An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels *NISAN KIWO❄️* _Mom Islam Page1 "Shin kinsan da cewar ciwon mahaifiyarki baya buƙatar damuwa akan me zaki dinga kusantar ta bayan tace babu abinda ta tsana kamar ta buɗe ido ta ganki?" Cikin shesheƙar kuka Anum tace "akan me zata dinga furta min irin waɗannan kalaman kodan saboda taga Allah yayini da Halitta ba irin taku ba?" Tai maganar tana toshe da hannu saboda kuka yaci ƙarfinta. cike da tsananin damuwa gami da tsantsar tausayi Jannat ta kamo hannun Anum suka fito daga ɗakin da Ummu take, a parking space suka tsaya, inda jerin danƙara-danƙaran motocin masu gidan ke a parke, "Anum nasani abin da ciwo ace mahaifiyarka wace ta ɗauki cikinka tun yana watanni ɗai-ɗai har tara da kwanaki yau a wayi gari tace bata ƙaunarka duk inda zakaje kaje wannan sam ba ɗabi'a bace, sannan gaskiya anyiwa Allah butulci" Jannat ta faɗa tana dafa kafaɗar Anum, magana take son yiwa Jannat ɗin amma ina bakinta da zuciyarta gabaki ɗaya rawa sukeyi yayinda takejin kanta nayi mata matsanancin ciwo kamar zai tsage, cikin ƙarfin hali tana dafe da kanta tace "anty Jannat Ummu fa musamman ta baro gidanmu saboda ni, ta dawo gidan mutanen da ba danginta ba ta tare, tace inci gaba da zama acan, nikam bazan iya zama ni kaɗai a gidan ba duk da akwai Arshi" "Haba Anum ya ya inason kawo miki ingantacciyar shawara kina kawomin wani zaman gidanku, ki nutsu ki saurareni, duk da cewar Allah yayi miki Halitta guda biyu, mace da namiji kinga mudai ba wani hali ne damu da zamu iya taimakawa ayi miki aiki ba, tabbas Arshi tana bani tausayi kodan Lalurar juyewar ƙwaƙwalwa da take tare dashi, amma wlhi nafi tausaya miki, dama shawarar da zan baki itace.." Kiran Ummu ya katse Jannat, ta amsa tare rugawa a guje. Anum ta durƙushe a gurin zuciyarta na faman yi mata zafi, ta kalli takalmin mazan dake a ƙafarta sannan ta shafi gashin bakin da ko ta aske gurin a baƙi yake zama, sannan ta kalli nonuwanta da suke a tsaye ƙyam kafin ta taɓo gabanta da ya kasance akwai na maza a jiki, ta ɗaga idanunta sama tare da dawo dasu ƙara hawaye na zuba sharr kamar an buɗe famfo, "Jannat wlhi tallahi idan kika ƙara dawomin da Anum cikin gidannan mai rabani dake sai Allah tunda na gaya miki bana sonta bana sonta ko ana dole ne? inace ni na haifeta sannan nace bana ƙaunarta?" Ummu tai maganar tana nuna Jannat dake tsaye a bakin ƙofa bata ma samu damar ƙarasa shigowa ba, a hankali ta tako tare da zama gefen Ummu cikin tausasa murya tace Ummu mai yasa kikeyin abu sai kace ba musulma ba, karki manta idan har kina tunanin kin gujeta ne, nan gidan da kike gadara dashi wlhi masu gidan suna iya dawowa a koda wane lokaci sannan sai sun tozartaki dan ba isasshen mutunci ne dasu ba" Ummu ta miƙe kamar mai shirin yin tafiya, sai ta dawo da baya ta watsawa Jannat mari tana hoci tace "kar Allah yasa su bari inkai safiya, gidane nazo bazan fita ba tunda dai kema bana ubanki bane ai saiki barni da masu gidan ko?" Dafe da kumatu ta miƙe daga zaman da tayi akan gado, kana ta miƙe jiki a sanyaye ta raɓa ta gefen Ummu ta fice, tana fitowa harabar gidan ta hango Anum na a durƙushe a gurin da ta barta ga uban rana da akeyi mai zafi, da sauri ta karasa gurin Anum ɗin tare da kamo hannunta, sukayi hanyar fita bakin get. Jiki a sanyaye Jannat ta buɗe get ɗin suka fice, duk da shirun da ya ratsa anguwar bai hanasu samun wani dakali a ƙofar gidan dake a kusa da wanda suka fito suka zauna ba, har yanzu Anum kuka takeyi, Jannat ta sanya hannu ta buɗe kan Anum, da sauri ta fashe da kuka tare da rungume Anum, cikin kukan take cewa "Anum akwai matsaloli a tare dake masu tarin yawa, gashin kanki irin na maza ga gemu sannan kuma ga nono bayan nan.." "Anty Jannat ki sanar dani abinda kikeson gayamin lokacin da Ummu ta kiraki" Anum ta faɗa sbda wannan dogon lissafin da sukeyi ba wani ƙarewa zeyi ba, Jannat ta mammatsa hannayenta kafin ta shafi gefen fuskarta da yayi jajir sannan tace "naji kafin nan gayamin nan gurin ya tashi ko?" Kallon kumatun nata Anum tayi cikin raunatacciyar murya tace "Ummu ce ta mareki ko?" Jannat ta gyaɗa kai kana tace "karki damu idan Ummu ce zatayimin abinda yafi haka tunda yanzu ina tare dake, amma bata tunanin rayuwar Hajna?" Sosai takaici ya kama Anum sbda a halin yanzu zuciyarta ta fara bushewa sam bata tunanin wata Hajna tunda dukkansu abin a taimaka musu ne, amma yanzu kam kanta take tunani, "ki mance da Hajna" Anum ta faɗa. "Toh shikenan, dama shawarar itace kinga yau baki da gurin kwana, sannan a gidanmu ma ba lallai su yarda mu kwana a tare dake ba, amma da zaki yarda da nayiwa ƙanwar momyna magana ta ɗaukeki aiki duk wata kina turomin da kuɗin cikin account ɗina, sai mu dinga tarawa har ya isa wanda za'ayi miki aiki, wlhi har makaranta zata saki, matsalar ɗaya ce dole ki kasance a suffar mace saboda wlhi mijinta baya ƙaunar namiji a gidansa, akan hakan matarsa ta tsayar da aihuwa, yaransu biyu Jumayma da Arshi, hamshaƙin mai kuɗi ne sannan kuma dole ƴan aiki tare da yaransa suke kwana, amma fa ansha kawo masa ƴan aiki wlhi yana korarsu dan ranar da naji ƙanwar momyn tana faɗa ƴan aikin da aka yi musu korar kare sunkai su ashirin" Anum ta zaro ido kafin tace "Anty Jannat gaskiya bazan iya ba, saboda daga lokacin da suka tabbatar da ni MATA MAZA ce kinsan na shiga uku, inaga nikam kasheni zeyi kamar inda Ummu take buƙata" Jannat ta toshe mata baki, tare da cewa "haba kisa, shidai ya kasance mai baƙar zuciya ne, dan wlhi nima nan da kika ganni ko gidan bana zuwa saboda akwai ranar da Arshi tayimin leifi na duketa bakiga ɗan dukan ba wlhi yana shigowa ya tambayeta tace nice, kawai sai nayi tsuru-tsuru, gashi sangameme ya tako har inda nake zaune saman kujera ya shaƙemin wuya, yace min, wai su biyun sune rayuwarsa zai iya kashe kowa a kansu in kiyaye, Sosai hantar cikin Anum ta kaɗa, cikin karyar zuciya Anum tace "tunda kince yaran basu da kunya aiko dai bazamu shirya ba, Gara na shimfiɗa kwali na nemi gurin kwana ko a gefen titi" "No ki bari muje a gyara miki gashin bakinnan, saboda nikam bazan iya ganinki cikin damuwa ba" Jannat ta faɗa tana rausayar da kanta. Sosai tausayin Anum ɗin ya kama Jannat, Shiru ne ya biyo baya na ƴan wasu lokuta kafin Jannat tace "bazaki kwana akan titi ba, zan tafi dake gidanmu zuwa gobe da Asbha kafin su momy su fito sai muyi shawarar abinda ya dace" Tabbas Anum tana jinjina tausayi tare da jarumtaka irin na Jannat sbda tasan idan har iyayen Jannat ɗin suka samu labarin Jannat ɗin ta kwana tare da Anum tabbas zata fuskanci mummunan hukunci, domin mutane da yawa suna suffantata da namiji, ita kuma Anum ɗin abinda bata taɓa kawowa kanta ba kenan, tana sawa a ranta koda yaushe ita mace ce, "toh" Anum tace dan itama kanta ta fara tsoron kwana a titin. "Inda abin zai kasance, tunda tsakaninki da gidanku akwai nisa sosai gashi har an fara kiran sallah, zan fara shiga gidanmu, sannan da zarar na shiga zan yaudare mai gadi akan yazo ya dubamin wani abu acan baya, kinaji nace "subahanallah sai ki shigo a hankali ki ɓuya gurin motocin Dady, nikuma zan zo sai muyi shawarar inda za'ayi ki shiga ciki" Anum ta kalli Jannnat dake ta faman kawo musu mafita, kafin tace "Nagode anty Jannat Ubangiji ya saka miki da alkairi" Jannat ɗin ta miƙe tana cewa "karki damu fatan nasara zakiyi mana" Suka fara tafiya riƙe da hannun juna, koda suka fito bakin titi da yake gidansu Jannat ɗin dole sai sun tsallaka titi, mutane sai kallon Anum sukeyi, wasu na tsokanarta wasu na nunata da yatsa, daga Anum ɗin har Jannat ɗin sunji zafin hakan, musamman ma wacce abin yake a kanta, cikin tausasa murya Jannat tace "Anum daga yau karki sake yawo babu hijabi kinji?" Anum ta zura hannayenta cikin aljihun wandonta kamar dai inda maza sukeyi kafin tace, "anty Jannat tun ina ƙarama Ummu ta sabarmin da rayuwa a haka, wlhi rannan da na kwatanta sanya hijabi jinayi ya shaƙemin wuya sai naji sam babu daɗi dole na cire" Jannat ta zaro ido tare da cewa "aiko inhar bazaki dinga saka hijabi ba wlhi duk gidan aikin da za'a kaiki matsala zaki samu indai ba aikin gida kamar mai gadi da dai sauransu zaki samu ba" "Anty Jannat wlhi dan kawai kar inyi miki musu ne, amma duk sanda na kalli kaina a mirror sai tausayin kaina ya kamani, duk da nasan saɓo nakeyi nakance, mai yasa Allah bai dauki rayuwata ba tun inda jaririya, dan bana raye babu wani ƙalubale da zan fuskanta musamman ma ga mutane uwa uba harda mahaifiyata" Jannat ta dafe kanta, kana tace "idan har bazaki godewa Allah da baiwar da yayi miki ba wlhi bazaki godewa azabarsa ba, inaso ki sani kefa da ranki da lafiyarki sannan zaki iya yin komai na aiyuka banbancin halittace ce dake, ƴar uwarki fa? da yanzu zakiga ana wasa da dariya da ita yanzu zata juye kamar ba ita ba?" Anum tace "inayiwa Allah godiya, kinsan sharrin zuciya babu abinda bata aiyyanowa ɗan adam musamman ma idan yana fuskantar tsangwama da tsana.." Isowarsu bakin get ɗin gidansu Jannat ne yasa dukkansu yin shiru tare da kallon juna, Jannat takai bakinta dai-dai saitin kunnen Anum, kome ta gaya mata oho naji Anum ɗin tace "toh" Anum ta koma can baya Jannat ɗin taje kusa da get tayi nocking lokacin har an fito sallahar magriba, "waye" mai gadi ya faɗa, "Nice haba malam Lado ka buɗemin mana" Ƙaramar ƙofar ya buɗe kafin ya washe haƙora yana cewa "aiko Hajiya jannatu ki shirya karɓar faɗa daga gurin Hajiya domin kuwa tun tuni take sababi" ya ƙare maganar yana tafa hannu, taɓe baki tayi tare da nuna shi da yatsanta kafin tace "ni dan Allah karka dameni ka matsamin in wuce" Tai maganar tana gyara ɗan siririn mayafin dake a kafaɗarta, da sauri ya bata guri ta wuce, da sauri ta nufi can bayan ɗakin mai gadin gurin ya kasance da kyawawan flowers masu kyau da ban sha'awa, tsala ihu tayi tana cewa "Lado dan Allah zoka taimaka min Please bansan meye a gurin ba" yana tafe yana jin radio yana cewa "kedai Hajiya wani lokacin idan kina abu sai kace ƴar yaye, ke da zaki wuce ɓangarenku mai ya kawoki ɓangare na, koda ya iso gurin tana tsugunne kanta a ƙasa, ƙarar horn ɗin motar dadynta da ta karaɗe musu kunnuwa ne yasa tai saurin dafe ƙirji tare da waro ido sbda gabaki ɗaya zuciyarta ta tsinke ta riga ta gama rayawa a zuciyarta Dady yaga Anum angama shikenan kashinta ya bushe....! Mai kuke tunani Anum zata samu damar shiga gidansu Jannat kuwa? Idan masu gidan da Ummu take suka dawo ya zatayi? Ya kuke tunanin Arshi zatayi bayan babu kowa a gidan sai ita kaɗai? Amsarku tana cikin littafin NISAN KIWO Drop your comments saboda ku samu update akan lokaci, and then karku manta kuyi following account ɗina a arewabook Page2 "Oyoyo Alhaji Barka da dawowa" Lado mai gadi ya faɗa yana shirin zuwa buɗe masa get, kafin ya samu damar fara tafiya Jannat ta janyo wuyansa, murya ƙasa-ƙasa tace "wlhi inhar kace ina gurinnan sai na lahira ya fika samun rahama" tai maganar tana jujuya masa kunnuwa, Yana rawar jiki gami da leƙen kada yai laifi saboda bai je ya buɗewa shugabansa get ba, yace "dan Allah ki barni inje kinsan halin Alhaji" ta sake ɓuya acan gurin flowers ɗin sbda tasan idan har ta koma gida babu wanda zai barta ta sake fitowa, daga Dadyn har momy, bayan mai gadin ya buɗe masa get ya shigo kai tsaye parking space ya wuce, acan yai parking motar kafin ya fito da sauri ya nufi ciki. Cikin sanɗa Jannat ta fito tare da kallon Lado mai gadi kafin tace "Allah ya taimakeka" sannan ta buɗe get ta fice, murya ƙasa-ƙasa take cewa "Anum am sorry please kiyi haƙuri ki fito karkiyi fushi" tsahon wani lokaci bataji muryar Anum ɗin ba, sosai hankalinta yai mummunan tashi taci gaba da zagaye layin nasu da babu hayaniyar kowa tana kiran sunan Anum, ta cikin wani lungu Anum ɗin ta fito ta wani haɗa zufa sosai dan a tunaninta Dadyn Jannat ya ganta, "Anty Jannat babu wanda dai ya ganni ko?" Anum tayi maganar zuciyarta na a tsinke, "karki damu Anum babu wanda ya ganki inaso ki tsaya a bakin get kinsan Lado munafuki ne, nikuma zan yi magana sai ki biyoni" "Oky insha Allah" Anum ta faɗa idanunta sun ciciko da hawaye, Jannat ta buɗe get ɗin a hankali kafin ta iso gurin Lado tace masa, kaje can gurin da na tsuguna ɗazu na yarda ɗari biyar idan ka gani nabaka" Tana gama magana ya wuce da gudu yana tsalle, Da sauri ta sake buɗe ƙofar dake jikin get ɗin ta fara ƙwalawa Anum kira murya a hankali, Anum ɗin ta taho ta kanannaɗe hannayenta a ƙirjinta da alamu sanyi takeji, Jannnat ta kamo hannunta suka shige ciki, har suka wuce mai gadi bai fito ba, ta ƙofar baya sukabi wanda idan ka shiga, hanyar zata sadaka da cikin gidan amma bata ɓangarensu momy ba, hanyar ta kasance akwai ɗakin Jannnat a gurin, daga buɗe ƙofar har shigarsu cikin sanɗa sukeyi sai kace masu kama kifi, har suka iso ƙofar ɗakin Jannat ɗin, a hankali Jannat ɗin ta buɗe door ɗin tare da tura Anum ciki, kafin itama tasa kai zata shige "waye....?" sukaji muryar momy tana magana, cikin ɗaga murya Jannat tace "nice momy" Muryar momy ta tsinkayo tana balbala masifa tana cewa "tunda kin raina mutane yau zakiyimin bayanin inda kika tafi wlhi zaki karɓi hukunci a gurin dadynki" tuni jikinta ya fara kyarma, sbda tasan Halinsa akwai tsanani ta kalli Anum da ta zauna saman lallausar katifar Jannat ɗin ita kuma Jannat ɗin tana riƙe da door ɗin murya ƙasa-ƙasa tace "Anum Please ki kula da zarar kinji motsin za'a shigo ko nice ki san inda zakiyi ki ɓuya wlhi momy komai nayi sai ta gayawa dady ina zuwa Kinga yanzu ma kirana takeyi, ki buɗe fridge inaga akwai hollondia ki fara sha kafin in shiga kitchen in samo mana abinci", Jannat ta ƙarashe maganar tana rufe ƙofar ta wuce gurin Momy, suna zaune a parlo amma suna jiyo ƙus-ƙus na maganar da take yiwa Anum, "Jannat wannan shine last time da zan gindaya miki sharaɗi, saboda momynki tasha kawomin ƙorafin idan kika fita sai dare kike dawowa" Jannat ta zube guwaiwoyinta akan carpet tare da sunkuyar da kai tana nazarin kalaman da zata ƙwaci kanta dashi, cikin sanyin murya tace "Dady jikin Arshi ne ya tashi yarinyar Ummu mahaifiyar Anum" cikin sauri tare da ɓacin rai Dady ya miƙe yana nuna Jannat da yatsansa kana yace "Jannat ashe dama baki ji gargaɗin da nayi Miki akan zuwa gidan mutanen nan ba, mai yasa kika fiye taurin kai ne?" Momy ta katse masa zancen ta hanyar cewa "batada wani aboki da ya wuce mata maza yaron Ummu, wlhi Dadyn Jannat ko san ganinsa banayi, sbda idan ka gansa kamarsa ma wlhi abin ƙyama ce, amma jannat take taraiyya dashi nikam ka shiga tsakaninta dashi kafin yaje yayi mata ciki" Momy na rufe baki Dady ya waro ido gami da cewa "mata maza" ya ciro belt dake a jikin wandon jeans ɗinsa kana yace "kaf cikin danginmu babu wace ta taɓa ɗauko mana abin kunya ina tunanin kekam sai nayi miki tabon da idan kika ganshi zaki tuna da faɗan da nakeyi miki" Jannat ta miƙe tana ja da baya Dady ya ɗaya bulala zai kai mata ta ruga ɗakinta da gudu, takowa yakeyi zuwa hanyar ɗakinta yana hoci tare da masifa, Anum na ganin haka ta shige ciki babbar drowar dake can gefe tunda tanada zurfin da zata ɗauketa, saƙata tasa ta ciki, Jannat ɗin na kuka tana murɗa key a drowar tana jin shigowar Dady ta tura key ɗin ƙarƙashin gado, "kina tunanin kin tsira ne ko? da nayi tunanin ƙyaleki tunda akace abota kikeyi da mata maza wlhi yau sai kin banbance min, ya zabga mata bulala, Jannat ta saki kuka tana cewa "Dady dan Allah kayi haƙuri bazan sake ba" zama yayi a bakin gado tare da kallon drowa da wani abu ke gangarowa kamar ruwa, da sauri ya miƙe gami da zuwa gurin drowar yana cewa "wannan kamar ruwa kamar fitsari dan na jishi da zarni" cikin Jannat ya kaɗa sosai, har wani ƙugi yakeyi tanada yaƙinin tana zuwa toilet gudawa zatayi, da sauri ta shiga toilet sbda hankalin Dadyn ya koma gurin drowar, tana tsuga gudawa tana matsar ƙwallah, sosai cikinta ya rikice dan har wani murɗawa yakeyi, "shin idan Dady ya buɗe drowar nan ya hango Anum a ciki itakam ƙaddarawa zatayi ta mutu saboda zai iya kasheta, ta daɗe a toilet ɗin bata fito ba har wani gumi take yakicewa, daga ƙarshe tayi tsarki tare da kora ruwa ta fito jikinta babu inda baya ɓari, ji tayi Dady yana cigaba da cewa "wato yarinyar nan ajiyar ruwa tayi ko meye a cikin drowar nan oho, nidai zarni nakeji, cikin kakkausar murya Dadyn ya kalli Jannat da cikinta ya ɗuri ruwa yace "tashi ki kawomin key inga meye a ciki" Yanzu kam tafi kowane lokaci rikicewa dan bakinta har ɓari ya kamayi, murya na rawa tace "Dady ban...ba..ba...bansaaa..inda..." Dady ya daka mata tsawa, "ace abin yana ɗakinki kicemin wani bakisan inda yake ba, ko ba anan kike ajiyar kayanki ba?" "Eh bana ajiy anan" Jannat ta faɗa jiki na rawa, Dady zai ƙara magana sukaji tusa ɓurrrrrrr, mai masifar wari kuma ta cikin drowar, da sauri dukkansu suka toshe hanci, momy ta shigo tana cewa "Dady kazo kayi wanka dare yayi sosai" da gudu ta fice sakamakon wani uban wari daya bugi hancinta, Dady na riƙe da belt a hannunsa yace "akwai mutum a ɗakinan" Cikin sauri Jannat tace "Dady babu kowa bansan dai ko magen da na kawo daga gidansu Arshi ce ba" "Dan ubanki zoki fice da ita, bazaki kawo mana cuta gida ba" Dady ya fice zuwa neman buhun shinkafa a kitchen, Jannat tai saurin buɗewa Anum ƙofa ta shige toilet sannan ta kulle drowar, bayan Dadyn ya samu buhu sai da ya biya ta ɗakin momy ya karɓo key sbda drowar tasu iri ɗaya ce, kana ya dawo ɗakin Jannat ya fara ƙoƙarin buɗe drowar itako har yanzu gabanta bai dena lugude ba, yana buɗe drowar yaga wata leda ɓaka a ƙulle sai wari takeyi, daga can sama kuma kayan Jannat ɗinne, shikuma a nan tsakiya yana baƙar ledar, cikin tsagina gini ya kunce laidar abinda ya gani ne ya sanyashi ja da baya gabansa na tsananta faɗuwa, cikin ɗaga murya yace "kashi a leda Jannat dan ubanki waye a ɗakinan?" jannat tai wuri wuri da idanu, da Muryar kuka tace "Dady nikam bansan komai ba tare dakai muka shigo, Dady yace "fitsarin da ya gangaro shikuma fa?" Jannat ta dafe kanta, ta cikin toilet sukaji ana cewa "idan har bazaku bamu jini ba tabbas zamu iya yin komai.." Dady ya fice da gudu, sai gashi ya dawo hannunsa riƙe dana momy yace "zoki jiyewa kunnuwanki abinda nakeji daga toilet ɗinnan" Muryar da suka sake ji ta banbanta da ta ɗazu, aka sake cewa "duk inda kuka shiga sai mun bibiyeku muna gaiyyatarku zuwa ɗaurin auren Aljani ɗan duƙususu sannan kuje ku shirya domin a nan gidan za'ayi taron" Momy ta kalli Dady Dady ya kalli Jannat, itama ta kalleshi tare da waro ido, kan kace me momy ta ruga da gudu hakama Dady sukabar jannat ɗin a bedroom ɗin, ashe suna laɓe a bakin ƙofa, itama Anum ɗin taji maganar su, tunda window na toilet ɗin yana jikin inda suke tsaye, cikin ɗaga murya akace "hahahaha bazakuje ku shirya ba, gashi Aljani ɗan ƙarami harya shirya?" Momy da Dady suka ruga da uban gudu, kai tsaye ɗakin farko na momy suka shiga, sukayi tsuru-tsuru, ko wanne da abinda yake saƙawa a ransa, Muryar Anum ta katsesu, dan sun haɗa baki da Jannat tace "ta rama mata dukan da Dady yayi mata ta hanyar firgitasu" aiko Jannat taje window ɗin momy ta sake sauya murya tace "hahahaha ku kaɗai muke jira saboda Aljanu sun taru a can inda kuke cin abinci bil adama ne kawai babu, ado zakuyi irin na bikin bil adama saboda muma munsha kwalliya" cikin sauri Dady da momy sukayi zigidir, tare da shawarar wane kaya zasu sanya, "Lokaci fa yana wucewa karku fusata shugabanmu Aljani mai feshin wuta" su momy na jin haka jikinsu na cigaba da rawa kowanne ya ɗauko sabon kaya wanda suke burin sakawa a bikin ƙanwar Dady da za'ayi, sosai sukayi kyau, kasancewar momy fara ce kyakkyawa shima Dadyn yayi kyau sosai momy ta sanya shadda less ɗinkin doguwar riga shikuma Dady dakakkiyar shadda mai yauƙi kalar sararin samaniya sai ɗaukar ido takeyi yasa hula momy tasa mayafi marar nauyi, acan parlo sukaji sautin kiɗa na tashi, inda aketa waƙe-waƙe, Jannat tasanya muryoyi biyu domin su sake rikita su momy jannat ta koma ɗaki ita kuma Anum tana can bayan window na parlo, a hankali suka tako suka iso parlon Anum dake durƙushe ta leƙa ta hangosu, sai da tayi dariya mai isarta kafin tace "rawa zakuyi sannan kuyi a hankali karku bige ɗan autanmu" Dady ya maimaita "rawa kuma? nida ko rawa banayi za'acamin wani inyi rawa, gaskiya bazan iya ba, badan dare ba wlhi da barin gidannan zamuyi ya kalli momy yace "Aljanu ne suka saukar mana a gida ya kamata mu bar gidannan" "Zakuyi abinda muka ce ne ko sai mun fito muku a siffar mu?" Dady yana turo baki yace "zamuyi, momy ma tayi harara tana kumbure-kumbure kai kace yarinya tace "yifa mukeyi" Dady ya fara rawa shida momy sai wani sunkuyar da kai yakeyi, acan jikin window ɗin aka sake cewa "girki a cikin minti goma shinkafa da miya shawara ta rage gareku sai ku shiga kicin" Momy tace "damu suke" Dady yace "ke muda aka samu yin rawa taya za'a sakamu yin girki?" Wani rudududu sukaji ai da gudu suka wuce kitchen Dady ya kalli momy kana ya haye kujerar tare da rafka tagumi, momy tace "minti goma fa aka bamu"...! Drop your comments domin samun cigaba. Tabbas akwai cakwakiya a ciki muje zuwa.. Page3 Shiru ne ya ratsa gidan, hakan ya bawa Dady damar yin magana, "momyn Jannat inaga fa mutanen nan sun tafi tashi mu koma ɗakina dan wlhi bazani ɗakinki ba" Jikin momy na rawa tace "Dadyn Jannat karfa mu tafi su kuma dawowa" hannunta ya kamo kana yace "Allah ya fisu nikam nayi nan, tunda baki kunna gas ba zomu wuce, ina zamukai uban abincin da sukace a girka?" suna tafe suna waige har suka wuce hanyar ɗakin jannat, momy tace "Dadyn Jannat Please barin je in duba ko tana lafiya" hararta yayi sbda abin ta cikin ɗakin Jannat ɗin ya fara, kafin yace "babu inda zaki ga dukkan alamu garin yawace-yawacenta ne ta kwaso Aljanu gobe insha Allah zan nemi malamin da zai zo yayi mata ruqiya da sassafe zan fice" Dady ya faɗa yana buɗe door na ɗakinsa. Koda suka shiga ɗakin har yanzu shida momy a tsorace suke daga abu yayi ɓurum sai su miƙe a zabure, tsabar tsoro ko kayan basu cire ba haka suka kwanta, Acan ɗakin Jannat Anum ta fito daga toilet tana dafe ciki, Jannat dake kwance wari ya addabeta sannan ta kasa tashi ta kawar da ledar cikin faɗa tace "haba Anum bayan fitsari kuma harda kashi kinsan kin cutar dani sosai kuwa?" ƙarasowa gaban drowar Anum tayi kafin ta kalli Jannat ɗin sannan tace "dan Allah kiyi haƙuri na tsorata ne sosai, yanzu zan fita dashi" Anum ɗin tayi magana kamar zatayi kuka, Jannat na kwance ta fitar da kashin zuwa toilet ta juye kana ta kora ruwa ya tafi, ledar kuma ta buɗe ƙofar waje ta wurga ta katanga kana ta dawo ciki tasa omo ta goge sannan ta ɗauki room freshener ta fesa kana tazo zata kwanta, "Kinyi sallah?" Jannat ta tambayeta, a'a banyi ba naga kema bakiyi ba" banayi ne" Jannat ta bata amsa a taƙaice, toilet taje tayo alwalah kana ta fara haramar yin Sallah dan har ta shimfiɗa sallahya komai nata irin na maza sometimes kuma takanyi abu irin na mata, "mai yasa bazakisa hijab ba?" Anum ta juyo da kallonta ga Jannat tana yamutsa fuska tace "yana shaƙemin wuya" "Kince kinason ki zamo mace akan me zaki dinga abubuwan maza, ki ɗauki hijab ɗina kisa" Badan taso ba ta ɗauki hijab tasa a kaikaice sannan ta tada sallahar, magriba da isha'i tayi, bayan ta idar ta ɗaga hannunta sama tana roƙon Allah ta jima a gurin daga ƙarshe ta miƙe ta ninke sallahya da hijab ɗin ta haye gado, can gefe ta kwanta tare da takure jikinta, itakam Jannat ta riga da tayi barci, sam Anum ta kasa barci babbar damuwarta Arshi da kuma idan gari ya waye wane babin zata kama, sannan a wane irin hali Arshi ɗin take?" sosai zuciyarta ta tsinke ta ƙaddarawa zuciyarta bazata sake samun farinciki ba, ta juya ta kalli Jannat da sai barcinta takeyi, a zuciyarta tace "Allah sarki zaman mutunci ne ya haɗani da ita tun ina makarantar primary kafin in shiga secondary na fara fuskantar tsangwama da tsana" wasu zafafan hawaye suka samu nasarar zubowa a idanunta, ta sanya hannu ta share, tana cikin tunin barci yayi gaba da ita, Ƙarfe 4:am Jannat ta farka, kana ta miƙe zaune tare da jingina kanta da jikin gado, tunanin mafita da zasu fuskanta ne ya faɗo mata, tabbas tasan ba ƙaramin ganganci tayi ba, na shigo da Anum cikin gidannan hankali a tashe take ta saƙa da warwara sbda ta fara tunanin idan har ta samawa Anum Aiki a gidan ƴar uwar momy wataran idan momy taje ko sistern nata tazo zata labarta mata cewar itace ta kawo mata mai aiki, can kuma Jannat ta tura yatsanta ɗaya a baki sbda tanada burin ingantawa Anum rayuwa duk da itama a karkashin iyayenta take, mahaifinta yanada arziƙi amma bawai yana sakar mata bane, 5k ta tambaya sai tayi masa dogon bayani, hakan yasa wasu lokutan take zama sisi bata magani, juyin da Anum tayi ne yasa Jannat tashin ta cikin sanyin murya tace "Anum yanzu fa ba lokacin barci bane ki tashi mu fara shawarar inda zamu ɓullowa lamarin zuwanki gidan aiki idan kuma gidanku zaki koma Tom, saboda wlhi ina cikin wani hali ko da wanne lokaci su momy suna iya shigowa, tunda Kinga jiya hankalinsu ya tashi" "Anty Jannat nafi son zuwa gidan Aikin saboda in cika burina na komawa mace sannan inci gaba da karatu kamar kowa" Anum ta faɗa tana kallon Jannat ɗin. "Shikenan ana kiran sallahar Asbha ki shirya zan baki Naira ɗari wlhi bani da kuɗi, ki hau Adai-daita zuwa anguwarku nikuma anjima zan zo gidanku sai muyi magana" Anum tayiwa Jannat ɗin godiya, Anum ɗin ta sakko daga kan bed tare da shiga toilet, alwalah kawai tayi ta fito sannan ta ɗauki hijabi ta kabbara sallah, lokacin da ta zauna zaman yin adu'oi aka fara kiraye-kirayen sallaha, Har tayi sallah ta idar idon Jannat a kanta, tasan yanzu Dady bai dawo daga masallaci ba, ta miƙawa Anum Naira ɗari tace "muje in rakaki amma ki tabbatar kin saka hijabi ki tafi dashi na baki kyauta" godiya ta sake yiwa Jannat ɗin kafin suka fito harabar gidan, sai a lokacin ma Lado mai gadi yake yin Sallah, ta buɗewa Anum ta fice sannan ta rufe ƙofar kana ta tsaya tana jiran ya idar da sallah, tana tsaye yayi sallama sannan yayi adu'oinsa ya shafa, yana shirin naɗe dardumarsa tace "Lado idan har naji labarin ka gayawa wani fitar ƙawata da na raka yanzu wlhi zaka fuskanci mummun hukunci tunda kai ka iya munafurci" Ta faɗa tana nuna shi da yatsanta, jikinsa na rawa tabbas yasan barazanar kora takeyi masa, yace "insha Allah babu wanda zai ji" ta wuce ba tare da ta ƙara bi ta kansa ba. Cikin sanɗa ta wuce ɗakinta tare da kullo ƙofa ta haye gado sannan taja blanket ta rufa har kanta, A hankali momy ta turo ƙofa tare da yin sallama, momyn ta tsaya daga bakin ƙofa sabda a zahiri tsoron Jannat ɗin takeji, "Jannat kinyi sallah kuwa?" "Eh nayi" Jannat ɗin ta faɗa tana daga cikin blanket. Duk da tsoron Jannat ɗin da takeji bai hanata cewa "tashi mu shiga kitchen yau da asbha tafiya ta kama dadynki da wuri zai fita yana dawowa daga masallaci" Jannat ta zuro ƙafafunta ƙasa kafin ta miƙe tana turo baki, momy ta jinjina kai kana tace "wato wuyanki ya isa yanka ko? daga ki tayani aiki sau turo baki, na ma mance ina kwana?" Jannat ta sunkuyar da kanta ƙasa kafin tace "good morning momy" Kallon banza ta watsa mata kafin tace "wuce muje" Kai tsaye suka wuce kitchen suka fara hada hadar haɗa abin karyawa, momy take bata labarin abinda ya faru jiya, a maimakon Jannat ɗin ta jajanta musu sai kawai ta fashe da dariya harda tafa hannu, abin ya matuƙar bawa momy mamaki, Dady ya shigo lokacin gari ya fara haske, har ƙasa Jannat ta durƙusa ta gaishe shi kafin ta ɗago sukaci gaba da aiki, bayan ya amsa ya wuce bedroom ɗinsa, ƙarfe 8:am suka kammala komai da komai, lokacin Dady ya fito sanye da riga t-shirt fara da baƙin wandon jeans, Jannat taje tayi brush ta dawo dining suka fara karyawa bayan momy ta zubawa kowa. A hankali take tafiya har ta iso bakin titi, cikin sa'a tana tare wani mai napep ya tsaya, ta shiga tare da gaya mata anguwar da zai kaita, suna tafe tana ta tunani duk da dai ma tunanin nata bai wuce akan abu biyu ba, suna isowa ta fito kana ta miƙa masa kuɗinsa sannan ta fara tafiya har ta iso ƙofar gidansu, gidane da zamu iya kiransa da gida na masu ƙaramin ƙarfi dan su Anum ba wasu masu hali bane, sai Ummu tayi sana'ar siyarda kamu take samun kuɗin da zasu ci su sha, bakinta ɗauke da sallama Anum ta tura ƙofar galan galan ɗin gidansu, tana tafe tana tunanin koyaya Arshi ta kwana, sallama tasake yi kafin ta tura ƙofar ɗakin da suke kwana, juyowa tayi ta kalli ƙofar ɗakin Ummu ga mamakinta taga takalmi a gurin, fasa shiga ɗakin nasu tayi ta dawo da baya zuwa ɗakin Ummun, ta yaye labule tare da yin sallama, jin Muryar Anum yasa Ummu toshe kunnuwanta, cikin tsananin ɓacin rai da tsantsar tsana tace "mai ya dawo dake nan gidan ban riga da na sallameki ba? akan halittar nan taki mutane suka daina shigomin gida har cewa akeyi wai kina tsorata mutane, to yanzu hankalinki ya kwanta sun daina zuwa mun zauna bamu da cin yau bare na gobe" Ummu takai ƙarshen maganar tana miƙewa tsaye, "Haba Ummu wai shin ba Allah bane ya baki anty Anum ba?" Arshi tayi maganar tana zarewa Ummu idanu, "Allah ne ya bani ita nace bana sonta ko ana dole ne?" Arshi tayi wani irin gurnani kamar zaki kana ta taho da gudu tayi ciki da Ummu, ta kamo hannayenta ta kamo ƙafafuwanta ta haɗesu guri ɗaya kafin tace "ko kin ƙi ko kinzo anty Anum jininki ce babu inda za'ayi ki sauyata, Arshi tayi maganar cikin ƙaraji, zuciyar Anum na dukan uku-uku damuwarta kar Arshi ta yi kisan kai, duk da hawayen dake zubowa a idanunta jikinta na kyarma bai hanata ƙarasa shiga cikin ɗakin Ummun ba, ta sanya hannunta ana Arshi cikin Muryar kuka tace "ki rabu da ita koba komai taci darajar uwa a gurinmu" tabbas Ummu ta maguzu dan bakinnan yayi ƙato, dama gashi lafcece Arshi ta fice a ɗakin tana kamo hannun Anum, can ɗakinsu suka wuce, ta zauna akan tabarma kasancewar itace arziƙinsu a ɗakin sai katifa wace duk ta yayyage ga kuɗin cizo shima yana zuba shagalinsa, "anty Anum mai zai hana mu samawa kanmu mafita mubar gidannan" "Arshi Gara ma ke nikam duk inda naje guduna zasu dinga yi kekam matsalarki ɗaya ce, idan akayi miki maganin Aljanun kanki komai zai zo da sauƙi" rai a ɓace Arshi tace "anty Anum Please stop saying that bani da larurar komai, idan zaki yarda ki yarda Ummu bata sonmu" Muryar Ummun suka tsinkayo tana daga tsaye ta riƙe ƙugu tace "iya Anum nace tabar gidanan Arshi idan kika fita ba da yawona ba, Anum da abin yaso bata dariya duk da tana cikin takaici tace "wai Ummu ya akayi kika dawo daga wancan gidan bayan kince babu uban da ya isa?" Ummu tayi shiru batace komai ba, tana daga tsaye Arshi tace "Ummu tunda dai bakyason anty Anum nima zan tafi Kinga sai ki zauna ke kaɗai, "wato Allah ya kawo mu zamanin da ɗan cikinka sai ya gaya maka magana son ransa? duk kuyi zanyi maganinku, kekuma Arshi ki tashi ki shirya naji labarin wani mai maganin iskoki dan wlhi naci gaba da zama dake a cikin wannan gidan zuwa gaba kasheni kawai zakiyi" Ummu ta faɗa tana harar Anum. "Nikam babu inda zani" Arshi ta faɗa tana turo baki, Ummu na tafiya Arshi tace "kinga dole mu samowa kanmu mafita, naji labarin wai Ummu zatayi aure, wlhi tallahi idan tayi sai na saka mijin fitsari a wando, sun daɗe suna tattauna halin rayuwa, daga ƙarshe Anum ta miƙe tsaye, "ina zaki?" "Zan yi wanka in sauya kaya saboda anty Jannat tace zata rakani wani gida in fara aiki" Anum ta faɗa tana juya baya tare da samun zani ta ɗaura a ƙirjinta, Arshi na daga zaune tace " Wai labarin yayi muku kuwa? Dan Allah kuyi following account ɗina arewabook Drop your comments Shin wane ƙalubale zata fuskanta a gurin aiki, gafa maganar auren Ummu Arshi zata barta tasha ruwa kuwa? Page4 Shigarta wanka bayan ta cire zanin jikinta zuciyarta ta sake tsinkewa sbda ƙarewa halittar jikinta kallo da ta dinga yi, duk da cewa bawai baƙon abu bane a gurinta amma takanji rashin daɗin ganin halittarta a hakan, abinda ya sata daɗewa a wanka kenan dan har takai tsawon one hour tana wankan, itada ba ma'abociyar daɗewa a wanka ba, ta ɗaura zani taji Arshi na cewa "anty Anum kiyi sauri ki fito Anty Jannat tazo" Da sauri ta wanke sosan wankan kana ta fito tana washe baki, Ummu dake can ɗaki tana jiyo sallamar Jannat ɗin amma bata amsa ba. "Oyoyo antyna ta kaina" Anum ta faɗa tana washe haƙora, "Oyoyo ƙanwata da fatan kin shirya saboda time ɗin tafiyata school yayi, sbda kar in saɓa alƙawari ne yasa nace barin biyo idan na ajiye ki sai in wuce" Jannat ta faɗa tana yi mata murmushi, Arshi tace "anty Jannat ki ƙaraso ciki kafin ta shirya, nima zan biku" Cikin tausasa murya Jannat tace "kiyi haƙuri Arshi babbar matsalata Anum idan har ta samu mafaka insha Allah kema kamar kin samu ne" Arshi ta narke fuska kamar mai shirin yin kuka. Ɗakin su Anum ɗin Jannat ta shiga, a gurguje Anum ta shafa mai sannan ta ɗauko powder zata shafa, Jannat ta dakatar da ita tare da cewa "karki shafa sa kaya sannan muga wane za'ayi" duk cikin kayanta riga da wando ne na maza sai hula P/cap shi take sawa, sbda tun tana ƙarama haka Ummun take sanya mata, ta ɗauko wani ƙaton wando zata sanya Jannat ta ƙwace tare da cewa "karki manta a matsayin cikakkiyar budurwa zakije ba a namiji ba, mai yasa kayan maza zasu shigo ciki?" Anum ta shagwaɓe fuska kafin tace "bani da kayan da zasu dace" Jannat ta kalli Arshi kana tace"miƙomin ledar da nazo da ita" Arshi ɗin ta ɗauko ta kawo gaban Jannat, kasancewarta ƙwararriya ta fannin makeup batayi ƙasa a guwaiwa ba, ta fara fito da kayan kwalliya, sai da ta fara shaving ɗin gemun Anum ɗin sannan ta sanya cum ta gyara mata gashin kanta kafin ta fara tsara inda kwalliyar zata kasance, sun shafe tsawon lokaci anata gyaran fuska kafin daga ƙarshe ta ɓula mata kunne tasa mata ɗan kunne mai barima, sosai Anum tayi kyau, dan haka take kunnenta ko ɓuli babu, abin sai yai matuƙar burgeta duk da cewar taji zafin yin hakan, "Bamu da isasshen lokaci Anum har yanayin tafiyarki dole ki sauya saboda yawanci kinayin abu kamar na maza, sannan ki rage gwada wa abu ƙarfinki, magana ma ki dinga dai-daita wa, Saboda gudun kar mu fuskanci matsala" Jannat ta faɗa tana buɗe ledar ta ciro riga da skirt na atamfa mai kyau, ta miƙawa Anum, Anum ta jujuyasu tare da cewa "anty Jannat a jikina zan saka?" "Eh sakawa zakiyi idan har Allah ya bamu nasara zan gayawa Ƙanwar momyn cewar duk kwana uku zaki dinga dawowa gida" "Tom amma anty Jannat idan nasa kayannan kunyar tafiya dasu zan dinga ji" Cikin jin haushi Jannat ta watsa mata daƙuwa kafin tace"ana ga yaƙi kina ga ƙura, kinsan dai na gaya miki zan wuce school ko akan rashin zuwa da banayi malaminmu zai iya kiran Dady, idan kuma zaki bari inje in dawo idan na dawo sai in biyo tanan" Arshi dai tana kallonsu sosai tausayin Anum ɗin ya kamata, babu damuwa zan jiraki tunda ai bazaki daɗeba ko?" "Eh ba daɗewa zanyi ba, naso ace ma mu wuce hospital daga nan sbda mu samu wasu bayanai a kanki" "Shikenan babu damuwa Allah ya dawo dake lafiya" Anum ta faɗa cike da nuna kulawa. THAILAND Yangon Zaune suke a cikin wani hadaɗen parlo mai kyau sosai, parlon ya kasance madaidaici, yana ɗauke da tausasan kujeru guda uku, dukkansu masu zaman mutum ɗaɗɗaya ne, color na kujerun light blue ne, yayinda samansu yake kewaye da adon katako mai kyau, fentin jikin bangon fari ne, sannan kayan kallo da su fridge da sauransu, ɗakuna uku ne a gidan, bedroom biyu sai kitchen kowanne bedroom da toilet a cikinsa, acan parlo wasu kyawawan samari ne a zaune ko wanne fuskarsa babu walwalah dukkansu farare ne hakan shizai tabbatar muku da cewar haifaffun garinne, Masha Allah kaf cikinsu basu da wani makusa duk da cewar suɗin abokan juna ne, ɗaya daga cikin su mai suna Khair yace "ya kamata Ku hanzarta kunsan yau weekend su Leeela basa free idan har Allah ya bamu nasara sai mu taho da yaran" Aman ya kalli agogon dake ɗaure a tsintsiyar hannunsa kafin yace "tabbas bamu da wani enough time ku hanzarta" Bahi da sai yanzu yayi magana, murya a sanyaye yace "ni am ready ku nake jira" su biyun suka miƙe shima ya miƙe, dukkansu suka haɗa hannu alamar sunyiwa Juna alƙawarin babu wata matsala kana suka fito tare da kulle gidan, a inda suka tsara tun farko hakan ne ya kasance ko wanne zai hau tasa motar saboda tsaro, hakan yabawa Bahi damar kiran Leeela, ringing ɗaya Leela ɗin ya ɗaga, time ɗin yana tare da ƴan mata sai wani iyayi sukeyi masa, "oga su Aman fa basu daddara da gargaɗin da kayi musu ba, yanzu haka dukkanmu muna hanyar zuwa ɗibo ƴan matan ne" Cikin sauri Leela ya mike tsaye zuciyarsa na zafi yace "har akwai wani wanda zai tsallake min layin da na zana, inaaa!.." Yai maganar yana watsar da ƴan matan dake a kusa dashi, cikin zafin nama ya shiga wani ɗaki wanda ya kasance yana cike da makamai, ko me ya ɗauka oho ya fito ya ƙarasa ciki, kafin ya danna wasu numbobi a wayar tafi da gidanka, ringing ɗaya aka ɗaga cikin ɓacin rai yace "Raja kaje titin Haiphong cikin sauri akwai wasu motoci guda uku da zasuyi parking a gurin yanzu yanzu ka kawomin su nan" daga can ɓangaren Raja yace "an gama mai gida" Cikin shiri ya fito daga gida, Raja baƙi ne sosai daga ganin yanayin fuskarsa zaka tabbatar da babu mutunci. Suna cikin tafiya dukkansu ukun kafin su ƙarasa titin Haiphong ɗin motar Khair ta lalace, dama shi da Aman kusan a tare suke tafiya, shikam Bahi yayi nisa sosai, Aman ya fito cikin sauri tare da riƙe hannun Khair kafin yace "khair ga dukkan alamu Bahi bashi da gaskiya zomu juya komai zai iya faruwa damu anan" Hankali a tashe Aman yake magana, hakan kuma bai hana Khair durƙusawa a gaban motarsa ba, ya fara duba abinda yake bashi matsala, Aman ya kamo masa hannu Khair ɗin yana jan Aman, Aman yana jan khair, cikin zafin nama Khair ya mari Arman kafin yace "tabbas baka da hankali, mai yasa abokinmu aminin mu zaka dinga yi masa mummunan zato, Bahi bazai iya yarda a haɗa baki dashi.... Ƙarar Harbin bindigar da sukaji ne yasa ko wanne dai-daita nutsuwarsa, Arman yaja Khair suka gudu, saboda sun fara ƙure musu gudu, suna gudun har suka iso gurin motar Aman suka shiga cikin gaggawa ko rufe murfin motar basuyi ba, Arman ya fara driving, abin mamaki babu Bahi babu alamarsa, sukuma su Aman sunata gudu mutanen na binsu, mutanen Leeela suka dinga sakar musu bindiga har suka sace musu taya ɗaya, sosai tsoro ya kamasu tunda dai basu da wani makami da zasu kare kansu gashi kuma mutanen sunzo har gabansu, suka durƙusa a gurin kowannensu ya ɗaga hannu sama, cikin wata mummunar murya Raja yace "mai yasa zaku shiga hannun oga bayan kunsan bazaku iya dashi ba?" yai Maganar yana hanɓare Aman, wayar Khair ta fara ringing cikin tsoro ya kalli aljihunsa hannunsa na a sama, Raja ya sanya hannu ya ciro wayar kana ya kara a kunne, cikin ƙaraji yake cewa "wayeee!!" Nice kakarsa da fatan dai yana nan ƙalau ko?, yau ne birthday ɗinsa har mun shirya nida ƙanwarsa ina fatan zaka sanar masa" Raja ya daka mata tsawa cikin ƙaraji yace "keeee kaka, ba kaka kike ba ko kakus ne, jikanki ya shiga hannun Iyalan Leeela da fatan zaki cigaba da murnar shagalin bikin birthday ɗinsa" Hannun granny na rawa ta miƙawa Arya wayar hannun granny yana karkarwa, da sauri Arya ta tallafi granny tare da kallon ƙasan ƙafafunta tace "granny lafiya naga kamar fitsari kikeyi?" idanun granny sun kakkafe tace "ba dole ba, tun daga nan na fara jiyo jiniyar sojoji sun garƙame Khair, nima Gara in mutu kawai" Cikin kiɗima Arya tace "yimin bayani wani abun ne ya faru?" Wata uwar tusa da granny ta saki ne yasa Arya sake hannun granny tare da matsawa can gefe rai a ɓace tace "baki gayamin abinda ke faruwa ba, sannan kin cikawa mutane ciki da guba anya granny ba haka kikayi a yarintarki ba?" Da sauri granny ta buɗe ido, ta ɗorasu a na Arya, a zuciyarta tace "inafama da wani baƙincikin ta sake cusamin wani" tsabar takaici granny ta kasa furta koda kalma ɗaya, tana zaune a gurin ta dinga banko tusa mai wari, Arya kam guduwa tayi sbda cikinta ya fara rikicewa, da gudu ta nufi toilet ta fara tsuga gudawa har tana riƙe cikinta, sosai ta haɗa gumi sbda abin babu sauƙi, tana fama da kashi granny ta leƙo cikin rage murya tace "Arya ki fito zan shiga ina tunanin abincin da nayi mana jiya shine ya lalata mana ciki" sam Arya bata jinta bare tasan da ita takeyi, murya a narke granny ta sake cewa "Arya fito zanyi a ƙasa kinsan ba pant na saka ba" wata uwar tusa granny ta sake sakewa wacce tasa Arya ɓarowa daga gurin kashin, da rarrafe ta fice cikinta na murɗawa, idanuwan granny sunyi ƙulu ƙulu ta haye gurin kashin tare da zakin zawo ɓirrrrrr a hankali ta sauke ajiyar zuciya tare da lumshe ido, ta daɗe tana tsigawa dan har wani irin gumi takeyi gashi sam jikinta babu wani ƙwari, da ƙyar ta sakko tare da kunna ruwa a pampo ta ɗauki buta ta tara murya kamar an sanyata magana dole take cewa "oh wannan Arya ɗin haka ta fice ko kashin bata wanke ba, inda take ma bazan dosa ba" granny tayi maganar tana dafe kwankwaso, a duƙe ta fice waje bayan ta kora kashin ya wuce, ta jingina da jikin bango, kira ya sake shigowa, wayar na ajiye saman kujera, da sauri granny takai hannu ta amsa kiran cikin marairaice murya tace "waye dan Allah ku sakarmin jikana shi kaɗai nake dashi" Khair yana kuka taji muryarsa yana cewa "granny ki sakamu a adu'a yanzu haka gidansu Leeela zamu wuuuu..." Granny bata tsaya jin ƙarashen zancen ba ta zube a gurin ko numfashi batayi, Arya da ta koma ɗakinta ta watsa ruwa ta fito ta samu granny a kwance a gurin, ta kira sunanta yakai sau uku amma shiru bata amsa ba, hakan ya sake tabbatar mata da suma tayi, da sauri ta buɗe fridge ta ɗauko ruwa mai ƙanƙara ta tsiyaye a fuskar granny tana daga tsaye, a zabure granny ta miƙe tare da cakumo wuyan Arya tana cewa "Leeela ka sakarmin jikana kokuma inzo in gwada maka wasan dambe wanda nayishi tare da kakanka" Arya ta waro idanu sam har yanzu bata fahimci inda granny ɗin ta dosa ba, sai wasu abubuwa takeyi kamar mai taɓin hankali, "shaƙe mata wuyan da granny ta sake yi a karo na biyu ne yasa ta fincike hannunta cikin rashin sa'a granny ta zube akan markaɗaɗen Attahiru dake a hannun Arya zata shiga kitchen samawa kanta abinci, sbda kashin da tayi cikinta ya zazzage, ihu granny ta kurma, cewa takeyi babu wando ku taimaka babu wando, Arya ɗauko min Vaseline in shafa ko pipi zeyi min sauƙi, ai duk kece muguwa mai hali irin na uwarta, nace Miki babu wando ki kawomin koda sabulu ne in wanke" Arya ta tsaya tana ta cashewa da rawa har da juyi cewa take new birthday in this time lol....! Ina mutanen granny tace muku babu wando🤣🤣 5 Da ƙyar Granny ta samu ta dafa bango kana ta miƙe, tsabar ruɗu da azaba ya sanya ta cire bujen skirt ɗin dake jikinta, ta ƙarasa ɗakinta da gudu, tana zuwa ta kunna fanka ta matso da fankar jikin gadon, ta inda iska zai dinga ratsata sosai, da sauri ta haye gado tare da wangale ƙafafunta ta lumshe ido, duk da haka dai zafin na shigarta, sai can anjima barcin wahala ya ɗauketa, Arya na tsaye har bayan tafiyar Granny gabaki ɗaya bata jin walwalah sbda tunowa da Khair da tayi rabonsa da gida tun safe dan har sunyi waya yake ce musu zai je anguwa idan ya dawo sai yayi musu photo dukkansu na murnar birthday ɗin nasa, ringing ɗin da wayar Granny ɗin tayi ne yasa Arya ɗagawa sbda new number ce, kafin tayi magana taji ance "ashe dai ba rayuwar ɗan naku bane a gabanku, kaka idan bakisan waye Leela ba yau zan gaya miki, shine masheƙi makashi wanda baya bari sannan kuma mayunwacin zaki ne shi bayan haka ran mutum tamkar ran kiyashi ne a gurinsa" jikin Arya a sanyaye ta kalli wayar kafin ta katse kiran, zuciyarta nayi mata zafi ta wuce ɗakin Granny, buɗe labulen da zatayi ta hango pipi a wangale, da sauri ta mayar da labulen ta rufe tare da fashewa da kuka, tana cewa Khair mai yasa ka kai kanka inda za'a halaka ka, sosai zuciyarta take yi mata zafi yayinda take ƙarfafawa ranta zuwa taimakonsa koda zata fuskanci wasu ƙalubale matsawar bazai taɓa mutuncinta ba, da wannan tunanin ta shiga ɗakinta ta fara haɗa kaya a ɗan madai-daicin akwati, haɗaɗun kaya masu masifar kyau ta zuba kana ta rufe akwatin, sannan ta ɗibi takardu masu muhimmaci a gareta kafin ta zuba a ƴar jakarta, kai tsaye ta faɗa toilet wanka tayi a gurguje kafin ta fito, ƙirjinta ɗaure da towel ta zauna gaban mudubi, so takeyi tayi haɗaɗiyar kwalliya duk da itaɗin mai kyau ce, ko bata shafa komai ba, tunowa da tayi da aikin dake gabanta yasa ta kawar da duk wasu tunani ta fara tsara kwalliya cikin nutsuwa, sosai tayi kyau dan idan ka ganta kamar ka saceta ka gudu tsabar kyau, ta ɗauko Pakistan milk color mai adon golden ɗin stone masu sheƙi da ɗaukar ido, sosai kayan suka amshi jikinta, mayafin ta rataye shi a kafaɗarta, kana ta maƙala ƴan kunne wajen guda huɗu sannan tasa zobe da warwaro da ƴar siririyar sarƙa, Masha Allah tayi kyau sosai, musamman ma da ta sake gyara gashinta wanda ya zubo mata har gadon baya ta sake tsaga tsakiyar gashin tayi style dashi tacan gefe, tasa abin kwantar da gashi ta kwantar ta mulke shi da mai, tana sunkuye tana ɗaura igiyar takalminta Granny ta shigo tana mutsike ido, "Arya ina zakije bayan kinsan daga ni har ke rayuwarmu tana cikin hatsari, na shiga tashin hankali tunda naji ance Khair yana gurin Leela duk shine sanadiyar rikicewar cikina, yanzu ina zakije?" Arya ta dafa kafaɗar Granny kafin tace "kowanne bawa da tasa ƙaddarar insha Allah bazan bari su cutar min da khair ba, koda yaushe mafarki na shine ace munyi aure dani dashi" Granny ta katse ta da cewa "Arya duk wannan lissafin da kike bakida ƙarfi da ikon tunkarar Leela" Zan jarraba nayi miki alƙawarin tare zamu dawo dashi" Arya ta faɗa tana saka madai-daiciyar wayarta a cikin handbag, kafin ta sake kallon kanta a mudubi tace "Granny ayimana fatan nasara" Gabaki ɗaya gani takeyi kamar ta rasa su ne an gama, Ta yi tagumi hawaye na zubowa, KANO NIGERIA A ƙurarrren lokaci Jannat ta dawo, duk da yamma da tayi bai hanata biyowa ta gidansu Anum ba, sai dai abinda kunnuwanta suka jiyo mata, "Wlhi tallahi aure kamar nayi shi babu abinda zai hanani yin aure, dan ubanku tun zawarawan arziƙi suna zuwarmin musamman ke Arshi kinsa na koresu yanzu wanda zuciyata da hankalina ya kwanta dashi shima baza'a barni in aureshi ba? to albishirinku har na karɓi sadaki an gama komai, jiya ma munje gurin masu kayan ɗaki, kekuma mata maza karki sake ki zauna min a gida wlhi tsab zaki iya kashemin aure, kekuma Arshi kamar inda na faɗa idan kika tafi wani guri wlhi ban yafe Miki ba, jibi za'ayi ɗaurin aure da tarewa, kisan inda dare yayi miki, jikin Anum a sanyaye ta miƙe daga zaman da take idanunta na zubar da hawaye tace "tunda na taso nake fuskantar tsangwama da kyara daga gurinki, gami da kalmar kora da cewa kin yafeni, tabbas Ummu kalmar yau tafi ko wacce ɗaga min hankali duba da inda kike furicin in bar miki gida zakiyi aure, har kike kirana da mata maza Ummu kodai ba kece kika haifeni ba?" Cikin azama Ummun ta matso zata wanka mata Mari Jannat ta tare Anum marin ya sauka a gefen fuskarta, cikin Muryar kuka Anum ta riƙe hannun Jannat kana tace "akan mai yasa zakiyi haka anty Jannat?" Rai a ɓace Jannat tace Babu, ɗibo kayanki kizo mu tafi, kekuma Ummu ki jira saƙo daga gidan barrister na zuwar musu gida da kikayi, an nemi dubu hamsin ba'a gani ba" Jannat na gama faɗar haka ta kamo hannun Anum suka wuce ɗakinsu, a kwance suka samu arshi sai kuka take yi, Jannat ta dafa kafaɗarta kana tace "zata dinga leƙo ku kedai ki nutsu tunda Ummunku tana sonki" Jannat tayi maganar cikin ƙarfin hali ne dan ko a tarihi bata taɓa jin tarihin uwar da ta watsar da ƴaƴanta har take aibantasu ba sai Ummu. Ummu na daga ɗaki tace "sai su nemi ɓarawonsu nida ko kwana ma banyi a gidan ba, to ina ni ina dubu hamsin uban me zanci da ita, A gaggauce suka shirya komai, ita da ta saba da sanya kayan maza da tasa atamfa sai taji wani iri, gabaki ɗaya ta takura, bayan sun kammala shiri Jannat ta ce "Anum kiyiwa Ummu sallama" Anum ta kawar da kanta gefe gami da ɗaukar mayafi ta rataya a wuya kamar za'a ɗaure wuyan saniya, da sauri Jannat ta janyota tare da cewa "tun yanzu kina neman bamu problems ko?" Anum ta sunkuyar da kanta ƙasa. "Allah ya kiyaye hanya anty Anum dan Allah ki dinga waiwayomu karki damu da cin mutuncin da Ummu take yi miki" Sosai takejin idanuwanta duk sun ciko sbda tasan dole zatayi kewar ƙanwar tata, hawaye na shirin zubowa Anum tace "karki damu insha Allah, "kar dai ki sake kiyi kuka ki ɓata makeup dan wlhi zaki sake ja mana aiki" Jannat ta faɗa tana sanya tissue tana gyara mata gefen idanunta, dole ta mayar da kukan suka fito tsakar gida dukkansu, Ummu tana waya dole yasa suka tsaya har ta kammala, ashe ɗaurin auren nata gobe ne, kaf cikinsu basu da labari, Jannat tai ƙarfin halin cewa "Ummu mun fito" washe da baki Ummun ta yaye labule tana daga zaune da wasu kwalaben magunguna a gabanta tace "Allah ya tsare da fatan zaki haramtawa kanki zuwa gidana" ta gayawa Anum kafin ta sauke labulen suka wuce, suna tafe har da Arshi idanunta sunyi jajir sbda kewar yayar Tata, wayar Jannat tayi ringing, da sauri ta ɗaga cikin shagoɓa naji tace "Anty muna hanya ne, kinsan yarinyar yanada mata lafiya, so sai da ta gama sallamarta tukunna" Jannat ɗin ta kai ƙarshen zancen da cewa "insha Allah mun kusa" Tunda suka fita can waje gaban Anum yake ta faɗuwa, ga yamma tayi dan ƙarfe 5:pm zatayi, Kai tsaye suka fito zuwa gurin drivernsu Jannat, Arshi na kuka Anum ta shiga mota backside ita da Jannat suna ɗaga mata hannu, har motarsu ta wuce bata koma gida ba sai da taga an fara iska alamar gari ya haɗa hadari, jiki a sanyaye ta kaucewa jinginar da tayi a bango kafin ta ƙarasa cikin gidan, zuciyarta a cunkushe ta wuce ɗakinsu tare da kwanciya a didigaggiyar katifar da a yanzu ta kasance nata, sosai take kuka bakinta har wani karkarwa yake, can ta tsinkayo Muryar Ummu a ɗakinta tana yiwa bazawarin da zata aura kirari, jin Ummun tace "Tom idan ka ƙaraso sai ka kirani a waya in fito" Anum ta sauke sassanyar ajiyar zuciya, a fili tace " yanzu wasan ya fara billahi". Tana kwance ƙamshin wani haɗaɗen turare ya doki hancinta, a hankali ta tashi zaune gami da ware idanunta, "Arshi na fito ki kula da gida, sannan ki tace min kamu yanzu zamu ci gaba da sana'a, ga ɗari biyar kiyi abincin rana da na dare" Arshi ta taso tazo bakin ƙofa inda Ummun take tsaye tana sanye da riga da zani na leshi light blue, Ummun tayi kyau sosai, " Ummu mai zan siya na ɗari biyar rana da dare?" "Ubanki ne ke ciyar dake ko ni? Tunda garin Allah ya waye ko ruwa ban kai bakina ba" Arshi tace "muma ai babu abinda mukaci" "Kinga ko me kikaga dama ki dafa nikam natafi siyayya" Ummu ta faɗa tana cigaba da tafiya. Bayan fitar Ummun da jimawa Arshi ta shiga ɗakin Ummu, wanda rabonta da shiga tunda ta fara nuna musu bambanci tsakaninta da yayarta, tana daga tsaye jingine da bango ta hango wani ɗan akwati mai kyau, ta sakko dashi ƙasa kana ta mimmiƙe ƙafafu, kafin ta zuge zip ɗin idanunta suka fara cin karo da wasu kwalaben magunguna, a jikin wasu harda hoton nono da mace babu wando, kasancewar tayi karatu kuma ta iya Hausar boko da turanci, yasa ta fara karanta amfanin maganin tunda yana a rubuce jikin kwalbar, tunda taga an rubuta yana matse gaban mace, tai saurin mikewa taje ɗakinsu ta ɗauko man da take shafawa a bayanta, ta dawo ɗakin Ummu ta lakaci man ta kwaɓa da maganin matsin, cikin sauri ta cigaba da firfito da ragowar tana lakatawa tana zubawa daga ƙarshe ta gyara ta inda baza'a gane ba, sannan ta rufe akwatin ta mayar tana dariyar, kwalbar hannunta ta kalla sai kuma ta sake tuntsurewa da dariya a fili yana cewa "Aboniki haɗe da Loko" sai kuma ta tafa hannayenta ta koma ɗakinsu, ta ɗauko hijab sannan ta fito waje, shafi ta wuce ta siyi yoghurt da cincin irin ɗan kanti, kana ta koma gida ta gyara zama ta buɗe murfin gorar, tana sha tana lumshe idanu. Suna tafe a mota yana jifanta da wani irin kallo mai cike da so da ƙauna, bazamu kirashi da yaro ba, dan a ƙalla zaiyi shekaru 45yrs a duniya, Ummu kuma zatayi shekaru 40yrs "Babban farincikina bai wuce inji an ɗaura aurenmu ba" Ummu tayi murmushi gami da cewa "me kakaci na baka na zuba, aure inhar munada rai da lafiya ai kamar yau ne" tayi maganar tana jifansa da murmushi, "kinsan me?" "A'a" Ummu ta bashi amsa. "Akwai wani gida da mai gidana ya bani kafin in kammala nawa, acan zamu zauna, ya kamata in kaiki ki ganshi," "Ummu ta rausayar da kai, "na gaji mu bari har gobe in Allah ya kaimu yanzu dai muje kasuwar kawai" "Na mance ban sanar dake ba, ai ɗazu mama ta kirani wai an gama siyayya shine nace to bari ko can gidan muje sai a duba abinda ya dace a siya" Itakam har ga Allah ba haka taso ba, karta fara complain ne kawai yasa yace "masa kanta na ciwo ya dawo da ita gida, shima ya ɗan fahimci wani abu sai ya basar"...! Page6 Washe gari tun safe ƙawayen Ummu suka cika gida, anata hada hadar ɗora tukunyar abinci, abinka da Ummu ƴar gaye ansha kitso da lalle tayi rass abinta, babu wanda zai san da akwai Arshi a cikin gidan idai ba ɗakinsu ka leƙa ba, anyi hidimar biki an kammala ko ƙofar ɗaki bata fito ba, Allah ma yasa bata sallah kawai tai kwanciyarta,da la asar aka wuce da Ummu gidanta Masha Allah gidan babu makusa domin na mutum ɗaya ne sai ɗakuna uku harda kicin huɗu, da yake bata samu matsala dashi gurin sanar masa da zata tare da Arshi ba, ya riga ya amince, da akazo tafiya Arshi kam cewa tayi sam babu inda zataje, daƙyar da siɗin goshi ta yarda ta bisu, suna isowa gidan bayan sun sauka an fara firfitowa ta leƙa ɗakunan, babu laifi tsaf tsaf suke, ta nemi ɗakin dake can gefe kusa dana Ummu ta zauna a ciki, dan har da ƴar madai-daiciyar katifa da pillow, kowa sai sam barka yake har maƙota duk sunyi kara an rako Ummu, zuwa magriba duk aka watse ya rage daga Ummu sai Arshi a gidan, ɗakin na Ummu ciki da parlo ne, duk da ba wasu tarkace ne a ciki ba yayi kyau, parlon kuwa kujeru uku ne a ciki, irin na hannu sai Tv irin wanda ake ajiye shi asaman tebur, tsakar ɗakin malale yake da ledar tsakar daki, acan waje, cikin kitchen jerin tukwane ne da kuloli sai randar ruwa, sai da akayi sallahar isha'i sannan Ummu ta fito tana sanye da atamfa ɗinkin doguwar riga yayi mata kyau, tai sallama a ɗakin Arshi, murya a sanyaye arshi ɗin ta amsa da "wa'alaikumussalam" kafin ta miƙe daga zaman da take ta kwanta, Ummu ta ajiye abincin saman kujera ƙarama kafin tace "ki tashi kici abinci banga amfanin zama da yunwa ba" Arshi ta yamutsa fuska gami da cewa "zanci" Ummun ta fice, tana komawa ɗaki ta sake gyara kanta tare da feshe ko ina da turaruka, wayarta dake ajiye saman kujera tayi ringing, da sauri ta ɗaga tare da karawa a kunnenta cikin ƙissa take cewa "aminci Allah ya tabbata ga Alhajin Allah" daga can ɓangaren yace "tare dake Hajiya, ina fatan an shirya komai aiki kawai zan fara" Ummu ta kwashe da dariya kana tace "wasu ma sai kazo a sake shirya su" yana dariya yace gani a ƙofar gida, ai ko abokai na hana su rakoni" ya katse kiran. Fuskarsa ɗauke da fara'a yai sallama gami da ƙarasowa ciki, Ummu na daga ɗaki tana cewa "Alhajin Allah sannu da ƙarasowa" tare da zuwa tai hugging ɗinsa" kiss ya yi mata a goshi tare da rungumeta suka zauna, bayan yayi mata ya gajiyar biki ya ajiye ledar a saman tebur na katako mai ɗan faɗi, ta mike ta fito zuwa kitchen ta ɗauko plate da cokali tare da cup ta kawo, already an riga da an yayyanka naman juyewa kawai tayi, suka fara ci, bayan sun kammala sai ragowa ta rufe kana suka sha drinks ɗin sannan ta kawar da kayan, ta nufi toilet tunda yana a cikin ɗakin, bayan ta fito shima ya shiga, ta wuce taje tasa sleeping dress mai shara-shara, Alhajinku yahau haɗiyar miyau, ya kasa haƙuri har sai da yaje gareta "ina maganin da na baki ajiya?" Ummu na murmishi ta nuna masa wani ɗan ƙaramin akwati, kasancewar dukkansu suna uwar ɗaki ne, bayan ta buɗe ta miƙa masa ya lakata ya shafa a gabansa, itama ta shafa nata, cikin sauri naga ya riƙe gurin, hankali a tashe yace "anya habiba masu siyar da maganinan ba bugar hancinmu sukayi ba kuwa?" Itama ta wani yamutsa fuska cikin nuna dauriya tace "me kaji?" Zai yi magana ya kasa ya kurma ihu saboda Aboniki da Loko sun fara aiki, sai rawa yakeyi da sauri ya cire wando tare da ɗaukar mafifici yahau fifita, Arshi na jiyo hayaniyarsu sai dariya take, a hankali ta mike tare da fitowa waje ƙafarta babu ko takalmi kai tsaye ta wuce kitchen, tana shiga ta buɗe murfin butocin dukka sannan ta ɗauko dakaken barkonu wanda yake a cikin roba mai murfi ta zuba a duka butocin kana ta rufe sannan ta jijiga ta koma ɗaki a hankali, komawarta keda wuya taji Ummu na ihu tana cewa "Auwalu nikam wlhi zafin da nakeji ya ninka naka" ta wani sake kurma ihu, shi ma yi yake har da wani gwalo ido wani mahaukacin zafi da ya ratsa Ummu ta ƙamƙame shi tana cewa "wayo Allah asibiti kusa, nikam kayi ko zafin zai ragu" Malam Auwalu ya haɗa zufa cikin mawuyacin hali yace "inyi me? kina ganin gabaki ɗaya na ƙurje gurin tsabar susa da azaba" A tare suka fito, Ummu ta ɗauki babbar buta da sabulu shima ya ɗauki butar, murya ƙasa-ƙasa yake cewa "idan kin saɓa sabulun nima ki bani" suka wuce banɗakin dake waje, Kamar haɗin baki, koda yake dama da tsautsayi, a tare sukayi tsarkin sannan a tare suka sake butar a ƙasa, tare da kurma wata mahaukaciyar ƙara, jikin Auwalu har yana ɓari, Ummu da zafin barkono ya gama gigitata cewa tayi "da safe ya kawo mai ruqiyya ƙila Aljanu sun tayata haɗa kaya ne lokacin da zata taho, yana kuka tana kuka, dukkansu sunyi shaɓe-shaɓe da majina sai kuka sukeyi tsabar ruwan azaba, Arshi kam har tayi barci cikin kwanciyar hankali tare da mafarkin Anum ɗinta, wai ta kawo musu ziyara sunata yawo. Ihun da ke ratsa kunnuwanta ne yasa ta farka tare da miƙewa zaune, a fili ta furta "Ummu da Ango mai ke faruwa?" Sai kuma ta koma ta kwanta taci gaba da barci, Gabaki ɗaya robar Vaseline na baby care sun kusa shafeshi a pipinsu, amma yaji da zafi ga iska dake shiga bai daina ba, a ranar dai sun jima suna bidiri dan Ummu zama ya gagareta, daga ƙarshe nashi yai sauƙi nata kam yana nan yanayi taci kuka idanu sunyi jajir, har yayi barcin wahala ko wando babu a wangale itako idanu sun kumbura, sai wajen ƙarfe 3:am na dare kafin barci ya ɗauketa. "Anum ki nutsu dan Allah kinga babbar damuwata itace rashin iya dressing da baki iya ba, sannan sometimes kinayin abu kamar namiji Please idan aka samu matsala zan iya fuskantar hukunci dan har gidanmu zata zo" Jannat ta faɗa tana kallon Anum. Jikin Anum ɗin a sanyaye tace "insha Allah zan yi ƙoƙarin kiyayewa anty Jannat karki damu" Jannat ta saka mata shaving cream a bag ɗin da ta bawa Anum ɗin, isowarsu anguwar ne yasa Anum raina kanta, dan ko a mafarki bata taɓa ganin haɗaɗun gine gine irin waɗannan ba, sabda babu inda take zuwa, yawanci rayuwarta a cikin gidansu ta yi ta, duk wasu kayan alatu na more rayuwa bata sansu ba, a bakin wani tafkeken get drivern ya tsaya tare da yin horn, zuciyar Anum taci gaba da lugude sbda Gabaki ɗaya ta rasa nutsuwarta, sai da Jannat ɗin ta fito mai gadi ya ganta kafin ya shiga ya nema musu izinin shiga, sannan ya barsu suka ƙarasa ciki, suna tafe Anum na ganin ɗawisu sunata yawo, ga wani dogon titi da suke ta lulaƙawa, a zuciyarta tace "gidanma gari guda ne" abinda ya bata mamaki ba wai gida take gani a tafiyar tasu ba, kyawawan shuke shuke ne irin na turawa, daga ƙarshe dai drivern yayi kwana zuwa wani farin get shikam a buɗe yake kuma da securities a gurin, sosai cikinta ya sake ɗurar ruwa dan a tunaninta lalubesu za'ayi, Jannat ta ɗaga musu hannu tana dariya, suma dariyar sukayi mata kana suka ɗaga musu hannu suka wuce, sosai Anum take ware idanu sakamakon ganin wani get da suka sake shiga wanda shine na ƙarshe daga shi sai cikin gidan, babu kowa anan hakan ya basu damar ƙarasawa drivern yayi parking a inda aka tanada dan ajiye motoci, motoci biyar ne a parke dukkansu sabbi sannan kuma masu tsadar gaske, Jannat ta kalli Anum kafin tace "mun iso ki kula Please nikam Allah yasa mugunnan baya nan" Jannat ta faɗa tana kamo hannun Anum suka shige ciki. Kafin su kai ga shiga asalin parlon sai da sukaci karo da wata haɗaɗiyar ƙofa ta Glass, Anum kam tsayawa kallo tayi dan Gabaki ɗaya kanta ya kanta ya kulle, suna kutsa kai ciki ana kiran sallahar magriba a masallacin dake gidan, gaban Jannat ya bata rass sbda tasan ba lallai antyn ta barta ta fito daga gidan ba, da shigarsu wani irin ni'imtaccen ƙamshi ya bugi hancinsu, a hankali suka ƙarasa ciki Anum kam tana ta bawa idanunta abinci, a zuciyarta ko cewa take "gaskiya ginin gidannan yayi kyau, wani gurin ma har ka mutu bazaka shigesa ba, ga parlo kamar baza'a mutu ba, anya kuwa ba ƙamshin Aljannah na fara jiyowa ba" zaunar da ita da Jannat tayi ne yasa numfashinta yin sama "ya ilahi wannan kujera sai kace tsafaffiya, ina zama tana bada wani lumm tare da ƙamshi mai daɗi, Anum ta sake ƙarewa parlon kallo kafin ta daidaita nutsuwarta, sbda taga wata yarinya ta fito daga wani ɗaki, "Oyoyo Jannat wannan kuma waye mai fuskar maza?" Jannat ta harari Budurwar kafin tace "bana son iskanci ya za'ayi ki kalli mace kice namiji" "Hamm barin kira mom da Dad su ganta" budurwar ta faɗa tana juyawa, ba Anum kaɗai ba, har Jannat cikinta ƙugi yakeyi saboda ta fara tuno makomarta a gurin Dad ɗin su, baya ƙaunar yaga mai kama da namiji a gidansa inhar ba ɗan uwansa bane, Jumayma kenan itace babba kuma budurwa ce, zatakai 18yrs, tana shigewa Arshi ƙanwarta ta fito, harara ce ta haɗasu da Jannat dan ko gaisuwa babu, duk da ƙaracin shekarunta sam batada kunya ko kaɗan, "momy tace tana zuwa" Arshi ta faɗa tana juyawa, Anum ta kalli Jannat kafin tace "anya zan iya kuwa?" Jannat ta harareta kafin tace "zaki iya mana, duk wahala da ɗaukar rainin nan da nake fuskanta duk saboda ke ne amma kicemin bazaki iya ba wlhi da kin taƙaitani" Anum ta haɗiyi wani irin miyau kafin ta sunkuyar da kai tana wasa da ƴan yatsunta, "Aslamu alaikum" mom tayi sallama, tana sanye da dakakken leshi mai tsadar gaske anyi mata ɗinkin doguwar riga, harda aljihu a gefe da gefe, fara ce tasss kamar inda momyn Jannat take fara, sannan sunada fashin goshi hakan ya sake ƙawata fuskar tata, bakinta baƙi ne amma ba sosai ba, sai ƙamshi ke fita a jikinta, washe da baki ta ƙaraso tana cewa "my Janna yau kece a gidan namu?" Jannat tayi murmushi har yanzu gabanta na faɗuwa sbda idan burinta bai cika na nemawa Anum aiki ba, sam bazataji daɗi ba, ga ƙalu balen da ta dinga fuskanta daga gurin iyayenta har yanzu ma bata tunanin ta tsira tunda basu gama da nan ɗinba, "Mom wlhi na kawo ƴar uwar Dadyna ne ki taimaka mata, basu da cin yau bare na gobe sannan tanada ƙanwa mai ciwon larura, shine nace barin kawota ta dinga yi muku aiki kuna biyanta" Jannat ta faɗa muryarta na karkarwa, Anum kam gabaki ɗaya ta haɗa gumi saura ƙiris ya rage ta saki fitsari saboda wani irin kallo da mom ɗin keyi mata, shigowar Jumayma ne ya katse musu shirun, wani irin kallo take bin Anum dashi cikin suɓutar baki tace...! Page 7 "Mom wannan bata yi miki kama da namiji?" Sanin ciwon mayar da jinsin mace i zuwa namiji ne yasa Mom cewa "Jumayma kinada hankali kuwa? mace ce gata nan kina ganinta amma kike kiranta da sunan namiji?" Jumayma ta turo baki tare da mikewa tabar gurin, mom ta sake ƙarewa Anum kallo a karo na biyu, kafin ta juyar da kallonta ga Jannat, "Momynki tasan da zuwanki?" Bakin Jannat na rawa tace "ba..bata..sani ba mom Please karki gaya mata, tsorona ma bai wuce dare da yayi ba" mom tace "shikenan barin kirata" Sosai Jannat ta damu da kiran da taga mom ɗin na yi zuciyarta ma bata gama tsinkewa ba sai da taji mom tace "eh gurina tazo,aiki ne yayimin yawa shine nace tazo ta tayani ashe ma bata sanar miki ba?" Daga can ɓangaren momy tace "dama Dadynta ne yake faɗa shiyasa duk nabi na damu, amma tunda tana gurinki babu damuwa" Kasancewar wayar a handsfree mom ɗin tasa, Jannat har tana sauke gauron numfashi, Anum ma taji daɗi sosai da hakan ta kasance, abinda bai yiwa Jannat daɗi ba, ɓatawa drivern time da tayi, amma ta fita ta bashi haƙuri akan ya kwana gobe insha Allah sai ya mayar da ita gida da wuri, bai nuna mata damuwarsa ba, yace "Allah ya kaimu" Sai da sukayi sallahar magriba da isha'i sannan aka zauna zaman cin abinci, Jumayma da Arshi ƙanwarta ƙin fitowa sukayi, a cewarsu Anum tana basu ƙyama, babu inda mom ɗin ta iya dasu dan bata isa ta dakesu ko tayi musu tsawa ba, sai fitina ta tashi ta ɓangaren Dadynsu, Bayan sun gama ci Jannat ta karɓi na driver ta kai masa kana ta dawo, mom ta nuna musu ɗaki suka shiga, Komai na gidan yana matuƙar burge Jannat damuwarta bai wuce wulaƙanci da tozarcin da zata fuskanta a gidan ba, "Anum nan shine ɗakin da zaki dinga kwana" Jannat ta faɗa yayin da take kwanciya a kan bed, Ɗago kanta tayi tare da kallon Anum ɗin da tayi nisa cikin tunani, Jannat ta taɓo ta kafin tace "Anum tunanin mai kikeyi, a tunanina farinciki zakiyi? tunda har mom ta karɓeki hannu bibbiyu" "Babu komai anty Jannat Nagode Allah ya saka da alkairi kin yimin halacci Allah ya bani abinda zan saka Miki" Jannat tayi murmushi kana tace "ki kwanta kawai, mom tace zuwa gobe zata nuna miki aiyukan da zaki dinga yi, ki kwantar da hankalinki, shima mijin nata idan kika karanci halinsa bazaki wani sha wahala ba" "Insha Allah zanyi ƙoƙarin kiyayewa" Anum ta faɗa tana kwanciya can nesa da Jannat. Can cikin dare bayan jannat tayi barci ta farka, ta tashi zaune tare da ƙarewa Anum kallo, tasani Allah ne ya haɗa jininta da na Anum amma kuma idan aka ƙyamaceta tana matuƙar jin takaici da ɗacin rai, Abu ɗaya ne yake firgitata da Anum bai wuce gabanta dake nuna alamun akwai halittar namiji a jiki ba, sai gashin bakin dake yawan fitowa, to idan ta ɗauki tsawon lokaci bata da abinda zata aske fa? Duk da dai ta siya mata man shafawa a gurin, ga nonuwa suma tubarkalla abin da sai dai ace Allah buwayi gagara misali" ta mayar da kanta kan pillow ta kwanta zuciyarta ta kasa nutsuwa da zamanta a gidan, Washe gari kiran sallahar farko a kunnen Anum, ta tashi zaune tana rarraba idanu, ɗazu Jannat ce ta nuna mata inda zatayi ta kunna pampo yanzu kam koda taje ba iyawa zatayi ba dan tama mance, "anty Jannat tashi asbha tayi, dan Allah taimaka min da kunna pampo" jannat ɗin ta buɗe idanunta tare da tashi ta zauna kana ta mike ta je toilet ɗin ta kunnawa Anum ɗin sannan ta fito, Alwalah tayi kana ta fito,Jannat ta shiga, kasancewar tun jiya da safe ta fara sallah, tana fitowa tayi tsaki tare da cewa "dole ki sauya sallahar nan idan har ba so kikeyi a dinga kiranki da sunan namiji ba" Tama mance Jannat tayi mata faɗan yin Sallah babu hijabi, batace komai ba ta zuge zip na jakar kayan da Jannat ɗin ta bata sannan ta ɗauko ƙaton hijabi tasa a kaikaice sannan ta kabbara sallah, tana yin sallama ta yakice hijabin, sannan ta fara adu'oi, gabaki ɗaya ɗankwalin kanta ya isheta, ta cire shi ta ajiye a gefe, Jannat na idar da sallah tana shafa adu'a tace "Anum wannan wane irin abu ne, kina neman ki janyomin duka ne ko? wlhi tallahi inhar suka gano suffar da kike kin shiga uku tunda bakiji abinda na gaya miki ba koh?" Anum ta dinga bawa Jannat haƙuri zuciyarta babu daɗi, Suna cikin tattaunawa mom ta turo ƙofa, Allah ya taimaki Anum ta ɗaura ɗankwali, bayan sun gaishe ta, tace "Anum tazo mu shiga kitchen yau zata fara aiki, sbda zuwa yamma dad yana hanya" jiki a sanyaye Anum ta miƙe tana kallon Jannat, mom ta riga da tayi gaba, a hanyar da zai sadaka da kitchen ta tsaya Anum ta taho ta sameta a gurin, abin ya matuƙar bata mamaki duk wasu abubuwa da take tunanin koyawa Anum ta iyasu, sakamakon yawan karance karance da takeyi, a safiyar yau ita ta haɗa musu breakfast mai rai da lafiya, dukkansu suka hallara a dining har dasu Jumayma da Arshi, sosai Jannat da mom suketa santin abincin, yayinda Arshi ta miƙe da gudu tana riƙe da wuya sai kakatun amai takeyi, hankali a tashe mom tayi gurinta, Jumayma ma ta rufa mata baya, kai tsaye ta wuce toilet ɗinsu ta fara yunƙurin amai amma yaƙi zuwa, idanunta sunyi jajir ta ɗago ta kalli Mom kafin tace "nikam bana son cin wannan abincin momy gaskiya a sauya wannan ƴar aikin" mom tace "ke Arshi bana son iskanci in zaki nutsu ki nutsu babu inda zataje" Jumayma ta wani harari mom kafin tace "komai na naɗe a memory idan Dad ya dawo zai ji labari da ɗuminsa" Mom tace "yanzu ma zaku iya kiransa ku gaya masa" Anum da Jannat kam abin yafara fin ƙarfinsu, Jannat sai kwantarwa da Anum hankali take tana rarrashinta, damuwarta bai wuce Jannat ɗin ta tafi ta barta ba, tasan zatasha baƙar wuya a gurin yarannan, THAILAND Yangon Ko parking space granny ta kasa yiwa Arya rakiya, sai kuka take harda majina. Tana zuwa parking space ta shiga ƴar madai-daiciyar motarta fara mai kyau sannan ta ajiye kayanta a backside handbag ɗinta a kusa da ita, sannan tayiwa motar key, a hankali ta fice daga gidan yayinda ta hau titi ta fara gudu kamar zata tashi sama, tun kafin ta shiga mota take gwada number Khair shiru a kashe, duk da tanajin karayar zuciya sai ta basar ta hanyar ƙarfafawa kanta, tayi nisa sosai a tafiyarta wayarta tayi ringing "tana driving da hannun dama ta riƙe wayar da hannun hagu tare da sanyawa a kunne bayan ta danna kore "Granny ina hanya ne zan kiraki idan na sauka" cikin dakusashuyar murya Granny tace "Arya ki riƙe waya karki katse ki dawo gida bana son kema in rasaki please Arya karki ƙarasa gurinsu" wani irin ƙara Granny taji ƙiiiiiiiiii, hankali a tashe ta kalli wayarta da number Arya taga kuɗi nata tafiya amma bata jin motsin komai sai numfashi mai kama da kuka, ido waje Granny ya zaro tare da tsala ihu tana cewa "wannan wace irin ƙaddara ce, Ubangiji ka kawo mana komai da sauƙi shikenan sun kashe Arya" hawaye wanda ya ninka na da ya fara zarya a kumatun Granny, ta taɓi zaninta da ya jiƙe da fitsari, kan kace me ta saki tusa kamar ɗazu Booom, kasancewarta mai saurin shiga ruɗu, Tana ƙoƙarin yakice zanin jikinta wayarta tayi ringing, ganin number Arya yasa ta yin saurin ɗagawa sai yarari take da fitsari, "Arya babu abinda da dai sukayi miki ko?" "Muryar Arya na cikin firgici tace "Granny ban ma kai ga zuwa gurinsu ba, na bige wata budurwa ne wlhi har taji ciwo yanzu ma hospital zamu wuce" Granny tayi ajiyar zuciya Kafin ta cire zanin ta sanya a bucket sannan tace "to alhamdulilah ya jikin ita yarinyar" Granny zan kiraki anjima ko numfashi batayi" Granny ta zaro ido tana shirin yin magana Arya ta katse kiran, Budurwar sa'ar Arya ɗinne koda zata girme mata bai fi da one year ba dan ita kanta Arya ɗin zatayi 20yrs, hankali a tashe Arya ta riƙe hand bag ɗin dake rataye a kafaɗar yarinyar sannan ta fara ƙokarin goge mata jinin dake zuba a hannunta, cikin ƙarfin hali da jarumtaka ta turata a mota sannan ta rufe, tana isowa hospital batayi ƙasa a guwaiwa ba gurin kiran ɗan uwan Granny dake aiki a hospital ɗin kuma jam'i ne na sirri, a harabar Asibitin yazo ya sameta hawaye ya gama wanke mata fuska, kasa cewar tayi masa bayanin komai da taimakonsa aka kwantar da Budurwar tare da fara bata kulawar gaggawa, bayan wasu lokuta Likitoci suka sanar musu hannunta ne kawai ya samu matsala sai kuma ciwon jiki amma babu wani abu da ya sameta bayan haka, Arya da ɗan uwan Granny suka fito waje, cikin sanyin murya tace "Monir muna cikin matsala ga wata ta sake afkuwa" cikin rashin fahimta ɗan uwan Granny da ta kira da Monir yace "ban gane mai kike nufi ba, wace irin matsala?" "Khair shida abokansa suna hannun Leela sannan ga wannan wace na kawo, zata tsallaka titi na bigeta ban sani ba" Arya tai maganar muryarta a raunace, "Subahanallah mai ya haɗa su Khair da Leela kuma, ita wannan ai ko yau ana iya sallamarta, matsalar dai bata wuce na su khair ɗin ba" ta share hawayen da suka zubo mata kafin tace "zan taimaka masa koda zan rasa rayuwata" Monir yai murmushi kana yace "ki dai yi fatan rabuwa da Leela lafiya dan idan ka shiga gonarsa faɗansa ba mai ƙarewa bane" Sosai Monir ɗin ya sake ƙarfafa mata guwaiwa tare da bata shawarwari, Bayan fitar su Arya Budurwar dake kwance kan gadon asibitin ta ciro wayarta wata ƴar mitsitsiya a cikin aljihun skirt ɗin jeans na jikinta, ta danna wata number, magana takeyi ƙasa-ƙasa wacce nima bansan me take cewa ba, tai saurin mayar da wayar cikin aljihu kana ta koma ta kwanta kamar inda suka barta, A tare suka shigo, ko wanne fuskarsa ɗauke da tausayi, hannun Monir riƙe da leda mai kyau wanda kayan marmari ne a cikinta, har suka zauna bata buɗe ido ba, Monir ya ɗan taɓi ciwon hannunta, buɗe idanu tayi a hankali tare da yamutsa fuska ta kalli Arya sannan ta kalli Monir ɗin kana ta saukar da idanunta ƙasa, "ya ƙarfin jikin?" Arya ta faɗa tana yiwa Budurwar murmushi, itama murmishin tayi kana tace "yayi sauƙi" haka ma Monir yayi mata ya jiki tare da gaya mata sunansa sannan ya faɗa mata sunan Arya, wani irin kallo tabi Arya dashi, wanda dukkansu basu san tayishi ba, kafin ta ƙirƙiro murmishi, Arya tace "baki faɗa mana sunanki ba" Sai da ta cije lips kafin tace "Anan" Monir yace "suna mai daɗi, kafin yaci gaba da cewa ina tunanin yau za'a sallameki anjima ai zaki iya zuwa gida ko?" Anan ta wani marairaice murya kafin tace "bani da kowa iyayena dangina duk ya kashe su" Monir yai saurin cewa "waye?" Bakinta na rawa tace "lee..Le ..la" Monir ya kalli Arya kana suka kalli Anan a tare...! Page 8 Gobe akwai zazzafar cakwakiya da safe zan ɗora page 9 a arewabook ammafa idan kukayi following ɗina tare da comments 👇 https://arewabooks.com/u/momislam11 "Turr da wannan mummunan hali irin na Leela, ya zamo shaiɗani azzalumi marar tausayi da tunanin abinda zuwa gaba zai riska" Arya ta faɗa tana tafa hannayenta, Da sauri ta matso kusa da Anan, cikin sanyin murya tace "idan har kina ganin kin shirya ɗaukar fansar abinda yayi miki a shirye nake da in taimaka miki" Anan ta gyaɗa kai da sauri, kafin ta share hawayen dake sintiri a fuskarta, sannan tace "na amince, hakiƙe ke Alkairi ce" Anan ta faɗa tana ƙoƙarin ɗago hannun ciwon. "Amman dai yanzu bakya jin ciwo a jikinki koh?" Monir ya tambayeta. "Eh sai dai hannuna da yake yimin ciwo amma babbar damuwata shine inda zan nufa" takai ƙarshen maganar tana sake fashewa da kuka, Monir ya matso kusa da ita tare da dafa kafaɗarta cikin ƙarfafa mata guwaiwa yace "tabbas idan aka daure aka jure sannan aka jajirce za'a iya cin galabar Leela abin abin tsoron anan shine, idan shine yaci galaba fa?" Arya ta matso kusa dashi, sai da ta sauke gauron numfashi kafin tace "bana tunanin hakan" Sun daɗe suna shawarar inda zasu ɓulowa lamarin, har doctor ya shigo ya rubutawa Anan sallama tare da magunguna, ganin takarda mai nuna alamun an biya kuɗi yasa Arya kallon Monir kafin tace "kaine koh?" Gira ya ɗaga mata tayi masa godiya kana sukaci gaba da shawarwarin har zuwa ƙarfe 3:pm, "Yanzu tunda case ɗin Anan ya shigo ciki dole ku koma ku sake shiri saboda cimma nasara a tafiyarku" "Eh Monir hakan za'ayi amma inason ka taimakeni da nemo wasu muhimman bayanai akan Leela shima hakan nasan zai taimaka mana koh Anan?" Arya ta faɗa tana kallon Anan. Anan ɗin ta gyaɗa kai tana jingine da jikin bango dan ta tashi zaune, "Babu damuwa Arya zanyi komai cikin hikima dan Allah ki kula da Anan Please kinsan yanzu dole ta zamo tana cikin ƙarkashin kulawar mu" Monir ya faɗa yana kallon agogon dake ɗaure a tsintsiyar hannunsa. Arya ta gyara zaman gashin kanta da ya zubo mata har fuska, duk da mayafin da tasa ta yane kanta dashi, kafin tace "zan kula da Anan kamar inda zan kula da kaina Please ka duba mana duk abinda ka samu ka turomin Whatsapp zamu zama cikin shiri" Ya amsa musu da "toh" kana yace su fito tunda anyi sallama, Anan bata samu damar cin komai ba, har sai da suka shiga mota ta ɗan ci apple suka ɗaga masa hannu yayinda Arya tayiwa motar key suka wuce. "Yanzu ina kike ganin zan ajiye ki" Anan da ta gaji da gayawa Arya damuwarta tace "bani da kowa" Arya ta juyo ta kalleta kana ta mayar da hankalinta ga titi sannan tace "shikenan zan wuce dake gidanmu nima ina tare da kakata ne, tun bayan rasuwar iyayena sunyi hatsari a zuwa bikin cikarsu shekara goma da aure, an rasa ya akayi hatsarin ya faru, daga ƙarshe ba wani tsananta bincike akayi ba, ni kaɗai ce na rayu kuma ni kaɗai suka haifa, ban bi motarsu ba, ina tare da granny, shikuma Shakur da mahaifinsa da mahaifina uwarsu ɗaya ubansu ɗaya, Kinga ta inda zumuncinmu ya ƙullu ko? duk a tare iyayen namu sukayi hatsarin, shine kakarmu wato mahaifiyar su babanmu ta ɗaukemu muke tare da ita, gashi Shakur ya faɗa hannun Leela nayi alƙawari rayuwarsa bazata wulaƙanta ba, sbda ina matuƙar sonsa shine mafarkina" Tunda Arya ta fara bada labari, Anan take ta kallonta cike da tausayawa kafin daga ƙarshe tace "Allah sarki Allah ya gafarta musu" Arya ta amsa da "Amen lokacin tayi kwanar shigowa anguwarsu, Koda Anum taga zubin gidan nasu tasan ba talakawa bane su ɗin, sannan kuma ba za'a kirasu da hamshaƙan masu kuɗi ba, Granny na daga kan bed a kwance taji motsin tsayuwar mota, daga ita sai gajeren wando ta fito tana cewa "oyoyo Shakur ina fatan dai Arya babu abinda ya samu Shakur?" Arya ta dafe goshinta tare da takowa tazo kusa da granny ta dafa kafaɗarta cikin tausasa murya gami da kwantar da hankali tace "ba tare muka dawo ba, Granny ki tayani da murna yarinyar da na bige har nace Miki zamuje hospital itama su Leela ne suka kashe iyayenta, Kinga na samu mai taimakamin,mun rabu da Monir ma yace "mu tsaya muyi komai cikin nutsuwa sannan yace zai taimaka mana" Granny ta sauke ajiyar zuciya Kafin ta kalli Anan dake zaune gaban mota tana ta watsa da yatsun hannunta, Granny tace "tare da ita kenan zamu zauna?" Eh Granny inason mu haɗa aikin da ita ne" Arya ta faɗa tana waigen anan ɗin. "Toh shikenan kice mata ta fito" sai a lokacin Arya ta lura da ɗan gajeren wandon dake jikin Granny ta tuntsure da dariya tana cewa "Granny kin ganki kuwa" sunkuyar da kanta tayi ta kalli wandon kana ta ruga da gudu tana cewa "Arya kwai shegiyar yarinya yanzu wandon nawa kikeyiwa dariya ai na mance dashi na fito" Anan ma dake cikin mota, da ta ɗago kai yanzu ta sheƙe da dariya, ganin Arya ta taho zata buɗe murfin motar yasa Anan ɗin daidaita nutsuwarta, "Ki fito barkanki da zuwa gidanmu Allah yasa zaki iya zama da granny dan akwaita da yawan surutu" Anan tayi dariya kafin tai rau-rau da idanu, kafin tace "Allah sarki harda kakata mai sanyani nishaɗi mutanen Leela suka kashe" sai kuma ta kawar da kanta gefe, Sosai Arya take tausaya mata, duk da tausayin kanta da takeyi na rashin iyaye sai taga ai gara ita tunda tanada Granny gashi sam bata son taga ɓacin ranta. Riƙe da hannun juna suka ƙaraso cikin gidan, kai tsaye babban parlon Granny suka shiga, tana kitchen tana haɗo musu abinci, Arya tace "ina zuwa barin duba mai tsohuwar nan take yi ne" Anan tayi mata murmushi. A tare suka dawo da Arya da granny duka hannun su riƙe da tray wanda aka jere abinci a kai da ruwa, a saman carpet suka ajiye, tare da ruwan wanke hannu, Anan tayi musu godiya lokacin da granny take ce mata ta sauko suci abinci. Sunaci Granny na basu labarin abin dariya sai dariya sukeyi har sukaci suka ƙoshi. Arya ta kwashe kayan abincin takai kitchen kana ta dawo tace wa Anan "muje ɗakina" granny tace "babu inda zataje sai ta bani labarin ahalinta" Arya ta ɓata rai kafin tace "a yanzu dai hutawa zatayi sai dai zuwa gobe" Arya ɗin ta kalli Anan tace "ki sha magani kiyi sallah sai ki kwanta" "Toh" Anan ɗin tace dan ita ba musulma bace bama tasan ya akeyin sallahar ba, amma ta ƙudurta a ranta zata dinga kallon inda Arya ɗin takeyi itama ta dinga kwatantawa saboda kar Arya taga gane bata sallah tasan ƴan garin da riƙon Addini basa son munafurcin addini musamman ita da take son zama cikinsu. A tare suka shiga ɗakin Arya ɗin, suna shiga Anan ta nemi guri a saman bed ta kwanta, Arya ta fara zuwa tayi alwalah ta fito, Anan ta ƙare mata kallo na tsanaki kafin ta kalli ƙafafuwanta suma taga a jike suke, tana kwance Arya ta kabbara sallah, sosai ta mayar da hankali ga abubuwan da Arya ɗin takeyi har ta kammala, sannan ta miƙe ta shiga toilet ɗin, ta daɗe a tsaye daga ƙarshe ta shafa ruwa a fuskarta kana ta shafa a hannunta da ƙafafuwanta sannan ta fito, lokacin Arya ta riga da ta fita, hakan ya bata damar sakewa sosai bata yi sallahar ba, amma ta zauna kan sallahya ta ɗaga hannu sama sai motsi take da bakinta, ko me take cewa oho, daga ƙarshe ta cire hijab ɗin ta ninke ta tashi akan sallayar kana ta dawo kan gado ta kwanta, Hayaniyar da taji a tsakar gida ne yasa ta fitowa da sauri, a bakin ƙofa ta tsaya tana rarraba idanu, "Arya ki bari nace miki cikina har yau be gyaru ba mai yasa zaki yi mana abinci wanda nan da nan zai sake rikice mana ciki?" Granny ta faɗa tana lallatsa wayarta, "Ki kwantar da hankalinki kamar kin mutu" Granny tabi Arya da gudu har tana faɗuwa sabda santsin ɓawon ayaba da ya kwashe ta ji kake Timmm ta tsala ihu tana cewa "ke baƙuwar nan zoki ɗagani ki dubamin cinyoyina ko wata tsokar ta fice dan naji naman cinyata yana ƙuluf-ƙuluf" Anan ta taho da sauri tana cewa "Arya zomu taimaki Granny mana" Kafin Anan ɗin ta ƙarasa idda magana Arya ta fito ta kama Granny suka ɗagata, cikin hikima Granny ta dage ta mintsini Ayra a hannu, Ayra dake riƙe da ita sun kusa zuwa ɗaki ta saketa a ƙasa, dama tafi Anan ƙarfi tunda ƙirar jikinsu ma ba ɗaya ba, Ayra tanada jiki anan kuwa siririya ce, "wayo Allah yau naga aihuwar asara yarinya ta biyo halin uwarta" Granny ta faɗa tana mimiƙe ƙafafu, Anan kam tsayuwa tayi tare da jingina da jikin bango, dariya take son yi amma tana tsoron Granny dole ta haɗiye dariya ta juya zata wuce ɗakin Arya ɗin. "Ke baƙuwa harda ke a guduna ko kun haɗa baki ne?" Anan ta girgiza kai alamar a'a kafin ta taho gurin Granny tace "bazan iya ɗagaki ni kaɗai ba" Granny tayi tsaki mtsew tare da cewa "amma wanda ke baku abinci yayi asara gaskiya ace duk tsayin nan naki kamar bishiya bazaki iya ɗagani ba, niɗin guda nawa nake ko ance Miki inada nauyi ne?" Dariya ce ta kufcewa Anan sai da tayi mai isarta kafin ta kamo hannun Granny daƙyar ta taimaka mata ta miƙe, ga yanayi na jikin tsufa, cikin ƙarfin hali suke tafiyar Granny na dafe da bango har suka ƙarasa ɗakinta, tayiwa Anan godiya tare da zaunar da ita tace ta zauna suyi hira, Anan tayi murmushi kafin ta zauna a saman carpet tana kallon Granny da ta karkace hular dake kanta, "Akwai wani jikana, in gaya miki jarumi ne kyakkyawa mai kyau da cikar zati ga iya biyayya, hamm yaron nan ina matuƙar sonsa, iyayensa ne suka yi hatsarin mota duka suka mutu, shine na riƙeshi, yanzu an wayi gari ya barni wanda ya fimu ƙarfin arziƙi ya sacemin shi" Granny tai maganar tana share hawayen dake kwaranyowa a idanunta" "Kiyi haƙuri granny zai fito nayi miki alƙawari" da sauri Granny ta share hawayen tare da yin murmushi kafin tace "kinyi min alƙawari?" Anan tace "eh nayi" sunata hirarsu wanda har yanzu anan ɗin bata basu labarin addininta da wasu abubuwa da suka shafeta ba. Acan kitchen Arya ta kammala girkin dare, tazo ta jere a dining, batayi musu magana ba ta wuce ɗakinta tayi wanka ta sauya kaya sannan ta fito ta goge jikinta kana ta shafa mayuka masu gyara jiki da ƙamshi, sosai zagin mahaifiyarta da granny tayi ya ɓata mata rai, yau kam sunyi faɗa fushi take yi da granny dan ko maganar ta kammala batayi ba, duk da tasan Granny ɗin da saurin jin yunwa, tun kafin ayi magriba take cin abinci, itakam ta riga da ta ɗauro alwalah koda ta duba agogo lokaci ya ƙure, haka tayi sallar zuciyarta babu daɗi dan batason kaucewa lokacin sallah, kasancewar la'asar tayi. Hamdala tayi na kammala girkin da wuri ta haye gado tare da kunna Whatsapp ta kunna data, saƙon Monir ne a farko dan haka ta fara dubawa sabda saƙonnin sunyi mugun jan hankalinta a hankali ta furta ya ilahi kafin ta fara karantawa kamar haka....! Following ɗina shine zai sa ku dinga samun update a arewabook sau biyu a rana, Please masoyan gaskiya ku nunamin love ta hanyar following ɗina@momislam11 # Granny # Arya # Anan # Monir # Leela Drop your comments waye gwaninku🤸 Page9 "Arya na samu duk wasu bayanai na sirri akan Leela ku zamo cikin shiri" Da sauri ta gyara zama kafin tayi masa voice. "Monir na yake shawarar zamu je a matsayin masu neman taimako, daga nan kaga zai ɗaukemu a matsayin masu yi masa hidima, ni zan fito a matsayin makauniya ita kuma Anan zata fito a matsayin gurguwa, kana ganin hakan yayi?" Tai maganar tana tura masa emoji mai alamar damuwa, Ya ɗan jima bai bata amsa akan mafitar da ta samo ba, daga ƙarshe ya fara yi mata typing.. "Bakya tunanin za'a iya samun matsala idan har ya gano Basaja kukayi masa?" Arya tayi murmushi kafin ta mayar masa da cewar "zamuyi ƙoƙarin kiyaye faruwar matsalar" ya turo mata da amsar Allah ya bada Sa'a zanci gaba da bincika muku" "Amin" tace tana saukowa daga kan gado. KANO NIGERIA Ƙarfe 8:am lokacin Jannat ta kammala shirin tafiya gida, tun kafin su fito parlo take gargaɗin Anum kar tayi kuka ko da bayan tafiyarta ne, tunda ta lura da yanayin fuskar Anum ɗin, iya mom da Anum ne suka rakata parking space inda motarsu take, driver yayiwa motar key Jannat tana ɗagawa Anum hannu, mom tayi murmushi kafin tace "ki saki jikinki babu wata matsala" A tare suka dawo ciki, "Allah sarki rayuwa" Anum ta faɗa a zuciyarta, kamar inda mom ɗin ta faɗa yau Dad yake hanya, tun bayan tafiyar Jannat suka shiga kitchen suke ta hada-hadar haɗa abinci, su sauke wannan su ɗora wancan, Anum kam tunda taji mom tace dad yana airport gabaki ɗaya hankalinta ya tashi, zuciyarta ta tsinke, amma duk da hakan bata bari mom din ta gano ta ba, ƙarar shigowar motoci ne yaja hankalinta, wanda ko ba a gaya mata ba, tasan baya rasa nasaba da isowar mai gidan, hankali a tashe ta tsame hannunta a ruwan kumfa na wanke-wanken da takeyi na kayan da sukaɓata, tana tsaye a kitchen ɗin kamar wacce ruwa ya cinye ta dafe hannayenta a ƙirji taji sallamar mom, da sauri ta waiga tare da ƙoƙarin kawar da damuwar dake shinfiɗe a fuskarta, "Anum yi sauri ki ɗauki wannan kunun tunda an kammala ki miƙawa Dad yana parlo ki tabbatar da kin nutsu gurin bashi" wani irin mummunan faɗuwa gabanta yayi, lokaci ɗaya gumi yayi mata lulluɓi, kamar wacce ta watsa ruwa, kanta a sunkuye ta miƙa hannu ta karɓi kyakkyawan jug ɗin, Mom ta miƙa mata tana cewa "zan taho masa da ƙosan kin sanshi" Tsabar kiɗimewa har tana mancewa da hanyar da zata sadata da parlo, sai da ta juyo ta dawo kitchen jikinta na rawa tace "Hajiya hanyar parlon fa?" Mom tayi murmushi kafin tace "Anum ko ɗazu mafa ke kika fita da kanki yau kuma kin mance?, zo muje in nuna miki" koda suka fito da hannu mom tayi mata nuni kana ta koma kitchen, tafiya ta fara yi kamar wacce ƙwai ya fashewa a ciki, tsananin tsoro gami da fargaba sun dirar mata ƙahon zuciya, tana tafe tana ambaton innalililahi wa Inna ilahiri raji'un, tsawar da ya daka mata ne yasa tai saurin ƙarasowa, domin kuwa ya riga da ya ganta har yanayin tafiyar da takeyi, kamar zata kifa tsabar sauri, ta ƙaraso gurinsa murya na rawa tace... "Barka da isowa Alhaji" sai da ya ƙare mata kallo kafin yace "barka" kasancewarsa mai ƙaramin jiki yasa yawan shekarunsa ɓuya, sbda a ƙalla zaiyi shekaru hamsin a duniya, fari ne amma ba can ba, sannan yanada cikar zati da kwarjini gami da isa tare da tsaurarawa, Har ta miƙe zata juya ya kirata da Cold voice ɗinsa, jikinta na rawa ta dawo ta tsuguna kafin tace "gani" ƙafafunsa suna saman table ya jingina kansa da kujera ya ɗan matso kusa kafin ya ɗaga hannu ya watsa mata Mari, da sauri ta miƙe ita ba kuka ba ita ba jimami ba, tana tsaye kanta a sunkuye yace "a gidanku haka kike yiwa mahaifinki ko dama baki samu ingantacciyar tarbiyya bane?" Da sauri ta ɗago idanuwanta ta kalleshi, kafin ta juyar da kai gefe, a zuciyarta tana maimaita "da mahaifina yana da rai ko kallo baka isheni ba, duk da shiɗin talaka ne" ta faɗi hakan kusan sau uku, tsinkayo tsawar da ya daka mata da tayi ne yasa tai saurin barin gurin ta dawo kitchen, "sannu da Aiki Hajiya" Anum ta faɗa hawaye na shirin zubowa a idanunta, "yauwa sannu amma Anum banji daɗin abinda kikayiwa Dad ba yanzu ya kirani yake gayamin bakisan waye dad ba ko?" "Hajiya kiyi haƙuri insha Allah hakan bazata sake faruwa ba" Jumayma da Arshi suka fito, 📢kasancewar sunan Arshi yazo ɗaya da na ƙanwar Anum zamu dinga kiranta da sunan da Dad yake kiranta dashi, Little Hajo, sunan yayarsa kenan Hajo. Dariyarsu da yaji ne yasa shi saurin ɗago kansa tare da faɗaɗa fara'arsa cike da nuna kulawa ya ware musu hannayensa alamar su taho, da gudu suka taho har suna rige rige, yana dariya yace "Jumayma kekam bakya girma" Little Hajo ta kamo hannunsa kafin tace "Dad munyi missing ɗinka amma dai bazaka ƙara komawa ba ko?" janyota yayi kana ya ɗorata a saman cinyarsa cike da nuna kulawa yace "idan kikace kar in koma zan zauna my Little" dariya tayi wanda yasa point ɗin dake kumatunta loɓawa kafin tace "Dad an kawo sabuwar ƴar aiki ka ganta?" Sai a lokacin Jumayma dake gefen Dad ɗin tayi magana, "Dad Please ka ce ta koma gidansu nikam bana sonta" "Big girl menene dalilin da yasa bakya sonta tayi miki wani abunne" Jumayma ta turo baki tare da gyaɗa kai alamar a'a, "Idan har naga zata takura muku dole ta koma inda ta fito" Dad ya faɗa yana mikewa tsaye, "Dad bakasha kunun ba ga ƙosan nan" Jumayma ta faɗa tana kallonsa, "eh kusha kawai" Ya faɗa yana wucewa ciki, Dad wani irin mutum ne, wanda idan har yayi faɗa akan abu to bazai cishi ba komi muƙaminsa kuma komai sonsa da abin. Kai tsaye ɗakinsa ya wuce, mom kuma sun kammala komai dan ƙosan ma Jumayma ta bawa ta kawo ta ajiye masa, iya Anum ce a kitchen ɗin, itama da ta kammala ta dawo ɗakin da yake a mazaunin nata, ta zabga tagumi, tunani takeyi anya zamanta zai ɗore a wannan gidan kuwa?" Tayi nisa a tunani taji an hankaɗo labule, cikin isa da gadara take cewa "ki tashi ki soyamin bread and egg yanzu yanzu" sam bata ma ɗauki murya ba, dan bata san wace a tsaye a kanta ba, sai da ta ɗago da idanunta ta kalleta kafin tace "dan Allah kiyi haƙuri wlhi na gaji, akwai ragowar wanda aka soyawa Alhaji a kitchen nasan zai isheki" Little Hajo ta wani galla mata harara tare da nunata da yatsa, bata dai ce mata komai ba, ta fice, da kuka ta ƙarasa bedroom ɗin mom ta samu mom ɗin tana sallahar magriba, cikin shagoɓa ta fice fuuu tare da wucewa bedroom ɗin dad, yana tsaye ya sanya farar jallabiya yana ɓalle botir na gaban rigarsa ta rungumeshi murya kamar zatayi kuka tace "Dad kayi wa ƴar aiki magana inason cin bredi da ƙwai taƙi soyamin nidai Dad shi zanci" da sauri ya fito fuu zai wuce, ganin mom a tsaye ta rungume hannaye tana jifansa da murmushi yasa shi tahowa gurinta, cikin faɗa yake cewa "kiyi gaggawar korar waccar yarinyar, matsawar bazata yi mana biyayya ba ta yiwa ƴayana wlhi bazata zauna min a gida ba" tunda ya fara maganar mom take rungume dashi har ya kammala, ta janyo hannunsa suka dawo ɗakinta, wani haɗaɗen ƙamshi yayiwa hancinsa sallama, "kayi sallah ne?" "Eh nayi isha'i nake jira" Dad ya faɗa yana kashe mata ido, tasani bai ci abinda Anum ta kawo masa ba, dan haka wanda ta kawo ɗakinta ta bashi da kanta har sai da ya ƙoshi, sam bata yi masa maganar Anum ba, tafison zuwa safiya su tattauna akanta, "Dad idan kayi sallah ka kwanta ka huta kasha hanya" mom ta faɗa cike da nuna kulawa" wane irin Hutu zanyi bayan gaki" yau a gunki zan warware gajiya hajiyata" Little Hajo dake saman bed ɗin dad tana jiran dawowarsa sannan taji hukuncin da ya yanke akan Anum, har barci ya fara ɗaukarta bai dawo ɗakin nasa ba, tun tana barcin tana buɗe ido har mai ƙarfin yayi gaba da ita, Tunda Jannat ta gargaɗeta akan yin Sallah da hijab, bata saɓa alƙawarin da tayiwa Jannat ɗin ba, a tsakanin 2days har ta fara sabawa, bayan ta idar da sallahar isha'i ta ɗaga hannunta sama tare da fashewa da kuka ta fara gayawa Ubangiji halin da take ciki tare da rokonsa ya kawo mata mafita, sannan ta shafa adu'ar hawaye na bin kumatunta, tunowa da tozarcin da take fuskanta a gurin mahaifiyarta yasa ta sake ƙarfafawa kanta guwaiwa, tasan a halin yanzu Allah gatanta Jannat gatanta sannan wannan gidan da take aiki shima gatanta, babban abin da yake damunta bai wuce ace mahaifiyarka wace ta ɗauki cikinka ta jure laulayi da naƙuda da raino amma daga baya ta nuna bata ƙaunarka dama hakan tana faruwa?" Sai da tayi kuka mai isarta kafin ta dafe kanta dake tsananin sara mata, idanunta sunyi jajir ta miƙe tsaye ta cire hijab tare da ninke sallahya ta haye gado bayan ta ajiye su a mazauninsu, Bataji sallamarta ba shigowarta kawai taji cikin masifa take cewa "tashi ki haɗamin tea" Anum ta ɗago jajayen idanunta da sam bata wani iya buɗesu sosai saboda tsabar ciwo da kanta yakeyi mata har wani duhu take gani, kafin ta riƙe kan nata sanan tace "dan Allah kuyi haƙuri Kinga yanzu ina fama da ciwon kai ne, akwai ruwan zafi a flaks ɗazu Hajiya ta sani na dafa harda su na'ana a ciki" Jumayma dake tsaye ta riƙe ƙugu tace "ke kalleni ubanwa kike gayawa haka? ta sake yin maganar cikin ɗaga murya, "Nace ubanwa kike gayawa haka, dama Hutu kikazo yi? gida babu AC da lallausar katifa ko? to bazan je in haɗa da kaina ba, idan bazakije ki haɗamin ba ki barshi tunda ni kina ganin damata zan isar da saƙon ga Dad" Anum ta miƙe jiki karkarwa kafin ta dafe kanta ta raɓa ta gefen Jumayma ta wuce, koda ta shiga kitchen ɗin, dole sai da ta sake ɗora wani ruwan shayin sbda flaks ɗin ma baya kitchen, tana cikin dafawa tana tunani, ruwan yana tafasa ta tsumbula hannu, da sauri ta cire tare da matsar ƙwalla tana yarfe hannu, Ta juye a cup kenan Jannat ta shigo tana ce mata, "idan kin gama dafawa ki shanye time ɗin barcina yayi" Tana faɗar haka ta juya tabar gurin. Zuciyar Anum na yi mata ƙuna, ta jingina da bango tare da ƙarewa shayin da ta dafa ta juyeshi a cup kallo, ta jima a tsaye tana kallonsa, daga ƙarshe ta rufe da murfin cup ɗin ta barshi a gurin dan ko kuɗi za'a bata bazata iya kaishi bakinta ba, sai da ta tabbatar da ta kashe komai wanda yake aiki da wutar lantarki kafin ta koma ɗakinta ta turo ƙofa dan bata saka key ba, duk da sanyin AC dake ratsa fatar jikinta bai hanata jin zufa na damuna ba, ta yakice ɗankwalin kanta kanta wanda ya kasance babu gashi irin na maza ya bayyana, sannan ta cire riga da skirt a taƙaice dai tayi zigidir, alamun shigowar da taji za'ayi ne yasa ta....! Afuwan masoya makaranta littafin NISAN KIWO jiya ban samu damar yi muku posting ba kuyi haƙuri. Me kuke tunani shin waye yazo ɗakin Anum sannan a wane hali zai ganta? # Anum # Jumayma #Dad #Little Hajo Waye gwaninku? Kar a manta ayi following ɗina arewabook momislam11 Ga wanda sukeson number wayata ga tan kuyi saving 08141799224 nima kuyimin magana inyi taku sannan zanyi adding ɗinku a group wanda nake posting. Page10 Janyo ƙaton hijabin da Jannat ta bata tayi, cikin sauri ta sanya ta tare da zubawa ƙofa ido, "Anum kinci abinci kuwa naga kamar bakici komai ba" Mom ta tambayeta yayin da take ƙarasowa cikin ɗakin, "Eh naci Hajiya" Anum ta mayar mata da amsar kanta a ƙasa, mom ta ƙarasa shigowa tana cewa "yauwa dama ina son in gargaɗeki game da Dad, gobe insha Allah zai zo ya tambaye ki akan ki koma aiki gidan wansa, gaskiya wanda mugu ne walhi idan kika kuskura kikaje zaki gwammace kiɗa da karatu dan bashi da tausayi, Anum ta ɗago jajayen idanuwanta kafin ta ɗorasu a fuskar mom, a ranta tace "kenan har ya zarce Alhaji a mugunta?" da sauri tace "Hajiya in Allah ya yarda bazan jeba, har mom ta juya zata fice, Anum tace "sai dai Hajiya ina tsoron sake haɗa fuska dashi" Mom tayi murmushi batace mata komai ba ta fice. Har gari ya waye kaf ɗinsu babu wanda yasan anyi sallahar Asbha, sabda basu samu damar yin barci da wuri ba, can tsakar gida tun kafin gari yayi haske ta share ko ina tare da kafa kujera ta zauna, da kaganta zaka san babu lafiya, tana sanye da atamfa ɗinkin riga da zani kasancewar ɗankwalin wadatacce ne yasa ta kafa ɗauri, a zaune take amma hankalinta sam baya jikinta, idanuwanta sun wani juye ita kanta bata san halin da take ciki ba, Ƙarfe 7:am mijin Ummu Auwalu ya fito daga ɗakin Ummu yana hamma, kallo ɗaya tayi masa kana ta kawar da kanta gefe, cikin wata iriyar murya mai sanya wanda ya saurareta shiga ruɗu da tsananin firgici, "Kai Auwalu yalo ina zakaje zo ka fara yin tsallen kwaɗo" mijin Ummu ya zaro ido tare da cewa "ke Arwa kike ko Arshi? in banda fitsara da tacewar rashin kunya ina mijin mahaifiyarki inda kara ai ni mahaifinki ne, amma kike rainani" Yana gama faɗar maganar ya fara tafiya kenan ya sule ya faɗi a gurin timm, Arshi na zaune sam Bama shi take kallo ba, ya miƙe daƙyar zai fara tafiya ya sake jin murya irin ta ɗazu wacce Arshi ɗin tayi masa, "idan har kana son zaman lafiya dole kayi tsallen kwaɗo saboda ka saɓawa Allah, lokaci ya ƙure a safiyar yau aljanu miliyan biyu ne suka je ƙasar Makka suka dawo kai kana barcin asara, tunda yaji ance Aljanu ai ya fice da uban gudu ko takalmi babu, yana gudun yana cewa "wlhi gamo nayi jama'a ku taimaka min nayi gamo da mutanen ɓoye" Yayi gudu wanda idan da kuɗi zai bawa mai Adai-daita sai ya biya ɗari da hamsin in few minutes yayi tafiyar da bai san yayita ba, dai-dai shagon abokinsa ya yada zango, tunda ya hangoshi a furgice ya fito a shagon nasa cikin tuhuma yake cewa "Auwalu mai ya faru, kai da ya kamata ace kana gida gurin amaryarka?" "Wace amarya ina cikin gararin rayuwa, tun daga gida nake ta tafiya da uban gudu na rasa inda zan dosa ne kawai nayo nan" "Kardai kace min baka da kuɗin mashin?" "A'a Hayatu inada kuɗi wlhi masifa ce ta koroni" Hayatu mai shago ya kamo hannun Auwalu suka shiga shagon nasa, ya ƙarewa Auwalu kallo kafin yace "tabbas fuskarka ta nuna alamun kana cikin tashin hankali amma bani labari meye matsalar?" Auwalu ya numfasa kafin yace "wato yarinyar matar da na aura gidan Aljanu gareta dan har cewa takeyi wai aljanu miliyan ne sukaje inane ma tace" kai koma dai menene wlhi yau idan na koma gida dole ta zaɓi ɗaya, ko zama dani ko tasan inda zatayi da wannan ƴar Tata mai ruwan Aljanu" Hayatu mai shago ya tuntsure da dariya tare da buga tebur kana yace "wato kace Allah ya haɗaka da ƙarfen ƙafa, ni tunda Allah ya haɗa aurena da Zainabu lutiya wlhi na kasa tsinana abin arziƙi, na rasa ya akeyi ko nayi ciniki a shago sai na tattaro kuɗin na kawo mata wannan ja'iba tayi yawa, kai Auwalu Gara kai sau dubu" Hayatu ya ƙare maganar cikin jimami da tausayin kansa, Tunowa da maganar sallah yasa shi cewa "Hayatu ko sallah banyi ba, nikam na shiga uku" Hayatu ya zaro ido tare da kallon Auwalu kafin yace "yanzu ai lokacin yin sallahar walha ne" Auwalu ya miƙe tare da wucewa inda butoci suke ya ɗauka tare da nufar banɗakin dake raɓe da shagon, sai da yayi alwalah kana ya dawo shagon ya karɓi sallahya kana ya kabbara sallah, koda ya idar bai tashi a gurin ba, ya daɗe yana zaune har gyangyaɗi ya fara, Hayatu ya taɓoshi tare da cewa "mutumina ya kamata ka koma gida fa" "Eh wlhi kam dan ko Abin karin kumallo ban bar musu ba" Auwalu ya faɗa yana shafa kansa, zai sake magana wayarsa tayi ringing, ya zura hannunsa a aljihu ya Ciro wayar tare da duba waye mai kiran nasa, ganin sunan Ummu yasa shi ɗagawa da sauri "Alhajin Allah lafiya kuwa daga zuwa yin alwalah har yanzu baka dawo ba?" Ummu tai maganar tana sake danna saƙata a ɗakinta dan Arshi ta kafa ta tsare wai sai dai Ummu ta haura ta katanga ta kawo mata Anum, Tunda Ummu taji haka ta danna saƙata a ƙofa dama lekowa tayi, kiran Auwalu da tayi neman agaji take dan idan Aljanun Arshi suka tashi ko gangar cochi albarka gurin dokuwa, Har yanzu tana nan zaune a tsakar gidan, hannunta riƙe da shimfiɗeɗiyar bulala sai karkaɗa ƙafafu takeyi. Iya nera Ɗari ne a aljihunsa, da ƙafa ya dawo daga shagon Hayatu, amma ya ciyo bashin Madara ƴar ɗari da milo, ya biya gurin mai ƙosai ya siyo na ɗari, a ƙafa ya dawo gida, yana tafe yana cewa "ina tunanin akwai ragowar sugan jiya da bredi ya ishemu shan shayi, Yana tafe yana lissafin kuɗin abincin rana har Allah ya kawoshi ƙofar gidan, sai da ya gyara wuyan rigarsa sannan ya shigo gidan da sallama, kafin ya ƙarasa shiga gidan ya ciro wayarsa dake ruri a aljihu ya kara a kunne, yana tafe yana waya, cikin rashin tsammani yaji saukar bulala a bayansa, ware idanu ya shiga yi ko zai ga wanda yai hakan, tana zaune ta hakimce akan kujera gashi shi kuma yana tsaye a ƙofar ɗakin Ummu, ita kuma tana zaune a saitin ƙofar ɗakinta dan tana kallonsa duk da tsakaninsa da inda take zaune akwai rata, "bani abinda ke hannunka" Arshi ta faɗa cikin wata iriyar murya wacce tayi daban da ta ɗazu a taƙaice ma Muryar tafi kamanni da na jarirai, hankali a tashe jikinsa na rawa ya miƙa mata, ta miƙe tsaye tare da ajiye ƙosan akan kujera, yana tsaye yana kallonta ta zazzage madara da milo akan ƙosan kana ta koma ta zauna tare da nunashi da bulala, tsananin tsoro ya sanyashi sakin fitsari cikin daga murya yace "dan Allah Hajiya ki buɗe ina cikin gararin rayuwa" Ummu dake manne a jikin ƙofa tace "aiko idan baka koma inda ta fito ba, zuwa anjima sai ka sauya kamanni" Auwalu ya zame a gurin babu numfashi, bayan ta gama cin ƙosan ta koma ɗakinta tana kwashewa da dariya, ta window Ummu ta ɗan leƙo tare da yaye labule, ganin ba kowa yasa ta leƙa Auwalu ko ya tafi, ga mamakinta sai taji gurnanin mutum, sosai ta tsorata ta buɗe ƙofa, tare da tahowa gurinsa da gudu, cikin Muryar kuka take cewa "dan Allah ka tashi karka mutu na roƙeka, tana maganar hawaye nabin kumatunta, atishawar Arshi da taji ne yasa ta yin hamdala tasan mutanen kan nata sun tafi, cikin ɗaga murya tace "Arshi dan Allah kizo Kinga abinda kika janyomin ko?" Arshi ta fito a ɗakinta tana mutsike ido, "menayi?" Arshi ta tambaya dan bata ma san tayi ba, "Insha Allah yau ɗinnan zamu tafi gidan magani ko kinƙi ko kinso wlhi wataran kashemu aljanunki zasuyi" Arshi ta taɓe baki, kafin tace "Ummu nifa ban gane abinda kike nufi ba, wane aljanu?" Ummu ta harareta kana tace "bani ruwa a buta" Arshi ta kawo mata, ta yayyafawa Auwalu ya mike zumbur tana cewa "wlhi dole a cikin biyu ayi ɗaya" Ummu ta riƙe baki tare da fara jera masa sannu, Arshi ma sannu tayi masa ya watsa mata harara tare da kawar da kai gefe, a fusace ya wuce ɗakin Ummu cike da masifa yafara magana "Na dai gaya miki, yaufa kwana ɗaya da auranmu har mun fara fuskantar masifu nikam bazan iya zama da wannan yarinyar ba, kisan nayi da ita" yai maganar in seriously" Cikin firgici Ummu tace "Auwalu ita kenan min fa ina kakeso in kaita?" "Akwai wani abokina da matarsa take gallaza masa, tanayin Tuwon siyarwa ni bance tayi tallah ba, ko aikin abincin ta dinga tayata amma bazata dinga kwana mana a gida ba" Har yanzu Ummu bata aminta da shawarsa ba, suna tsaka da magana akayo sallama, Ummu na daga ɗaki ta amsa sallamar tare da mikewa ta fito, Anty Hadiza ta gani a tsaye, Ummu ta washe baki tare da cewa "oyoyo mutuniyar kirki jiya na gama maganarki shiga nan ina zuwa" Anty Hadiza tai sallama a ɗakin Arshi, Arshi ta amsa tare da washe baki, Anty Hadiza tace "Masha Allah Arshi anata girma ina Anum?" "Tayi tafiya" Arshi ta faɗa a takaice. Ummu ko na can ɗaki Auwalu nayi maga gargaɗin Arshi, Ummu tace masa "idan muka dai-daita da Hadiza sai su tafi tare amma bazan iya bada Arshi zuwa aikatau ba" Ummu ta fito tana cewa "Hadiza kiyi haƙuri gani nan zuwa" Ummu ta shigo suka gaisa Hadiza take tambayarta ya bayan rabuwa? Hadiza tace "uhm ni Bama wannan ya kawoni ba, labari naji ashe bayan tafiyarmu ƙasar waje kin karɓi key na gidanmu kin shiga ciki, to wlhi Alhaji yayi ajiyar kuɗi a lokar bedroom ɗinsa dubu ɗari bakwai an nemi dubu hamsin an rasa, kuma mutanen anguwa sunce babu wanda ya shiga gidan idan ba ke ba, dan haka ki fito masa da kuɗinsa, bari kiji recording ɗin maganarsa da nayi. "Idan bata bata baki kuɗin ba, kice hukuma ce zata rabani da ita, idan bata taɓa kwana a bayan kanta ba yau zataje ko kaffara bazanyi ba sai ta biyani kuɗina" Ummu ta waro ido tare da kallon wayar Anty Hadiza kafin tace"wato ya mayar dani ɓarauniya ko? Ubanme zanci da kuɗin wani ba nawa ba, to ko sisi ban gani ba bare in taɓa, na ɗauka zancen arziƙi ne ya kawoki ashe sharri kikazo ki laƙaba min" Hadiza ta mike cike da rashin mutunci, kafin ta nuna Ummu da yatsa tace "zaki amsa kira a station ki jira dawowata" Hadiza ta ɗauki jakarta ta wuce fuuuu tabar ɗakin. Hadiza na fita Arshi ta kalli Ummu kafin tace "Ummu idan kece kika ɗaukar musu kuɗi kiyi gaggawar basu dan nashiga ban ɗauka ba bata fidda ɓarawo, Ummu ta zaro ido kana tace "dan ubanki kema zargina kikeyi? daga naje shan AC da fanka shine abin zargi?" Ummu ta ƙarashe maganar kamar zata rufe Arshi da duka, "babu abinda suka isa suyi wanda Allah beyishi ba, ina nan daram babu inda zani" Ummu tai maganar tana shewa, Auwalu da ya shiga wanka ya fito yana sanye da jallabiya ya buɗe labulen ɗakin Arshi sai da ya karewa Arshi ɗin kallo yaga idanun nata ba irin na ɗazu ba, sannan yace "wai meke faruwa ne? Cikin masifa Ummu tace "yo Kai kuma meye naka banda gulma da tsegumi me kazo ji....! Page11 Ina miƙa saƙon godiyata ga masoyana jiki Alhmdulilah Nagode sosai. "Allah ya baki haƙuri naji kamar cewa akayi kuɗi ya ɓata" Auwalu ya faɗa yana juyawa zuwa ɗakin Ummu, "Da ka tsaya mana, in banda gulma da kinibibi mitsw" Ummu tai tsaki tare da washe baki kamar ba itace ta gama masifa ba, "Arshi dan Allah ki amince da zuwa gidan Hadiza kwata-kwata aikin da zakiyi na wata biyu ne, Kinga an biyasu dubu hamsin ɗinsu kafin su miƙamu ga hukuma, gara muyi komai cikin rufin asiri" "Ummu naji zanje amma da sharaɗin dole Anum ta dawo gidannan" Arshi ta faɗa tana jinjina kai alamar maganar fa da gaske take yi, Jikin Ummu na rawa tace "indai Anum ce kamar ta dawo an gama nayi miki alƙawari kedai kawai ki shirya ranar da zaki dawo ranar zansa Jannat ta kawo Anum ɗin" Arshi ta janyo jakar kayanta ta fara zaɓar wanda zataje dashi gidan anty Hadiza, wata ƴar ƙaramar jaka ta ɗauka wacce zata ci kaya kamar kala goma, sannan ta zuge zip ɗin bayan ta gama shiryawa, tana daga tsaye tace "Ummu yunwa nake ji ƙarfe 10:am ko karin kumallo banyi ba" "Yo nima me nasa a bakina? ya fice tun tuni ya dawo hannu rabbana" Cikin ɗaga murya Ummu tace "Auwalu ina abin karyarwar da kace zaka kawo?" Yana leƙowa ta labule sukayi ido biyu da Arshi yaga idanunta na bashi tsoro cikin rawar murya yace "naajeee...najeee" Ummu ta fito a ɗakin tare da riƙe ƙugu kafin tace "turr da wannan rayuwa tun ba'aje ko ina ba ciyar dani yana neman gagarar ka? To wlhi ko kaƙi ko kaso sana'a zan kama yi wacce zan tsira da mutunci na" Gabaki ɗaya bakinsa ya rufe kamar an ɗaureshi sam ya kasa bata amsa kwata-kwata, sai kallonta da yake yi, a cikin ransa kuma mamakin maganganun da ta gaggaya masa yakeyi, Ummu ta kunto bakin zaninta ta miƙawa Arshi ɗari biyar, kana tace "ki siyo mana katin Mtn na ɗari sannan ki karɓo kamu na ɗari suga na ɗari sai ƙosai shima na ɗari, yanzu zan haɗa gawayi insa ruwa kafin ki dawo Arshi kiyi sauri" Ummu ta faɗa tana harar Auwalu. Hijab ɗinta ta ɗauka ta fice, kai tsaye ta sissiyo abubuwan da Ummu ta gaya mata, bata wani jima ba ta dawo lokacin wutar ta kama har Ummu ta ɗora ƴar tukunya, "Ɗauko wayata a ɗaki kisa katinnan zan kirawo Hadiza yanzu" Ummu ta faɗa tana yiwa Arshi nuni da hannu. Bayan ta sanya katin ta miƙawa Ummu tare da danna number Anty Hadiza, Ringing ɗaya zuwa biyu ta ɗaga kasancewar tanada number Ummu, "Nace ga Arshi nan zata zo tayi miki aiki na wata biyu a madadin kuɗinku ayi haƙuri nidai ba ni na ɗauki wannan kudi da ake zargina dashi ba, ko da yake nashiga ban ɗauka ba ai bata fidda ɓarawo" Ummu ta faɗa tana karyar da murya, Sai da Hadizan ta ɗau tsawon lokaci kafin tace "wlhi kin taimaki kanki, gashi nan breakfast yakeyi na shigo na sameshi ya gama shiryawa barin gaya masa abinda yace sai ki shirya" ta katse kiran. Alhaji Kasim kenan, babban ɗan kasuwa wanda duniya tasan da zamansa, ba a iya nan ya tsaya ba, kasuwanci har a ƙasashen Turai yana taɓawa, ya kawo kayan su Nigeria sannan ya ɗibi na Nigeria wanda sukeso ya kai musu, Zaune yake a saman lallausar kujara mai zaman mutum biyu, Anty Hadiza tana gefensa, cike da nuna kulawa tace "Yaya maganar ɗazu ce da ka turani gidan matar nan da tazo ta tare mana a gida bayan tafiyarmu London, tace wai yanzu zata turo yarinyarta.." Alhaji Kasim ya dakatar da ita, kafin yace"zata turo yarinyarta me zatayi mana?" "Aiki a madadin kuɗin nikuma na nuna amincewata tunda basu da halin nemo kuɗin bare su biya" Anty Hadiza ta faɗa tana shafo gemunsa. "Shikenan amman dai kinsan bana son hayaniya ko, idan har zata kiyaye ace mata tazo" Sai da anty Hadiza tayi masa kiss kafin ta danna number Ummu tace "arshi ɗin tazo" Ummu tace tana nan tahowa, Sai da Arshi ɗan tayi karin kumallo kafin ta sake wanka dan gwana ce ta fannin tsafta kana ta sanya hijab sannan ta fito hannunta riƙe da jaka tace "Ummu na tafi" "Ummu na ɗora ruwan wanka tace "ai ban baki kuɗin Adai-daita ba, dan Allah Arshi karki nuna musu halinki daga kinji ranki ya ɓaci ki ambaci sunan Allah ki samu ki kammala wannan aikin cikin kwanciyar hankali arshi ki taimakeni kinji?" Gyaɗa kai tayi tare da karɓar ɗari biyu da Ummu ta miƙa mata kana ta fice, dama Auwalu yana laɓe a banɗaki, burinsa bai wuce yaga Arshi tabar gidan ba, yana tsananin son Ummu bayajin zai iya rabuwa da ita, komi wulaƙancin da zatayi masa, duk da dai ba wata ƙwaƙwarar sana'a bace dashi ba, amma yasan a hakan zasu dinga rufawa juna asiri. Da sauri ya ajiye buta ya shige ɗakin Ummu sbda bata waje ta shige ciki, tana tsaye tayi ɗaurin ƙirji ya ƙaraso da fara'arsa, "Hajiyata a taimakeni a bani haƙƙina, da tunaninki na wuni yau" Auwalu ya faɗa yana wani sake matsowa kusa da ita, sai da ta harareshi kafin tace "yunwa nake ji kasan kuwa babu abinda zan iya taɓukawa" Ya zaro idanu, shidai yaji ta bada kuɗi a siyo kamu amma baiga inda sukayi dashi ba, daga ita har Arshi ɗin, saboda kar ya sake taso da wata masifar yasa shi cewa"dan Allah ko sau ɗaya ki bari inyi wlhi zan samo miki abinci haba me amfanin nemana idan ban ciyar da hajiyata ba" Auwalu na rungume da Ummu ta rage murya kafin tace, "idan ka amince zan fara siyarda maganin maza kanayi min tallah, kaga ribar sai mu dinga rabawa nikuma ina siyar da maganin mata" Ido waje yake kallonta, yayin da yaji abun wani banbarakwai babu daɗin ji, "haba hajiyata kamar ni da girmana da mutuncina da ƙimata a ganni ina tallan maganin maza ai zance ya ɓaci ina banzan iya ba" Ummu ta riƙe ƙugu tana matsar da jikinta a nasa tace "aiko cefane safe da rana da dare ya zamo maka farillah aure kwana ɗaya?" Koda Arshi ta fita bata wani sha wahala ba gurin samun abin hawa, kai tsaye anguwarsu Anty Hadiza aka wuce da ita, suna isowa ta mikawa mai Adai-daita kuɗinsa sannan ta fara nocking a jikin get ɗin gidan, mai gadi ya buɗe mata yana washe baki, kasancewar ya santa dan Ummu tana yawan aikosu gidan yawancin zuwan nasu ma roƙo yafi yawa, bayan sun gaisa ta shige ciki. Koda ta iso bakin ƙofar shiga parlon nan ma nocking tayi, da kansa yazo ya buɗe mata kasancewar yana kusa da bakin ƙofa. Har ƙasa ta durƙusa ta gaishe shi, ya amsa fuska ba yabo babu fallasa kana yace "kece Arshi?" "Eh tace masa tana murmushi, yayi mata izinin shiga, koda ta shiga a ƙasa kan carpet ta zauna tare da takure ƴan ƙafafunta ta ɗaga kanta sama idanuwanta suka sauka kan tafkeken Tv dake ta aiki, "Sanu da zuwa Arshi da fatan Ummu tayi miki bayanin abinda zakiyi?" "Eh tace tare da sunkuyar da kai ƙasa" "Okay shara wanke-wanke wanke toilet gyaran ɗaki parlo ɗakin yaya da kitchen da girki" Gaban Arshi sai da ya faɗi, ita kam tunda take a gida bata taɓa wani haɗawa kanta aiyuka sosai ba. "Banji kince komai ba, mahaifiyarki ce ta ja miki" Da sauri Arshi ta kalli anty Hadiza kafin ta cije lip ɗinta na ƙasa, cikin takaici. Shigowar Alhaji Kasim ne yasa Anty Hadiza mikewa taje ta rungumeshi a gaban Arshi, sai wani mannata yakeyi a jikinsa a haka suka wuce bedroom suka barta a parlo, Kallon agogo tayi ƙarfe 12:pm zaman ya isheta ta miƙe tsaye tana ƙarewa frame na photon su Alhaji Kasim da Anty Hadiza sunyi kyau sosai, bayan wasu mintuna time ɗin ta dawo ta zauna, anty Hadiza ta fito sanye da ƙananun kaya, kana ta jefawa Arshi bedsheet cikin gadara tace "ki wanka yanzu, washing machine ɗina ya lalace, hannu zakisa gurinnan da yayi farin abu ki dirjeshi" Babu musu ta mike tsaye tare da rungume zanin gadon a jikinta, sam bata san meye a jiki ba, ko da anty Hadizan ta nuna mata gurin yin wankin ta barta a gurin, kai tsaye ta nufi gurin akwai omo da sabulu da bucket, ta tari ruwa a famfo kana ta zuba omo, tana ɗago bedsheet ɗin taga wani irin farin Ruwa kwance a bedsheet ɗin, cikin ƙyanƙyami ta ɗauko tsintsiyar shara ta wanke kana ta sakashi a bucket ta sake wankewa, sannan ta ɗauraye ta shanya, har ta dawo parlon ƙyanƙyamin kanta takeyi, ƙarfe 1:pm Any Hadiza tace ta shiga kitchen, "me za a dafa?" kanki zaki dafa" anty Hadiza ta faɗa tana daga ɗaki, Arshi taji zafin maganar amma sai ta basar ta shige kitchen ɗin, tunanin abinda zata ɗora ta fara yi, kwatsam shawarar faten tsaki ta faɗo mata, cikin ƙanƙanin lokaci ta haɗa abubuwan buƙata kama daga yakuwa da ƙashi da sauransu, bayan ta kammala taje ta jere musu a dining, sannan ta dawo gurin jakar kayanta dake anan parlo wacce har yanzu ba'a nema mata gurin zama ba, ba wata gwanar cin abinci bace, ta nemi guri ta zauna. A tare suka fito, lokacin har an shiga sallah, ta rakashi har bakin ƙofa ya wuce ita kuma ta dawo ciki, "me kika dafa?" Faten tsaki" Arshi ta faɗa ba tare da fargaba ba saboda ita a ganinta abin marmari ne. "Kutumar bura'uba faten tsaki a gidana sannan a tukunya ta?" Anty Hadiza ta faɗa tana bugar ƙirji, "Gani nayi ai kince in dafa duk abinda..." Kafin takai ƙarshen magana anty Hadiza ta watsa mata Mari, lokaci ɗaya idanuwan Arshi suka sauya launi, duk anty Hadiza bata lura ba sai balbala masifa takeyi, daga bayanta taji anata zuba mata bulala ana dariya da Muryar yara ita kuma Arshi tana tsaye dafe da kumatu, anty Hadiza ta fara ihu tana cewa "haba yaya, kai fa kace ka daina mai yasa zaka dawo da wannan mummunan halin?" Wasu muryoyi guda biyu a tare sukayi magana, "Muguwa daga yau a gidannan zamu dinga kwana tare dake" Ta kwasa a guje tare da nufar ƙofar bedroom taji a rufe, ta duba kitchen nanma a rufe, sannan ta je buɗe ƙofar bedroom na Alhaji Kasim nan ma a rufe, cikin kiɗima tace "wai shin mutum ko aljan?" Kafin a bata amsa aka sake zula mata bulala ta durƙushe a gurin, tashi ɗaya jikinta ya hau ƙaiƙayi, ta fara ihu tare da fara cire kayan jikinta cikin gaggawa tana cewa "ke Arshi dan ubanki bazaki taimaka min ba, har yanzu bata lura da yanayin Arshi ɗin ba, kan kace me tayi zigidir daga ita sai pant sai rawa take tana ihu tana cewa asosa a durje idan an gama asamin kaya, sai ihu take, daga ƙarshe tai saurin zuwa gurin Arshi tana shirin wanka mata Mari hannunta ya maƙale, dai dai lokacin Alhaji Kasim ya turo ƙofar parlo, hankali a tashe ya ƙaraso Anty Hadiza taje da gudu ta rungume shi, hhh ta kuwa shafa masa rabonsa, dan shima sai da yayi zigidir sai sama yake yana ƙasa, Arshi ta mike jiki a sanyaye dan abin ya fara sakinta ta ɗauki remote ta kunna musu waƙa kana ta barsu a gurin...! [11/1, 9:28 PM] Mom Islam 🍹💋: *NISAN KIWO❄️* Page 12 Mom Islam Cikin zafin rai Anty Hadiza ta kalli Alhaji Kasim kafin ta kalli jikinta sannan tace "yaya banda zubar da girma a gaban ƴar cikinka kake rawa?" Sai da ya harareta lokacin ƙaiƙayin ya ɗan sakeshi kafin yace "har na kaiki da kikayi zigidir a gabanta?" Tsaki taja mtsew tare da barin parlon ta wuce hanyar bedroom ɗinta, anan ta samu Arshi a zaune ta takure ta rusa tagumi, "ke ƙaramar makira uban me ya kawoki nan?" "Baki nunamin ɗakin da zan zauna ba kuma sanyi nakeji" Arshi ta faɗa haƙoranta na kaɗawa. Anty Hadiza tai fatali da ƙafarta tare da tura door na bedroom ɗinta, tasa ƙafa ɗaya zata sanya ta biyu kawai ta sule suuuu, ƙafarta ɗaya a gaba ɗaya a baya, ta kurma ihu tana cewa "Arshi kiramin yaya dan Allah zan mutu ƙila ma karyewa nayi" Arshi na zaune a inda anty Hadiza ta barta tsabar kaɗuwa da jikinta keyi, sai samun guri tayi ta kwanta sai wani irin numfarfashi takeyi, Alhaji Kasim ya taho da rigarsa a kafaɗa, sam bai lura da tana kwance a tsakankanin ƙofarsa da ta anty Hadiza ba, jin ƙafarsa ta dunguri abu yasa shi ja da baya, kafin ya ƙarewa Arshi kallo, sannan yace "ke mai ya kawoki nan?" ta kasa bashi amsa sai riƙe kanta da takeyi sbda zazzaɓi ya dirar mata tashi ɗaya, har zai tsuguna yaji ihun anty Hadiza tana cewa "yaya idan ma a gurin wannan yarinyar kake wlhi ka gaggauta kaucewa dan aljana ce ba mutum ba" Alhaji Kasim ya zaro ido, ya fara tafiya da baya da baya har sai da ya fito parlo, da ƙyar anty Hadiza ta samu ta rarrafo zuwa bakin ƙofa, ga mamakinta sai taga kamar idanunta gizo sukeyi mata da abinda suka gane mata, tsantsar tsoro ya bayyana a zuciyarta da idanuwanta, da sauri ta cigaba da jan ɗuwawu ta koma ciki, anan cikin ma ƙarar wacce take kama da na guguwa ne ya kewayeta, cikin ɗaga murya take cewa "wa innahu sulaimanu wa innahu jafaru, sai maimaitawa takeyi tana sake ja da baya, ita dai Arshi tana mugun bata tsoro dan fuskarta ta fara gani, bayan Arshi ɗin na kwance a ƙofar ɗaki, tashi ɗaya taji abun kamar anyi ruwa an ɗauke, cikin sauri ta miƙe dan ƙafafun sunyi mata dama dama, ta tako a hankali gabanta na ci gaba da faɗuwa, a tsorace ta tsallake Arshi ta wuce, dan a cewarta ta daina kulata tunda ta zamo musu masifa, koda ta fito parlo babu Alhaji babu alamarsa, ɗan zanin da ta samu ta ɗaure ƙirjinta ta gyara kafin ta fito harabar gidan taga babu motar da yake fita da ita, cikin ɗaga murya tace "mai gadi Alhaji ya fita ne?" "Eh ya fita yanzu ma kuwa?" Tai ƙwafa tare da komawa ciki. ****** Yau kwananta uku da barin gida, bayan fitar mom daga gurinta bata sake shigowa ba, sai dai suna haɗuwa a kitchen suyi aiki sannan kuma tana zuwa gaishe ta duk safiya, alhamdulilah taji sauƙin ƙuncin da take ciki, babbar damuwarta ranar da suka gane halittarta ta fita daban da tasu, 6:am tana tsaye gaban mirror tana sake aske kewayen bakinta inda gashi ke fitowa, duk da yiwa ƙofar key da tayi, tsananin tsoro ya matuƙar baiyyana a zuciyarta, hankali a tashe take gyara gemun nata, bayan ta gama ta gyara gurin ta gogo sannan ta shiga toilet ta tara ruwa ta cire kayan jikinta kana ta fara shirin yin wanka, babban abin tsoron bai wuce mantawa da ɗankwalinta da tayi a parlo ba, gashi ta cire kaya. Tana cikin tunani aka turo ƙofa tunda ta waje ma akwai extra key guda ɗaya, muryar Little Hajo ne ya bugi dodon kunnenta, ƴar aiki kizo inji anty Jumayma" bata bata amsa ba, taci gaba da wankanta, har ta kammala, tana tsugune aka turo ƙofar toilet da sauri ta matse ƙafafunta tare da runtse idanu cikin sigar lallashi tace "Hajo dan Allah ki rufeni zansa kaya" cikin ɗaga murya Hajo tace "mai kan maza" Anum ta mike da sauri tare da sanya hannu a baki alamar little Hajo tayi shiru, itako Hajo tayi ido biyu da gaban Anum ta zube a gurin sumammiya hankali a tashe Anum tayo parlo sai da ta zura doguwar rigar atamfa tare da ɗaura ƙaton ɗankwali kafin tazo gurin little Hajo dake kwance rai a hannun Allah, jin horn na motar dad yasa Anum jingina da bango tare da ƙaddarawa kanta kwananta ya riga da ya ƙare dan idan ya shigo ya samu Hajo a wannan halin tama gama yanke wa kanta hukuncin kasheta zaiyi. THAILAND A satinnan suke da niyar kammala duk wani shiri da ya shafi Leeela domin kuwa Monir ya samo musu mafita harma da shigar da ta dace suyi, yau kwanan Anan biyu kenan da zuwa gidansu Arya sun saba da granny sosai kai kace sun shekara, a ƴan kwanakin nan Arya sam bata cikin walwalah damuwarta da burinta shine ta ganta gata ga Khair, Washe gari. Ƙarfe 2:pm Monir yazo gidansu, dukkansu suka taru a parlo yana yi musu example na inda abin zai kasance, Anan ta ɗaga hannu sama tare da cewa "ya kamata kafin mu shigar masa mu sami wani na hannun damarsa ina ganin abin zai fi ko, amma shawara ce" Monir ya zuba mata idanu, kafin yace "komai cikin sirri ake yinsa Babu buƙatar wani sai yaji" yai maganar in seriously. "Okay tom shikenan" Arya ta faɗa hannunta na riƙe da biro da wata ƙatuwar takarda, cikin nutsuwa ta fara zane wanda take yinsa cikin ilimi da ƙwarewa, "a shawarar da ka yanke kace ni zan fito a matsayin wawuya ko? ita kuma Anan a matsayin gurguwa" eh hakane ta hakane zaku samu duk wasu muhimman abubuwa, yai maganar yana miƙewa tsaye. Jikin Granny a sanyaye tace "Ubangiji ya bada Sa'a nikam zuciyata ta mugun tsinkewa amma nasan da izinin Ubangiji akwai Sa'a a tare daku" Monir ya mike tare da gyara zaman jakar hannunsa, kana yace "ni zan wuce kuyi ƙoƙari ku cimma nasara kunji" Dunkansu suka gyaɗa kai alamar "toh" Granny ta rakashi har parking space inda motarsa take sukayi sallama ya wuce. Har Arya ta miƙe Anan ma ta miƙe tsaye kafin tace "zan ɗan fita zuwa out ko akwai abinda kike buƙata?" Arya ta girgiza kai, kana takai biro bakinta, tana kallo Anan ta fice zuciyarta cike da waswasi. Lokacin da Anan ta fito Granny ta koma ɗaki, dan haka ta samu damar ficewa kai tsaye. Tana tafe tana waigen bayanta har ta iso bakin get, juyowar da zatayi suka haɗa ido da Arya, cikin zafin rai ta ƙarasa gurinta tare da kallon ƙwayar idanunta kafin tace "kodai akwai wata matsalar ne?" Anan tai saurin girgiza kai tare da daburburcewa tace "inaa so..son.." Arya tayi murmushi kafin ta sake matsowa inda take kana tace "karki damu sis ki faɗi abinda kikeson faɗa Kinga time ɗin la'asar yayi muje muyi sallah sai in rakaki ki siyo" Ba haka taso ba gudun kar Arya ta fahimci wani abu yasa tace "toh muje" Suna shigowa ana kiran sallahar la'asar Arya ta shiga tayi alwalah, tace Anan taje tayi alwalah, jiki a sanyaye ta nufi hanyar toilet tare da shigewa ta matsa jikin bango tare da jingina kanta, a zuciyarta tana cewa "itafa wannan sallahar da takeyi bazata iya aikin wahala ba, sai ta jiƙa fuska sannan tazo ta dungura goshi a ƙasa gaskiya aikin yayi yawa, "Anan lafiya kuwa na jiki shiru har yanzu baki fito ba?" Arya ta faɗa lokacin da take ƙarasawa gaban mirror tana sake gyara fuskarta, "Zan fito yanzu" Anan ɗin tace tana tsaye dan ta ma mance inda Arya tayi alwalah har ta kwaikwaya tayi, cikin sauri ta ɗan dangwalo ruwa ta shafa a fuskarta kana ta shafa a ƙafarta da hannu, sannan ta fito tana ɗan gyara gashin kanta da suka zubo, Arya tana zaune gaban mirror ta hangota ta fito, cikin zolaya tace "Anan kodai kema cikinki ya rikice ne irin na Granny?" Anan tayi murmushi dan ita kaɗai tasan halin da take ciki, sbda a halin yanzu tunaninta taya zatayi sallah Arya tana zaune a gurin, tana ta tsaye har sai da Arya tace "ki ɗauki sallahya mana ga hijab nan a gurin" jiki a sanyaye ta isa gurin sallahyar tare da sanya hijab ɗin ta kalli yamma, sbda ta mance a yaya tayi jiya, daga cikin mirror Arya take kallonta "ba nan zaki kalla ba, a tunanina kin riga da kinsan gabas naga kinyi sallah shekaranjiya da jiya" Anan ta dafe ƙirji zatayi magana Granny ta shigo, sai da ta ƙare musu kallo kafin tace "yanzu mukayi waya da Khair ammafa yana cikin mawuyacin hali dan muryarsa bata fita sosai anya tafiyar nan ba tare dani zakuyita ba" Arya ta harari Granny tare da ficewa a ɗakin, itama Granny bayanta tabi lokacin da granny ta iso ɗakinta har Arya ta shige ta ɗauki wayarta tana gwada number Khair, cikin Sa'a ta shiga yana ɗagawa ta fashe da kuka tare da cewa "khair kana cikin ƙoshin lafiya ko? karka damu zanzo in dawo dakai gida insha Allah kayi haƙuri kana raina" "Arya bana cikin kwanciyar hankali rabonmu da abinci tun shekaranjiya tunda muka zo sau ɗaya aka bamu coffee sai ruwa da ake kawo mana koda yaushe, a gigice tace "Khair babu inda zakayi ka gudo?" "Arya da akwai da tuni kin ganni, Aman kam sai dai ku tayashi da adu'a saboda Gara halin da nake ciki..." Wani irin ihu khair ɗin ya tsala wanda yasa Granny da Arya shiga tsananin firgici, tashi ɗaya wayar ta katse, sunbi kiran amma shiru babu alamar zata shiga, Arya ta zube a gurin hawaye na wanke mata fuska, cikin Muryar kuka tace "gobe zamu fara aiki da izinin Ubangiji bazan iya ƙara koda kwana biyu bane ban ceto rayuwar Khair ba, Granny ta dafa kafaɗarta cikin Muryar ƙarfin hali tace "tabbas ke jinin Alee ce, akwai wata sarƙa da zan baki ki ɗaura a ƙafarki da zarar kin shiga gurin hankalin kowa zai ɗauke har ki shiga kiyi abinda zakiyi ki fito, Anan dake raɓe a jikin ƙofar Granny tai saurin ja da baya tare da komawa ɗakin Arya ta zauna saman sallahya tare da mimmiƙe ƙafafunta alamar tayi sallah, tsabar takaici da baƙinciki Arya kwanciya tayi a gadon Granny har lokacin kiran sallahar magriba tayi, Granny kam hankalinta in yayi dubu ya tashi, ta ɗaga hannu sama tana gayawa Ubangiji damuwarta tare da adu'ar Allah ya kawo musu mafita ta Alkairi. Ganin gidan yayi shiru sosai, yasa ta miƙe bayan ta cire hijab ɗin ta shiga toilet ta kunna ƴar ƙaramar wayarta dake silent koda wane lokaci, gurin text message naga ta shiga, ko me take rubutawa oho sai ta tura saƙon sannan ta kashe wayar ta mayar aljihun wandonta na ciki, Da sauri ta fito sai haɗa gumi take alamomin rashin gaskiya suna neman su fara baiyana a kanta, lokaci ɗaya sannan kuma tashi ɗaya, sai kewaye ɗakin take tana haɗe hannayenta guri guda...! Hii fans mai kuke tunanin Anan tana ƙullawa Free pages yana daf da ƙarewa. Littafin NISAN KIWO na kuɗi ne 500 normal group posting sau ɗaya a rana. 1k posting sau biyu a rana har weekend. Account number 3175689751 Zainab habibu first bank shaidar biya tanan👉08141799224 zanyi adding ɗinki a paid group Karku manta Book1&2 Ƴan Niger katin Airtel zaku tura ku ɗauki hotonsa ku turomin ta wannan number 08141799224 Wanda basa da account katin Mtn zaku tura screen shot ki turomin ta numberta 08141799224 Please banda vtu Karfa ki bari ayi tafiyar babu keee💃 Mutanena na facebook da Whatsapp ina miƙo saƙon gaisuwa. [11/3, 7:39 PM] Mom Islam 🍹💋: *NISAN KIWO❄️* Page 13 Mom Islam Masu amfani da arewabook zaku dinga ganin update ammafa idan kukayi following ɗina👇 https://arewabooks.com/u/momislam11 "Anan gobe fa zamuyi tafiyar nan" Arya ta faɗa muryarta a dashe, sbda taci kuka ta godewa Allah. Tun safe suke ɗaki ita da granny da Anan, dan babu wani abu da suka ɓoye mata na game da sirrikansu, har yamma duk suna ta tufka da warwara, Arya tana ta kanta bata sake bi ta kan Anan akan sallah ba, sbda tasan ai ita ba ƙaramar yarinya bace da za'ayita mata bita kullum. Washe gari sun kammala shiri, shigar da sukayi kusan iri ɗaya ce, Pakistan ne na riga da wando pink color wandonsa milk color sai mayafinsa siriri shima milk yasha adon stone masu ɗaukar ido, sosai sukayi kyau gunin birgewa sbda shigar tasu ta amshi jikinsu, ba wani makeup sukayi ba, iya powder da lipstick da suka goga a lips ɗinsu, tunda suka fara shiri jikin Granny yake a sanyaye, ta wani ɓangaren tana ƙarawa kanta ƙwarin guwaiwar tafiyar tasu, Anan kam bata da wasu kaya na canji, dole Arya ta ware mata kala huɗu wanda suka haɗa a tare a bag guda, ba wani abincin kirki sukaci ba, koda yake Gara ma Anan ta cinye wanda Granny ta saka mata, suka miƙe suna yi mata sallama, har parking space ta rakasu, ji take kamar idan suka tafi bazasu dawo ba, "zanyi kewarku" Granny ta faɗa zuciyarta a karye, sam ta kasa samawa kanta sukuni sbda alhinin tafiyar tasu, har suka shiga ƴar madai-daiciyar motar Arya tana tsaye a gurin har suka bar gidan idanunta na hanyar da suka fice, "Allah yasa fitarku da aikin da kuka tunkara ya zamo Alkairi da nasara" Granny ta faɗa take komawa ciki. Hawansu babban titi yasa Anan sake waro idanuwanta tare da ƙarewa hanyoyin da suke bi kallo, sunyi tafiya mai nisan gaske kafin suka iso wata hanya wacce yawancin mutane basu san da zamanta ba, Arya ta matsa zoben dake hannunta get ɗin dake kange a gurin ya buɗe, ta kusa motar ciki suka ci gaba da tafiya, a ƙofa ta ƙarshe ne sai da ta matsa zoben sai uku kafin ta buɗe suka shiga, "welcome to Leela guest house" Abinda sukaga an rubuta kenan, har yanzu Anan tana kallon hanya ko runtse ido batayi. A nesa da hanyar shiga tayi parking, lokacin da ta matsa zobenta lokacinwata babbar ƙofa ta faɗo, Khair da Aman suka fito jikinsu duk jini fuskarsu da bakinsu, cikin sauri Anan ta riƙe hannunsu cikin ɗaga murya take cewa "Arya zan tafi dasu ki taho da mota" Arya tace "babu buƙatar yin magana da ƙarfi Please ki rage sautin muryarki, Lokacin da Anan ta riƙe hannun Khair da Aman aka saki bindiga mai masifar ƙara, wacce ta sauka a kan ƙafar Arya, khair Anan da Aman duka a idanunsu akayi amma babu wanda yai yunƙurin tsayawa taimaka mata sai Aman dake cewa "Khair ƙanwarka ce bai kamata kayi mata haka ba, khair idan kayi haka Kaci amana" Aman yana maganar suna gudu har suka iso gurin mota Anan ta shigar dasu suka ƙarawa motar wuta, "Nasan bakusan koni wacce ba, Ubangiji ya turoni ne domin in taimaka muku bisa ga halin da kuka shiga" gyara zaman sumar kanta tayi wanda ya rufe mata fuska kafin taci gaba da cewa "waye khair a cikinku?" Khair da tunda ta fara magana yake ƙarewa bakinta da hancinta kallo yanajin wani abu na tsirga masa tun daga tsakiyar kansa har zuwa tafin ƙafarsa, a hankali ya nuna kansa tare da share jinin dake cigaba da fito masa a gefen baki, "okay yanzu hospital zan wuce daku akwai wani asibiti da Dadyna yake aiki bazaku samu matsala ba" Tai maganar tana ƙarewa Khair kallo. Driving take cikin ƙwarewa, suna tafe tana yi musu hirar Arya, sam na kasa jiyo me take gaya musu na game da Granny da Arya ɗin, lokaci ɗaya Khair yace "bazamu koma gida ba" Aman yai saurin kallonsa sai kuma ya kawar da kai. Har ta nufi wata hanyar, cikin sauri ta juya akalar motarta a hanyar da zata sadata da hospital, abin ya matuƙar bata tsoro kafin su kai ga shiga cikin asibitin duk babu numfashi a tare dasu, tsananin tsoro da firgici ya dirar mata a zuciya, jiki a sanyaye tai parking inda aka tanada dan ajiyar motoci, hankali a tashe ta fito tare da yaye ɗankwalin dake yane a kanta, ta wurga mota sannan ta tura hannunta cikin aljihun wandonta ta ciro wayarta ta danna wata number, ringing ɗaya zuwa biyu aka ɗaga, murya irin ta wacce ta kiɗima tace "Papa wlhi ina cikin wani hali, Papa nazo da wasu hospital ɗinka Please I need your help Papa" ta ƙarashe maganar tana fashewa da kuka mai tsuma zuciya, A kiɗime Papa yace "ina tiyata room amma ki shigo ciki akwai Amer zanyi masa bayanin komai" Hankali a tashe ta shige ciki da waya a hannunta, cikin Sa'a tayi arba dashi tana shiga, ta cakumeshi hawaye na ambaliya a idanunta tace "bro kayi taimakon ceton rai wlhi idan kace a'a zasu iya mutuwa dan Allah ka kace wani abu" zai yi magana kiran Papa ya shigo wayarsa, bayan ya ɗaga sukayi magana da Papa sannan ya kalli Anan lokacin da yake katse kiran yana sanya wayar a aljihu kafin ya kalli Anan ɗin yace "karki damu duk wasu abubuwa da suka dace zanyi amma akwai wata papper da zaki da hannu" "Babu damuwa kawo" Anan ta faɗa sanya yatsanta manuniya tayi baya da gashin kanta da ya ɗan zubo mata. Yana miƙo mata tasa hannu ta miƙa masa cikin gaggawa aka shigar dasu, Likitoci hudu ne suka haɗu a kansu ko wanne da aikin da yake yi, ita kuma tana can mota ta samu Hankey tana goge inda jini ya ɓata, Har aka gama musu treatment dukkansu basu sani ba, dan har da ɗinki, musamman ma Aman da yafi Khair jin ciwo, Tunda ta shigo cikin asibitin take ta Safa da marwa hankalinta ya matuƙar tashi, babbar damuwarta kar su mutu dan bata burin hakan ko a mafarki, Fitowar Amer yasata isowa gurinsa da gudu tare da riƙe hannunsa tace "bro ya jikin nasu?" "Akwai alamun sauƙi ƙanwata ki kwantar da hankalinki dole suna buƙatar kulawa ta musamman gaskiya a yau kaɗai bazasu farfaɗo ba, zuwa gobe ma bamu da tabbas amma muna bukatarki a office" Ƙirjinta ne ya bada dum dan ko wace irin tambaya sukayi mata bata da amsar da zata basu. Sbda kar ya zargi wani abun yasa tai saurin binsa office ɗin, umarnin mazauni yayi mata kana ya cire farin gilashin dake manne a idonsa, kafin yace "akwai wasu tambayoyi da suka zamo dole ayi miki su" Yai maganar yana kafeta da ido. Sunkuyar da kanta tayi, kafin ta fara kuka, sai kuma ta tsayar da kukan tace "doctor dukkansu yayuna ne, farin shine wanda zan aura ɗayan kuma abokinsa ne, sun haɗu da ƴan fashi shine suka yi musu illah haka mu kanmu bamu san inda suka shiga ba kwana biyu, daga baya aka zubasu a ƙofar gidanmu, nazo fitowa naci karo dasu gashi mahaifiyarmu bata nan shine na sakasu a mota na taho dasu ai nayiwa Papa bayanin komai" Cikin gamsuwa doctor yace "okay Babu damuwa Allah ya daɗa karewa" Ta amsa da cewa "Amin" Sai a lokacin ta samu damar yin ajiyar zuciya mai cike da nuna ta tsira. Ƙarfe 6:pm Papa ya fito yana sanye da kaya na gida, Anan na ganinsa taje da gudu ta rungume shi tana cewa i miss You my Papa" wani irin so da ƙaunarta ne ke ratsa ko ina na jikinsa, yana shafa kanta yace "miss You too my lovely daughter daga tafiya ziyara shikenan, bani labari" Rausayar da kanta tayi tare da cewa "Papa a kula da marasa lafiyar da na kawo zanyi maka bayani soon ta shiga mota tabar gurin. Girgiza kai yayi yana murmushi har motar ta ɓace ma ganinsa, kafin ya koma cikin asibitin. NIGERIA. wani irin murɗawa cikinta keyi mata, yayinda wasu ƴan matan likitoci ke kanta, yarinya ce wanda a ƙalla bazata wuce 18yrs ba, "Maryam kiyi Nishi insha Allah zaki aihu lafiya sannan ki riƙe ƙafar gadonnan da kyau" Sosai wacce suka kira da Maryam ɗin ta haɗa zufa, duk da ƴar madai-daiciyar Fanka dake bada iska daga sama, cikin ikon Allah tayi Nishi mai ƙarfi tare da ambaton sunan Allah, sai ga yaro nan ya fito, bayan nan mahaifa, Mama na gefe a zaune ta rafka tagumi tana ta kallon hidimar da likitocin keyi, jin muryar Amanda mai kaya yasa mama miƙewa zumbur tare da rungumeta, sosai sukayi murna da ganin juna sai washe wa juna baki sukeyi, jiyo kukan jariri yasa Amanda cewa "a ina kika sami yaro kamar ma sabon aihuwa" mama ta kawar da kanta gefe tare da cewa ƴarki ce ta aihu" Amanda ta fatalar da jakar dake rataye a kafaɗarta kafin ta kutsa kai ciki, lokacin har sun gyara boy ɗin an juye ruwan wanka anyi masa, abin mamaki da takaici a towel aka naɗeshi bai samu arziƙin kayan sawa ba, bayan sun gama aikinsu suka miƙawa mama dake zaune ita da Amanda, sannan suka umarci Maryam da ta tashi ta gyara jikinta tunda ta huta, da taimakonsu taje toilet suka gyarata sannan ta fito zuciyarta nayi mata zafi, suma kansu sunyi mamakin rashin kulasu da maman barayi ba, bayan sun kammala mama tace "nawa ne kudin ku?" Sukace 10k, ta ƙirgo ta miƙa musu suka fice suna godiya, ko kallon jaririn mama bata wani yi ba, ta miƙawa Amanda bayan Amanda ta karɓa mama tace "wannan jaririn da kike ganinsa na mallaka miki shi halaka malak gobe insha Allah zamuje ayi masa takardar yarjejeniya tabbas ya zamo naki na cika alƙawari". Jin haka yasa Maryam waro idanu cikin galabaitacciyar murya tace "haba mama ya zakiyi min haka, ke da kanki kikace babu uwar da zata haifi ɗa ta gujeshi shin kina ganin kinyi dai-dai kenan, Anty Amanda fa ba musulma bace akan me zaki bata yarona?" "Kin gama? nace kin gama? bazan san nasiha kikeyi min ba sai kinzo daidai saitin fuskata kin wankamin mari tukunna, Amanda ki kwantar da hankalinki babu wani abu dazai rabaki da yaronnan ki saka masa duk sunan da yai dai-dai da zuciyarki idan har kin amince yanzu ma sai mu wuce ayi takardar" Jikinta na rawa ta janyo hand bag ɗinta tare da ciro kuɗi bandir na dubu ɗai ɗai har biyar ta ajiye a gaban Maryam kana suka fice tana rungume da jaririn, jakarta na kafaɗarta. Tsabar takaici da baƙinciki ko kallon kuɗin Maryam batayi ba, dama jiri take gani a halin yanzu komai ya koma mata sabo, ciwon kai ya dawo tsananin jiri wanda yasa ko gabanta bata kallo duk ya dawo mata, har ta mike tsaye taji sam bazata iya tafiya ba ta durƙushe a gurin idanunta na zubar da zafafan hawaye. Suna tafe a mota Amanda tana rungume da jaririn tana driving wani irin nishaɗi takeji a zuciyarta kuwa tana hasaso inda zata tafiyar da jaririn da take tunanin sunan da zata kaisa coci a sanya masa... Zazzafar cakwakiya biki bidiri anan na kawo ƙarshen Free pages idan kinason ci gaba ga hanyoyin biya nan Littafin NISAN KIWO na kuɗi ne 500 normal group posting sau ɗaya a rana. 1k posting sau biyu a rana har weekend. Account number 3175689751 Zainab habibu first bank shaidar biya tanan👉08141799224 zanyi adding ɗinki a paid group Karku manta Book1&2 Ƴan Niger katin Airtel zaku tura ku ɗauki hotonsa ku turomin ta wannan number 08141799224 Wanda basa da account katin Mtn zaku tura screen shot ki turomin ta numberta 08141799224 Please banda vtu Masu tambayar document ɗinsa suyi haƙuri dan bazanyi document ba idan kinaso ki biya ki karanta👏 Sai mun haɗu a paid group ko a arewabook Karfa ki bari ayi tafiyar babu keee💃 Mutanena na facebook da Whatsapp ina miƙo saƙon gaisuwa. An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels