Safiya kirjinta ne ke dukan uku uku don tasan dole mummyn ta zata yi amfani da agogon, cikin sanyin murya Tace "Mummy Ina Zaki je?"
"Gun aiki ana nema na urgently"
"Ha'aah I thought ba Kya zuwa ranar juma'a?"
"Eh ta kamane,Bari naje na shirya" ta shafa Kan safiya said ta haura sama cikin sauri.
Safiya ta kalli asiya tace "yau kashi na ya bushe"
"Kar ki damu ki ci abinci"
Bayan sun gama ci suka koma d'akin Asiyah.
B'angaren Baraka ta gama Shirin tsaf ta d'auko a gogon Nan zata sa sai ta ga bayayi a fili Tace "Me kuma ya faru da agogon Nan"
Rai a 'bace ta Fara Kiran sunan "Asiyah, Safiya ina yaran Nan suke?idan na biye musu zasu haukatani"
Cikin zafin nama ta Shiga d'akin a Tsawace Tace "acikin ku Wace ce ta tab'a min agogona"
Safiya tayi saurin cewa "Nice "
Asiyah Tace "Safiya ki daina karb'an laifin da ba naki ba mummy nice"
Wata mahaukaciyar mari tayi wa Asiyah had'e da fad'in sau nawa nake ce Miki ki daina kirana da mummy Ni ban haifi mayya ba" Asiyah Marin da ta Mata ya gigita ta har sai da ta Fad'i a Kan gado, Baraka ganin hakan ta hau Ruwan cikin ta sai aikin dukan ta take, Safiya Kuma na kokarin riko ta.
Sai da ta yi Mai isarta ta fice daga d'akin, tana fita ta d'auko makullin mota, Mai gadi na gani a zaune hannun sa rike da wayar sa Yana kallon film Wanda na kasa gane wane iri ne lashe la'b'ban sa yake had'e da rike wandon sa sai lumshe Ido t
Yake.
Baraka Tace "Audu d'ako min jakar Nan da ake sa petir Kuma ka bud'e min gate" sai ta shige mota ganin bai taso ba hakan yasa tazo ta bayan sa ta leka Ashe film d'in basa yake kallon kad'a Kai tayi had'e da ciza Baki wata muguwar rankwashi ta Masa yayi saurin mikewa had'e da tare gaban sa, Tace "Wawa soko a Haka zaka Kare kana kallon blue film, jibi yanda Wando ka ya jike, da wata akwalar chaina phone ka d'ako jarkan Nan kasa min a mota"
Sai hakuri yake ta Bata,yayi saurin d'auko jarkan yasa a bayan mortar sannan ya Koma ya bud'e gate d'in,saita fice.
Safiya kuka take sosai tana bawa Asiyah hakuri Amma Asiyah ta nuna Mata hakan ba komai bace.
Audu na gani da Altine a Kan gado Yana zaune daga shi sai gajeren Wando ita Kuma zani kawaii ta d'aura a kirjinta Jin nayi tace "Yau ta bazan baka ba, sabida ban yarda da Kai ba nasan ba Sona kake ba"
Langwab'e Kai yayi yace "Kar kimin haka wallahi ina sonki"
'daga kafad'a tayi Tace "ita Kuma Mai ayabar Nan da kullum sai tazo gunka in fatan ba sonta kake ba?"
"Haba my altine,Ina dake me zanyi da wata mai ayaba? Ni ke nake so ba ita ba"
"Ka tabbata Ni kake so?"
"Eh wallahi da gaske nake"
"Toh in dai hakan ne kamin Abu d'aya"
"Mene ne ki fad'i komai Ni Mai yi mikene"
Murmushi tayi Tace "Maruka biyu kawaii zan maka in ka jure Shikenan"
Zaro Ido yayi yace "Mari kawai?"
Ta amsa da "Eh"
Yace "Ta kwana gidan sauki" gyara Zama yayi had'e da juya Mata kumatun sa wata jahilar Mari ta masa.
Jinayi yayi ihu, ya bud'e idon sa ganin Altine a tsaye a kansa ya bud'e idon sa da kyau, hannu a kwankwason ta tana girgiza kafa Tace "Audu mafarki kake ko? Kuma Wace Shegiyar kake cewa I love you?" Rai a b'ace.
Tashi yayi ya tsaya yace "Wallahi kece,ban Sona tashi ba kin ganki kuwa a mafarkin Nan u look so viciously sexy"
Hannu ta d'aga Masa Tace "Me Kuma Vivi....kaga Ni Kar ka zageni don bana Jin turanci"
"A'a cewa nayi kinyi kyau sosai, ai yallao Naji yake fad'awa hajiya hakan kamun ya rasu"
"Kai kasan da Wannan,Dama abin ci na kawo maka, na shige Ciki"
Tsuman tsaye yayi ganin yanda take tafiya bayan ta ya na kad'awa dake altine na da mazaunai manya manya, hakan ya tafi da imanin sa.
Bayan ta gama abinda taje yi a office ta biya gidan Kawarta Nana.
"Nana Gaskiya na gaji da abinda yarinyar Nan take min"
Nana Tace "Anya ba mugunta bace kuwa? In ko ba mugunta bace tabbas tana da bakin aljanu, nasha fad'a Miki ki kasheta kawai ki huta"
"Zan kashe ta Amma ba yanzu ba sai na gana Mata azaba"
"Da dai yafi Miki Kam"
A Haka sukayi ta hirar su ta duniya sai dare liss ta koma gida.
💦💦💦💦💦💦💦💦💦💦💦
Kuyi hakuri fans ina kallon Comments d'inku Amma bani da lokacin reply,nagode sosai Kuma Ina Jin dadin kaunar da kuke yi wa littafin Nan ina muku son so fisabillah.
Mu had'u a page na gaba
Milhaat ce
Yar Terawa
💦💦 *MATAR UBA* 💦💦
_(A True Life Story)_
*Short story*
```Story and written by FADEELAH YAKUB (MILHAAT)```
Follow me on Wattpad @Milhaat
Join my group on Telegram https://t.me/joinchat/IhnmqM7EjtZ02IV0
🌎 *MANAZARTA WRITERS ASSOCATION*📚🖊️
_'kungiya d'aya tamkar da dubu_
https://www.facebook.com/107980080946102?referer=whatsa
_____________________________
*MATAR UBA* Labarine Wanda ya faru dagaske banyi shi don cin zarafin kowa ba face don nayiwa Yan Uwa Mata nasiha,Allah ya bani ikon gama shi lafiya kamar yanda na Fara lafiya ameen.
Dedicated to *MUHAMMAD KARIM MK* Much Love.
*BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM*
Not Edited
CHAPTER 7
💦💦💦💦💦💦💦💦💦💦💦
..............Haka Rayuwa ta kasance wa Asiyah kullum cikin duka take, wasu lokutan Baraka na Jin tausayin amma Kuma Nana ke Kara hura wa abin wuta, safiya na matukar Kaunar Yar uwar ta, Baraka na Jin haushin hakan, hakan yasa kudiri aniyar raba su ko ta halin Kaka.
Da Murmushi ta ke saukowa daga steps tafiya take cike da takama da izza, ta nemi gu ta zauna a Kan wata doguwar sofa dake parlon, gyara murya tayi Kan ta Fara Kiran sunan altine.
Cikin sauri ta fito daga kitchen hannun ta d'auke da plate Hannun ta duk kumfa da alama wanka wanke take.
Wani irin kallo Baraka ta Mata sannan tace "Je ki wanko hannunki ki dawo Nan, cikin sauri ta Shiga kitchen d'in ba dad'ewa ta dawo, cikin girmamawa Tace "Hajiya gani na dawo"
Wasu makudan kud'i ta cire daga cikin purse d'inta Zaki Kai kimanin dubu d'ari uku, mikawa altine tayi had'e da fad'in "Ga Wannan dubu d'ari uku ne na baki su ki je ki nemi jari ki tattara tsumma karanki ki bar min gida"
Cikin rashin fahimta da fargaba altine Tace "Hajiya Dan Allah kiyi hakuri Ina son aiki na, Yan kauyen mu duka sun San Ina aiki Kuma suna alfahari dani Dan Al....."
Hannu ta d'aga Maya had'e da fad'in "Bana bukatar jin komai daga gare ki,sannan babu abinda Kika min Haka kawai naji bana bukatar aiki kin gane ko?"
Cikin Rawar murya Tace "Hajiya Amma...."
"Altine idan Kika sake furta wata kalma anan zan kwace kud'in Nan Kuma na koreki kin fahimta?" A tsawace Baraka ke Maganar Nan.
Jiki ba Karfi altine ta fice daga parlon, Nan Baraka ta shiga Kiran Asiyah da safiya, da Sallama suka shigo sannan suka gaida ta cikin girmamawa ta amsa ta wani irin murmushin da yasa hankalin su ya kasa kwanciya, Baraka sabida kullum fuskar ta a tamke take idan kaga tan Murmushi tabbas akwai abinda take shiryawa ne.
Gyara Zama tayi had'e da gyara murya wata bakar leda ta d'auko dake gefen ta tun d'azu Maida kallon ta tayi ga Asiyah tace "gashi" had'e da Mika Mata ledar jiki ba Karfi ta mike ta karb'a.
Baraka ganin Asiyah bata bud'e ledar ba ta tsaya kallon ta Tace "Ki bud'e Mana" jiki na rawa ta bud'e,ga mamakin ta, Uniform ta gani da sandals har da safa irin na safiya, Baraka Tace "Zaki Koma makarant"
Yar karamar dariya Asiyah tayi tace "Nagode Mummy"
Baraka jin ta ambaci kalamar mummy ta tamke fuskar ta had'e da fad'in "Ke don uwar ki sau nawa na fad'a Miki Ni ba mummyn ki bace ki daina kirana da mummy"
Kai a kasa cikin sanyin murya Tace "Am sorry"
"Sorry for yourself, kina jina?"
Kai Asiyah ta girgiza alamun eh ba tare da ta kalli Baraka ba, tana kokarin b'oye hawayen da ke kokarin saukowa da ga fuskar ta.
Baraka Tace "Zaki Fara zuwa makaranta ba don komai ba sai don alkawarin da nayiwa Mahaifin ki, a lokacin da yake kwance a asibiti"
Safiya cikin Zuciyar Tace "Iko sai Allah yau kimanin shekaru shida Kenan da rasuwar Daddy Amma take cewa alkawarin sa, wani aji zata kaini yanzu dai na fi karfin primary sabida na girma, sai lokaci lokaci take Bari na je makarantar ko Kuma sai ta dai daici za a Fara exam sai ta hanani,Ya rabb gani gare ka, kayi saurin kawo min karshen wannan abun na gaji"
"Kuma ki sani aikin gidan Nan kece Wacce Zaki Rika yi Kama daga kan shara wanke wanke, ko da yake kin San komai ai na sai na fad'a Miki ba"
Safiya cikin kuka Tace "Haba mummy me yasa kike Haka ne aunty Asiyah 'yace kamar kowa"
A tsawace Tace " Safiya ban hanaki idan ina magana da mayyar Nan ki daina samin baki ba, ko da yake ba laifin ki bane nasan Shegiyar Yarinyar Nan tsinanniyace ta ke hura Miki kunne Amma ba komai, komai yazo karshe da yardan Allah, tashi ku wuce kuci abinci ko Wacce ta d'auki food flask d'in ta."
A hankali suke tafiyar kamar tura su ake har suka Isa dinning table d'in bayan sun gama cin abinci ko Wacce ta Koma d'akin ta dake bayan sallar Isha ne.
*WASHE GARI*
Asiyah na murna zata Fara zuwa school duk ta tasan a barta a baya Kuma uniform d'in ya d'an ban ban ta dana safiya da alama senior class zata, bayan ta idar da sallah ta Fara gyare gyaran gidan Kan gari ya waye ta gama sai kamshi gidan yake, ta Koma kitchen ta had'a Breakfast sannan ta jera a dinning table Koma d'akin ta tayi wanka had'e da sanya uniform a jikin ta.
Bayan ta sauko ta Samu Baraka da mummy na cin abinci da Sallama ta karasa inda suke cikin girmamawa ta gaishe ta, kallon ta kawai tayi ta cigaba da cin Abincin ta, ganin bata kulata ba hakan yasa ta ajiye Jakarta ta jaa kujera ta zauna,kallon safiya tayi Wacce kanta KE kasa abincin ta take ci hankalin ta a kwance, Murmushi Asiyah tayi Tace "Safiya yau ba magana ne?"
Shiru bata d'aga kanta ba bare ta amsa, tambayar ta sake maimaita a karo na biyu, a tsawace Baraka Tace "Ke bana son hauka idan baza kici abincin ba ki tashi ki fita"
Shiru Asiyah tayi ta Fara cin Abincin cin abincin take Amma Bata Jin d'adin ta, shayi kawaii ta Sha sai ta fita, ta Shiga motar da mummy Tace dashi za'a Rika kaisu makaranta driver na zaune a gaban motar ta gaishe ya amsa yace "in d'ayar?"
"Tana fitowa" rufe bakinta ke da wuya sai ta hango Baraka da Safiya hannun su a cikin na juna, Baraka da kanta ta bud'e Mata motar, safiya na Zama ta fita da sauri toshe hancin ta tayi had'e da fad'in "Ni gaskiya mummy bazan iya xama da ita ba"
Murmushin gefen baki Baraka tayi sannan lokaci guda kamar ba ita tayi ba Tace "Kamar baza ki iya ba?"
"Mummy wallahi warin Kashi take Ni dai gaskiya ta fita ko a raba Mana motar" ta karasa Maganar cikin kuka had'e bubbuga kafarta.
Asiyah baki a bud'e take kallon su cikin mamaki na Jin abinda kunnuwan ta ke ji Kuma idanuwan ta ke gani.
"Kwantar da hankalinki kinji yanda kikeso Haka za'a yi"
Sai ta Maida kallonta ga Asiyah a tsawace Tace "Ke mayya fito nan" a tsorace Asiyah ta fito ganin irin tsawar da mata.
Driver Baki ya bud'e ya tsaya Yana kallon ikon Allah, Baraka Tace "Sai ki san inda dare ya Miki maza ki Kama hanya ki tafi makaranta, tunda safiya Bata son had'a hanya dake.
Murmushin takaici tayi sannan ta nufi gate d'in ta San Kai ta fice.
Safiya ta Shiga motar, shi kuwa ya tada motar Audu ya bud'e Masa gate ya fita.
Tafiyar almost one hour ne tsakanin makaranta da gidan su a mota, in da kafa ne zai Kai more than two hours, a gajiye ta Isa makarantar tana Isa gate ta samu ana dukan latti, bata tsoron bulala sabida duka ya Zama Mata tamkar man shafawane, bulala goma aka Mata ganin yanda safan ta sukayi datti sai ta shige class, dayawa daga cikin ajinsu sunji d'adin ganin ta musamman shamsiyya har sai da ta rungume ta, Asiyah ganin shamsiyya sai taji kamar an wanke mata dukkanin damuwar dake damin ta, sai karfe biyu suka tashi.
Bayan ta fita sai faman neman Safiya take har sai da ta Shiga class d'in su, wat ce Tace Mata "Ai yanzun Nan driver ya fita da ita"
Kirkiran Murmushi tayi Tace "Nagode"
Sai ta fice daga makarantar, ta d'anyi nisa sai Taji ana Kiran sunan ta ganin Wacce ke kiranta ne yasa ta saki Murmushi.
"Asiyah ina driver d'inku?"
"Kinga sun gaji jirana ne suka tafi"
"Kamarya sun gaji yanzu fa a ka tashe mu?"
Murmushi kawaii ta Mata Tace "Zo mu rage Miki hanya to"
Asiyah dake dama duk kafafun nata zafi suke mata Bata Musa ba tayi saurin bin bayanta tare suka shige motar.
Suna Hira har suka Kai inda zasu rabu,Amma zatayi tafiya kusan na mintuna talatin Kan ta Isa gida godiya tayi was shamsiyya Kan ta fita.
Tana Isa gida Kai tsaye palor ta nufa ta Samu safiya da mummy nacin abinci ta Karasa gun Tace "safiya shine kuka tafi Kuka barni?
Safiya kallon ta kawai tayi tana yagar Naman dake hannun ta, Baraka Tace "Ke don uwarki Baki iya gaisuwa ba?"
Murya na rawa Tace "Ina wuni"
Muguwar harara ta wurga Mata sannan tace "dame Kika dawo?"
"Da kafa"
"Karya kike Munafuka daga makarantar nakune zakice min da kafa ai da baki iso ba har yanzu"
"Wallahi mummy da kafa na dawo"
"Ni Zaki dubi tsabar idona kimin karya,ok wato Saurayin kine ya dawo dake ko?"
Murya na rawa Tace "A' a wallahi mummy ba Haka bane"
Asiyah batayi aune ba sai saukar Mari da taji Baraka tayi Mata, "bance ki daina kirana da mummy ba, Munafuka, tashi ki bani waje ki Shiga kitchen akwai garin kwake a bakar leda ki jika Kisha Kuma Kar ki yarda ki tab'a min sugar kinji na gaya miki."
Mahaukaciyar Mari ta Mata hakan yasa ta buge goshin ta Alan tiles na gun sai jini take zubarwa Amma ko a jikinta.
💦💦💦💦💦💦💦💦💦💦💦
Ina ganin Comments d'inku Kuma Ina Jin d'adin
Allah ya bar kauna.
Comments and share
MILHAAT CE
YAR TERAWA
💦💦 *MATAR UBA* 💦💦
_(A True Life Story)_
*Short story*
```Story and written by FADEELAH YAKUB (MILHAAT)```
Follow me on Wattpad @Milhaat
Join my group on Telegram https://t.me/joinchat/IhnmqM7EjtZ02IV0
🌎 *MANAZARTA WRITERS ASSOCATION*📚🖊️
_'kungiya d'aya tamkar da dubu_
https://www.facebook.com/107980080946102?referer=whatsa
_____________________________
*MATAR UBA* Labarine Wanda ya faru dagaske banyi shi don cin zarafin kowa ba face don nayiwa Yan Uwa Mata nasiha,Allah ya bani ikon gama shi lafiya kamar yanda na Fara lafiya ameen.
Dedicated to *MUHAMMAD KARIM MK* Much Love.
*BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM*
Not Edited
CHAPTER 8
💦💦💦💦💦💦💦💦💦💦💦
........... Asiyah jiki ba Karfi ta tashi ta mike ta haura bedroom d'inta, a galabaice ta Shiga bathroom ta Watsa ruwa had'i da alwala, tana fitowa ta shafa Mai sannan ta d'auko doguwar Riga da doguwar Hijab d'in da take sallah ta zurma sannan ta tada sallah bayan ta idar ta jero addu'o'in neman tsari da ga sharrin Baraka da Kuma nema mata gafara da Kuma neman gafara wa Daddy, mummyn ta da Kuma Anisah.
Jiki a Sanyaye take saukowa daga step din ganin ba kowa a parlor hakan yasa ta kusa kanta a cikin kitchen, dube dube ta Shiga yi ko zata Samu sauran Abinci Amma babu duk an wanke kwanukan, girgiza Kai tayi Had'i da rike kwankwason ta a fili Tace "Ya Allah ka kawo min karshen wannan abun" Nan ta hangi wata bakar leda akan dakalin kitchen d'in tayi saurin bud'ewa ganin garin kwaki ne a Ciki hakan yasa ta San shine abincin ta gashi d'an kad'an ne tasan bazai koshar da ita ba murmushin gefen baki kawaii tayi ta nufi washing hand basin ta d'auki roba ta juye a ciki, ba b'ata lokaci ta jika ta Shiga Sha sai da ta Shanye,ji tayi kamar bata Sha komai ba amma ko ba komai ya tare Mata wani gun, d'akin ta ta Koma ta gabatar da sallar la'asar bayan ta idar ne ta d'auko uniform d'in islamiyar ta sannan ta d'auki jakarta ta fice daga gidan, dake ba nisa daga gidan su Bata d'au lokaci ba ta Isa, bayan sun tashi suna tsaye da shamsiyya sai ta ga wucewar motar gidan su ya shigo, wani irin muguwar harara safiyya tayi musu had'i da tskai Mai Kara sannan ta shige motar suka fice daga makarantar.
Shamsiyya mamaki ne ya rufe ta baki a bud'e take kallon bayan motar har suka fice ta daina ganin su sannan ne ta Maida kallon ga Asiyah Tace "kamar safiyya na gani ko? Ko ba ita bace?"
Murmushi tayi sannan tace "Eh itace" tana maganar ne tana kokarin b'oye abinda ke damin ta, Kai shamsiyya ta girgiza Tace "Kina so kice min har yanzu Mummy Baraka Bata daina abinda take ba?"
"Shamsiyya sai ma abinda ya karo kawai ki cigaba da sani a addu'a"
"Ina kai Qawata Amma Ni abinda ya bani mamaki shine naga har safiyya ta wuce ba tare da ta mana Magana ba sai ma wani irin kallo da ta mana"
"Ni kaina lamarin safiyya na d'aure mini Kai, daga jiya zuwa yau ta sauya min na rasa dalili"
Tab'e baki tayi Tace "Ai nasan Dole za a Rina, ta yaza a yi mummy ta zuba Muku Ido bayan irin son da safiyya take Miki Kuma ta barku, idan ba ta Mata muguwar hud'u ba, to tabbas ta Mata wani abun"
"Ke dai Allah ya shirye ki baza ki canza Hali ba ya kamata ki sani shi fa zato zunubine ko da ya kasance gaskiya ne"
"Zaki Fara wannan wa'azin naki" karar horn da ta ji ne yasa su juyo was a tare, shamsiyya Tace "Zo Muje ganan driver d'in mu sai mu ajiye a hanya"
"A a Kar ki damu zan taka da kafa na ai ba nisa" shamsiyya tayi tayi da ita Amma ta ki hakan yasa sukayi sallama ta shige motar, Asiyah Kuma ta nufi hanyar gida.
A nitse take tafiya damuwar duniya ta had'u ta Mata yawa hakan Shiyasa ta Fara tilawar haddar ta acikin zuciyar ta.