotah.
Bayan d'an lokaci kadan tai mata sallama tare da kama hanya zuwa garinsu wato Kadunah..

Aliyu da Nafisa kuwa wata shaquwa ke kara shiga tskaninsu, suna son junansu a matasyin yan uwan junah..
A wannan rana dea a d'akin ummi suka kwana dukansu.
Washe gari!
Da asuba aliyu yay d'akinshi yay sallah, ya zauna yana tunanin mamanshi, shi ko yama zayyi ya ganta bai sani ba.
Nana ce ta bud'e d'akin sad'af2 kaman wadda zatayi satan wani abu ta shiga, tana shiga ta maida kopan ta rufe...😳🙆🏾
Waiyyo dear little aliyu lion😰
®Kausar Luv💞
[11/15, 5:19 PM] Kausar~Luv: [8/1, 8:13 AM] Kausar Luv💞: *ALIYU_HAYDAR*
Page ((13))

©Kausar M Hassan

Tana shiga ta dubie aliyu, kan kujera ta zauna
End Ads