x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 1 - SUGAR MUMMIES complete romance hausa novel

  • 1 words
  • 3000 words
  • Out of 16624 words

Category: Romance Story +18

Views 318

18 Aug 2025
Start ads
After Image Ads

An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

[11/22, 16:08] أم افنان✍️💞: *🫧SUGAR MUMMIES🫧*
Na
Hassana Bamalli
(Oum Aphnan)

0️⃣1️⃣

بسم الله الرحمن الرحيم

*SHIMFIƊA*
The worthy successor has emerged,with her gorgeous novel SUGAR MUMMIES .That writer that published d remarkable novel in 2020 under d title JARABABBEN NAMIJI,As beyond d horizon HARIJI in the yr 2021 and AKAN DADIRONA A yr or so later GIDAN DAƊI.we now pay homage to her next novel,simply and omniously titled SUGAR MUMMIES.
There's more than ample evidence that these above works constitutes an important trilogy and must be read as such.
The first 4 Novels have already attracted enthusiastic critical attention ,most of them focusing on BI_SEXUAL relationship i.e different gender .
Now I wanna migrate my consideration in portraying the plight of women in a merciless world dominated by greedy , irresponsible ,lesbianism and under handed harlots by the GRANNIES and BIG MA'AMS and often cruel men in their life.
Kun shirya?? In kun shirya to nima na shirya , Ina ma Fans ɗina fatan Alkhairi da fatan gamawa lpy


•°•••°•••°•••°•••°•••°•••°•••°•••°
_JAPAN_

"knock knock here...Noor ! I'm home kina Ina?" Muryar ta da ya soma karaɗe ƙayataccen falon kenan,a maimakon sallama, daidai sanda ake turo ƙofar shigowa.

Wata ƴar gayun mace ce ,Fara tar mai yankakken hanci ma'abociyar dulu²n idanuwa ,duguwa shal har taso yin doro siririyace ƙwarai kamar a karya,Amma kallon farko zaka sakata sahun classy mata masu ji da gayu,Hutu ,aji da kuma uwa uba Kuɗi.

Zame _Sun shade_ ɗin fuskar ta tayi a hankali sannan ta ɗan hure iskar bakinta tana sauke siririn veil ɗin wuyanta ta haɗe su ta riƙe da ƴar ficilin jakan hannunta .

Ta waiga tana ƙarewa matsakaicin living room ɗin kallo ,ko'ina ƙal ƙal sai ƙamshin turaren ɗaki yakeyi.
Gyara zaman labulen da ta yaye tayi a jikin ƙarfensa

Sannan cikin yanga da takun isasun matan da ya zame mata jiki, ta cigaba da takawa cikin falon

"Wa'aaah cooking... cooking...cooking nice
Noor! ,wani daɗin kike mana ne ƙamshi zai cika mana ciki tun ynz?"


Ta wani ƙofa da yike jikin falon ya fito saye da 3qtr ɗin wando da T_shirt brown a jikinsa...Cikin sanɗa ya Saɗaɗo ta bayanta ba tare da ta sani ba kawai taji anyi sama da ita .
Ƙara ta fasa ,shikuma saurin saita kunnenta yayi ya hura mata iska ,ai da sauri ta fara wushirshire da ƙafarta a iska,Bai ƙyaleta ba sai ma riƙe ta dam da yayi ya raɗa mata a kunne"Noor ko? Kin fi son Noor akan Ahmed ko?"

Ƙyalƙyacewa da dariya ta cigaba dayi ,a hankali ya direta ta juya ta kama gefen kuncinsa tana shafa kyakyawar gashin gemunsa "Wait You scared me fa😌😃 amma me kake yi a gida,ba na Barka zaka tafi aiki ba?" Ta ƙare tana tsatsaresa da ido tana nunasa da yatsa

Washe mata duk haƙoransa yayi "Girki"
Zaro ido tayi cikin mamaki ,saidai kafin ta samu zarafin magana ,ya maza ya saka mata yatsa a saman laɓɓanta "Shissshh 🤫to Touprise You durling kuma hakan ne ta faru"

"Oh my God , doubt still me yasa girki ,meye amfanin noor"
Share tambayarta yayi ,ta hanyar juyar da tunaninta da sumba (kiss) kissing ɗin ta yake,takoina tun daga wuyarta ,saman ƙirjita har goshinta ,yina mata ƴan sambatu "Nayi kewarki sosai, my one ,I missed you umuhhh💋ummuhh💋" ya cigaba da kissing ɗinta
Rungumesa tayi tana dariya sosai da sosai ,kanta na kafaɗarsa tace "I miss you more my love"

Ɗan cikashi tayi tana kallonsa "Auchhh I'm so empty without youuuu😌" tayi magana kamar zatayi kuka,tana shafa gefen sajen fuskarsa

Tsare ta da ido yayi eye ball into eye ball,sannan ya tambayeta da "Really?"
Gyaɗa masa kai tayi "Ehem"
"To shikenan yanzu dai je kiyi wanka,ki canja wannan dirty kayan ,sai inzo in kula da matata da kyau ko?"

Kafin ta bashi amsa ,wata matashiyar budurwa ta shigo living room ɗin saye cikin wata ƙatuwar rigar sanyi har gwuiwa da streght skirt, ta rufe kanta da wata ƙatuwar hular sanyi .
Kyakyawa ce zubin ƙarshe fara ce amma ba tar ba, komai nata matsakaicine tun daga kan tsayinta ,bakinta ,idanuwarta komai nata ya saje da zubin halittarta abu ɗaya ne yayi mata yawa mazaunai ,gasunan a baje kamar zasu rabu da jikinta .

Tunda ta shigo falon sukayi tsit kamar mutuwa ta gifta ,Shikam Ahmad ƙyam ya tsaida idonsa a kanta yinason ganin réaction ɗin ta.

Kallo ɗaya ta masa ta fakaici idon Fauza ta banka masa harara ,da sauri ya sunkuyar da kansa ƙasa

Muryarta a dushe tace " Sannu da zuwa Anty yau kin dawo da wuri"

Lafewa tayi a jikin mijinta ,tana shafa masa baya "Eh wallahi ,shine kikabar love da girkin gida ko? Me kikeyi ke ? Kinacan ɗaki a ƙunƙume kina kukan nan mara amfani ko? Wai me nake maki ne noor da har yau kinƙi sakin jiki dani?"

Duk yanda taso daurewa hakan bai samu ba saida ta fashe da kuka ,muryarta na rawa tace "I'm sorry aunty zan gyara "

"Zaki gyara amma kike kuka?...hey Mr Man kaji da ita Plz wallahi banda strength ɗin rarrashi I'm completely tired,Ka bata baki ƙila zatafi jin naka"

Tana rufe baki ta juya zata wuce .Janyota yayi ya sake rungumeta ta baya ya haɗe hannuwarsa a ƙasan maranta

"No, bana so ki tafi "

"No plz na gaji let me go and freshing up first"

Kautar da fuska Noor tayi ita ba abun ta tafi ba ace ta gwada baƙin hali ,dole ta jira su gama iskancin su da tsotse tsotsen bakin.

Sa haƙoransa yayi ya cija ƙasan lilin kunnenta a hankali "I'm lucky to have you my wife"

"Yes you are. Amma yanzu ka soma gamawa da assignment ɗin da na baka tukunna"


Da sauri ta ƙwace hannunsa daga jikinta ta wuce sauri² don kar ya sake damƙota

Ɗaga murya yayi da ƙarfi

"I love You"

"Me too"

Saida ya tabbatar ta wuce bayan ya ɗan miƙa wuya yagama leƙen hanyar da ta bi ya tabbatar ta wucen sannan ya dawo kan Noor da ta hade hannuwarta a ƙirji ,basai an tambayi ɓacin rai ba a wannan wajen.

Washe baki yayi , cikin Muryar raɗa yace "Tona mana asiri da zakiyi Nuratu a gabanta?"

Kallonsa tayi ta huro hanci tana hararansa

"Aaha gyara zancen ka. Kace tona maka asiri nike son yi? Don dai Ni mai gaskiya ce banda abun ɓoyo dazanji tsoron a sani..."

Yin mata alama yayi da hannu ,ma'ana ta rage sautinta kar a jiyo su

"Yanzu me kike so? Ki fadi mun ko me kike so wallahi zan maki amma ki Barni in mori kiwon da nayi a wajen nan,Nuratu kin ginu kin batse kin cika kin tara ruwa ,har zullumin barci nake don da na kwanta barci mafarki na nike tare dake a wani dausayi mai ni'ima...."

"Subhanallh ,kaico! Anya da ɓurɓushin imani a ranka kuwa? Zama cikin turawa yasa ka manta zaka mutu! To in ka manta matsayina a wajenka ne bari in tuna maka _Ƴar Amana_ in kuma zakaci amanar iyayena ne to bissmillah"

"Yes nasan da hakan amma nima ki tausaya mun sha'awar ki kullum ƙara hauhawa take a cikin jinina ,sau ɗaya rak! Ɗaya tal zamuyi daga nan bazan sake kulaki ba"

Siririn tsaki taja ,kawai sai ta juya ,ta fara tafiya da zafinta ,tanajin inda za'a barta da Ahmad zata iya kashesa.

Shi yanda ɗuwawunkata ke juyi ma wani nishadi yake sashi
Tana tafe ɗuwawukanta suna jujjuyawa sama da kasa

Pointing ɗin Ass ɗinta ya ringayi da duk manunan yatsun sa biyu(Index fingers) ya na karkaɗa yatsun sama da ƙasa kamar yanda Mazaunanta ke juyawa , yana rera ma mazaunan waƙa "sittin saba'in...sittin saba'in ...sittin saba'in"


Kasa daurewa tayi kawai sai ta tsage da ihu ta falla ɗaki da gudu tana diddirke ƙafafuwa

Fauza ta ɗaura towel kenan ,zata shiga wanka ta fyallo da gudu jin kukan Nuratu

"Love bance ka duketa ba fa ,Nasiha nace kawai"

Sosa ƙeya yayi na ƴan bariki "Ke kike ƙara sangarta yarinyar nan shikenan na tsame hannuna a kanta kuje can ku ƙarata"

Ƙanƙance ido tayi gamida riƙe kwankwaso "Kenan dukanta kayi?"

Shiru yayi yina lalubo amsar da zai bata

"Love dukanta kayi?! Haba wai meyasa har yanzu baka gane cewa Noor yanzu ta zama budurwa ne,kana maltreating dinta kamar small kid ?"

"Banfa duketa ba daga fada sai ta fashe mun da kuka "

"Zagin ta kayi kenan badly."

Zuwa yayi ya kamo shafaffen ƙugunta "Is alright muje in tayaki wankan"

Ture masa hannu tayi "Girkin fa wa zai ƙarasa?"

Sosa ƙeya yayi ,ya wuce kichen da sauri

•°•°°•°•°•°°•°•°°•°•°•°°•°•°•°°•

2.30pm
Bakajin motsin komai sai cokula da suke ƙara akan dishes en,sai lokaci bayan lokaci kaji ƙarar drink ana tsiyayawa a cikin glass cup .
Babu mai magana a tsakanin su ukun kowa abincinsa kawai yikeci.

Gyaran Muryar Fauza shi ya tsinke shirun kana ta soma magana

"Love kasan menene?" Ajiye fork din Hannunsa yayi akan empty plate ,sannan ya haɗe hannunta guri guda yina kallonta "Ehem ya akayi uwargidata,ban sani ba sai kin faɗa"

"Kasan wasan ƙwallon nan yayi zafi kuwa? Jibi za'a buga wasa tsakanin real madrid da Arsenal "

"Oh wow kice jibi ba zuwa aiki zamu zauna kallon ƙwallo"

Turo baki tayi "Haba love Ni fa can England ɗin da zasu buga wasan zanje ayi komai a gabana ,I can't wait inga yanda real zata yi wa Arsenal biji² Kaga gida da waje kenan."

Nuratu tana ɗebo abinci a spoon ta tsayar ta kasa zubashi a baki ,wannan wani irin baalain Son Kallon ƙwallone Allah ya jarrabi Fauza dashi? Ya wuce kalla a gida da sukeyi wata zubin su fita dashi su je kallon ƙwallon a gidajen kallon ƙwallon na kuɗi ,A'a yanzu binsu har ƙasar su zatayi? To bari muga sallamammen zai hanata ne ko kuwa zai barta ta tafi ?...

Yanke tunanin Nuratu Ahmed ɗin yayi da cewa "Thats great! Allah ya kiyaye hanya yaushe zaki tafi kuma kwana nawa zakiyi?"

"Gobe zan tafi ,mijin Ajoke ƙawata ma ya yankan mana ticket kasan acan yike ,to kodai menene bazan wuce 5_7 days ba"

A sanyaye Nuratu ta watsa abincin a bakinta daƙyar ta tauna ta hadiye,ba abunda ya shafesa sai hiransu ma suka cigaba dayi tana sake bashi labarin yanda players din suke sarrafa ƙwallo a field.

Jan kujera Nuratu tayi ta mike "Ya dai Noor kardai kin fara missing ɗina ai bazan dade ba"

"Hum " kawai tace ta wuce daki tana tunanin yanda za'a barta gida ɗaya da wannan kwarton mijin nata .

Washekari

Da sassafe ya kaita filin jirgi ,suka rankaya birnin London ita da ƙawarta Ajoke
Saida yaga tashin jirginsu sannan ya biya mini mall ya jibgo ma Noor siyayyar kayan ƙwalam ya taho gida



_...Ga ɓarawo ga mai kaya_
_Ga Noor ga Ahmed😋 Gida su kaɗai ƙara ƙaƙa ƙaƙa_






#Comment
#Share
#Thank you
#Bamalli's care🥰
09065990265
[11/23, 14:36] أم افنان✍️💞: *🫧SUGAR MUMMIES🫧*

Na
Oum Aphnan
2️⃣


_Look For the hidden asset/opportunity_
#Ahmad
#Noor
#3 Super ma'ams


Nuratu kam tunda Auntynta Fauza ta fita gidan ,ta shige ɗaki ta rufe kanta a ciki ,zama tayi ta zuba tagumi ta rasa ma tunanin me zatayi ne? Kaɗaicin da take ciki ko kuwa zullumin zamanta gida ɗaya daga ita sai Ahmed da ya kasance ƙwallon ɗan iska !..Anya bazan gudu ba in koma Nigeria ba?

Wasu zafafan hawaye ne suka surnano mata a ido ,take ta soma girgiza kai tana rarrashin kanta da kanta ta hanyar sambatun da batasan ma tanayi ba

_Allah sarki Nuratu baiwar Allah ,in kin koma Nigeria wajen wa zakije ? Ai basa sonki suma gudunki sukeyi ,kawai kuɗinki da kike turo masu daga nan suke so ,suna facaka dashi suna yinma ƴan ƙauye gadara da arzikin da kike tura masu. ,amma duk cikansu babu mai son kuyi inuwa guda bare a kirasa da makusantanki ,ke ɗin karuwace kuma karuwanci kikeyi a Japan ,Me yayi saura?...ALLAH YA ISA NA INNA ABU_

Kuka tayi mai Isarta saida ta gaji don kanta ,ta rarrashi kanta ta mike taje ta ɗaurayo fuskarta ,ta sauya kayan jikinta zuwa wata gown me yalwa har ƙasa mai ruwan jinin kare(maroon) sai sheƙin duwatsu sukeyi kai ba sai an tambayi tsadar su ba ,ta ɗauki kallabinsa ta naɗe fuskarta dashi ta fito sak kamar ƴar Morocco ɗin nan.

_Study room_ ɗin gidan ta shiga ta zauna a kan _Table_ ɗin kayan karatunta ta janyo wani littafi _The rules of wealth na Richard templar_ Ta ɓallo fejin da ta tsaya a hankali ta maƙala fari tar ɗin glasses ɗin karatun ta ta fara duddubawa tana bin turancin a nutse tana _Digesting_ saƙon da ke ciki

Ahmad da _Spare key_ ɗinsa yayi amfani wajen buɗe ƙofar apartment ɗinsu ,har ya gama shiga da kayan baiji motsinta ba ,ɗakinta ya shiga a wangale yake bata bar komai ba sai ƙamshinta ,tuni hankalinsa yaji ya ƙara tashi ,yanda yaga wajen neat abin ya burgesa ,bazai taɓa tuna yaushene yaga gadonsa a gyare haka tsaf² ba ,wato,ita dai Fauza daidai da gyaran gado bata iya ba saidai Ahmad in datti ya ishesa ya karkaɗe ko ya sauya wani

Don haka yau ɗaya da ya sama damar shigowa ɗakin Nuratu ya ƙare masa kallo sai ya gane lallai ya shigo ɗakin mace ba Ballagazaba.

Girgiza kai yayi kawai ya wuce kicin ko tana can nan ma wayam,turus yayi wani zuciyar yana raya masa kardai yarinyar nan guduwa tayi?

Jimmm ya ɗanyi cikin tunani kafin ya wuce ɗakin karatunsu da sauri

Buɗe ƙofar yayi ya raba biyu da hannunsa yina kallonta,wani sassanyar ajiyar zuciyane ta ƙwace masa komai nata mai kyau ne ,daidai da zamanta irin na manyan mata ne ,Mazaunanta sun gama bajewa sun zauna dandaɓasɓas akan kujeran da take kai

Gyaran murya yayi "Ƴar amanata "wani sanyi taji a ranta ,wani wawiyar ajiyar zuciya ta saki tanajin kamar an ɗebe mata kaso casain na damuwar da take ciki ,bata mantawa sunan da yake kiranta dashi kenan ,duk in yaso rarrashinta ,A lokacin da yike mutunin kirki in ya ganta tana kuka a ƙarƙashin bishiyoyin gonakin ƙauyansu,sanda yake bautar ƙasa a makarantansu.

A sanyaye ta ɗago ta watsa masa lumsassun idonta

"Me kikeyi ke ɗaya "
"Karatu!"

"Ba kunyi jarabawa ba ,karatun me kuma ,inga littafin?"

Ya ƙarasa shigowa ɗakin ya karɓi littafin hannunta ,ya juya ya karanta sunan littafin ,basai sanda ya tuntsure da dariya ba

"Topah me zakiyi da littafin nan kuma? "

"Inaso Inyi kuɗine"

"Me yasa na gaza da yi maki hidimar da ya dace ne ehem ,fada mun me kike so wanda ba na maki? Ko aikin da Fauza take sakine bakiso a daina...ehem ki fada mun kinji Nuratu na"
Muryarsa a take ya sauya gabaɗaya ya rude kamar wanda ake tuhumarsa da wani gagarumin laifi

Hawayene ya fara gangaro mata a fuska "Yaya Ahmad A'ah ,kayi mun komai a duniyar nan,wanda iyaye na ma suka sake yimun ka cika mun burina ka baro Ni da rayuwar ƙauye rayuwar ƙunci ,da ina kwana a ƙasan taburman kaba ,yau gani a gadon laushi a raɓan AC ,ada ina ganin yara a ajujuwa suna ɗaukan darasi suna bani sha'awa ,kwatsam sai ka tsamo rayuwata ka sani a makaranta mai kyau ba a ƙasata ba ,ka zaɓar mun kwas ɗin da nike mafarkin inga na zama wato ƴar jarida ,nikam bazan zama yarinya mai yawan godiya ba ,in kullum ƙasan ƙafarku nike sharewa bazan taɓa biyan ku abunda kukayi mun ba saidai Allah ya biyaku..."

Sa hannu yayi ya rufe mata baki "Ya isheni ,zan maki tambaya na ƙarshe in baki bani amsa ba nayi alƙawarin bazan sake tambayarki ba...me yasa kike yawan kuka? Kuma mai yasa kike sa kike karanta wannan littafin har kike cemun kudi kike so kiyi?"

Lumshe Ido tayi ta ɗan yi jim na wani lokaci "
End Ads