x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 6 - MAYRAAH free pages

  • 15001 words
  • 18000 words
  • Out of 54184 words

Category: Love Stories

Views 158

25 Aug 2025
Start ads
After Image Ads
ba, Mayraah dai bata ce komai ba ta wuce bandaki, Badiyya ta bi ta da wani kallo, ba a dau lokaci ba Mayraah ta fito rike da sabulunta da shower gel sai towel, har ta fita daga dakin Badiyya bata daina bin ta da kallo ba, Mayraah ta tafi dakin Maheer ta shiga bandakinsa tayi wanka, ta wanke bakinta da mouthwash dinsa ta fito, Hijab dinta ta dauka ta saka bayan ta goge jiki sannan ta koma dakinta don daukan kayan da zata sa da duk wani abu da zata bukata, Badiyya bata fasa bin ta da kallo ba, bayan fitarta ta ajiye spoon din hannunta tana nazarin abubuwa iri iri.... Bayan kusan minti goma Mayraah ta fito daga dakin Maheer cikin shirinta, Hijab ne har kasa jikinta tana rike da handbag dinta ta nufi dakin Ammi ta sanar mata Musharraf na jiranta a waje, Ammi tace "Toh Allah ya tsare, sai a kula, kuma kar ki wuce karfe shidda, Abbanku ma yau zai dawo" Mayraah tace "Toh Ammi, Allah ya dawo da shi lafiya" Daga haka ta sauka downstairs, zaune taga Badiyya a parlon da plate din abincin da take ci, Mayraah ta kalleta tace "Sai na dawo Aunty Badiyya" Badiyya tace "Ina za ki?" Mayraah tace "Ana jirana ne a waje" Badiyya tace "Wa yake jiranki?" Mayraah da kamar bazata ce komai ba, sai kuma tace "Baƙo nayi" Daga haka ta juya ta bar parlon, Badiyya ta mike ta nufi window da sauri tana leka compound din gidan amma bata ga kowa ba, sai da ta ga fitar Mayraah daga compound din sannan ta fito har tana tuntube ta nufi gate tana leka kofar gida, sosai gabanta ya fadi ganin motar dake barin kofar gidan, Dr Musharraf! Abinda ta fada kenan a zuciyarta... Bayan sun bar layin Musharraf yace "A ina ake siyar da kayan ne?" Mayraah ta zaro ido tace "How will i know?" Yace "Ke ba er kano bace" Mayraah bata ce komai ba, Yace "kin yi shiru" A hankali tace "Kasuwa za mu je" Yace "Aa bazan je wani kasuwa ba, babu boutique ne irin na mata?" Murmushi kawai Mayraah tayi still bata ce masa komai ba, Idan tana masa wannan murmushin confusing dinsa take, ya gangara yayi parking gefen hanya, Calmly yace "Kin yi shiru" Mayraah ta sunkuyar da kanta tace "To me zan ce?" Yayi kasa da murya yace "Kinsan me zai faru Mimi?" Ta kallesa da sauri don Ya Maheer da Ammi kawai ke kiranta Mimi, ta girgiza masa kai, kana ganinta kasan she is uncomfortable, After few seconds of staring at her yace "I think it will be better in tura maki kudin kayan nan, ku hada a can gida, idan ma kudin basu isa ba sai ki sanar min" Sai a sannan Mayraah ta daga kai ta kallesa, A hankali yace "That will be better wife" Ita dai bata ce komai ba, Yace "Nawa account dinki ke iya dauka at a time?" Mayraah tayi shiru, sanin she might not even say anything yace "Ohk i will transfer 7M to you now for a start" Da sauri Mayraah ta kallesa ganin ya dau wayarsa tace "Kudin yayi yawa ai" Ya kalleta yace "Ba atamfofin dubu talatin talatin nace ku je ku siya ba Mayraah, and the 7M i am sending u is just for a start, sannan banda kudin Boxes a ciki da Abaya with jewelries, Mami ta riga tayi ordering dinsu" Mayraah bata kuma ce masa komai ba, Tana ganin ya fara danna wayarsa tayi saurin cewa "Seriously that amount is much" Ya kalleta for few seconds, sai kuma ya ci gaba da danna wayarsa, babu bata lokaci alert ya shigo wayarta, ta dinga kallon screen din wayar ganin 7M ya tura mata, can ta juya ta kallesa, ya jinginar da kansa jikin kujeran motar yana kallonta yace "Since we won't be going out for the shopping today kinsan me zai faru?" Ta ajiye wayarta tana sauraron abinda zai ce, Yayi kasa da murya yace "Akwai gidan Yayana da ya bani idan muna son zama ciki after the wedding, and i have my house da na gama wannan shekaran, sai kuma one of our houses, so i will be taking you to each and every one of them ki zabi inda ya maki" Ko rufe baki bai yi ba Mayraah tace "No, I don't think that will be possible, duk wanda yayi maka is okay, just drop me home now" Kallonta ya dinga yi, taki yarda su hada ido, lkci daya yanayinsa ya canza yace "Saboda ban yi deserving kiyi trusting dina ba?" Mayraah that is becoming uncomfortable ta girgiza kai da sauri tace "Ni ba haka nace ba, i just don't have choice duk abinda ka zaba is okay by me" Yace "No, ke zaki zaɓa ba ni ba" Ta kallesa da sauri ganin zai fara driving bata san sanda ta sakar masa kuka ba tace "Don Allah kayi hakuri ka maida ni gidanmu tunda baza mu je siyayyan ba" Da mamaki yake kallonta ganin hawaye a idonta kamar jira take, Bai kuma cewa komai ba ya ci gaba da driving dinsa, Mayraah sai bin hanya take da kallo gabanta na faduwa tana jiran ganin inda suka nufa, ai bata san sanda ta sauke ajiyar zuciya ba ganin inda za su koma, suna isa kofar gidana bayan yayi reverse ta juya ta kallesa a hankali tace "Nagode" Ya gyada mata kai kawai, ta bude motar ta sauka tana kulle kofar ya ja motarsa ya bar layin ta bi sa da kallo, lokaci daya jikinta yayi sanyi, bayan few seconds ta juya ta nufi cikin gidan tana duba agogon wayarta dake nuni da karfe hudu da rabi. Ammi dake zaune parlor ta dinga kallonta tace "Wai har kun dawo" Mayraah ta zauna gefen Ammi tace "Kinsan me Ammi? Kawai cewa yayi it's better ya bada kudin mu siya kayan ba sai mun dinga yawon siyayya ba tare, so he sent me 7M" Ammi ta buda baki tace "Kika amsa?? Uban me za a hada maki na 7m Mayraah da zaki amsar masa kudade haka?" Mayraah ta marairaice tace "Wallahi nace masa yayi yawa amma yaki ji na Ammi, kuma wai banda boxes da Abaya and jewelries a kudin" Ammi dai ta kasa cewa komai, Mayraah dai sai kallonta take, can Ammi tace "To shikenan, Allah Ubangiji ya sanya alkhairi, shi kuma Allah ya kara masa budi" Mayraah ta sunkuyar da kanta, Ammi tace "Je ki canza kayanki mu je kitchen mu nema ma Abbanku abinda zai ci anjima, tun dazu nake nan nake nazarin abinda zan girka" Mayraah tace "To" Har ta mike zata wuce sama zuwa dakinta Badiyya ta fado mata, can ta juya a hankali ta kalli Ammi tace "Aunty Badiyya na sama ne?" Ammi tace "Aa wai taje amso littafinta a gidan kawarta" Mayraah dai bata ce komai ba ta wuce sama zuwa dakinta, tana bude kofar dakin ta dinga bin ko ina da kallo, ji tayi kamar tayi kuka, what is all this plss? kaya can, kaya nan, everywhere so littered with clothes kamar warce tayi sati a dakin, ta karasa ciki, within few minutes ta hada wasu abubuwanta da tasan zata bukata ta fice daga dakin ta tafi dakin yaya Maheer ta ajiyesu sannan ta cire Hijab dinta ta linke ta canza kayanta ta fita daga dakin ta dawo parlor... Sai kusan karfe shidda suka gama girkin Ammi ta fito parlor, Mayraah kuma ta hau gyara ko ina na kitchen din, Ammi na zaune parlor Maheer ya shigo gidan, bayan ya gaida Ammi ya wuce sama, Ba a wani dau lokaci ba ya dawo downstairs yana kallon Ammi yace "Ina Mimi?" Ammi tace "Tana kitchen" Ya nufi kitchen din, Mayraah na ganinsa tace "Yaya sannu da dawowa" Ya kulle kofar kitchen din yace "Me kayanki yake yi a dakina?" Mayraah ta marairaice tace "Yaya Aunty Badiyya ce ta dawo gidan nan, and she's already scattering everywhere in my room" Maheer yace "Yaushe ta zo?" Mayraah tace "Dazu" Yace "Shine kika cika min daki da kayanki? Me yasa baki kai dakin Usman ba?" Ta zaro ido tace "Kana son yayi min fling dinsu idan ya dawo?" Juyawa Maheer yayi ya fita daga kitchen din Mayraah ta ci gaba da abinda take. Ammi na zaune parlon Abba bayan ya gama cin abinci wajajen karfe tara, tana kallonsa tace "Yallabai dama nace sai ka dawo zan sanar maka, Badiyya ta dawo gidan nan da zama yanzu" Abba yace "To maa sha Allah, ai haka ake so, Allah yasa ta zauna wannan karan" Ammi tace "Ameen, sannan kuma kaga biki na ta karatowa ban ga kace a fara shirye shiryen komai ba" Abba yace "Wannan ai ba damuwa bane, a rana daya za a siya furnitures da duk wani abu da za a kai mata, so ko ana saura kwana biyu bikin ne za a iya yin wannan ko?" Ammi tace "Haka ne" Abba yace "Abinci kuma zuwa next week, za a kawo buhunhunan shinkafa da flour da su mangyada, taliya, manja da dai sauransu, duk a ajiye a store" Ammi tace "Toh Allah ya kara budi Yallabai" Yace "Ameen, akwai kudin saniya da raguna uku da na bada shekaranjiya, Usman kuma yace min zai siya lemo da ruwa da za a bukata na taro" Ammi tace "To maa sha Allah" Abba ya jawo wani envelope ya bude ya ciro wasu takardu ya mika ma Ammi ta amsa tana kallonsa tace "Na menene wannan din?" Yace "Wani Plaza aka min tallansa 2 weeks ago, to akwai wani business da nayi an samu kudi Alhamdulillah shine na yanke shawaran siyan wajen da sunan Mayraah, ki ajiye mata takardun gun yan uwansu" Ammi ta sauke idonta bata ce komai ba ta mayar da takardun cikin envelope din ta mike ta nufi Bedroom dinsa, Abba ya bi ta da kallo yace "Next one da sunanki za a siya, then Umar" murmushi kawai tayi ta shiga dakin. Wajajen karfe goma Mayraah ta shigo dakin Ya Maheer, yana zaune yana danna waya, ya bi ta da ido yace "Baki kwanta ba?" Tace "Ni fa a nan zan kwanta yaya, tayi occupy din ko ina" Yace "To ke tsoronta kike ji je da baza ki ce mata ta gyara zaki kwanta ba" Mayraah tace "Aa dama ni ba dakin zan kwana ba ai" Yace "You are disturbing me Mayraah ki tafi dakin Usman mana" Ta kallesa ta marairaice tace "To kai kaje ka kwanta mana he won't say anything, amma idan ni ce zai min masifa kai ma ka sani" Maheer bai sake ce mata komai ba ya ci gaba da danna wayarsa, ta lallaba ta kwanta karshen gadon kafin ya canza mind ya koreta, tana kwanciya babu ɓata lokaci bacci ya dauketa, Maheer ya dau wayarsa ya koma dakin Usman ya ci gaba da abinda yake, wajen karfe daya yaji yana jin yunwa, har ya kwanta yaji bazai iya jure yunwar ba ya tashi ya sauko downstairs, kunna fitilar parlon yayi ga mamakinsa ya ga Ammi zaune, ya nufeta da sauri yace "Ammi baki kwanta ba?" Ammi tayi saurin goge hawayen idonta wanda tuni Maheer ya gani, ya zauna yana facing dinta da damuwa yace "Ammi are you okay? Me yake faruwa ne" Ammi ta kirkiro murmushi tace "Sallah nayi shine na dawo nan na zauna" Yace "No, kuka fa kike Ammi" Ammi tace "Kukan rashin mahaifina da 'yar uwata sannan kanina, hakan har ya zame min jiki kai ma ka sani Maheer" Maheer ya kwantar da murya yace "Ammi addu'a kawai zaki dinga bin su da shi ba kukan nan ba, don Allah ki daina haka kar ki je wani ciwon ya shige ki" Ammi ta gyada masa kai tace "In sha Allah Maheer" Yace "Ki tashi kije ki kwanta" Tace "Kai me ka sakko yi" Yace "Abinci zan ci" Ammi tace "In ko baka daina cin abincin tsakar dare ba zaka ajiye tumbi ne" Yayi murmushi yana shafa cikinsa yace "Yau ne fa kawai Ammi, kuma kaɗan zan ci, bari ma in zubo ki ga" Daga haka ya mike ya tafi kitchen, ba a dau lokaci ba ya fito rike da plate din abinci, yana ci suna hira da Ammi a parlon, har ya gama, tare suka koma sama ganin ya nufi dakin Usman tace "Can zaka kwanta?" Yace "To tayi hijacking min dakin" yana fadin haka ya shige dakin Usman ya kulle, Ammi ta bude kofar dakin nasa a hankali ta kunna wuta tana kallonta, tana kwance tana bacci, Ammi ta karasa cikin dakin ta lulluba mata bargo a hankali sannan ta juya ta kashe wutan dakin ta fita ta tafi nata dakin.




07087865788✍🏻

WhatsApp only, no phone call ...
[5/29, 6:36 PM] Khaleesat Haiydar💖: 💖💖 *MAYRAAH*💖💖




By _Khaleesat Haiydar_📚✍🏻




5......


Washegari sai kusan karfe goma Mayraah tayi realizing basu yi waya da Dr Musharraf ba tun bayan da ya dawo da ita jiya, ta karasa wanke wanken da take yi a kitchen ta fito, Sabira ce kadai parlon tana goge goge, Mayraah ta wuce sama ta shiga dakin Maheer, tun karfe takwas ya fita aiki, yana fita kuma ta gyara masa dakin ta wanke bandaki, wayarta ta dauka ta zauna gefen gado tayi dialing number Dr Musharraf, har ya katse ba ayi responding ba, da har zata sake dialing kawai kuma ta fasa, ta daga kai jin an bude kofar dakin, Ammi ce ta shigo, Ammi ta karaso tana kallonta tace "Meye da dakin naki da kika yi hijira daga can yanzu?" Mayraah ta ɗan yi murmushi tace "Aa ba komai, kawai ina son Aunty Badiyya ta zama comfortable ne shi yasa" Ammi tace "To bana son haka, kuma kar in sake ganin haka, ki tattara yanzun nan ki koma dakin ki, kar ki sake cewa zaki kwana dakin Maheer saboda Badiyya na dakinki, as far as tana gidan nan to daki daya za ku zauna" a hankali Mayraah tace "Toh" Ammi tace "In ke tayi ma haka zaki ji dadi? Saboda ita ki ki zaman dakinki kamar ba er uwarki ba, naga dai ko cacan baki bai taɓa hada ku ba balle kice, to me ya janyo wannan abu haka? In kinyi hakuri duka duka ma kwana nawa ya rage maki a dakin Mayraah" Mayraah ta sunkuyar da kanta cikin sanyin murya tace "Kiyi hakuri Ammi" Ammi tace "Ki tashi ki koma dakin ki" Daga haka ta juya ta bar dakin, Mayraah ta bi ta da kallo. A hankali Mayraah ta bude kofar dakinta ta shiga ciki da sallama, Badiyya dake shiryawa bata ko amsa sallaman nata ba balle ta kalli inda take sai ma wani tsuke fuska da tayi, Mayraah ta karasa cikin dakin ta ajiye wayarta gefen gado sannan ta shiga bandaki rike da shower gel dinta da towel, Badiyya ta bi ta da kallon gefen ido har ta kulle kofar bandakin, Badiyya ta wani taɓe baki ta ci gaba da shafa cream dinta, ko minti biyar Mayraah bata yi a bandaki ba wayarta da ta ajiye gefen gado ya fara vibrate, Badiyya ta juya tana kallon wayar, da sauri ta dauka tana kallon number jikin screen din don da Emoji aka yi saving maimakon suna, wayarta ta jawo tayi snapping screen din sannan ta mayar da wayar inda yake ta ajiye da sauri, babu bata lokaci ta haddace number sa tayi snapping ta shiga True caller don ganin number waye, Musharraf Abdallah taga ya fito, wanda sai da gabanta ya fadi ganin sunansa kadai, a sanyaye ta ajiye wayarta ta karasa shafe shafenta ta mike ta dau kayanta ta saka ta koma gefen gado ta zauna, tayi nisa cikin tunanin da take bayan kusan minti ashirin taji fitowar Mayraah daga bandaki, mikewa Badiyya tayi ta figi wayarta ta fita daga dakin, Mayraah ta bi ta da ido, ganin bata kulle mata kofar ba ta karasa ta kulle kofarta.
Musharraf ya shigo parlorn Maminsa ya zauna opposite dinta yana kallonta yace "Gani Mami" Mami tace "Why ain't u picking ur brother's call?" Yana karasa buttoning din t-shirt dinsa yace "Bana kusa da wayan" Mami tace "To ka kirasa za ku yi magana" Musharraf yace "Ohk" daga haka ya mike, Mami tace "Ina kuma za ka? koma ka zauna ka kirasa yanzu, don nasan ba kiransa zaka yi ba" Musharraf ya kalleta yace "Mami sauri fa nake, ba ni nace maki zan kirasa ba" Mami tace "Musharraf" Komawa yayi ya zauna ya jinginar da kansa da kujera, Mami tace "Kira sa yanzu" Musharraf ya hade rai yace "Mami shi fa gayen nan baya taɓa kiran mutum haka kawai, i know there is definitely something annoying that he wants to say to me" Mami tace "Why don't u respect the fact that he is ur elder brother Musharraf?" Musharraf bai ce mata komai ba ya dau wayarsa yayi dialing number brother din nasa wanda ko saving dinsa ma bai yi a wayarsa ba, yana fara ring ya sa handsfree, Mami dai sai kallonsa take, sai da ya kusa katsewa aka daga from the other side, Musharraf yace "Good morning" Yayan nasa yace "Baka ganin kirana ne?" Musharraf yace "Eh yanzu naga kiran" Daga daya bangaren brothern nasa da ake kira da Daddy yace "Akwai personal discussion da nake son mu yi akan auren nan da zaka yi" Musharraf ya ɗan yi jim, sai kuma yace "Ina ji" Daddy yace "Ok, amma da farko ina son sanin ko kana da issue da Farrah ne?" Musharraf yace "Wacece haka?" Ita dai Mami kallonsa kawai take, Daddy yace "Farrah ce baka sani ba?" Musharraf yace "Oh, me yasa ka min wannan tambayar?" Daddy yace "At the first place.... Why did u decide to date somewhere else ga er uwarka that has all qualities also" Musharraf bai san sanda ya mike tsaye ba yace "Is that so? Since ni ban yi ba ai kai zaka iya yi a madadina it's still not too late, look yaya ni dama nasan there is nothing good da zaka kirani ka gaya min, and sorry to say bana son kowa ya kara sa bakinsa a lamarin aurena, not even you! Hatta su Aunty
End Ads