An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng
"Alhaji dan darajar Allah kayi hak'uri ni bansan laifin da nai maka ba, mai ya kawo maganari saki"???
Cewar yar matashiyar matan dake tsaye a gaban wannan dattijon, wadda ta kasance ita ba fara ba ita kuma ba baq'a ba, shekarunta bazasu wuce 30 ba.
"Hajiya na fad'amaki cewan na' sakeki saki daya saboda hka idan Allah y baki miji kiyi aure"
Yana gama fad'in yaja rigarsa fuuu y wuce.
Kai kawea ta girgizah saboda tasan tabbas mutum baya tab'a wuce kaddararsa, hakan yasa ta koma d'akinta ta tattara kayanta a cikin jaka ta had'a ta dau mayafinta ta fito, zuciyanta cike da k'una da bakin ciki, tana kawowa tsakiyan gidan d'anta na dawowa dga makaranta, jakar makarantar shi ya yarda akasa, da gudu ya isa gareta.
"Mame tafiya zamuyi ne naganki da jaka a hannu"?
Rage tsayenta tai dea2 nashi tasa hannunta ta dafa kanshi
"Aliyu ba tafiya zamuyi ba, nidea zan tafie, kuma a nan zan barka, ina mai maka nasiha da kazama namiji, kazama mai hakuri da juirya akan duk abunda zai biyo bayanka"
"Mame dan Allah kada ki tafie ki barni, wallahi zan rik'a jin magana, bazan k'ara fasa kwano ko d'aya a gidan nan ba, zan rik'a share ko ina, mame dan Allah".
Rungumeshi tai tana zubar da hawayen rabuwa da d'anta, wanda yake shine sanyin idaniyanta.
"Aliyu ni wnnn duk baya damuna, ko wanne yaro haka yake, hasali ma ni kullum addu'ah nake maka akan Allah ya shiryaka, nasan kuwa Allah zai amshe addu'ahta"
Gyaran muryan da tajine ya katsie mata zancen da takeyi
"Kai zubairu amso min yaron chan" ya fad'a murya a fusace.
Zubairu dake kusa dasu, yasa hannu yana raba uwa da d'anta.
Zubairu ya amsheshi, hajiya ta juya ta nupie kopan dake fita gidan.
"Mame dan Allah ki dawo kada ki tafie, mame!!!".
Haka ta fice ta barshi a gidan zuciyoyinsu cike da tarin bakin ciki mara misaltuwa...
[7/29, 11:50 AM] Kausar Luv💞: *ALIYU_HAYDAR*
Page ((2))
Ganin baida mafita sea ta Allah, yasa ya cigaba da huci kaman wani sabo zakin daya fito neman abunci, hannun zubairu ya garzawa cizo, wnda hakn yay sanadiyar sakinshi da zubairu da yay, da gudu y haura gidan saman, ya bud'e wani d'aki wnda da alama wannan shine d'akinshi, banka kopar yay ya maida y kulle da padlock ya hau kan d'an karamin gadonshi ya kwanta ya cigaba da kuka.
Alhj baiji dad'in kasantuwar hakan ba, shi kanshi baisan maisa yay hkn ba.
Cike da tak'aicin abunda ya aikata y kama hanyar shiga d'akinshi. Wata mata na hango fara tas da itah, iya inda akeso mace takai to ta kai, sanye cikin dogowan riga bak'a tasa dan k'aramin hijab, da baqaqen takalmi, chewing gum ne a bakinta tana tauna Karas_karas.
Ganin Alhj da tai yasa taja ta tsaya chack kaman gunkin da aka ajiye.
"Alhj ina hajiya salma"?
Shiru yay jim kad'an tukkuna ya nisa
"Na saketa hajjah rabi, kuma nace idan ta samu miji to tayi aure.
Kirji ta daka cike da nuna rashin jin dad'i fal a fuskanta
"Haba Alhj dan Allah, kayi hkuri ka dawo da ita mana mai yay zafi haka shi ba wuta ba"?
A fusace ya bata amsa
"Kinga na gama magana, kuma bana so a k'ara dawomin da ita farko"
Zatayi wata magana ya ra6ata ya wuce, kai ta girgizah tukunna ta qaraso tsakar gidan, ganin jakar Aliyu da tai yasa ta tabbatar da cewan ya dawo dga makaranta.
"Zubairu!!!" Hajjah ta hau kiran sunanshi
Jiki na rawa ya amsa kiran da take masa
"Na'am hajiya gani" ya karaso kusa da ita cikin ladabi.
"Aliyu y dawo dga makaranta ne"?
"Eh hajjjah ya dawo"
"Yana inane"?
"Yana d'akinshi hajiya"
Alama tai masa da hannu wadda ke nuna cewan ya wuce, da sauri y kama hanya y bar falon.
Hajjah rai a 6ace ta hau gidan saman, dai_dai d'akin aliyu taja ta tsaya, a hnkli ta fara kwan_kwasa kopar.
Aliyu daya riga ya hasala ya fara magana
"Wanene"?
"Aliyu nice mamanka ka bud'e kopan nan"
"Nifa ummi bazan bud'e ba sea abbi ya dawo min da mame"
Shiru tai tukkuna ta qara cewan
"Ka bud'e d'ana zan maka komai kake so kana so kasa mamanka kuka ne, kasan idan bana ganinka bana jin dad'i'
Cikin muryar shagwa6a ya bud'e baki
"Ummi zaki hana anty nana ta daken"
"Na maka alkawari bazata kara dukanka a gabana ba kaji aliyuna jan gwarzo zakin fama, ka bud'e dakin".
Tasowa yay ya bud'e dakin, da gudu ya fad'a jikin ummi, ummi ta rungumeshi sosai, a jikinta ya matuqar bata tausayi har a cikin zuciyanta"
"Yi shiru d'ana ka deana kuka, ga umminka nan tare dakai, zan baka dukkan gatan da mame dinka ke baka kaji ko"?
Kai ya d'aga tare da cewan
"To ummina"
Murmushi tai masa taja hannunshi zuwa d'akinta.
Tana isa ta tarar da nana zaune a d'akin, cike da hasala ta taso akanshi
"Ummi ya zaki shigo mana da yaron nan a d'aki sarai kinsan bayajin magana ynxn nan zai fara fasa mana kaya"
"Ke"! Ummi ta daka mata tsawa
"Bana son iskanci da d'iban albarka, ke kinsan da ya nai renonki ne, kowanne yaro haka yake, kurciya ce idan yay ta kuma zata wuce, komai lokacine"
Nana ta dubie aliyu ta dubie ummi
"Naji ummi amma gskya nifa...
"Kefa mi? Bazaki zauna da d'an uwanki lpy bane? Tsaya kiji wallahi nai maki iyaka da yaron nan, fice ki bani guri'
Baki ta tunzure ta kama hanyar fitah dga d'akin, yayinda ummi ta juya ta dubie Aliyu
"Kada ka damu kaji d'ana mamanka na nan tare dakai"
Mujie in baka chocolate"
Murmushi yay ya saki ranshi, suka wuce chan kuryar dakinta
Yayinda Nana tai d'akinta ta maida ta kulle, zuciyanta nai mata k'una sbd ita a duniya ta tsani aliyu, bata sonshi ko kad'an a cikin rayuwanta...
Meye dalilil"?...
®Kausar Luv💞
[11/15, 5:18 PM] Kausar~Luv: *ALIYU_HAYDAR*
Page ((3))
A chan bangaren hajiya salma kuwa tana fitah dga gidan kai tsaye taxi ta tsayar tasa jakarta a ciki.
"Malam mai taxi unguwar shanu zaka kaini"
"To hajiya"
Suka kama hanya sea unguwar shanu, suna isa dea2 kopan gidan da zata shiga ta tsayar da mai taxi di'n ta ciro kudi'nshi naira d'ari ta bashi, ta dauki jakarta, dea2 kopan ta tsaya tana kallonshi, rabonta da gidan tun ranar da aka sata lallen aurenta sea kuma yau datazo, kuma zuwan bana wuni ba na zama gabad'aya, hawayenta ta share tasa kafanta a gidan daya kasance matsakaici tare dayin sallamanta.
Yar dattijowan dake zaune akan kujera ta d'ago idanunta, ganin "yarta da tai yasa ta d'ago ta dubeta
"Salma ina Aliyu"?
Wannan shine tambyan da tafara yimatah
Kuka ta fashe dashi tai zaune dirshan akasa
"Mama alhj ya sakeni, kuma yace "idan nasamu miji inyi aure".
Dattijowan ta girgizah kai
"Bkomai salma Allah yasa haka shine mafi alkhairi, dauki jakarki ki shiga da ita dga ciki"
Hakan ko akayi ta dauki jakarta ta shiga dakin da rabonta dashi shekara goma shaa biyu. Rayuwa kenan.
Karfe takwas na daren wannan rana ta alhamis.
Aliyu ne kwance akan kafafun ummi, yana wasa da d'an super man d'in roba, anty nana ce ta shigo a d'akin ta zauna kusa da ummi.
"Ummi abbi na kira"
Ummi ta tashi zaune ta dubie aliyu duba na soyayya
"Aliyu ka jirani ynxn nan zan dawo, bance kai fad'a da kowa ba, kaji ko?
Kai y girgizah ya cigaba da magana dashi da super man dinshi kaman ynda yake daukan yanayi.
Ummi ta kama hanyar fita d'akin yayinda ya rage dga anty nana sea aliyu.
Kallonshi tai tun daga sama har k'asa ta watsar tasa hannu ta rik'e masa kunne
"Kai dan ubanka waye yace ka shigo d'akin nan"?
Shiru yay, yaja jinin jikinshi sbd tsabar tsoron nana dayakeyi.
"kana jina kayi shiru kasan cewa bana son ina magana ana kyaleni ko"?
Cikin rawar murya ya fara magana
"Anty nana mai nai maiki dan Allah? ynxn fa zaune nake banyi komai ba"
"Taras"! Kaji saukan mari a fuskan aliyu , wnda hakan yay sanadiyyan sakin mutum butumin super man din dake hannunshi ya kwallah k'ara saboda zafin marin dayaji.
Tashi tai ta kalleshi
"Dan ubanka ka sake ka fad'awa ummi sea na maka wnda yafi wannan"
Sheisheikar kuka ya hauyi sbda anty nana ta hanashi kukan, da gudu yay kuryan d'akin ummi kan gadonta ya cigaba da kukanshi
"Mame kina inane, dan Allah kizo plsss"
Haka ya dinga fad'a har bacci yay awon gaba dashi...
Wanene Aliyu?
Wanene Abbi (alhj)?
Wacece Nana?
Wacece mame?
Wacece ummi?
Ya ya alaqar su take a cikin gidan"?
Ku biyoni ni kausar M Hassan dmn jin wannan labari
®Kausar Luv💞
[11/15, 5:19 PM] Kausar~Luv: [7/30, 6:22 PM] Kausar Luv💞: *ALIYU_HAYDAR*
Page ((4))
Aliyu haydar, d'ana ga Alh shuraihu isah shine dea d'anshi namiji a duniya d'aya tamkar da dubu, wnda ya dauki son duniya y d'ora masa, kasancewar, shi d'ayane d'anshi namiji a duniya, aliyu dea farine mai matsakaicin baki, dogon hancinshi ya k'ara masa kyau gashi da d'an jikinshi kadan dea2 misali, shekarunsa bazasu zarce tara zuwa goma ba ynxn haka yana primary 5 ne a matakin karatun zamani, a b'angaren addini kuwa yana karatunshi dea2 gwargwado kaman ynda ya kamata.
Wacece mame?
Ainahin sunanta salma, itace matar alhj, cewa da baban aliyu ta 2, yana sonta sosai, kasancewar itace ya aura bayan ya auri maman nana, aliyu ne kad'ai d'anta a duniyah, hajiya salma mace ce mai addini da son ibada, batada matsala a rayuwanta ko kad'an.
Wacece ummi?
Ainahin sunanta rabi'atu usman, wadda aka fisani da hajjah, itace matar alh shuraihu ta farko, tanada yara 2 tare dashi "Nana asma'u da kuma nafisa, nafisa tana gurin kanwar mamanta mai suna zaliha, a chan take karatu kimanin shekarunta 8 a duniya..
Ummi ta kasance mace mai kamar maza, kasancewar ta uwar gida ga Alhj shuraihu, ta tsaya tsayen daka gurin ganin tai hakuri da komai ke biyowa bayah. Duk da ba ita ta haipie aliyu ba tana matuqar sonshi da gskya, ko kusa bata daukanshi d'an kishiyarta, ta daukeshi tamkar d'anta data haifah...
Wacece Nana?
Nana asma'ah shuraihu isah wannan shine sunanta, kimanin shekarunta 18 a duniyah, idan akuy wanda ta tsana a gidan to bai wuce aliyu ba, sanadiyyar wannan kiyaya kuwa itace tana ganin mahaipinsu Alhj shuraihu y nuna masu banbanci tsakaninsu da d'anshi namiji wato aliyu a ynda take gani, nana fara ce, mai d'an matsakaicin jiki, da manya_manyan idanunta masu kama dana mage, ma shaa Allah nana Allah ya bata kyauwun fuska amma bbu kyauwun hali, tana s.s.3 a matakin karatun zamani..
wannan kenan.
Wanene Alhj shuraihu??
Alhj shuraihu mutum ne mai arziki, yana d'an shekara 25 yay aure, ya auri hajjah, shekarunsu 7 a tare amma Allah bai bata haihuwa ba, bayan wad'an nan shekarun ta haipie yarta ta farko mai suna jamila, bata jima ba Allah yay mata rasuwah, haka ta dinga haihuwa har sau hud'u tana jiro "ya "ya mata suna rasuwa tukkuna Allah y bata nana, bayan ta haipie nana sea da tai shekara 5 bata kara haihuwa ba, byn alhj ya auro hajiya salma ta haipie aliyu, bayan shekara 2 itakuma ta haipie nafisah. Wannan kenan....
[7/30, 6:23 PM] Kausar Luv💞: *ALIYU_HAYDAR*
Page ((5))
Washe garin ranar ta kama juma'ah, bayan ummi ta shiryawa aliyu ta had'a masa kayanshi da lunch box d'inshi gaba da'yah.
"To aliyu sai ka dawo ko"?
Kiss ya manna mata a kumatu
"Bye ummi sea na dawo"
Murmushi unmi tai tukkuna tai masa hannu.
Da gudu ya ruga ya shiga cikin motan, nana ce a gidan baya, shikuma ya bud'e gidan gaba ya shigah, cike da murmushi ya gaidah driver d'in dke kaisu makaranta mai suna musa
"Ina kwana kawu musa"?
Murmushi yay ya amsa da
"Lpy qlw aliyu zakin fama, aliyu ikon Allah"
Harara nana ta aika masa mai rai da lpy
"Kai dallah malam kajamu ka kaimu makaranta ka tsaya kana yima mutane wani surutun banza"
Humm! Y fad'a kawea yaja motan aka bud'e masa gate suka bar gidan zuwa makarantarsu dake nesa da gidan sosai.
Suna isa yay parking suka fita, suka karasa kowanne yay 6angarenshi, kasancewar makarantar su primary and secondary school ne. School d'insu d'aya.
******
Hajiya salma ce zaune a d'aki bayan ta had'a karin komallo taci ta zauna gata ga mama, hajiya salma tayi shiru tana tunanin duniya.
Mama ta kalleta ta dubieta
"Salma dan Allah ki deana tunanin nan, kada ki sawa kanki hawan jini".
Juyawa tai ta dubie mama
"Mama bana tunanin komai a raina face d'ana aliyu, aliyu yana bani tausayi sosai sbd shi kad'ai na haifah, duk da nasan hajjah na kulamin dashi, amma ina tsoron nana, sbd nana batada kirki bata son yaron nan kuma bansan dalili ba"
Mama ta dafa kafad'anta
"Salma kiyi hkuri, kicigaba dayi masa addu'ah, Allah yana amsa addu'ar iyaye musamman ma ta uwa zuwa ga "ya "yanta".
"To mama" ta fad'a jiki a sanyaye..
Karfe 1pm aka tashi su aliyu dga mkrntah, jakarsa ya dauka tare da abokinshi mai suna shafi'u suka kama hanyar fita dga mkrntar, kasancewar ko sun tashi dga makaranta sea ya jira an tashi su nana sea azo a d'aukesu su dawo tare.
Shafi'u shine babban abokin aliyu a makaranta, koda yaushe tare kake ganinsu, abunda ya k'arwa abotarsu amarshi shine shima shafi'u yayarshi ajinsu d'aya da nana kuma k'awartace sosai..
[7/30, 6:23 PM] Kausar Luv💞: *ALIYU_HAYDAR*
Page ((6))
Dea2 bus stop din skul din suka tsaya shida sauran wad'anda ke jira azo a daukesu.
Wasa sukeyi Yar boya, shida shafi'u, su nana suka fitoh, yana ganinta ya natsu abunshi ya daukie jakarshi ya daura a bayanshi.
"Tashi ka wuce"
Sim2 ya tashi y wuce, shida shafi'u, yayinda nana ta zauna itada kawarta siyama yayar shafi'u abokin aliyu.
Bayan sun zauna siyama ta kallie nana
"Haba nana wea mai yasa kika tsani yaron nan dan Allah"?
Nana ta d'ago idanunta ta dubie siyama
"Siyama kisani cewa mahaipina shi yaja komai"
Ta tashi tsaye ta kallie siyama
"Bara in baki labarin abunda yasa na tsani aliyu siyama a rayuwata"
" Abbi d'inmu mutum mai son jama'ah da mutane, gidanmu ya kasance babban gidah, gidan sama ne, d'aku nan dake gidanmu sunyi 10 saboda yawan bakin da ziyartarmu da kuma yan uwah, lokacin da mahaipiyata ta haifeni mahipina ya nuna min soyayya dea2 gwargwado, yana kula dani, hka ummi da kuma mame, bayan wasu shekaru Allah y baiwa mame ciki ta haipie Aliyu.
A lokacin mahaipina ya daukie son duniya ya daura mashi, komai yay baya laipie, sea in nema abu a gurinshi ya hanani ya dauka ya bashi, bazan manta ba tun yanada shekara 8 yake d'aukanshi suna yawo duniyah, yama manta da wata y"a wea ita Nana