An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels ABOKAN GABA MUKHTAR I. KWALISA 08069524699 G imbiya Lusa tana gaba akan ingaraman dokinta ta yi shiga ta bajinta cikin sulke da aka yi masa ado da koren qyalqyali. Daga nesa idan ka kalleta sai ka xauka wani barde ne mai qarfin dantse amma idan ta matso kusa sai kaga ashe mace ce. Sai tauri a duniyar sadaukai idan suka ganta suna saurin rainata, amma abinda ba su sani ba shi ne da mutum ya raina Gimbiya Lusa ya xauketa ba wani abu ba gwara ya sha guba da za ta hallakar da shi a sa’o’I uku domin Gimbiya lusa ta fi guba saurin kisa. Ita xaya take faman kaiwa da komowa a cikin duniya tana ta faman farauce rayukan sadaukai da jarumai tun daga lokacin da aka bata labarin cewar wani sadauki zai bayyana ya sace ruhin mahaifinta wato sarkin aljanu mai girman daraja sarki Gamsu. A duk duniya babu wanda gimbiya lusa take matuqar qauna kamar mahaifinta sarkin aljanu gamsu duk da zamtowar ita ba aljana bace ta kasance mutum bil’adama amma mahaifinta aljani ne. Gimbiya lusa ta kasace mace ma’abociyar kyau da a faxin duniya babu tamkarta a zamanin. Ta kasance doguwar mace mai yalwar jiki ba wai sosai ba tana da faffaxaar fuska mai xauke da fararen idanuwa. Tafi iya murmushi fiye da komai. A duk lokacin daka ganota daga nesa gani za ka yi har wani xaukar idanu take yi, tana da qirar jarumta tana da ruwan tausayi, kyawunta yafi jarumtakarta. A yanzu Gimbiya lusa tana tsaye a gaban wani saurayin namiji mai cike da yalwar kyawu da cikar zati, mai kwarjinin fuska da jarumta. Wannan saurayin da yake tsaye a gabanta shi kaxai ne jarumin da ya yi saura wanda bata farauce ransa ba, a cikin mutanen da take tsammanin za su iya zuwa har fadar sarkin aljanu domin sato ruhinsa. A duk jaruman da su ka yi gwagwaarmaya da ita wannan shi ne kaxai jarumin da kwarjinsa ya cika mata fuska. Suka jima a tsaye suna kallon junansu, a hankali ya dubeta yace mata. “Tun da nake a rayuwata ban tava ganin mace da kyawunta ya girgiza mun ruhi ba sai ke… na yi matuqar baqin ciki da kika zamo mace mai yin hidima ga aljanu, kike farauce rayukan ‘yan uwanki mutane akan kare ruhin wani tsohon aljani don gudun sace shi”.Ya yi maganar yana mai dubanta kafin ya ci gaba da magana cikin isa da izza. “Kar ki mance duniya tana da yawa kuma qaddara ta riga fata” Gimbiya lusa ta yi murmushi kafin ta mayar masa da martani cikin wani irin sautin murya. “Ina da tabbacin idan na farauce rayuwarka zan kawo qarshen matsalar dake shirin faruwa ga mahaifina zai zamo cikin walwala da nishaxi, don haka yanzu zan kawo qarshen numfashinka kamar yadda na aikata ga sauran jarumai ‘yan uwanka” Da muryar jarumta tace masa. Cike da jimami yace mata “Duniya ta zamo mafaka ta mutane daban-daban ina fatan baki mance da yanki baqar fata ba?” Yana mai tsareta da idanu. Ta yi murmushi. “Baqar fata ba su da wayewar da har za su san amfanin ruhin mahaifina a garesu, mutanen da ba su fahimci kansu ba, taya za su fahimci amfanin wani abu” Ya girgiza kai. “Xan hakin daka raina shi ke tsone maka ido”. suka yi shiru su duka suna kallon juna na tsawon lokaci daga bisani ya qara dubanta sannan cikin isa da taqama yace mata. “Lallai ina mai tabbatar miki ruhina yafi qarfin ki farauce shi don ba za ki tava samun nasara akai na ba”. Maganarshi ta zamto tamkar wuta ya watsa mata, ta dube shi da qunar rai da tafarshashiyar zuciya tace masa. “Babu wani jarumi a duniya da ba zan sami nasara akan shi ba, domin na farauce rayukan sadaukai irinka waxanda suka fika jarumta da nuna bajinta a duniya, don haka kaima lallai ina baka tabbacin zan kawo qarshen numfashinka ka zamto kamar ba a yi ka ba”.Gimbiya Lusa ta tabbatar masa. Ya girgiza kanshi sannan lokaci xaya ya gyara ruqon da ya yiwa takobinshi ya kalleta sosai a hankali yace mata. “Bana buqatar ki zamto abokiyar gabata” Ya yi shiru yana kallonta a hankali ya kuma ce mata. “Kinyi gaggawa wurin yarda da cewar wani aljani ne mahaifinki,bayan aljani bai isa ya haifi halitta kamar ki kyakkyawa mai kyawun fuska da kyawun idanu da kyawun shataccen baki ja”. “Bana buqatar yawan surutu don haka ka shirya tarata gani nan tafe zuwa gareka” ta ce masa cikin tsawar murya, sannan lokaci xaya tayi xauki zuwa gareshi shima ya taso ma ta lokci xaya suka gamu da juna a tsakiyar fili, su ka kaiwa junansu sara da takubbansu, makamansu suka gamu wuri xaya, qarar haxuwar makaman ta cika wurin suka gauraye wuri xaya suka soma qoqarin farautar rayuwar juna, suka dinga kai sara ga junansu. Gimbiya Lusa t sami sadaukin ba yadda ta tsammace shi ba. Lokaci xaya suka yi jina-jina duk jikinsu idan ka duba jikinsu ya yi kaca-kaca da ciwuka. Haa suka ci gaba da saran juna kafin daga bisani suka yanke jiki suka faxi suka yi kare-jini-biri-jini. “Ba za ki tava samun nasara a kaina ba, domin ina son ki sani Ubangiji da nake bautawa, wato Ubangijin da ya yi horo da bin addinin musulunci wanda shi ne ya hanaki samun nasara a kaina” Ya tabbatar mata. Gimbiya Lusa ta girgiza kanta cike da gamsuwa domin ta tabbata bata samu nasara ba ga wannan jarumin. Ta xago kanta a hankali ta dube shi taga yadda jini yake malalowa daga jikin raunukan da tayi msa. A hankali itama ta dubi jikinta taga yadda itama jini yake ta faman xuba daga jikinta ta girgiza kanta. ‘Babu makawa ba za ta iya samun nasara ba akan wannan jarumin sai dai su yi Mutuwar kasko, tun da suka yi kare-jini-biri-jini” Gimbiya Lusa ta zuba masa idanuwa tana kallonsa shima ya zuba mata idanuwa yana kallonta. Kowa ya ajiye makamin shi a gefe xaya. Wannan ita ce rana ta farko da Gimbiya Lusa ta tava ganin jarumin da jarumtarsa ta birgeta, wannan rana ita ce rana ta farko da Gimbiya Lusa ta ji tana son wani sadauki mutum kamarta a cikin ranta. Amma ta fidda rai, raunukan da yake a jikinta da jikinshi ba za su barsu su ci gaba da rayuwa ba. Ta lumshe idanuwanta sunan shi ya dawo mata a cikin zuciyarta. “Ansar”. A dai-dai lokacin da ta furta hakan a cikin ranta, a dai-dai lokacin wani mummmunan aljani mafi girma ya sauka a gabanta, yana sauka ya suretaa da hannunsa ya juya ya yi sama da ita a guje, tamkar an harba kibiya. Gimbiya Lusa ta buxe idanuwanta a hankali ta kuma kallon Ansar da yake kwance a wurin. Ta mayar da idanuwanta ta lumshe su. Ungulaye suka ci gba da yin shawagi, suna jiran Ansar ya qarasa mutuwa su sami damar yin kalaci da namanshi. NAHIYAR BAQAR FATA Nahiya ce data yi fice ta kuma shahara wajen siye da siyarwa ta bayi. Don haka baqar fata ba shi da wata daraja a wajen larabawa da nasarawa, domin suna masa kallon ba shi da wani amfani idan ba bautarwa ba. Farsu ya kasance baqar fata mai kaifin basira da dabara. Ya zamto jarumi mai yawan bajinta, farsu ya kasance bawa ne ga bokanya Namsu wacce ta kasance baqar fatar bokanya data shahara a fagen sihiri, don haka a cikin tsafinta ta gano amfanin ruhin sarkin aljanu Gamsu a gareta. Domin ya bayyanar mata matuqar tana son ta mulki duniyar bokanci ya zamo duk duniya babu kamarta to sai ta mallaki ruhin sarkin aljanu hakan yasa ta bazama duniyar tsafi da bincike akan yadda zata mallaki ruhin, amma sai ta gano qarfi sihirin tsafi ba zai tava sakawa ta mallake shi ba. Haka ma tsananin jarumta. Wanan lamarin ya matuqar tayarwa da bokanya Namsu hankali ta rasa meye yake mata daxi, tayi ta nazari ta rasa samun mafita. Sai daga baya tayi tunanin tura bawanta Farsu yaje ya gwada sato mata shi. Tunda shi Farsu gwani ne wajen iya sata kamar sidabaru haka yake iya sace abu. Tana gama tunanin ta nufi inda yake ta same shi a zaune yana gyara makaminsa. Ta dube shi ido cikin ido. Farsu ya yi gaggawar zubewa a gabanta domin girmamawa Bokanya Namsu a hankali ta soma yi masa magana. “Lokaci ya yi daya kamaya ka yi mun bauta ta qarshe daya kamata na ‘yanta ka” Ta saurara tana kallonsa sannan ta ci gaba da magana. “Samun nasaraka a wannan karon tamkar ka sami ‘yanci ne, don haka wannan damace gareka ta barin qangi na bauta” Ta basa tabbaci. Farsu ya xago idanu yana duban bokanya Namsu, wannan shi ne zance mafi daxin ji daya tava ji daga bakinta a iya zamanshi a qarqashinta. Don haka cike da qwarin gwiwa yace mata. “Wannan wane irin aikine haka?” Bokanya Namsu tayi murmushi domin ganin tarkonta ya kamar kurciya, a hankali tace masa “Ruhin sarkin aljanu Gamsu nake son ka sato mun”. Maganar ta zo masa a bazata ya sauke wani gwauron numfashi kafin yace mata. “Zan sato miki shi matuqar zan samu ‘yanci na kuvuta daga qangin bauta” Ya tabbatar mata. Ta dube shi cike da jin daxi tace masa. “Wannan itace bauta ta qarshe da za ka yi mun a rayuwarka, don haka idan ka sami nasara ka zamto kuvutacce, ‘yantace. Yanzu zan haxaka da aljanin da zai xaukeka ya kaika har cikin fadar sarkin aljanu Gamsu” Ta kammala maganar tana dubanshi kafin ta qara cewa da shi. “Ko kan da wata buqatar ta yin shiri?” Ya girgiza kai gami da faxin. “Bana buqatar yin ko wanne shiri ya shugabar bokaye”. Bokanya Namsu ta yi dariya jin sunan daya kirata, take ta shafi xamararta kamar qiftawar ido wata jibgegeyar halitta ta bayyana mai tsananin girma da tsananin muni. Tana da dogon wuya kamar raqumin dawa da manya-manya kunuwa farakam-farakam sun lanqwasa kamar alamar tambaya(?) yana da fuka-fukai kimanin guda ashirin da bakwi. Bokanya Namsu ta dube shi tace masa. “Maza ka xauki bawana Farsu ka kai shi fadar sarkin aljanu Gamsu” Take aljanin ya girgiza kai cike da girmamawa, Bokanya Namsu ta dubi Farsu tace masa “Idan ka shirya kuna iya tafiya”. Farsu ya dubi bayan aljanin ya dubi kayan makamansa ya sunkuya ya xebesu ya naxesu a cikin wata rigar fatarsa da yake amfani da ita a lokacin tsananin sanyi, ya daka tsalle ya haye bayan aljanin kafin yace masa. “Muna iya tafiya”. Bokanya Namsu ta dube shi gami da xauko wani makami ta cilla mishi kafin tace masa. “Ga wannan zai taimake ka” Farsu ya zuba mata ido yana dubanta, a daidai lokacin aljanin ya buxe fuka-fukanshi ya soma tashi cikin sararin samaniya suka luluqa suka nutse a cikin gajimare. Haka suka xaui tsawon wata xaya da sati xaya suna tafiya sannan suka qaraso fadar sarkin aljanu Gamsu, wanda tun daga nesa farsu ya ga rundunar aljanu tsaitsaye cikin shirin yaqi ko ina ka duba sune. An qawata fadar da ado mai jan hankali da zane-zane abubuwa masu matuqar kyau da ban sha’awa. A hankali aljanin ya yo qasa-qasa ya shiga ciki fadar, ga matuqar mamakin farsu sai yaga babu wani aljani daya damu da shi, ko wanne sabgogin gabanshi yake yi a haka suka dangana har cikin fadar, wanda a can ciki ne suka samu wasu zaratan aljanu tsaitsaye suna ta faman muzurai ko wanne aljani yana cikin shiga irin ta yaqi irin wacce farsu bai tava ganin irinta ba. A zaue akan wata kujera ta farin qarfe wani dattijon aljani ne xan kimanin shekara dubu takwas yana zaune cikin isa da taqama. Aljanin daya xauko shi ya sauke shi, kafin ya matsa zuwa ga sarkin aljanu ya faxi ya yi gaisuwa, sarkin aljanu ya dubi Farsu dake zaune a bayan aljanin xan tsurut! Da shi kamar ruwan aski yace masa. “Kai bil’adama mai ya kawo ka cikin babbar fadar duniya ta sarkin aljanu Gamsu?” Farsu ya sauko daga bayan aljanin ya dubi sarkin aljanu Gamsu cike da girmamawa sannan ya zube a gabanshi ya yi gaisuwa a hankali yace masa. “Ya mai darja mai girman daraja wanda sarakunan mutane suke shayi, kayi sani cewar na zo ne gareka domin ganewa idanuna wani abu da ake gayaa mani ban aminta ba wanda aka ce duk duniya kai kaxai ne a duniyar mutum da aljan kake da ikon haka” sarkin aljanu gamsu ya dubi Farsu da duban nutsuwa sannan yace masa. ‘Wannan wane abune haka da har duniyar mutane suke girmamani dominsa? Na kuma zamto ni kaxai ne mai iko da shi?” Ya tambayi farsu yana duban shi da idanunsa farsu ya sunkuyar da kansa qasa domin gudun kar sarkin aljanu ya gano qaryar da yake shirin yi masa sannan yace masa. “An ce a duk duniya mutum da aljan kai xaya ne ruhinka yake a cikin kwlba, ma’ana kana iya cireshi daga jikinka idan ka so ka kan ajiye shi a gefe xaya gangar jikinka ta zamo babu ruhi ka zamto tamkar matacce har sai an mayar da ruhin. Don haka na zo domin ganewa idanuwana wannan abin mamakin, wanda ya gagari duniyar sarakunan mutane” Sarki aljanu Gamsu ya dubi farsu da idanunshi da duban nutsuwa ya xauki tsawon lokaci yana dubanshi daga bisani ya nisa a hankali yace masa. “Ina fatan kana da masaniyar domin ‘yarta Gimbiya Lusa ta samu labarin cewar wani jarumi zai zo domin sace ruhina shi yasa ta sauka duniyar mutane domin halaka duk wani jarumi?’ Ya tambaye shi yana tsare shi da idanuwanshi, farsu ya kuma sunkuayar da kansa cikin ladabi sannan yace masa. “Ni ban zamto jarumi ba, face na shahara a wajen zuwa ganin duk wani abun mamaki da bajinta wanda hakan shi yasa da na samu labarin irin wannan bajinta taka ta cire ruhina daga jikinka ya sani na taho domin na ganewa idanuwana. In fatan zan sami biyan buqatar ta a nuna mun wannan abin mamakin” Farsu yace masa. Sarin aljanu Gamsu ya dube shi ya yi murmushi wani turiri ya fita ta cikin qofofin kunuwanshi, sannan a hankali ya cewa farsu. “Tun kafin sarakunan mutane su farka daga bacci mu muka rigaya muka je inda zamu. Don haka bajintata ta yi nisa a duniya ta kuma gagari duk wani bil’adama sai mu gagararun aljanu.don haka zan nuna maka ruhina domin na san ko kayi yunqurin guduwa ba za ka iya kai labari ba, domin rundunar aljanu tafi qarfin duk wani bil’adama” Sarki aljanu Gamsu ya tabbatar masa sannan ya ci gaba da ce masa. “Kayi sani cewar ruhina ya zamto a cikin kwalbar tsafi wanda idan babu shi a jikina zan zamto tamkar matacce har sai an dawo mun da shi jikina an saka mun shi a qirjina yadda yake, don haka ka yi sani cewar za ka zamto xan Adam na farko daya soma ganinsa wanda a duk faxin duniya babu wani mutum ko aljani daya tava ganinsa sai kai, amma idan ka gansa hukunci na gareka shi ne zan halakaka” Da murmushin mugunta ya faxa. Farsu ya yi shiru yana kallon tsohon aljanin da yake gabanshi mai kama da siffar bididigin kwaxo sannan da murya jarumtaka yace masa. “Na amince matuqar burina zai cika na ganin wannan babbar bajinta da wani mahaluki bai tava yinta ba. Kuma na tabbatar zan zama mutum na farko da duniya zata riqa tunawa da shi a matsayin wanda ya tava ganin wannan ruhin naka” Ya kammala maganar yana mai duban fuskar sarkin Aljanu wanda yake dubanshi da haxaxxiyar fuskar data tattare kamar busashiyar fata sannan ya yi dariya yace. “Haka nake son naga mutum ya zamto mai zuciyar jarumta da rashin tsoro, don haka maza ka shirya ganin ruhina yanzu nan” Yace masa yana dubanshi sannan a hankali ya miqe tsaye ya yi wata irin girgiza da ta haddasa tashin wata maxaukakiyar guguwa. A sannu a hankali guguwar ta soma yayewa sannan wasu fuka-fukai suka fito a jikin shi daga bisani suka soma bubuxewa a tsakiyar qirjinshi wata kwalba ta bayyana. Ya dubi Farsu sannan yace “Matso ka ga ruhina”. Cikin jarumta ya tunkareshi ya qarasa gabanshi ya tsaya yana zubawa ruhin na shi da yake cikin kwalba idanu yana kallonshi cike da mamaki. A hankali ruhin yake motsi a cikin kwalba. Cikin tsananin zafin nama na bazata Farsu ya miqa hannu ya cafi ruhin sannan ya fisgoshi daga cikin inda yake. Sarkin aljanu Gamsu ya qwarara wata qara a razane, sannan lokaci xaya ya soma bushewa yana komawa kamar busashen karmami, a haka ya gama bushewa ya zama kamar gunki. Farsu ya dubi ruhin dake hannunsa ya dubi busashiyar gangar jikin sarkin aljanu Gamsu yace masa “Baka san hikimar mutane bane shi yasa ka yi gaggawar amincewa da ni”. Yana gama maganar ya buxe jakarsa da ya yi xamara da ita ya cilla ruhin a ciki sannan ya juya. A lokacin rundunar aljanun da suke a fadar suka zaburo masa domin amsar ruhin sarki aljanu Gamsu. Farsu ya zare takobinsa ya jinjina ta a hannunsa ya dubi yawan rundunar aljannun ya lumshe idanunshi ya buxe ya kuma gyara riqon da ya yi wa takobinsa. Adadin rundunar suka matso ganin sun kusa zuwa gareshi ya sa shima ya nufe su a guje suka gamu a wuri xaya, kasuwar yaqi ta soma ci rayuka suka soma salwanta, mutuwa ta soma shawagi tana farauce rayuka, jini ya soma fantsama kawuna suka dinga yawo a sama kamar tsintsaye makamai suka riqa zubewa qasa daga hannun mariqansu. Yawan adadin rundunar aljanun ya dinga raguwa domin irin yadda Farsu yake farauce ruhinsu yaqi ya ci gaba da tsawaita a garesu mutuwa ta ci gaba da shawagi a tsakaninsu duk wurin daya saka gaba sai dai kaga matattu suna zubowa qasa a haka ya ci gaba da yaqarsu suma suna qara danno shi. Haka suka xauki tsawon kwanaki biyu suna wannan gwagwarmaya shi bai saduda ya gaji ba suma ba su qare ba, yaqi ya ci gaba da gudana mutuwa ta ci gaba da shawagi tana xauke rayukansu. Can bayan tsawon lokaci a lokacin gajiya ta soma kama Farsu ya soma sauya salon yaqin a zuciyarshi yana mai tunanin abinda ya kamata ya yi a lokacin ne bai yi aune ba wata qara gami da walqiya ta cika cikin fadar, sannan lokaci xaya wani baqin aljani mai girman gami da mummunar siffa ya bayyana da ganinsa sai duk rundunar aljanun suka tunzura suka razana suka zubar da makamansu suka ruga a guje. Ya juya ya dubi Farsu ba tare daya ce masa komai ba ya miqa hannu xaya ya damqoshi ya buxe fuka-fukanshi ya tashi sama da shi suka fice daga cikin fadar sarkin aljanu Gamsu. Farsu ya leqo qasa da idanunshi ya dubi gawarwakin aljanun da suke kwance fululu. ** A hankali Gimbiya Lusa ta saka hannu ta xauko jakarta ta buxeta ta xauko wani garin magani ta buxe bakinta ta zazzagashi tana gama haxiye maganin take taji qarfi a jikinta, lokaci guda ta yi murmushi ta yunqura ta tashi ta dubi aljanin daya xaukota cikin murya qasa-qasa tace masa. “Waye ya aiko ka ka tafi da ni?” aljanin ya ci gaba da karkaxa fuka-fukanshi sannan ya bata amsa da cewar “Ni bawan mahaifinki ne sarkin aljanu Gamsu, a yanzu na baro wani bil’adama yana yaqar jama’armu bayan ya sace ruhin mahaifinki” Wannan maganar ta zo wa Gimbiya Luna a bazata, tun data samu wannan labarin ta fita take yaqar duk wani sadauki da take tsammanin zai iya zuwa ya sace ruhin mahaifinta amman ashe qaddara ta riga fata, bata san lokacin data kwarara wani irin ihu ba, take idanunta suka kaxa suka yi ja, saboda tsananin fusata cikin damuwa tace wa aljanin. ‘Qara gaggawa domin mu samu mu qarasa gareshi domin na yi gagawar sadashi da ajalinsa” Aljanin ya qara qarfin karkaxa fuka-fukansa suka tunkari fadar sarkin aljanu Gamsu. A lokacin da rana ta kusa faxuwa Suka qaraso fadar tun daga nesa Gimbiya Lusa ta riqa hango gawarwakin aljanu a kwankwance bila adadi, suka qaraso cikin fadar Gimbiya Lusa ta dubi gawarwakin aljanun dake kwance a cikin jini wani baqin ciki ya lulluve mata rai. Wannan shi ne karon farko da wani ya tava shigowa cikin fadar sarkin aljanu Gamsu ya yi nasara ga rundunarshi. Ta mayar da dubanta ga karagar sarkin aljanu Gamsu, ta gano gangar jikinshi a zaune a kan karagar babu ruhi a jikinsa, da gudu ta nufi wajen da yake taje gabansa ta tsaya tana kallonshi hawaye yana kwaranya daga cikin idanunta. Takaici da baqin ciki ya cika mata cikin zuciyarta, hawayen ta ya ci gaba da kwaranya daga cikin idanunta, ta ci gaba da kallon gangar jikin sarkin aljanu Gamsu. A rayuwarta ta duniya babu wani mahaluki da taji tana matuqar qaunarsa kamar mahaifinta sarkin aljanu Gamsu ta yi matuqar mamaki yadda ta shaqu da shi kamar yadda mafiya yawan lokuta take matuqar mamakin yadda kamanin halitarsu suka bambanta, sau tari tana iya lokutan da take kallon surata a jikin madubi, sannan ta dubi ta kuyanginta ‘yan matan aljanu sai taga akwai matuqar bambanci sosai da su, domin ita tsarin jikinta jiki ne mai santsi babu gashi sai farar fatarta da take faman sheqi da xaukar idanuwa. Qafafunta suna tattare da ‘yan yatsu su kuma dukansu suna da kofato tamkar na dawakai, tsarin surasu bai yi kama ba sam. Sau tari idan sun so sukan sauya kamanin halittarsu daga kyawawa zuwa munana, amma ita bata iya sauya kamani kamar yadda suke sauyawa. A lokacin tana da quruciya ta sha tambayar mahaifinta sarki aljanu Gamsu ko mai yasa kamaninta suka bambanta da na su kamanin? Mafi yawan lokuta yakan dubeta sannan yace mata. “Akwai lokacin da za ki gamu da wasu halita waxanda zubin halitarku iri xaya ne” Wannan maganar ya tabbatarwa Gimbiya Lusa bambanci da take gani a bayyane yake. Lokacin farko data soma shigowa cikin bil’adama data ga jinsi mai irin nata sai mamaki ya cikata, ta kuma haqiqance a cikin ranta wannan zubin halitar sune jinsinta sune ‘yan uwanta amma da yake ba buqatar sanin asalinta da halittarta ne ya fito da ita ba don haka bata mayar da hankali kan haka ba. A lokacin ta fito ne domin nemo sadaukin da aka bata labarin zai zo ya sace ruhin mahaifinta. Duk data samu nasara kashe sadaukai, amman nasara bata yi mata amfani ba, ta gama farauce rayukan jaruman wanda suka yi suna suka sami xaukaka a duniya amma wani baqar fata wanda ba a saka shi a cikin lisaffin jaruman duniya ya zo ya sace ruhin. Wannan shi ne anyi ba a yi ba! Ta rufe qofa da varawo. Duk abubuwan da suke ta faman zuwar wa Gimbiya Lusa a rai, suka gama zuwar mata, ta dubi makamanta da kayan yaqinta bata buqatar sauya wasu ta mayar da dubanta ga sarkin aljanu Gamsu da yake zaune babu ruhi a jikinsa taji damuwarta ta qaru da fusatar zuciya tace “Halaka ta tabbata a gareka maqasqancin bawa, tabbas gani nan zuwa gareka domin farauce ranka” Da xaga murya tace, a lokaci xaya ta dubi aljanin daya xakota tace masa/ “Ka xaukeni bisa gaggawa ka kani domin riskar ABOKIN GABA domin mu yi GABA DA GABA da shi” Tana gama maganarta tayi tsalle ta haye bayansa shi kuma aljanin ya buxe fuka-fukansa ya tashi da ita sararin samaniya. Gimbiya Lusa ta jiyo ta dubi gangar jikin sarki Gamsu lokaci xaya tana jin hawaye suna kwaranyo mata, a hankali ta kai hannunta ta shafi takobinta. ‘Zan ladaftar da kai BAQAR FATA’ tace a ranta. SADAUKI ANSAR Yana kwance cikin tagaiyara da fidda rai daga tsammanin ci gaba da rayuwa, domin irin raunikan da suke jikinsa. Lokaci zuwa lokaci ya kan xan tuna cewar wannan shi ne yaqi xaya a duniya da suka tava kare jini-biri-biri-jini da abokin gabarshi. A irin jarumtar da yake da ita babu wani sadauki da ya tava xaukar sa’a xaya a gabanshi ba tare da ya farauce ranshi ba. Amman sai gashi mace ta wanzu tsawon wasu lokuta a gabanshi suna xauki ba daxi. Wannan abun mamaki ne ga sadauki mai sadaukantaka kamar Ansar wannan baqon abu ne a gareshi da bai tava tsammanin faruwarshi ba. A hankali ya xaga idanunshi ya dubi ungulayen da suke ta faman shawagi a sararin samaniya suna jiran ya hallaka domin su samu suyi kalaci da namanshi. A hankali ya buxe bakinshi ya soma faxin “Allah kai ne ubangiji xaya wanda ya halicci komai, kai muke bautawa, Allah kar ka wulaqanta gangar jikina na zamto na hallaka na zamto abincin ungulaye, Allah ka suturta gangar jikina”. Ya gama addu’ar tashi yana mai lumshe idanunshi a lokacin ya ji saukar wani abu a kusa da shi ya yi saurin buxe idanunshi ya dubi abinda ya sauka a kusa da shi. Wani farin aljani ne mai kyawun siffa daga cikin jinsi aljanu dudud shekarunsa ba za su gaza xari uku zuwa huxu ba, wannan aljanin ya zamto mai ganiyar quruciya a jikin shi kuma mai ji da sadaukantaka. Yana sauka ya dubi sadauki Ansar yace masa “Ungulaye ba za su ci gangar jikinka ba domin ranar mutuwarka ba yi ba” Yana gama faxar hakan ya yi gaggawar xauko wata buta ya zubawa sadauki Ansar wani ruwan da yake cikin butar a gangar jikinsa nan da nan sadauki Ansar ya soma jin qarfin jikinshi ya soma dawowa jikinshi. Bayan wucewar awanni uku sadauki Ansar ya ji duk wata gajiya da wajen da yake masa ciwo ya daina, ya zamto tamkar wani abu bai tava samunshi ba, ya dubi farin aljaninan da duban girmamawa sannan a hankali yace masa. “Godiya gareka da ka zamto ka taimakaeni ka kuvutar da rayuwata” Sadaukin Ansar yace masa. Shi kuma ya dubi Ansar a hankali yace masa “Sunana aljani zammaru na zamto xaya daga cikin ‘yan qabilar bamu shammat, kuma na zamto daga cikin jinsi aljanu mabiya addinin musulunci na zo ne domin na taimakeka na kuvutar da kai daga halaka, domin duniya tana buqatarka idan ka halaka za a rasa jarumin da zai sasanta rigimar da zata mamaye duka duniya ta sace ruhin sarkin aljanu gamsu” Sadauki Ansar ya dubi Aljani zammaru da matuqar mamaki sannan yace masa. “Ta ya zan sasanta rigimar da dominta aka so hallakani? Ni musulmine babu ruwana da abinda ya shafi kafirai” Ya tabbatar masa. Aljani zammaru ya yi murmushi sannan yace “Akwai matsala babba tun da aka sato ruhin sarki aljanu Gamsu matsalar ita ce sarkin aljanu Gamsu ya zamto adalin sarki mai taimakon talakawa mai kare addinin musulman aljanu duk da cewar ya zamto shi ba ma’abocin musulunci bane, hakan yasa a lokacin da aka sace ruhin na shi duk wani musulmin aljani ya shiga cikin fargaba da tsoro domin sun san za su soma samun tursasawa daga sauran azzaluman sarakunan aljanu, shi yasa na zo gareka domin neman ka taimaki musulmai ‘yan uwanka a sassanta a dawowa da adalin sarki ruhinsa ko ma ci gaba da ibada a cikin kwanciyar hankali ba tare da zullumi ba”. Sadauki Anwar ya yi shiru na tsawon wani lokaci yana tunani daga bisani ya xago da kanshi ya dubi aljani zammaru yace masa. “Na yadda zan nemo wannan ruhin duk inda yake domin mayarwa da sarkin aljanu Gamsu koda hakan yana nufin sai an gabza yaqi, da izinin Allah nasara tana gareni” Ya kammala maganar yana dubansa kafin ya qara da cewar “Yanzu ina za mu riski wanda ya sace wannan ruhin?” Aljani zammaruu ya dube shi sannan ya bashi amsa da cewar. “Wata bokanya ce baqar fata, ta saka wani hatsabibin bawanta shima baqar fata ya sato wannan ruhin, domin haka za mu iya riskarsa a hanya kafin ya qarasa zuwa gareta” Sadauki Ansar ya girgiza kanshi cikin gamsuwa sannan yace wa aljani zammaru “Za mu iya yin gaggawa domin zuwa riskarsa” Yana gama maganar ya yi tsalle ya haye bayan aljani zammaru lokaci xaya shima ya buxe fuka-fukanshi ya tashi da shi sararin samaniya. Suka bi bayan baqar fata bawa Farsu daya sace ruhin sarkin aljanu Gamsu. BAQAR FATA BAWA FARSU Yana zaune a bayan aljani a ranshi yana jinjina irin girman siffa da muni da wannan aljanin yake da shi. Suka zo tsakiyar wani teku mai girma da faxi, tun da farsu yake a rayuwarsa bai tava ganin teku mai girma tamkar wannan ba. A hankali ya leqo da kanshi yana kallon ruwan tekun yana cike da al’ajabi. A dai-dai lokacin da suka zo dai-dai tsakiyar tekun a lokacin tamkar walqiya su Gimbiya Lusa suka bayyana a gabansu. Aljanin da yake xauke da Farsu ya dakata da tafiya da yake yi cike da tsoro da fargaba. Ganin ya dakata yasa Farsu ya dawo da hankalinsa gabansa idanunsa suka gane masa su ya girgiza kansa cike da jimami. A hankali su Gimbiya Lusa suka matso daf da juna ta miqe tsaye daga kan aljanin da take kai, tana zuwa dai-dai inda aljanin da Farsu uake kai ta daka wani tsalle ta dawo kanshi. Farsu ya yi gaggawar miqewa domin ganin ganin abinda ya faru, suka tsaya suna kallon-kallo da shi da Gimbiya Lusa. Cikin tsananin hasala tace masa. “Na zo domin amsar ruhin mahaifina sarkin aljanu Gamsu wanda ka sace” farsu ya dubeta a fusace shima yace mata “Amman kin yaudari kanki ‘yar budurwa da kike kiran aljani mahaifinki, kin tava ganin aljani ya haifi mutum? Sannan saboda tsananin ganganci shi ne za ki sadaukar da rayuwarki domin ki halaka kika biyoni domin amsar ruhin” Ya saurara kafin ya qara da cewar. “Yar kyakkyawar budurwa duk kyawun surarki hakan ba zai hanani saka takobi na a tsakiyar siririn wuyanki na raba kanki da kyakkyawan gangar jikinki” Ya gama magana yana mata wani shu’umin murmushi. “Kai baqar fata gafalalle kayi sani cewar ni ce Gimbiya Lusa mai maganin duk wani xan iska! Dan haka ka bani ruhin da ka sato cikin ruwan sanyi ya fiye maka kafin wannan mummunar baqar fuskar taka ta gamu da azabar kaifin takobina wacce bata san komai ba sai shan jinin sadaukai ma su ji da jarumtaka da taurin kai” Cikin murya tsawa-tsawa tace masa. Farsu ya dubeta a fusace cikin daka tsawa yace da ita “Ahir! Xinki da dubana ki gayamun irin waxannan kalaman bana tunanin akwai wani jarumi da zai iya tsoratani da jarumtakarsa ko kalamansa na kurari na baki, balle ke mace mai raunin jarumtaka” Gimbiya Lusa ta girgiza kanta cikin tsananin takaici ta sassauta murya tamkar mai yi masa raxa tace da shi cikin fushi. “Ka yaudari kanka da har kake tunanin gwara na amshi ruhin da tsananin jarumtaka, a yanzu ne za ka san cewar ka yi gagarumin kuskure kuma zaka rabe tsakanin aya da tsakuwa, domin yanzu zan farauce ranka na kuma cilla wannan mummunar gawar taka cikin teku” Tana gama faxa masa ta zare takobinta lokaci xaya ta dubeshi tace “Yau zamu yi gaba da gaba da kai domin sanin bambanci a bayyane yake”. Ta sake yin murmushi. “Ni da kai ABOKAN GABA ne, don haka mu kan iya soma farautar rayukan junanmu” Tana gama maganar ta kai masa wani wawan sara da zumar tsinke zaren da yake sarqe da ruhin cikin zafin nama ya kaucewa saran sannan ya wuce tare da wani hucin iska mai qarfi. Farsu ya dubeta ya girgiza kanshi, sannan ya gyara riqon takobinsa. Suka yi xauki kan junansu lokaci xaya suka gauraya da mummunan artabu a wuri xaya suna musayar kai sara da suka.qara gami da tartsatsin haxuwar makamansu ya karaxe sararin saman tekun. Ko wannensu ya himmatu domin ganin ya samu nasara akan abokin gabansa. Gimbiya Lusa ta samu Farus ba yanda ta yi tsamaninsa ba, domin ta same shi dakakken namiji mai tsananin jarumtaka, turjiya gami da zafin nama. Haka shima Farsu ya sami Gimbiya Lusa cikakiyar jaruma mai qarfin damtse da zafin nama wajen kai sara da kare kanta. Jarumar da tafi jarumai da dama qwarewa da sanin salo-salo na yaqi. Haka suka ci gaba da mummunan gwamza yaqi mai tsananin ban mamaki a tsakaninsu, suka wanzu wajen kaiwa junansu miyagun sara da suka da niyar farauce ran juna. Bayan sun xaki dogon lokaci suna wannan fafatawar a lokacin wani abu ya sauka a tsakaninsu. Jin saukar abin shi ne ya tilasta musu dakatawa da yin yaqin su duka suka dubi abun. A lokacin idanun Farsu ya sauka akan Bokanya Namsu uwar gidanshi da ta saka shi aikin idan ya sami nasara zata ‘yanta shi. Ganinta ya saka ya ji wani daxi ya lulluve shi. Bokanya Namsu tace masa cikin sassauta murya. “Maza miqo mun ruhin naga ko wannan qaramar qwaruwar zata iya amsa a wajena, kai yanzu ka kammala aikinka ka gama yi mun bauta don haka na ‘yanta ka” Waxannan kalaman sun matuqar qayatar da zuciyar Farsu. Don haka cikin gaggawa ya miqa hannu ya xauko ruhin daga cikin inda ya adana shi ya dubi Bokanya Namsu itama ta dubi Ruhin. Gambiya Lusa ta dubi ruhin mahaifinta sarkin Aljanu Gamsu. Ba su yi aune ba sai jin dirar wani abu suka kuma ji Yif! Kamar an sauke nannauyan dutse cikin gaggawa suka kai kallonsu idanun Farsu ya kuma ganin wata Bokanya Namsu a tsaye ya dubeta cikin tsananin mamaki yanzu sun zama su biyu ma su kama iri xaya sak kamar an tsaga kara. “Wace ce kenan ta gaskiyar?” Ya tambayi kansa kamar amsar tambayarsa ya ji ance masa. “Ni ce uwar gidanka Bokanya Namsu” Da kakkausar murya tace masa. Xayar itama ta matso gareshi tace masa “Ni ce uwar gidanka Bokanya Namsu”. Farsu ya zuba musu idanu yana kallonsu cikin ruxani ya kasa tantance wace ce ta gaskiyar wace ce ta qarya. A lokacin aljani Zammnaru ya qaraso shima xauke da sadauki Ansar a bayansa shima ya bi ruhin da kallo ya mayar da kallonsa ga Gimbiya Lusa sanna ya haske mata fuska da murmushi lokaci guda kuma cikin tsananin zafin nama ya zare takobi ya kaiwa farsu sara a hannun da yake xauke da Ruhin sarkin Aljanu Gamsu take ruhin ya zame daga hannunsa ya yi qasan teku. Farsu ya juya ya dube shi ya kuma dubi Gimbiya Lusa yace mata “To kyakkyawa ruhin mahaifinki ya faxa cikin teku, ko za ki biyoni cikin tekun mu ci gaba da fafatawa” Yana gama maganar ya sulmiyo daga kan aljanin ya biyo ruhin daya sulmiyo qasan teku. Gimbiya Lusa ta girgiza kanta tunda take a rayuwarta ba ta tava ganin hatsabibin mutum kamar wannan baqar fatar ba. Itama ta daka tsalle ta biyo bayanshi. Ganin haka ne ya sa sadauki Ansar shima ya sulmiyo ya yo qasa shima ya biyo bayan Ruhin sarkin Aljanu Gamsu da ya yo qasan taiku. A cikin tekun sarauniyar aljanun cikin ruwa ta tara mayaqanta suna tsaye suna sauraren qarasowar ruhin sarkin aljanu Gamsu. Tun kamin shekaru xari uku Bokanta ya faxa mata cewar Ruhin zai faxo a nan wurin tun lokacin ta zauna zaman jiran faxowarsa. Ruhin ya faxa cikin ruwan tekun ya zamto tamkar an cilla wani nannauyan dutse mai nauyi lokaci xaya ya yi qasan teku. Sarauniyar aljanun cikin ruwa tana zaune akan karagarta tana jiran faxowar ruhin. Tsayin shekara xari uku kenan tana zaune zaman jiran faxowarsa. A lokacin da bata yi aune ba taji faxowar abu akanta tayi gagawar buxe idanunta ta dubi abin da idanunta suka gane mata abinda ta jima tana zaune zaman jira tsawon shekaru, tabbas Ruhin sarkin aljanu Gamsu ne wani daxi ya mamaye cikin zuciyarta da gaggawa ta miqe cikin azama ta miqa hannunta ta xauki ruhin ta zuba masa idanu tana kallonsa. Ta juya cikin gaggawa ta xagashi sama a gaban idanun jama’arta cikin xaga murya tace musu “Abinda muka jima muna zaman jiran shi yau mun same shi” Duka hankalin dakarun ya tattara akanta suka zuba mata idanuwa suna kallon ruhin sarkin aljanu Gamsu da yake riqe a hannunta sannan lokaci xaya suka ruxe da shewa da kururuwa suna ma su xaga makamansu sama. A lokacin Bawa Farsu ya faxo tsakiyar wurin ya miqe tsaye da matuwar mamaki domin a tsammaninsa zai yi nutsu a cikin ruwa ya yi qasan tekun amma ga matuqar mamakinsa sai ya ga ya faxo tsakiyar wani fili mai yanyame da dakarun aljanu cikin shirin yaqi. Ya zuba musu idanu yana kallonsu suma suka zubo masa idanu aka soma kallon-kallo a tsakaninsu kamar akuya da kura. A lokacin suma su Gimbiya Lusa suka faxo tsakiyar wurin suka miqe tsaye suka zubawa wurin idanu cike da matuqar mamaki. Sarauniyar aljanun cikin ruwa ta dube su cikin mamaki lokaci xaya yanayin fuskarta ya sauya daga farin ciki zuwa vacin rai ta dubi Ruhin sarkin aljanu Gamsu da yake hannunta ta yi murmushi sannan ta buxe wata jaka da take xaure a gefen qugunta ta saka Ruhin a ciki ta mayar ta rufe kafin ta mayar da dubanta zuwa ga su Farsu dake tsaye carko-carko kamar wasu zakaru cikin murya tsawa-tsawa tace musu. “Kai baqar fata wanne irin shisshigine ya kawoka cikin fadata” Farsu ya dubeta cikin nutsuwa kafin ya bata amsa. “Ni ne baqar fata Farsu na zo ne domin amsar Ruhin da yake hannunki domin bai dace da ke ba” Maganarshi ta zamto tamkar sukar kibiya a cikin zuciyar sarauniyar aljanun cikin ruwa, ta yi zaman shekara xari uku tana jiran abu yau ta same shi sannan wasu za su ce sun zo domin su rabata da shi? Ta dube shi sheqeqe. “Babu makawa duk duniya babu wani wanda yake da jarumtar da zai iya amsar wannan Ruhin daga hannuna, idan kuma akwai jarumi to yana iya gwadawa” Cikin izza ta faxa. Gimbiya Lusa ta dubeta sannan cikin xaga murya tace mata “Na yi zaton mutane ne kawai suke son sace ruhin mahaifina sarkin aljanu Gamsu, ashe ba haka bane a cikin duniyar aljanu ma akwai masu buqatar shi, don haka ina mai tabbatar miki cewar za ki zamto aljana ta farko da zan soma sadarwa zuwa ga ajalinta” Jin haka yasa sarauniyar aljanun cikin ruwa ta yi dariya sannan ta nunata da yatsa tace mata. “Duniya ta daxe da wayewa Gimbiya Lusa don haka na gaba ya yi gaba” Gimbniya Lusa itama ta xaga hannu ta nunata. “Babu makawa zan dawo da na gaba baya, domin duk tsohon da bai ji kunyar hawa jaki ba to shima jaki ba zai ji kunyar kayar da shi ba. Da mai jini a jika shi ne wanda zamani yake tafiya da shi, don haka ke mai tashe ce ni kuma mai zamani, saboda haka za ki bani ta lumana ko kuwa sai kin ga jinin sadaukanki yana malala tamkar magunar ruwa” Maganar ta zamto tamkar ta watsawa sarauniyar aljanun cikin ruwa wuta a zuciyarta cike da fusata ta dubeta. “Lallai za ki yi nadamar wannan furucin naki, domin sai na ladaftar dake bisa kuskuren da kika yi” Tana rufe baki ta dubi yawan dakarunta da suke mamaye da wajen cikin isa da qasaita tace mu musu “Maza ku yi mun maganin waxannan qananin halitar” tana rufe bakinta dakarun suka zaburo a fusace makamansu a zare za su yi sukuwar sallah akan su. Hausa qarasowa zuwa garesu suna tsaye suna kallonsu, sai da ya zamto baifi sauran taku goma ba sannan Ansar ya daka musu tsawa, wanda hakan ya haddasa musu tsawa waj e xaya lokaci guda yace wa sarauniyar aljanun cikin ruwa. “Kin yi babban kuskure wurin turo dakarunki domin su yaqe mu, don haka ki saurara kiga yadda za mu qare da su kafin mu qaraso gareki” Yana gama maganar ya zare takobinsa sannan cikin azama ta bazata ya yi xauki garesu, ganin tahowarsa yasa suma dakarun suka kuma zaburowa suka gamu a tsakiya kasuwar yaqi da saye da sayarwa rayuka ta soma ci mutuwa ta soma shawagi tana farauce ruhin aljanun cikin ruwa. Masifa irin ta yaqi ta dunga sauka a wurin kai sara da kai suka ya yawaita zubar jini da malalarsa ya wanzu a wurin qasan tekun ya hautsine wanda hakan yasa ruwan tekun ya soma tambal-tambal tamkar zai malalo cikin duniya. Bawa Farsu ya zamo tamkar wata annoba ta wuta a cikin tsakiyar gonar auduga domin duk wurin da ya sa kai sai dfai ka ga kawuna suna yawo a sama tamkar tsuntsaye, jikuna suna zubewa qasa babu kawuna haka itama Gimbiya Lusa ta wanzu tana saukar musu da azabar yaqi. Kafin wani lokaci sun yiwa rundunar fata-fata sai tsirarun xaixaikun dakarun suka rage ganin sun zama tsiraru ya saka sauran suka yadda makamansu suka yi mubaya’a. ganin haka ya sa ran sarauniyar aljanun cikin ruwa ya matuqar dugunzuma ta dube su cikin tsawa tace musu “Qasqanci ya tabbata a gareku halaka ta zama dole a gareku” Tana gama maganar ta zare takobinta dake xaure a xamarata sannan lokaci xaya ta tunkaresu da zumar ta yaqe su ganin irin wannan tahowar da ta yi ya sa bawa Farsu ya taryeta tun kafin ta qaraso suka yi wata muguwar haxuwa takubbansu suka gamu a wuri xaya, wata qara mai qarfi ta cika wurin sannan wata wuta ta buga ta yi sama, suka soma musayar sara da suka a tsakaninsu zuwa tsawon lokaci, ganin lokaci yana tafiya a banza ya sa bawa Farsu ya tunzura ya qara qaimi wurin kai sara da suka gareta can ya xauki numnfashinta ya kai mata wani kaitattacen sara a wuya da zumar tsinke mata kai. Ganin tahowar saran ya sa sarauniyar aljanun cikin ruwa yin qoqarin kaucewa domin kar saran ya sameta amman ta makara domin sai da saran ya sameta kaxan a wuyanta. Ba don wata sarqa da take rateye a wuyanta ba wacce saran ya tsaya akanta, amman banda haka da saran ya yi tasiri akanta da tuni wani labarin ake yi ba nata ba. Sarqa ta zamo daga wuyanta ta sulmiyo ta yo qasa. Bawa Farsu ya ga tahowarta ya miqa hannunsa ya taryota ya riqeta a cikin tafin hannunsa ya yi zamiya yana kallonta. Ita ma ta dube shi na wani lokaci, a tsawon rayuwarta yau ita ce ranar farko da wani sadauki ya tava wanzuwa a gabanta tsawon lokaci har ya ke qoqarin samun nasara akanta, a rayuwarta bata xaukar wani tsawon lokaci suna fafatawa da wani sadauki, sai ta farauce rayuwarsa amma ga mamakinta sai ga baqar fata ya zamar mata ciwon ido. Suka zubawa junansu idanu suna kallon juna bawa Farsu ya dubi sarauniyar aljanun cikin ruwa ya dubi sarqa da take riqe a hannunsa ya xagata sama ya nuna mata ita ta bi sarqa da kallo cike da mamaki da baqin cikin ganin ya qwace ta daga gareta annurin da ya yi saura akan fuskarta ya soma narkewa daga kan fuskarta. Tana gama kallon sarqa da Bawa Farsu ya xaga mata akan fuskarta sai ta juya ta dubi hanya sosai sannan tace masa “Wannan sarqa da ka xagata akan idanuna dole na gudu tunda ka xagata na ganta da idanuna, domin sirrin tsafin dake jikinta, amman ba don haka ba da yau sai na halakar da ruhinka, don haka ka jirani a haxuwa ta gaba da za mu yi”. Tana qarasa faxar haka ta dubi hanya ya falfala da wani azababben gudu kafin su farga har ta vace musu daga gani. Bawa Farsu ya bi sarqa da kallo cike da mamaki ya juya ta zuwa ga su Gimbiya Lusa da sadauki Ansar ya fuskance su sosai yana kallonsu cike da mamaki ita kuma sarqa sai qyalqyali take tana xaukar idanu Gimbiya Lusa ta miqa hannu zata amsa Bawa Farsu yace mata. “Dakata” Ga matuqar mamakinsa sai yaga ta qame tamkar gunki ya dubeta sosai ya yi murmushi ya nuna sadauki Ansar da ita shima yace masa “Qame!” Take Ansar ya maqale shi ma tamkar busashen itace. Bawa Farsu ya dube shi a qame kamar busasun itatuwa ya qyalqyale da dariya cike da gamsuwa ya matsa gaban Gimbiya Lusa ya shafi fuskarta a hankali yace mata. “Qaramar mara kunya”. ** Bokanya Namsu ta dubu xayar da take tsaye a kusa da ita da duban matuqar mamaki mai matuqar yawa domin ganin matuqar kama da su ka yi da junansu. Ta yi murmushi akan faffaxar fuskarta sannan cikin murya fushi tace. “Ka yi mana asara biyu, dukkanmu mun rasa abin don haka kakan iya dawowa sufaffarka ta ainahi kafin na halakaka bisa wannan zunibin da ka aikata mun” tana gama maganar tana duban xayar da ke tsaye a gabanta, aka yi wata dariya mai xauke da isgilanci sannan cikin taqama aka ce mata “BOKA SHARBANGA shi kaxai ne wanda ya kamata ya mallaki ruhin sarkin Aljanu Gamsu domin na fi kowa sanin muhimmancinsa a duniyar mutane, domin haka kafin ki halakani ni yanzu zan salwantar da ruhinki domin ke kaxaice bokanya da za ki iya bani matsala a cikin lamarina’. Ya gama maganar yana mai yin wata girgiza tamkar tsuntswa nan take duk kayan da suke sanye a jikinsa suka zube a qasa, ya komo ainahin surarshi ta ainahi, wato namiji basamuden qato mai mummunan kama ya dubi Bokaya Namsu ya yi murmushi. Ta dubeshi itama cikin tsananin fushi mai tarin yawa tace masa. “A yau bokanya xaya a tsakiyar mazaje zata daka maka gumba a hannunka, ta nuna maka cewar akwai bambanci tsakanin aya da tsakuwa” Ta gama maganar tata tana mai miqa hannunta cikin gashin kanta ta zaro wani xan guntun itace ta cilla masa shi, take wuta ta kama itacen ta soma ci ganga-ganga lokaci xaya aljanin da suke kai ya kurma wani ihu mai tunzura zuciya sannan lokaci xaya wutar ya narkashi ya narke tamkar ruwa, ya riqa xiga yana zagwanyewa lokaci guda wutar ta doshi Boka sharbanga. Bokanya Namsu ta miqe ta yi sama tamkar wata tsuntsuwa ta tsaya akan iska ta bi wutar da kallo tana da tabbacin ta gama halaka boka sharbanga. Wutar tana zuwa wurin da boka sharbanga yake tsaye ya narke ya zama ruwa wutar ta ratsa ta cikinsa, wuta da ruwa suka bada wata qara sannan lokaci xaya wutar ta mutu boka sharbanga ya yi dariya yana kallonta yace mata. “Ke qaramar mara kunya maza bisa kanki” Yana rufe bakinsa ya yi wata fitar burtu ya tasar mata yana zuwa kusa da ita suka sake tashi a sama kamar tsuntsaye, nan take ya buxe qirjinsa suka taso suka qaxa qirji da qirji nan take suka yi baya kamar an watsa yakuwa a cikin teku, suka sake tasowa juna a guje suka yi suka yiwa juna karo kamar raguna suka yi baya taga-taga. Wajen da suka yi gware take ya fashe jini ya soma zuba boka sharbanga ya miqa hannunsa sama take wata takobi ta bayyana ya yi xauki akan bokanya Namsu kafin ya qarasa gareta itama ta miqa hannu cikin iska, lokaci guda wata takobi ta bayyana a hannunta itama tayi xauki kansa suka yi wata gamuwa mai muni suka soma kaiwa junansu sara da suka ko wanne yana qoqarin farauce rayuwar xan uwansa duk wanda ya sari wani a cikinsu sai dai kaji kamar wani qarfe da qarfe ne suka gamu a waje guda. Haka suka tafiyar da tsawon lokaci suna faman fafatawa a tsakaninsu ba tare da wani a cikinsu ya sami nasara akan xan uwansa ba, can suna cikin wannan gumurzun sai Boka sharbanga ya faki numfashin bokanya Namsu ya zaro wata farar hoda daga cikin jakarsa ta bokanci ya watsa mata. Hodar tana sauka a jikinta nan take ta soma jin jikinta duk ya saki, ta saki makamin da yake hannunta sannan lokaci guda ta zube a qasa, ya dubeta a wulaqance sannan ya qyalqyale da dariya. “Wanda ya fiki himma ya riga ya sha kanki, don haka yanzunnan zan halaka ki”. Yana gama maganar shi ya buxe jakar bokancinsa ya xauko wata wuqa da aka yi da qashin haqarqarin mutum ua xago da idanunshi ya kalleta gami da qyaqyacewa da dariya kafin ya sake cewa da ita. “Duk duniya babu wani mai sihiri da wannan wuqar ba zata huda shi ba, don haka yanzunnan zan halakar da ruhinki, ki zamto tamkar ba a tava yinki na doron qasa ba” Yana gama maganar tashi lokaci xaya ya xaga wuqar a sama ya dubi qirjinta daidai inda zai luma wuqar sannan yace mata. “Sai wata rana ABOKIYAR GABATA, Bokanya Namsu” Yana gama maganar ya nufi qirjinta cikin sauri da zumar soka wuqar a gaban qirjinta. ** Sarauniyar aljanun cikin ruwa ta wanzu tsawon lokaci tana tafiya babu qaqautawa ita da kanta tana da masaniyar duk duniya babu wani mahaluki da yake da gaggawar da zai iya biyo bayanta har ya cimmata don haka ganin ta yi nisa da wurin su bawa Farsu sai ta rage gaggawar da take yi ta samu wuri ta tsaya. A hankali ta miqa hannunta ta shafi wuyanta cike da takaici da baqin ciki domin rasa sarqarta da ta yi. Duk duniya babu abinda tafi qauna a rayuwarta kamar sarqa domin duk wani sirri nata ya ta’allaqa a jikinta. Duk abubuwan duk abubuwan ba su ne vacin ranta ba, babban vacin ranta na rashin samun damar buxe jakar da ta saka ruhin sarkin aljanu Gamsu wanda dole sai ta yi amfani da sarqa ta zata buxe jakar. Wannan abun shi ne abu mai muni da sarauniyar aljanun cikin ruwa ta tava cin karo da shi a tsawon shekarunta da ta yi a duniya. Ta xaga kanta sama ta soma qoqarin tunani da zumar ta tunano hanyar da zata bi domin ganin ta samo mafita akan abinda ya dameta. Abubuwa da yawa suka yi ta zuwar mata cikin ranta, amma duk ba su haska mata tunanin yadda zata dawo da sarqarta ba. Haka sa’o’i masu dama suka wuce tana faman tunane-tunane bayan tsawon lokaci wata dabara ta faxo mata, wannan dabarar ba qaramun faranta mata rai tayi ba, domin ta yi imani itace hanya guda da zata dawo da sarqarta gareta cikin ruwan sanyi. Don haka cikin gaggawa ta miqe tsaye ta lalubi gefen qungunta ta xauko wani madubin tsafi ta dubi kanta a ciki ta yi murmushi sannu a hankali ta soma karanto wasu xalasimai na tsafi tana duban kanta a jikin madubin, bata xauki wani lokaci a haka ba take kamaninta suka soma juyewa zuwa na bil’adama. A hankali ta juya kama zuwa ga surar mace baqar fata mai kyawun gaske, yadda duk wani namiji idan ya kalleta sai ya yi mafarkin kyawunta, ta dubi kanta a jikin madubin har sheqi take yi tamkar ta shafa shuni a jikin fatarta, ga manyan fararen idanu da jan shacin bakinta tayi wa kanta tattausan murmushi a hankali tace. “Wannan surar Gimbiya Zailu na aro, duk duniyar baqaqe babu mai kyawunta zan yaudari baqar fatar nan na amshi sarqata daga hannunsa kafin na halakar da ruhinsa ya zamto na shafe shi daga doron qasa” Ta qarasa magana tana qyaqyacewa da dariya kafin lokaci guda ta nufi wajen teku ta wajen da tana da tabbacin tanan su Bawa Farsu za su fito. Iska teku ta ci gaba da kaxawa a hankali. ** Tsawon lokaci suka xauka a tsaye a wurin bawa farsu yana kallonsu yana yi musu dariya. Kafin ya miqa hannu ya xauki sadauki Ansar ya mayar da shi can wani wuri yua ajiye shi, ya xauko wasu sassa na gawarwaki halittun da suka yi yaqi da su ya xoxxora masa a jikinsa. Ya dawo itama Gimbiya Lusa ya zuba mata idanu yana kallonta ya qare mata kallo a hankali. Ban tava tsayawa na qare miki kallo ba sai yau, ashe daman haka kike da tsantsar kyau, ya saurara yana dubanta ya dubi idanunta da suke a buxe manya da su, farare qal. “Tunda nake a rayuwata ban tava ganin kyawawan qwayar idanuwa kamar naki ba, surarki zata xauki hankalin sarakuna da attajirai ma su ji da kansu” Ya kammala maganar yana dubanta. Ya juya ga sadauki Ansar yace masa “Ka koma yadda kake” Yana faxar haka sai sadauki Ansar ya ci gaba da motsi kamar yadda ya ke a baya, ya tsaya yana duban kansa cike da mamaki ya mayar da kallonsa ga Bawa Farsu yaga yadda ya tsaya a gaban Gimbiya Lusa cikin tsawa yace masa. “Meye haka? Maza ka matsa daga wajenta” Ya juyo yana dubansa fuskarsa xauke da murmushi. “Kana da alaqa da ita ne?” Ya jefa masa tambayar sadauki Ansar shima ya tsare sa da ido. “Wanne sihiri ka samo kake aikatawa a gare mu, don haka ina mai sanar maka lallai kayi gaggawar rabuwa da shi, idan kuma ba haka ba zan amshe shi da qarfin tsiya na lalatashi” Kalamansa ya baiwa bawa Farsu dariya ya fuskance shi sosai sannan yace masa. “Bana jin akwai wani sadauki da zai iya amsar wannan abun daga hannuna da zunzurutun jarumtaka don haka idan kana ganin cewar za ka iya to ga fili ga mai doki, daga ni sai kai sai kuma Gimbiya Lusa” Ya gama maganar yana mai dubanta “Ci gaba da rayuwarki” yana rufe bakinsa itama ta dawo yadda take ta dubi kanta cike da mamaki, ta mayar da kallonta ga sadauki Ansar cikin mamaki ta tambaye shi. “Kaima abinda ya faru da ni ya sameka?” ya gyaxa kai. “Ga wanda ya aikata mana sihirin tsafi, kuma yanzu nan zan ladaftar da shi akan wannan laifin daya aikata mana. Domin zan amshi sihirin na lalata shi”. Gimbiya Lusa ta juya ta dubi Bawa Farsu a fusace tace masa gwara tun cikin ruwan sanyi ka bamu sihirin da ka aikata akanmu mu lalatashi domin idan ba haka ba zamu amshe shi da qarfin tsiya, sannan mu mayar da shi kanka” Bawa farsu ya dubeta ya yi murmushi kafin yace mata. “Ba irin mu ake yiwa barazana ba domin mun sha jarumtaka a nono, mun zama dutsen dake cikin ruwa bamu san ana rana ba. Saboda haka duk wanda yake ganin zai iya amsa da qarfin damtse to ga fili ga mai doki” Ya gama magana yana dubansu. Sadauki Anwar ya miqa hannunsa ya zaro takubinsa ya riqeta sosai a hannunsa ya dubi Bawa Farsu ganin haka shima ya zare nasa makamin ya dubi sadauki Anwar suka fuskanci juna ko wanne a cikinsu yana jujjuya makaminsa. Tsawon lokaci suna tsaye carko-carko kamar zakaru kafin daga bisani Anwar ya yi xauki ga bawa Farsu da zumar ya yi tafiyar guguwa da shi,ganin tahowarsa ya saka shima bawa Farsu ya tare shi suka yi wata qazamar gamuwa data girgiza qasan tekun, makamansu suka bayar da wata maxaukakiyar qara, su ka yi zamiya suka kuma juyowa suka gauraya suka soma musayar sara da suka a tsakaninsu. A haka suka xauki tsawon lokaci suna faman fafatawa bayan tsawon wani lokaci sannan bawa Farsu ya sauya salon yaqinsa nan take ya takura Sadauki Ansar duk da irin tsananin jarumtar da yake da ita. Wannan shi ne salon yaqi xaya da aka tava sauya masa a tsawon rayuwarshi ta duniya bai san ta yadda zai qare kanshi ba a ‘yan lokuta kaxan bawa Farsu ya gajiyar da shi ainun! Ganin abinda yake shirin faruwa ya sa Gimbiya Lusa itama ta zare makaminta ta yi xauki akansa da wata irin zuciya mai kama da dutse, jin motsinta ya saka ya yi saurin juyawa tana zuwa ta kai masa wani sara a kaikace cikin zafin nama ya kaucewa saran, nan suka soma kai sara da suka ya zamana su biyu wato Gimbiya Lusa da sadauki Ansar sun rufarwa Bawa Farsu a tsakiya. Qura ta turniqe a wurin babu abunda zaka dunga juyowa sai qarar haxuwar makamansu da gilmawar kai sara da suka a tsakaninsu walqiya da motsin wucewar makamansu ya karaxe ilahirin wurin. Kai komo da sintiri suka rika yi a wajen ko wanne a cikinsu yana burin ganin ya samu galaba akan xan uwansa. Su Gimbiya Lusa suka kasa samun nasara akan Bawa Farsu haka shima ya kasa samun nasara akan su, har suka gaji dukansu suka zame qasa a jigace numfashinsu yana fita da sauri da sauri. A daidai lokacin wani aljani ya keto qasa ya fito ya tsaya a gaban Gimbiya Lusa ya yi gaisuwa a gareta ta dubeshi sannan ta ce masa cikin muryar gajiya “Maza ka xauke mu ka fitar da mu gavar teku” Bata gama rufe bakinta ba ya sunkuya ya xaukesu ya ajiye su a bayansa sannan lokaci xaya ya vace daga wurin. Ilahirin wajen ya zamto tamkar wata halitta mai rai bata tava wanzuwa ba, babu komai a wurin da ya yi saura, sai gawarwakin matattun dakarun sarauniyar aljanun cikin ruwa. ** Bokanya Namsu tana kwance ta na kallon tsinin wuqar boka sharbanga ta tunkaro qirjinta ta ta lumshe idanunta tana da tabbacin yau itace ranar mutuwarta, domin babu wani mahaluki da zai iya zuwa domin ya ceci rayuwarta daga halakar da take ciki. Duk da runtse idanunta da tayi hakan bai hanata ganin kakkaifar wuqar boka sharbanga ba, haka ya sa ta yi gaggawar buxe idanunta a lokacin ya nufo qirjinta da wuqar da zumar ya soka mata Bokanya Namsu ta runtse idanunta karo na biyu wannan karon ta fi tsorata fiye da kowanne lokaci. Kafin kaifin wuqar ya qarasa qirjin bokanya Namsu, wata kibiya ta qaraso ta samu matsuguni a hannun Boka Sharbanga ya qwala wata razananniyar qara da amonta ya watsu ko ina da ina na illahirin sararin samaniyar tekun. Hakan ya sa Bokanya Namsu ta yi gaggawar buxe idanunta domin ganin abunda ya sa Boka Sharbanga qwala ihu. Tana buxewa ta ga Boka Sharbanga ya yi tsalle gefe xaya yana qoqarin zare kibiyar da ta samu matsuguni a jikin hannunsa. A lokacin wani saurayin aljani ya qaraso wurin wata budurwa mai kyawun fuska ta sako daga kansa ta tsaya gaban Boka Sharbanga ta tsaya a hannunta riqe da wata kwari da baka qirar mutanen nahiyar baqaqen fata. Wannan budurwa dake tsaye akan Boka Sharbanga itama baqar fata ce kamar Bokanya Namsu, sai dai ita yarince xanya domin du-du-du shekarunta ba su fi goma sha tara ba, tana da qirar cika na mace ta tattare gashinta a wuri xaya, tana sanye da kayan yaqi koraye, waxanda suka matuqar yi mata kyawu a bayanta tana rataye da wata takobi mai koren mariqi da aka yi mata ado da farin qyalqyali, akwai alamomin jarumtaka a jikinta. Ta sunkuya ta buxe gefen takalminta ta xauko wata hoda ta watsata a jikin Bokanya Namsu nan take ta ji duk kuzarinta da ta rasa ya dawo, cikin sauri ta miqe ta tsaya gaban budurwa tana dubanta, a lokacin Boka Sharbanga ya zare kibiyar daga hannunsa ya miqe tsaye a fusace ya dubi budurwa da fushin murya yace mata. “Wacce ce ke da har kika aikata wannan laifin a gareni?” Budurwa ta dubeshi fuska da fuska kana ta ba shi amsa da cewar. “Ni ce Sultan”. Boka sharbanga ya zuba mata idanu cikin tsananin mamaki, yana da labarinya ya santa a matsayin jaruma mai tsananin jarumtaka duk wajen dataje a rayuwarta sai anyi tsananin zubar da jini, bata zuwa wani waje ba tare da wani ya mutu ba, wannan shi ne abinda kawai ya sani akanta. Ya juma yana kallonta, sannan cikin xaukar numfashi ya shammaceta ya yi wuf! Ya zare takobinsa ya afka mata suka gauraya a wuri xaya suka soma musayar kai wa juna sara da suka mutuwa ta soma shawagi a tsakaninsu musayar kai sara da suka ya karaxe wurin suka xauki tsawon lokaci suna fafatawa. Ganin lokaci yana tafiya ya sa Sultan ta sauya salon fafatawar bayan wasu ‘yan lokuta ta xauki numfashin Boka Sharbanga ta tafka masa wani nagartaccen sara a dokin wuya ta tsinke masa kai gangar jikin ta zube a wurin kan ya faxa cikin teku. Ta juya ta dubi Bokanya Namsu cikin kwantar da murya tace mata. “Ni ce ‘yarki Sultum”. Bokanya Namsu ta rungumeta cike da farin ciki da jin daxi a yau burinta ya cika ‘yarta ta zamto jaruma mai ji da jarumtaka ga tsafi daga gada a gareta, wannan ranace da take fatan zuwanta take xaukin zuwanta, ga shi ta ganta suka juma a rungume da juna daga bisani suka rabu a hankali Bokanya Namsu ta ce mata “Ya aka yi kika san ina nan?” Sultum ta dubeta da murmushi sannan tace mata. “Wani madubi na tsafi na samo a hannun wani boka da muka yi yaqi da shi a duk lokacin da na buqaci zuwa wurin mutum ina ambatar sunan shi sai na duba jikin madubin zanga inda yake, to da na so dawowa gida wurinki shi ne na ambaci sunanki sai na ganoki kuna fafatawa da boka sharbanga shi ne na yi gaggawar tahowa gareki, domin kawo miki xauki domin nasan halinsa gwani ne wajen iya yaudara” Ta gama faxa mata tana mai fitowa da madubin ta nunawa Bokanya Namsu ta amshi madubin tana nazarinsa lokaci xaya ta yi murmushi “Ina fatan baki halaka Bokan da kika amso wannan madubin ba?” Sultum ta dubi mahaifiyarta cike da mamaki sannan ta bata amsa da cewar “Ina mai fargabar ce miki Bokan ba zai tava halaka ba, har sai wa’adinsa ya yi domin na sameshi tsayayen jarumi mai jarumtaka wayeyye a fannin sihiri na sirri ya karantu ya yi nisa a tsafi da sanin alqaluman tsafi, ya mallaka min shi domin ya yaba da jarumtakata”. Bokanya Namsu ta yi ajiyar zuciya lokaci xaya ta yi murmushi. Sultum ta dube shi cike da mamaki ta qara cewa da ita “Ko kin san shi ne?” Bokanya Namsu ta dubeta ta sake yin murmushi kafin ta bata amsa da cewar “Shi ne mahaifinki ba domin yasan ke ‘yarsa bace da ba zai tava mallaka miki wannan madubin tsafin ba, ya yi hakane kuma domin duk inda kike ya kasance yana kallonki irin wannan madubin guda uku ya haxa ya xauki biyu ya mallaka min xaya kafin mu rabu da shi” Ta gama faxa mata hakan tana mai xauko mata nata madubin Sultan ta saka hannunta ta amsa ta yi nazarinsa ba shi da bambanci da nata ta girgiza kanta. Bokanya Namsu ta dubi wanda ya ke riqe a hannunta a hankali tace “Ina son sanin inda bawa Farsu yake” Tana gama rufe bakinta sai bakin gavar tekun ta bayyana a jikin madubin sannan hoton aljanin da ya xaukosu ya bayyana shi ma kai tsaye ya nufi gabashin tekun da su. Ta mayar da madubin ga ‘yarta kafin tace mata “Mu nufi bakin gavar tekun ta hanyar gabas”A hankali suka nufi bakin gavar wajen da su gimbiya lusa suka nufa. ** Nahiyar yamma maso kudu ita ce mahaxa da ta tattara taron baqa fata wanda adadinsu ba zai qidudugu ba, amman duk bayi ne qasar Margas ta zamto fitattaciyar qasa da ta ke yankin. Domin ta zama qasa da mutanen cikinta suka gwanance wurin sana’ar kamun kifi wato ma sunta ne, sai kuma saye da siyar da baya hakan yasa qasar ta zamto mahaxa ta nahiyar yammaci. Ko wacce safiya jama’ar qasar sukan fito bakin tekun garin su yi kamun kifi amman banda ranar juma’a da asabar wannan ranakun ba sa zuwa kamun kifaye. Sarauniya Zultum itace ke mulkin qasar, ta hau mulkin qasar kimanin shekaru uku da suka gabata a lokacin shekarunta ba su gaza sha takwas ba, a rayuwar sarauniya Zultum babu abinda yake birgeta tamkar ganin mutum ya nuna wata bajinta ta ban mamaki, wannan dalilin ya saka duk shekara a qasar take saka gasar kamun kifi duk wanda ya kama wanda ya fi na kowa girma to za a yi masa kyauta mai qayatarwa talakawan qasarta suna matuqar jin daxin wannan gasar da sarauniya Zultum ta ke sawa. A wannan shekarar gasar ta sauya salo domin sarauniya Zultum ta fito da kanta ita ma zata yi kallon gasar savanin sauran lokutan baya sai dai ta tura wakilai kuma ta yi alqawarin cewar zata auri duk wanda ya samu nasara a gasar amma zata faxa masa sharuxan sadakinta wanda ta tabbatar ba qaramin namiji ne zai samu nasara a gasar ba har ya aureta. Wannan kalamin nata ya sa masoyanta suka dunga varkowa daga duniya mafiya yawansu ‘ya ‘yan sarakai ne sai tsarukansu ‘ya ‘yan attajirai da talakawa domin daman masoyanta sun daxe suna jiran su ji sharuxan aurenta. ‘Ya ‘yan sarakuna da attajirai suka yi ta neman sa’a a wurin bokaye da masu sihiri domin su samu su shiga cikin tekun ba tare da wata matsala ba kuma sa’a ta tabbata a garesu. Habaru ya kasance saurayi matashi mai tsananin taqadiranci da rashin jin magana a kullum sai Habaru ya janyowa iyayenshi magana, ba a kawo qararsa gida wajen iyayenshi a rana ba a kawo qara sau saba’in ko ma fiye da haka domin duk wurin da ya je sai an kawo qarashi. Baban Habaru wani tsohon masunci ne da sana’ar sa bata magance masa komai game da talaucin da suke ciki. Habaru bai wani tsaya ya mayar da hankali ya koyi sana’ar babanshi ba ga kuma tsufa sosai ya kama shi. A yayin da shi kuma Habaru kullum tunaninsa ta yaya zai mallaki dukiya ta wata hanyar, domin shi dai ya yi duba sosai ya ga cewar a duk masu sana’ar kamun kifi bai tava ganin wanda ya yi kuxi da sana’ar ba. A lokacin da labarin gasar sarauniya ya zo masa sai shima ya ji cewar ya kamata ya shiga domin ko banza idan ya samu nasara zai samu damar auren sarauniya shima ya shiga cikin ma su mulki, ya kasance ana kaxa masa tambari tare da kirarin. Sai Habaru xan tsohon masunci, talaka mai qashin arziqi. Wannan tunanin da ya yi shi ya ja hankalinsa ya je ya bayar da sunansa a cikin masu shiga gasar. A lokacin da labari da labari ya watsu cewar Habaru ya shiga gasar auren sarauniya sai jama’a da dama suka riqa yin addu’a Allah yasa ya mutu a wurin gasar domin sun gaji da irin taqadirancinsa. Mahaifin Habaru yasan babu wani abu da xansa zai iya kuma lokaci ya qure balle ya koya masa dabaru na kamun kifi don haka ya kirashi domin ya yi masa nasiha. Da Habaru ya samu mahaifinsa sai ya samu wuri ya zauna ya yi shiru yana kallonsa mahaifinsa ya dubeshi a hankali yace masa. “Abubuwa biyu zan gaya maka” Ya yi shiru yana kallonsa sannan ya ci gaba da cewar “Na farko ka saka a ranka cewar nasara Allah shi ne yake bayarwa ga wanda ya so” Ya kuma yin shiru karo na biyu yana dubansa kafin ya ci gaba da magana “Na biyu ka yi addu’a a koda yaushe domin Allah yana taimakon bawansa” Ya sake saurarawa kafin ya ci gaba da magana “Waxannan abubuwan su kaxai zan gaya maka daga su babu wani abu da zan iya yi maka sai fatan alheri xana”. Habaru ya yi shiru yana kallon fuskar mahaifinsa wadda ta tattare domin tsufa da ya kamashi, wannan shi ne karo na farko da mahaifinsa ya gaya masa wani abu da zai amfaneshi a rayuwarsa. Domin abunda Habaru ya xauka game da mahaifinsa a baya babu abinda zai iya faxa masa.babu kuma wani abu da zai tsinana masa sai talauci da ya yi masa qabe-qabe a rayuwarsa. Habaru ya tashi a kasalance ya koma xakinsa ya zauna ya yi shiru yana tunanin abubuwa da dama da suka zo masa kai da kuma waxanda suka tunkaro rayuwarshi. A zahiri yana da masaniyar cewar ba shi da wata dabara ko qwarewa da zata taimaki rayuwarshi har ya kai ga samun nasara, ba shi da wata mafita kawai dai zai jarraba sa’arsa a sana’ar da iyayensa suka gada. Habaru ya tashi a hankali ya je ya yo alwala ya yi sallah ya xaga hannunsa sama ya soma roqon Allah akan ya ba shi nasara game da gasar daya shiga. A haka ya tafiyar da lokacinsa. Rana ta xaga bakin teku ya cika maqil da mutane kowa yana jiran ya ga yadda gasar zata kasance da kuma ganin wanda zai samu nasarar zama wanda zai auri sarauniya zultum. Duk waxanda suka shiga cikin gasar sun gama halarta a wurin suna juran zuwan sarauniya Zultum domin soma gudanar da gasae duk wanda ka duba za ka samu ya shirinsa wasu sun rataya kayan tsatsubarsu a wuyansu wasu kuma a ciki, wasu a baki kowa ka kalla akwai irin shirinsa.. Xan Boka Margadasy ya fi kowa qwarin gwiwar samun nasara tana gareshi domin mahaifinsa ya ba shi wata sanda da ya riqeta a hannunsa wanda da zarar lokacin fitowa ya yi idan ya fito zata rikixa ta zama qatoton kifi da babu wanda zai kama kamarsa domin babanshi mashahurin matsafi ne da shahararshi ta kai ko ina. A haka lokaci ya yi sarauniya zultum ta qaraso wurin ta samu wuri ta zauna a cikin tanti da aka tanadar mata, daga wajen da take zaune tana kallon duk abinda yake faruwa ‘yan takara suka gabato gabanta suka yi gaisuwa ta girmamawa ta dunga kallonsu xaya bayan xaya a haka suka kammala zuwa daga nan aka bada damar shiga cikin teku domin soma gabatar da gasa. Makaxa da mawaqa suka soma kaxawa masu gasar kixa suna kambama gwanayensu da kalamai da suke qara musu qwarin gwiwa a haka har suka qarasa zuwa ga bakin teku kowa ya gama shirinsa sanna aka soma shiha cikin ruwa domin fara gudanar da gasar. Habaru ya juma a tsaye a wurin yana addu’a domin neman samun nasara a wajen ubangiji daga nan ya yi tsalle ya faxa cikin teku ya nutse ya yi qasan ruwan domin laluben kifin da zai kamo. A hankali lokacin ya tafi waxanda suka shiga cikin gasar suka soma fitowa xan Voka margadasu ne ya fara fitowa daga cikin tekun janye da wani murgujejejn kifi daya baiwa kowa mamaki domin a tarihi ba a tava ganin wani wanda ya kamo tamkarshi ba tun daga lokacin kowa ya saduda ya yarda cewar lallai shi ne mai nasara a gasar babu wani da zai iya kamo wanda ya fi nashi. Sarauniya zultum tana zaune tana kallon duk abubuwan da suke tafiya duk wanda ya fito sai ya fito da kifin da bai yi ko da rabin na shi ba da zarar ya qyallara idanu ya ga sihirtaccen kifin da xan Boka Margadasu ya fito da shi sai ya yarda nashi domin yana da tabbacin ba zai kai labari ba. Xan Boka ya yi ta qyalqyala musu dariyar mugunta yana mai alfahari da yiwa kansa kirari gami da ambaton nasaba a haka kowa ya gama fitowa ya kasance sauran Habaru can bayan tsawon wani lokaci sannan Habaru ya fito yana janye da wani abu da qyar domin matuqar nauyi da ya yi masa idanuwan kowa ya koma kanshi. Habaru ya fito daga cikin ruwan yana janye da wani murgujejen kifi wanda ya ninka na xan Boka Margadasu sau biyu, domin yana ganin na shi shima ya tsorata da ganinsa domin tunda yake a rayuwarshi bai tava tsammanin wani xan Adam zai iya kamo kifi kamar wannan ba. Jama’a duk aka bar kallon sihirtaccen kifin da xan boka Margadusu ya kamo aka koma kallon na Habaru sarauniya Zultum da kanta ta tashi ta je ta taryo Habaru da kanta ta yi masa jinjina bisa nasara daya samu. Mafarkin da Habaru ya yi ya kusa zama gaskiya. Washe gari Habaru ya zo fada cikin kayan alfarma fadawa suna take masa baya, ya zube gaban sarauniya ya yi gaisuwa ya sunkuyar da kansa yana jiran ya ji abinda za a yanke masa a matsayin sadakin auren sarauniya zultum bayan wucewar wasu ‘yan lokuta sannan ta nisa gami da faxin “A yau na tsayar da mijin aurena, sannan kuma a yau zan yanka masa sadakin aurena ko a yanzu ya samo ya kawo mun shi za a xaura mana aure” Ta xan yi shiru kafin ta ci gaba da magana cikin nutsuwa “Ka yi sani cewar a lokacin da mahaifinmu ya haifemu mun kasance ‘yan biyu mahaifiyarmu ta haifa. Duka mu biyun kamarmu xata babu wani bambanci wata rana sai wani aljani ya sace xaya daga cikinmu domin tsabar son rai nasa wannan abun ya matuqar qonawa mahaifinmu rai wanda sanadin wannan baqin cikin shi ya zama ajalinsa, ita kuma mahaifiyata tun lokacin take fama da baqin cikin abun kullum tana cikin kuka. Saboda haka wannan ‘yar uwar tawa nake son ka nemo mun wacce a yanzu haka tana cikin wannan duniyar tamu wannan shi ne sadakin aurena” Ta xan yi shiru sannan ta qara da cewar. “Kamarmu xaya sunanta Gimbiya Lusa”. Habaru ya yi shiru yana jinjina lamarin a ranshi, a rayuwarshi wannan shi ne karo na farko da zai aikata aikin wahala ya sunkuya yace mata. “Insha Allahu zan nemo miki ita” Fadawa suka yi kabbara domin qarfafa masa gwiwa. Washe gari Habaru ya gama shirinsa ya fita mahaifinshi ya rakasa har bakin qofar gari ya xauko wata takobi ya ba shi suka yi sallama da juna. ** Su gimbiya Lusa suka sauka a daidai gavar teku suka yi shiru suna duban-duba suna tunanin abinda ya kamata su yi, suka soma shawarwarin hanyar da ya kamata su bi. Suna cikin shawara ne bawa Farsy ya hango mace a kwance a gefen gavar tekun ga alama ruwa ne ya ciyota da sauri ya nufi wurin ya qarasa ya janyota ya fito da ita ya dubeta a nutse ya ganta baqar fata kyakkyawa wacce idanuwanshi ba su tava ganin mai kyawunta ba ya zuba mata idanu yana kallonta cike da mamakin irin kyawu da ya gani tana da shi, a haka su Gimbiya Lusa suka qaraso suka sameshi. Gimbiya lusa ta tsuguna a gabanta ta saka hannunta ta danna qirjinta take ta soma aman ruwan data sha, zuwa wani xan lokaci ta farfaxo ta zuba musu idanu tana kallonsu har zuwa wasu ‘yan sakani kafin tace mata “Na gode da taimakon da kika mun”. Bawa farsu ya yi murmushi a hankali yace mata “Ba komai dolen mu ai mu taimaki kyakkyawa kamarki” Ya gama maganar yana mai wasa da sarqa tsafin dake hannunsa. Ta kalleta kafin ta sake cewa “Wannan sarqa tana da kyau, ta matarka ce?” Ya dubeta ya dubi sarqa ya bata amsa da cewar. “Ba ta matata bace, ni bani da mata” Ta yi murmushi tare da qara kashe murya tace masa. “Na ga tana da kyau za a iya bani na ganta?” Bawa Farsu ya kalleta ya kalli sarqa ya xanyi shiru na wasu ‘yan sakani tamkar ba zai bata ba daga bisani ya miqa mata ta miqa hannu zata amsa sai Gimbiya Lusa ta yi sauri riqe hannunsa su duka suka mayar da kallonsu gareta a hankali tace da bawa Farsu “Kar ka yarda da ita mayaudariya ce”. Maganar ta tsaya wa bawa faru a rai ya juya ya kalli fuskar budurwa kyawun fuskarta ya mamaye masa rai ya juya ya dubi Gimbiya lusa yace mata. “Ba mayaudariya bace sai dai kece mayaudariya” Yana gama gaya mata ya juya ya miqa mata sarqa a hankali yace mata “Ga ta ki gani ki dawo mun da kayata” Tana saka hannu ta amsa ta dubeta a tsanake sannan ta dubi bawa farsu ta qyalqyale da dariya ya dubeta a tsorace dariyar ta janyo hankalinsu. Suka zuba mata idanu suna kallonsu ga mamakinsu sai suka ga ta miqe ta yi wata girgiza take kamaninta suka sauya zuwa na sarauniyar aljanun cikin ruwa ta xaga sarqa akan idanunsu kafin tace musu. “Ta tafi kuma ta dawo, don haka yanzu zan halakar da ruhinku gaba xayanku” Tana gama maganar bawa Farsu ya zare takobinsa da sauri ya kai mata sara, tayi tsalle gefe xaya saran ya wuce ta yi tsalle akan iska ta koma can gefe nesa kaxan da su, ta dube su ta yi nuni da hannunta zuwa ga wani wuri nan da nan wuta ta kama itatuwan da suke dajin ta nufi wurin da suke da zumar halakar da ruhinsu. Sarauniyar aljanun cikin ruwa ta qyalqyale da dariya. Bawa farsu ya dubi sihirtaciyar wutar data yo kansu tana cinye duk abinda ta samu, sai ya juya ya dubi su Gimbiya Lusa yace musu. “Duk wanda zai iya yakan iya biyoni” Yana gama maganar ya nufi wurin da wutar take tahowa a guje takobinsa a zare. Gimbiya Lusa ta bishi da kallo a hankali ta juya ta dubi sadauki Ansar tace masa. “Wannan baqar fatar ba qaramun hatsabibi bane, ban tava ganin mutum kamarshi a”> Wutar ta ci gaba da nufosu da zumar halakar da su… Alhamdulillahi masha Allah. Sauran labarin zai zo muku a cikin littafin ABOKAN GABA 3 An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels