saki yaron kawai in yaso idan munje sai mu fada musu su rufe mata baki, kuma su shiga tsakaninta da yaron, kuma su kara mata son Sirleem a ranta, shi kuma Sirleem din a rabashi da wacan yarinyar idan ya kama a haukarta da ita duk ayi, ni ma kuma ga tawa matsalar ina son su saka Waziri ya fasa maganar auren nan”
“Haka na yi niya daman, na fadawa Jarma a saki yaron, yau idan ya dawo zan masa maganar zuwa garin, kuma tun yau zan fadawa Mai Martaba cewar Hajiya Hansai bata da lafiya ina son naje dubata jibi, sai mu wuce kawai domin zama be gan mu ba, kin ga idan muka je ma sai su fada mana wacece Fadimen har ita din mu yi maganinta, tun kam ma ta shigo ciwon kan ya mana yawa”
“Eh haka ne, sai dai wani hanzari ba gudu ba, kin san Jarma be san da ni ba a lamarin nan idan ya san da ni za a tafi asirina zai iya tonuwa”
“Karki ji komai, ai ba fada masa zan yi cewar ga abun da zai kaiki ba, zance zaki rakani ne kawai, ke kuma sai ki fara shirinki tun yau”
“Eh tun yau zan fara, gobe zan bar gidan daman ina da zimmar yin yaji saboda auren nan, to daga gobe ma zan bar gidan na koma gidan Yaya Rakiya zan fada mata komai ta nan zan samu hanyar zuwa, domin na san halin Waziri wani irin murdaden mutum ne, ba zai nemi ba sai an kwana biyu”
“Ni mamakina ta ina Sirleem yasan yarinyar nan? Har yana fadar wai ban san halin da take ciki ba?”
“Shine abun mamaki ai, amman dai idan muka je can ai zamu ji”
“Bari ma na kira Jarma tun yanzu”
Hajiya ta dauko wayarta ta lalabo number, bata dade tana ringing ba ya daga.
“Hello Hajiya, na fada musu a sake shi, gani nan a mota gani nan hanyar zuwa Masarauta yanzu”
“Tau yayi sai ka iso”
Ta sauke wayar tana wani kankance ido, irin na manyan matan nan dake cikin damuwa.
“Yace gashi nan a hanya, sai ki wuce kamin ya iso”
Hajiya Talatu ta mike tsaye da sauri tare da daukar jakarta.
“Kara na tafi kar ya tararda ni a nan kam, duk yadda kuka yi sai ki sanar min a waya”
Kai Kawai Hajiya Babba ta iya daga mata, ta maida dubanta gurin window dakin, abubuwan nan biyu sun tsaya mata a rai.
Hajiya Talatu bata dade da fita ba, Jarma ya shigo dakin da sallama, kamin ya zauna Jurry ta turo kofar dakin ta shigo ita ma, ta zauna kusa da Hajiya. Jarma ya zauna yana kallonta domin duk abun da suke be taba magana da Hajiya a gabanta ba sai dai idan ya tashi Hajiya ta labarta mata komai. Kamin Jarma yace komai Hajiya Babba ta kalleshi cike da damuwa ta ce.
“Jarma ina son zuwa garin mutanen nan jibin nan”
Jarma ya kalli Jurry kamin ya kalleta.
“Jibi fa kika ce Hajiya”
“Eh mana Jarma, baka ga halin da muke ciki ba? Ina da tabbacin mutanen nan ne kadai za su iya man maganinta, tun ba aje ko'ina ba mun fara ganin lalacewar shiri balle kuma nan gaba? Me kake tsammani? Daman kace sun fada Falmata Sardauna da kuma Fadime za su lalata mana shiri ga shi kuma mun fara gani tun yanzu, ba kuma lalacewar shirin ba tonuwar asiri wanda zai saka mu ji kunya”
Jarma ta sauke ajiya zuciya yana kallon Jurry, so yake yai magana kuma yana jin nauyinta domin be taba irin wannan maganar da Hajiya a gabanta ba, ganin yadda yake dari-dari da Jurry yasa Hajiya tace.
“Karka damu Jarma, Jurry ta san komai na san ka sani, tafiyar nan ma da ita za ayi da yardar Allah, ka sake jikinka kai magana”
“Hajiya kina ganin tafiya jibi jibin nan be yi sauri ba?”
“Ba wani sauri ni idan zan samu dama ma yau zan tafi Wallahi, yanzu haka ji nake kamar a kaya, idan fa mu ka yi wasa za mu ga wasa”
“Haka ne gaskiya, to ai ni bani da matsala, sai na fara shirina tun yanzu, ba ma sai mun je da wannan abokin nawa ba gudun kar ya ganki ko kuma ya gano wani abu, sai mu tafi kai tsaye a can Katsina din, in ya so kamin mu shiga garin sai na sami abokin wannan wanda yai mana jagora ya sake mana”
“Haka za'ayi, Juwairiyya zata siya mana tickets din jirgin Katsina, sai mu hadu a airport amman fa shirgar burtu zaka kai dan kar wani yace ya gan ni tare da kai”
“Haba Hajiya kamar ba ki san ni ba, na san yadda zan yi ai, sai dai matsalar kar sai mun sauka can wani ya fadawa Shattima ya gan mu tun da kin san a Katsina yake aiki”
“Ai ba shiga zamu yi cikin garin katsina mu zauna ba, kuma tun kam mi isa zan fadawa Hajiya Amutu ta sama mana mota mai bakin gilashi, ni idan son samu ne ai ranar da muka je Kt din mu isa garin mutanen washe gari sai mu dawo, har tickets din dawowa Juwairiyya sai ki siya mana, ni wlh na matsu na ganni garin mutanen nan”
“Okay ba matsala Hajiya, duk yau zan siya inshallah”
Cewar Jurry tana amsawa Hajiya Babba.
Jarma yayi murmushi.
“Wani abun ma sai kin je Hajiya, bokan nan makaho ne, amman zai karanta miki komai kamar gabansa aka yi, ni kaina sai da na tsorata da lamarinsu musamman yanzu daya kasance duk abun da suka fada shi ke faruwa”
“Hmmmm”
Shine kawai abun da Hajiya ta fada tana dauke kai.
FALMATA POV.
Tun da Sirleem ya saka ta a motarsa ta kasa magana sai hawaye take, kana ganinta ka san a rikice take, irin rikicewar nan ta mai gaskiya daya rasa abun fada, ga bakinta yayi mata nauyi ji take kamar an saka super glue and manne bakin. Driving yake ba dan yasan inda za shi ba, ko kuma inda zai kaita, abun da kawai yake ganin ya dace shine ta yi nisa da gidan for a while. Slowly yake driving din yana kallon fuskarta, the way da hawaye suke mata zuba sai yasa jin wani iri gashi ta kasa cewa komai tun da suka shigo motar.
“Falmata”
Ta juyo daker ta kalleshi still hawayen na sauko mata, har yanzu ta kasa yarda ba mafarki take ba.
“Ki ce wani abu mana, ko da ban dauka ba, kazafi tai min, ko kuma ki fada min yadda komai ya faru”
Ya fada yana kallonta, can kuma ya kalli titi yana tukin, tsoro yake kar bakinciki yasa ta kasa magana gaba daya, gashi bata wani ji sosai, wannan kiran da yai mata ma da be daga murya ba da na zata ji ba. A zahiri motoci da gidaje Falmata take kallo a badini kam tunanin yadda Baba da Umma zasu yanka namanta su soya shi shi ne, ko kuma su gasa ta da wuta, idan har ta koma musu gida da wannan labarin, ta dayan bangaren kuma tana tunani irin korar wulakancin da Ammy da Shattima za su mata, ta san ba zasu taba zama da ita ba tun da har aka samu yan kunnen Luma a dankwalinta. Sai a lokacin ne ta samu damar tausayawa kanta har ta fashe da wani irin kuka.
“Me na mata miyasa zata min haka, miyasa ta laka min sata? Yanzu Ammy ba zata yarda da ni ba, kuma Baba idan ya ji zai iya min wani abun ko Umma ta saka ya koreni”
Ta fada daker kuka n cinta yana taushe mata numfashi. Sirleem ya kalleta ya sauke idonsa har gudin wuyanta, damarar daya gani a wuyanta ya matukar burgeshi yana son mace da damarar wuya.
“Ammy tace wani abu ne?”
“Aa... Aa.. Amman na san zata kore ni ne saboda ba da izininta na tafi ba, lokacin da zan tafi ban fadawa kowa ba, kuma ya bani yan kunnen yara tace na daure a dankwalina ta kwance min dankwalin a gaban Ammy tace na saci na yan kunnen Luma, kuma Wallahi ban dauka ba...”
Ta kara fashewa da kuka. Kallonta ya sake yi, ba tare da ya ce komai ba ya dauke idonsa ya cigaba da tukin.
“Na taba yin irin wannan kukan da kika yi”
Ta kalleshi still tana ta rera kukan a hankali.
“Lokacin da na zabi yin sana'ar waka, a lokacin ban wuce 14 years ba, My Dad yace ba zan yi ba, ya rufe a daki, Hajiya ma tace ba zan yi ba, wai abun kunya ne a gurinsu ace ina waka ina dan former vice president? A daki nake wuni bana fita ko'ina sai idan school zan je duk wata hidima za'ayi ni ina daki a boye, Dad dina ya dauka hakan zai saka na cire rai da abun da nake so, ni kuma hakan sai ya bani damar rubuta wasu wakokin da yawa”
Ya dan yi murmushi.
“Na sha wahala fa kamin na kawo yanzu, saboda family na basa so a wacan lokaci, but look at me now! Siblings dina har cewa su ke ni dan'uwansu saboda su burge mutane ne, and before my father died shi da kansa ya bude min studio”
Ya karasa still smiling. Daga haka be sake cewa komai ba har ya isa gaban gate din Hajiya, ya saba faka motarsa waje, ya fita ya shiga cikin gidan, sai dai ganin Falmata bata da mayafi a jiki gashi rana ne ba dare ba yasa yai horn mai gadin ya bude masa gate, ya shiga harabar gidan ya faka daf da entrance din Momy har lokacin Falmata kuka take marar sauti. Sai da ya kalli Ameer dake tsaye entrance din rike da jakar laptop sannan ya kalli Falmata.
“Jira ni a nan zan fito yanzu”
Kamar yasan ba zata ce mishi komai ba, ya bude motar ya fita ba tare da jiran abun da zata fada ba, hannu ya mikawa Ameer suka gaisa sannan ya danna door bell din falon, after like 10 minutes Momy ta bude masa ya shiga ciki ya maido kofar ya rufe. Da hannu Ameer yai ma Falmata alama da ta zo, sai ta bude motar ta fito tana share hawayenta, gaba daya ta manta da wani mayafi bata mayafi take ba, ta tashin hankalin dake gabanta take yi, bata cikin kwanciyar hankali amman hakan be hanata tafiya a natse ba, be kawar da komai daga tarbiyarta da tsantsan da kai ba. Gaban entrance din ta tsaya kanta a kasa hawayen kuma sun ki daina mata zuba, ganin bata karaso ba yasa shi takowa ya sauko inda take ya tsaya.
“Me kike yi ma kuka?”
Ta kasa magana sai kokarin hade kukan take, duk da bata iya jin abun da ya fada ba.
“Me ke tsakaninki da Sirleem?”
Wannan kam ta ji domin ya kara matse tazarar dake tsakaninsa da ita kamin ya furta mata tambayar, ta girgiza masa kai alamar babu komai, sai dai bata furta masa komai ba.
“Zauna”
Ya fada yana nuna mata, sai dai kamin ta komai ya rigata kai wa kasa yai ma kansa mazauni a gurin. A hankali ta daga idonta ta kalleshi sannan ta zauna tana jin kamar an yanke mata kukanta.
“Miyasa kike kuka?”
Ya tambaya da rada, he just need to know because shi kanshi yana kallon Sirleem as bad guy saboda wasu celebrities sun batawa wasu suna.
“An kore a gurin aikina”
“Shi zai saka ki kuka?”
Ya tambaya da mamaki domin shi be ga abun kuka ba dan an koreta a gurin aikinta, ko bata fada b ya san na aikin office ba ne, domin ba tai kama da masu aikin office ba, ta ma yi kankanta da irin wannan aikin.
“Idan na koma gida Umma zata iya min duka Baba ma haka?”
“Mamanki?”
Ta girgiza kai.
“Mamana ta rasu, abokiyar zamanta dai”
“Oh. Sorry”
Ya furta yana jin wani iri, haka yake samun kansa a duk lokacin daya hadu da marar uwa mace ko namiji yana tausaya masu.
“Rashin uwa ba dadi, idan mutum ya rasa uwa ya rasa babban jigo”
Ya fada yana kallon harabar gidan alamar yana kokarin nisawa a duniyar tunani.
“Kai ma ta ka ta rasu?”
Unexpected Falmata tai masa tambayar, juyowa yai ya kalleta sai ya sakar mata murmushi.
“No i don't think so, i can't say a ina mahaifiyata take a yanzu, and i can't say me ya raba ni da ita, i just got lucky na samu Momy tana kula da ni sosai not like other step mothers, and i hope wata rana Mama na zata nemi ni, ban san abun da ya hana ta zuwa gareni ba, ni ma kuma ban san abun da ya hanani nemanta ba, a duk lokacin da nai unkurin haka sai na kasa amman ina fatar sake ganin fuskarta ko da sau daya ne a rayuwa, i need to meet my biological mother”
Ya sake kallon Falmata yana ta kokarin kirkirar wani murmushi ya yaba a fuskarsa, domin yana samun kansa cikin damuwa a duk lokacin da ya tuna da mahaifiyarsa.
“Ya sunanki ma?”
A maimakon tace masa Falmata ko Fulani sai ta zabi fada masa ainahin sunanta.
“Fateema”
“Nice name, ni kuma sunana Ameer ko ki ce black wato baki kamar ke, mun yi anko, ni baki ke baka hakan na nuna ba mu yi gadon farin ba kenan”
Ta yi murmushi kamar ba ita ce ta gama kuka a yanzu ba.
“Ni Babana fari ne, Mamana ce baka”
“Ni kam Mamana da Babana duka bakake ne, sai dai Mamana ta fi baki but tana da kyau sosai, sai dai a kamani Babana na dauko ban biyo Mama ba”
“Ni ma fuskar Baba na dauko, amman bakin na Mamana ne, har Umma tana cewa wai ba dan ina da kamanin Baba ba da sai ace ni ba yarsa bace, wai na cika baki kamar zunubi”
Ta fada da dan karamin murmushi fuskarta, ido ya kura mata hakan nan yake jin ta kwanta masa a rai sai ya ke jin kamar daman can ya santa ba, kamar yadda ita ma take jin sakewa da shi.
“Hakan ya nuna babanki yana da kyau”
Ta yi murmushi, shi ma murmushin yai ya mike tsaye yana duba agogonsa.
“Momy kar nai latti fa”
“Ina zaka je?”
Ta tambaya tana mikewa tsaye.
“Airport zata kai ni na bi jirgin Abuja, zan koma makaranta ne America”
“Wata kasa?”
“Yeah hutu ya kawo ni nan, amman na kusa gamawa na dawo gaba daya, ke ina kike karatu?”
“Ni bana makaranta ban taba zama aji ba”
“Da gaske?”
“Eeh”
Sai ya ji taba shi tausayi.
“Ina mayafinki?”
Sai a lokacin kunya ta lullube ta, domin ta manta da wani zancen mayafi har sai da yai magana.
“A can gidan na bar shi...”
Tana rufe baki Momy ta bude kofar falon ta fito Sirleem na bayanta sai dai shi yana rike da kofar falon ne. A nan wata sabuwar kunya ta sake lullube Falmata haka cikin dauriya ta risina ta gaishe da Momy.
“Momy ina kwana”
Momy ta amsa mata tana mata kallon tausayi.
“Lafiya Kalau ai wuni yayi 12 bata kusa ba?”
Falmata ta sunkuyar da kanta.
“Ki shiga ciki, zan aje Ameer airport na dawo, Sirleem ka sama mata Hijab ta saka”
Daga bakin kofar da Sirleem yake tsaye ya amsa da Okay, sai da Falmata ta kalli Ameer din sannan ta taka zuwa gaban kofar Sirleem ya bude mata ta shiga. A kasa ta zauna tana shi kuma ya wuce sama ya shiga dakin Ammy, be dade ba ya sauko rike da karamin veil kusa da ita ya zaune, sai dai shi a saman kujera yayinda da ita kuma take zaune a kasa.
“Saka wannan ban ga hijaban ba”
Ta mika hannunta biyu ta karba ta yafa, ya ciro wayarsa yana dannawa ba tare daya ya kalleta ba.
“Na fada ma Momy komai, and i hope zata dauke ki a aiki a nan, idan ma bata son aiki as i know bata son yar aiki zaki rika wuni a nan sai dare ki koma, idan lokacin biyan kudin aikin ki yayi zan baki sai ki bata, ina fatar hakan ya miki? Ba sai sun san an koreki ba balle su yi miki horo...”
Tun da ya fara maganar ta daga kai tana kallonsa sai idonta ya cika da hawayen farinciki, kura masa ido tai tana ta kallonsa wani irin kaunarsa ce take jin tana kirkirar muhallin a zuciyarta. Jin ta yi shiru bata ce komai ba yasa ya kalleta sai ya ga hawaye a sauko mata.
“Hakan be miki ba ne?”
Ta girgiza masa kai a hankali.
“Da ace zan iya, da na bude maka zuciyata kaga yadda kimarka ta cika ta, da ace kowa kamar kai yake da duniya ta zauna lafiya, kana da kirki fiye da tunanina, kana da kyautata ga masu bukata, baka kyamar kowa baka da girman kai, har yanzu na zuciyata ta kasa aminta cewar kai ne Sirleem M2, ina rokon Allah yai maka fiye da yadda kai min, ya zama gatanka, yai maka jagora ya shiga maka gaba akan dukan al'amurranka”
Yayi murmushi yana mata wani kallo mai wuyar fassara, kalamanta na ratsa jini da jiniyar jikinsa.
“Wata mace mai kalar shekarunki ko kasa dake, ko sama da ke bata taba fada min kalamai masu dadi kamar yadda kika fada min ba, ina jindadi idan na yayewa wani bakinciki, ina jin dadi idan nai taimako, amman ke... Ina ji kamar ace zan iya yaye miki damuwarki fiye da kowa, kina bani tausayi sosai, and yadda kaddara take ta hada mu maybe you need me the most, zuciyata ta cika da tausayinki, yadda kika da natsuwa, hankali, juriya, hakuri, sai kika burge ni, duk da kasancin shekarunki kin iya magana mai kyau Falmata, kin cika yadda ake so ko wace mace mijinki yayi dace...”
Ta yi kasa da kanta, bayan yabon da yai mata a mota na cewar tana da kyau yau ma ya kara yabonta da wasu hawaye da dabi'u da bata taba sanin tana da su ba.
“You know sometimes idan Allah zai taimake ka, na wai zai maka taimakon ba ne kai tsaye, sai ya kawo wani wanda ta dalilinsa zaka samu taimako ko kuma wani abu da kake nema, so ina daukar kamar haka ne a tsakanina da ke”
Bata sake dago kan ba, kuma bata sake ce masa komai ba har ya